TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

RAGON MIJI page 31-32

 RAGON MIJI


*Bismillahirrahmanirrahim*


*fans inajin dadin comments dinku, naga yadda ku ka caccaki faseelat 😂,kusani faseelat yarinya ce ,kuma dan adam ajizine kuyi mata uzuri mana inafatan zaku cigaba da biyoni dan jin cigaban labarin*








Yayinda itakuma ta sunkuyar da kai kasa, ashe duk abinta na chart ne kawai yanzu gashi ta ganshi takasa komi, gabadaya ya mata kwarjini bata kara sanin shi kyakykyawa bane  se yanzu data ganshi face to face. 



Shi ko kallonta ya cigaba da yi, yeah she's that girl to mi yakawota nan? yake tambayar kanshi yana cigaba da kallonta tayi mai kyau sosai ba abunda yakara burgeshi se shigarta in long hijab, 


Zuwa can ya dauke ido ya cigaba da aiki a system dinshi, 


Faseelat kamar kwai ya fashe mata aciki taja kafa taje ta samu wuri ta zauna, ta dan saci kallonshi yana ta aikinshi hankali kwance, siririn hancinshi da dan karamin bakinshi   lebunansa pink color ga abinda take mutuwar so sajen shi a kwance yana sheki, 


Ta dauke ido ta hadiyi miyau tana matse kafa, shiru 2mnt bawanda yayi magana cikin jarumta irin tata tace "ina wuni "


Yayi banza be amsa ba kuma yajita sarai sede ya dago suka hade ido tai sauri ta dauke nata, ya kara kallonta na wasu seconds ya koma ya cigaba da aikinshi, kawai yana mamakin Karfin halinta, yadda taiya yi mishi magana,


Faseelat ganin shiru yasa ta fiddo waya ta kira maman amira, 


Maman amira da ke wajen saloon ta dauka tace "momyn amira yaushe zaki zo ne? Ko kintaho?"


Faseelat tace "anty gani nazo "


Maman amira tace "ayya wlh bansan zakizo da wuri ba nazata seda marece, gashi ni ina wurin saloon, zaaimin da wankin kafa, ita kuma amira ai mata kitso "


faseelat tace "to bakomi anty bari natashi natafi se bayan salla in Allah yakaimu "


Maman amira tace "au kina ciki kenan, ashe daddyn amira ya dawo, to tunda kina ciki kijira ni mana daman dan kar in shanyaki waje, ki bani 30 to 40 minutes inazuwa "


Faseelat tace "Tom anty se kindawo "

Ta yanke kiran dan koda 2 hrs maman amira tace tozata iya jira saboda ko kamshin turaren fahad kawai da ya mamaye falon yasa ta tsaya bare ga kyakykyawar fuskar shi tana kallo, 


Tunda tafara waya yake kallonta se lokacin ya samu amsar tambayarshi wato kawar aisha ce, he wonder ina ta samo wannan, ya meda kanshi kan aikinshi cikin ranshi yana cewa "she has sweet voice too"


Faseelat tai zaune dukda de adarare take amma she love the moment, a dan sace take samu tana karemishi kallo, yana sanye cikin white shirt blue trouser, yayi kyau sosai ta cigaba da satar kallonshi she don't think ta fishi da wani abu dan inma fari ne har ya fita ,


Suna zaune ahaka shima suna musayar ido da wannan ya dauke nashi se wannan ya soma, 


Can de fahad yameda hankalinshi kacokam kan system nashi, 


Faseelat ta rasa abinyi zaman yafara isarta seta jawo waya takira aisha, maman amira na dauka faseelat tace "anty I'm feeling hungry "


Maman amira tace "ayya I don't think zaki samu abinci amma ki bude fridge na hanyar dining ki samu ko snack ne da drink kici "


faseelat tace "ayya anty ni abinci nikeso fa "


Maman amira tace "no be problem kishiga kitchen ki dafa abunda kikeso kafin na dawo "


Faseelat tace "OK I'm waiting "


Ta kashe kiran ta tashi tsaye ta ajiye Jakarta takama hanyar kitchen fahad yabi bayanta da kallo hijab din jikinta roba ce ta dan fito mata da shape kadan, 



tana shiga kitchen tabude freezer wow ga freez chicken nan ga fish, liver and kidney ga chicken breast nan ma na company "


Ta danyi tsaye tana tunanin mi zatayi, can zuwa tace "le me do yam porridge and toastedchicken "


Ta fiddo kaza da sauri da ice fish ta wanke tasa kasu a oven on law heat don  Ice din dake jikinsu tayi melting, 


Ta fiddo kayan miya tai blending tadora tukunya a gas tafara soya su, 


Ta fiddo kazar da fish din har sunfara zafi ta ajiye tai grettin tarugu da albasa tazo tai hadin kazar ta shafa mata ta kai fridge don tayi marinated ta cigaba da aikinta for like 20 mnt ta fiddo ta ,ta saka a foil paper takara hada mata spice tasaka a oven, 


Ta koma ta cigaba da hada faten doyanta for like 30 mnt da shigarta kitchen yaji kamshi yana kawowa inda yake, 



40 mnt dede ta gama komi ta dan zuba wanda zata ci a plate ta zuba nasu a hotter takai dining, 


Yana zaune yaga tafara zarya dining to kitchen yatashi ya dauki system dinshi ya haye sama, faseelat na fitowa bataganshi ba, 


Tasaki murmushi "kagama duk wani jiji dakanka zaka shigo hannu ne "tafada saboda karfin hali,yo karfin hali mana🤣 


Ta zo ta zauna tana cin nata hankali kwance tana gamawa takira maman amira, tana dauka tace "anty har yanzu kusan 1hr fa kenan da zuwana "


Maman amira tai dariya "sorry gamu kan hanya "


Takashe kiran tana magana da amira "zakiga momy ko? "


Amira ta daga kai tana murna,


Faseelat na zaune amira ta shigo da gudu ta rungume faseelat, faseelat ta dauketa tana jindadi, aisha ta shigo tana faraa tareda cewa "sorry I keep you waiting "


Faseelat tai dariya "bakomi anty "


Ta cigaba da wasa da amira, 


Maman amira ta haura sama, ta samu fahad nata aikinshi tafada jikinshi tana fadin "washhh! "


Tace "yaya I'm very tired "tana shige mai, 


Ya matsar da laptop din ya kara jawota sosai kan cinyarsa yana Shafa kanta "kinyi kyau sosai honey "


Aisha tai Far da ido tace "thanks you my heart beat "


Ya na mata kallon bukata yadora hannu kan boob's dinta yana matsawa yace "I want to have you ..."


Ta katseshi "but not now yaya kaga fa inada bakuwa plss kabari na sallameta sannan "


Yayi murmushi yace "who is she to you "


Tace "just a friend "


Yace "good"


Ta tashi tsaye "let me attend her karta ga na dade "


Kallo kawai yabita dashi har tafita, tana fita yasa hannu ya na shafar sajenshi tareda furta "ahmmmmm" 



aisha na fita ta hangi warmers akan dining tayi gun ta bude tace "wow so delicious "


Ta rufe tafito tana zama tace "faseelat har wahala kika bawa kanki? "


Faseelat tace "a, a bawata wahala anty "


Aisha tace "thank you yau zamuci ur delicious cooking gaskiya kin iya girki "


Faseelat tai dariya tana cewa amira "my angel kitsonki yayi kyau, anty nima fa naiya kitso ni zanwa faseelat na salla "


Aisha tai dariya "kinada kokari gaskiya Allah yakaimu, da inayin kitso da har ni zakiwa to sede bana kitso daddinta bayaso ya fison ganin gashi haka "


faseelat tai murmushi ta dubi agogo to 2 ta mike tsaye "anty bari nayi salla nawuce "


aisha tace OK, "ga toilet nan daga kofar fita kitchen, bari nakawo miki carpet "


Faseelat ta juya ta tafi tayo alwala ta dawo tai salla suka dan yi labari ta tashi zata tafi maman amira tamata kyautar perfume, ganin zata tafi amira tafasa ihu wanda yasa fahad lekowa daga saman bene, 


Amira tana kuka tace "i want to follow you mommy "da maganarta da bata ida gogewa ba, ta rikewa faseelat hijab, 


Faseelat tana rarrashi aisha nayi faseelat har suka fita, fahad na Sama yana kallo su basuma san yanayi ba, suna fita ya saki murmushi, 



Faseelat tabar gidan sannan aisha ta dawo tanata wa amira wasa har ta samu tai shiru, sega fahad ya sauko tace "yaya muje muyi lunch I'm hungry "


ya amshi amira yana fadin "my blood what do you want ?"


Aisha tace "rabu daita ta cika rigima "


Har kan kujera ya zaunar da amira ya zauna aisha tai sarving dinsu ta zauna tafara ci, spoon daya tayi ta rumtse ido tana fadin "yummy"tana juya kai, 


amira tuni take ta kai spoon baki tanacin abincin yana zaune yanata kallonsu, baya tunanin waccan insane girl din zatayi wani abun kirki, 


Can zuwa ya daure ya kai spoon baki, wani dadi ya ziyarci kwakwalwarshi ya rumtse ido, inda akabar aisha baya kenan ba ruwanta tana ma iyayin sati batai musu abinci ba sede suje waje suci ko yayi musu da kanshi, tun tana gida mommy ta shagwabar dasu komi se me aiki ce keyi baruwansu sede charting bacci da kallo, 


fahad yaji taste yakara dauko spoon yakai baki besan lokacin da yace "wow" idonshi rumtse, 


Aisha har ta dau spoon zata kai baki ta meda ta ajiye wani haushi da kishi suka taso mata, taja plate din gabanshi "girrrrr "

Ta medoshi gabanta, 


Ya bude ido yana kallonta idanunta har sunyi ja tatashi tafara hada abincin cikin cooler har da wanda amira keci, 


Yana kallonta idonta tab da kishi yace "aisha plsss mana kibari muci abincinnan yamin dadi "


Ta watsa mishi harara hawaye na neman fito mata tace "wlh baba tsoho zan kaiwa shi bawanda zeci abincin nan "


Ta cigaba da juye abincin, yahade hannu wuri daya yana kallonta, ta gama juyewa ta rufe kular ta dauka, 


Amira tafasa kuka "daddy talk to mommy to bring my food back "


aisha tawatsa mata harara tai waje, 


Yabita da ido ya girgiza kai, ya jawo amira yana tapping dinta yace "it's okay bari muje restaurant muci kinji? "


amira ta cigaba da kuka, yana cikin rarrashinta aisha ta shigo tana ta hade fuska ta hau step din bene har takusa hayewa ya kira sunanta "Aisha! "


ta juyo fuskarta da hawaye tana kallonshi......

RAGON MIJI


*Bismillahirrahmanirrahim*




*dedicated to yan amana 🤣*





Se yaji badadi ganin hawaye fuskarta yayi alamar tausayi da fuskarshi, bata jira shiba ta haye sama, yayi murmushin takaici ,bega wani laifinsa ba ita ta gayyato shi cin abincin honestly speaking abincin yayi dadi b4 yafara santi she's the one that begin, ya juya kan amira yace " angel muje mu rarrashi momy she's angry with us "


Yaja amira suka haye sama, suka shiga dakinta aisha tahaye saman bed tana rusa kuka yanaganin abinda take ya dafe goshi, yaja hannun amira suka fita yakaita dakinshi yabata game ya fito ya koma gun aisha, 


Tana kwance tana shan kukanta yazo yazauna kan bed din yajawota jikinshi, ta cigaba da kuka don wani katon abu taji yatsaya mata a wuya, 


Yana rungume daita tana cigaba da kuka yace "ya Allah"yana rumtse ido dan jin kukanta yake har cikin zuciya, 


Magana yafara mata "aisha plss stop this crying, kukan ki na tabamin zuciya,nayi lefi kiyi hakuri plss, bansan zakiji zafi ba da bance abincin yayi dadi ba "


Ta dago ido tana cigaba da kuka tace "i love you yaya bazan iya hakurin abinda kayi ba inajin ciwo a zuciya ta sosai "


Ya fara share mata hawaye yana cewa "it's okay haka baze kara faruwa ba, nifa nakine ke daya sweety dan haka just wipe your tears and stop this crying "


Ta dago ido tana kallonshi yace "plss mana ko kinaso nima nayi kukan? "


Ta girgiza kai yace "toki hakuri my one and only "


Yana kashe mata ido daya, batasan lokacin da murmushi ya kufcemata, yayi murmushi shima yace "that's my girl "ya kai mata kisss, ya riga yasan aisha akwai kishi amma tana da saurin hakuri, 


Yasamu ya rarrasheta sannan suka tafi Chinese restaurant cin abinci, 



Faseelat tana isa gida tai ta juyi itakadai tarasa ina zata saka kanta don dadi finally yau de taganshi ,


Ta zauna kan kujera ta jawo wayarta ta tura mishi "kayi kyau sosai "


Ta ajiye wayar tai shiru tanajin haushin kanta yadda tai da ta ganshi. 


Ko da khalil ya dawo da daddare take ce masa maman amira nagaidashi kuma tabata turare, 


Yace "Allah sarki tanada kirki sosai gaskiya "



Lokacin da fahad yaga message din faseelat dariya ma abun yabashi yana tunanin yadda yaganta a tsorace, se ya tura mata smiling face, tana gani ko seda taji dadi. 



Ana haka aka shiga watan azumi, tunda aka fara azumi shikenan khalil ko romance din ma yadena yi da yayi bude baki ze cigaba da jan cazbi daganan yawuce masjid suyi isha da tarawih ya dawo da yagama cin abinci ya cigaba da laziminshi itakuma taita charting dinta da friends, 



Har akayi azumi 15 wani problem da faseelat ke fuskanta azumi ake amma ita shaawar karuwa take dan ko baccin rana takeyi mafarki take, 


shi ko khalil gajiyar azumi da aiki ce tahanashi katabus, 


Abun ya damu faseelat ta rasa ina zata saka kanta taji dadi, atleast ma tasamu wanda tafadawa zata rage wani abu, 



Yau bayan ya dawo daga tarawihi ya zauna yana lazimi, ita ko faseelat sede ta juya ta kalleshi tayi tsoki kasa Kasa "waishi khalil miyake nufi ne?akace masa su uztazan basa bawa matansu lokacinsu ne? Basa wata fira me tsayi be taba cewa yana sonta ba sede aukin santi in yana cin abinci, 


Hakanan taji tana son sharing problem dinta da maman amira, akai saa tana online faseelat ta tura mata "anty ansha ruwa lpy? Anty ina cikin matsala, shaawa tamin yawa, mijina be damu dani ba "


Maman amira na karantawa taji badadi tai mata reply "subhanallah, abu beyi dadi ba kiyi hakuri "


ta tura mata "anty shawara zakibani"


Maman amira tace "shawarata kije ki sameshi ki masa maganar, mijinki ne fa ba wata kunya tsakanin ku, ki masa maganar ku zauna kushawo problem din"


Faseelat tace "to Nagode anty "


maman amira tace "bakomi ai anzama daya "



Faseelat ta sauka online tana tunanin ta ina zata fara, don gaskiya hakurinta ya tafi karewa, 


Har Sun kwanta takasa mishi maganar can de tai ta maza ta fara kiran sunanshi ya amsa yana saurarenta, 


Tace "khalil banajin dadin yadda muke having sex"


Tana inda -inda tace "ni se nake ganin kamar baka lpya ya kamata kanemi magani "


Yayi shiru yana nazarin maganarta ya jawota jikinshi yace "I'm sorry faseelat,amma ni lpyata lau banaso na fara shaye shayen magani nafiso ki saba dani ahaka, faseelat bantaba koda rike hannun mace ba seke bantaba muamala da mata ba nike ganin shiyasa abubuwannan suke faruwa haka kiyi hakuri zuwa gaba komi ze dedeta "


Tai shiru ya dan matse ta cikin wasa yace "kinji "


Ta daga kai, yace "kuma cikin azuminnan wlh agajiye nake aiki yamin yawa shiyasa ko feeling banaji amma kiyi hakuri bayan salla komi will be normal "


Tace "to "tanajin haushi aranta itade tagama yarda da zuciyarta bashi lpya,ya zaai yace rashin sabo ne wata 7 ba kwana bakwai bane, suna haka bacci ya daukeshi while ita ko bacci batai ba, 



Bayan kwana biyu de abun na cigaba da damunta ta rubuta tambaya ta tafi daita wajen tafsir, ta saka a akwati, 


Kaidar malamin seya fara karanta questions sannan afara karatu tana zaune aka karanto tambayarta, 

"Aslm inama malam fatan alheri Allah ya shirya zuria yakara ilimi, malam munyi wata 7 da mijina amma be taba kusanta ta ba ,da abun ya daman namasa maganar yace min lpyarshi lau inyi hakuri dashi ahaka, malam ina cutuwa sosai, har ya kai matakin da bazan iya hakuri ba ina neman shawarar malam "


Bayan yagama karanta tambayar yace "bewar Allah kina cikin jarabawa daga cikin jarabawoyin duniya akwai shaawa, saboda tana saurin halakar da mutum, shawarar da zanbaki ki hakuri ki cigaba da kame kanki, sannan ki kai maganar ga magabata tunda kinmishi be gyara ba,inaba maza shawara kuji tsoron Allah kurika sauke hakkin matanku na aure saduwa shine banban ginshikin aure bazaka ajiye mata dan kabata ci da sha da sutura ba kace kagama mata komi, a, a akwai hakkoki da suka rataya akanka daga ciki harda kawar mata da shaawarta, da zama daita kuyi wasa da dariya bata labari da debe mata duk wata kewa da zata hanata ganin wani namiji awaje, dan wasu mazan iyakarsu sex shikenan ba dariya ba magana me dadi, mata suna bukatar kulawa sosai saboda masu rauni ne, muna miki fatan zaku dedeta da mijinki Allah ya dedeta tsakanin ku, idan kuma anfada wa magabatan be dena ba kina iya neman ya sakeki, saboda auren ya haramta tunda akwai cutarwa ciki Allahu aalam "


Faseelat tunda taji an amsa tambayarta memakon taji sauki se ma tashin hankali da tashiga wa zata samu da maganar 'ummi? Gaskiya baxata iya ba gwara de ya sawwake mata yafi, tai shiru tana tunanin khalil gaskiya yana matukar sonta kuma yana da halin kirki sede tarin kayan haushin shi, tai shiru tanajin tausayinshi, 



tana komawa gida takira maman amira awaya dan itakadai ce tasan matsalar kuma itama bata fada mata gaskiya ba tunda bacewa tai be taba kusantar ta ba, 


Maman amira na dauka jiki badadi faseelat ke bata labarin tambayar da tayiwa malam da amsar da yabada, 


maman amira cikin jimami tace "kiyi hakuri faseelat komi zewuce "


Tace "nagaji ne maman amira haryanzu zuciya ta takasa sonshi har nafara son wani daban "


Maman amira tace "subhanallah gaskiya be dace ba tunda de kinajin bazaki iyaba ki rokeshi ya sakekin"


Faseelat tace "to anty Allah yatemakeni ya yarda"


Takashe kiran ta zauna dabass kan kujera tanajin tausayin khalil, 



bangaren fahad ko yanzu sunfara charting da faseelat don yafara meda mata reply shima hakanan yakejin wani feeling akanta saboda pic datake ta turomishi any how, 

Kuma sosai yakejin dadin adduoin da take mai saboda bayada me mishi addua, mommy batayi befi tace mishi good luck ba a wayance, haka maman amira sede tace mashi best of luck, ko safe trip ko something de, 



Faseelat sosai tasha kuka saboda batajin dadi kwata kwata hakanan taji bazata iya tarar khalil  da maganar ba, 


Aranta tace "kayi hakuri khalil dole se nayi abubuwan da zesa ka sakeni "

Post a Comment

0 Comments