TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

RAGON MIJI page 33-34

 RAGON MIJI


*Bismillahirrahmanirrahim*





*Kad aflahal muuminuun...... wallazinahum anil lagwi muuriduun*






*Dedicated to golden pen writers, ko nima zansamu aban matsayin gimbiya😂🤭 kuzabe ni plss ni nacancanta abawa, 🤭ina maku gaisuwa da rokon iri👏🏼😂*





Wajen karfe biyu khalil ya dawo gida don dukda ana azumi yakan dawo da rana ya dan huta, har lokacin faseelat na zaune tana faman kuka da sake sake yana shigowa yaganta zaune idanu jawur da sauri ya isa wurinta  ,ya durkusa ya dafa cinyoyinta yace "faseelat lpya meyafaru? "


Faseelat naganin yanda ya rude ganin tana cikin damuwa tana sheshsheka tace "bakomi kawai azumin ne ke bani wahala "


Yatsaya kallonta don be yadda da maganar ba, 


Can zuwa yace "faseelat karya bataimiki kyau ba, saboda baki sabayi ba kifadamin meke damunki plsss" yariko hannunta .


wani kukan ya kufcemata cikin kukan tace "wurin waazi ne akai waazi akan azabar da akewa yan wuta shine ya firgitani"


Ya dubi hijabinta dake gefenta don tunda ta dawo take nan ya rumtse ido ya bude yakara damke hannunta yace "idan anji waazi ba kuka akeba komawa ake ga Allah ta hanyar kaucewa aikata duk wani sabo da kara kaimi wurin aikata alheri, ke mi zesa ki daga hankalinki, kina karkashin inuwar aure, manzon Allah (S. A. W) yace duk macen da ta mutu kuma mijinta ya yarda daita zata shiga, akwai hadisin da kuma yace idan mace takiyaye sallolinta biyar, ta kiyaye azuminta da farjinta da hakkin mijinta to zata shiga aljanna ta kofar da taga dama, me ze dameki kina min biyayya bamu taba samun sabani ba kuma kina da yawan ibada, ki shakuruminki ni dake duk yan aljanna ne gabadaya in Allah yaso, "


Ta kureshi da ido tana jinjina maganganunsa, 


Ganin takure sa da ido ya sa hannu yana sharemata hawaye yana cewa "ki kwantar da hankalinki mata ta yar aljanna "


Tai shiru tana zazzare idanu wani mugun tsoro nakara shigarta. 


Ganin tayi shiru sannan ya tashi," bari naje na dan kwanta kitashi kiyi salla "



yawuce cikin daki, har bayan 15 mnt da shigar shi faseelat takasa tashi, dakyar ta mike ta shiga don yin salla, 


Bayan tafito ne wayar ta tafara ringing ta dauka tana dedeta maganarta ishak yace "yaya kin sauke? Ni har nafara ta biyu "yana murna 


Faseelat tai dariya tana tabe baki "lazy boy dani kakeso kaja? Hhhh dasauranka ni kaga nakusa sauke na biyu, ina ummi tayi ta farko ma? "


Yana dariya yace "ummi najin azumi fa ta de kusa yin rabin sauka "



Faseelat ta babbake da dariya "kafadamata se ta taho "


yayi dariya "anti kina kokari asamu a addua "


Tace "karka damu ka gaida kowa, kuma kafadamasu se suntaho "


Takashe wayar tana dariya, wato su yar rige sukeyi a sauka cikin azumi wanda ya wuce kowa ummi na mashi kyauta ta musamman, 


Ajiye wayar tayi tafara karatu seda akai laasar ta shiga kitchen, 



bayan ansha ruwa khalil ya tafi masjid ita kuma har tagama tata tarawihi ta dauko wayarta, tana Bin chart dinta da fahad, duk reply dinshi bewuce thanks, ameen, i love it, ko u look pretty good, tai dariya tana jindadi, ta rumtse ido tana tuno yanda yake ta aiki a tsanake ranar nan yanzu muryar shi kawai takeson ji, zataso taji ya voice nashi tasan jinta kadai zesa tai bacci cikin farin ciki, 


Batare da jinkiri ba ta bi numbers tai dialing my hope, 


Fahad dawowarshi kenan daga masjid yana cikin mota ko fita beba wayarshi tafara vibrate, 


yana ganin number yagane number insane girl dinshi ce, 


Ya dauka yayi shiru jin andauka faseelat tai Kasa da murya tai sallama, ya amsa yana lumshe ido tareda dora kanshi kan seat, 


Faseelat wani irin dadi muryarshi tai mata jitai kamar ba muryar namiji ba tsabar dadi, 


Tadanyi jimm sannan tace "inafatan kasha ruwa lpya? "


Yace "yeah "yana mamakin yanda yakejin wani abu namasa yawo 


tace "Allah ya karbi ibada, ina anty da my meera "


Yace"they're all fine "


tace "naji dadin jin hakan, Inajin muryarka kamar honey or sweet ,nakirawo ne naji muryar ka ko nasamu peace of mind, daddin amira tun ranar da naga pic naka i fall for you "


yayi shiru cikin ranshi yace, "u have nice voice too "



jinshiru tace "I'm sorry na takura maka it's your love that make me gone crazy,im sorry for all my disturbances, "



Yayi murmushi me sauti wanda yasa taji wani abu na zubo mata yace "why do you force me to start loving you, yeah you force me to fall for you ,u know what? I love everything about you, ur smile ur voice , ur duas for me ur cooking and your beauty, I love everything about you"


Saboda dadi faseelat batasan lokacin da ta mike tsaye ba, sautin muryarshi nata kaikawo a brain dinta, 


Wata irin dariya ce marar tsayi takeyi me cike da mamaki tana rufe baki tace "did you? ....."


Takasa karasawa, kamar yasan me zatace yace "yes I love you, I love you beauty "


Dadi yakashe faseelat da karfi tace "thank you so much I love you too "


Ta datse kiran tana tsalle ,can zuwa takwara baki tace "I love you "


Saboda zafin da ake tsakar gida take sallan, khalil tsayuwar mashin dinshi kenan yaji maganar ta da karfi tana fadin I love you, 


ya shigo gidan don bude gate, tanajin karar kofa tai tsaye wayarta rungume da kirji, 


Yana mata kallon mamaki yace "kedawa kike waya kike daga murya haka? "


Tana inda inda tace "ya omer ne munkwana biyu ba mugaisa ba shine yamin albishir nakejin dadi "


Yajuya kawai ya bude gate din yafita, tasaki ajiyar zuciya tana zaro ido waje ta shige daki, 



Fahad jin yanda take murna yakara sashi cikin wani Yanayi, Ya rumtse ido shikadai yasan yanda yakeji gameda ita, brain dinshi tana hasko mishi irin murnar da takeyi yace "be happy always my cutie, 

Ya samu yashige gida ya je ya sauke duk abinda yakeji gun aisha. 




tundaga ranar kullum se faseelat ta mishi barka da shan ruwa kuma suna chart suna fadawa juna zafafan words da suke kara narkar da zuciyoyinsu. 




Salla saura 5 days maman amira ta fadawa faseelat zasuje dubai acan zasuyi salla, faseelat kamar tai hauka takira fahad, he was busy doing office work be dauka ba seta turamishi message "zanyi kewarka my heart, inamaka fatan nasara akowane abu da Kasa agaba Allah ya ya kaika lpya ya medoka lpya "


Seda aiki ya lafa yaga miss call nata da message yana gama karantawa yayi murmushi ya tura mata "why did you fell sad, we will continue chatting with each other and I will call you time to time stop worrying your self we will only spend 10 days only going to miss you too "



ya turamata tana ganin message din tai murmushi, 


ko minti biyu baaiba yakirata yana rarrashi yace taturamasa account number dinta ta tura masa nan take taji alert din 200,000.



kusan zaucewa tayi tanata kara karanta zero zeron taga ko de bata karanta dede ba.

RAGON MIJI


She's very happy, his gift is the best gift for her, can kuma setaji murnar duk ta tafi she don't want his money she want him ,not the money he own, bayan 15 mnt da turomata ta kirashi ya dauka yana driving to home, yace "menene kuma cutie? "


Tai murmushi "naji alert a account dina, bazance banyi murna ba saboda kyautar will always be the best gift amma ni I don't want the money, kai nake so ba kudi ba, zanmeda ma kudinka, Nagode sosai "


Yayi dogon murmushi yace "naji kuma nasan hakan ,amma inkin medo min kudin bazanji dadi ba, zama ki tabbatarminne bakisona kina fadane kurum "


Tace "Tom bazan medoba dan banason ranka ya baci "


Yace "kokefa yanzu I entered home se munyi waya anjima "


Tace "wait nifa bansan me zanyi da kudinnan ba "


Yayi dariya yace "kisa su a bola kinji ko "ya datse kiran yana dariya, yace " you're not serious "


Tanajin ya kashe kiran ta saki murmushi, ta rungume wayar, 


Khalil yaga sauyawar faseelat sede be dauki abun serious ba,



Da daddare ya kirata don gobe ne zasu tafi ta dauka tana shagwaba shi kam dariya kawai take bashi yanajin dadin yadda take shagwaba"plsss i don't want to you to go there pleas"


Yayi dariya "OK shikenan nafasa tafiyar are you happy? "


Tai dariya tana zaro ido " wasa kake ko? "


Yaja numfashi "dagaske nake munfasa tafiyar tunda bakiso saboda banason abinda zesaki damuwa "


Tace "a, a,kuje kawai kunriga fa kungama komai se kufasa? Na hakura kuyi tafiyar ku"


shima yayi muryar shagwaba yace "a, a ni de nafasa saboda kar masoyiyata tashiga tunani "


Tafashe da dariya tana zumbura baki tace "plss mana kutafiyarku"


Ya fashe da dariya sannan yace "OK, OK zamuje tunda kince, me zaki bani na bankwana? "


Tace "kome kakeso "


Yace "I want hot kiss from you "


Tai dariya "how i will do it bayan bama tare? "


Yace "muna tare idanuna suna hangomin yanda bakinki ke motsawa a yanzu da yadda kike shagwaba, kiyimin kiss a waya I will feel like kamar azahiri ne "


Tace "zaka samu fiye da yadda ka bukata, where do you want me to kiss ?"



Yace "my cheek "


tace "alright "


Muahw!


Taiwa wayar kiss 


Yace ash yana dafe cheek dinshi alamun yaji dadin nan tai dariya tace "do you want more "


Yace "yes's "


Tace "where I'm going to kiss now? "


Yace "my lips "


Tai murmushi takara jan wani deep kiss, wanda yasa fahad kusan haukacewa yanda yaji sautin, 


Tana gamawa tace "want more? "


Yace "noo" muryarshi a dishe 



tace "why? "


Ya shafi sajenshi yana rumtse ido yace "i will die if I have the third kiss "


Tafashe da dariya yayi shiru saboda his Mood is totally change jiyake dama tana kusa he want to squeeze her body, he's in need .


jin dariyar ta nakara mishi kaimin jin desire the way she's laughing is different saboda tanayi ne tana jan numfashi wanda yakejin shi kamar they're doing sex ne takeyinshi, 


Dole yatafi gurin aisha yasamu relief, 


Yacewa faseelat "baby I'm going inside take care of yourself, I will call you the time we have reach there "


Tabata fuska sannan tace "miss you my handsome man "


Yace "going to miss you too tace care bye "


Yakatse kiran yanajin double feeling, yadan zauna ya dan dedeta kanshi sannan yashiga gida, 



Wannan karon banda amira zasu yanzu tana gidan momy, yana shiga daki aisha nata charting dinta, yaje ya zauna kan bed din yafara balle maballe, Aisha ta juyo ta kalleshi tana ganinshi tasan what he capable of doing, ta sakarmishi murmushi ya meda mata yana jawota jikinshi suka cigaba da kissing juna kan su afka ga babbar sunnah,



Seda sukagama tana kwance tana huce gajiya yamusu parking suka shiga toilet sukayo wanka sannan suka kwanta don 12 jirginsu ze daga. 



12 dede jirginsu ya tashi going to Dubai 





Faseelat nagama wayar ta shige toilet don yin tsarki kaida ne inhar sukai irin firannan se ta kama ruwa dan jikewa take jagabb, 



Tana fitowa khalil yashigo gidan taimasa sannu da zuwa ,yazo ya zauna ya aje ledar hannunshi ya mikawa faseelat yace "kizabi kalar da kikeso guda biyu sauran na hjya ne "


Tabude ledojin atamfofi biyu da laces biyu, ta kara binsu da kallo ai wannan dama yariga ya tsarosu da kaloli masu duhu da masu haske tasan masu duhunne dede ita, 


Ta dago ta tabe baki tace "meyasa baka daukeni naje nazabo kalar da nakeso ba? Ni ko agida nikeyin siyayyata bayimin ake ba, "


Tunda tafara magana  yake kallonta ya rasa meke damunta ranshi ne yabaci ya tashi tsaye ze shige daki yace "ni agida na mace bata zuwa kasuwa, ko super market ko wani wuri kingane ai "



Tace "to wlh kaxo ka dauke kayanka bana bukatarsu kuma senaje super market din sede kayi abinda zakai "


Har yazo shigewa ya juyo cikeda mamaki yace "faseelat ni kike fadawa magana haka? "


Tace "anje anfada maka gobennan zanfita insiyo abinda yayi min, zaka wani kawomin wadannan banzayen kayan kadauke abunka bani so, kahada su duka ka kaiwa saratu ta dinka "



Gabanshi yayi wani mummunan faduwa jin ta ambaci uwarshi kai tsaye, ya dafe zuciyarshi sannan yace "faseelat kinsan abinda kike fadi? "


Tace "bansaniba tunda ni mahaukaciya ce, sakarai kawai da komi nashi na kauyanci ne bawani wayewa, harni zakaiwa kaya iri daya da hjya? Ai atleas ka tambayeni wace color nakeso, ka kwashi kayanka bani bukata matsiyaci kawai "


Jijiyoyin kan khalil tuni suka firfito yayi tsaye yana kyarma yana kalonta tana xaune tana shuka rashin mutunci hankali kwance jiya ke kamar ya rufeta da duka, ya dunkule hannunshi yakaiwa iska naushi. 


Kutstsss, hhhhhh tafashe da dariya tana yamutsa fuska tace "ran yan maza ya baci, ta kwashe da dariya "yo shi iska miye nashi nice nan nayi lefi azo a daken in an isa "tana jinjina wa sekace inyazo bugunta zata iya katabus, 


Rai bace yabar wurin taja tsoki tace "mtswww wlh damma cikin azumine Allah yakaimu bayan salla kasha mamaki "




ta hau what's up ta danyi replying na messages da akaimata ta sauka don yanzu ko tana online basu cika charting da aisha ba inde fahad na online. 



Seda ta ga dama sannan ta kwashi ledojin ta shiga daki  yana kwance yanata kallon silin hannu saman kai mamaki da bakin ciki Sun addabeshi be ji shigowarta ba sede yaji kaya samanshi "ridididif "


Ya tashi zaune zuciyarshi na harbawa da sauri yace "faseelat kina tsoron Allah kuwa? "


Tana banka mishi harara tace "inbanji tsoron Allah ba tsoronka zanji? "


Ta wani murguda baki ta rike kugu sannan ta juya ta shige dakin ko minti biyu ba aiba ta fito cikin sleeping dress ta wuceshi, yana zaune sede yaji ta bude dakinshi ta shige da alamu can zata kwana. 


Ya dade zaune dan gabadaya gani yake kamar anmasa musanya, dakyar ya samu yayi bacci, 


Dasafe tun kafin tafito yabar gidan don wani mugun tsoronta ne ya shigeshi. 


Yana zuwa gidan hiya bayan sungaisa ya mika mata Nata kayan sallar, ta amsa ayatsine tace?"Allah yasa albarka "


Badadi yabar gidan kanshi na mugun ciwo, 


Shiko fahad karfe 11 da rabi na safe yakira faseelat yafadamata sun sauka taimishi ya gajiya sukai sallama saboda azumi. 



Haka faseelat ta bullo da wasu sabbin abubuwa da suka rikita ma khalil kwakwalwa, da yanzu tsoron shiga gida yake inko yashigo har kyarma yake wani lokaci ma da yashigo sede kiji kwammmm! Mashin yafadi daga hannunshi saboda yanda hannunshi ke rawa, ba ruwan faseelat da taji karar faduwar tai ta babbakar dariya se tagama taja tsoki, gaba daya ya rikice idanunshi kullum awaje yana rarrabasu more especially inya shigo gida. 



Ranar salla faseelat taci gayu ta turawa fahad, yayi ta kodata don bakaramin haduwa taiba don seda taje kasuwarnan ta zabo materials masu kyau takai akamata dinki, 


Yanata aikomata da kisses daga karshe yakirata suka cigaba da waya, 


Wan safen salla, khalil ya dauki faseelat a mashin zasuje suyiwa su ummi barka da salla, 


Hankalinta kwance shiko yana tuki hannu na rawa, se warning takemasa "wlh kabini asannu don inka kadani Kasa  naji ciwo wlh abakin aurenka don dolenka se ka sakeni "


Yayi shiru sede hannunshi daya kara gafgaf yana rawa saboda bacin rai tana kallonshi tana dariya kasakasa da farko tausayi yake bata intana mishi tsiya Amman yanzu haushi da takaici yakebata tana ganinshi kamar ba namiji ba da wani ne da tuni yabata red card dinta ahannu. 



Tana ganin an hau titin da ze kaika gidansu tace "dakata, dakata "


Yaja burki ya juyo yazata ko zata gyara zama ne, yana kallonta ta tunzuro baki gaba ta sauka tace "ina zakakaini ne naga munyi nan? "


Yace "gidan hajya zamu fara zuwa sannan muwuce gidanku "


Tana mishi kallon raini tace "wace hjyar? Wai hjya saratu? To banzuwa kaje ka gaida uwarka nima inje ingaida tawa "


Rumtse ido yayi da yanabiye zuciya da tuni yafara jibgarta, 


Cikin tsawa yace "faseelat !ya isheki kiyimin duk wulakanci amma karki kara ambatar sunan mahaifiyata "


tace "me zaka iyayi?innafada inba raba ido ba, "taja tsoki da Allah kakara gaba inkaje ka gaida saratun "


ta juya, cikin zafin rai yaja mashin yabi bayanta.

Post a Comment

0 Comments