TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Ragon miji Page 94

 9⃣4⃣






*Allah (S.A)yace :- wal asr,innal insana lafi kusr ,illallazina amanu wa amilussalihati wa tawasau bil hakki wa tawa sau bissabr*



*Manzon Allah (S.A.W)yace kaji tsoron Allah a duk inda kake kuma kabiyar da kyakkyawan aiki akan mummuna don ya shafeshi,kuma ka muamalanci mutane da kyakkyawar dabi'a*






Jijjigashi take tana kuka shi kuma yadade da dena  numfashi tana ta kuka tana tari ta dauko wayarshi tana kuka tace doctor yazo ba jimawa ya kamo hanya,


Ta koma kan fahad tana ta kuka tana cikin tarin ta kako jini tasa hannu ta duba still de jini ne zuciyarta na ciwo amma ta mijinta take,


Sabeer jin shiru fahad be zoba ya nufi gidanshi atare suka isa da doctor shide yaga likitan ya shiga gidan dasauri,


Yanata mamaki yafito yabi bayanshi,


Doctor na zuwa faseelat tatashi tana kuka tana cewa "Dan Allah katemakamin baya numfashi baya motsi"


Doctor yafara bakin kokarinsa wurin ceto rayuwar fahad,


Sabeer na shigowa cikin gidan ya samu yara nata kuka dan faseelat ta aiki ladidi gidan Umma gefe guda ga kukan ita faseelat din,


Dakin yaran ya nufa ya dauko biyu masu kukan ya sabasu akafada zuciyarshi na bugawa ya nufi bedroom dinsu,


Yana shiga fahad na farkowa ya farko da tarin jini nakara fitowa ,sabeer ya rikice jikinshi yafara rawa,


Ga itama faseelat gefe tana ta tari hannunta akan zuciyarta,


Yakarasa cikin dakin dasauri yaisa wurin faseelat dake gefen bed yace"me ke faruwa  ? Me ya sameshi?"


Tana kuka tace "I don't know Dan Allah sabeer ku temakamin plsss"


Ya mika mata yaran ta amshesu hannunta nata rawa ta rasa me zatai musu,


Shi kuma yaje wurin doctor dake kara duba chest dinshi ya dora kan fahad jikinshi yanata hawaye,


Doctor yakara dubashi ya mishi duk abinda yakamata hakan yasa tarin yatsaya jinin ma amma zuciyarshi bata bar zafin ba tade rage ,hada alluran bacci akamasa amma besamu baccin ba sede idonshi daya lumshe jikinshi kuma ya saki,


Sabeer ya kalli doctor yace"meke damunsa haka ?"


Doctor yace"heart attack ,zuciyarshi tadena functioning yadda yakamata as a result of stress,ku kula da abinda bayaso da Wanda yakeso adena fadamishi mummunan labari but for now he's safe akiyaye gaba"



Faseelat tana hawaye tace "he just leave here some minutes back segashi yadawo haka I don't know meyafaru da yasa shi wannan halin"


Doctor yace"maybe yaji abinda yafi karfin brain dinsa ne kukula dashi zanje nakawo drugs"


Sabeer ya kalli faseelat yace"check on her plsss kamar jini abakinta"


Faseelat tace"noo I will be okay "


Doctor yace"no let me help you "


Dole ya dubata yanata girgiza kai,ya tafi siyo masu drugs,


Lokacin me aikin ta dawo tafara kula da yaran ita,


Sunanan aka kawo maganin tasha sabeer yabawa fahad ,


Suna nan zaune sunata kallonshi har allurar tafara sakinshi ya bude ido ya kalli sabeer yace "friend meyasa komi ke faruwa dani ne ?se yaushe abubuwa zasu dena samuna?"


Sabeer na hawaye yace "kayi hakuri fahad komi ya sameka kafi wasu jindadin rayuwa "


Fahad yayi shiru yanata hawaye ,


Mommy ta dauki lokaci toilet hawan jinin ta yataso jin tana niyyar tafiya lahira sanan tafito tasha magani tai kwance tana hawaye batare da ta kauda kudin ba sede ta watsar dasu daga kan bed din domin bata bukatarsu ko ganinsu ,



Se bayan laasar sabeer ya tafi ganin fahad din yadan samu relief ,


Suma can gida Su ramlat sundawo suka samu mommy nata kuka suka zauna tayata,


Fahad na kwance kan cinyar faseelat tana shafa sumar kanshi tana hawaye tace "abbu plsss tell me menene yasaka a wannan halin ?  u left here kana farin ciki kadawo cikin mawuyacin hali plsss tell me menene?"


Hawaye masu zafi suka zubomishi yace "bakomi ciwon ne kawai yazo "


Ta tsaya da shafar sumar tace "bana ganin akwai abinda yakamata kaboyemun a rayuwarka nice fa faseelat ur wife ur secret"


Ya riko hannunta yana hawaye yace "I will tell you amma its my secret banson kowa yaji ki boyeshi kamar yadda zan boyeshi"


Tace"I promise you bazan fadawa wani ba"


Ya saki hannunta yanata motsa baki yana so maganar ta fito yasamu yace"mommy is the one that send armed robber's to me ,can u believe it mommy ce ta turo a amshi kudi awurina"

Hawaye suka wanke mai fuska yace"mommy nafa the woman that take care of me and brought me up, nakasa yadda da abinda nagani  some kudin da aka dauka awurinta akan gadonta faseelat wannan wace irin jarabawa ce takesamu na ?"


Faseelat tafashe da kuka tana share mai hawaye ta rika girgiza kai don itama takasa yadda tace"mommy baza tai maka haka ba she love you bazata iya wannan ba"


Yace "but she did I swear itace because ta nuna hakan ta yadda ta tsorata kuma me yakawo kudin a gidanmu?"


Faseelat ta girgiza kai tace "kayi hakuri plss "


Yace"I luv mom ta kula dani tamin duk gata daban samu awurin mahaifiyata ba ,wannan baze sa nadena daukarta uwa ba bazesa namanta alherin da tamin ba plsss kirike min amana"


Ta daga kai tana hawaye yayi shiru yace "mommy ?mommy saboda kudi......."



Ladidi da tazo bakin kofa takira faseelat don duk yaran suntashi taji komi tace "chabbbb secret manya " ta koma dakinta jikinta na bari takira Umma ,


Umma suna kwance itada daddy ta dauka tace "Ladidi miye nakiran daga tafiyarki"


Ladidi tai kasa da murya tace "Hjy wlh inasonki duk abinda naga ze cutar da ko ahalinki ne bazan bari ba "


Umma tace "eh yaakai ?"


Ladidi tace"fashinnan da akaiwa alhaji fahad ashe Matar nan ta babanshi ce ta tura masa yanfashin yanzu naji yana fada wa ita Hjy don dazun yadawo yana a man jini seda aka kira doctor naji yana cewa its secret"


Umma da tundazu ta mike tsaye tace"secret din banza wlh seta fiddo kudinnan kaga makirar mata daita mukaita kukan abun a time din Ashe itace tsinannar kai nagode Ladidi zanbaki wani abu don jindadin wannan labarin"


Ladidi tafara godiya Umma takashe wayar tanata huci tafadawa daddy shima ya hau sosai don rashin imanin yayi yawa danka? Yatashi yayi wanka yafita be zame koina ba se police station, yafada masu sukai gidan mommy ,


Tana ta kuka police suka shiga megadi ya fada mata tayi baki domin da personal kaya ajikinsu ,


Tafito idonta kumbure tanata kallonsu tace"bangane ku ba"


Suka fiddo I'd card nasu sukace "mu police ne munxo ne muyi bincike a gidanki"


Mommy tafashe da kuka tabasu hanya tace"enter" suka shiga suna bincike Su ramlat suka fito sukai cirko cirko suna kuka ba jimawa police suka fito da kudin suka tasa mommy gaba suka tafi police daita,


Su ramlat sunata ihu ta koma cikin gida ta dauko waya ta kira fahad ,


Faseelat ta dauka takara mai a kunne ,


Ramlat na kuka tace "yaya munshiga ukku police sunzo sun tafi da mommy ka temaka mana "


Besan lokacin da yamike xaune ba yana kallon faseelat bakinshi na kyarma yace "how will this be possible yanzu mukai maganar dake yaakai har wasu sunji?"


Tana hawaye tace "wlh bani bace kasanni hero Allah bancika fadi ma wani damuwa ta ba bare kuma wannan da kace amana"


Jikinshi na rawa jijiyoyinshi duk suntashi yace"yazaai na bari mommy tai prison baze yiwuba "


Ya fita dasauri ,faseelat nata kiranshi yafita kamar bame ciwo ba,


Yafita ya nufi police station,


Faseelat ta fito tana kuka taisa dakin yara tace "Ladidi waya saki fadin wannan maganar dama ke munafuka ce ko?"


Ladidi ta fiddo ido tana sallallami tace"wlh Hjy alkawari ne na dauka duk abinda nagani koji dangane da Umma ko zuriarta se inda karfina yakare kuma ni wlh bana labe nadeje kiranki naji kuna maganar dabe kamata akirata sirri ba"


Faseelat tace"to kinyi dede ni bazaki cigaba da zama anan ba ki tafi can wurin ummar ni bazan zauna dake ba"


Ladidi tace"to Allah yabaku hakuri "


Tafita ta kwashi dilarta se gidan Umma ,



Fahad na zuwa police station har an garkame Umma ,dakyar yasamu akabarshi yaje ganinta mommy tana ta kuka ,


Ya rungumeta yana kuka yace "mommy kiyafemin plsss wlh bani bane "


Ta rufe mai baki tace "nasani dana nasan bazaka tabamin haka ba kana sona don Allah nikuma inason ka ne ba donshi ba ,da nasoka ne saboda mahaifinka yakara sona kuma nasamu daga baya kuma inasonka ne saboda kudinka ,amma yanzu son tsakani da Allah ne nake ma na tausaya ma halin dana jefaka tabbas ni natura su amma bance Su taba minkai ba nace musu kudin kawai zasu amso"


Fahad yanata hawaye yace"why ?why? Mom!! mommy kinga abinda kika jawomana duniya zatasan abinda kikayi mommy zaai mana gori makiyan mu zasuyi dariya"


Mommy tace"kayi hakuri plsss sherin shedanne"


Sunata kuka aka meda mom don inspectors sunzo zasuyi mata tambayoyi ,


Fahad yakoma mota yayita kuka,


Aciki ko Su ukku sunsa mommy gaba cikin tsawa yace"saboda me kika tura masa yanfashi ?"


Mommy tace"kudinne kawai nakeso"


Wani yace "don ba danki bane rikonshi kawai kk?"


Tace"bahaka bane"


Ya kwalha mata mari mommy ta dafe kuncin tana kuka,


 yace"to ya abun yake? mutumniyar banza kin batawa yaranki da danginki suna kinsawa yaranki bakin ciki"


Mommy ta cigaba da kuka dan me saukin cikinsu yace"a ina yan fashin suke dama tare kuke suna maki aiki?"


Mommy ta girgiza kai tace "wlh bansan suba through cellular nasan su kuma wlh bance su yiwa kowa komi ba"


Police yace"wacece cellular? "


Tace"she's my freind "


Insp yace"kibamu address na armed robbers naki daita wacce tahadaki dasu dan ubanta "


Mommy jiki na rawa tafadi address nakowa ne ,


Suka tashi sunajin haushinta suka fara shirin cafkosu ,



Kwana sukai suna tsarawa ,yadda zasuyi yayinda Su fahad da danginshi basu rumtsa ba an kulle masu uwa,


Karfe 6am polices suka isa gidansu oteka sunata bacci don jiya sunje aiki kuma sun debo gajiya domin seda suka fatattake yanmatan mutumin da matarshi ,


Polices suka shiga suka damko Su sunyi mamaki don basubar wani evidence ba don su har sun manta da case din mommy,


Seda aka kaisu sannan suka gane aka cigaba da horasu da kulkai,


Aka damko cellular itama ana sata cell suka fara dambatawa ita da mommy ita mommy na Allah yaisa ta cuceta ita kuma tana maganar donme zata fadi sunanta,


Saudat dataji labarin takwaso tataho da tsohon cikinta tana ta kuka da sunje ganin mommy cewa take batason ganinsu saboda kunya ,,


Saudat ta tafi gidan fahad ta samu bayanan ta durkushe kasa tana kuka tana rokon faseelat, faseelat ta rungumeta tana kuka tace"kuyi hakuri Dan Allah kuyi mata addua insha Allah zata fito "


Tuni news ya yadu ankama wadanda suka kaiwa governor hari sukayi wa fahad fashi,



Fahad ko office yaje yamikawa manager kayansu ,


Manager ya kalleshi yace"me kakeyi haka ?"


Fahad idonshi jawur yace"nabar aiki daga yau kayankune idan namanta da wani abu akirani "


Yajuya ze fita manager yace"kayi hakuri nasan company mu beyi maka sauki ba amma zamu zauna musake rules kuma zamu kara maka matsayi domin kabawa wannan company gudunmuwa sosai"


Fahad yace "bana bukata" yayi tafiyarshi manager yafara hada zufa dama sabeer da mutum daya suma sun tafi,


Yaje wurin Governor ya mishi godiya governor ya mika mai cheques da aka ba shi da kuma wasu kudade sun kai 50millions,yayi ta godiya ya tafi banki he can't believe it more than 2billions in his account kai masha Allah yayi murna ya godewa Allah,



Bayan 2 days 



Su oteka sunata shan azaba while mommy anbada bell dinta dakyar bayan fahad ya biya million 5,


Kullum seyaje gaida mommy nothing change ga kulawar da yake mata kullum in yaje setayi kuka tana neman afuwa yafada mata he forgive her ina takasa hakura,




Yau aka hadu kotu gasu oteka a kumbure gaban alkali ,


Mommy ko tunda taga alkalin ta bude sabon babin kuka don kuwa mahaifin Aisha ne bazata manta lokacin da tai ta mishi rashin mutunci ba don beda kudi tasa ya saketa har diyarshi dayake zuwa gani basu bari dole ya hakura shine yayi zuciya ya tashi yakaro ilimi yayi wani aure yagina sabon family,



Aka gabatar da shariar ,aka kirawo mommy sama ,


Alkali shima daya ganta ya tuna rayuwar baya so dabanne har yanzu be manta da irin soyayyar da sukayi baya ba kafin ta botsare masa,


Lauya yace"Malama ko kinsan wadannan?"

Ya nuna su oteka ,


Mommy ido jawur tace "eh nasan su"


Lauyanta yace "meye alakarki dasu?"


Tana hawaye tace "na kai musu aiki ne "


Yace "wane irin aiki kenan?"


Murya na rawa tace"natura sune suje suyiwa dana fashi Su amso wasu kudade danaji ze amsa amma nace karda Su tabashi wlh bansasu kisa ko taba lpyar wani ba"


Alkali ya jinjina ,mutane sunata Allah wade daita ,


Lauya ya koma wurin Su oteka yace"ko kunsan wannan matar?"


Oteka yayi dunduruss dashi shida tiger while die hard daya gama taushi kuma duk sunfishi shekaru yace"eh munsanta customer ce"


Lauya yace "aikin me ta kai maku ?"


Yace"kudi tace mu amso wurin danta"


Lauya yace"bayannan fa? shin itace tasaku ku kashe gate man kuma ku harbi shi dantan da kuma police guda biyu?"


Tunkan yayi magana oteka yace"ita tasaka mu police kuma kwanan Su ne yakare"


Mommy tafashe da kuka tana girgiza kai ,


Tana cewa "wlh karyane ni bance Su taba kowa ba"


Wuri yayi tsittt inba kukanta ba bakajin nakowa Su saudat na zaune suna kallo suna hawaye don ita ko gorin kishiyoyi ya isheta bakin ciki,


Die hard dake son yasamu rangwame yace"baita tasamu ba tace mukawo kudinne kawai batace akashe kowa ko a harbi kowa ba,bayan ma nan tazo tana kuka bataji dadin aikin ba "


Lauya yace "waye yakashe megadi cikinku?"


Die hard ya kalli Su oteka daketa harara suna bashi signal yace "tiger shi yakashe shi ,lion shi ya harbi megidan akafa kuma ankasheshi saboda musayar wuta da police "


Lauya yace"dama kunsan da zuwan police kenan ?"


Yace"aa harbin da lion yayine yajawo hankalinsu wurinmu Dan Allah kuyi hakuri wlh natuba zan gyara rayuwata inaso nayi joining musulunci"😂


Lauya ya juya yace"ya me girma me sharia inafatan kotu taji kuma tagamsu da bayanan da akagabatar nagode"

Alkali yayi rubuce rubuce yace"kotu ta daga kara se nanda 3days"


Akatashi mommy nata danasani suka tafi gida ,

Fahad ko besamu yaje ba don baze iya jura ba,



Tunda akamedasu oteka prison sukarika dirkar die hard seda aka sauya mai wuri,


Bayan 3 days aka dawo alkali ya tambaya ba me abun cewa ,


Ya dago ya kalli Su oteka yace"shekara nawa kukai kuna wannan aikin?"


Oteka yace"may be 10yrs  kuma mu Sana'a ce mukeyi bawani abuba"


Alkali ya kura mai ido yace " zaka iya gane mutum nawa ka kashe?"


Yace"yawane dasu ai kila sunkai 50 ko 60 hakade"


Alkali yace"subhanallah"


"Nasani kowa yasani acikin bible ba inda aka halatta wa cristian kwace da kisan juna da ketawa mata haddi da nakasa masu lpy kuma bawani littafi naku dayace haka ,kuna matasa kuna da karfi ku tsaya ga fashi da makami a matsayin Sana'a ,bawani littafi acikin littattafanku dayace kuyi haka ,kun aikata laifi kuma kunsan laifine kunada hukunci kamar yadda sharia ta tanada"


Ya kalli takardar gabanshi da yagama tsara komi yagama nemo komi yace "sakamakon hayar yanfashi da mommy tayi Wanda hakan ya sabawa sharia  kotu ta Yanke mata hukuncin zaman gidan yari na shekara biyu da horo me tsanani zata biya kudi nera millions 20 ,itako cellular zatayi 10yrs a can domin itace me kawomasu costumers kuma ta turasu sunyi fashi agidan kishiyarta tasa suka kasheta,zata biya kudin da suka kwato  da kudi  5millons abawa yanuwan matar ,oteka ,tiger,die hard sun dade suna aikata aika aika ,sunshiga gidaje da dama sunyi barna zasu biya kudin da suka amshe agidan  kuma kotu takwace duka kudinsu,sannan kotu ta yanke musu hukuncin kisa ta hanyar bindigewa"


Su oteka suka fara raba ido jin mutuwa kusa,



Die hard ya fashe da kuka yana begging "Dan Allah kuyi hakuri wlh natuba inason musulunci Dan Allah kubarni na rayu"


Alkali yace"sakamakon die hard ya fadi gaskiya beba kotu wahala ba ya kuma yi ikirarin yanason musulunci bazamu hanashi damarshi ba don haka kotu ta masa sassauci ta yanke masa hukuncin zama gidan yari na tsawon rayuwarsa batare da horo ba"


"Zaa iya daukaka kara kafin nanda 2weeks"


Ya buga guduma aka mike mommy nata kuka cellular die hard kuka Su oteka sunata  raba ido da alamu zuciyar bazata sauko ba,



Su ramlat suka rungume mommy dazaa wuce daita suna kuka zasu rabu da mahaifiyarsu,


Fahad da yasamu yazo se hawaye yake mommy taje ta rungumeshi tana kuka tace"kuyi hakuri ku yafemin"


Sunata kuka akajata akai prison daita,



Samm fahad yakasa natsuwa hukuncin be masa ba ya daga karai cikin kwana ukku kacal ,


Umma taita fada shide he can't forget mommy alheri ,haryanzu gidansu faseelat ba natsuwa,


Bayan 7days akashiga wata kotun nan kuma aka yankewa mommy hukuncin 1yr ko tabiya30 billions ,


Hakan yayiwa fahad dadi anagamawa suka rungume mommy shida kannenshi sunata kuka,



Umma kam taji haushi aida yabari taje taga rayuwar gidan yarin da yadda take takara tsoron Allah,



Bayan 3days fahad yabiya kudi aka sako mommy tadawo gida tana jin son fahad fiyeda yaranta,



Aka biya fahad kudinsa 50millions dollars,


Aka amshe kudinsu oteka aka bindigesu ,die hard kuma yana prison yayi joining musulunci yana cigaba da istigfareee,



Sabeer de yasamu aiki a marocco ,daddy ya samarwa fahad aiki a abuja awani diamond company amatsayin accounter donme matsayin ya rasu shi yasamu,


Mommy kullum kunyar fahad takeji abunda ta masa ganin bayanunawa yasa ta saki jiki itama,



Jarabawar data samu fahad tazama alheri agareshi domin kudin da yarasa ya samu linkinsu gashi yasamu wani aikin Wanda yafi nada.




Post a Comment

0 Comments