TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

RAGON MIJI page 25-26

 RAGON MIJI

*PAGE2⃣5⃣*


*Da sunan Allah me rahma me jinkai

*Dedicated this page to my mamy i luv u my dear 💋*




Fahad dawud shine sunanshi cikakken namiji me kyau da kudi wanda kowace mace zataso ta mallaka, mahaifinshi dawood me kudi ne sosai lokacin da yaga maman fahad rukayya yanaso ita kuma bashi take soba tanada wani saurayi dankwallo Ahmed musa ba 😜shine ya tafi France shiru bashi ba labarinshi ,amma ita rukayya kullum dashi take kwana take tashi, mahaifin fahad yayi iyakar yinshi ya shawo kanta taso shi amma firr taki amincewa dashi, shiko yaki Hakura yaje yayita zubawa iyayenta kudi suka auramishi ita dondole ba Don tanaso ba ,bayan anyi aure ba jimawa ta haifi fahad amma sam inde dawood nanan bata nuna masa soyayya se in bayanan taita kula da abinta ana haka har yayi 3yrs, kwatsam se Ahmed ya shigo gari aljihunshi taff da nera yazo da wata mota wai ita benz tana farkon shi gowa, har yau yanason rukayya kuma yama dawo ne saboda ita se yaji wai ammata aure nanfa yafara hauka irin nasu na yan ball,ya rasa ina zesaka kanshi, yaje ya samu kawar maman fahad ya bata makudan kudi yace taje ta shawo mashi kan rukayya, tana murna ta amsa tana zuwa tafara kodashi tana bawa rukayya labarin yadda yakara haduwa, rukayya ko tsohuwar soyayya na nan ,nan da nan idanunta suka rufe kawar ta kira Ahmed sukai magana da rukayya, nan take taji tana son komamishi yadda taji yana nuna mata soyayya a wayar yanayin maganarshi kadai yaisheta jindadi, saboda baban fahad baya ma da lokacinta se dare yayi wannan fa ba fashi ya dauki a wanni yana hakarta amma da rana neman kudi kawai yake, don haka ta tatada balai a gidan tadena mishi girki tadena bashi kanta tadena kula da fahad, har akayi week baban fahad ya zuba mata ido kawai saboda yana sonta sosai. 


Watarana da daddare ta tashi taita balai ta hana baban fahad bacci ita wlh seya saketa tagaji dashi, ya mata banza sede kallonta kawai da yake dama can be cika surutu ba, shouting da takeyi ya tada fahad a barci ya taho yana kiran umma! Umma!! Yana zowa gab daita ta daukeshi da mari nan ya kife wurin cikin tashin hankali dawood ya diro daga kan bed yayi wurin fahad don duk duniya ba abinda yafiso irinshi sanin hakan nema yasa ta tai wannan wulakancin ,ya dago fahad har ya suma ga jini a bakinshi dawood ya rude yanata jijjiga fahad itakanta seda hankalinta ya tashi amma ta dake tai kamar bata damuba, yanata jijjiga fahad shiru ba ya motsi idanunshi sunyi jawur yace"kije na sakekin saki ukku "


Jiki na bari ta saka hijab tabar gidan dan Sheri cikin dare ne sosai kusan 1:30am amma tafita tai tafiyarta gidansu, shi kuma yakira likita dakyar aka samu fahad ya dawo hankalinshi amma seda ya dade yana jinyar kunnensa saboda zafi ya rika masa, 


Iyayen mamansa ido ga nera tuni suka aurawa rukayya Ahmed Bayan tagama idda, Sukai tafiyar su francer. 


Shi kuma mahaifin fahad se ya hadu da maman aisha, yanzu shi burinshi be wuce me kula mashi da danshi ba, da yaganta da yarinya shine yakara yadda daita yana tunanin zata kula mashi da yaro, 


Haka kau akai momy tarika nunamasa duk kulawa fiye da wadda take nuna ma yayanta wannan yasa mahaifin fahad tsananin sonta, sunata haihuwa har tai haihuwa ukku duk mata bata samu namiji ba se kuma haihuwar ta tsaya, itama maman fahad bata kara samun namiji ba hartayi yara 5 duk mata gabadaya son danta ya dabaibayeta amma ba yadda zaai ta ko ganshi se daga baya ne take danasanin abunda tai anahaka mijinta ya samu matsala a kafa karo na baadadi wannan yasa doctor yabashi shawarar dena ball, dasuna can France din daga baya ta matsamishi suka dawo gida Nigeria saboda yaranta suyi aure anan. 



To ita kuma momy kullum cikin ba fahad labarin abinda mamanshi taiwa mahaifinshi dashi take wannan yasa ya tsaneta ko kadan be damu daita ba, lokacin da ya girma ya tafi Mexico yayi Master's akan computer, sannan ya dawo lokacin da ya dawo bakaramin haduwa yakara yiba dama tun tasowarsu akwai shakuwa tsakaninshi da Aisha ita kuma sonshi ne take, ko da ya dawo momy taiwa daddinsu magana akan suna soyayya yaji dadi sosai saboda jindadi har kyauta yabata, ba boka ba malam de ta mallake dawood, 


Daddy kiran fahad kawai yayi yace yasaka ranar aurensu da aisha, abin yabashi mamaki tunda baya sonta amma se be nuna ba saboda soyayyar da mahaifinshi ya ke masa yana ganin komi ze masa be biya shi ba, gashi dama yana bukatar auren don Allah nema kadai ya tsare sa acan da tuni ya afka neman mata, itako aisha dadi har kunne, Akayi biki aka sha shagali ,baa Dade da bikinsu ba yafara aiki companin daddy, as manager, ba adade ba kuma wani company da ke China suka yi branch Nigeria daddynshi ya mishi hanya aka daukesa a internet bus manager yana kullum aikinshi kawai tuttura kudi, kaya through internet, wani lokaci aikin dare yake wani time safe wani time da rana, wani lokaci ko fita bayayi agida yake aikinsa. 


Bayan one year aka haifi amira wanda Allah ne kadai yasa zata zo duniya saboda tasha fama saboda yawan sex baadade da haihuwarta ba daddy ya rasu, 


Gabadaya fahad baya tunanin mamanshi, kullum burinshi yayi abinda zesa momy jindadi saboda kaunar da take nuna masa,wannan yasa yake kula da aisha kuma yake matukar sonta,  fahad mutum ne me barkwanci sede fa komai da lokacinsa akwai lokacin dariya akwai na aiki akwaina..... In yana aiki sam baya son wasa, sannan in yana kan network kukan yaro be hanashi bari, yana matukar son amira don ko kuka tai se ran aisha ya baci, shi kullum akan bukata yake maana de hariji ne dukdade Aisha bata da son sex irin matannan ne wadanda basa son sex amma hakanan take Hakura tai tabashi, fahad bayason raini kuma saurin duka ne dashi tun gida in yan miskilancin suka motsa da kayi abu ze zane kannensa aisha na ganin in sunyi aure zedena dukanta amma ina ko yanzu intayi mishi badede ba Zaneta yakeyi hankali kwance kuma ko yana cikin bugunta yaji shaawar shi ta motsa se yayi abunsa, in kuwa tana period a takure yake yayita kumbure kumbure abu kadan fada, amma yana nuna mata soyayya sosai shi be damu tai girki ko kartayi ba shide kawai akula da shimfidarshi, be damu tana kwance tana chart ko bacci ba ya gyara gida yayi wa amira wanka yayi girki ba saboda yasan tana kokari sosai dashi, ko unguwa zasu many time shiyske parking tana charting dinta, shi baya son yan aiki agida aganinshi zasu takurashi tunda kusan kullum yana gida, megadi kadai garesu shima tsoho tuguff ne, wato fahad na da matsanancn kishi  Aisha ko fita zatayi to ko Vaseline bata shafawa inko tayi makeup to baya bari, da yake dan boko ne kuma be koshi da islamiya ba shiyasa be damu yasata saka nikab da hijab ba, da gyalenta take yawo. 


Aisha nada problems duk da tasan yana da yawan bukata amma kullum se anjamashi aji sannan ya samu, kuma ita kadai ta mashi kadan amma hakanan yake hakuri saboda beda tsarin auran mata fiye da daya, kuma bata damu da kula da jikinta ba tana shan kayan mata kam amma banda gyaran jiki, gata itama da tsinannan kishi kamar shi agari, inkagansu dole su burgeka ka kara kallonsu

Cigaban labari

faseelat ta meda wayarta jaka tafita gidan tatari adedeta tace "G. R. A zanje nan gaba kadan da kalamu wahid shopping mall"

Me adedeta yace "muje hjy "

Tashiga tanata sakin murmushi ita kadai.

wai kode akwai abinda faseelat ke shiryawa ne 🤔

RAGON MIJI


PAGE2⃣6⃣*




*Dedicated to RAGGON MIJI FANS GROUP 1* 


*KUSANI INAJIN DADIN COMMENTS NAKU YANA SA INJI CIKINA ZE FASHE SABODA DARIYA INA MA ZAN IYA LISSAFO KU AMMA KUNYI YAWA, KUSANI PAGE DINGA NAKU NE MAMAN MAMY NA GODIYA DA  NUNA KAUNA*


*INA FASEELAT MUTANEN NIGER🤣the harija🤭inamiki sonso ana mugun tare*





Ta fiddo wayarta ta kira maman amira tace "gani fa nafito yanzu kinganni, wane kalar gate nema kikace? "


Aisha tace "black and golden color "


Faseelat setaji muryar maman amira very silent kamar Marar lpya se taji ba dadi tace "lpya de kike ko? "


Maman amira tace "sede Kinzo inajiranki"ta datse kiran, 


Faseelat tai shiru tana tunanin ko me ke damun maman amira oho, ta danna wayarta screen saver nata ya bayyana ta cigaba da kallon pic din ta. 



Suna zuwa bakin gate din gidan tace me adedeta ya ajiyeta gidan beda wuyar ganewa saboda yayi bakin titi sannan ko da kwatancen gate din gidan kawai zaka iya ganewa tangamemen gate ne yasha zanen golden,ta mikawa me adedeta kudinshi ta isa bakin gate din tafara kwankwasawa tana kallon saman katangar gidan duk flowers Sun baibayeta. 


Me gadi ya bude yana kallonta ya gaisheta ta amsa tana meda mishi gaisuwar ya bata hanya tashiga ya bita da kallo yana iya cewa tunda yafara gadi gidan ba macen da yataba gani tazo da hijab se faseelat, sede suzo da gyale, after,ko himar, ko hakanan gidigai-gidigai, yakoma ya zauna yana cigaba da sakar hulunanshi. 


Faseelat tunda ta shiga gidan ta sake baki tana kallon girma da kyan gidan ga yan rumfuna nan irin wanda bature yayi acikin gidan ansa masu furnitures kamar wurin shakatawa, sannan ga dan karamin swimming pool dinsu  ga wurin ajiye motoci, motoci reras sunfi biyar a pake masu kyau da tsada, ga wurin wasan amira anzuba masa kayan wasa iri iri, kai gidanfa ya hadu komi yaji, ta samu ta yakice kauyancinta don kare girma 🤪 ta isa bakin kofar shiga ainihin gidan tafara danna door bell, 


Maman amira na kwance kan bed taji ana danna bell tafito tana kara rage damuwarta don baadade ba fahad ya mare ta sabida kawai tana bawa amira ruwa seta kware shikenan ya dauketa da mari yaja diyarshi sukabar gidan tasha kuka sosai shiyasa har muryarta ta canza har faseelat tagane, taje tabude kofar tana kakaro murmushi, 


Faseelat ta saki murmushi tanajin dadi tai tsaye bata shiga ba, maman amira taje ta rungumota tajawota ciki tana cewa "wow kanwata kinganki kuwa? Wai dama haka kike?wlh pic muni ma yake miki kinhadu "ta saketa tana kara kallonta, 


Faseelat tai dariya "hmm anti kenan wai miya sameki naga idanunki sunyi ja kamar ma kumburi a fuskarki "tana kara kallon fuskar, 


Maman amira ta waske maganar "ki zauna mana kinyi tsaye ya hanya yaude Allah yayi naga kawata kuma kanwata "


Faseelat tai shiru tana kallon aisha tace "anti bazaki fadamin ba? Ga muryarki nan har ta canza miya sameki jiya fa lpya lau mukayi waya da daddare "


maman amira tai murmushin jindadi "why faseelat zaki damu kanki bugewa nai da kofa na zauna nasha kuka na shinefa kikaga muryata har ta sauya"


faseelat tace "sannu anty gaskiya banji dadi ba Allah ya baki lpya "tana bata fuska alamun tausayinnan, 


maman amira tai dariya "zo, zo "tajata har kan kujera irin kujerun nan masu amfani da AC inba ita suna saurin lalacewa, 


itama ta zauna tana fuskantar faseelat tace "ya amarci ya jindadi? "


Faseelat tai murmushi tace "ehinnn anti kenan "


Maman amira ta juya ido tana mata hararan wasa tace "bari nakawomiki abinsha "tatashi tai hanyar kitchen, faseelat tasaki ajiyar zuciya ,ta daga kai tana kallon gidan daga main palo se daku na biyu se kitchen se upstairs,kai gaskiya gidannan yafi karfin gida sede akirashi da mansion 🤣ta dawo da kallonta cikin Main falon tana bawa idanunta hakki, idonta ya sauka kan pic din fahad tangamemen enlargement shikadai ta na kallon pic din tagane ya kwana biyu saboda yanzu yafi cika tazama magidanci, ga sunan pictures birjik wasu shida maman amira wani su da amira,, wani pic takurama ido ya ruko maman amira ta baya itakuma tana dariya shima yanayi, dandanan taji idanunta suncika da kwalla tai sauri tasa yatsa ta debe wadanda suka zubo ta cigaba da kokarin meda sauran, sega maman amira ta fito daga hanyar kitchen din dauke da babban plate tazo ta ajiye, gaban faseelat tana ta kakaro faraa saboda bata saba ba tanayi ne kawai don faseelat tagane tayi murna da zuwanta, 


ta zukuna ta bude drink din berries king non alcoholic ta tsiyaya mata a cup cikin plate din kuma ga wani snack nan a ledanshi ta mike tace" bismillah"

tana komawa tazauna kan kujera, 


faseelat tai murmushin dole don tana ganin pic din nan duk ta nemi farin cikin ta rasa ta dauki cup din ta kurba ta meda ta ajiye, 


Ta dago ta kalli maman amira tana mata kallon kurilla, abun yabata mamaki tana cikin  irin gidannan amma gatanan a rame, duk dade kiba halittace amma ita ta ramar daka gani  kana iya cewa rashin abinci ne ko damuwa, 


Tana cikin tunani maman amira data meda idonta akan katuwar plasma dake mamaye a bangon falon kallo, ta dawo da dubanta kan faseelat tace "to ya megidannaki yana lpya? "don abinda yasa tai saurin kara sakin jiki daita kenan jin tayi aure shiyasa har ta barta tazo gidanta. 


Faseelat tace "lpya lau ,anti wai ina my daughter zuwannan fa Nata ne ita kadai ba Don ke ba "


maman amira tai murmushi tace "dazunnan suka fita itada daddinta amma tunda kikaga sundade haka to ya kaita wurin momy ne, kuma nasan bazata barta ta dawo yau ba don nasan tayi missing dinta sosai "


Faseelat ta bata fuska tareda cewa "ayya banji dadi ba gaskiya naso yau taga antin ta itama kullum sede muyi waya, gaskiya banji dadi ba "acikin ranta harda rashin jindadin ganin fahad ,


Maman amira tace "I'm sorry, ko da bakizo ba nidakaina zan kai miki ita watarana har gida "


Faseelat tace "hmmm "


Maman amira tai dariya "take it serious, dagaske nake "


Faseelat tace "Allah yakaimu "


Sukai shiru maman amira tayi kokari sosai jan faseelat da wannan doguwar firar duk tanayi ne don faseelat ta sakijiki sosai, don yanzu ma data ganta taji takara son muamala daita ganinta cikin decent dressed kuma looking wisely and educative, 


Can zuwa maman amira tace "ina charting ananan ana fama ko? "


faseelat tai murmushi "anty ai kinfini zama online kusan anytime kina online har mamaki nake "


Maman amira tai dariya tace "wani lokaci kina ganina online ne kurum amma bana kai, wani lokaci kuma I'm  doing nothing shiyasa nake hawa in samu in rage kewa ,ina wayar ki ne? "


Gaban faseelat yabada dummm har seda yan hanjinta suka motsa saboda kaduwa se yanzu take danasanin saka pic din fahad as wallpaper and screen saver, 


Hannunta na Rawa ta zage zif ta fiddota tace "gatanan"


Maman amira ta amsa tana jujjuya ta aganinta faseelat tafi karfin rike wagga wayar infinix hot 6, 


Itako faseelat cikinta kuka kawai yake dan tasan inde maman amira taga pic din kashinta ya bushe, 


Maman amira tamika mata wayar batare da ta ko danna taba tana tabe baki don ita ba Mace bace me binciken abin wani ba, faseelat ta amsa tana godiya ga Allah aranta, 


sede taga maman amira ta tashi ta haye upstairs dasauri, 


Faseelat ta saki katuwar ajiyar zuciya tana kallon wayar tai sauri ta sakata jaka, aranta tace bari ta tashi ta tafi hakanan, 


Can bayan kusan 20 mnt maman amira ta sauko daga upstair din tunda ta sauko faseelat ke kallonta gaskiya ba lefi aisha na da kyau itama matsalarta daya de rashin kayan aikin boob da bombom 🤣 rigar jikinta faseelat tabi da kallo green din gownt ce tabi koina na jikinta dayake roba ce, seta tuna fahad fa yana ganin wagga shigar , ranta ya baci ta dauke kai tana jin kishi a ranta, maman amira ta sauko takaraso wurin tana cewa "sorry na barki ke daya "


faseelat tace "bakomi anty "


Maman amira ta daga wayarta tana latsa, faseelat tabi wayar da kallo dagani tsadadda ce bata saniba ko tama shigo Nigeria oho, 


Maman amira ta jawo kwalin iPhone 7 da ta ajiye gefenta ta mikawa faseelat tace" ga tsarabarki"


Faseelat ta amsa tana murmushi tana dubawa taga kwalin waya ne da sauri ta fiddo ido waje ganin an rubuta iPhone7  ta dago tace "anti wannan ce tsarabata? "


Maman amira ta daga mata ido, 


faseelat takara kallon wayar inbata manta ba dubu 150 kwanaki taji abul na cewa take, 


Tai shiru ta rasa ma me zata ce, 


Maman amira tace "karfa ki tunanin nabaki wata kyauta wannan ba komi bane kinfi karfin ta agurina wlh, ki amsa plsss karki medo min in kika ki amsa bazanji dadi ba kuma zanji cewar baki dauki kawancen mu yanda na dauka ba "


Faseelat tai murmushi ai dama Batai niyar medawa ba tace "to Nagode anty Allah yasaka da alhairi ya kara budi "


maman amira tace "amin ya kuma barni da habibina "


Faseelat tai yake tace "amin "


Maman amira tai dariya tace "nafison irin wannan adduar fiye da kowace, don inde inatare da dad din amira to nagama samun komi "


Faseelat tai yake tace "anty ni zanwuce "


Maman amira tace "tunyanzu? To jira na dauko mayafina na kaiki "


Faseelat tace "anty dama kinbarshi karki wahalar da kanki zan hau napep "


Maman amira tamike tsaye tana Cewa "inani ina barin momyn amira ta hau napep? Allah se na kaiki daganan se naga gidanki kinga innatashi zuwa base kintsaya yimin kwatance ba "


bata jira cewar faseelat ba ta haye bene ta dauko key da gyale ta zo ta yafa tace wa faseelat "muje to "


Faseelat tai gaba tana mamakin yadda zata fita da wannan rigar dukda de driving zatai amma rigar ta kamata sosai ga gyalen dan tsito, 


Maman amira tafita taja kofar Tawuce gaba faseelat na binta abaya har bakin mota ta shiga ta bude faseelat ta bude ta shiga, taiwa me gadi horn ya hangame mata gate tafita da motar, 


Suna hawan titi fahad na isowa bakin gidan ,yabi motar Aisha da kallo yana mamakin ina zata, dama megadi be rufe gate ba ya shigar da motarshi cikin gidan. 


Su faseelat na tafiya suna fira, alhamdulillah maman amira taji dadin zuwan faseelat dan yanzu jinta take wasai kamar ba abinda ke damunta, 


Faseelat kau firar kawai ake amma hankalinta na can tana tunanin yau tayi rashin ganin fahad to yaushe zata ganshi ?


Tanawa maman amira kwatance har lungun su, ana zuwa kofar gate din gidanta tace atsaya, maman amira ta tsaya ta juya ta kalli gidan tace "nan ne gidanki, insha Allah ki tsammaci zuwanmu nida amira, "


Faseelat tace "se kunzo Nagode sosai anty bazan taba mantawa dake ba "


maman amira tai murmushi tace "nima haka "


faseelat ta bude motar ta fita tana kallon gate din gidanta seta ganshi very small .


Maman amira taja motar ta tabar wurin, faseelat tabude kofa tashiga, tana Shiga falo ta zube kan kujera tana lumshe ido a ranta tace" yaushe ne zanaganka inji sautin muryarka? "

Se kuma tai shiru afili tace "anty nada kirki sosai i love her kindness and the love that she is showing to me "ta dago kwalin wayarta tai kissing tace "nasamu makamin yaki "

Tai dariya, 


Ta duba wallwatch taga to 6 ta mike tana jan tsaki tace "bari naje naiwa wannan alaramman tuwon da yace kafin yazo yafaramin makyarkyata 🤣

Post a Comment

0 Comments