TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

RAGON MIJI PAGE 39

 



3⃣9⃣







Dasauri taisa gunshi ta tallaboshi tana kuka "khalil dan Allah katashi karka tafi kabarni "


Rakiya hankali tashe tai waje ta taro me napep da temakonsu akasashi ciki suka tafi asibity, rakiya naganin Sun wuce tai gida hankali tashe don ita aganinta temakon hjya tayi, 


Sun isa hospital aka wuce dashi emergency room ana bashi temakon gaggawa, 


Hjya na waje nata kuka ta kira kanin babanshi tafada mishi nan take ya taho hospital din, takira siyama tafada mata, kafin kace me sega siyama cikin asibitin hankali tashe tana ta kuka suka rungume juna da hjya sukai tayi, 



Lokacin da kanin mahaifinshi yazo shine yayi ta basu hakuri sannan suka dena kwarar bakin yin kuka amma basuiya tsayar da hawayen su ba, 


Acikin theater room ko khalil be farfadoba, jin zuciyarshi na harbawa dasauri alamun da ranshi sukai masa wasu allurori tareda yi mishi dinki a inda kan shi ya bugu sannnan aka fito dashi aka wuce dashi  bedrest, 


Tunda aka fito dashi hjya takara shiga tashin hankali domin kwance kawai yake ba mara barsa da gawa, 


Tsoro ya shigeta sosai ta tashi tai waje tai alwala ta dawo dakin tafara kawo nafilfili tana rokon Allah ya tashi kafadun danta. 




Da isha'i baba babba yazo gidan su faseelat gashi ga ummi ga abba aka kira faseelat, faseelat gabanta faduwa kawai yake tazo ta zauna, 


Baba babba yana harararta don duk amfada mishi abinda akai yace "faseelat abinda kika zabawa kanki kenan? Ki kaso aurenki ki dawo gida ko? Wai kece ke gayyato maza gidanki? "


Faseelat tana girgiza kai tace "dan Allah kuyi hakuri  wlh bazan sake ba "tana zubda hawaye. 


Baba babba yace "to ai shikenan tunda ya sake ki kuma yayi dede wannan hukuncin da ya miki, amma kisani ranar da ya dawo yace ya medaki ranar zaki koma kinajina? "

Ta daga kai tana share hawaye yace "tashi kibawa mutane wuri mutuniyar banza kawai "


Ta tashi dasauri tana tuntube tabar dakin tana isa dakinta tafasa kuka ta jawo wayar ta takara kiran fahad wayar nata ringing har ta tsinke be daukaba ,ta cigaba da kuka ita yanzu duk tashin hankalinta be wuce rabuwa da fahad ba. 



Wasa wasa har seda akai 2 days sannan khalil ya farka idanunshi suka sauka kan hjya dake zaune tana ta lazimi, tana ganin ya Bude ido ta matso tafara hawaye ya juyar da kai don ba yason ko ganinta ta riko mishi hannu cikin nadama take cewa "khalil dan Allah kamin hakuri ka yafemin na zalunceka, wlh rakiya ce ta cuceni dan Allah kayi hakuri nayi hakanne don kada na rasa ka "


Yana ji tana magana be juyo ba, tunani kawai yake wace irin uwa ce Allah yabasu da ita da kanta zata cutar dasu,


Hjy ganin ya kyaleta tasaka kuka harda shesheka, jin sheshshekarta ya juyo da kanshi Yana kallonta se lokacin hawaye suka fara zubomishi, daace wani ya masa wannan abun baze ji ciwo ba akan yadda yakeji yanzu, 


Kukan hjya bakaramin tabashi yake ba, baze iya u

jure ganin wadda ta dauki cikin shi tasha wahalar haihuwarshi tana kuka ba, 


Yana rumtse ido ya damke hannuta hjya ta bude ido da sukai ja tana kallonshi, 


Cikin dauriya yace "kidena kuka hjya ni nayafemiki duk abinda kikamin, da wanda nasani da wanda bansaniba ki share hawayenki, komi kikamin bazan mance matsayinki awuri na ba, kuma bazan iya biyanki abunda kikamin, na dauki wannan abun da yafaru a matsayin kaddara ne, haka Allah yariga ya tsaro kuma lokacin mutuwar alhaji ne yayi shiyasa ya rasu, ina rokonki ki kwantar da hankalinki kidena Damuwa zan warke da yardar Allah adduar ki kawai nake bukata "


Hjya ta dago hannunshi ta dora a fuska tana kara fasa kuka na nadama, ita ta riga ta sani Allah be bata yaya masu halinta ba shiyasa take kara godiya ga Allah akodayaushe, 


Khalil yanajin dumin hawayenta suna bin hannunshi yace "plsss hjya ki dena zubar da hawaye yanamin ciwo a raina"


hjya tai shiru tana share hawaye kanta kasa, khalil kallonta kawai yake, su siyama suka shigo room din, yana ganinta ya dan Saki murmushi dukda azabar ciwon da yakeji, siyama ta matsa tana mashi ya jiki, 



Sati biyu khalil yayi asibity sannan aka sallamoshi, duk yabi ya rame tunani barkatai sun hanashi sukuni, shi da kanshi yake rokon Allah duk salla akan ya cire mishi son faseelat saboda samarwa hjya kwanciyar hankali, amma da ba haka ba da tuni ya meda princess dinshi dakinta, gabadaya yanzu gidan hjya ya dawo kwata kwata besan ganin ko tunanin abinda ze tuno mishi da faseelat, 



Shiru shiru hjya bata kira ummi ba ,don ummi nata tunanin zasu kira amma shiru ganin har anyi 1 month basu neme suba akaje aka kwaso kayan faseelat aka siyar, ummi nata tunanin cewa khalil zargin faseelat yake shiyasa be medata dakintaba sam bata bawa hjya laifi ba, 



faseelat se rama take tana ganin rabuwa da fahad abu ne me sauki ashe ba sauki abun, gashi dukda ya shareta abinda yake nuni da bayasonta amma takasa hakura kullum seta kira amma baya dauka ta tura message a what's up yana viewing ammaba reply sosai hankalinta ke tashi, kwata kwata bata maganar khalil ta fahad kawai take, 


Hjya da kanta take ansowa khalil ilajis sihir a Islamic chemist ma banbanta ,


Ganin khalil ya samu lpya har yafara zuwa school ,taga be kamata yayi ta zama haka ba dan har yanzu wani lokaci se ya zauna yayi shiru yayi ta tunani, takira shi tai masa maganar aure yace "hjya ki samo duk wacce tai miki ni kuma zan aure ta, amma dan Allah hjya karki nemo wadda zakizo kina kinta, nafison wacce ranki ya kwanta daita farin cikin ki shi nakeso banaso a memeta abunda yafaru"


Hjya tace "Nagode khalil Allah yamaka albarka ya baka abinda kakeso duniya da lahira "


Yace "amin"ya tashi ya fita, kawai ya amince ne don taji dadi ya tabbatar wa kanshi hjyarsu nasan shi saboda yadda ta rude da bashi lpya kadai ze masa bayani,sede bayajin ze kara son wata kamar  yadda yaso faseelat, hakanan hjya ke ganin kamar kyan faseelat ne yafiso, batasan cewa faseelat na da wasu abubuwa ba da ba kowace Mace Allah yayi ma wannan bewar ba, 


Hjya ta gama shawararta zataje batsari nemomishi auren jamila, diyar kanwar mijin siyama so daya ta taba ganin yarinyar kuma taga tana da kyau don fara ce sal ga ruman cinta tasha, 



Lokacin da tajewa maman jamila da maganar ba tai musu ba, tunda tasan ko su waye su,


Tun kafin khalil yaje ganinta aka kai komi na aure akasa rana nanda wata daya duk cikin sati daya akai wannan hidimar, 


Seda hjya ta matsawa khalil sannan yaje wurin jamila, yes tanada kyau amma daga ganinta yarinya ce dan shekararta 17 amma tana da girman jiki kana iya cewa takai 19 jss kawai tayi, jamila na da shegen wayon tsiya sannan akwaita da kwadayin balai don duk yadda zatayi taci nama setayi rumawa kenan😜bata iya girki ba tana de koyo ne sannan batai wani ilimin addini ba, hakanan suka gaisa da khalil ya masu sha tara ta arziki ya wuce gida. 


Itako jamila khalil ya mata ita bata wani damu da bakinshi ko tsayin shi ba itade ta samu wurin da zata huta, kuma dama burinta tai aure cikin birni gashi ta samu, 


Khalil be wani matsawa kanshi ba akan zarya zuwa wurinta ba, hjya ma da kanta ta saiwa jamila waya da tarkace akabawa siyama takai mata, kafin khalil yayi wa jamila kira daya ta yi mishi biyar, 


a rana se ta kirashi so ukku, Ahankali yadan fara sakarmata fuska saboda yar ban dariya ce dolenka intai wani abun kayi dariya ganin tana yawan sa kati ta kirashi seya fara tura mata kati a sati 500 kuma yana iya cewa duk akiranshi suke karewa, 


bewani rawar kai akan bikin amma hjya yadda takeyi kamar zeyi auren farko, khalil se gashi yafara tsumin kanshi 😂🙈 baya ga Islamic chemist har wani super market ya ke zuwa yana siyo kayan karin kuzari yasha wasu, wasu kuma yana ajiyewa se nangaba, dan seda gabaya da damuwa ta mishi yawa yake bawa amininshi labari shine yake bashi shawara yakara wayarmishi da kai anan yagano musabbabin raina shi da faseelat tayi shiyasa yanzu ya dage neman tsira da mutunci, 


Siyama har yau batasan illar da hjya taiwa khalil ba har yau hjya bata kuma kara sa rakiya ido ba, 



cikin sati biyu aka hada lefe aka kai akwati 10 reras aka kaiwa jamila, jamila nata murna ganin lefenta ta kira khalil tana mishi godiya "yaya Nagode sosai ni banma san taya zannuna maka jindadi na ba "


Yace "Allah? "


Tace "wlh kuwa se ganin lefe na ake zuwayi ana cewa nayi goshi "


Ya babbake da dariya  itama tana dariyar tace "kana sona sosai yaya Nagode "


Yace "to ai dole na so ki jamila tunda kema kina sona "


Tace "yaushe zaka zo inason ganinka "


Yace "a, a gimbiya na kira na ai dole nayi sauri nazo ina nan zuwa gobe "


Tana murna tace "se kazo in zakazo kamin tsarabar kaza me dawafi "


Yana dariya yace "angama gimbiya "


Sukai sallama shi ba shi ya hada lefenba su hjya sukai abinsu itada siyama, ita siyama tanata karason abun don dangin mijinta ne, 


Dole khalil ya so jamila yarinya ce kuma tana kula dashi abunda be samuba wurin faseelat ba gata da ban dariya ba ta jiran kauyancin shi yace yana sonta itake cewa tana sonshi, wani abu da yagane daita bata taba boye abinda takeso magana takeyi haka abinda be mata ba, 


Biki nata matsowa suleman ne yaketa kara bawa khalil shawarwari da nuna masa abinda mata su keso dan shima yayi aure, da kanshi ya budawa khalil su facebook su what's up insta twee dasauransu yana kara fadamashi amfaninsu saboda kan mutum nakara wayewa inyanayin su kuma zaka rika sanin abinda duniya ke ciki, 


Sosai khalil ya gano amfanin sharing problem da masoyi saboda zaka samu mafita da shawarwari har ta kai yanzu ba abunda suke boyewa juna shida Suleiman dama can rashin sakin jikin khalil ne yasa basa irin firar nan ,sosai khalil yagane kurakuran da yayi tayi a cikin zamansu da faseelat kuma baze karayinsu a wannan aurenba, yanzu bema da tym bare yayi tunanin faseelat suna busy hidimar biki, 



Ranar biki taro yayi taro murna kowa yake ana abubuwa a wadace cikin kwanciyar hankali ba kamar bikin shi da faseelat ba, 



bangaren amarya jamila dadi kawai takeji kokadan taki wani kuka ko ramar da akeyi batayi ba don Batasan miye  aurenba ma, anata fahimtar jindadi kawai ne aure ka girka abinda kakeso, kai abinda kakeso a gidanka, 


Karfe biyu aka daura auren khalil da jamila, ba laifi ancika kuma khalil ma yanata murna akai reception, 


Jamila aka zaunar daita ana mata nasiha da bin miji da masa biyayya da yin duk wani abu da ze masa dadi dason danginshi da girmama mahaifanshi, da bashi hakkinshi akowne lokaci yaso, 


se lokacin jamila tafara kuka da akazo daukar amarya dakyar aka bambareta daga jikin mamanta, aka tafi daita dakin mijinta katsina, 



Karfe 5 ankaita 6 dede aka medo yan rakiya gida, aka baro amarya jamila dakinta. 



Tunda taga gidanta da jeren dakinta tsit tai shiru, suna tafiya akabar yan cikin katsina suma karfe 7 :30 suka tafi bayan angyara mata gidanta ,suna barin gidan tafito tana zagayawa tana jindadi duk gidanta ne ita kadai, tuni ta manta da waazi murna kawai take, 



Karfe 8:30 Suleiman ya rako khalil gidan amarya ta sanyo hijab tafito falo, Suleiman yafara musu nasiha da cewa...... "





*first knight a next page 😂maybe ango khalil ya samu zuwa duniyar bakwai🙈*




*Kusani inasonku zanyi iya kokarina don faranta maku, fan's adduar ku kawai nake bukata Allah ya cikamin burina*




Post a Comment

0 Comments