TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

RAGON MIJI PAGE 83

 8⃣3⃣






*dedicated to me dambu,kinasani jindadi walle ,comment dinki nasani dariya sosai nagode Allah yabar soyayya😘me dambures🤣azubo mana idan ya gama turara 😂,*






*manzon Allah (S. A. W) yace wanda yaje wurin boka ko dan duba Kuma ya gasgata shi  hakika ya kafirta abunda aka saukarwa manzo (S. A. W)* muslim

👇🏼

*Manzon Allah (S. A. W) yace wanda yaje wurin boka ko dan duba ya tambayeshi wani abu bazaa karbi sallar shi ba ta kwana arbain* Muslim 





*adede wannan gabar dole ne nayi kira ga yanuwana mata, mata! Mata!! muji tsoron Allah musani cewa duniya ba matabbata ba ce, mu gyara halinmu mu gyara zukatan mu,manzon Allah (S. A. W)dama yace mafi yawa acikin wuta mata ne, meyasa bamu aiki da ilimi da hankali meyasa wasunmu basuda imani?saboda namiji kin yarda musulunci kin tuge imaninki sister kin shirya zama cikin wuta ko? zaki iya kisa saboda namiji ,yanzu haukan har mijin kashewa ake anya anya munaso mugama da duniya lpy kuwa ?kin watsa mishi ruwan zafi kin cire mai 🍌wata ta mishi yankan rago kin yanka jariri, kinyi zina, kinyi madigo kai tirrrr wlh ,mata idan har bamu gyara ba tun anan duniya semunga sakamako, zakiiya  zuwa wurin boka kisa aiwa kishiyarki kurciya ko akasheta don kisamu miji,ko mijinku yana bakin kokarinshi wurin yi muku adalci kisa a juya tunanin shi yadawo sonki ke kadai saboda zalunci kirika juyashi son rai, ko mijinku baya muku adalci kikaishi yadawo ke kadai yakeso su sauran suma yadena musu anya muna son kanmu kuwa? Meyasa bazamu rika yiwa mazajen mu addua ba? Akan surika adalci, meyasa baza muyi hakuri ba akan jarabawar da muke fuskanta kinsan ladar da Allah yake rubuta miki saboda hakurinki? Baki sani ba amma seki kwashi kafa ki tafi wurin katon kafiri neman biyan bukata kin yadda imaninki kin Yi shirka, saboda namiji shi adalci ne beyi muku ba, kuma Allah baze barshi ba seya fiddawa kowacenku hakkinta sannan ranar kiyama zetashi da paralyzed,to shifa paralyzed ze tashi daita maybe Allah ya mishi rahma ya tafi aljanna ko yasamu ceto awurin manzon rahma, kefa? katuwar kafira mushrika me hada Allah dawani direct wuta kikai hjy ,domin Allah baya yafe shirka idan kinmutu akanta sede yakan iya yafe miki in kin tuba idan yaso, to kinada tabbacin zaki kai lokacin tubar? idan kika mutu agun bokan fa kafin ma kibaro wurinsa?idan kika mutu kafin ki tuba fa? To inamiki albishir da cewa ke yar wuta ce, idan har baki tuba ba ,maza ki tuba kafin lokaci ya kure miki, maza ki koma ga Allah kafin malaikan mutuwa yazo gareki, duniya mun dauketa kamar zamu dawwama acikinta,mundena Tuna lahira munata aikata aika aika kuma kina tunanin Allah ze miki rahma dan bacewar basira, idan aka tambayeki ma huwal iman cewa zakiyi laadari,bakiiya komai daga addininki ba amma kin iya biyar malamai da bokaye,abu daya kikarike (innallaha gafurur rahimm)inbaki tuba ba fa hjy? Ko ahakan kina tunanin shiga aljannar, kishin me? duniyar kanta Nawa take dukkanta ,donme baza mu hakura mu koma ga Allah da bukatun muba shine me biyan bukata ba wani ba, Allah(SA) yace bakomai bace rayuwar duniya se lokaci kididdigagge, bakomai bace  duniya se rayuwa yar kadan , yace rayuwar lahira itace rayuwa , ya kuma cewa kafirai kuji dadi kadan sanan makomar ku wuta ce kuna me dawwama acikinta*


*ya Allah kakaremu daga aikata kowane sabo ka kara mana imani da tauhidi da tawakkali ya rabbul alamin*😭


*Allah yace mutuwa zata zo muku kuna masu shagaltuwa da duniya sekuce ya Allah ajinkirta mana se yace Allah baya jinkirtawa bawa idan waadinsa yayi*


*mu tuba kafin ranar da hannuwanmu da kafafuwanmu zasu bada shaida akan abinda muka   aikata,ranarda zaa bijrowa kowace rai da abinda ta aikata,aranar ne kafirai zasu rika kuka suna cewa amedosu duniya zasu aikata aikin kwarai*



*Allah yace wadanda sukai imani kuma sukai aikin kwarai zamu sakamasu da aljanna koramu na gudana daga karkashinta suna masu dawwama acikinta ladar abinda suka kasance suna aikatawa,yace sune wadanda sukayi hakuri kuma ga Allah kadai sukai dogaro*




*mudage mu zama daga cikinsu yanuwa cikin wadanda hakurinsu da dogaro da Allah ze kaisu ajanna*






Hawaye cikeda idonta batare da tabari sun zuboba tace "nabaka kwana bakwan in ma bata samu sauki ba zakaiya wuce haka na amince"


Ya fiddo ido yace "dagaske? "


Tace "eh na amince"


ya rungumeta yace "nagode Aisha Allah yakara miki hakuri yakara rage miki kishi ya barmu tare har gobe kiyama"


tace "amin" tana yatsina fuska tade amsa ne kawai amma bawai don tana so ba, 


Ya fara aika mata da kisses tai lamo tana jinshi yagama kidansa da rawarsa ya rungumeta har bacci ya daukeshi ita kuwa idonta biyu takasa bacci hawayen da batai ba seda tayisu zuciyarta na zafi ta tashi ta sha magani takoma ta kwanta har bacci ya dauketa, 



tunda asuba da yayi wanka ya fita masallaci yana dawowa be kara komawa dakinba ya na dakin faseelat koda yafada mata Aisha tabar mata kwana 7 yake kawai tayi amma tasan Aisha bazata iya barin mata ba hakanan dole ranta beso ba tabayar,


can da rana zazzabin ya sauka, tace"hero muje falo mana mudanyi kallo kafin zazzabin yadawo yaushe rabon da na ko leka shi "


yace "angama sarauniya acikin zuma, yawwa dan Allah atemakamin plsss yau 1month inagani sede nahade miyau tunda yanzu da sauki kidan budamin kafin jikin yadawo I'm very sure da daddare bazan samu ba"ya kwabe fuska 


ta yunkura ta tashi daga kan bed din tafara tafiya majestically yabita da kallo tana cikin tafiyar takusa kai kofa tace "nagudu dan yanzunnan duk yar lpyar dana samu seka kwasheta duk ruwan dake jikina se sun kare kan kabarni.."


bata rufe baki ba taji ya rungumeta ta baya ya dagata sama yana dariya yace "niba ruwan da lpyar dazan kwasa keda zan temakawa in kara miki ruwa da fresh milk medadin gaske "


Faseelat tana dariya tace "plssss banaso kabarni nayafe dadin nan"


Aisha tazo kiran fahad lunch taji sunata gaggabar dariya, 


zuciyarta na harbawa ta juya daki idonta cike da hawaye, azuciyarta take magana "wai wannan ce zaace ma marar lpy tana ta kwasar dariyarta ahakan ciwo take, sunata soyewarsu a matsayin jinya ni ina kwasar aiki da bakin ciki ,bazan iyaba tafiya ta zanyi "hawaye suka wanko mata a fuska ta kwashesu da hannu ,ta bude wardrobe tasa hijab ta fita daga gidan, 



suko sunsha dariyarsu da wasanni don kan bed suka koma hardasu jefe jefen pillows da bugu da wasa, 


suna gamawa suka fita shi yawuce dining ga kuloli nan amma ba Aisha yahau yashiga dakinta be ganta ba yafita har garden koina bata, yayi tsaye yarike kugu yasande tana gidan mommy to meyasa bata fadamishi ba? ya daga kafada ya koma wurin faseelat beko ci abincinba, 



Aisha na shiga gidansu tafita daga mota da gudu tana kuka tashiga gida, 



Mommy tai zaman dirshan kasa sadiya auta na kwance kan cinyarta Tanai mata tsifa Aisha ta shigo tafada jikin mommy tana kuka, sadiya tai wuffff ta tashi zaune, 



mommy na raba ido tace "Aisha menene kuma kede matsala bata karewa daga gareki "


Aisha numfashinta na sarkewa take magana "mommy yaya yadena sona yadena kula da rayuwata, faseelat ciki ne daita yaya namin gori yana fadamin ina bakin ciki nake daita "tafashe da kuka tacigaba da kuka tace "mommy yaya yazo yace nabashi kwanaki har seta samu lpy ze dawo gareni gabadaya hankalinshi yana kan cikinta kuma lpyarta lau wlh "


Mommy ranta bace take kallon Aishar,tana dasa aya tace "ubanshi yaci uwatai ita me ciki harwani lokacin lpy ne daita, saboda tana da ciki seya ida kashemin  ke, dan ubanki meyasa baki fadamin tuntuni ba seyanzu "?



Aisha tana ta kuka tace "baniso in tayarmiki da hankali ne mommy shiyasa nai shiru"



mommy tace "aiko shegen cikinnan baze zo duniya da rai ba share hawayenki kingama kukan bakin cikin shi daga yau wlh "


"Ke sadiya tashi daukomun waya ta daki", 


Tatashi ta tafi sama dasauri, Aisha nata ajiyar zuciya hawaye na kara zubomata mommy tace "shi har yaisa ya miki gorin haihuwa shegen cikin ze bare kuma dole yarabu da shegiyar nan"



sadiya ta dawo da waya hannunta ,mommy ta latso number anty salma takara akunne tace "auta kishirya wurin katon boka nakeso kikaini kowani jibgegen malami wanda dana fadi bukata ta tagama biya "


anty salma tace "tofa anty lpy meyafaru? "



Rai bace tace "kome ma yafaru fahad so yake ya kashemin Aisha kawai wai dan kishiyarta nada ciki shine yake mata gori harda cewa tabarmishi kwanakinta wlh bazan bari ba wannan karan kishirya gamunan zuwa"


anty salma tatabe baki tace "ai dama zuba maku ido nayi tuntuni yakamata ace anwuce wurin base yanzu ba da Aisha tagama wahala, niko keda malaman da zan kaiku gunsu aiki kamar yankan wuka, akwai boka gumurzun duniya ya kware da aikinshi ga lasting, akwai malan halilu megani har hanji kina zuwa ze biya miki bukatunki cikin sauki "


Mommy tace "gamunan tafe nagaji wlh ni kaina abun yana affecting dina some time bana barci idan nakira likita yana fadamin jinina yahau sede munzo "takashe kiran, 



Aisha najin abinda tace tai tsit ita gabadaya hankalinta ya gushe mijinta kawai takeso yadawo gareta ta kowane hali, 


Sadiya datun dazun take zare ido tace "mommy bade wurin boka zakuba?"


Mommy na harararta tace "can muka nufa ko sadiya "



sadiya tace "mommy kinsan fa Wanda yaje wurin boka yayi shirka kamar hada Allah da wani ne, kuma fa bukatunku bazasu biya ba seya so, meze hana anty takara hakuri kuyita addua in ma wani asiri aka masa seya kare amma karkuje wurin boka plss mommy "



mommy tace"ke sefa munje sena kwato mata yancinta duk wa yaja inba itaba danubanta inata bata shawara taki dauka, tunda nake ko malamin zaure bantaba lekawa ba amma yau dole ne se munje wlh "


sadiya zatai magana mommy ta kai mata bugu, ta janye tana tunzuro baki, 


mommy tace "sena ci ubanki da shiga maganar manya tashi kidaukomun gyalena ke Aisha da jikka ta ki duba a closet ki daukomun rapar 1k guda 3 tashi maza "



Aisha ta tashi tana share hawaye ta haye sama jim kadan tafito da kayan tabawa mommy tasaka suka fita, 


Suna fita sadiya tafashe da kuka tace "Allah yaganar daku gaskiya"


Basu tsaya koina ba se gidan salma suna shiga ta sabo mayafi suka fito a motar ta suka nufi gidan boka gumurzun duniya suka lula kamar zasu tafi jibiya sannan sukabi hanyar datayi dankama suka cigaba da tafiya, 


Sunayi suna labari mommy tace "inta haihu aini nabani bare inta haifi namiji shikenan ita zata cigaba da ruling gida in ita wannan banzar bata kara haifuwa ba shikenan natashi atutar babu nayi renon banza"


Anty salma tace "ki kwantar da hankalinki anty kome yazo karshe"


Sunata tafiya suka tsaya a bakin titi suka sauka sukabi wata yar karamar hanya tundaga kan titin kana hango rufin bukkar bokan, bawata tafiya sosai suka iso wurin yana bakin bukkar wurin ba rufi amma bakikirin yake kamar anyi rufin kwano gawani mugun wari dake tashi gawasu layu da kawunan  dabbobi gefenshi, tunda suka tunkari wurin suka rikajin ihunshi da maganganun shi da bakaken aljanu wadanda yake musu hidima su kuma suna biya mishi bukatocinshi,


dukkansu ba wacce ta tsorata har gara mommy danshi kanshi bokan abun tsoro ne shirgegen kato ne baki wulik daga shi se dan bante ya rufe kugunshi, 


Anty salma ta bude baki tana fadin "gafara de gafara de,"



Suka zo zasu zauna gabanshi nesa dashi, 


Tunkan su zauna ya kwasa masu tsawa dukkansu seda suka tsorata muryarshi na amo yace "Allah ya gaza? Ya gaza ne "?


Dukkansu suka rika gyada kai suna fadin "eh yagaza"


ya kwashe da dariya yayi yan surutanshi da aljanu dawani kalar yare, 


Duk suka samu wuri suka zauna, 



boka ya kallesu daya bayan daya idanunshi kore kore yellow yellow yanata zaresu, ya nuna Aisha yadaka mata tsawa yace "me kkso a musu?"


Aisha ta girgiza ,jikinta na rawa tace "so nake a zubar da cikinta asa mishi tsanarta amma karya saketa yanzu harse ta kamu da ciwon zuciya"


boka ya babbake da dariya "hahahahahahahahaha bukatarki zata biya yarinya amma dan dukununu nason ganin tsiraicinki aljani betau yanason shan maniyinki,aljani mugu yanason ya sadu dake daganan kuma bukatarki tagama biya har'abada hahahaha "


mommy ta zaro ido waje jikinta yana rawa ta kalli salma ta banka mata harara, 


Aisha zatai magana mommy tai karaf tace "muna zuwa boka zamuyi shawara"


Yayi ta dumumuwanshi kamar beji taba yanata juya hannuwa, 



ta wurga musu harara duk suka mike suka bar wurin seda suka kai gaf titi, mommy ta kalli salma tace "amma wlh salma bakida hankali kirasa wurin wanda zaki kawomu se wannan bakin arnen wanda in ance rabonshi da wanka yafi shekara baa gardama ,ahakan ze kwanta da diyata wlh batayiwu wa dan nasan duk cutukan duniya babu wacce bazaa samu a jikinshi ba "


Salma tace "aa anty bawani ciwo kuma seme dan ya kwanta daita inde bukata zata biya Allah anty aikinshi na lasting wani lokaci mutu karaba"


Mommy tace "keni inason diyata ban shirya ganin gawarta ba bazan bada ita shida aljanunshi suyi wartambe da jikinta ba wancan katon idan yahaye ta na tabbata seta ji kamar bata taba sanin namiji a rayuwarta ba "



taja hannun Aisha tace "mutafi wurin dayan mugani"


Aisha ta riko gyalen mommy tace "mommy kibari plssss "


Mommy ta balla mata harara tace "inbari wancan laanannen Allan ya tumurmusheki? Lalle bakida hankali Aisha nida sauran hankali na"


Taja ta da tsiya suka shiga mota suka bi ta ring road sunata tafiya seda suka bullo cikin batagarawa suka kutsa kai can ciki can wata unguwa daba mutane sosai se daidaya suka faka bakin wani gidan bulo, 


suka firfito salma nagaba tanajin haushin mommy ta bude labulen dake wani daki awajen gidan suka shiga, 



wani dattijon mutum ne zaune da katon tray da kasa cike dashi ga casbaha yanaja zut zut kai kace ba abinda yake fada casbahar kadai yake ja, 


suna shiga yadago yabisu da kallo da daidaya, 


suka samu wuri suka russuna, 



Sukai tsitttt, ya dukar dakai yayita jan carbi sannan ya dago ya kalli aisha yakura mata ido yace "mijinki yafi son amaryarki, yanzu tanada ciki yakara fifitata akanki?"



Aisha ta girgiza kai kamar kadangaruwa, 


yasa yatsa yafara zane jikin kasar yace "ba'ita ce ta kashemiki diya ba dodon matsafa ya bukaci jininta suka bashi, bataiwa mijinki komi ba sonta kawai yake, me kkso a mata? "


tace "so nake yaji ya tsaneta sannan azubda cikin jikinta kuma data kamu da ciwon zuciya ya saketa"



ya cigaba da rubutu yana jijjiga kai, 


mommy de shiru tayi wato Aisha seta dau fansa takeso ya saketa lalle Aisha ta azabtu sosai, 



bayan lokaci ya dago yace "ze tsaneta bazeso ko hada ido daita ba, sede cikin jikinta baze zubdu ba saboda tana adduoi kuma cikin na yan baiwa ne dole se sunzo duniya sede akwai mafita idan cikin ya tsufa yakai watan haihuwa zakizo nabaki wani magani data fara nakuda ki mata turarenshi cikin kwana ukku yaran zasuyita ciwo su mutu su duka "


Aisha ta daga kai alamun ta yadda, 



ya bude wata kwarya dake gefenshi ya dauko magani daya tallin tall kulle a leda ya mika mata jiki na bari ta amsa, 


Yace "da kinkoma Gida kiyi turarensa akoina acikin gidan ki tabbatar ya shaki hayakin kafin awa biyu dayinsa daganan kuma aikinki zefara "


Mommy tace "mungode sosai tome zaa bada? "


Yace "zakubada 100k idan wata takwas sukayi zata dawo ta amshi cikon maganinta"


abun yawa mommy sauki da yawa, ta zuge zip na jaka ta fiddo 200k ta ajiye agabanshi tace "ga wadannan idan aiki yayi kyau yaran suka mutu zan kawo maka wasu 200k din "



malam yace "da kyau se kundawo"


Suka tashi suka fita sunata godiya, 



Suna fita mommy ta kalli salma tace "keda kinsan wannan yafi sauki kika kaimu can? "



Salma tace "Ai kuma waccan aikinshi yafi lasting kuma dashine har cikin seya zube amma wannan ma semujira lokacin da yace "



Aisha na murmushi tace "nagode anty "


anty salma ta harareta tace "shasha seki meda hankali kiyi yadda yace, kuma kita abubuwan da shegiyar zuciyar ta zata buga karshen ciwo ma"


Aisha tai dariya suka hau mota sunata labari suka koma gidan anty salma daga nan suka dau motarsu suka wuce gidan mommy, 


Lokacin marece yayi sosai acan gida faseelat suna zaune da hero a main falo tana jikinshi da shagwaba tace"hero ice cream vanilla essence plss "


yace "akwai fa acikin fridge bari na dauko miki"


Tace "nide bashi ba vanilla nakeso"


Ya dafa cikinta yace "baby kacika shan sanyi ka rage kar mura takama minkai"


faseelat tai dariya tace "yaji plsss yanzu nakeso sena sha nakejin dadi"


Yace "bari nafita na siyo miki bayanshi seme? "


Ta langwabe kai tace "mutafi tare mana kaga senaga wani abun danikeso din "


yace"bafa ki lpy honey kiyi zamanki"


tace "nide senaje "tai kamar zatayi kuka, 


yace "no don't cry bari na daukomiki hijab "


ya hau sama ya dawo da hijab tana zaune yasa mata yakamata suka fita, 


Suka shiga mota se oasis bakery ,


suna fita ya bude mota yafita yabude mata murfi tafito tana mai murmushi tace "thank you "


suka jera yana rike da hannunta suka shiga ciki, 


khalil da yaje siyo musu bread da zasuyi breakfast gobe,yana ciki a upstairs sukuma suna down, 


suna shiga tafara dube dube abinda ze burgeta bayan ice cream din, 


sega khalil ya sauko seya hangeta, ya kura mata ido tsohuwar soyayyar da yake mata tuni ta dawo, 


faseelat batasan dashi ba tana juyowa taganshi, yana payment, ta kalli dressing dinshi yana cikin maroon yadi black hula da takalma black kayan sun masa dede batasan lokacin da murmushi ya kwacemata ba, sannan tai sauri ta juya wurin fahad dake mata magana ita kuma hankalin na wurin khalil da yayi sororo yana kallonsu ganin hannunta cikin na fahad, 


fahad zuciyarshi cunkushe yanata kokawa da kishin dake cin shi, 


dandanan faseelat ta waiga ta kalli khalil gaskiya she's happy yadda rayuwarshi ta sauya, 


khalil yaji yakamata su gaisa ya doso inda suke faseelat na ganin yataho ta daburce gabanta na faduwa, 


Har khalil yazo gabansu da murmushi kan fuskarshi ya mikawa fahad hannu su gaisa, 


Zuciyarshi na zafi memakon yabashi hannun seya wanka mishi mari 


wanda seda khalil yakusa kifewa, idonshi jawur ya dago yasa hannu ya shafo gefen bakinshi yaga jini, ya meda kallonshi ga fahad daketa huci, ya kuma Kalli faseelat tana ta girgiza kai, 


Be wata ba ya kaiwa fahad naushi a hanci nan take se jini yafara zuba,kobin jinin dake zuba jikinshi beba da zafin da yakeji yakara wankama khalil mari, tassss khalil ya rama, 


Faseelat tafashe da kuka mutanen dake wurin suka taso suka ririkesu suna basu hakuri, 


khalil ya fita daga wurin batare da yabibiyi ledar bread dinshi ba, 


rai bace fahad ya jawota kiiiiii suka fito daga wurin ya buda mota ya wurgata ciki ya rufe ya zagaya ciki ya zauna, ya fiddo handkerchief yana goge jinin dake kara fitowa daga hancin shi, 


faseelat nata kuka ta matso zata rike mai kai cikeda tausayinshi, 


Cikin fada yace "karki tabani munafuka ina tare dake ma amma kina yiwa wani murmushi, marar kamunkai banza ballagaza sokuwa"yanata goge hanci yake maganar


tanata kuka tace "call me with every name hero amma wlh ba abinda kake tunani bane wannan shine khalil tsohon mijina"


kalmar tsohon mijina ta tabashi yace "kinsan kina sonshi meyasa kika rabu dashi?kika zo kika shiga rayuwa ta kika sani dole nafara sonki,meyasa baki tsaya gareshi ba tunda u love each other"


takara volume na kukanta tace "wlh bahaka bane ni kai nakeso...."ya katseta da tsawa" kimin shiru"


tai shiru tanata kallonshi yatada mota dagudu ya doshi gida, 


daga gidan mommy Aisha ta dauko motar ta tadawo gidan tana ta murna, tunda tashigo taji gidan tsit taje kofar dakin  faseelat takasa kunne taji tsit, tace "to ina sukaje? "


tace"amma hakan ma yayi bari nazo nai aikina kafin sudawo nasan kafin Maghreb dole su dawo, 


jiki na rawa tashiga daki ta ajiye gyale da waya tafito da maganin taje falo ta jona burner dandanan tai jawur ta zuba maganin kaffff dandanan hiyaki ya turnuke gidan ga kauri dagaji anhada tsurface tsurface dayawa aciki, 


ta zare wayar tarika yawo dashi tana turara gidan tana ta murmushi ,


harta gama shiru shiru basu shigoba tace "nabani karsuki shigowa fa "tana ta duba wall clock, 


taji budewar gate tasaki murmushi ta tashi ta haye sama, 


fahad na ajiye mota yabude yafita dasauri ya shige gida ranshi bace ba bismillah bakomi, 


Yana shiga tsakiyar falon yaji kanshi na juyawa, yayi tsaye wuri daya ya dafen kan yana yamutsa fuska, 


faseelat ta bude tafito tanajin juwwa na daukarta saboda kukan data sha, tana kuka tashiga gidan yana tsaye yaba kofa baya taje bayanshi tana kuka tace "Dan Allah Hero kayi hakuri bazan sake ba "


yayi mata shiru yanajin maganarta kamar kukan jakai, 


ta dawo gabanshi tana kallonshi hawaye na zuba tace "kayi hakuri Dan Allah kadena fushi dani, banjin dadin ganin fushinka naci albarkacin cikin dake jikina "


yanzu a duniya ba halittar daya tsana kamar ta, ganin ta yake kamar karya agabanshi tana mishi haushi ya tsaneta he hate her like hell bayason ganinta bare jin maganarta, 


ta bude baki zatai mishi magana ya dauketa da gigitaccen marin da seda  ta zube awurin a sume, yaja dogon tsoki ya haye sama yashiga dakinshi, dashi ma yasha turare ya wuce toilet yana wanke fuskarshi da jini yabata yanayi yana kallon madubi seyakeji kamar bashi ba, 


faseelat dama gata sauran ciwo tananan kife cikin hijab se 7:5  Aisha tafito tanata rera waka ta Abdul d one "kasani aranka kar infita inka barni abaya zansha wuya"


Tun kan ta sauko daga step ta hangi faseelat kife, ta tabe baki takarasa wurin tana tsaye tace "ke!!! Ke!!! "taji tsit, 


ta duka ta dagota taganta sume tace "innalillahi ba yanzu ba my kishiya ina son ganinki a raye "


ta aje ta ta ruga da gudu ta dauko ruwa tazo ta sheka mata, 


faseelat ta farko da tari da kuka hawaye masu zafi nabin fuskarta"


Aisha tai fuskar tausayi tace "sannu faseelat meyasa meki ne haka"?


batace mata komi ba tatashi tana dafe da cikinta ta haye sama zuwa dakin hero dinta.

[9/6, 3:52 PM] Ikra Rukayyat: ➰➰➰➰➰




Post a Comment

0 Comments