TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

RAGON MIJI PAGE 69

 6⃣9⃣





*wannan page din goron barka da salla ne ga duk masoyan raggon miji ina maku barka da salla Allah ya memeta mana ya amshi ibadun mu*






Jamila tayi rarrashi tayi magiya yaci abinci ya mata banza tai kuka har tagaji uffan bece mata ba ,seda lokacin salla yayi sannan ya tashi jikinshi rau ya fito jamila ta biyoshi tsakar gida, 


Fuska a kumbure taje ta rike kan mashin dinshi da yake niyyar tadawa tace "Dan Allah yaya kafadamin meke faruwa in kuma tun lefin jiyanne sena sani tundazu kashigo inata bakin kokari na kamin banza"


Ya daga ido yana mata wani kallo,


Ta sadda kai kasa yace "daace kinada hankali da nafada maki problem dina amma baki dashi don haka kibarni da matsalata I will fine my solution"


Ta daga ido ta kalleshi tana nuna mishi ka tausayamin ya kauda fuska ,


Ta daga kai kurum ta sakar mishi mashin ta koma cikin daki,


yaja tsoki ya tafi masjid, bayan Sun gama salla ya wuce wurin kawu manu, 


Tunda ya Kalli fuskar shi yasan da matsala yana zaune kan dandamalin gidan shi khalil na gefe a zukunne kai kasa yafara yiwa kawu manu bayani tun daga farko har karshe, daga karshe yace "Dan Allah kawu kabata hakuri maybe ta hakura kuma Dan Allah ka nusashsheta ta gyara saboda gaba,ni nasan in aka cigaba ahaka duk wacce na auro abinda zeta faruwa kenan"


Tunda khalil yafara magana kawu manu ya rike baki cikeda alajabin lamarin, 


Bayan khalil yayi shiru ne kawu manu yaja numfashi yace"da farko de zanfara da baka hakuri ka kara hakuri akan nada, hjy uwace bazaa gaji da yi mata biyayya ba ,zanje na gwada saa dan kasan tanada wuyar shaani zanyi bakin kokarina na fahimtar daita kuma zan bata hakuri saboda yarinyar bata kyauta ba idan Allah yasa ta hakura shikenan "



Khalil yace "to nagode kawu Allah yasa ta hakuran "


kawu manu yace "Amin sede zan bari se zuwa dare Sannan naje wurin tan lokacin takara hucewa"


Khalil yace "nagode sosai kawu  gobe zan dawo inji yadda kukayi"


ya tashi ya tafi kawu manu yanata tunanin maganar yana jinjina halin hjya da yarintar jamila, 


shifa khalil be wasa da cikinshi tun akan hanya ya fara jin yunwa dan haka yana isa gida ya shige daki ya jawo tray da jamila ta ajiye yayi sarving kanshi yaci abinshi jamila nata bacci abinta ya kalleta aranshi yace,"da kinsan abinda ke faruwa kila ko barawon bacci baze dauke ki ba "


Ya tashi yasha ruwa da magani ya fita yabar gidan don karma ta farka ta ganshi tafara masa shagwaba da ta saba. 



Da daddare kawu manu yaje gidan hjy tanajin sallamar shi ta daure fuska don tariga tasan maganar da yazo yi mata, 


Ba don taso ba tai masa maraba tace ya shigo ciki, 


Yace Tom ya shiga suka dan gaisa kowa yayi shiru bayan wani lokaci sannan yace "dama wata magana ce ke tafe dani, khalil yazo ya sameni yamin bayani akan abinda yafaru tabbas babu dadi amma Dan Allah kiyi hakuri kima yarinyar uzuri kuma yakamata ace kin dena shiga harkar yara don ba abinda ya jawo hakan se yawan damuwa dasu da kikai, dan Allah de kiyi hakuri kibar maganar sakin nan ko dan tsohon cikin jikinta taci darajar iyayenta"


tunda yafara magana hjya ta cije baki akagare take yagama yana kai aya tace "wato khalil kara ta yakai wurinka?to yayi mishi kyau manu yakamata kagane ni na haifi dana dole nadamu dashi inason kayana, batun Saki kuma sefa ya sake ta saboda ba macen aure bace duk macen dake wulakanta maka mahaifiya ai ba mace bace amma dayake khalil sauna ne yana sonta ahakan ,to ko yanasonta dole ya rabu daita ciki idan ta haifa akawomin zan rike kayana iyayenta kuma matsalar su ce"


Kawu manu ya girgiza kai yace "nasani hjy amma dukda haka bekamata kina tsaurarawa ba yakamata kisan matar shi ma tana da hakki akanshi na kulawa daita wlh hjy idan baki gyara ba kowacece ze auro haka zatayi"


Tace "wani abu ne dan naso hira da dana ko kwana yake gidana?duk wacce ya auro idan tsari na be mata ba se ya saketa ga mata nan rututu kamar awaki fara ja baka koriya seya zaba "


kallonta kawai yake yace "nasande inada kima a idonki idan har dasauranta na rokeki ki kyale yarannan tare ki rabu dasu ki hakura da maganar sakinnan"


Hjy tai shiru, ya cigaba da cewa "kiyi hakuri dan Allah insha Allah wannan baze kara faruwa ba, yara se hakuri "


Hjy tai nazari takasa manta masifar da jamila ta mata kuma tanajin nauyin manu saboda yana kula daita da yaranta, 


Ta kalleshi tace "manu wlh zuciya ta bazata iya hakura da wannan abun haka ba, khalil de beyi mata ba na hakura nabarta saboda kai amma dole yakara aure nanda dan karamin lokaci kuwa"


Ya riga yasanta sarai ahakan ma yanaganin ta mishi alfarma ya bude baki yace "to Allah yasa haka shine mafi alheri ,kuma Dan Allah akara hakuri da harkar yara "


Yatashi tsaye yace "zan tafi se Allah yakaimu"


Hjy tace "to nagode kwarai Allah yabar zumunci agaida mutanen gidan"


Manu yajuya ya fita ta tabe baki kasa kasa tace "ai bazata zauna tanajin dadi tana iskanci ba aure zeyi Allah yasa asamu wadda zatai ta cin uwarta shegiya marar daa"


kawu manu kau tuni ya tafi ,yanata jinjina maganganun da sukayi "


Duk yadda khalil yaso ya share jamila kasawa yayi dan taki ko cin abinci shiko besan abinda ze taba lpyar unborn cikin dare yakasa bacci ya tashi ya sameta falo zaune tayi tagumi yunwa nacin ta cikin ta nata motsi amma taki cin abinci,


Be tsaya wurin ta ba ya nufi kitchen ya zubo abinci ya dawo, ya zauna kusa daita ya kira sunanta "jamila! "


ta kalleshi ido tafff da hawaye yace "nayi laifi kiyi hakuri kici abinci karki wahalar da kanki da yaron dake cikinki"


Jamila se hawaye tace "yaya miye kake boyemin? Hjy ce ko? ta ce ka sakeni? "


Ya girgizakai yace "niban fadi haka ba yanzu de kici abinci"


Ya debo a spoon zekai bakinta ta kauda kai tace "bazanci abinci ba, nakoshi yaya kafadamin mike faruwa "


Ya ajiye cokalin yace "wai ya kkso ne kefa kika dauko fitinar nan miye amfanin tada hankali ?ainasa kin shirya ma abubuwan da zasu faru to hjy ce taita fada nabata hakuri ta hakura shikenan kici abinci"


jamila tace "nasan I made a very big mistake amma Hakan baze kara faruwa ba Dan Allah kamanta komi kakara bata hakuri kuma "


Ya debo abinci yakai bakinta yace "namanta just eat the food"


Ta bude baki taita amsa seda ta cinyeshi tasss sannan suka nufi bedroom tai brush tana kwanciya se bacci shiko idanunshi biyu yanata tunani, 



Da safe lpy lau ya nunawa jamila ya tafi school be je ko gaida hjy ba, anayin breakfast ya tafi wurin aikin kawu manu ya sameshi, kawu manu yafada mashi yadda sukayi da hjya,


Yace "inaga kai auren shine maslaha tunda ta hakura da maganar sakin kuma kanada halin yin auren "


Zufa tarika karyowa khalil ya cire hularshi yafara fifita cikin tashin hankali yake cewa kawu manu "kawu da akwai matsala wlh nide harga Allah bazan iya rike mace fiyeda daya ba saboda ba nauyin ciyarwa ne kadai ze rataya awuyana ba Dan Allah ina rokon kasake koma wa ka rokar min ita kai kadaine yanzu Wanda zaka taimakamin"


Kawu manu yace "to sede nabaka hakuri khalil dan bazan iya komawa wurinta ba kariga kasan halin mahaifiyar ka "


Khalil yayi shiru kanshi kasa yanata hada zufa, 


Kawu manu yace "kaje kamata bayani kila ta fahimceka "


Khalil yace"to nagode sosai kawu ni zantafi agaida mutanen gida"


Ya tashi ya tafi, tashin hankali kenan  bema san ta ina zefara ba, memakon ya koma school se ya nufi gidan hjy, da shigar shi ya tarar tana baccin tohon gira ze juya ta bude ido "kai dogore dawo nan "


Khalil dake ta zufa kamar ya hadiyi kwado ya dawo ya zauna kasa ,


hjy na kwanciyarta tace "ainasa bazaka zo gaidani ba tunda zan rabaka da matarka,shine kaje kakai karata shi kawunnaka yafada ma sakona ko? "


Khalil ya daga kai tace "to dole kai daya ko ka saketa ko ka kara aure,


Dubara ta rage taka tashi kabarmin gida marar tunani, kwana biyu nabaka kagama duk shawarar ka"


Khalil yayi zaune dakyar ya samu yace "Dan Allah hjy kiyi hakuri wlh bazan iya auran mace fiyeda daya ba "


Tace "shikenan hakan yafi sekaje ka Saki waccan bakar dagar"


Ya dago ya kalleta yace "amma hjy.... "


Ta katse shi "amma me? Amma baa kyauta ma iyayen ta ba ni ta kyauta min? ni wlh khalil se naita ganin kamar anmin musanyar ka har atabani ka kyale, toni bazan bari ba katafi ka saketan tunda kai raggo ne baka iya auran mata biyu "


Ya buda baki ze magana tace "get out from my house karka sake zuwamin wawa marar kishin zuci"su hjy antuno school 🤣


sumi sumi khalil ya tashi ya fita ta bishi da harara tace "idan ka saketan zan nemo maka ustaziya wadda ko hoda bata shafawa in zata fita saboda tsoron Allah 🤣ai akwaisu "



Haka khalil ya koma school yanata tunani, sama sama yake komi beiya tunkarar amininshi da maganar ba, 


Wan safe yakasa zuwa gidan hjy, hjy nata zuba ido har dare shiru, ta cika tai fam, 


wansafe khalil bejeba again kuma befadawa jamila komi ba sede duk ya rame saboda zullumi da tunani bakomi ya hanashi zuwa gidan hjy ba se tsoron abinda zefaru,har dare shiru hakurin hjy yakare kodayake dama bashi gareta ba, 


Aka kara kwana arana ta ukku karfe 9:00am ta shirya ta nufi gidan khalil, 


ta shiga tanata kwada sallama da karfi, 


Jamila dake bacci  ta fito hankali tashe jin muryar hjy, 


hannun hjy akugu tabita da kallo tundaga sama har kasa turtsetsen cikin jamila yayi sororo a tsaye, 


Jamila ta sunkuyar dakai tana hadiyar wani miyau me daci, 


Hjy tace "ke dan ubanki me kike jira  kinbi kin manne wa dana sekace shine ubanki ki maza ki dauko tsummar hijabinki kibar gidannan yanzunnan mahaukaciyar banza da wofi "



Jamila ta zube akan gwiwa tafara begging" Dan Allah hjy kiyi hakuri wlh sherin shedan ne bazan sake ba "



Hjy tace "wato dagaske da hankalinki kika jemin kikamin dibar albarka, to dan ubanshi shedan din daga yau baze kara Saki kiyi wani abu da auren dana ba maza tashi ki dauko hijab kibar gidannan ki nufi kauyenku"


Jamila tasaka kuka "hjy kiyi hakuri dan girman Allah "



Hjy tace "ai sekiyi "

Fuuuu ta shige dakin su ta dauko mata hijab tadawo ta tillamata ta wurga mata 1000 tace "aje can aiwa tsoffi badeniba "


Jamila tana kuka ta dauki hijab din tasaka tasa slippers ta dauki kudin ta fita daga gidan, 


Hjy taja tsoki ta saka keys ta kulle gidan takoma gida tana ta banbami ita kadai, 



2:pm khalil ya dawo cin abinci amma gida gar kame da sabon padlock ,yayi shiru yanata tunani gabanshi inba faduwa ba ba abinda yake yi hakanan zuciyarshi tabashi hjy takora jamila gida, 


Ya dauko waya yayi dialling number jamila tana ta ringing baa dauka ba , ya gaji ya tada mashin ya nufi gidan hjya, 


Ya sameta tana ta hidimar ta hankali kwance, 


Tana ganinshi ta tabe baki tace "se yau mijin jamila? Kamanta kana da uwa ta hakkin matarka kawai kake shasha to ni na korar maka ita tana gidan ubanta yanzu haka "


Khalil kamar ze kuka ya samu wuri ya zauna ya dafe kai da hannu biyu, 


Hjy ta cigaba da aiyukanta tanayi tana fada, 


"wawa kawai mutum kamar ba namiji ba yayi ta abu kamar mace ina amfanin me irin zuciyarka"


Can sede taji kukan khalil, ido waje ta leko daga kitchen taga lalle kuka ne yake, tafita tasameshi tai tsaye kanshi tace"kuka kakeyi kenan saboda ankora ma mata " ta dauko keys ta jefa mai tace "gashinan kaje ka dawo daita tunda tafini agunka, katashi katafi ka dawo daita tunda abun yazama ciwo sena tashi neman maka magani tunda ko wata tsigagga ka auro haka zaka mutu kanta"


Khalil be dauki keys dinba yatashi ya fita daga gidan, 


Hjy tabi bayanshi da kallo "kai Allah ya wadaran naka ya lalace mtswww"



Khalil betsaya ko daukar mashin ba ya nufi tasha ya shiga motar batsari tana cika suka dauki hanya 



fahad jinya biyu yayi gata faseelat gata Aisha ,faseelat abunma gaba yake karawa memakon asamu sauki, 


Yau suna zaune a main palo faseelat tafito tana yamutsa fuska hannunta dafe da kanta , tun a bene yaji kamar yaje ya daukota ,


Saboda Aisha nagun ya danne ya zauna har taiso besan lokacin da ya mika mata hannu takama tazo ta zauna gefenshi, shi yariga yasan yafi ma yawan taba Aisha akan faseelat sede dukda haka yana kiyaye maganar aishan dan ta zauna lpy, ya saci kallon Aisha dake wa amira tsifa tacika tai fammmm fuska daure, 


Fahad beko kara kallonta ba ya cigaba da aikinshi a system, 


Faseelat ta kalli Aisha tace "Dan Allah anty kiyi hakuri wlh dan banajin dadi ne shiyasa ban sauya mata wani kitson ba amma dama inada niyyar zuwa gobe nai mata "dayake tunda tazo gidan ita ke mata, 


Aisha tace " karkidamu"atakaice



Faseelat tai yake abun Aisha kullum gaba yakeyi taki saukowa zamansu kusan 1month 2wks amma basuyi maganar awa daya daita ba, 


Ta kwanta kan kafadar fahad tace "hero Dan Allah kabarni naje gidan baba babba gobe jumaa tunda nayi aure banje ba gashi jibi ummi zata dawo bansan su ganni batare da naje ba "


Fahad yayi kamar bejiba ya cigaba da aikinshi tariko hannunshi tace "plssss mana "


Ya bude baki ahankali yace "bazaki ba "


Tafara shagwaba ta turo baki gaba "Dan Allah Hero bawani jimawa zanba"


Ya kalleta yace "keda baki lpy amma kike neman fita "


Tace "naji sauki ai daga can semu wuce gidan umma "


Ya tabe baki yace "salon kije kita sakarci da mazan gidan ko?bazaki ba "


Faseelat tace"haba hero zumunci ne fa ,ni neman ladar kawai nake badon wani abu ba saboda girmanshi manzon Allah (S. A. W)yace meyankewa baze shiga aljanna ba yana nufin meyanke zumunci,kadaure kabarni naje plsss"


Yayi shiru tai sauri tace "gidan  ma ba maza  biyu ne kuma suntafi karatu "tamishi karya, 



Seda yadau lokaci yanata aikinshi sannan yace "naji ki shirya "


Faseelat takai mashi kisss a cheek tace "thank you my one and only "



Aisha daketa kallonsu tundazu ta tabe baki cikin ranta tace "zakici ubanki ne muje zuwa "


Ranar girkin Aisha ne wansafe na faseelat tun 10am suka fita dan yaki barinta tai driving wai bazata iyaba, 


Suna zuwa ya kalleta yace "ki shirya da anfito masallaci zanzo mutafi gidan ummar "


Tace"karka samu damuwa sena jiraka ma "taiwa wuyanshi kisss tace "take care of ur self "ta bude motar tafita, 


Yabi bayanta da kallo hijab ce jikinta amma tabi tai kwance bayanta ita kuma ga yanayin tafiyar ta kamar tana yi da gayya, 


Har tashige yaja tsoki"i hate all this kind of dress dole nasamo wasu different hijab din " ya tada mota ya tafi, 


Su baaba sosai sukai murnar zuwanta sunata nan nan daita, 



Karfe 2:20 yaiso kofar gidan yakira ta, ta dauki hijab tasa taiwa baaba bankwana azaure tahadu da farhan dan shekara sha biyar yafito daga dakin zaure ya kalleta yace "aa anty tafiya zakiyi muje kawo jikkar nataka miki"dan tunda taje kwance take duk sungane komi 


Faseelat tai yake tace " da kabarshi yana nan kofar gida yana jira na"


Farhan "yace kikawo anty baniso ki wahala ne "


Ya mika hannu dan dole tabashi jikkar tana hada zufa, suka fita atare, 


Tundazu fahad yazo kofar gidan dama yaga  wani dogon saurayi ya fito daga gidan sekuma ga wanan dan iskanci ma har da rike mata jaka, 


Yanata kallonsu ta cikin glass har suka karaso yaran yabude mata mota ya leka ya gaida fahad, fahad yayi banza ya meda hankalinshi kan wayarshi, 


faseelat tai yake tace "beji bane farhann bani jakar nagode ka gaida su yaya "

Ta amsa ta shiga ya rufe motar ya nufi gida, 



fahad yanata memeta sunan farhannn din yadda takirashi murya a sauke,yanajin dan banzan kishi, 


Faseelat da tun dazu take kallonshi murya sanyaye tace "kayi hakuri dan Allah nasan namaka karya amma..."


Ya daga mata hannu batare da ya kalleta ba yace "just shut ur mouth off, naga kome ai no need kisake min wata karyar "

Ya tada mota yakama hanyar gida, 


Faseelat tai narai narai da idanu tana kallonshi amma yaki ko kallonta, ganin dandanan seya furzar da iska yasa tai gummm da bakinta, dukda de taso suje gidan umma tunda harta fada musu tasan suna can sunata mata hidima, 


Beko shiga  cikin gidan ba yatsaya yace mata tafita, ta kalleshi tafita ta shige ciki, 


Yaja tsoki ya nufi gidan ummar shi sunata tambayarshi ita yace musu bacci ya dauketa shine yabarta be tada taba, 


Daganan yawuce gidan mommy Aisha ma nacan acan suka shantake se 6pm ya wuce chamber dinsu dasu sabeer, 



Agida faseelat ta dage tai musu special dinner abincin very tasty, tai wanka ta tsara kanta cikin wata long riga roba duk tabi jikinta jar color tadora yellow din gyale tana ta zuba kamshi sotake ta mantar dashi lefinta 


Ta zauna jiranshi se 8:5pm ya shigo taje ta taroshi ya kauce ya wuceta ya haye sama ,


Tai tsaye taba kanta hakuri tabishi dakinshi, 


Har yashiga wanka ta nufi toilet din da niyyar shiga tajishi gam yasa key, tai shiru taje ta fiddomai kaya marassa nauyi ta zauna kan bed jiranshi, 


Ba jimawa ya fito yana tsane lemar jikinshi kallo daya ya mata ya dauke kai yafara shirin shi, 


Taje zata tayashi yace"i don't need ur help "



Kamar zatayi kuka tace "haba mana hero kayi hakuri nasan ban kyauta ba amma da banmaka karya ba da bazaka amince ba kayi hakuri plsss "


Yaja tsoki cikin fada yace "kin rainani kenan ni tsaranki ne? anfada maki anamin karya get out from here "


faseelat ta kalleshi ta juya tafita tabar dakin kamar yadda ya bukata, 


Takoma daki tanajin haushi duk wuyar girkin da tasha abanza baze ci ba ita dama baiya ci zatai ba, ta tashi ta leka dining su Aisha har sungama cin abinsu ,



Ta dawo ta kwanta tana tunani, karfe 9:00pm ta koma dakin, har yakashe light ya kwanta ranshi duk badadi, idanunshi arumtse suke amma ba barci yake ba , 


Yaji shigowarta jin shiru kuma ya bude ido  da niyyar ganin ko tafita ne, 


Yaga haske tan garam a dakin ita kuma ta sabule rigar jikinta tana cire pant, yakura mata ido yana kallon tsarin jikinta, har ta cire ba kunya ta karasa kan bed din shiko yakasa ce mata komi, ta haye samanshi tafara kwance  mishi notikan brain, 


da zafafan romance ya rude ya cigaba da meda mata kamar zasu cinye juna, 


Sunata nishi tace "hero!"


Yace "hmmmm!"


Tace "kayi hakuri "


Yace "shitttttt! "alamun bayason maganar, ta daure ta ware mishi kafa yaci iyacin shi har ya gamsu sannan yabarta ankwana biyu baai dogon sex irin haka ba ya rungumeta yanata fada mata how he enjoyed her itako tai shiru dan zafi takeji a maranta, sukayo wanka atare suka zo suka kwanta, 



Da safe tun karfe 5 jirgin su ummi ya sauka Nigeria tana ta murna itako zata ga ummi dinta, 



weekend ne zaune yake kanta kan cinyarshi wurin karfe 10:am tana chatting yana latsar system tace "hero karfe nawa zanje wurin ummi din"


Ya kalleta yace "tashi kishirya na kaiki "


Tai wufff ta ajiye wayar hannunta tana murna ta shige toilet 



Yayi murmushi yabita da kallo , ko 5mnt baai da shigarta ba kira ya shigo wayrta ya kai hannu ya dauko wayar yaga kiran what's up ne ga pics din wani kato ajiki ,


Yayi rejecting kiran yabi charts din har kan number ya shiga cikin chart din, 


Batama buda chart dinshi nayau ba ya bude messages din tundaga farkon charts din"me kyau kina lpy kinmanta ni dan kinyi aure ko "


Tace "ayya bangane ba"


Seya turomata pic fahad ya bude hannunshi na rawa saboda kishi, 


Faseelat itada baffa a mota fuskar faseelat kusada tashi kafadunsu ahade sunyi selfie faseelat harda turo baki gaba kamar de yadda akeyi ,

Zuciyar fahad harbawa kawai take kishi ya rufemai ido, 


 betsaya bin sauran chats dinba ya nufi hanyar toilet zuciyanshi na zafi jikinshi na rawa faseelat tagama wanka tana cikin dauraye jikinta taji anjawo ta waje da karfin tsiya, 


Ta fiddo ido waje har yafiddota gabanta na faduwa ,jikinta ya dauki rawa ganin yanayin shi idanunshi awaje jijiyoyinshi duk Sun tashi kamar bashi ba ,


Zuciyarshi na tafasa Ya hasko mata wayar idonshi rufe cikin tsawa yace "ubanwa ye wannan? "


tanaganin hoton ta zaro ido waje ,bakinta yafara kyarma magana take sonyi takasa fitowa saboda tsoron yanayinshi , 


rai bace fahad ya kwada wayar da kasa ta tarwatse faseelat ta juya dasauri zata koma toilet ta kulle ,ko taku ba taiba ya damkota tas !tass !!tasss !!!tasss!!!! Tasss!!!!!tasssssss!!!!!! Ya dauketa da lpyanyun maruka guda shidda lokaci daya, 


faseelat ta zube awurin bakinta a fashe yana fidda jini tafashe da kuka tafara matsawa baya, tana girgiza  mishi kai tana juya hanuwa ,


Yana huci Idonshi rufe ba abinda yake hangowa se fuskarsu da tahadu har sajenshi ya taba cheek dinta ba tsayawa ya rika kai mata harbi da kafa ta koina, 


Jin azaba Faseelat ta tashi da gudu zata bar dakin ganin ze kasheta ya bita ya jawota ya cigaba da duka da harbi, 


Su Aisha na daki tajiyosu ta tabe baki itade Allah yahutashsheta yanzu faseelat kadai ke shan jibga, ihu kawai faseelat keyi amira tasa hannu biyu tadade kunnuwanta zuciyarta na bugawa da karfi, 



seda yamata lisss sannan yakoma saman seat ya zauna badon yadena jin abinda yakejiba ya dukar dakai ya dafeshi da hannuwa yana ta bubbuga kafarshi kasa yanajin kamar ya cire zuciyarshi akan azabar da yakeji, 



Muryar faseelat ta dishe nishi kawai take iyayi tana sheme tsakiyar bedroom din dafe da mararta dake ta juyawa kamar zaa cireta, Kuma tanajin jinin daketa fitowa daga Virgina dinta, 


Tanata nishi domin  tana cikin matsanancin ciwo, shiko fahad ko damuwa da nishin beba bayan wani lokaci, yaji kafarshi dayake motsawa tana taka ruwa ya bude ido still kanshi na kasa, 


Yaga jini ya zaro ido gabanshi yayi mummunar faduwa firgigit ya dago ya cire hannuwa daga kai ya kalli gun faseelat tundaga can jini ya malalo har inda yake,


Besan lokacin da ya kwala kara ba yayi kanta agigice hankali tashe.... 



Post a Comment

0 Comments