TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

RAGON MIJI page 37-38

 6


Tanajin khalil nakwala mata kira gabanta yafara faduwa ,segashi yashigo dakin komi na jikishi na kyarma yana nunata da hannu yace "ubanwa ye ya ajiye ki yanzu? "


Duk tsoro yakamata ganin yanda ya rikice sosai ta tattaro duk jarumtar tahadiye miyon tsoro tana mishi wani kallo tace "masoyi na mana wanda nike mutuwar so "taida da murguda baki. 


Cikin zafin rai yace "keeeee "yakaiwa bango naushi nan hannunshi yafara zubda jini, 



Batare da ya damu da ciwon ba yace "kina da hankali kuwa faseelat ko kinfara shaye shaye ne bansaniba? "


takara hadiye tsoro tace "hankali na garas sede giyar soyayya dake dibata"


Yana ciccije baki yakara kaiwa bango naushi cikin bacin rai yace "ke danubanki ni kike fadawa haka? Zan babballaki, anan"


Tana mai kallon sama da Kasa tace "Allah ko? To bismillah "


Yakara ciccije baki jijiyoyin wuyanshi awaje yace "da aure na kike fira da wani kuma kirika fita dashi? Wai faseelat kinason kiga annabi kuwa? "


Taja tsoki "yazaai inso ganinshi aise ku waliye,"


Yana binta da kallon bacin rai Ya samu wuri ya zauna ya dafe kai don inya cigaba da tsayuwa ba abunda baze faruba, Da kuma tunawa da koyar War manzo (S. A. W) da yace inkayi fushi ka canza mazauninka inkana tsaye ka zauna inkana zaune Ka kwanta in a kwancene ka sauya wuri, 


Tatabe baki "ni wlh kana bani kunya mutum ba zuciya nace ka sawwakamin kaki kai wlh uwarka tayi asarar haihuwa don bata Haifi namiji ba anan "


Tuni ya mike tsaye ranshi yakara baci yace "faseelattttttttt"


Da karfi wanda seda yan hanjinta suka kada ya juya yakara kaiwa bango naushi hanninshi ya rika tarara jini, yanata huci yana waige waige kamar wanda ke neman wani abu, 


tace "kuma ka sawwakemin inka haihu ga uwarka da ubanka"



Ya rika nunata da yatsa yakasa cewa komi, 


Ta juya ta yaye hijabin jikinta tana jan tsoki tace "andeji haushi wlh saratu de tayi asarar haihuwarka "


yana kyarma yana ciccije makoshi yace "ke ke kije kije na sake kin "yanata huci duk ya harmutse. 


Ta juyo ta mai kallon sama da Kasa tace "simple abu amma katsaya bani wahala kabawa kanka, to yanzu nasan ka haihu, Allah yabamu alheri "


Ta meda hijab dinta ta shiga bedroom don ajiye ledar hannunta cikin kayanta, 


Khalil ya durkushe wurin yafasa kara yana kuka sosai hannunshi biyu yana tumurmuza gashin kanshi dasu, ga jini yanata Bin hannun. 


Ta ajiye kayanta ta dauki new phone dinta tafito tana kallonshi duk yabata tausayi, 


har tafita ta dawo idanunta na zubda hawaye tazo ta durkusa gabanshi tana kuka ta jawo hannunshi ta ciro head din kanta tajashi ya yage tafara kulle masa hannun nashi, 


Tunda ta dafa shi yake kallonta har zuwa yanzu da take kulle mishi hannu ,


Cikin kuka tace "kayi hakuri khalil ka yafemin duk abinda namaka dan Allah ,wlh duk nayi ne saboda ka sawwakamin, amma abinda kagani yanzu ba haka yake ba Allah bantaba zina ba, kayi hakuri banso natafi da hakkinka, inaso kayafemin dan soyayyar da kakemin,dukda nasan be kamata Ka yafemin ba na cutar da kai na kuntata zuciyarka pls forgive me "

Tana gama kulle mishi tasa tafukan hannuwanta ta rufe fuska tana kuka, 


Shegina faseelat seda tagama tsula tsiyarta take neman afuwa hohoho 😂🤸🏼‍♀



Yana kallonta cikin zubda hawaye bece komi ba ,


ganin bece komi ba ta tashi tsaye ta juya zata tafi ya riko hannunta ta juya tana kallonshi tana zubda hawaye, shima hawayenne ke fita daga idonshi ya girgiza mata kai yace "karki tafi faseelat plsss ki hakura ki zauna dani haryanzu inasonki "


Ta sa hannunta daya ta zare nashi tana zubda hawaye tace "khalil zama na da kai hatsari ne arayuwarmu duka, domin zan jefa kaina cikin sabon Allah kai kuma zan cigaba da tauye maka hakkinka rabuwar mu shine yafi zama alheri Nagode da duk soyayyar da kanunamin da kulawar da kabani "


Ta juya tafita dasauri tana kuka shima kukan yakara kufce mai, ya zauna yayi tayi, 


Tana fita har anfara kiran Maghreb tasamu adedeta tahaye se gida, 


Shima yatashi ya wanko fuska ya fito daga gidan ya tada mashin dinshi ya nufi gidan hjya ko yaje yarage jin ciwon da yakeji a duk ilahirin jikinshi. 



Me adedeta na ajiye ta ta mika mai 200 ta shige gida tana kara volume din kukanta. 




Ummi na ta aikin dare Mubarak na alwala ummi na kiran" auta yi sauri kagani karka rasa sal......."bata idaba faseelat tashigo tana kuka, 


Ummi ta tashi tsaye faseelat ta ruga ta rungumeta, ummi innalillahi kawai take memetawa gabanta na faduwa, Mubarak me alwala tuni yamike, 


ummi tasamu tace "ke lpya? Kika shigo kina kuka haka ?"



Faseelat ta dago ido da hanci jagege tace "ummi khalil ya sakeni "


Ummi ta dafe kirji "saki? Ke karya kike khalil baze sakeki ba, to ma ubanme kikamishi ya sakeki?"


Faseelat tace "banmishi komi ba kawai saki na yayi "


Ummi tace" karya kike ai ruwa baya tsami banza, hakanan khalil baze sakeki ba yaro me hankali da girmama manya, bari nakira hjya inji miyafaru "

Ta saki faseelat tai daki dauko waya takira hjya, 


Mubarak yaje ya dafa faseelat yana tayata kuka. 




Khalil kau yana isa yashiga ya haye saman slope din hjya ya cigaba da kuka, hjya na toilet tafito taji kukan mutum tafito waje cikin tashin hankali tace "khalil lpya kake kuka haka kamar yaro "


Yana kukan yace "na Saki faseelat hjya"


Hjya ta tabe baki "to mi taimaka ka saketa? "



yana kuka yace "hjya nasamu faseelat na fira da wani akofar gidana "


Hjy tafara sallallami tana tafa hannu sannan tace "oh Albasa batai halin ruwa ba to kai miye na kuka kamar an aiko maka sakon mutuwa ta? "


Ya girgiza kai yace "inasonta hjya wlh inason faseelat "


Hjya ta wurga mai harara tace "gafara can marar wayau kawai tana bin mazan zakace kana sonta, ai gwara da ka saketa tundade yariska ce "


Ya girgiza kai "hjya inasonta sosai bazan iya rayuwa babu ita ba "


Ta banka mai harara tace "tsaf kau zaka cigaba da rayuwa se kace bakada kishi zaka nace ma yariska, hmm ai nasan ba komi ne yakejan hankalinka ba se farinnan da yan abubuwan duniyar kasha kuruminka insha Allah zansamo maka wadda tafita a komai "


Ya rika girgiza kai yana kuka seta lura da hannunshi dake kulle jinin har ya dan fito tai sauri ta matso wurinshi takama hannun, tana kallo, ya cigaba da kukanshi 


Hjya cikin jin tausayi ta kwantar da kanshi kan jikinta tana rarrashin shi "kayi hakuri kaji dana haka Allah yaso ka daure, dubo duk kaji ciwo saboda zuciya, "

Ya dena kukan yana ajiyar zuciya yana tunanin faseelat, maganar da tai masa akarshe, 



Wayar hannun hjya tai ring, hjya ta dauka da sallama daga can bangaren ummi tace "faseelat ce tadawo gida tana kuka wai khalil ya saketa shine abun ya dauremin kai nace bari nakiraki naji ko kinsan wani abu don nasan khalil baze saki faseelat hakanan ba, "



Murya a raunane hjya tace "gashinan shima kukan yake, tonima haka yake fadamin ya saketan "



ummi tace "antaba Saki hakanan ba wani laifi? "


hjya tace "to ya de ce samunta yayi tana fira da saurayinta "


Ummi taja salati tace "hjya dan Allah kibawa khalil hakuri, Nagode se anjima "


Tai tsaye ta kurawa faseelat ido faseelat nata kuka ummi tace "kai Mubarak yi tafiyar ka masallaci "


Ya tashi yafita faseelat batai aune ba taji ummi ta rufeta da bugu ta koina, ta samu tatashi tana zagaye gidan ummi tana binta tana tafka "sena kashe ki yau dinnan ni xaki kunyata baki isaba "tana fada cikin nishi, 



Kwatsam sega abba yayi sallama da gudu faseelat taje bayanshi ta boye ummi tazo tana nishi tace "alhaji bani yarinyar nan inci ubanta dan Allah "


Yace "haba hjya meyafaru haka kike mata irin wannan bugun da baki mata a yarinta ba "


"wai alhaji yarinyar nan dan bata tsoron Allah take kawo maza suna fira kamar wata budurwa, wama yasan iyakar abinda takeyi kabani ita ingama cin ubanta kuma sena medata gidan khalil dole tabashi hakuri, yo da hakanan ya aka kare bare yanzu datasan dadin namiji,"


Faseelat na labe bayan abba tana tari, cikin dan dauriya ta manya yace "kiyi hakuri mu zauna muji ta bakinta wuce mushiga ciki "


Ummi tace hmm tai gaba shikuma yajawo faseelat daga bayanshi tana ta zubda hawaye yajata suka shiga dakinshi. 


To ko faseelat zata fasa Kwan? 

Ko zaa sasantasu ta koma gidan khalil? 


To muje de zuwa yanuwa, 


7

Ummi na zaune kan kujera haka abba itako faseelat tai zaman dirshan kasa kanta kasa, ummi se banka mata harara take saboda takaici, 


Abba ya kalli faseelat yace"faseelatdagaske yaganki da saurayi kuna fira ?"


Ta daga kai tana share hawaye ummi tai kukan kura zata riko faseelat abba yariketa, faseelat takara matsawa can nesa, 


Ummi ta kalli abba tace "alhaji dan Allah kabari Inci ubanta ko na rage jin zafin dake raina wannan fa karamar bazawara ce agabanka, ni banma ko yadda a fira abun yatsaya ba maybe ma kamasu yayi cikin daki suna iskanci "


Abba yayi saurin cewa "subhanallahi"


Faseelat tafara girgiza kai tanayin baya baya "ummi wlh a, a dan Allah kiyi hakuri "


Abba yace "faseelat da ilimin ki kika aikata irin wannan sakarcin? Haba kinbani mamaki ai amfanin ilimi aiki dashi ina duk ilimin naki ya tafi har kikabari shedan yayi nasara akan ki eye? "


Faseelat tana kuka tace "dan Allah abba kayi hakuri, bazan sake ba Allah "


Ummi tai wuf ta hau kanta tana jibga tana fadin "kinci ubanki da sakewar yar iska kawai "tana ta jibgarta faseelat ihu kawai take abba yayi zaune yana ta kallonsu don kafafuwanshi Sun mashi nauyi, 


Kuwa kawai faseelat keyi ana haka wayar abba tafara ringing ganin baba babba ne ya dauka sede baaji dole yatashi ya fita yana fita kofar dakin yagasu ishak sunbi layi kowa jiki mace,yawuce yafita daga gidan yana magana da alhajin, 


Baba babba yace "wai lpya gidannaku yake? Naji anata kuwwa haka? "


Abba yace "wlh ba lpya ba faseelat ce takaso aurenta wai mijin yaganta tana fira da wani awaje, shine ita asiyar taki hakura cewa tayi ma medata zatayi "


Baba babba yace "subhanallah, kaje kabata hakuri, sannan kace nace karta medata abari nadawo daga nijar inason ganin faseelat din "


Abba yace "Tom hakan zaai "


Baba babba yakashe wayar batare da yayi maganar dalilin kiran nashi ba, 


Abba yana shiga gida ya samu ya kwaci faseelat, ai tanajin an dagata wuf da gudu tai waje ta shige dakinta tasaka Key, 


Abba ya zaunar da ummi saboda hawaye ma take yace "haba asiya in rai ya baci bekamata hankali ya gushe ba, kiyi hakuri dan Allah ta samu natsuwa musan yadda zaai "


Ummi tace "dole na zubda hawaye yarinyar nan shikenan tabata sunanta dana gidannan, kowa se yaji ankamata da wani "


Abba cikin hadiye nashi fushin yace "kiyi hakuri abinda Allah ya kaddara ba makawa se yafaru, ki cire maganar nan aranki karki ta shiga damuwa saboda ita alhaji yace abari ya dawo zesan me zaiyi"


Ummi shiru kawai tayi amma batun karta damu be ma tasoba saboda dole ne ta damu ita tasan kowacece faseelat mugun tsoron zaman ta haka takeyi. 


Ya samu ya rarrasheta ta fito tai daki don tayi salla, 



Faseelat na shiga daki ta haye gado tai ta rusar kuka ita kadai, se yanzu ne takejin ciwon abinda tayi dama bata biyewa son zuciyarta ba, har tagaji ta kwanta tana meda numfashi bacci ya dauketa, 



Kusan karfe 8:15pm wayarta tafara vibrate ta sa hannu ta jawo ta daga brezia dan duk abinda ake bata yarda Iphone8s dinta tabar jikinta ba, 


tana dubawa taga ansa handsome, bata dauka ba ta ajiye ta, 


Be hakura ba yakara kira dan wannan ganin da yamata yakara afka shi cikin sonta da shaawarta be taba soyayya ba,shiyasa yakejin faseelat different aranshi .



Wannan Karon ma bata dauka ba se gabanshi ya fadi he is scared tunda yake daita be taba kiranta fiyeda biyu ba nan hankslinshi ya dan tashi ,


Itama kamar ta dauka takeji sede tsoro ne fal aranta ga muryarta data dishe saboda ihun da tasha amma jinkiran take kamar me, 


After 3 mnt yakasa hakura ya kira ,kiss dinnan de datace se awaya yake so tamishi saboda yanzu yafi jindadi idan faseelat ce ta tadamishi da desire dinshi fiyeda yadda yakeji da aisha,


Wannan Karon takasa hakura ta dauka tai shiru, jin andauka yayi murmushi yace "cutie yau se anjamin aji sannan zaa dau kirana? "




Tai shiru batace komi ba yayi murmushi,"ko sena roka zaamin magana? "


tai shiru batace komi ba yace "any way kimin kiss da kikamin alkawari saboda har kagara nayi dare yayi, u know what? Ina matukar jindadi idan muna tare, anya cutie zan'iya hakurin one month batare da kinzama tawa ba "


Faseelat tafashe da kuka jin abinda yace tana tsoron ma kar yace baya sonta inyaji ita zawara ce, 


Da yana jingine da resting chair ne a harabar gidanshi besan lokacin da ya mike tsaye ba, 


Cikin jin ciwon kukanta a zuciya yace "cutie why are you crying did I said something wrong? "


Ta cigaba da kuka, hankalinshi ya matukar tashi jin yadda muryarta ta zama donshi yasan muryar cutie dinshi sosai inba wahala ba ba yadda zaai takoma haka, ya dafe kai tare da fadin "oh my God, for God sake bazaki fadamin mike damunki ba? Kinaso kiga nima inayi ne ?kifadamin me yafaru ko hankalina ze kwanta"


Taki magana sede ta rage volume din kukan yace "cutie it's me fa ur heartbeat kimin magana "


Maganar da yayi takara tado mata kukan tai sauri ta kashe kiran ta cigaba da kuka, she's so scared ranar da zesan ta taba aure, don he's her life bazata iya rayuwa babu shi ba, 


Yana jin takashe kiran yayi tsaye yanabin screen din wayar da kallo, yana tambayar kanshi meke faruwa daita ne ko someone in there family ne ya mutu abun da mamaki sosai dazun yaganta normal yanzu kuma tana kuka, ya koma ya zauna besake kiranta ba saboda kukan it torching him ,yanata sake sake har kusan 15 minutes sannan ya shiga cikin gida  ,



Faseelat tasha kuka tagaji tai shiru Allah ya temaketa she's offf bata salla, amma wani mugun fitsari takeji don mararta cike take taff, amma tsoro yahanata fita, 


Koda yan mazan gidan suka dawo ba wanda ya bukaci abinci suka shige suka kwanta kowa jikinshi sanyaye don suma sunyi mamakin abinda yayarsu tayi, 


Karfe 9 35 tai shahada tabude dakin tafita dasauri tayo fitsarin ta dawo takara garkame kofa, su ummi na dakin abba tanajin fitowarta amma ta kyaleta saboda abba da yayi ta mata nasiha, 



Duk yadda taso bacci kasawa tayi hakan yasa ta bude Data daga cikin messages din da suka shigo harda na aisha, ta shiga, tana karantawa "the jawara ya kk..... Lol mundawo fa yau dinnan baki missing dina ba kenan shiyasa koki neme ni, alright mundawo se Kinzo ganin diyarki "


Faseelat ta yatsina fuska, saboda ba mood din dariya take ba, ta tura mata "welcome back anty I will surely coming anytime great meera for me"




Suddenly se message din fahad ya shigo tayi mamaki mi yahanashi bacci har yanzu tasan de kamar yanzu Yana wurin matarshi tabude tafara karantawa "nakasa bacci baby tunaninki ya addabi ruhina naji tsoro jin muryarki a dazun, zakiiya fadamin matsalarki? I thought nidake yanzu bawani boye boye, don mun amince da juna, we have to share sorrow and happiness together, plss what is wrong with you? "


Ta tabe baki hawaye na zubo mata aranta tana jin duk duniyar tama ta zafi ,


Yanzu kunyar kowa takeji especially her parents, 


Tafara tunani tunyanzu is better ta fadawa fahad ko mikenan in ya rabu daita shikenan hakan yafi saboda kullum kara sonshi take ,


Ta dade tana kallon wayar sannan ta tura mishi "I'm scared I don't want to lose  u, I know you can leave me if I told you my problems"


Akagare yake yana ganin amsar ta yace "don't think like that please I will not going to do that to you, faseelat kina ganin kanki kadan awajena, wlh u have big space in my heart honestly speaking I don't think I can let u go duk wuya just tell me I'm ur lover "


Tace "hmmmm "tana tabe baki zuciyarta ta bata shawara tafada mishi kawai is better ya rabu daita yanzu ko bakin ciki yakasheta ta huta "



Ta tura mishi "I'm  widow ,will you marry me like that? "


Ta tura mishi yana gani ya ji kanshi na mashi nauyi yana zaune ne kan bed su Aisha kau tuni tayi barci, ya bude ido yakara karanta wa yana tunanin ko shi ke be gani sosai ba, 


Still abu daya yake karantawa wata juwa juwwa yaji tana daukarshi ya rumtse ido ya bude ya girgiza kai ko yasamu ya dawo dede, wani irin kishi ne ya taso mishi, yanzu wani namiji yasan komi na faseelat dinshi, yayi squeezing dinta yanda yaso a lokacin da yaga dama, wani yaji yaji ya rika taso mai a makoshi, ya dafe wuyanshi. 


Faseelat taji shiru shiru ba reply nan zuciyarta tafara zafi, dama tasani ze rabu daita ne da yagano hakan, ta fashe da kuka tana fadin"karkamin haka fahad "


Da kyar ya samu ya tura mata "why did you do this to me?"


Yaji baze iya typing dinba ya kashe wayar gaba daya ya mike tsaye yafara sintiri cikin dakin, yana ta tunanin yaudararshi da faseelat tayi, duk yadda yake mabukaci duk dare se ankashe arna wannan daren kam ba shaawa ba labarinta, dukda be barci ba gabadaya daren, 


Tunaninshi kwata kwata ya kulle yanada kishi sosai bejin zeiya aurar kingin wani, kuma bangare daya na zuciyarshi bejin zeiya rabuwa da faseelat, 


Itama batai bacci ba ganin sakonshi ma yakara tabbatar mata da tunaninta ta tashi taita rusa kuka harse da abba yazo bakin window dinta yamata magana akan tai hakuri ta kwanta hakanan. 


Tunda asuba aisha ta farka tana mamakin rashin ganin fahad kwance da dalilin rashin yin sex din donko tana off se ya samarwa kanshi natsuwa yake barci,


Ta tashi ta sauka daga gadon dasauri tayo waje daga saman bene ta hangoshi zaune ta sauko ta nufi wurinshi.



Post a Comment

0 Comments