TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

RAGON MIJI PAGE 62

 6⃣2⃣






Amma yau kwana ukku kacal da aure fahad ya nakada mata duka, ga ciwon jiki ga zafin zuciya nan da nan masassara ta rufeta kuma kunsan dama farar fata basu cika kwari ba lol, 



Tunda ya fita driving yake amma hankalin shi baya kai kukan faseelat ne keta yawo a kunnuwanshi lokacin da yake jibgarta, zuciyarshi tace to kanme zata daki Aisha ai wannan hukuncin shine dede ita yaja tsoki , wata zuciyar tace be kamata ba tara su yakamata kai kaja masu kunne dukansu yakara jan tsoki, gabadaya zuciyarshi ta cunkushe zafi yakeji kamar me, ya gangara gefen titi yayi parking ya dukar da kai jikin sitiyari, maganganun faseelat da tafada mai jiya sune suka fado mai akaro na baadadi daga jiya zuwa yau da yayi tunanin umma, amma da ya tuno yadda tai watsi dashi, se yaja tsoki ,yayi tsoki fin 10 office yake son zuwa don akwai meeting da zasuyi kamar yakoma gida ya rarrashi gimbiya ya tada mota ya nufi office, 


A office ana meeting amma rabin hankalinshi na wurin faseelat dandanan kanshi yafara ciwo , 



Dakyar amira tai shiru ta Kalli Aisha tace "mommy u once told me in kasance me hakuri a rayuwa "


Aisha tace "eh, me hakuri baze taba wulakanta ba "



Amira tace "mommy to meyasa ku baku hakurin? "


Aisha tace "kiyi hakuri amira hakan will not happen again"


Taja ta suka shiga daki, 



Da kyar faseelat ta tashi ta shiga toilet anata kiraye kirayen salla, ta kunna shower using warm water don bata wanka da ruwan sanyi, ta tube tana ta bin inda ya fashe ajikinta tana tabawa tana kuka ta shiga cikin shower, wani mugun zafi tarika ji ta koina tai sauri ta fito zuciyarta na harbawa tana kuka ta dora tawul tai alwala tafito ta kabbara salla, 



A can su fahad sukai Maghreb da ishai sannan ya nufo gida gabanshi nata faduwa, 


Karfe 9 yashigo gida

A main falo ya samu Aisha har ta kwantar da amira tai bacci, ta taso wurinshi batare da ta ida kaiwa jikinshi ba tace "sannu da dawowa"kanta duke tasan halin kayanta sarai yanaiya dawowa kanta, 


Ya kalleta up and down yace "yawwa "ya haye sama, taki binshi ta zauna jiranshi dan mood dinshi kadai ya mata bayann sauran, 



Daki ya shiga ya watsa ruwa don ya dan samu relief sannan ya fito yasa jumper short nashi da singlet, yayi tsaye yana kallon kanshi a madubi wata irin kunya ce ta kamashi he want to see her to me zece mata ma? Be kwana daita ba kuma yazo yakara wa kanshi laifi, yayi ta maza ya tashi ya fita don ko zaman yayi hankalin shi ba kwanciya ze ba inbe ga halinda take ciki ba, 


Faseelat tunda tai ishai tai zaune kan mirror daga ita se towel ta sabule shi kasa tana ta kallon jikinta tana kuka koina yayi rudu rudu jajir wani wuri ya farfashe jikinta zau da masassara amma takasa kwanciya, 


Ji kawai tai Anturo kofar dakin, bata wai waya ba kuma bata rufe jikinta ba se kukan da takara volume dinshi ,ai gara yaga barnar da yayi. 


Fahad kamar wanda Kwai ya fashewa ya ida shigowa gabanshi na faduwa, 


Hango ta da yayi jikinta koina sashin belt yasa zuciyarshi tai mugun bugawa a 360 yaisa wurinta ya zukunna gabanta yana kallon jikinta koina belt har kan twins dinshi su ma duk sun samu ,ya dafe kai yana danasani, faseelat ko kallonshi batai ba, 


zafi zafi yaji yana hurowa daga jikinta ya dauki hannu ya dora a jikinta tai sauri ta kabe mai hannu tana kuka tace "karka kara tabani dama ba sona kake ba jiki na kawai kakeso, ka riga kagama dibar abinda kakeso shine zaka lalatamin fata ko? To Nagode da kalar wannan soyayyar hero, a tunani na bazaka taba wulakan ta niba, na nuna maka duk soyayyata amma abinda zaka sakamin dashi kenan? Yau only 3 days da aurenmu amma kamin dukan mutuwa "


Tai shiru tana tuna irin wulakanci da tai ta shukawa khalil amma ko tsinkuli be taba mata ba, 


fahad zuciyar shi karye idanunshi sunyi jajir ganin dukan da yamata kuma shi besan lokacin da yayi haka ba ya sha dukan Aisha amma be taba gani jikinta ya farfashe haka ba, 


Ya dafa cinyarta ta kabe mai hannu tanajin haushin shi saboda Aisha ya mareta ya daketa, fahad yace "kimin hakuri honey baa cikin hayyacina hakan ya faru ba, ki yafemin tundazu bana cikin natsuwa ta saboda abinda na miki amma ai kema baki kyauta ba meyasa zaki mareta seda fa kikamin alkawari bazakiyi zaman kishi daita ba amma kitashi ki mareta agaban diyarta haba "


Faseelat hawaye masu zafi sharrrr suka zubo mata tace "seta zageni na kyaleta? Tunda nazo gidannan take fadamin bakaken maganganu na shareta, ta kaini karshe ne har na mata haka meyasa kai baka tsaya Ka tambayi baasi ba adalci ne wannan? Kuma nifa matarka ce ba diyarka ba ba baiwarka ba da zaka dakeni manzon Allah,S.A.W ya hana dukan mata harma yake cewa shin dayanku bayajin kunya? Ya daki matarshi da rana kamar yadda yake dukan bawa, sannan da dare ya sadu daita amma yastahyi? See my body plsss yadda ka fatattaka min skin wlh bakamin adalci ba"


fahad ya dafe kanshi dake sarawa ya rumtse ido yace "kiyi hakuri honey wlh naji kunyar zuwa gareki seda na tattaro duk courage dina sanan, I hate myself saboda haka, duk lokacin da na taba lapiyarki se naji duk duniya tamin zafi I'm sorry "


Yazo ze rungumota ta kauce yayi fuskar tausayi yace "kiyi hakuri hakanan plsss kibari naduba jikin"


faseelat tace"kagama tabamin jikina tunda banda wata daraja a wurinka "


Yace "don't say that inasonki kuma kina da daraja sosai awurina, kuma ai jikinki is mine yanzu haka nafiki jin zafin da kikeji kibari na dubaki"


Ya dauketa cak ya dora saman bed yayi tsaye yana kallon yadda jikinta duk yaji ciwo faseelat ta kauda fuska tana hawaye, ya juya ya fita adakin, yaje dakinshi ya dauko pain killer tablet pcm da ibuprofen da abonike ya dawo dakinta, 


Tana nan kwance yadda ya barta ya bude fridge ya ciro cocktail ya hau gadon ya balli maganin ya tada ta zaune yace"kisha magani zaki ji sauki"


Faseelat ta kwaci maganin daga hannunshi ta shanye sannan cikin fada tace "niba wani sauki da zanji, yadda ka wulakanta ni gaban anty "


Yace "nace kiyi hakuri haba honey nine fa hero dinki"



Ta daga ido ta kalleshi ya marairaice fuska "kiyi hakuri plss pardon me "



Jin shiru be fito ba Aisha ta tashi ta haura sama ta duba baya dakinshi tai dakin faseelat ta tsaya bakin kofa ta kasa kunne, 


Ya jawota ya bude murfin abonike ya fara shafa mata, tarika fidda numfashi saboda zafi tana fadin "ashhh, uhmmmmm"


Cike da tausayi yake shafa mata yadda take ta mommotsawa tana magana yasa shi jin shaawa ta taso mishi yafara shafarta cikin salo , 


Daga shafawa faseelat taji ya sauya salon, 


Faseelat ta daga ido ta ballamai harara,cikin gajiyawa yace "I'm sorry please wai so nawa zan baki hakuri ne amma kinki kiyi nace kiyi hakuri insha Allah hannuna baze kara taba jikinki dasunan duka ba "


Faseelat tace "bazanyi hakurin ba dole ne senayi? katashi kabarmin daki kuma ko nankusa karkai tunanin zankara amincewa da kai"


Fahad ya tsura mata ido haryagaji da bata hakuri se yau yakara ganin hakurin da Aisha takeyi dashi can zuwa yace "faseelat ni kike kora daga dakinki ?saboda slice mistake kuma nabaki hakuri ai yakamata ki hakura, mijinki ne nifa dukda na zalunceki amma ai seki hakura Allah nason fa masu hakuri "


faseelat tamai wani kallo cikin tausayin umma tace "kai kana da hakurin ne ?ummanka tana ta zarya baka hakuri amma kaki hakura abu shekara da shekaru se yaushe ne zaka yafemata wai ko se tabar duniyar sannan ,this is what I want you to understand dole ne amaka laifi kuma dole kaima kayi ma wani seka yafemishi tunda kaima kanason a yafemaka"


Fahad yayi shiru yana tunani faseelat tace "think good,yesterday umma was crying asking for ur forgiveness tana tunanin kaine ka dauki wayar "


Fahad yayi shiru yace "OK I will think about it yanzu de ki yi hakuri kinji? "


Tace "bazanyi ba seka wa umma hakuri itama Ka yafemata just a single slap ne kaketa magana kanshi nifa u slapped me and beat me togather"


Fahad brain dinshi nakara tuno mishi abubuwan da umma ta mishi yace "ba marin ya fimin zafi ba bari na datayi nida mahaifina ta zabi wani shine yafimin ciwo "



Faseelat ta kama hannunshi tana kallonshi cikin kwantar da murya tace "it's ur fate, ko dayaushe musulmi yakamata ya rika daukar kaddara me kyau da Marar kyau kayi hakuri haka Allah ya kaddara ze faru "


"yanzu kayafema ta?"


Yayi shiru yana kallonta tace "idan ka yafemata ba karamar lada zaka samu ba, nima kuma na hakura duk da wannan likimon da kamin "ta Kalli jikinta 


Fahad ya yamutsa fuska seda ya hadiye miyau yace "na yafemata amma saboda ke "


Faseelat tai murmushi ta rungumeshi tace "Nagode hero can I ask a favor? Again "


ya daga mata ido tace "please karika sauraranta in ta kira ka, koda na minty biyu ne hakan zemin dadi "


Ya cusa fuska cikin gashinta yace "I didn't promise you about that "

Ya fara mata kisses, 


Aisha na bakin kofa labe tanajin su ,jikinta na rawa da tsananin kishi ta shiga dakinta tai dialing number mommy, 


Mommy ta dauka tace "lpy kira goman dare? "



Aisha tace "ba lpya ba mommy wai yarinyar can daga zuwanta shekaran jiyar nan har tafara communicating da umman yaya, yanzunnan naji tana rokon ya yafe ma ummar abinda ta mishi "


Cikin jin haushi mommy tace "to yayafematan ne? "


Aisha tace "yace ya yafematan har ma rokonshi tayi wai ya rika daukar wayarta inta kirashi yace beyi alkawari ba"


Mommy tai dariya tace"ko ya yafemata rukayya bazata fini ba agunshi saboda hannuna ya taso reno nane, don haka ki zuba musu ido kawai, ya gidan naku yake dazun ya shigo gaisheni a harmutse"


Aisha tace "hmmmm anty salma ce tazo daga fitar ta naje na amshi amira tarike ta wai itama diyarta ce muka fara cacar baki wlh mommy sede naji mari a fuska ta, ashe yana kallo aikuwa yazo ya dauketa da mari yace tabani hakuri taki shine ya jibgeta ya fita "



Mommy tace "good yayi dede amma Aisha kidena yarda ko cacar baki tana hada ku saboda raina ki zatayi kibar shiga harkarta kuma kinsan inde ta salma zakibi kema jibgar zakitasha kinsanta batada tunani da hakuri ko kadan ki kama kanki kar in kara jin hakan tafaru"


Aisha tace "naji mommy "


Mommy tace "to seda safe ki kula da kanki "ta kashe kiran, 



Aisha tai zaune tana tunanin baya, waifa faseelat ce yarinyar da take mata biyayya itace ta mareta, ta dafe kunci tana kara jin zafin marin, 




Faseelat ta rike fuskar fahad tace "hero yau ba dare na bane ur heartbeat is there waiting for you, katashi ka tafi tunda dama a kagauce kake "



Yayi murmushi yana tuno dazun dan taji kishi kawai yayi haka don ya rama abinda tayi jiya, besan yadda ze kwatanta mata ba cewar besan tana waya da maza ba kosu dangintan, 


Yaja hancin ta yace "korata ma kike ko? "


Ta girgiza kai tace "baniso anty taji badadi yadda kadade nan gwara katafi nasan tana can tana jiranka "


Yace "OK amma plsss kidena biyewa Aisha ki daure kirika bata girmanta ki mata biyayya kuma kiyi hakuri daita , banson tashin hankali a rayuwata "


Faseelat tace "insha Allah hakan baze kara faruwa ba, gobe zanma bata hakuri, a kullum bazan manta alherin da anty tamin ba yau ma bacin raine ya rufemin ido, itada yayarta suncimin mutunci bayannan anty tazo zata amshi amira awurina wai kada nabata mata tarbiyyar diya ni me bin maza da aure na, nafada mata kuskurene hakan da nayi amma me yahada haka da amira se cewa tai wai kila awurin ta gida na koya, naji zafi sosai da takirani mebin maza kuma tahada da mahaifiyata, wlh hero bantaba ko yin saurayi ba ,soyayyarka ce tarufemin ido har na manta auren dake kaina "



Fahad ya lumshe ido yanajin ciwon maganar da Aisha ta mata yace "naji kuma zan mata magana amma kiyi kokari kuhada kanku shine farin ciki na kuma kwanciyar hankali na"



Faseelat tace "insha Allah katashi katafi seda safe ,zanyi kewarka "


ya taba wuyanta "har yanzu da zafi jikinki fa "


Faseelat tace "ai ni na warke tunda ka yafewa umma, fatana de Allah ya dedeta tsakanin ku "



Yace "himmmmm diyar umma kenan "



Faseelat tai dariya ya mata good night kiss sannan yafita, 



Dakinshi ya wucewarshi yana shiga yaga Aisha zaune tayi tagumi, bece mata komi ba ya haye gado ya kwanta , 


Aisha ta tashi tsaye kanta kasa taje bakin gadon ta zauna murya sanyaye tace "Dan Allah kayi hakuri yaya akan abinda ya faru baze kara faruwa ba "


Ya tashi zaune ya kalleta yace "meyasa zaki zageta eyeee, saboda neman fitina? inkin lura faseelat tana sonki son da take miki nema harya shafi diyarki ,laifine dan tana koyawa amira karatu? inda batason ki da bazata jata jiki ba ko da muna tare, kisani raini ne kike jawowa kanki kina zubda wa kanki girma awurinta duk biyayyar da take miki tadena"


Cikin ran aisha tace shegiyar fada maka abinda yafaru tai kenan ,ta jinjina tace "kayi hakuri yaya bazan sake ba, kuskure ne nayi "


Yana kallonta yace " Allah yasa amma kinbata min rai sosai"


Ta matsa ta haye saman cinyarshi tarika shafa sumar kanshi tana kashe ido da gantsaro kirji tace "ayya I'm sorry my sweetheart Allah yahuci zuciyarka" tarika lasar lips, 


Yaja numfashi saboda yadda joystick dinsa ta motsa ya sa hannu yafara sabule mata riga, 




yana fita faseelat ta shiga toilet tayo alwalan bacci tazo ta kwanta da temakon maganin datasha bacci ya dauketa, 



ana kiran farko ta tashi jikinta duk yayi tsami sede fever din ta sauka, tana ya mutsa fuska ta shiga toilet ta gasa jikinta tafito ta balli maganin ta tsiyayi warm water a dispensa ta sha tazo ta kabbara sallar rakaatanil fajr, 


Shima fahad yanajin kiran sallan ya tashi da yake Sun kwana suna jindadi yasa dole yayi wanka yayi salla ya nufi masjid da counter dinshi a yatsa, 



faseelat nagama salla ta tafi dakin amira ta tada ta tai salla suka fara karatu, 


kasancewar Monday ce amira zataje school yasa Aisha bayan tayi salla ta shiga kitchen tafara hada breakfast, 


Yau dawuri fahad ze fita don basugama tattaunawa da bakinsu ba hakan yasa bayan yadawo masjid ya shiga dakin faseelat ganin suna karatu ya fito, yadanyi aiki a system ya tashi ya shiga wanka, 


Bayan sungama karatu faseelat ta wa amira wanka tana saka mata kaya tace"me mommy tafi dafa miki kitafi school dashi? "


Amira tace "tafi soyamin indomie da kwai , amma ba sosai ba sede natafi da cornflakes golden moon, cupcake,snacks da dudu milk, amma mommy tanayo dambun nama takawomin ina zuwa dashi sosai "


Faseelat tai dariya tace "ke mi kikafiso?"


Amira tace "inason tuwon shinkafa sosai mommy bata mana tuwo "


Faseelat ta zaro ido tana dariya tace "tuwo kuma princess? "


amira tace "eh anty friends dina suna zuwa da diffirent food a school,amma ni nafi shaawar tuwon "


Faseelat tana gyaramata maballi tace "yau ko zaki ci tuwo "


Turo dakin da akayi ne yasa suka kalli kofar Aisha ce tai tsaye tana kallonsu zuwa tai ta shirya amira ta samesu haka , 


Faseelat ta sadda kai tace "anty ina kwana"


Aisha tace "lpya "ta shigo dakin ta shafi kan amira tace "tunda kinshirya muje kiyi break daddy ya saukeki don shima fita zeyi "


Taja hannunta suka fita akabar faseelat a zukunne, bayan Sun fita faseelat ta girgiza kai ta tashi ta shiga daki don kimtsawa, 


Bayan tafito wanka tai makeup tana saka riga fahad ya shigo dakin fuskarta nata sheki , 


Faseelat ta sakar mishi murmushi shima da murmushi a fuskarshi yazo ya rungumeta ta baya tsamm, 


Tace "washhh" saboda ciwon ta da ya fama,, 

Ya saketa ya Kalli jikin nata da haryanzu yake jawur ya dafe goshi, 


Faseelat tace"ina kwana? "


Yayi shiru cikin jin tausayi yace "ya jikinmu?"


Faseelat ta kalleshi tace"lpya ta lau hero inafatan ka samu sallar asuba "


Yace, "nasamu ai naji dadin yin sallar a cikin mutane, shiyasa nayi setting alarm na tashi "


Tace "shiyasa nake sonka sosai "


Ta ida jan doguwar rigar kasa, 


Fahad yayi karamin murmushi yace "muje muyi breakfast ko? "


Faseelat tace "inazuwa zansameka kasan "

Ya kalleta ya juya, ta sauke ajiyar zuciya tariga tasan idan suka fita tare basu kyauta ba, 


Seda sukayi nisada cin abinci tafito tazo ta zauna tai sarving kanta pepper meat tafara ci, 


Tunda ta zauna hankalin fahad ya koma gunta ta burgeshi sosai yadda batai zuciya da amira ba kuma ta hakura dukda seda yasha fama sannan , se kallon yadda take taunar naman bakinta cikin kwanciyar hankali yake, ya gangaro da kallonshi a wuyanta zuwa saman rigarta da breast suka turo sama ya lashi lips dinshi, 


Aisha ta kalleshi ta kalli inda yake kallo cikin haushi tace "yaya zakuyi lati fa it's to 8 "


yaja numfashi ya kalli amira yace "mutafi princess "

Ta sauka Aisha rike da jikar laptop dinshi ta rakasu suka shiga mota tana masu waving suka fita daga gidan, 


Ta sauke numfashi ta koma ciki ba tsayawa ta haye sama tafara gyaran dakinta, 


Seda faseelat ta koshi ta kauda kayan ta shiga gyaran gidan 9:30 tagama ta koma daki ta kwanta duk abinda take dauriya ce kawai take amma batajin dadin jikinta tunkafin ma ya jibgeta, tana ta tunani aranta har bacci ya dauketa, 


Karfe 12 :40pm ta farka ta shiga toilet tai fitsari ta fito ta sauka kasa ta shiga kitchen Aisha na girki faseelat tace mata "sannu anty ko da akwai abinda zan kamamiki? "



ko waiwayo wa Aisha batai ba tace "babu"atakaice 


Faseelat tace "to shikenan amma Dan Allah anty kiyi hakuri abinda yafaru jiya sherin shedanne "


Aisha tacigaba da aikinta tace "naji "


Faseelat tai shiru tana kallon bayanta jin yadda take ta amsa maganar kamar dole, batakara cewa komi ba ta koma dakinta ,tai kwanciyarta ta kunna data, 



da daddare faseelat ta amshi girki da dauriya tai musu tuwon shinkafa miyar egusi ta shiga toilet tai wanka ta dawo tai simple makeup, 


Fahad duk yabi ya zuzuce wurin kallonta dakyar yafita ishai yana dawowa sukai dinner, 


Ya riga kowa tashi saboda he's eager yajishi cikinta, 


gaban faseelat har faduwa yarikayi dan kar ta takurashi da tabarwa Aisha kwanan saboda batajin dadin jikinta samm, 


bawani shirin bacci tana shigowa yafara romancing dinta tafara hawaye besani ba seda ya tubeta yakara ganin jikinta dake jawur sede kumburin ya sabe, seyaji yakasa yin komi ya jawota jikinshi yana rarrashi itako tafara kuka, dakyar ya rarrasheta ,ya ciro waya yakira doctor ya mata bayani tafada mishi sunan magani biyu daya tablet daya cream cikin daren yafita ya siyo su kafin ya dawo faseelat ta kwafe number umma wadda har yanzu tana nan a tsohon sunanta bad woman, awayarta tai saving da my in-law ,ta shiga contact na fahad ta sauyawa number umma suna da umma ta, 


Yana dawowa ya shafa mata na shafawa yabata nasha, faseelat da kanta tace yaje wurin Aisha yaki suna rungume da juna sukai bacci can cikin dare shaawarshi ta motsa ya tashi yabar dakin ko 15mnt baaiba faseelat ta gane baya dakin ta bude ido, kasa kasa tanajin duminshi yana sabbatuwa Aisha, 



Bayan 4 day's faseelat ta warke simul sede cream na bacewar tabo dataketa shafawa don ta samu tabunan su bace ,


Har yau fahad be daukar kiran umma kuma koda yaga sauyin suna yasan aikin faseelat ne se yabarshi ahaka, 


Ranar jumaa ce tunda safe yafada masu karfe 3pm zai kaisu gaida mommy, 


Bayan sunyi lunch suka shiga suka shirya yana zaune yana aiki Aisha tazo ta zauna tana sanye da riga da sket na lace da gyale a kafada, itakuma faseelat ta sanyo riga da sket atamfa da gyale sede ta yafashi ne tundaga saman kai, hannunta rike da amira dake sanye da doguwar riga, 


Ya dago ya kallesu su duka ya meda kallonshi gun faseelat kayan Sun mata shape sosai komai awaje gyalen yayi shara shara ,ya meda hankalinshi kan computer dinshi sannan yace "honey queen kije ki sauya kaya "


Faseelat ta Kalli kanta tundaga sama har kasa ta kalli Aisha tace "hero miye illar kayan jikina? nagafa anty irinsu ne jikinta "


Ya dago yana mata wani kallo cike da kishi yace "eh iri daya ne amma ita be fito mata structure ba kije ki sauya "


Aisha ko kallonsu batai ba hankalinta na kan chatting, 


Faseelat ta haye sama can zuwa ta fito ta doro Arabian hijab saman kayan, 


Fahad ya dago ya kalleta, rigar tai kwance kan breast dinta, yace"kije ki sauya dressing nace"


Faseelat ta turo baki ta koma ta sanyo gownt da bakin gyale shi kuma cotton amma karami, ya kalleta ya Kalli hips dinta yace "basuyi ba"


Cikin haushi takoma ta sako English wears da t

Dubai hijab ,ya dago ya kalleta sunmata mugun kyau yace "go and change them "


Ta koma ranta cunkushe ta sanyo riga da single zane ta dora after sama ta fito, tundaga saman bene ya dago ya na kallont




Post a Comment

0 Comments