TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

RAGON MIJI PAGE 70

 7⃣0⃣







*Dedicated to my lover (Mrs Ibrahim)* *I love you badly😍,Allah yabawa teeman mu lpy*







Hankali tashe yayi zaman dirshan agabanta ya rungumota jikinshi wasu tsokoki yagani a gun ya saki kara yana kuka yake girgizata "faseelat dan Allah karkimun haka karki bari cikinnan ya fita "


Faseelat ko batasan halin da take ciki ba don hankalinta ya dade da barin gangar jikinta ya cigaba da kuka yana kara ya kuma rungumeta tsam a jikinshi difff numfashin faseelat ya dauke wanda shi besani ba, 



Aisha jin karar shi tayi yawa yasa ta dakata da chatting da take ta zaro ido waje tace "innalillahi karde ya kashemusu diya? "ta ajiye wayar ta fita daga dakin da gudu ta nufi dakin faseelat, tana zuwa ta murda handle ta tura kofar, abunda tagani seda hanjinta suka motsa jinin har yakusa kawo bakin kofar dakin ga faseelat zindir rungume a jikinshi yanata rusa kuka da ihu, 


Aisha ta zaro ido ta rufe baki da hannunta dake rawa tai tsaye takasa shiga ciki , 


Amira naganin Aisha ta gudu itama ta biyo bayanta tana tafiya ahankali saboda tsoron da takeji zuciyarta nata harbawa da karfin tsiya, 


Fahad yana ta kuka besan ma Aisha ta shigo ba yakasa temaka wa faseelat ya kaita asibity don baya cikin hayyacin shi, 


Bazato Aisha taga jini gabanta, se sannan ta kara zaro ido tai cikin dakin dasauri ganin jinin daketa zuba, ta bude wardrobe din faseelat ta zaro shirt da single zane ta iso wurin da suke jikinta nata rawa tace"yaya kasa mata kayanta ka kaita asibity jininta ze kare "


Fahad ya dago face duk hawaye yace "Aisha ta mutu ko? Na kasheta wayyo Allah na "


Aisha ta dafa shi tace "bata mutu ba yaya kasa mata kaya mutafi asibity jininta na zuba "ta mika mai kayan,hannunshi duk jini yana rawa ya amsa ya rikesu ya dago fuskar faseelat yaga ko numfashi batayi yakara rikicewa yana kiran sunanta da karfi, 


Aisha na tsaye hannunta yakasa barin bakinta duk ilahirin jikinta nata rawa kunsan jini beda kyan gani bare wannan da yayi yawa, 


Amira tana dari dari ta shiga dakin ganin abinda ke faruwa yasa ta firgita ta fiddo ido waje zuciyarta takara gudu wanda har kirjinta yake dagawa sama, 


Kamar ance ta kalli kasan ta, ta ga jini har yazo kafanta ,ta sulale wurin a sume, 


Aisha batasan da shigowar amira ba tana ta kallonsu ,kamar ance ta kalli kofa ta hango amira kwance cikin jini, 


Aisha tafasa kara da gudu ta isa wurin amira tana kuka ta tallabo ta ta rika tapping face dinta "amira! Amira !! "shiru amira bata amsa ba idanunta a rufe, 


Aisha na kuka ta dauketa batako kara waigen su fahad ba tai waje ko mayafi bata tsaya dauka ba se key data dauka akan kujera tafita ta shiga mota tabar gidan takama hanyar asibity, tana tuki tana kuka, 


Karar da Aisha tayi ne ya medo fahad tunaninshi sauri sauri yasawa faseelat riga ya dora mata zanen ya daukota ya fito yasata a mota gidan baya ya shiga ya figi motar, megadi bema ida bude gate dinba fahad ya fita da motar da speed up, 


tuki ne kawai yake amma hankalinshi baya tare dashi da temakon Allah suka isa alhayat prvt hospital, 


Ya bude motar yana kuka ya dauko faseelat dake lifeless tana ta bleeding ya shiga daita da gudu, 


nurses suka tarbeshi aka dora ta akan gado aka tukata zuwa emergency room, fahad ya zube  akan gwiwowinshi ya rufe fuska da tafukan hannaye yana kuka me ban tausayi da karya zuciya, 


Itama Aisha a asibitin takawo amira dan akwai specialist doctors a asibitin suna kokari sosai wurin gudanar da aikinsu, anbasu room ansawa amira ledar ruwa an kuma yi mata alluran bacci don ta samu hutu, Aisha na zaune gefenta tai tagumi lokaci to lokaci hawaye na zubarmata ,



ya omer yana da wani friends da suka hadu a facebook tun yana Niger da yadawo Nigeria sun zama friends sosai dan suna kawowa juna ziyara akai -akai tun yana Niger yake dora pics dinshi da faseelat a facebook page nashi, friend din seda ya taya omer yafada mishi matar aure ce sister dinshi ce , duk da haka friend din yayi saving din pic din  saboda sun burgeshi sosai ,shima yakan dora pics din kuma omer nagani sede ya mishi godiya, 



a asibitin yake aiki karamin likita ne  ya kanyi dressing small injures allurai har da  magani yakan bada, ya fito daga office dinsu yaga anwuce da faseelat akan bed gashi awarwatse fuska a kumbure ga jini duk ajikinta, inda besan ta sosai ba baze iya gane ta ba ,

Hankalin shi ya tashi ba tsayawa ya fiddo waya ya dannawa omer kira, 


Omer da yagama waya kenan da fadilarshi kiran abokinnasa bello ya shigo wayar, ya dauka da murmushi kan fuskarshi yace "likita manyan gari yau antuno dani kenan"


Doctor bello da becika hayaniya ba kamar de omer sede har ma yafi omer shiru shiru, muryarshi very cool yace "hold on, yanzunnan naga ankawo wata patient me kama da sisternka tana ta bleeding I don't know ko idona ne se naga kamar ita "


omer dake kwance ya tashi zaune kanshi na sarawa gabanshi na faduwa yace wa bello "waya kawota mace ko namiji? "


Bello yace "namiji wani dogo fari kyakkyawa yana da saje, shima de hankalinshi a tashe dan se kuka  yake"


omer ya bata fuska kamar ze kuka zuciyar shi a cunkushe yace "itace wlh dan Allah kadubamun room da zaakai ta gani nan zuwa yanzunnan"


difff yakashe kiran ya dafe kai yanajin kamar yayi kuka kamar an tsikareshi ya tashi  yayi dakin ummi dasauri da key dinshi a hannu ,


ummi na zaune da baki dake zuwa mata murna ya shigo dakin kallo daya ta mishi tagane ba lpy ba, muryarshi na rawa yace "ummi faseelat bata lpy yanzu haka suna asibity "


Ummi tace "subhanallahi miiyasameta ne? "


Idanunshi jawur yace "inaga tayi miscarriage ne "


matan dake dakin suka taya ummi sallallami ummi ta mike jikinta har rawa yake ta dauko hijab tace "mutafi asibitin naganta "


omer ya fita ummi na bayanshi Suka shiga mota suka kama hanyar hospital din, 



acikin emergency room anyiwa faseelat allurar tsayarda jini jinin ya tsaya akamata allurar bacci akasa mata ledar jini don sunada jini a blood bank, sannan aka fito daita, 


Fahad na durkushe yaci kuka har yagaji aka fito da faseelat ya tashi jikinshi na bari ya bi bayansu aka shigarda ita awani daki suka kwantar daita yayi tsaye yanata kallon fuskarta da ta kumbura gashi har yanzu bata dawo hayyacin ta ba ,


nurses nagama shiryata suka juya suka fita adakin fahad yakarasa bakin gadon yayi kneeling ya dora kai jikin gadon yana zubar da hawaye yana sambatu "nacuceki faseelat na rabaki da farin cikinki nayi sanadiyyar zubewar gudan jini na ihate myself kiyafemin plssss..."


Dukda saurin da omer keyi ummi gani takeyi kamar baa tafiya dandanan ta tambaya baaisa asibitin ba? 


Har suka isa sunata sauri su dukan burinsu suga halin da take ciki, 


omer yakira bello yazo ya samesu suka tafi ya nuna musu dakin yana jimami, be iya shiga dakin ba ya juya, 


su ummi suka tura dakin suka shiga, fahad na durkeshe suka shigo ya dago face duk hawaye ya kallesu seda gabanshi yafadi ganin su awurin adede wannan lokacin, 


Dasauri ummi takarasa kan bed din ta zauna gefe fahad ya matsa yabata wuri kanshi kasa, ganin halinda faseelat ke ciki ta fara salati jikinta nata rawa fuskar faseelat kamar ba tata ba ga jinin da yake jikin zanenta daba a sauya ba, ummi ta juyo ta kalli fahad tace "wai miyasameta ne accident tayi komi? "


Fahad yayi shiru kanshi kasa, ummi tace "I'm asking u meyafaru? "


Fahad yace "accident ne"Muryarshi a sarke 



ummi hannunta na rawa ta kaishi bisa kan faseelat ta shafoshi hawaye suka gangaro mata, 


omer tunda ya shigo yaga halin da take ciki ya rungume hannayenshi zuciyarshi awuya se cije lips yake dan ya riga yagama observing abinda yafaru, 



Suna haka for some minutes har lokacin fahad na zukunne se amira tafado mai arai yadda Aisha tafita daita batako numfashi ya dago kai dasauri, 


ya yunkura ya tashi jikinshi a mace yabar dakin ,ya nufi office din doctor okato, 


Omer yakara matsawa gaf da gadon ya kurawa fuskar faseelat ido besan lokacin da hawaye suka zubomishi ba, 


Ummi da take dafe da kanta tana hawaye ta waigo da kanta tace "omer kaina ya kulle wane irin accident ne wannan?jibarta duk yadda takoma lokaci daya kamar ba faseelat dita ba"


Omer jijiyoyin kanshi awaje yace "bawani accident ummi duka ne ya meda diyarki haka tun kafin bikinsu yafara marinta amma faseelat sonshi be bari taga laifinshi ba namata magana seta nunamin bazata iya barinshi ba, ki dubata sosai ga wasu tsoffin tabo nan ajikinta wanda nasan ba dasu tayi aure ba "yaida maganar dakyar kamar ze kuka, 



Ummi tajuya wurin faseelat tafara kallonta daga sama zuwa kasa duk ga sashin belt nan a wuyanta be ida bacewa ba, ga wasu jikin kafafunta, bata damu da omer dake tsayeba ta dage zanen jikin faseelat sama nanma duk sashin belt ne, hawaye suka gangarowa omer, 


ran ummi bace ta kalli omer  tace "zoka zaremata wannan jinin dake shiga jikinta ka dauketa mutafi wani asibitin inason diyata ban bashi ita don yakashemin ita ba "


Ta matsa ta bashi wuri omer ya zare jinin ya sargafe shi ya dauki faseelat suka fita daga dakin sunata sauri, 


sede bello yaga sunfito daita yabisu yana wa omer magana "ina zaku kaita kubarta plsss tana cikin hali "


Omer ko jinshi bayayi bello nabiye dasu saboda ganin bello securities basu Hana ba suna zaton an sauya musu asibity ne har bakin mota ummi ta bude mishi yasa faseelat itama tashiga ya kulle kofar, ya juyo wurin bello ya dafa kafadarshi yace "karkadamu zamu kaita better place thanks for your help "


ya wuceshi ya shiga motar yajata da gudu suka fita asibityn, 


bello ya dafe kai yace "what I put my self into?"




daga alhayat specialist hospital suka wuce turai yaraduwa daita, anan ma a emergency aka amsheta ba jimawa aka fara dibar jinin omer akasa mata, kuma ana bukatar leda biyu, 





fahad wurin likita ya shiga doctor yace mishi ya zauna yaki yace yanason sanin dakin da akai admitting amira, 


doctor ya fadamishi dakin, fahad yafita ya nufi dakin ,


Yana turawa Aisha da tai tagumi ta dago ta kalleshi shima ya kalleta.






Insha Allah angama samun tsaikon posting bazan ko numfasa ba se na kai karshe mahakurci mawadaci ,kungama hakuri insha Allah 😍matsala tazama labari.




Post a Comment

0 Comments