TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

RAGON MIJI PAGE 63

 6⃣3⃣





Dedicated to my fan's 





Faseelat na shiga ciki tai zaman dirshan a kasan tyles ta rufe fuska da tafin hannuwa ta saki kuka, ba jimawa ya shigo fuskarshi tamau ya ganta zaune kasa rai bace yace "kee me kike nufi ne kitashi ki wuce mutafi"


Faseelat ta sauke hannuwa fuska jagab da hawaye ta Kalle shi tace "ba inda zanje kuyi tafiyarku"



Yace "are you crying? Kukan me kike? "


Murya na sarkewa tace "ba dole nai kuka ba, hero duk yadda zaka batamin rai sekayi miye laifina da har zakace wai kullum anty ce zata rika zama agaban motarka? Ni I don't care da zaman motar   daga yau bazan kara shiga motar ba  shikenan ko "


Yayi tsaye yana kallonta zuciyar shi na ciwo wai meyasa bazata gane ba?jikinta yana kyau da duk dressing shi kuma bayason wani ya ganta yayi shaawa, 


Ta tashi zata haye sama jiki sanyaye ya riko hannunta batare da ta waiwayo ba ya kalleta yace "banason bacin ranki, kisani farin cikinki shine nawa banyi haka don ranki ya baci ba, banaso ne kowa yana ganinki I love you very much ina tsananin kishinki ne honey don Allah kidena sa wani abu a ranki "


Faseelat ta juyo ta kalleshi idanuwanshi jawur yace "kiyi hakuri mutafi mommy wants to see you, she's the one that ask me to take you there "


Yajawota jikinshi yasa handkerchief dinshi dake fidda sassanyar kamshinshi ya fara share mata hawaye yana kallon fuskarta yake cewa "kiyi hakuri ki zauna bayan kinji zansa ayo miki hijabs daga yau shikenan, amin hakuri kar zuciya ta tai ciwo kinji gimbiya? "


Ta daga ido ta harareshi ta danyi dariya yace "that's my sweet wife, mutafi to kije ki gano mommy ta matsu ta ganki "


yajata suka fara tafiya tana jikinshi faseelat tuni tafara tunani tana matukar mamakin yadda fahad keson mommy she don't think umma zata taba samun irinshi koda Sun dedeta ,


Fahad ya mintsili bayanta ta daga kai ta kalleshi yana dariya yace "I'm happy da kukan ki saboda ya temakamin wurin bata kwalliyar da kikai "


Faseelat tai dariya tace "bazan sake yi ba tunda bakaso "


Sunata murmushi a makale sukazo zasu shiga mota Aisha data hangosu haka tace "ji bassu wawaye kawai "


Yazo yabude wa Aisha gaba ya kalleta yace "Aisha come to the front seat "


Ta tashi tana ya mutsa fuska ta koma faseelat ta zauna baya amira ta tashi takoma bayan ya shiga yaja suka tafi malali quarters, 


Suna shiga cikin gidan Aisha tai saman benen, faseelat ta zauna kan kujera ta dan Kalli yanayin gidan, ramlat dake zaune palo ta tashi tai room dinsu tana tabe baki ganin yadda fahad da faseelat suka zauna a kujera daya, amira ma bin bayan Aisha tayi tana kwalawa big mommy kira, 


Acan ciki Aisha na shiga dakin mommy, mommy ta tashi zaune tace "aa har kunzo kenan "


Aisha tace "eh gashi can ya taho da matar so wai ta gaidaki "


Mommy tai dariya tace "ni nace yakawota ai, ai diyata ce yakamata nadamu daita,abinda nakeso yagane keda ita daya ne guna "


Aisha tai dariya tace "mommy bakida kirki wlh ni zaki hada da waccan banzar I hate her well the way I hate my death "


Mommy tace "ihmmm bari nafita ni harma kyauta zanmata don nakara samun shiga "ta tashi tsaye 


Aisha ta fashe da dariya har da rike ciki tace "wlh ina mugun sonki mommy kin iya kissa da tuggu "


Mommy tace "abinda ake koyamiki kenan kin kasa fahimta daace kina nuna kina sonta ina tabbatar miki da sekinfi haka agunshi amma kinki"


Aisha ta tabe baki mommy tafita, sam Aisha bata iya acting,betrying ba in tanason abu to tana sonshi in taki abu kuma ko afili zata nuna, 


Mommy tana taka step tana faraa gab zata sauko tace" maraba da diyata "


faseelat ta kara masgwadawa nesa da fahad ta sunkuyar da kai ,


Har mommy tazo ta zauna faseelat tace "mommy inawuni "


Mommy fuska sake tace "lpy lau diyata ya bakunta? "


Faseelat tai shiru mommy tai murmushi ta kalli fahad daketa kallon faseelat kamar ze medata ciki tace "fahad kabarsu nan zuwa dare seku tafi bayan kunyi dinner don nakara gaisawa da ita "


Yayi murmushi yace "tom mommy bari natafi akwai Wanda ke nema na "ya tashi ya fita, 


Mommy tabi bayanshi da kallo ta yatsina fuska Batasan cewa faseelat na kallonta ta cikin gyale ba ,acikin ran faseelat tace "Allah sarki mijina ka dauku da soyayyar wadda bata sonka Allah ya medo hankalinka awurin daya dace, umma ce kemaka son gaskiya ba mommy ba datake acting "


Mommy ta kira jummala jummala tazo dasauri mommy tace "ki kawomata pepper chicken din da drinks"


Jummala ta tashi mommy tadan zauna tana latsar waya, bayan jummala ta kawomata ta tashi tahaye sama ta samu Aisha suka hada kawuna suna tattauna wa ,


Faseelat ta dau exotic ta tsiyaya tasha ta fiddo waya tana latsa, 


Can zuwa sega ramlat tafito tazo ta zauna tana bankawa faseelat harara, so daya faseelat ta dago ta kalleta ta meda hankali gun wayarta, 


Ramlat taja dogon tsoki ta tashi ta haye sama, faseelat ta dago tabi bayanta da kallo ta girgiza kai ta cigaba da abinda take, 



faseelat nanan zaune anan tayi salloli, bayan ishai fahad Ya dawo lokacin kuma duk su mommy sundawo Palo suna kallo sunata dariyar daso da suke kallo acikin wani film tana cewa "ke ni namiji beisa yasani ciwon kai ba yo miye namijin?ban taba bawa namiji amana ba kinganni nan aure na 5 dukkansu dan ubansu ni na sake su da kaina basu suka sakeni ba yo MI akai akai namiji "


itakam faseelat abun haushi ya bata ,


yana kallon fuskar faseelat yazo Ya zauna faseelat ta sakar mai murmushi ya meda mata ,


Sukayi dinner sannan suka tashi zasu koma gida, mommy ta dauko turare me tsada dake a leda tabawa faseelat, faseelat ta amsa tai godiya suka tafi, sosai fahad yaji dadin kyautar da mommy taimata da kuma yadda ta tarbeta, 


Suna shiga gida kowa Ya nufi dakinshi amira na like da faseelat ta mata wanka ta kwantar daita sannan ta shiga toilet tayi nata ta fito ta shafa humra dasu roll on ta saka sleeping dress dinta ta haye gado, 


Tana charting fahad Ya shigo da katuwar leda a hannu ta tashi zaune tana gyara zaman rigarta, 


Yazo Ya zauna gefen gadon idonshi akan breast dinta da rabinsu ke waje, yace "honey ga hijabs din ki bada wadancan plsss "


Tace "karkadamu nima nafi jindadin hijab din akan wadannan "


Ya tashi Ya haye gadon Ya dora hannu saman breast dinta dake waje yafara shafawa yana lumshe ido, 


faseelat tai murmushi ta kalleshi yadda idanunshi duk suka kankance ta janye mai hannu ya kuma medawa, 


Faseelat tace "katashi ka tafi plsss banason haka "


Ya ware ido akanta yace "me ke bakiso? dan Allah kibari nadan yi wasa da babies dina wlh bana gajiya dasu bayan hq naki dake zoy ba abinda nafiso se su plsss let me suck them before leaving" Ya tura hannu cikin rigar yafara matsasu 


faseelat ta lumshe ido ta bude tana matukar jindadin yadda fahad ke juyata Ya kware wurin rikita mata tunani ta daure ta zare mishi hannu ta kalleshi jiki mace tace "ni taka ce hero komai nawa is urs kuma zakaiya samun su kowane lokaci dan kullum cikin shiri nake amma ba yanzu ba, saboda zaka shiga hakkin wata ni kuma banason karika kauce hanya don inason mugudu tare mu tsira tare kabari gobe ne fa"


Ya lumshe ido yace "bazaki gane ba kwana dayan inajinshi kamar shekara "


Tai dariya tace "se hakuri, gobe inason natafi gida kasan jibi su ummi zasu tafi saudi shine nakeso inje  muyi bankwana"


Nan take fahad Ya bata fuska yace "se dare zan kaiki tunda bankwana ne zakije"


Faseelat ta saki baki tana kallonshi ta marairaice fuska tace "haba hero wurin ummi ne fa wlh I'm missing her "


Ya kara tamke fuska tuno yadda take shagwaba wa omer wai tayi missing nashi ya sauka daga gadon Ya zuba hannuwa a cikin aljihu yace "ko kuma kinyi missing yayanki ba "


Faseelat ta kalleshi cikin mamaki tace "yaya kuma to mi yakawo yaya acikin maganar nan "



Yace "karki rainamin wayo zakisa bansan kina waya dashi ba, ki zauna kita mashi shagwaba wai kinyi missing dinshi "


Faseelat tace "haba hero yaya fa uwarmu daya ubanmu daya be kamata kana kishi dashi ba, kuma aiba laifi bane dan nace nayi missing dinshi saboda he love me so much he's gentle and caring, mun shaku sosai shima nasan yana missing dina dan Allah kabari natafi da safe da marece sena dawo saboda mugaisa da yanuwana ina missing dinsu all "


Haushi maganarta tabashi yace "dan iyayenku daya shi ba namiji bane seki zauna kita shashanci gabanshi yayi ta kallonki yanajin dadi,nafada maki se dare zamu tafi "


Ya juya yabar mata dakin


Faseelat tabishi da kallo tace"bangane abinda mutuminnan ke nufi ba fa "


Da safe suna dining fuskar faseelat ahade shima tashi ahade ta gaidashi ya mata banza amira ta kalli fahad tace "hero anty nagaisheka "


Faseelat ta zaro ido tana gumtse dariya, fahad fuska ta mau yacewa amira "I don't heard Her well just eat ur food "


Aisha haushi Ya cikata ta kalli amira tace "kar nakara jin wannan sunan he's ur dad call him daddy kina jina? "ta zare mata ido 


Amira ta bata fuska tace "mommy ni inajin dadin sunan da anty ke kiran shine"


Aisha tazo zata tashi fahad Ya riketa tana hararar faseelat ta koma ta zauna, 


Faseelat ta tabe baki ta tashi tafara gyaran gidan dan tunda tazo gidan Aisha bata kara dora ko da mofa ba da sunan gyara sede faseelat tayi, 


tana gamawa tai wanka amira tazo suka fara bita ,


Shiru har azahar ba faseelat ba labarinta ummi tace bari nakira de naji ko lpya, ta dauki waya takira ta, 


Faseelat ta dauka tana magana Ahankali, 


Ummi tace "wai amarya bazaki zo mana bankwana ba inata dubar hanyar ki tundazu "


Faseelat tace "ummi Ya hana wai se dare "


Ummi tace "to ai ba matsala duk daya ne Allah yakaimu daren kiyi hakuri kinji "


Faseelat tace "to ummi "


Ummi takashe kiran, ba jimawa kiran umma ya shigo dan yanzu suna magana faseelat so biyu tana kiranta, 


Faseelat ta dauka tana faraa tace "umma ina wuni "


Umma tace "lpy lau diyata Ya kuke? "


Faseelat tace "lpy lau umma "


Umma tace "alhamdulillah, dama cewa nai bari nakira ki dan kina debemin kewar fahad, ga kannenki duk sunason su ganki "


Faseelat tace "Nagode umma nima inason nagansu "


Kanwar fahad ta ukku Mansura (lady😉) tai sauri ta karbe wayar daga hannun umma dama kanta a jikin umma yake itada 2 sisters nata sun zagaye umma don sosai sukeson danuwansu amma su dashi sede suga pic dinshi a media ,tace "anty muna sonki sosai yaushe zamu ganki?"


Faseelat tace "koda yaushe nima inasonku sosai kuma ina gayyatar ku gobe dafatan zaku zo "


Mansura tana farin ciki tace "zamu zo anty insha Allah "


Faseelat tace "to se kunzo ina gaida sauran sisters nawa"


Su Mansura suka fara surutu suna fadawa umma abinda tace faseelat tai dariya takashe kiran dan murna basuma san basu kashe kiran ba, 


Duk yinin fahad be leka dakin faseelat ba da Maghreb tai masu dinner takoma daki tai wanka, bata ko shafa mai ba bare powder tade shafa humrah ta saka riga da sket material lace orange color ,


Tana zuge zip fahad Ya shigo bata ko kalle shi ba, 


Yana shan kamshi yace mata "ki saka hijab mutafi na ajiye karfe tara zanzo daukarki "


Batare da tai mishi magana ba ta ida zuge zip din ta juya tabude wardrobe ta dauko hijab dinta, fahad yabi bayanta da kallo sket din Ya mata cif dammm ta saka hijab cikin jin haushi fahad yace "idan kinje karki cire hijab dinnan kuma karki amfani da hannun hijabin "


Hawaye suka cika mata ido ta kalleshi kamar zatai kuka tace "wace irin rayuwa ce wannan? Shikenan bazan kara sakin jiki a gidanmu ba dannayi aure? A cikin gidan na taso tun yarinta har girma na, yaya de kake magana kanshi har kashi ya wanke mun, kuma duk cikin gidan muharramai na ne ko kamutu ba aure tsakaninmu miye na damuwa kode kanason matsa ma rayuwata ne? "


Taja numfashi tace "to shikenan bazanje ba bazan kara zuwa koina ba tunda bakaso ko yaushe zan kasance mai maka biyayya "


Tafara zare hijab din jikinta, 


Fahad ya rike mata hannu murya sanyaye yace "kiyi hakuri da hali na faseelat wlh bansan koda kuda namiji ya tabaki, duk sonki ne yajawo haka kimin uzuri,"


Ya jawota jikinshi Ya gyara mata hijab yace "mutafi muyiwa su ummi bankwana kinji my honey"


Tai kwance jikinshi suka fito, amira tace tana zuwa suka tafi tare, 


Atare suka shiga shima Ya gaidasu ummi yabawa ummi 200k Ya tashi Ya fita, 


faseelat murna kawai take ta yaye hijab ta matsa wurin ummi, ummi ta kalleta taga duk ta rame sede tai haske dan gangariyar madarar da fahad ke zuba mata lol.


Ummi tace "ya gidannaku Ya kishiyarki? "


Faseelat tace "muna lpy ummi "


Ummi tace "senaga kamar kin rame "



Faseelat tace "hakanan ne kurum "


Ummi tace "Ya naga kamar baki baki a wuyanki da gefen hannunki? "


Faseelat tafara inda inda tace "konewa nayi ummi wlh Allah Ya temakeni daddyn  amira Ya siyomin wani cream nake shafawa shine Ya koma haka "



Ummi tace "to Allah yakyauta gaba ga wani tsimi nan na siyo miki kishashi yanzu ga wasu nanma a leda kitafi dasu kin kusa shanye wadancan ko? "


Faseelat tace "eh saura kadan ai ummi bani sanya"


ummi ta rike gemu tace "Allahu Akbar Allah abin godiya "

Faseelat ta rufe fuska, ummi ta mika mata tace "gasunan ki kara himma to "


Faseelat ta dauka ta shanye tsumin tass suka cigaba da fira bayan isha Ya omer Ya dawo murna kamar zata kasheta shima haka sukaita labari su ishak su abul su Mubarak kamar zasu cinyeta, 

Abba Ya dawo taje suka gaisa yanata sa mata albarka, 


Karfe tara fahad ya kira ta ta tashi tasa hijab ta sabi amira dake bacci ummi ta taho yi mata rakiya zuwa bakin kofa, 


Faseelat  suna isa kofar ta ta juyo ta kalli ummi tace "ummi zanyi missing naku Allah yasa ayi karbabba dan Allah ummi kimin addua Allah Ya amshi adduoina "


Ummi tace "insha Allah diyata Allah Ya kara baku zaman lpy"


Tace "amin Nagode ummi Allah yakiyaye"



Mubarak yazo Ya amshi amira suka fita, abayan mota Ya kwantar daita ya masu se da safe ya koma gida, 


Tunkan hanya faseelat tafara rikita fahad saboda tsumin da yafara aikinshi, 


Tana ta shash shafa shi tana Yi mai kiss yana driving, se lumshe ido yake dakyar suka isa gida shi Ya dauki amira ya kaita dakinta Ya koma suka cigaba da rikita juna, 


Da daddare faseelat kasa bacci tayi hakanan taji farin ciki Ya dabaibayeta na zuwan sisters nashi , har fahad yayi bacci Ya barta tana ta kallonshi tai masa kiss's ta tashi tayo wanka ta kabbara salla tana ta adduar Allah Ya gyara mata mijinta ya sulhunta tsakaninshi da yan uwanshi , 




Tun asuba bata zauna karatu ba tai sauri ta gyara gidan sannan tai masu simple breakfast, 


Ko sleeping dress bata cire ba ta zauna sukai breakfast fahad se kallonta yake yadda take ta murmushi ita kadai, Ya lumshe ido ya bude Ya saki ajiyar zuciya cikin ranshi yace "honey kaunar ki zata kasheni "


Shaf shaf ta samu ta karya ta wuce kitchen tafara aiki zatai wa umma meat pie da spring roll su Mansura su kai mata, 


Fahad na daki kasancewar weekend ne shiru bata shigoba har 12 na rana shi kuma yanason yayi ninkaya Ya tashi ya nufi kitchen, 


Kitchen din nata kamshi yayi tsaye yana kallonta tanata aiki dasauri, ta juyo ta kalleshi jin kamshin turaren shi, 


Ya harde hannuwa yace "wai yau shirin mi kike? "


tana aikin tace "wlh hero baki zanyi kuma they're special and dear to me "


Fahad yayi murmushi yace "lalle kinaji da bakinnan tow Allah yakawosu lpy but ni antakura ni "



Faseelat tace "haba ga anty nan just go to her tunda ni ina busy "


Yana mata kallon mamaki yace"keda kanki kike tura ni, yau ko dan kishi na bakiyi"


Faseelat tai dariya tace "bahaka bane hero dan kasamu natsuwa nace kaje wurinta amma ai ina kishin ka sosai "


Yace "ai kece natsuwa ta, any way natafi kar na hanaki aiki "


Tai murmushi ya juya Ya tafi wurin Aisha , 



Agidan umma su Mansura da safiyya da ummu salma shiri suke tayi sunata doki, 


Umma tace "kai yau faseelat se kanta yayi ciwo nasan "


Mansura tace "umma dan Allah kizo mutafi tare, daganan kiga yaya kuma nasan anty zataji dadi da zuwanki"


umma tace "ni tsoron ma ganinshi nake sede inason naga daughter eye to eye wlh inasonta yarinyar kirki ga daa gaskiya Allah yana son fahad da yabashi ita,bari nafadawa daddinku se na shirya mutafi "


Ta shiga tafada mishi  yace ba matsala don shima sosai yakeson su shirya da danta, 


Karfe 1 tagama komi har abinci ta masu ta wuce daki a gaggauce tai wanka tasaka gownt light purple atamfa tai simple makeup, 



Karfe 1:15 su umma suka fito umma na driving su kuma sunata labari suna jindadi, Mansura takira faseelat, faseelat na cikin shiryawa ta dauka, 


Mansura tace "anty gamu a hanya kinsan me? Harda umma saboda takagara taganki azahiri "


Faseelat tace "amazing I'm very happy se kunzo kuyi  sauri dan Allah "


Mansura tace "OK anty "


Ta juyo ta kallesu tana dariya tace "kunji fa anty tace ai sauri "


Karfe 1:30 suka isa kofar gidan sukai horn megadi Ya bude suka shiga ciki, 


Suka firfito sunata kallon gidan sukaje bakin kofa suka danna door bell, 


Da gudu faseelat taje ta bude, 


Ta gansu tsaye dukkansu sunyi kama da fahad more especially Mansura, tarika murmushi, 


Duk sunkare umma, 


faseelat tace "ina umma? "


Suka fashe da dariya suka bata wuri, faseelat ta fada jikin umma kamar sun dade tare tanajin matukar dadi itama umma dadi takeji ,


Su Mansura abun Ya birgesu yadda faseelat taiwa ummansu, 


faseelat tai breaking hug din tace "umma kushigo sannunku da zuwa "


suka shiga suka zazzauna faseelat ta zauna gefen umma tace "ina wuni umma Ya hanya "


umma tace "lpy lau Ya ta Nagode da karramamu da kikai"


Faseelat tace "umma kidena min godiya ai kamar uwa kike aguna "


Umma tai murmushi su Mansura se kallonta suke kamar su hadiye ta tashi ta kawo masu abunsha ta zuzzuba musu ta dawo ta zauna, 


Suka dauka suka sha, 


Sunata kallon gidan duk pics din su fahad da Aisha pic daya ne na faseelat, 


Kamar sundade tare suka matsa suka fara hotuna harda umma fuskarsu dauke da farin ciki, 


Suna haka fahad Ya fito zai fita har yayi wanka Ya na sanye da blue shirt white jeans, tundaga step yagane ko su waye bakin faseelat, Ya daure fuska Ya cigaba da saukowa yana kallonsu da mamaki a fuskarshi, 


Jin ana saukowa suka meda hankali gun step din, ganinshi duk suka sha ruwan jikinsu, 


Fahad yaida saukowa yana harararsu yaja tsoki yawuce ze fita, 


Umma ta mike tsaye tace "son Dan Allah kayi hakuri ka yafemin nida yanuwanka duk muna da bukatar ka "


Fahad yaja wani dogon tsoki, faseelat ta zaro ido jin yawa umma tsoki tai zumburr ta mike tsaye ta buda murya sosai tarika cewa "innalillahi wainna ilaihi rajiun,innalillahi wainna ilaihi rajiun"!!!


Fahad yayi sauri ya juyo saboda seda hanjinshi  ya juya saboda yadda take maganar zuciyarshi ta rika bugawa da karfi he is expecting something bad happened to her, Ya ganta tsaye se juya kai take tana hawaye tace "ina tausayin ka mijina saboda sanin idan ka mutu yanzu akwai azabar dake jiranka, hero ka dawo hayyacinka ,ka rika tuna lahira ba duniya kadai ba,umma ce wannan mahaifiyarka data dauki cikinka tasha wuyar nakudar ka ita kake wulakantawa  baka tsoron azabar Allah ne? Manzon Allah S. A. W yace 


عن ﺃﺑﻲ ﻫﺮﻳﺮﺓ ﻋﻦ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﷺ ﻗﺎﻝ: ‏« ﺭﻏﻢ ﺃﻧﻒ، ﺛﻢ ﺭﻏﻢ ﺃﻧﻒ، ﺛﻢ ﺭﻏﻢ ﺃﻧﻒ ﻣﻦ ﺃﺩﺭﻙ ﺃﺑﻮﻳﻪ ﻋﻨﺪ ﺍﻟﻜﺒﺮ ﺃﺣﺪُﻫﻤﺎ ﺃﻭ ﻛﻼﻫﻤﺎ ﻓﻠﻢ ﻳﺪﺧﻞ ﺍﻟﺠﻨﺔ ‏» . ﺭﻭﺍﻩ ﻣﺴﻠﻢ.


_An Kar6o daga Abi-Hurairah, Daga Annabi Yace: *“An  Turmusa Hancinsa a Wuta.  An Turmusa Hancinsa a Wuta. An Turmusa Hancinsa a Wuta. Wanda Duk Ya Riske Iyayensa da Girmansa, Dayansu Ko Duka Biyun; Sannan Be Shiga Aljannah ba”*.


Tana haki ta cigaba da cewa "se yaushe hankalinka ze dawo jikinka ne? umma na raye bata mutu ba shin bazaka nemi aljannarka ba se lokaci Ya kure maka sannan, kabude idonka sosai ka duba da kyau hawaye ne a fuskar umma kai baka da tausayi ne ga kannen ka nan duk suna kuka saboda yadda kake wulakanta masu uwa, amma duk da haka suna sonka kana gudunsu"


fahad yabisu da kallo duk sunata hawaye musamman umma da suketa zuba akan gyalenta, 


dole asamu tausayi ko kadanne a tsakanin uwa da da saboda bond dake tsakaninsu kuma haka Allah yasaka akowane kirjin Dan Adam so da tausayi tsakanin da da mahaifiya, fahad bema taba tsayawa sauraren umma ba be ko kallonta bare ta bashi tausayi yanzu da yaganta haka duk jikinshi yayi sanyi fuskar umma kasa tana ta faman share hawaye, 


Be aune ba yaji hawaye suna bin fuskarshi jikinshi yafara rawa, 


Faseelat tace " Dan Allah ka mance baya ka kama mahaifiyar ka ka jikanta kai mata duk kyautatawa ,tanason ka, tanason ta rika jin duminka ajikin ta, hero "


Kuka ne yazo mishi lips dinshi suka rika rawa hawaye nata zarya ,, ido rufe yatafi ya rungume umma ya saki kuka me kashe jiki, 


Umma ta rungume danta tanajin kamar andawo mata da wani sashin jikinta data rasa, 


su Mansura suna kuka suma suka tafi suka rugumesu suka cigaba da kuka, 


Saboda tsananin farin ciki kafafun faseelat suka gaza tsayuwar takoma ragab zaune saman kujera ta rufe fuska da hannuwa ta saki kuka me sauti,




Post a Comment

0 Comments