TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Mugun so page 50

 𝕄𝕌𝔾𝕌ℕ 𝕊𝕆❤️‍🔥


*Written by Fateemah MG


🌸💕🌸💕🌸💕

#Zayn Abideen

#Safeerah♡

#Love

#Romance


               ....ᖴᗩTᗴᗴ ᗰᗩᕼ

ᗩᒪᕼᗩᗰᗪᑌᒪIᒪᒪᗩᕼ_(◕‿◕✿)


🫶🏻💕 

Page 5️⃣0️⃣


_____

A Napep Yusra tayi tsaki tace, "Ni fah shys bana son zuwa gidan Yaya amma kika jawo ni ki kalli abun takaicin da na tarar.." dariyar dole Zaytoona tayi tace, "Gara ki saba ai tunda na kusa shiga gidan kuma wallahi sae ta yaba wa aya zaƙi, kuttt.." cize leɓe tayi ta ma kasa magana duk suna jira su isa gida su feshewa Aunty Luba da Umma labari dan gulmar har cizon su take yi. 


Suna ƙarasawa parlourn Umma suka tarar da Aunty Luba da Umma suna hira dan tunda suka ɗinke suka koma basu da aiki sae gulma da yi da mutane, suna isa Zaytoona ta samu guri ta zauna bbu ko sallama, idanu Umma da Aunty Luba suka bita dashi suna mamakin me yake damun yarinyar nan, can Umma tace, "Luba anya wannan yarinyar bata tareda mutanen ɓoye?" Kallonsu Zaytoona tayi tana turo baki tace, "Ni ƙalau nake" tsaki Umma tayi tace, "Ke Yusra ko basu nan ne?" Taɓe baki tayi tace, "Da muka je basu nan sae daga baya suka dawo daga gurin koyar mota" da sauri Umma ta gyara zama tace, "Koyar mota kuma?" Kai Yusra ta ɗaga nan Zaytoona ta karɓa tace, "Mota Yaya ya siyawa matarsa kuma Mercedes ce" da sauri Umma ta saka hannu ta dafe ƙirjinta daya tsinke tana faɗin, "Innalillahi wa inna ilaihir Rajiun..." idanu Aunty Luba ta zuba mata tace, "Ai duk ke kika ja ace yaro baya jin maganar ki ko kaɗan!" Huci Umma tayi kafin tace, "Ku tashi ku shiga daga ciki.." baki a taɓe dae suka miƙe suka shiga cikin ɗakin Yusra.


"Wallahi yarinyar nan ta mallake miki yaro, duk ta maƙalƙale shi ne" tsuka Umma taja tace, "Ai banyi zaton haka take ba shys banyi komai ba amma..." taɓe baki Aunty Luba tayi tace, "Haka kike cewa ai ko yaushe gashi har yau maganar aurensa da wannan yarinya shiru ai.." shiru Umma tayi tana tunani, taɓo ta Aunty Luba tayi tace, "Sha kuruminki na san wani malami aikinsa kamar yankan wuƙa, ki shirya kawai muje" kai Umma tayi saurin ɗagawa duk da bata taɓa zuwa gurin malami ko boka ba amma gashi ta fara niyyar zuwa, cize leɓe tayi tace, "Wallahi idan ba'a yi auren yarinyar nan da yaron nan ba toh gawa ta ko tasa aka yi wa sallah" murmushi Luba tayi tace, "Kwantar da hankalinki ba sae anje nan ba ma" 


....

Yusra ce ta taɓo Zaytoona dake laɓe da jikin ƙofa tana son ji amma bata ji komai ba, zabura tayi kafin su biyu duka suka koma kan gado suka zauna, kwanciya Zaytoona tayi tana kallon saman ɗakin nan Yusra tace, "Kin dage sae kin auri Yaya" saurin tashi daga kwance tayi tace, "Eh mana, kin san yadda nake sonshi ne kuma wallahi bazan iya haƙura ba" Yusra na jin haka tayi shiru bata sake cewa komai ba inda Zaytoona ta koma gado ta kwanta tana tuno lokacin da yake tambayarta ko mararta zae iya ɗaukarsa, murmushi tayi sannan tayi saurin juyawa Yusra baya. (*Zaki ji jiki ne*🔥🥂)


Washe gari Abideen yasa Safeerah ta shirya suka kama hanyar gidansu, part ɗin Umma suka shiga amma parlourn Abba suka wuce direct, a zaune suka ga Abba, Umma da Hajiya, suna shiga suka durƙusa har ƙasa suka gaishe da duk wainda suke a parlour inda Abba ya amsa gaisuwar Safeerah da, "Lafiya daughter, ya jikin naki?" Murmushi tayi tace, "Naji sauƙi Abba" kallonsa Umma tayi tace, "Bata da lafiya ne?" Kallonta Abba yyi yana mamakin rashin sani da ta nuna bayan suna gari ɗaya, shi da yake wani gari har yaji ita bata sani ba, ajiyar zuciya yyi yace, "Eh!" A haka ya katse maganar amma hakan bae fasa saka zuciyar Umma fara bugu ba tana tunanin ko ciki ne da ita, can da aka gama gaisawa Abba ya kalli Abideen yace, "Babana?" Kai Abideen ya ɗaga yace, "Na'am Abba!" Numfashi Abba ya sauke yace, "Kai ka buƙaci ƙara aure?" Kamar saukar aradu Safeerah taji maganar cikin kunnenta, wani tsorata tayi tareda saurin kafe Abideen da ido, Umma da ke kallonta sae taji wani daɗi ganin bata san da maganar ba, shaf Abideen ya shafa'a bae faɗawa Safeerah ba gashi bae ji daɗin yadda maganar tazo mata ba, Hajiya dake zaune tace, "Ƴan nan ki jira mijin naki a waje kinji ƴar albarka!" Kai Safeerah ta ɗaga kafin ta miƙe ta fice daga parlourn jiki a sanyaye, kowa na kallon yanda Abideen ya juya yana kallon matarsa har ta fice daga parlourn, dawo da kansa yyi kafin yace, "Eh Abba.." nan Abba ya ɗaura da, "Kun shirya da ita yarinta Zaytoonan?" Kai ya ɗaga kafin yace, "Eh Abba.." sosai Umma ke jin daɗin abunda ke faruwa sae farin ciki ya rufeta sosai.


Safeerah na ƙarasawa parlourn Umma ta tarar da Aunty Luba ta kama ƙugu, gaishe da Aunty Luba tayi amma tayi banza da ita sae ma ƙarasowa gabanta da tayi haka nan tace, "Munafuka kawai, aure dae yi bbu fashi Abideen sae ya sake aure!" Kallonta kawai Safeerah tayi bata ce komai ba sae ga Umma ta fito, tana ƙarasowa ta kamo kunnen Safeerah tace, "Munafuka mayya, daga shiga gidan yaro shine har kinbi kin mallakeshi?" Kai Safeerah ta duƙar hawaye na zuba daga idanunta ga zafin kama kunnen da Umma tayi mata, sakin kunnen Umma tayi tace, "Munafuka kuma ki sani auren Abideen da Zaytoona bbu fashi sae dae idan bana numfashi!!" Jin da wacce za'a yi auren ma sae abun ya sake taso mata da sabbin hawaye, Aunty Luba tace, "Munafuka yi kuka, ƴar ƙaramar ki dake amma bbu bokan da baki sani ba ko?" 


Ɗago kai tayi tana jin ƙazafin da ake wurga mata, da ƙarfin gaske Umma ta dungure mata kai wanda yasa ta faɗi har ƙasa kusa da kujera nan Aunty Luba tace, "Faɗa mana gurin wani bokan kike zuwa da har yake yawo da pant ɗinki a motarsa?" Shiru Safeerah tayi tana mamakin abunda Abideen ke yi haka, amma yanzu bashi bane damuwarta, tsaki Umma tayi tace, "Gantalalliya faɗa mana, duk kin mallake yaro ko? Ya siya maki mota ya siya miki waya duk bae ishe ki ba ko? Yanzu kuma mae zae siyan miki?" Dariya Aunty Luba tayi tace, "Toh gidaje nawa ya mallaka miki?" Shiru suka yi suna jiran amsarta amma shiru daga baya Umma tace, "Mayya ko zaki mutu sae ya sake aure, mayya kawai ƙila ma ke kika kashe uwarki" Safeerah dake durƙusa wani sabon kukan ne ya taso mata hakan yasa ta sakawa kukan nata sauti, tsaye ta miƙe ta fauci jakanta ta fice daga parlourn, binta waje Aunty Luba tayi tace, "Mayya! Tafi can kuruwar mu kurrr, naman mu ɗaci gareshi.." Safeerah na jin hka kuwa hawayen ƙin tsayawa ma suka yi hakan yasa tayi hanyar wajen gidan da gudu tana tafe tana share hawaye, sosai abun ya dameta duk maraicin da take bae dame su ba sae ma kiranta mayya da suke harda cewa ita ta kashe uwarta. 🥹🥹


*An sako mu gaba!🥹

Follow up for more!🥂🔥💕


©️Fateemah MG



Post a Comment

0 Comments