TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

'YAN UWA NA NE PAGE 5

 👭❤ *'YAN UWA NANE!*❤👭

         💎 _they're my relatives..!_💎



Written by: *BILLY S FARI💎*


Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*


Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*


_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_



💎Page_____5💎



    Baya Ummi taja had'e da rik'o hannuwan Bilkisu da Bilal ta nufi part d'inta idanuwanta na zubar da hawayen tausayin Mahmud, ko shakka babu tasan tana matuk'ar  k'aunarsa aranta shi yasa bata iya jurewa idan ta gansa cikin damuwa, gashi yanzu tanaji tana ganinsa awani hali amma an haramta mata taimakonsa. Har ta kusa shiga part d'inta sai kuma ta juyo, 


Kallon inda su mom suke tayi har lokacin suna kan mahmud sun kasa bashi taimakon daya kamata. Goge hawayen idanuwanta tayi had'e da cewa.


"Bilkisu maza shiga ciki keda Bilal ina zuwa"


"Ummi ina zakije?"


"Kuje nace ina zuwa bakwa ganin d'an uwanku ba lafiya"


Wurin gate ta nufa ta yiwa maigadi knocking da saurinsa ya fito ya russana agabanta yana fad'in.


"Allah yatsareki hajia ina gaisuwa, me kike buk'ata ne yanzu nayi maki"


"Am malam habu ina saleh driver yake?"


"Bai jima da fita ba ya raka abokinsa da yazo wurinsa d'azu..." kafin ya rufe baki sai ga saleh driver ya iso yana rera 'yan wak'ok'insa, yana hango Ummi ya rugo aguje yana gaisheta.


"Yawwa saleh maza ka fiddo da mota ga Babana can ba lafiya kukai sa asibiti pls kayi sauri"


"Angama hajia" saleh ya fad'a tare da nufar wajen da motoci suke ajiye ita kuma ummi ta wuce part d'inta da nufin gyarawa tabi bayansu.


Saleh na fitowa da mota sai ga batool, cikin gadara tace,


"Kai saleh ina zakaje ne? to kajira zamu kai yaya Mahmud asibiti inji mom" 


Tana gama fad'a  masa tabar wajen. A wani private hospital _Jiddah specialist  hospital_ suka nufa kasancewar acan family doctor d'insu yake kuma a can duk 'yan gidan suke da folder, suna isa ba tare da b'ata lokaci ba aka shiga duba Mahmud, nan likita ya tabbatarwa da mom ba kome ke damun saba illah damuwa daya sa a ransa itace ke haifar masa da tsananin ciwon kai a duk lokacin da wani abun ya b'ata masa rai, don haka akula adena barinsa cikin damuwa domin hakan na iya tasiri ga zuciyarsa har yasa zuciyar ta fara yi masa ciwo.


Jikin mom ne yayi sanyi jin abunda likitan ya fad'a, kallonsa tayi kafin nan tace.


"Dr. toh ya jikin nasa yanzu?"


"Ki kwantar da hankalinki babu wata matsala yanzu haka anyi masa allurai tare da sanya masa drip bacci ya d'aukesa yana farkowa zaku iya wucewa gida, Amma dai ku kula sosai!"


"Insha Allah dr mun gode"


Rufe bakin mom keda wuya saiga Ummi ta shigo asibitin cikin damuwa ta nufi inda mom take,


"Momyn yara ya jikin baban nawa ina fatan da sauk'i ko?" ko kallon inda Ummi take mom ba tayi ba balle ta samu damar amsa mata. Hakan yasa Ummi ta samu kujerar dake gefe ta zauna, bata jima zaune ba sai ga family dr d'in su ya shigo,


"Ah...Hajia sannunku ina wuni,"


"Lpy klw dr" 


"Ya na ganku anan, waye ba lafiya?"


"Babana ne Mahmud ba lafiya"


"Ayya why not da ba'a kirani nazo har gida ba? me ya samesa?"


"To nima dai ban sani ba, amma muna tsaye kawai  mukaga ya fad'i k'asa had'e da dafe kansa..."


Kafin Ummi ta rufe baki mom ta Katseta da masifa,


"Ta yama za'ayi kisani kina nema ki kashe mun yaro to wallah....."


"Hajia hussaina!, hajia hussaina!! me nake shirin ji a bakin ki?, wannan sakarcin ne har cikin bainar jama'a?" muryar daddy ce suka jiyo da dirowarsa kenan ya samu labarin suna asibiti shine ya biyo baya, cike da b'acin ran abunda yaji mom na fad'a yake kallonta tare da narka mata harar mai tsanin nuna b'acin rai. Da sauri dr ya mik'a masa hannu yana fad'in


"U're welcm sir"


"Thank you dr jamil ya aiki?"


"Alhamdulillah how was the journey"


"Fine and good wallahi Dr isowata kenan yara ke fad'a mun my son is at hospital"


"Eh yanzu na keji ga hajia har nake tambayar don me ba'a kirani nazo gida ba, saboda tun d'azu ina gida yanzun nan na shigo urgently duba wata patient tawa"


"Nima da aka fad'amun haka nace why not daba akiraka ba"


Kallon mom dady yayi ta wani d'aure fuska had'e da kauda Kai gefe kafin ya maida kallonsa ga Ummi, Murmushi tayi tare da cewa,


"Sannu da hanya, an iso lafiya?"


"Lafiya lau hajia Aisha ya gidan?"


Wani murmushin ta sake sakar masa kafin tace.


"Gida kam yanzu ba dad'i tunda babana ba lafiya Amma kasan cewarka a nan yanzu nasan insha Allah komai zai dai-daita"


Wani mugun tsaki mom taja tabar wajen a hasale, Girgiza kai dady yayi sannan ya shiga room d'in da aka kwantar da Mahmud wanda ganin mom ta shiga ciki ya tabbatar masa da hakan, ita Ummi da dr sukabi bayansa.


Bayan an sallami Mahmud sun koma gida, da safe yana zaune ya jingina da jikin gadonsa cike da farin cikin dawowar mahaifinsa yace,


"Mom dama jiya daddy zai dawo shine baki fad'a mun ba" tab'e baki tayi had'e da mik'a masa cup d'in tea data gama had'a masa tana cewa,


"Ya za'a yi na sani bacin munafurci ya hana a sanar mani nima, tsabar rainin hankali ma dadyn naka kama wayoyinsa yayi yasa rufe tun shekaran jiya nake trying nasa ban samu bs ashe yasan me ya shirya tunda a wancan part d'in zai sauka..."



"Haba mom!, haba mom!!...yanzu dadyn ne kike cewa ya munafucceki bacin kinsan duk abunda zai yi agidansa baya nuna ban-banci, to wlh ni kaina saida na tambayi Ummi yaushe zai dawo, the same thing itama haka ta fad'a mani cewa bata sani ba don bata samun wayoyinsa idan ta kira, mom to meye ribar dady da Ummi idan sun b'oye maki wani abun? pls mom don Allah kidena irin wannan abun bai dace ba"


"Oho dai suma suka san dalilinsu ni idan ma ancuceni nida yarana wlh Allah ba zan yafe ba"


Shiru mahmud yayi yana kallon mom idanunsa cike da k'walla ya kasa ce mata komai, tunowa da kalaman likita ya sata sakin Murmushi tare da cewa.



"Sorry yayan B3 nadena dama da wasa nake yi maka"


Turo k'ofar d'akinsa da sukaji anyi yasa Mahmud ya kasa bawa mom amsa, Bilkisu ce ta shigo bakinta d'auke da sallama hannunta da k'aton tire da abinci ummi ta aikota ta kawowa mahmud d'in.


"Mom ina kwana, ya Mahmud ina kwana, sannu ya jiki, gashi ummi tace akawo maka tana gaisheka" 


Billy ta fad'a tana kallonsa, Dariya Mahmud yayi sannan ya ce


"Washhh...billy jepanis wannan surutu Mai had'e da tambayoyi to wace kike son na fara amsawa daga ciki?" saida ta turo baki jin sunan da yayi mata amfani wajan yi mata magana sannan ta duk'a da niyar ajiye tiren abincin mom da tund'azu ta cika tayi fam tasa hannu ya buge tiren duk abincin ya watse a k'asa ita kuma Billy ya b'ata mata jiki.


"Uban waye ya kawoki d'akin nan, anfad'a mata cewa bana iya kula da d'ana ne da har zata wani dafo wannan k'azamin girkin nata ta kawowa d'ana? maza kibar d'akin nan kafin nab'ata maki rai da wasu shegun idanuwanki kamar k'wayar gero!"


Da sauri mahmud ya taso ya rik'e hannun Bilkisu tare da cire rigar jikinsa yana goge mata kayanta inda abinci ya zubar mata bayan ya gama ya duk'a ya tattaro abincin daya zube a plate  sannan ya koma kan gado yasa hannu ya fara ci, sai da yayi kusan loma uku sannan ya d'ago kai yana Murmushi ya cewa billy.


"Sister kicewa Ummi na gode kuma abincin yayi dad'i sosai"


Kad'a masa kai tayi sannan ta duk'a da nufin gyara wajen yace


"Sister jeki zansa a gyara wajen"


 Jiki ba k'wari tabar d'akin yanzu kam inda sabo tafara sabawa da abubuwan da mom keyi mata, tana fita taci karo da Bilal zai shiga d'akin da sauri ta rik'o hannunsa,


"Bilal karka shiga mom na ciki" duk'owa tayi tana gwada masa yanda jikinta ya b'aci "kagani daga shiga in kaiwa yaya abinci shine ta kifar da abincin k'..."


Rufemata baki yayi tare da cewa 


"Aunty Billy kidena fad'a Ummi tace mudinga hak'uri idan anyi mana wani abun tunda 'yan uwan mune"


"Shikenan Bilal yanzu duk  abunda aka yi mana hak'uri zamu yi tayi babu wanda zamu fad'awa? Ai wannan basu suka yi ba mom ce tayi"


"Aunty ai itama mom 'yar uwar muce tunda mom tace k'anwar tace"


Rungumesa tayi "Bilal kai yaro ne k'arami amma kana da fahimtar da nikaina bani da ita" bata ankara ba taji ya hura mata iska a kunne ya ruga aguje yana dariya, binsa itama tayi aguje tana dariya don izuwa yanzu ta fahimci ko meyasa yake yi mata haka,


A b'angaren mahmud kuwa Billy na fita ya kirawo wayar Basmah.


"Hello yaya mahmud  ya jiki?" ba tare da ya amsa mata ba yace.


"Kizo d'akina yanzu" sannan ya kashe wayarsa, kallon mom yayi yace



"Mom for Godness sake me yasa kika zubar da abincin da Ummi ta aiko min dashi?"


"Saboda bana so kaci kuma ka watsan kasa a ido, waya san ko meta saka maka a ciki don ta kashe ka tunda bata son ganin 'ya'yana a raye"


"Kamar ya kenan mom?, kinsan adadin ko sau nawa inacin abincinta? Idan Ummi na son kashe maki 'ya'ya da tun-tuni muna yara zata kashemu, ko kin manta lokacin da kukaje egypt da daddy kika barta mu a hannunta har na tsawon shekara d'aya, meyasa lokacin bata kashemu ba sai yanzu da muka girma, duk da bawani wayo ne dani ba, bana manta wahalar da tayi da basmah lokacin ko shekara biyu bata yi ba a duniya, ko kad'an bata barin Ummi bacci da tsohon cikin Billy haka Ummi ke goyon Basmah abayanta idan tana rigima har sai tayi bacci me yasa bata kashe mu ba sai yanzu....? pls mom ko ba zaki so Ummi ba  Atleast ya kamata kiso yaranta kamar yanda take son mu"


Wata muguwar harara mom tayi masa had'e da maka masa pillow ajiki.. 


"Rufemin baki shanyayye ai gashinan garin kwad'ayinka an shanyeka zaka dameni da wani tsohon labari, bari in fad'a maka over my died body bana son Aisha da yaranta Don haka kaima tun wuri kasama ranka haka, dole ne karabu dasu don bana son tarayyarka dasu ko kad'an" sannan ta fice daga d'akin tana cigaba da masifa, dariya Mahmud yayi 


"Mom kenan ikon Allah!, kinsan gaskiya Amma bakyaso a fad'a, to nidai bansan ya za'a yi na rabu dasu ba don su d'in 'YAN UWANA NE na jini!"


Mom nafita taci karo da Basmah ko kallonta bata tsaya yiba saboda masifar da take yi ta wuce abinta, binta da kallo Basmah tayi had'e da tura k'ofar d'akin ba tare da tayi sallama ba


"yaya me aka yiwa mom naga ta fita tana masifa kamar irin rikitaccin tsofaffin nan?"


"Stupid koma kiyo sallama kafin na tashi na b'abb'allaki a gurin nan"


"Oh! yaya Allah ya baka hak'uri daga tambaya"


Komawa tayi tayo sallama ya amsa sannan yace ta shigo 


"Yawwa Basmah maza ki harhad'a kayan nan dake k'asa kishare abincin kiyi moping wurin sannan kishiga toilet d'ina ki wanko kwanonin Ina jiranki"


"To yaya amma waye yayi b'arin abincin?"


"Basmahhhh...! nifa shine yake had'ani dake wato yawan tambayar da kuma Shan batu, to mommy ce ta zubar da abincin shikenan?"


Had'e rai Basmah tayi don Ita bata son fad'a arayuwarta balle gwasalewa, aikin ta farayi tana qunquni har ta kammala.


"Yaya Nagama ga kwanonin"


"OK thank you Basmah ajiye munsu akan bedside zuwa anjima na kaisu"


"Yaya Mahmud kwanonin waye?"


"Na ummi ne" wani irin takaicin wanke su taji yataso mata aria, murmushin mugunta tayi  kafin tace.


"Bari na kai mata tunda ba kada lafiya"


"Ok sister say  a big thanks to her"


Jiki na rawa Basmah ta nufi part d'in Ummi tana qiyasta rashin mutunci da zata yi idan taje ciki....



  _SORRY FOR THE LATE UPDATE, AM TOO BUSY👏 yanzu ma nayi manage ne don d'ai naga cewa na faranta maku saboda zab'en da ake yi😍_




Post a Comment

0 Comments