TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

RAGON MIJI PAGE 75

 7⃣5⃣






*page dinkune yan group dina shalele novels group, kai jiya kun matukar burgeni wannan ruwan comments haka, naji dadi sosai Allah yasa ku dore 😍*



Ba wuya ya gane shagon shi ya shiga ciki da sallama bakinshi, 


Shagon ba kowa ciki don safiya ce mutane basu fito ba, abba ya amsa sallamar yana kallon sabeer, 


Sabeeer yaja bench ya zauna acikin ladabi yace  "abba ina kwana ya mejiki? "


Se sannan abba ya gane ba siyayya yazo ba yace " lpy lau dasauki "


Sabeer ya kara sunkuyar da kai yace "abba ni abokin fahad ne aminina ne sosai, nazo ne nakara baku hakuri akan abinda yayi wlh yayi nadama sosai yana cikin tashin hankali yanzu haka ma baya lafiya, Dan Allah abba amishi hakuri kar a rabasu domin yana sonta sosai kishi ne ya rufe mai ido har ya mata haka "


Abba yayi murmushinsu na manya yace "u only know about ur friend, yayanta da kannenta suna nan suma duk basajin dadi atare suke jinyar, kishi ai bahauka bane daze mata irin wannan dukan haka, don kishin ma nada kyau manzon Allah (S. A. W)cewa yayi wanda baya kishin matar sa baze shiga aljanna ba, amma shi nashi yawuce akira shi kishi gaskiya "


Sabeer yace "Dan Allah abba kuyi hakuri kudauki wannan abunda yafaru a matsayin kaddara "


Abba yace "mun dauki kaddara kam amma seya saketa "


Sabeer yace "kuyi hakuri dan Allah wlh duk gidannashi ya birkice rashin faseelat, shiba lpy matarshi ma yarshi ma, Dan Allah kuyi hakuri tunda yagane kuransa nasan nan gaba baze sake ba "


Abba yayi shiru sabeer ya cigaba da bada hakuri, 


Jim kadan abba yace "nifa nadade da yafemasa tunda ya sameni batun saki kuma bani zebawa hakuri ba seyabari idan alhaji yadawo daga Niger yaje yasameshi idan ya yafemishi shikenan danni haifuwar yara na kawai nayi amma alhaji yafini son su yafini kula dasu danhaka nabar masa ragamarsu seyajira shi har yadawo nanda kwana goma "


Cikin ran sabeer yace "tirkashi yo shi yana kai kwana goman ma "


Afili yace "to nagode sosai abba Dan Allah ina rokon alfarma abani address na asibitin da faseelat take ,wlh yar shi ma kullum kuka takeyi tanason ganin antin ta atemaka Dan Allah "yayi kamar maroki, 


Abba ya yamutsa fuska yace "nan ne asibitin turai room 9"


sabeer yace " nagode sosai abba ina kuma kara baku hakuri akan abinda abokina yayi "


abba yace "bakomi "

Sabeer ya mishi bankwana ya tafi, 


direct gidan fahad yawuce, Aisha ta budemai yashiga yana shiga dakin da fahad yake ya zauna gefen shi ya furzar da iska ya dan bugi fahad yace "katashi muyi magana "


fahad ya yamutsa fuska jikinshi na fidda wani irin suraci yace "komi zaka fada kafada inajinka kaje baka samesu ba ko? Bashi ne maganar ba "


Sabeer yaja tsoki yace "to wlh zanyi tafiya ta in baka tashi ba nasameshi har shagonshi nabishi amma zan tafiya ta "


fahad ya tashi yana yamutsa fuska yace "inajin ka "


sabeer ya kalleshi duk yadda ya koma yace "look at you hmm, na sameshi nabashi hakuri sosai yace shide ya yafe amma seka saketa da nai ta bashi hakuri yace shi yahakura sede kajira yayanshi da yatafi Niger  har yadawo kabashi hakuri in ya hakura shikenan yacemin nanda kwana goma ze dawo "


fahad ya tabe baki yace "kafin kwana goman na mutu ai ,wlh ina cikin hali zuciyata ciwo takemin kamar zata buga"


sabeer yace "kai kasani ai kana mutuwa ni kuma nasamu mata "


fahad ya wurga mai harara sabeer yayi karamin murmushi yace "eh mana ko haramunne?"


fahad ya koma ze kwanta sabeer yace "jira mana inada good news bayan bad one's nasamo maka asibitin da take da room number "


fahad yafasa kwanciyar yace "wace asibity room nawa? "


sabeer yace"turai room 9"


fahad naji ya yaye duvet din yatashi tsaye Aisha na gefe na kallon ikon Allah, 


ba bata lokaci ya bude wardrobe ya dauko jallabiya ya zira ya dauki key din mota yayi hanyar fita ,


sabeer yace " kai malam bazaka tsaya muida maganar ba? ko godiya aikatsaya kamin "


fahad ya juyo yace "thanks ,kuma kafitomin daga dakin mata "ya juya ya bude kofa yafita yana sauri, 


Sabeer yayi murmushi ya girgiza kai ya tashi tsaye, ya kalli Aisha yace "Allah yabashi lpy ni natafi aita hakuri lokacine "


Aisha batace komi ba, ya fita, 


Koda yafita har fahad yabar gidan ya shiga motarshi ya nufi office, 


fahad yayi ta sharara gudu cikin mintuna kalilan yaisa turai yana tafiya ahankali jikinshi ba kwari har yaisa kofar dakin, 


nan kuma gabanshi yarika faduwa yayi knocking so biyu omer da tunda yazo duba faseelat yakasa tafiya saboda yadda ya ganta yana zaune yana bata abinci yace "turo "


Jiki mace fahad ya tura kofar dakin yana shiga yaga faseelat jikin omer ,zuciyarshi tayi mummunar bugawa, (ana nanfa me hali.....) dasauri yafara a'uziya yana korar shedan aranshi 


Faseelat idonta a lumshe suke itakadai tasan yadda takeji abubuwa Sun jagule mata ba ciki ba fahad ga ciwo, kamshin fahad daya kewaye dakin yasa faseelat ta bude ido ta ganshi tsaye kamar bashi ba duk ya rame ya jeme yayi wani iri, tausayin kansu yakamata ta meda ido ta lumshe, 



kallo daya omer ya mishi ya daure fuska tamau, 


fahad yasamu yakara dedeta kanshi ya karasa ciki, 


Ya mikawa omer hannu, omer yabashi sukai musabaha kowa ya zare nashi, 


Omer ya dauki spoon yakara kaiwa setin bakin faseelat  ,ta kauda kai idonta lumshe, 


Omer ya kwantar da ita ya ajiye cup din yafita don in yatsaya bazaa kwashe lpy ba, 



Bakowa dakin domin ummi tafita, 


fahad yakarasa bakin gadon da faseelat take kwance yana kallonta tayi muguwar rama tayi fayau, 


Faseelat kam taji dama da taganshi amma bataji dadin yadda taganshi duk yafita hayyacin shi ba, 


Fahad Ya zauna kan bed din yanajin matsanancin tausayin ta ya dora hannu akan cikinta , yace "I'm sorry honey I hurt you, na rabaki da farin cikin ki I'm very sorry kiyafemin " hawaye suka zubomai ,


faseelat bata bude ido ba tai shiru se takara jin kewar cikinta don tunda yana 3wks yafara mata motsi, 



Fahad ya riko hannunta ya rungume a kirji ya saki kuka, tabude ido tana kallonshi ba tayi shiru dan tanajin haushin shiba ne tayi shiru ne don kartai magana tayi kuka don inde tabude baki kuka zatai, ganin yana kuka yasa tafara hawaye, 


irin muryar marassa lpy tana hadiye kukanta tace "hero kadena kuka,bakamin komi ba, nasani acikin tunaninka bazaka yimin haka ba,kayi hakuri kashare hawayenka banajin dadin ganinsu"


fahad yanata kallonta da jikakkun eye lashes dinsa tunda tafara magana ,yace "we lose our baby "


faseelat ta lumshe ido ta bude tace "Allah ze bamu wani,  kadena damuwa "


Fahad be dena hawaye ba na tausayi da kaunar faseelat yariga yasan tana sonshi sosai yanzu dabata yi fushi dashi ba sonta yakara ninkuwa a ruhinshi, 


faseelat tace "stop shedding ur tears pls, har yanzu inasonka mijina nayi kewar ka sosai, kewarka tafi ciwon jikina zafi amma na samu lpya da naganka "tasakar mishi murmushi, 


Ya share hawayenshi ya duka ya mata kiss a wuya yace "I miss you too kidubeni yadda sonki ya medani ina wahala honey "


faseelat tai murmushi tace "I'm very sorry ina Princess?ina anty I hope suna lpy "


Yakai hannunta dayake rungume dashi abaki ya mishi kisss yana karajin sonta yace "Aisha tana nan lpy, princess bata lpy, yanzu haka bata gida don tsoro na takeji saboda halin da ta ganki aciki, kiyi hakuri honey wlh bansan nayi ba bansan meke faruwa ba sede naganki cikin jini "


faseelat ta lumshe ido tana tunanin yadda yashigo toilet din ya fincikota, tace"i known kadena damuwa na yafe maka since,yakamata ka kawomin amira naganta kona ida warwarewa ina kewarta da surutun ta "


Yace "zan kawomiki ita meyasa baki fushi dani ba ?"


Tai murmushi tce"yazaai na iya fushi dakai, kaine rayuwata hero ina tsananin sonka bazan iya rayuwa in babu kai ba "


Yana tausayin kansu yace "gashi zasu rabamu abba is asking for ur divorce paper ,yan uwanki duk basu son kici gaba da zama dani "


faseelat ta dan bata fuska jin abinda ke faruwa tace"bazasu rabamu ba don inasonka sosai ka kwantar da hankalin ka ni takace, taka kai kadai my hero,u r my everything we will be together forever "


fahad yayi shiru yana aika mata da wani kallo me kashe jiki, itama ta rika aika masa da nata sihirtaccen kallon da murmushi kan fuskarta dukkansu Sun manta aina suke, 


ahankali fahad yake kasa da fuskarshi zuwa tata, har fuskokin su suka hade suka rika kissing juna passionately, dukansu sunajin matsanancin dadi,



Ummi da taje dubo diyar wata kawarta data haihu ta dawo omer har ya tafiyarshi yabar asibitin gabadaya, batare da tasan abinda ke faruwa ba ta tura kofar dakin tashiga, abinda tagani ne yasa ta fiddo ido waje, faseelat na kwance fahad agefenta azaune ya sunkuya har yadan danne ta sunata kissing bakunan juna a dimauce faseelat hardasa hannu tarike mai kai don duk sunyi kewar juna, 


ummi batasan lokacin da bakinta yafara hailala ba "Lailaha illal lah Muhammadur rasulillah (S. A. W) 


tun kan takarasa faseelat ta Saki kan fahad, ya tashi zaune ya sadda kai yana sosa keya, itako faseelat ta rumtse ido, 


kafin ummi tai magana umma ta turo dakin da faraa da sallama bakinta, 


Taga fahad zaune gefen faseelat ga ummi tsaye hannunta kan bakinta da alama yanzu tashigo, 


Umma tabata fuska tace "kai me kakeyi a nan?  "


fahad ya dago ya kalli umma ya kara sadda kai kasa, 


tace "tambayarka nake me kk anan da ba kasheta kaso kayi ba "


fahad yayi fuskar tausayi yace "umma nazo dubata ne, bawani abu ba "


tace "to tashi kafita tunda kagantan"


Fahad ya kalli faseelat da har lokacin idonta ke kulle tanajin matsanan ciyar kunya ya tashi ya fita yanajin kamar yayi kuka, faseelat jitayi kamar tajawo shi ya dawo ya zauna dan zamannan nashi setaji har karfin jiki tasamu, 


yana fita umma taja tsoki, har lokacin ummi na tsaye da hannu abaki, umma ta kalleta tace "se hakuri yaran zamani basu da kunya kokadan"batasan ma abinda sukayiba zaman shin agadon kadai ma taga bedace ba, 


Aran ummi tace "aini naga dahirrr"


umma takarasa ta ajiye kulas dake hannunta da ledoji ta zauna gefen faseelat tana kallon fuskarta, datake kamar meyin bacci, 


ta juya ta kalli ummi tace "bacci ma take ko? "


ummi tace "ihmmm idonta biyu "


umma ta riko hannunta tace "daughter yau bakison ganina ne? "


Faseelat ta bude ido badan taso ba, bata kalli gun ummi ba tace "sannu da zuwa umma "


Umma tace "yawwa ya jikin? "


faseelat tace "naji sauki"


ummi tace "kwarai kau taji sauki azoma a sallame mu mutafi gida haka ta karasa warwarewa acan"


Umma tai dariya tace "zaman asibiti akwai cin rai dama amma tunda ta samu lpy gwara ku koma gidan "


ummi tace "ai dole saboda banga amfanin zaman da muke ba "


umma tai dariya ta meda hankalinta gun faseelat tace "yau tuwon shinkafa miyar shuwaka na miki danta temaka jinin da yarage ya ida wankowa, inafatan zakiiya ci? "


faseelat ta daga kai, umma tafara zuba abincin faseelat ta saci kallon ummi taga har lokacin ita take kallo takara lumshe ido sosai, 


Umma nagama zubawa ta tadata zaune ta rika bata batajin yunwa bataci sosai ba tace takoshi, 


Umma na nan zaune zuwa sha biyu da 30 lady da safiyya suka zo sannan suka tafi tare, 


Suna fita kamar ummi najira tace "kede anyi jarababbar banza daga zuwanshi kin sakar mai jiki yakara dura miki wani cikin yakara zubardashi shasha wadda batasan ciwon kanta ba"


maganar ummi tabawa faseelat dariya aiko tadora hannu abaki tafara dariya ummi tace "dariya nabaki ko zata koma maki kuka don alhaji babba yace dole seya sakeki bazaki komaba kuma kinsan shi in abu yabata mai rai yana dadewa be sauko ba "


faseelat ta tashi zaune idonta taff da hawaye tace "ummi dan Allah kuyi hakuri kutemaka mana wlh kuskurene kuma bazaya kara faruwa ba "


ummi tace "seki bari seyazo seki fadamai nide ba ruwana aciki"


faseelat ta koma ta langwabe,ciwo yadawo ummi tace "kima tashi alhaji kawai nake jira yazo a sallame mu nagama wahala dake kuma "


Faseelat Tai shiru gabanta nata faduwa, 



Tunda fahad yafita Aisha take kuka, tayi danasani tayi danasanin sanin faseelat a rayuwarta tanata karajin mugun tsanarta a ranta, 


fahad ya nemi fever din jikinshi ya rasa yana cikin mota se lasar lips yake yana sakin murmushi shikadai, gsskiya he's missing he's messing soft and sweet hq na faseelat


yana zuwa gida ya shiga yasamu Aisha kwance taci kuka tagaji, yaje wurinta ya zauna ya medo kanta jikinshi yace "meke damunki ne Aisha?"


Aisha ta kalleshi cikin ranta tace shifa har ya warke, tace "zuciyata ke ciwo sosai"


Ya bata fuska yanajin tausayinta yace "sannu heart beat bari nakawo miki abinci da magani dan Allah kikara hakuri dani "ya aje kanta ya nufi kitchen, 


Aisha tabi bayanshi da kallo tanajin takaici tace "ga heart beat dinka can ni I'm only a sister kuma kasan baka kyautamin kenan har kake bani hakuri"


shima yunwa yakeji ya dafa musu indomi da kwai yadauko mata magungunanta itama yunwa takeji ta bude baki tadanci yabata magani sannan yaci nashi yana gamawa ya dauketa yanata mata sannu taita kallonshi kawai, 


ya sakarmata murmushi yace "I love you heart beat ina tsananin sonki"


aisha tai murmushi me ciwo tace "I love you yaya more than everything in this world "


Yace "thanks you so much dear ya kaimata kisss a head"


Akan bed yaajeta yashiga toilet ya watsa ruwan dumi don yakara jin karfin jikinshi yadawo har lokacin bacci be dauketa ba tana ta kallon shi kamar bashi ne ke kwance dazun ba, yazo ya haye bisa gadon ya matseta yafara aika mata da kisses, 


Bata hana shi ba don itama tayi kewar dumin jikinshi sambatunshi and his sweet words after sex, 


bayan komi yagama wakana ya rungumeta yana fada mata sweet words da kullum yake fadin sabbi kuma tanajin dadinsu ,har bacci ya dauketa yana rungume daita ya dade yana kallon fuskarta duk ta rame ya shafi gashinta ya tashi yayo wanka yasaka kaya ya nufi gidan mommy dauko amira yakaita wurin faseelat,


koda yaje yasamu amira kwance tana bacci ya Daukota beko gaisa da mommy ba ya nufi asibity, 


Tun kafin yakai amira tafarka tana ganinshi tafara kuka yace "princess wurin anty zan kaiki kiyi shiru kinji "


amira tace "aika kasheta ni kamedani wurin mommy "


yanajin zafin maganganunta yace "antinki bata mutu ba kiyi hakuri mutafi wurinta tanason ganinki, kinji?"


Tai ta kuka yanata rarrashi har suka isa ya fito ya dauketa suna Zuwa bakin kofar dakin ya tura yace tashiga, amira tashiga dakin wayam bakowa don an sallamesu, 


yana tsaye bakin kofa tafito tana kuka, ya riketa yace "me akamiki? "


tace "u lied to me bata ciki "


Ya tashi ya tura kofar wayam ba kowa, ya dafe kai yace "nashiga ukku"


amira ta kama hanya zatai tafiyarta yabita ya dauketa tana ta harbe harbe, har suka isa bakin mota ya dorata saman motar ya zaro mata ido rai bace yace "Dan ubanki natsu kimun gumm wlh kona zane ki "


amira tai gum tana ta hadiyar kukan, don betaba mata haka ba 


Idonshi jawur yace "in kara jin kin min kuka sena miki dan banzan duka "


ya dauketa yasata motar suka tafi gidansu faseelat gidan kau a bude yake, 


Ya fito ya dauketa yakaita har bakin kofa yace "she's inside enter "


a tsorace ta shiga cikin gidan, ummi nata yan aikace aikace amira ta shigo tana share hawaye 


Ummi tace "a, a amira kedawa? "


amira tace "daddy ne yace anty tananan in shigo "


ummi tajawo hannunta tace "antinki nanan kuwa"ta shigar daita dakin faseelat


faseelat na kwance bacci ya dauketa, amira ta tafi ta rungumeta tana kuka, 


faseelat ta bude ido taga amira ta riko fuskarta tace "princess yaakai me kikewa kuka? "


amira tace "inata nemanki banganki ba anty karki dawo gidanmu daddy yakara dukanki"


ummi tace "kwarai ko fadamata gaskiya tunda ita kwakwalwarta ta toshe"tajuya tafita tana surutai


Faseelat ta sa hannu tana sharewa faseelat hawaye tace"bakiso na dawo mu cigaba da cin abinci tare, karatu, wasa, bakiso? "


Amira tace "inaso amma daddy na dukanki bana so ya cigaba da dukanki"


Faseelat tajawota ta rungumeta tace "baze kara ba it was a mistake kuma it won't happen again kinji? Kidena jin tsoron daddynki he loves you baze miki komai ba"


Amira tace"he don't love me anymore, yanzu ma yafadamin ze zane ni"


faseelat tace "kidena tsoronshi baze miki komai ba, kinji ko maybe kin bata masa rai kuma I have told you baa batawa iyaye rai "


amira ta daga kai, sunanan kwance sunata dan labari amira nabata labarin abinda yafaru bayan batanan, 



fahad yana cikin mota zaune se tunani yake shifa he want to see her me yasa aka sallamesu acan zesamu damar ganinta anan ko baze samu ba "


omer yadawo daga aiki har yazo yashiga gida fahad be lura dashi ba yanata tunani, 


omer nashiga ummi na tsakar gida yace "lpy ummi naje asibitin naga bakwanan kuma naga har yanzu dasauran jikinta "


ummi tace "kai ke ganin haka  amma ita ta samu sauki ,ina dawowa dakin nasamu mijinta yazo ya danneta sunata tsotsar juna, shiyasa nace a sallame mu takarasa warware wa anan karma yadura mata wani cikin tun muna asibitin tunda de ita sakarai ce"



Omer ranshi ya baci yaja tsoki yace "yanzu ma nabaro shi kofar gida kome yake anan shima yasan baze samu ganin taba "


Ummi tace "yarshi yakawo tana ciki wurin ta"


omer yaja tsoki ya nufi dakin faseelat suna kwance ya janye amira, yace "kede anyi wawuya wadda batasan ciwon kanta ba, wato wannan karan ma bakiga laifinshi ba ko? To inke bakisan ciwon kanki ba mu munsan ciwon kanmu"

Yaja amira suka fita waje har bakin motar fahad da kofar ke bude ya tafi dogon tunani gwam gwam omer ya kwankwasa motar, fahad ya dago yana kallonshi, 


Omer ya tura amira wurinshi yace "take ur daughter and go karka sake dawowa kofar gidannan, I warned you kar nakara ganin ka anan idan kuma kazo to zaka sha mamaki"

Fuuuu yajuya cikin gida, 


Fahad yayi kasake yana ta kallon bayan shi, ya girmi omer amma gashi yanata datsa mishi magana, amira dake ta kuka tace "daddy ni awurin anty zan zauna"


Zuciyarshi na zafi ya dauketa yasata cikin motar suka nufi gida ita tana ta kuka shi kuma yanata tunani tunkafin suyi nisa zazzabin yadawo mishi, 


Itama faseelat tana can tana kuka. 







comments, comment's nikuma in rika antayo maku long page ko mungama.




Post a Comment

0 Comments