TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

RAGON MIJI PAGE 46

 RAGON MIJI


4⃣6⃣






*another page for you rukayya haroun(maman nour)* *and erminatou*




Ummi tace "gaskiya alhaji bazan kai diyata gidan kishiya ba "


Abba yace "haba asiya be kamata kina magana irin haka ba, ita ai ba budurwa bace jawara ce kinga mawuyacine tasamu saurayi, dan Allah kibarta tunda tanasonshi karki sage mata gwiwai "


Ummi tace "ni ban iya kishi ba bare ita hakanan kaje aimaka wani mugun abun kana zamanka lpya "


Abba yace "shikenan tunda zancen kikeso bari nabaki wuri inkingama mitar kikawomin fura ta "


Ya tashi yabata wuri, ummi tace "shikenan se inki magana, yanzun intayi auren ko nima hankali na ba kwanciya zeba bare ita, tunda taji tagani shikenan Amman dole na dage mata da gyara na musamman in inaso tai daraja " 



Ta tashi ta nufi dakin abba, 


Faseelat nashiga daki ta haye gado ta kunna data cikin farin ciki, 


Messages nagama shigowa tabude na maman amira wanda yanzu ta meda number ta da my anty , ta bude message nata "wai antyn amira kinmanta danine?ko duk zawarcinne ya boyeki?har munyi tafiya mundawo, in bazaki zoba kibani address naki zanzo ni saboda yarki ta matsamin "


Faseelat tai dariya ta tura mata "zanzo insha Allah zuwa jibi de nima ina missing naku "


Tafita tashiga contact na fahad ta turamishi "masoyi naji dadin kyautar ka, Allah yakara maka budi ya kareka daga sharrin makiya, kanata kara kyau miye sirrin ne?"


Ta turamishi tana murmushi ta kashe datar se barci, 


Da laasar fahad ya kirata suka kara shan vedio call sannan sukai sallama, 


Se dare ta samu tabude data bayan sunyi bankwana da habibinta, ta shiga message din maman amira "💃🏼💃🏼💃🏼thank se kinzo inanan ina zuba eyes"



Faseelat ta tura mata "don't mind"


Tafita alokacin fahad ya turomata reply kamar haka "amin cutie karki damu da kyauta da namiki bakomai bane danko raina kikeso zanbaki, kinason kisan sirrin?"


Faseelat tace "thanks eh inaso inji "


Cikin zolaya yace "aisha ce sirrin tana kula da service dina duk lokacin dana bukata ana bani "


Faseelat ta tura mishi "😏 To yayi kyau ,tunda ta isheka me zakai dani "?


Yace "I'm joking fa naga kinhau I just test you kinga kema kishinne dake zuwa zakuyi kuyita hadamin zafi "


Faseelat tace "aini bazanyi kishi da anty ba "


Yace "hmmm Allah yasa, gobe inanan zuwa fa, don kullum zanzo sekin gaji dani "


Tace "ai bazan gaji ba kazo yanzu ma "



Yace "kina tsoron nawa da rana ma yaaka kare? "


Tai murmushi ganin ya sauya zancen tace" good night sleep well 😘"


Yanagani yayi murmushi ya cigaba da aikinshi. 



Da safe abba yaje yasamu baba babba akan maganar fahad yace zesa amishi bincike akansa, 



Da marece faseelat taci gayu sosai tasaka kayan da ya siyomata, tafito ummi tace" kinyi kyau gaskiya ina zuwa halan? "


faseelat tace "fahad ne yace yana kan hanya "


Ummi tace "to waike bazaki ce yarika shigowa ba kullum fira a mota? "


Faseelat tace "to ummi zanmasa magana "


ummi tace "kibada asiyomiki dan juice mana kitafi mashi dashi yadansha "


faseelat tace "to bari nabawa Mubarak "


Ummi tace "sekinfa dage yarinya, don ba khalil bane wannan awaye yake kuma yanada mata "


Faseelat tace "nasani ummi bari naje "


Ta juya ummi tabita da kallo rigar duk tafito mata da shape dukda tanada fadi, kuma faseelat dan mayafin rigar kawai ta yafa, 


Karfe 5 yazo ya mata waya tafito, be fito daga mota ba ta cikin glass yake karemata kallo, harta zo tabude marfin motar ta shiga, 


Yaja numfashi ya sauke ta kalleshi tana turo baki, 


Ya lumshe ido ya bude yace "cutie wannan kwalliyar fa?"


Tace "i did it just for you "tana marmara ido cike da jan hankali, 


Yayi murmushi yanabinta da ido yace "thank you I'm happy, kinyi kyau sosai "


Tace "thanks ga ruwa"


ta mika mai water melon juice yana kallon kwalin yace "ni bazansha ba sede kibani a baki "


Ta bata fuska tana hararanshi yace "abinda aisha keyi kenan komi yimin take taimin wanka, tasmin kaya, ta bani abinci abaki, amma ke just kiban drink yagagara "


Ta harareshi tace "kabari kaga muyi auren ba wanka ba har goyonka ma zanrika yi "ya kyalkyace da dariya yace "sure? "


Ta daga mai kai yace "to fara tundaga yau mana mugani inda gaskene"



Ta tunzuro baki gaba tace "open ur mouth"


ya wage baki yana jiran tafara bashi, 


Tai dariya ta bude marfin ta dora mishi kwalin abaki, ya dage yayita kwankwada, tai sauri zata janye caraf ya rike hannun alamun ta cigaba da bashi, 


Ta dora mai yayi ta sha ta fiddo ido tana kallonshi tasss ya shanye yana meda numfashi ,tana mamaki ta sadda robar Kasa bakomi ciki ta dago tace "amma yau anty batai maku girki ba ko? "


yayi dariya yana goge bakinshi da handkerchief yace "yau nidakaina nashiga kitchen, bawani yunwa nakeji ba jindadin juice dinne yasa na shanye shi duka, kinsan duk abinda ya fito daga gunki dole yayi dadi "

Ya kashe mata ido daya, 


Ta rufe fuska tana dariya, 


ya dauko waya yace "kigyara nai miki pic, badani zaaiba bare kice danna samu na tabaki ne "


tace "OK, amma zamuyi da kai a wayata "


Ya saki murmushi yanajin dadi, 


Ta dan fiddo ido ta matse baki ya dauketa, pic din yayi mugun kyau kalar rigarta purple da baki ,


shiru be dagoba yanata kallon bakinta da ta matse kamar zatai kisss, 


Tana kallonshi tace "muyi atare mana "


cikin rashin sanin abinda yake yace "wait for me "


Ta turo baki ta matsa ta leka wayar yayi zooming bakinta yanata kallo ta fashe da dariya, 


yayi sauri ya dago cikin dawowa tunani, 


tana nunashi da yatsa tana dariya tace "Allah kacika jaraba dubi duk yadda idanunka suka koma "


Yayi murmushi ya jingina da seat ya juya ya kalleta yace "kamar kinsani kima shirya "


Ta canza maganar da matsawa kusa dashi ta dauke su pic, 


Tana dauka shiko hankalin nakanta tana samu tadauka ta matsa tana dubawa tace "yayi kyau sosai, kasan wani abu zan dorashi a status da insta "


Yayi murmushi yace "idan kuma bakisaka ba ni zan saka akan nawa "


Ta rufe baki "rufani kasayani ban shirya abinda zancewa anty ba, gobe ma zanzo ganin yata anty ma tace tayi missing dina "


yace "gobe munada special guest kenan Allah yakaimu "


Tace "amin bari natafi se munyi waya"


Yace "ammmmm"ya fiddo 1000 rafas biyu daga gaban motor ya mika mata yace "kibawa yara "


Ta girgiza kai tana murmushi tace,"bana son kudinka kai nikeso"


Yaji dadin maganarta ya lumshe ido ya bude kafin yace wani abu tabude tafita tana mai murmushin dauke numfashi, 


ya rumtse ido gam yanajin yadda zuciyarshi ke harbawa saboda tsananin sonta, 


sannan ya bude yana kallonta har ta shiga gida, seda ya dau 10 mnt sannan ya tada mota ya tafi, 


Yana kan hanya yamata transfer na 500,000,



faseelat mamaki ya cikata da tagani tanata tambayar kanta koshi bejin wuyar fidda kudine oho, ta nunawa ummi, ummi tace


 "duk kan gyaranki zasu kare ai"


faseelat tai dariya 


Next day tunda wuri faseelat tagama aikinta tatafi super market, ta kwashi kayan kitson yara danginsu beads ,robber band,robar kitso ,Brazil wool dasauransu sannan taje wurin kayan wasan yara, 



Wata big teddy me kyau ta baby ta burgeta ta dauka taje tabada ATM suka cire kudinsu kusan 50 thousands teddyn yakama tana dauke daita ta hau napep zuwa gidansu Aisha, 


Me napep na ajiyeta ta biya tai knocking ta gaida baba tsoho ta shiga, 


Amira na wurin wasanta ta hango faseelat da gudu taje ta rungumeta, 


Faseelat na dariya tace"daughter I  really miss you "


Amira tai dariya tanakai hannu kan teddy faseelat tabata tace "dama nakine gashinan "ta mika mata amira ta rungume babyn, 


Faseelat tace "ina anty? "


Amira hankalinta na kan teddy dukda tana da wadanda suka fisu setaga wannan tafi mata tace "she's inside "


faseelat tace "OK zo mushiga ciki "ta jawota suna tafiya tana kallon kitson kanta da yadan tsufa, 


Suka tsaya bakin kofa faseelat ta danna door bell shiru takara dannawa seda akai 15 mnt sannan aisha tazo tabude tana murmushi tace "maraba da anty "tana kallon kayan jikinta, 


Faseelat ta shigo tana murmushi, 


faseelat ta gaida aisha, ta amsa tana mata kallon up and down tace "a, a! Jawara kinfaso gari kinga yadda kika kara kyau kuwa? "tana dariya 


Faseelat tace "anty bawani kyau kina zaulayata ne "



Maman amira tace "Allah kinsauya gaskiya bazawarinki na kula dake "


Faseelat tai dariya tace "anty very soon de zanyi aure nahuta da kirana jawara da kike "


Aisha tace "Allah yakaimu muna murna ai, saboda mune kirjin biki "


faseelat tai murmushi, 


Aisha ta mike "baride nakawomiki drinks, inkoma ciki daddyn amira nanan, bacci ma muke kika tadamu "


Faseelat tace "ok"


Aisha tatafi kawo mata drinks ita kuma ta bude jaka ta fiddo kayan kitson amira ta dauki wasu da zatai amfani ta ajiye sauran ta ajesu a kasa, tafara wa amira tsifa, 


aisha nadawowa tagansu tace "yau ranar ta amira ce kenan naga harda katuwar teddy aka siyomata "


Faseelat tace "eh dan ita nazo "



aisha tace "to Nagode "ta ajiye mata ta haura sama, 


Seda tagama mata tsifa ta danzuba drink tasha, ta daga kai tana kallon benen jin aisha shiru, wani malolo yatsaya mata a makoshi ta daure ta farawa amira Twisting, 


Irin manyan nan ne masu guda ukku shaf shaf tagama mata aisha shiru bata fito ba, abun yabata mamaki kusan 1hr, 


Cikin dabara ta kalli amira tace "kitsonki yayi kyau jeki gwadowa mommy "


Amira ta gudu tana taka step, 


Ba jimawa segasu sunfito  Aisha rike da hannun fahad shi kuma ya dauki amira yana tambayarta wa ya mata kitso dan besan faseelat bace har tazo, 


Har suka sauko falo ahaka faseelat tunkan bene take kallonsu tanajin haushi, 


Fahad na dago ido yaga faseelat, 


Tayi kyau tana sanye cikin milk hijab da brown atamfa ya dan dauke ido daga kallonta, 


Aisha tace "yaya kaga teddyn da faseelat ta siyowa amira nan gashi harda kitso tai mata "


Faseelat cikin jin haushi tace "inayini "


yace "lpy thanks for your care for our child "


Tai banza dashi ya juya yacewa Aisha "sena dawo "


Ta matsa tai masa kisss a cheek tace "take care of yourself"


Faseelat ta cika tai famm yana satar kallon faseelat ya fita, 


aisha tazo ta zauna tajawo amira tana duba kitson tace "gaskiya kinyi kokari har kingama cikin sauri kiyi hakuri nabarki ke daya wlh se yanzu mukai wanka tundazu muna kwance "


Faseelat tace "badamuwa "tana yamutsa fuska tace "tafiya ma zanyi "


aisha tace "tunyanzu kitsaya mudanyi fira mana "


Wayar faseelat tahau ruri ta ciro ta duba taga fahad ne batare data dauka ba ta kalli Aisha tace "jirana akeyi dama nacika alkawari ne kawai "


Aisha tace "to shikenan Nagode kwarai faseelat Allah yabarki da masoyinki naga yanaji dake har iPhone 8s kike riko yanzu "faseelat tai yake, 


Aisha tace "bari nakawomiki tsarabarki "


Faseelat tace "dan Allah anty kibarta ina sauri "



aisha tai dariya tace "aikuwa har gida zan kawomiki wasu English dress ne masu kyau nasiyomki naga zasuyi kyau da jikinki dan Allah kima bari nakawomiki daukosu kawai zan yi "


Faseelat tace "tom"


Aisha ta juya faseelat taja tsoki, 


Can zuwa aishar ta dawo da ledar ta amsa tai godiya shaf shaf ta fita daga gidan, 


Tana fita taga motar fahad awaje tana sauri tai gaba yabi bayanta da motar, 


haryakai setin ta ya rage glass yace "kishigo in kaiki "


Tai banza takara sauri, 


Yakara binta yana cewa "meyafaru ne wai? Kishigo mutafi "


Takarayin gaba, cikn fushi yakashe motar yafito yabita yajawo hannunta tana ta kokarin kwacewa ya sakata motar yaja yabar unguwar, 


Faseelat ta duke tafashe da kuka me cinrai,



Post a Comment

0 Comments