TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

RAGON MIJI PAGE 72

 7⃣2⃣






*SHAFIN mommyn mufeeda da me dambu inajin dadi yadda kukasance daga cikin mabiyan buk dina ina kuma jin dadin comments naku thanks*




*yaruwa kinayin azkhar din safiya da marece kuwa? Koko aiki da son kwanciya barci ko saurin kunna data suna hanaki yi? Da kinsan falalar yinsu dako kina gudun ceton rai zaki rikayin su,in kuma kinsan falalarsu why kike sanya? Ko mantawa dasu? Azkhar suna haska rayuwa, yana sauya mummunan abu zuwa alheri, kariya ce daga sharrin kowane abu, yana kawo arziki dajin dadin rayuwa,yana gyara zuciya,yana kusantar da mutum ga ubangiji, yana kai mutum zuwa aljanna,shin me zesa kiyi sanya da yinsu? gasunan da yawa masu saukin karantawa se dumbin lada da falala, Dan Allah murika yin azkhar karmuyi sanya dasu don neman kusanci da kariya awurin ubangiji, duk abinda mukeyi mu daure murika yin azkhar dinnan koda muna kitchen ne, ko a mota going to office ko a school ko ina sau da dama Allah ya janyemiki sharri sanadin azkhar wanda ke baki sani ba, kinemi littafin azkhar a book shop's ki kara samun wasu ki hardace kitayi insha Allah zakiji dadinsu kuma zaki samu natsuwa*



*yaruwa kinada riyadul janna fi azkharul kitabu was sunna kuwa?littafi ne da ya tattara azkhar da adduoi wanda baakawosu hakanan ba seda akafara rubuto hadissan da aka samosu da wadanda suka ruwaito, acikinshi akwai adduoi da yawa wadanda wlh zakiji dadinsu an tattara duk adduoin dake cikin alkurani a littafin da kuma sunayen Allah kyawawa wadanda idan an rokeshi dasu yana amsawa wanda sukazo a alkurani me girma wanda suka jerosu tun daga fatiha to nas, ga kuma manyan adduoi a bayansu wanda Allah yake amsa addua in akayi su , na rungumi riyadul janna naji dadinshi matuka,idan bakidashi ina me baki/ka shawara ki nemi riyadul janna zaki samu biyan bukata kuma zakisamu kusanci da Allah (S.W).zaki sameshi a kasuwanni wurin masu littattafai ko bookshops wallafar yusuf bin Ismael ,bangonshi da hoton lambu  da flowers,nasan beda tsada ada bansaniba yanzu kiyi kokari ki mallakeshi don bukatarki, bakin cikinki,ko damuwarki zasu yaye,zaki godemin kede kinemi naki ki runguma*




Cikin gigicewa Hajiya take ce musu"nabani khalil dina ya mutu yayi accident ya mutu"


Matan suka dauki salati jikinsu yayi sanyi domin khalil mutum ne har mutum yana girmama mutane bazaka ce ga abokin fadanshi ba yana da hakuri uwa uba yawan ibada, 


Hjy tace "hjya rabi Dan Allah kuce be mutu ba, be mutu bako? Nasan baze mutu yabar niba bandashi cikin motar wlh babu shi"


matar daakace ma hiya rabi ta kalli abokiyar zamanta tace "hjya zaliha ki kira alhaji kifada mishi yafada ma manu naji labarin accident din yanzu inajin radio se suje su dubo indashi se suanso gawar ai mishi sutura "


Zaliha ta juya dasauri ta shiga gida ta dauki waya ta kira mijinsu tafada mai yayi ta sallallami yace "yanzunnan naji labarin accident din bari nakira manun donni ina jibia amma yanzunnan zan kamo hanya "


ya kashe kiran ya kira manu, kawu manu ya girgiza ba bata lokaci ya tafi gidan kaninshi suka nufi matuary dauko gawa, 



zaliha ba bata lokaci ta dannawa siyama kira ,siyama na kitchen wayar ta keta kara yaranta duk sun tafi islamiya jamila ta dauko wayar ta kawomata  ta juya ,


siyama ta dauka takara kunne da sallama a bakinta, 


Zaliha tace "siyama nice hjya zaliha ki taho gida khalil yayi accident ya rasu hjyar ku kuma bata lpy"diff takashe takoma gidan hjya dasauri, 


Siyama zuciyarta ta rika harbawa dasauri hawaye suka rika zuba a fuskarta masu zafin gaske, 


Tai cikin daki tana kuka, jamila dake zaune tayi tagumi taga siyamar tashigo tana kuka ta tashi tabita ciki siyama har tazira hijab jamila tana ta kallonta tace "anty lpy kike kuka? "


siyama tafashe da kuka tace "yaya khalil ne yayi accident ya rasu "


kamar saukar guduma jamila taji maganar ta yanke jiki tafadi, 


Siyama tai kanta tana kuka tana kiran sunanta "jamila! Jamila kitashi Dan Allah "


Mijinta babban mutum ne idan ya dawo aiki a kofar gidanshi yake zama wurin har yazama majalisa cika yake da maza,


 siyama ta tashi tafita waje dagudu bata tsaya koina ba se gaban mazan dake gun ta kalli mijinta tana kuka cikin tashin hankali tace "baban farida jamila ta fadi "


yace "subhanallahi ! "ya tashi yayi cikin gidan dasauri, siyama tabi bayanshi, 


Yana shiga ya samu jamila a sume da sauri ya bude fridge ya dauko ruwa masu sanyi ya sheka mata su a fuska, 


jamila tasaki ajiyar zuciya  ta bude ido wuf tatashi zaune tafara hawaye" anty yaya na ya rasu? Ya khalil dina fa"?


siyama daketa kuka tace "ya rasu jamila "



Marar jamila da tunda tafarko take murdawa kadan, ta  murda da karfi ,jamila ta dafe ciki da kugu tafara kuka tana nishi zufa tarika karyomata ta koina, 


Baban farida  yace "siyama me kike fada ne?"


siyama tace "yanzunnan aka kirani akace yayi accident ya rasu "


Baban farida yace "innalillahi wainna ilaihi rajiun!!!! ...


karar da jamila tayi ne ya katseshi, 


"wayyo Allah marata zata balle wayyo kuguna "


dashi da siyama suka rirriketa baban farida yace ma siyama "dauko min keys dina mutafi asibity"


Siyama ta saketa tana kuka tatafi dauko keys, shima idonshi jawur ya dauko jamila suka fito siyama ta bude mai yasa jamila baya tashiga yajasu suka nufi asibity, tsakanin jamila da siyama bazaka gane wake nakudar ba don dukkansu kuka suke riris, 



baban farida har kyarma yake wajen tuki dakyar suka isa Medical Center aka amshi jamila akashiga daita, 


siyama ta cigaba da kuka zuciyarta kamar zata fito duka yaushe sukai rashin alhaji yanzu kuma khalil, 


baban farida ya rungumota jikinshi yana rarrashi, 


ba jimawa wata nurse tafito wurinsu tana sauri tace "patient da kuka kawo labour take ayi sauri akawo kayan haihuwa "tajuya takoma dakin, 


baban farida ya zaunar da siyama akan seat ya fita anan bakin asibitin yasiyi kayan haihuwar ya koma ciki dasauri, 


Ba jimawa nurse tafito ta amshi kayan hankali tashe yace "ta haihu ne?"


nurse din tace "a, a dasauran lokaci kumata addua "takoma  ciki dasauri,


wayar baban farida tadau kara yana dubawa yaga mamar jamila ce, kamar kar yadauka ya dauka ya kanga akunne ,


acan bangaren tace "yaya kuna lpy kuwa dazun maman siyama ta kirani tana tambayar khalil ko yazonan bamu gama waya ba takashe wayar yanzu naji labarin accident da akayi ahanya shine hankalina ya tashi nace bari nakira "


Murya dishe yace "harda Khalil acikin accident din, yanzuma muna asibity jamila labour take "



maman jamila dake zaune ta mike tsaye tana salati tace "Allah yajikanshi, Allah yabata lpy nan bada jimawa ba zamu taho "takashe kiran tafara neman layin mijinta yana dauka tafada mishi ba jimawa yazo gida suka kama hanyar kt, 


Shiru shiru jamila bata haihu ba, hankalinshi duk da baa kwance yake ba yayi ta maza yacewa siyama tajira zeje yadawo, 


yanufi gidan hjy, 


Hjya tabi ta rude tayi sambatu har muryarta ta shake dole tai shiru tana ta kuka batsayawa, matan dake wurinta sunata bata hakuri, hjy rabi tafara mata nata waazi "haba hjy kinaso kinuna Allah be kyauta ba komi? kituna fa Allah ne yabaki shi kuma ya amshi kayansa meyasa bazaki hakuri ba? Kiyi hakuri kita innalillahi wainna ilaihi rajiun ki kuma cigaba da mishi addua ita yake bukata a yanzu ,insha Allah yanzu khalil ba abinda yakeso fiyeda akaishi makwancinsa inamishi kyakkyawan zato kiyi hakuri Allah seyabaki ladar hakurinki, ko kuma kita kuka da surutan har Allah yayi fushi dake, hjy bayau akafara miki mutuwa ba ina iyayenki ina mijinki? duk kin hakura donmi yanzu bazaki hakuri ba? kuka dole ne amma ba irin yadda kike ba kiyi hakuri Allah yamishi rahma "


hjya ta cigaba da kukanta danbata jin wani waazi yanzu, 




kawu manu sunje matuary mutane da yawa wadanda abun ya rutsa da yanuwansu ,har akazo kan su kawu manu aka tambayi sunan khalil suka fadi acikin list na fasinja harda khalil a motar su shidda ne ,


dandanan aka shiga dasu ciki akafara zaro maza daga lokokinsu ba kyangani abun, basuga khalil ba, abun yabasu mamaki ga sunanshi amma babushi dan sandan da kenan yace "to gaskiya kila babushi a motar don motocin duk sunyi ragaraga kaida ka gansu kasan ba  ran daze fita daga ciki kuma ba gawar da tazama toka donba kasusuwa kuma wurin ba wasu gawarwaki awaje munyi screening sosai kuje kukara bincikawa ko kafin accident sun saukeshi wani gari "


su kawu manu suka fita suka nufi gidan hjya, 


hjya na zaune tayi lakwas ko mutuwar alhaji bata girgizata haka ba, suka shigo suka zauna, 


ta dago tace "manu ina gawar khalil? Ko gawar tashi ma bazan samu gani ba? "


manu yace "se hakuri hjy, Allah kadai yasan komi munje acikin gawarwakin ba khalil kuma dasunanshi acikin list na passengers ,kila babu shi cikin motar"


Hjya tafashe da kuka da shakakkar muryarta tace "khalil ya zama toka ya zaai aganshi,ashe kallon bankwana nayi mishi ayau, naso ya mutu yanajin dadi ba cikin kunci ba "


baban farida yayi sallama yashiga ciki, 


kawu manu yace "ance ba gawar da ta kone, kode har yaisa batsarin shi?"


baban farida yace "a, a beje ba saboda yanzu mukayi waya da zulai tace beje ba "


hjya tace "khalil fa ya rasu shikenan banda kowa yanzu se siyama ba alhaji ba khalil "


Sukace "hakuri zakiyi hjya Allah yajikansu ya musu rahma "


Hjy ta kalli baban farida tace "ina siyamar? "



baban farida yace "suna asibity da jamila taji mutuwar se labour tataso mata  "


hawaye suka zuboma hjy jin wadda ma yatafi biko tana cikin garin, se tausayin jamilar yakamata tanason khalil sosai, se hjyar taji yanzu ba abunda takeson gani se dan ko yar khalil ,


Tana share hawaye tacewa baban farida "mutafi asibitin "


Ta tashi ta dauko abayarta, ta fita su kawu manu da baban farida suka biyo bayanta, su hjya rabi ko suna zaune jingum jingum, 


Baban farida ya budemata mota tashiga suka nufi asibity, 


Suna zuwa siyama ta rungume hjy tana ta kuka se yazama hjyarce ke rarrashin siyamar, suna tsaye ba abinda sukeji se kukan jamila dake fitowa daga cikin labour room, 




Fahad na isa gidan mommy yashiga jiki sabule ,ya fada kan kujera yayi zaune yanata tunani yanzu wane hali faseelat take ciki? zuciyarshi zafi kawai take for minutes sannan mommy tafito taganshi yanayinshi wani iri tace "lpy son naganka haka? "


yace "mommy amira bata lpy suna asibity tundazu "


mommy tace "subhanallahi tun yaushe? "


yace "tunda safe "


tace "shine se yanzu zakafadamin? "


Yayi shiru taja tsoki ta haye sama segata tafito da gyale da car key da jaka tazo zata wuceshi tafita, 


Yace "mommy kitafin musu da abinci don haryanzu Aisha bataci komi ba "


mommy ta harareshi tace "tunda safe ace haryanzu bataci komi ba kai miye amfaninka ne dabazaka zo kafadamin ba in ita hankalinta ya dauku wurin jinya? Mtsswww "taja tsoki tafara kwadawa jummai kira, jummai tazo dagudu mommy tace "kingama dinner? "


Jummai tace "a, a amma akwai abincin rana kuma cikin warmer yake "


Mommy tace "daukomunshi dasauri"


jummai takoma tadawo da kula mommy ta amsa ta fita tashiga mota tai asibity, 


Fahad nanan zaune dafe da kai yarasa yazayayi neman mafita yaketayi daga karshe yatashi yakoma kofar gidansu faseelat har lokacin kulle gidan yake yaja tsoki yanajin kamar yayi kuka ya bar unguwar, 



mommy nashiga wurinsu Aisha amira ta rungumeta tana hawaye tace "mommy kitafi dani gidanki banison gidan daddy "



mommy tace "yi hakuri princess dake zan tafi kinji ko? Ki kwantar da hankalinki "ta kwantar da amira jikinta, 


ta kalli Aisha dake koje koje tace "meya sameta?"


Aisha ta girgiza kai tace "zamuyi maganar after"


Mommy tace "okay kidaure kici abinci ko kadanne fahad yace bakici komi ba "


Aisha tace "banajin yunwa ruwa kawai nakeso "



Mommy tace "kibude jug gashinan ki zuba tea kisha amira nasa aka hadomashi itama ki zubamata "



Aisha tace "baride na zuba mata kibata ni zanfita nasamo mana drinks a reception "


Ta zuba tamikawa mommy ta dauki kudi ajakar mommy tafita, 



Mommy tayi tayi amira tasha amira taki sema tafara rigimar ita anty "mommy ni anty nakeson gani ki kaini wurin anty"mommy tai shiru tana tunani dan tagano akwai abinda ke faruwa, 



Su hjy na zaune sukaji kukan jariri yanata inyarrrr inyarrrr, hawaye suka zubowa hjya, dukda jamila ta haihu bata bar kuka ba nurses sukace ko ciwo takeji wani wuri batace musu komi ba tacigaba da kuka sunata fada itako bata fasa kukanta ba, suka shirya baby nurse tafito wurin su hjya dauke dashi, 


duk suka tashi tsaye hjya hannunta har rawa yake wurin son ta amshi yaron, ta amsheshi ta bude fuskarshi yaron sakkkkk khalil lokacin da yana jariri, hjy se kuka ita kuka siyama kuka, Allah assamad khalil yatafi khalil yadawo, nurse tai tsaye tana kallonsu ganin suduka suna kuka ta juya takoma ciki, 


Baban farida na tsaye ya rike hannu, 


bayan mintoci aka fito da jamila aka medata rest room, su hjya sukabi zuwa dakin, 


Jamila na kwance tana ta kuka suka shigo hjya ta mikawa baban farida jaririn ta matsa tariko hannun jamila tace "kiyi hakuri jamila, Allah yafimu san khalil shiyasa yadauki abunsa, "


fuska jage jage da majina da hawaye jamila ta kalli hjya tace "hjy kema kin yarda ya mutu? Wlh be mutu ba yana raye yananan zuwa baze tafi yabarni ba "


Hjya ta share hawaye tace "kiyi hakuri jamila kowa seya tafi can"



jamila takara fashewa da kuka, ko sanin me ta haifa ma batayi ba, hjy tasa hannu tana share mata hawaye tana rarrashinta, 


Baban farida besan lokacin da hawaye suka zubomishita gefen ido ba, duniya kenan gashide wanda suke fada kanshi ya rasu dukansu suna kukan rashi yasa hannu ya share, 


ana haka mamanta suka iso ,jamila takara wage baki tana kuka, duk dauriyar zulai seda tayi kuka, 



gaf Maghreb faseelat ta farfado tana nishi ,idonta arufe ta tuno abinda yafaru tabude ido dasauri hawaye na zubarmata ta dafa cikinta dake ciwo, hawaye masu zafi suka kara zubomata, 


ummi ta dafata tace "sannu faseelat ya kikeji?"


Se sannan faseelat tasan su ummi na wurin ta juyar dakai ga ummi abba,omer abul ishak da Mubarak harda baaba matar baba babba, 


hawaye na cigaba da zubomata murya dishe tace "ummi cikin ya zube ko? "


ummi tace "kiyi hakuri haka Allah yakaddara"


Faseelat ta juyar da kai tana hawaye ,tana tuno yadda fahad ya rikice yarika dukanta kamar ba mutum ba, yanzu shikenan cikin ya tafi,


Ummi takatse mata tunani tace "bari na temaka miki kisha tea kokadanne "


faseelat ta girgiza kai tace "nakoshi ummi bazan iya cin komi ba"


Ummi tace"kidaure ko kinsamu karfi "


faseelat ta girgiza kai, dukkansu suka matso suna mata sannu ta rumtse ido bata amsa suba, 


she wonder yaakai takenan ina fahad yaakai baya nan se su ummi kawai mike faruwa ne? Karde........zuciyarta tabuga da karfi, ta bude ido tace "ummi ina fahad? "


ya omer dake gefe zuciyarshi nacigaba da tafasa saboda halin da take ciki jin tana nemenshi yasa yaja dogon tsoki ya fita daga dakin, 


Ummi rai bace tace"wane  fahad kuma ke yanzu dan kina dakikiya ya nakada maki shegen duka daga farkowarki kifara tambayarshi wlh sunan fahad yafita daga bakinki ko natashi nai tafiya ta "


faseelat na hawaye tace "ummi waya kawoni nan?dan Allah kufadamin yana ina "


Ummi taja tsoki zatai magana abba yace "Dan Allah kibarta zafin ciwo ne bawani abu ba, kibari tadawo hankalinta sannan "


ummi ta tabe baki, faseelat ta cigaba da hawaye zuciyarta na harbawa tarasa gane meke faruwa, 





Maghreb tayi musa da yazo duba gonarshi daga  babbar riga, besamu yaje gonar bama seda aka kusa Maghreb don ya samu hadarin da yafaru, yagama abunda yake ya na cikin tafiya zuwa wurin da yayi parking motarshi yaga mutum sheme sanbal straight akwance acikin ciyayi, 


Ya matsa wurin khalil ba alamun ko rauni jikinshi ya zukunna ya fara duba shi, 


kamar wanda yayi bacci khalil  ya tashi zaune, yana salati ya jujjuya kai gabas da yamma kudu da arewa ,sannan yadafe goshi yana jin kuwwar mutane da salati da mutane sukai tayi lokacin accident din, 


musa ya dafashi yace "bawan Allah mekake anan yanzu da daddare? "


khalil idanunshi jawur zuciyarshi sanyaye yace "bansan yaakai nazo nan ba, nide nasan muna cikin mota, wata mota tahawo tamu daganan bazan iya tuna komi ba"


Musa yaja kabbara "Allahu akbar ,Allah me yadda yaso dama akwai ran da yafita a motocin can abun alajabi, bawan Allah lalle Allah nasonka daya barka da rai har zuwa yanzu domin acikin motocin bawanda ya fita duk sun kone "



khalil ya dago arazane, mutumen yace "eh duk sun mutu kaima ina mamakin ganin ka anan tunda yayi nisa da inda hadarin yafaru "


khalil yace "jinake kamar nayi bacci na farka amma nasan bakomi ne yasa Allah yatsareni ba se don yawan ambatonshi da nake kuma nakasance me kiyaye dokokinshi "


Musa yace "hakika wannan ba abun mamaki bane don ikon Allah yawuce mamaki azamanin manzon Allah (S. A. W) wata unguwa takama da wuta duk gidajen suka kone daakazo akafada ma sahabin daya daga cikin mutanen unguwar se ya karyata yace wlh banda gidana saboda bana fitowa gida harse nayi adduar da manzo ya koyar damu (fans namanta adduar) kuma ana zuwa akaga gidanshi lpya lau amma duk nakusa dashi akone,"


Ya cigaba da cewa" nan kusa akwai wani abokin mahaifina shide yakasance kullum baya manta karanta ayoyin karshen suratul tauba, lakadjaakum sau 7 koda yana tafiya yakan karanta ta koda besamu yin kowane azkhar ba yanayin wannan, se wani amininshi ya kawo mashi ziyara daga sudan shikuma abokin mahaifin nawa yana zaune a kaduna, bayan ya kwana se suka shirya suka nufi abuja don ziyarar abukkansu, tareda driver suke amma se abokin mahaifina yaamshi driving, kasancewar beiya dogon driving yake fara bacci suna cikin tafiya yafara gyangyadi dole yadawo gidan baya ya kwanta amininshi da driver suna gaba, baadade ba bacci ya daukeshi,yana bacci sukai accident koda yafarka sede yaganshi yashe a gefen titi mutane suna zagaye dashi bako kwarzane jikinshi, seyafada musu suna tare da yanuwanshi a mota, daaka bi daji ashe motar yankar daji tai taita tafiya tayi raga raga driver ya mutu yana ciki yayi jina jina, hankalinshi yatashi aka dukufa neman amininshi baagano amininshi ba se da akai tafiyar kilometers 25 sannan akaganshi kwance a mace cikin kungurmin daji, ya kidima sosai abun yabawa mutane mamaki, a kd akai janaizar amininshi da driver ana zaman gaisuwa wanda ina daga cikin wadanda ke gun anata jajanta lamarin sewani malami yake tambayar shi wace addua yayi ayau seyace "wlh ban karanta komi ba se lakadjaakum kafa 7 wanda kuma a riyadul janna nasamu falalarta hadisin da yakawota a rauda ta 18 ankarbo hadisin ne daga Muhammad bn abubakar  cewa wanda ya lazimci karanta lakadjaakum ila akirul sura lam ya mut hadman wala garqan wala harkan wala darban hadid,shine na lazimceta kowane lokaci "


,malamin yace"hakika karshen suratul tauba kariya ce daga dukkan abun ki, nima zankara dukufa wurin yinta "



Musa ya cigaba dacewa daganan sena rike ta inayi danaji falalarta ,ban wata biyu da riketa ba zanje Lagos motar mu ta kife karamar macapolo ce amma bawanda ya fita seni nima cikin jini nake domin naji ciwo sosai "ya bude kafarshi zuwa bakin gwiwa wani katon tabo ya bayyana harda rami ajiki yace "kaga tabon da yakasa bacewa daga cikin tabunnan danayi a kalla anyi shekara biyar amma har yanzu be cike ba sede ina tafiya da kafata lpy lau duk dan temakon Allah "(it's true life story ya faru dagaske)


khalil yace"ina yawan karantata domin tana daga cikin jerin azkhar dake cikin littafi na sede bansan falalarta ba, hakika nagode ma Allah daya kareni domin koda mutuwa hutuce aguna zanso nakara rayuwa dan nakara aikata aikin alheri ,inada mahaifiya ita kadai ta ragemin  inason na rayu har zuwa tsufanta zuwa lokacin da zata kasa yiwa kanta komi yazama nine me mata hidima don samun rahmar ubangiji da albarkarta dafatan Allah yabani wanda zemin haka nima"



musa yace "Allah ya yarda wane gari kake zan  temaka maka nakaika duk da dare yayi "


khalil yace "cikin katsina nake idan har zaka temaka mun ba gida nakeso kakaini ba, don ina samun matsala da matata da mahaifiyata nasan in sukaji labarin mutuwa ta zasu saduda mahaifiyata zata sauko domin tana sona sonda takemin ne yayi yawa haryake kawo mana matsala take kishi da matata kamar kishiyarta, inso samu ne zanso na zama bakonka nawani lokaci sannan zan koma garinmu "


Musa yace "ba matsala nima zanso nasamu ladar bakuntarka, na tausaya maka Allah ya ganar da mahaifiyarka"




Khalil yace "amin nagode Allah ya baka ladar "


musa yace"amin ni sunana musa ina zaune babbar riga da matata da yara na uku "


khalil yace "ni sunana khalil ina zaune a layout matata yarinya ce aurenmu beyi shekara ba"


musa yace "masha Allah Allah yabada zuria dayyiba zamu iya tafiya "


khalil yatashi suka nufi motar musa suka shiga suka kama hanyar babbar ruga batareda kowa yasan khalil na raye ba. 




ya Allah kajikan musulmai maza da mata ka musu rahma 👏🏼



*zakuji inata yiwa mamatanmu addua wata falala naji daga bakin sheikh daurawa cewa duk wanda ya nemawa muminai gafara zaarubuta masa lada adadin musulman da suka mutun , dukda de inayi akowace sallata domin nikan tuno da yanuwana da abokaina da suka rasu, to jiya kuma hatsarin nan yakara tadamin hankali har natuno garabasar nan shine nace bari nafada maku nasan akwai wadanda basu sani ba se sufarayi, Allah kakaramana ilimi*




Post a Comment

0 Comments