TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

RAGON MIJI page 11-12

 RAGON MIJI


1⃣1⃣




Kukan nata bame sauti bane ,zeyi wuya kaji shi inba dakin kake ba, 


Tadau tsayin minti 15  tanayi, se tafara magana da zuciyar ta, 


"ba kince bazaki kara kuka ba to me kikeyi yanzu"


Dayar zuciyar tace "i have to ko don na rage zafin da ke tsatstsafowa a raina"


Dayar zuciyar ta tace " you're only wasting your tear, ba abinda zaafasa, so you better stop it"


"you are right fa "ta sa hannu ta share hawayen nata. 


Tambayar zuciyarta take "to me yakamata nayi? "


Dayar tace "don't ever take decision in haste, kibari ayi auren mana "


Shiru tayi tana tunani 


Can zuwa ta Saki murmushi ita kadai tasan abinda ta kulla, se ta mike zaune, ta jawo wayarta ta fara chart. 


Bangaren khalil ko seda cikin shi ya cika tabbb sannan yasha ruwa sukafara labari da kanwar shi, har yabata number faseelat din kamar yadda ta bukata, shiru shiru Hjyrsu bata fito ba seya fita zuwa wurin best friend nashi wanda suke tun suna yara amma saboda irin yanayin khalil basa sharing problems nasu ma juna, ana taren ne kawai. 



Ummi na komawa abba yace "ba matsala tunda ta yarda ki kira ita hjyar ki fadamata yadda mukayi "


Ummi tace "to "

Ta kira hjy tafada mata duk da de hjy ba haka tasoba amma se tace "ai bakomi sati ai kamar gobe ne "


Alhaji najin yadda Sukai yace "to Allah yakaimu satin zanyiwa su yakubu magana dan su shirya da sunbamu rana se suje "


hjy saratu tai murmushin jindadi. 



Faseelat na tsaka da charting kiran siyama ya shigo ta dauka tai sallama, daga can bangaren aka amsa, 


Akace "antinmu inawuni "


Faseelat tace Anti kuma? Ai batada kanwa mace sannan bama haka ake kiran taba ta daure tace "wa ke magana? "


Siyama tace "kanwar mijinki ce siyama"





 sora kirisss faseelat tai ta bargaza dan harta hade baki da niyyar yin tsoki tai saurin fasawa, tace "ina yini "


Siyama tace "lpy lau anty dama cema yaya nayi yaban number ki mugaisa "


Faseelat tace "ihhhhn Nagode "


Siyama tace "bakomi se anjima agaida su ummi "


Faseelat tace "ihhhhm "takatse kiran ta turo baki gaba tare da cewa "Se kuyi tayi ai nide nawa ido"


Kiran wata number yashigo wayarta da alamu number Niger ce saboda digit din farkon number din, tadesan baze wuce danginsu ba ko ya umar, yaushe rabon ma suyi waya ankwana biyu 


Ta daga kiran ta kara wayar a kunne "assalamu alaikum"

Ta fada ,murmushi ya doki kunnenta akace "waalaikumussalam"


Tunda taji murmushin ta gane me magana, yanayin yanda ya amsa mata sallama da zolaya ya sata tafara dariya, 


Tana dariya tace "yaya na, kaine kamanta dani kwana biyu ko? "


shima yayi dariyan yace "ina ni ina mantawa dake duk in mukayi waya da ummi ina cewa ta gaidaki bata fadamiki ne? "


"Allah ni bata fadamin"ta zumburo baki kamar yana ganinta.


Yace "to laifin ummi ne ba nawa ba tunda kinsan bakida waya yanzu ma hakanan nace bari nakira layinki se gashi tafara ringing, kice baba babba har ya siyi wata, dan nasan ummi de bazata se miki waya ba tunda kudinta kaff suna karewa ne wurin se miki cosmetics, kuma nasan abba baze siyamiki waya ba ya fiso ki karatu besan shiririta "


Tace "a, a ba shi yasiyamin ba fa "


Daga can yace "to waye? "



Tadanyi shiru sannan tace "yaya su ummi da abba are planning to get me married"

Tai maganar kasa -kasa. 


yace "very soon haka  with whom? "


tace "wani ne sunanshi khalil dangidan kawarta "


Yace "to, what's in your mind did you like him "


Tai shiru 


Yace "faseelat are you with me? "


tace "yeah ,honestly yaya bana sonshi but I will marry him, as they wish"


Yayi shiru saboda problem da yaji daga wurinta can zuwa yace "will you... Se yayi shiru "faseelat zama da wanda baka so, will not give you a good and peaceful marriage life, akwai wani freind dina ya auri wadda bata sonshi at the end auren mutuwa yayi dan ko 5 months ba suyi ba, "


Tace "yaya tunda de ummi na so to zanyi hakuri in aure shi haka "


Ya fitar da iska "huuuuuuh, to naji Allah yasa haka shi yafi zama alheri all the best "


Tace "amin, ina su dije su hanne su fatouma su kawu "


Yace "actually i really don't know cos nayi Week  banje gidajen su ba "


Tace "kana nan wurinsu fadila sun rike ka "


Yace "bahaka bane fa, I'm very busy we are about to start exam ,karatu ne kurum ya hana .


tace "to Allah ya bada saa, agaida ammah da su fadila da husna ka fadamusu ina missing nasu "


Yace "OK bye "


Ya kashe kiran ta sauke ajiyar zuciya da ma ace kanwa na auren yaya da ya omer kawai zata aura, ji yadda yake magana gashi kyakkyawa ga daukar  wanka best dress dinta English dress, tace "gaskiya yaya matarka ta mo re wlh"



Abba bugawa baba babba waya yayi ya fadamasa abinda ake ciki, yace baya gari se next week ze dawo amma yanzu zeyi sqeesing ya dawo, saboda shine madaurin auren faseelat, 


Abba be yi kasa a gwiwaba ya fadawa abokinshi yace Dan Allah ya masa bincike akan khalil abokin nashi yace ba matsala, sannan ya wuce wurin kannenshi yafada masa shima yace ze bincika abokinnashi har unguwarsu khalil yaje ya tambayi manyan mutane gamedashi, hakan be isaba seda yaje yasamu principal din makarantar su ya mishi bayani shima, haka suka dage bincike. 



Bayan kwana hudu zuwan khalil gidansu faseelat ya ragu inyaje yau be zuwa gobe amma suna yin waya tunda ta samu lpya shikenan se hankalinshi ya kwanta amma fa duk zuwan da zeyi se ya ajiye mata bandir din 50 nera guda biyu da Alamu canzo kudi masu yawa yayi, in yabata bata amsa shiyasa yake ajiye mata kawai ya tafi. 


Bangaren faseelat ba wani improvement saboda har yanzu de ba sonshi take ba watarana in yan wulakancin na kai inyazo ko kallonshi batayi har yakara sa inda indarshi yatafi. 




bayan sati 


baba babba ya dawo shima yasa ammishi nashi binciken duk binciken da akeyi abu daya ne ke fitowa bakinsu cewa "mutum ne me kunya da ibada kuma me yawan ambaton Allah,  gaskiya khalil ya samu yabo wurin mutane, 


Hjy saratu ko tana nan ta zuba ido akan al'amuran khalil duk da de batason wainar da yake toyawa bayan idonta ba, 


yau ummi takira ta tafada mata zasu iya turowa jibi 


Hjy saratu taji dadi sosai alhaji yana dawowa tafada mishi shi kuma yafadawa wakilansa, 


Jibi nayi sitting room din baba babba ya cika da manyan mutane su 5, akai gaishe gaishe da ciye -ciye bayan sun gabatarda kansu, sannan suka bada nera dubu 100, 

Alhaji babba da yake dattijon mutum ne yace karsu kara kawo sisi duk radda suka shirya suka wo kayan sa rana, daya daga cikin wakalan yace su ko yanzu a shirye suke buga waya kawai zeyi akawo kayan sa rana, 

Baba babba da yake abba ya bashi labarin matsalar faseelat din ya amince ,akasa rana nan da wata ukku, ko minti 15 baaiba se ga kwalayen biscuits da huhun goro biyu manya manya ana shigowa dasu, dayake dama alhajinsu khalil yayi retire shine yabude babban supervision store da kudin retire nashi. 






da Faraa abba yashigo gida ummi na masa sannu da zuwa tace "wai lpy kake ta faraa "

Yayi dariya "surukanki har sunzo sun tafi "

Tace "eh se akai yaya? "

Yace "uban diya har yasaka rana nan da 3month ran Friday "

Ummi farin ciki ya lullubeta tace "to Allah yasa alheri "

faseelat na kitchen tanajin abinda suke fada lokaci daya cikinta ya juya ji Kake kululululu, ta tashi da sauri tatafi kewaye tafara fetsa zawo,

RAGON MIJI


1⃣2⃣




*dedicated to sis zulaihat*





 

Shikenan yanzu tagane kowa baya sonta har shima baba babba baya sonta, ta dauki mintuna kafin tafito, 


Su abba ko shigarta kewaye ba su gani ba  dan Sun riga sun shige daki, 


Faseelat wani dutse ne ya tsaya mata awaya, tana tuna firarsu da khalil ta jiya, wai ya mata missed call daya da safe be sake kiraba se dare, ana cikin fira yake tambayar ta wai bata ga missed call dinshiba? Tace tagani amma daya ne yace dayan ai, ai ni bana missed call biyu innayi daya ba bukatar insake maybe Wanda na kira yana busy "


Tace "ko? "


Bakaramin haushi maganar shi tabata ba, dazun da safe ma yakira bata daga ba, tariga tayi alwashin seta sakashi ya rika mata many missed calls. 


Lokacin da khalil yaji labarin bakaramin farin ciki ya shiga ba wanda yakasa boyuwa ko da akan fuskarsa ne, 


Hjy saratu ta banka mai harara tajin haushi tace "seka fara shirin biki bawai yin wata hidima ba "


Ya sosa kai "ai Hjy lefe ne kawai aiki na kinsan abba ya dade da bani wani gida da yagina can a layout fenti kawai zaayi se kantoci "


Tace "eh dukda haka lefen da Kake gani bakomi ba se yazama aiki, kai lefe fa yana cin kudi sosai ,dan haka yanzu kameda hankali kawai akan abinda ke gabanka "


Yace "to Hjy "ya tashi ya fita, tace "shashan banza kawai kamar anmasa bushara da aljanna ko kunya bayaji  mtsssw"


Shi ko dakinshi yawuce ya ciro wayarshi yayi dialing number faseelat, 


Faseelat na kitchen stew ma ce take soyawa wayar na hannunta tana chart ya kira, harta tsinke baa daga ba, ya ajiye wayar Ahankali murmushin dake kan fuskarshi Ahankali ya bace, gashi so kawai yake suyi magana, yace "bari na bari zuwa anjima"


Faseelat naganin kiran ya tsinke tace"kasake kira in abun ya matse ka "


Ta koma charting dinta, kawai se ga maman amira ta turo a group "slm yanuwa inamaku bankwana zamuyi tafiya ni da mijina zuwa Cyprus, se Allah ya mana dawowa I'm going to miss you "


Ta tura ma group din da tasa akasa ka faseelat,sega best wishes Nata shigowa, wasu naturo zamuyi missing naki muma da alamu ta dade da sabawa da yan group din, tun ranan da sukayi saving contact na juna basu kara magana PC ba sede a gaisa a group, 


se faseelat ta bita prvt "anty tafiya zakuyi ne? "


Maman amira ta tura mata "eh faseelat gobennan around 4am zamu tafi tareda mijina "


Faseelat tace "amira fa? "


Tace "wurin momy nakeso mu barta nima nadan huta, inde daddynta ya bari"


Faseelat tace "anty kitafi daita mana "


Maman amira tace "ai duk takare dole mutafi Daita dan daddynta bana tunanin zeiya 3wks batare daita ba "


Faseelat tatura smile emoji tace "yanzu se yaushe knan? "



Maman amira tatura "2 to 3 months only "


Faseelat tace "zanyi missing naki anty"


Maman amira tace "ki dena kira na anty kila ma kin girmeni "


faseelat tai dariya tace "yakamata ko insanki "


batare da bata lokaci ba maman amira taturo mata pic dinta a kasam sa ta rubuta "my name is aisha, I'm just 23 years old married with one girl name amira "


Faseelat na bude pic din ta tsaya kallonta kyakkyawa ce black beauty gajera ce amma baso saiba bata da kiba inde kaganta Zaka iya cewa shekarata 19 Daganinta tana jindadi, ko kayan jikinta Sun isheka kallo, 


Bata gama kallon Nata ba taga Anturo wani  ta bude kasan sa an rubuta "baby amira "

Ta tsaya kallon yarinyar yar 3yrs fara fesss irin farinnan ba ja ba gashegen kyau tana sanye da gownt fara tasha twisting, bakaramin burge faseelat yarinyar tai ba, tawani rike kugu ta sunkuya harda su turo baki gaba faseelat tace "duniya inda ranka kasha kallo yaran yanzu da zamananci ake haifarsu jibi yadda tai wani style "har cikin ran faseelat taji tanason amira, faseelat ta tura "wow maman amira kibani amira mana inasonta sosai "


Aisha tace "hmm faseelat da se me wannan diyar ya daureki, zande baki aro "


Faseelat ta tura dariya "nide wlh inasonta kunyi kyau sosai, amma duk da haka kingirme ni sunana faseelat b maaruf shekaru na 21 "


Ta tura hoton ta, 


Ta tashi tafara zuba miyar da take soyawa a cooler dan tuni ta sauketa har ma tafara kamu, tana juyewa ta bude wayar, 


Ga reply din maman amira "faseelat kina da kyau sosai inama ni ce ke danaji dadi Kindace a komi ko a suna "


Faseelat ta tura mata "Nagode sosai maman amira se anjima ko kuma ince Allah yamedoku lpya"


Maman amira tace "amin mommyn amira "


faseelat bata iya tura komi ba saboda kiran  khalil da ya shigo, tai rejecting abun yabashi mamaki ko second baaiba wani kiran ya shigo faseelat ta fashe da dariya "kai da kace baka kira biyu yanaga haka? "


takara datse kiran khalil besan lokacinda yakara kiranta ba ta dauka ta yamutsa fuska tai shiru, 


Yace "haba faseelat mi yayi zafi da zaki rika rejecting kira na?"


faseelat ta murguda baki "bakace bakayin missed call biyu ba? shine na ke gwadawa, ashe abun naka bame daurewa bane "tai dariyar rainin hankali. 


Yayi shiru "ba da wata manufa nai wannan maganar ba faseelat ,baki fahimceni bane"


Faseelat tace "na fahimta mana "


Yace "to kiyi hakuri in missed call din ne kikeso kinsamu shikenan? "


Tace "bansaniba"



Yace "to Allah yabaki hakuri se anjima"


Ya kashe kiran kiran ta ma yayi ya fadamata abun farinciki amma tasako wannan batun. 



maman amira kau itama sauka tai tunda tagama rabawa duniya cewar zasuje Cyprus dukda ba zuwanta waje na farko bane, 



A sannu lokaci ke tafiya abubuwa masu dadi da marar dadi na faruwa har anyi wata daya dasaka baikon su khalil gaba daya yangidansu faseelat bawanda be saba da shiba dukda de bai cika sakin fuska can-can ba, 


Faseelat kau gyara takesha daga sama har kasa, to da anyi na banza ma bare yanzu me dalili, 


Lefe Nata haduwa har ansiyi akwatuna anata zuba duk abinda ya samu akwati 6 ne setin hello Queen, Hjy bata nuna komi dan itama burinta ta fita kunya dan tana daga cikin masu zuwa ganin lefe gidaje inbe yiba aita surutu. 



Bangaren soyayyar khalil da faseelat kau abunde ba cigaba firarsu a waya bata wuce 2mnt saboda besan firar da zasuyi ba, be iya tsara mace ba sam, 

Inkuwa zuwa yayi to befi yayi 20mnt ba kusan rabin lokacin duk kan kallonta yake tafiya. 


Yau ya kirata zezo danhaka tafito tana hadamasa abinda zeci dan ummi ce ta koya mata yi masa girki da drinks in zezo.


Post a Comment

0 Comments