TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

RAGON MIJI PAGE 53

 5⃣3⃣





Tana guduwa cikin jin haushi ya kaiwa mota naushi tare da harbi ya rike kugu ya tallabo keya da hannu yana jan tsoki, ya bude motar yana kallon kofar gidansu ya shiga yaja yabar unguwar, 


Itako faseelat da gudu ta shige daki ummi tabita da kallo, tafada kan bed tana kuka me sauti, 


Ummi tai tsaye tana mamakin ta tabi bayanta zuwa dakin, 


Tana shiga ta sameta kwance tana kuka ummi hannu akan gemu tace "faseelat lpya de kika shigo kina kuka? "


Faseelat ta tashi zaune tana share hawayenta da bayan hannu cikin muryar kuka tace "wai tafiya zayayi dubai "hiding the fact 


Ummi ta bude baki tana kallonta tace "oh ni, faseelat don zeyi tafiya kike risgar irin wannan kuka haka to Allah yakyauta miki, ande kusa a mika ki can kima cinye shi saboda so "ta juya tabar dakin faseelat ta koma ta kwanta tana cigaba da share hawaye, 


Tunda yakama hanya yakejin be kyauta ba marinta da yayi, amma dukda haka yana ganin laifinta ko yayanta ne kanme zataje tai hugging nashi shiba namiji bane? Yaja tsoki yana shan round ya jawo waya yana kiranta, 


Faseelat naganin kiran taki picking gabadaya brain dinta ta cushe wai fahad ne ya mareta with out doing any offense ,



Har ta tsinke begajiba ya kara kira yana magana da kanshi "pick pick! pick it please "har ta tsinke baa dauka ba, ya sake kira cos he's regretting, 


Kiran nafara shiga faseelat tai rejecting kiran cikin jin haushin ya dameta, 


He felt very sad, for the first time da faseelat tai rejecting calls dinshi, kanshi yamishi nauyi ya gangara gefen titi yayi parking ya dora kai kan sitiyari few seconds ya dago still idanu jawur yanajin ciwo be taba jin haka ba idan ya mari aisha besan meyasa ba ,


Ya dauki waya ya mata text kamar haka "I'm sorry cutie plss forgive me, and pick my call I want to apologize for my misbehaving "ya tura mata 



Faseelat naganin message din tai deleting dinshi gabadaya, 


Fahad ya sake kira batai picking ba yaja tsoki ya ajiye wayar ya nufi gida ,


faseelat na nan kwance har akayi Maghreb sannan ta tashi tai salla, Omer besan ma abinda yake faruwa ba saboda lokacin da ta shigo gidan ya na toilet yana watsa ruwa,


Fahad yana isa gida ya bude mota jiki sanyaye ya shiga ciki, 


tsit gidan da alamu Aisha tafita yaja tsoki ya haye sama, 


Yadan kwanta idanunshi na kallon pop na dakin hannunshi daya nakan heart dinshi tana ta harbawa fat! Fat!!!, yanata tunanin faseelat, jin anyi kiran salla ya tashi yayi salla, yafara yi musu parking, 


se ishai yagama har lokacin Aisha bata dawoba shi kuma gabadaya hankalinshi nagun faseelat dukda baya zuwa gunta da dare, be tsaya shawara da zuciyarshi ba ya fita da sauri ya kama hanyar gidansu yanajin inbe ganta ba koyaje ma baze iya aikin komi ba, 


Omer ya fito zashi masjid yaga fahad tsaye kofar gidan, cikin jin haushin omer fahad yabashi hannu suka gaisa yace "Dan Allah kamin magana da faseelat inata kiran wayarta bata dauka "


Omer na mishi kallon up and down yace "ba damuwa "


Ya juya cikin gidan yafadawa ummi dake tsakar gida tana alwala cewa faseelat tayi bako ya juya yafita, 


Ummi ta shiga dakin faseelat tace "tsuntsuwar soyayya ga tsuntsun can yazo kitashi kije kiji ko lpy"


faseelat tace "To" ta mike zaune ,ummi ta juya ta shiga daki ta kabbara salla, 


Jin ummi ta shige daki faseelat ta koma tai kwanciyarta ,


Fahad yayi ta tsayuwa yanata kiranta bata dauka yaja tsoki sama da ashirin har omer ya dawo daga masjid yana tsaye, 


Omer ya shiga cikin gidan ya shiga dakin faseelat tana kwanciyarta har yanzu cikin bacin rai yace "ke ba kiranki ake ba? Tundazu almost 20mnt baki fita ba, kitashi ki je malama "


Ta tashi tana share hawaye taja hijab tafita ,


Ya omer yabi bayanta ya tsaya cikin zauren gidan da ba haske can waje ko da haske daga inda yake yana hango su faseelat din, 


Faseelat nafita ta juyawa fahad baya hannuwanta akan kirji ta harde su, be masan da zuwan ta ba don yabawa kofar gidan baya kuma he's busy thinking of her, kamshin jikinta ne ya sanardashi zuwanta ya juya yana Bin bayan ta da kallo, 

Yace "I'm sorry cutie kishinki ne yasa har na mareki I'm regretting "


Bata juyo ba ya koma gabanta yace "nace kiyi hakuri hakan baze kara faruwa ba"


Faseelat ta dafe kunci tana tuna zafin marin tafara kuka, 


Ya dafe kai yanajin kamar ya rungumota yace "kiyi hakuri cutie ni kaina I'm feeling the pain "


Faseelat cikin kuka tace "yo kishi hauka ne da zaka daga hannu ka mareni don kawai nayi welcoming danuwana "


fahad ranshi bace tuno irin wawar rungumar da omer yamata yace "don kina hauka seki je ki hugging dinshi ba namiji bane shi "


Faseelat ta bishi da kallon takaici ta juya zata shige gida, 


Ya bita yasha gabanta yace "okay kiyi hakuri, amma kema kigane kinada laifi, saboda it really hurt me ganinki a kirjin wani "


Ta zagaye shi zata wuce don takaici ya cikata, 

Ya riko hannunta yace "haba cutie gobe ne fa tafiya ta ko so kike wani abu ya sameni ne kiyi hakuri laifina ne to "


Tafashe da kuka, ya janyota jikinshi batare da yasan lokacin da yayi hakan ba yasa hannu ya tallabe ta cikin muryar rarrashi yace "stop crying please,inajin kukanki har cikin raina, kimin hakuri kinji my cutie kar natafi da fushinki bazan iya komi ba innaje can, kece farin ciki na, ki yafemini "


Ya omer dake zaure jiyayi kamar ya je ya janyeta yanajin haushi over 


Sukau basu san dashiba ma 


Jin ta rage volume na kukanta ya dago face dinta da 2 hands nashi yace "kinyafemin ko cutie na? "


Ta daga kai batare da ta kalleshi ba, 


yace "thank you so much ,I'm happy "


yana sharemata hawaye yace "smile mana ko hankalina ze dawo jikina "


ta harareshi tadan yi murmushi, cikin jindadi yace "ko kefa, kinga yanzu zantafi hankalina kwance da kau duk kin hargitsa ni, I'm going to miss you "


Cikin dasashshiyar murya tace "me too "


Yace "sure? "


Ta daga kai yace "karki damu zamu rika waya as usual, yanxu I want to go back home, and I want something from you "


Tace "what? "



Ya langabe kai "good bye kiss from you "


Ta danyi dariya ta dora hannu abaki yace "please "yana kara langabewa 


tace "nooo I can't, zan de yi maka addua, Allah ya tsareku ya kaiku lpy ya medoku lpy "


Yayi dariya "wayo zakimin ko? Ni yau I'm not happy with ur prayers, tunda bazaki min kiss ba let me have a good bye hug"

yamatso ze rungumeta taja baya tana dariya,, 


Shima yayi dariya yace "bazaki bari ba ko zaki shigo hannu ne "


Ya duba wayar shi kusan 9 :30 maybe sunyi 40mnt a tsaye, 


Ya meda kallonshi gunta yace "cutie I'm going se munyi waya kenan "


Tace "OK please take good care of yourself for me ,going to miss you hubby "


Yayi murmushi yace "I will insha Allah, kema ki kula min da kanki "


Tace "okay, agaidamin anty "


Ya daga kai ta na mishi waving ta wuce gida, 


Shi kuma cikin jindadi ya ja mota yabar kofar gidan, 



Acikin zaure faseelat tai kicibus da omer cikin tsoro tafara inda inda, 


Ya matsa yabata hanya yace "go inside "ta wuce dasauri yajuya yabi bayanta, 


Tana zuwa ta zauna gefen bed gabanta na faduwa tana fatan omer be ji firarsu ba, 


ko 2mnt baaiba omer ya shigo dakin fuska hade shima ya zauna gefen bed din batare da ya kalleta ba yace "wannan shine zabinki a matsayin mijinki jagoranki uban yayanki? "


Tai shiru batace komi ba yacigaba da cewa "mutumin da besan darajar kiba da ze iya daukar hannu ya mareki with out reason shine ze zama mijinki? "


tai shiru kanta kasa yace "kiyi tunani fa sister idan ya'iya marinki awaje inkina cikin gidanshi fa se duka kenan "


Ta girgiza kai yace "nasan duk problems nashi da zuwana nakara ganin wani, anya bakinaso kiyi ganganci da rayuwar kiba yakamata ki sauya tunani "


Murya slowly tace "yaya duk wani problems da kaji insha Allah ze gyara, kuma marin da yamin it was a mistake, na tabbata baa cikin hankalinshi yayi hakanba "


Ta nisa tace "inason shi sosai yaya banajin zan iya rabuwa dashi duk runtsi "


Tunda tafara magana omer yaketa kallonta tana kai aya yace "shikenan tunda kince haka amma karki kuka da kowa in aka kara samun matsala kamar yadda kika ki bin shawarata a can baya "


Ta girgiza kai tace "insha Allah ba abinda ze faru kamin adduan hakan "


Ya mike tsaye ze fita ta riko hannunshi tanaso tai kuka tace "yaya kayi hakuri plsss naga kamar ranka ya baci "


Ya janye hannunshi yasaka a aljihu ya sauke ajiyar heart yace "karki damu raina be wani baci ba, nadeji zafin marin da yamiki sosai "


Ta langabe kai "yaya plss don't tell ummi about it "


Yayi murmushi yace "bama haka dake seda safe "yajuya yafita, 


Tai shiru tana nazarin maganar omer,kafin ta tashi tafita danyin salla, 



Fahad na komawa gida lokacin aisha ta dawo, amma bata dade da dawowa ba tana fitowa wanka ya shigo room din yana binta da desire looking ya kwanta kan bed yanajin dadi feeling very comfy,


Aisha ta kalleshi ta zauna kan seat din mirror ta jawo mai tafara shafawa tace "mommy tace meyasa bakaje mata bankwana ba ?"


Ya na kallonta yace "I'm busy ne akwai wasu aiyuka da naje na kammala "


tai karamin murmushi tana shafa powder tace "a office kenan ? "


yace "noo "


Ta juya tana kallonshi tana murmushi tace "a wurin amarya ko? "


Ya zaro ido ya tashi zaune yana kallonta tai mishi farr da ido tace "yeah kobahaka bane "


Ya tashi yaje yayi hugging dinta ta baya ya na kallon ta ta cikin mirror yace"yaakai kika sani? "


tai yake tunda ya shigo dakin taji kamshin different perfumes wanda ba nashi kadai ba, yanzu da ya sunkuyo takara jin kamshin sosai that means sunhada jiki da faseelat, 


Tace "yaya hanci na ya dade da hardace kamshinka ko karamin canji akasamu zangane "


Ya mike tsaye dasauri yafara sosa keya ta juyo tana kallonshi tai dariya tace "karkaji komi she's your wife to be, maybe tai maka hugging din bankwana ne "


Yafara dariya ta mike tsaye da niyyar wuce shi yayi sauri ya dauketa ya dora saman bed yana mata cakulkuli sunata dariya daganan wasan ya sauya, 



*6am* jirginsu ya daga zuwa dubai.



Bayan Sun sauka beko tsaya hutawa ba yayi wanka yafita meeting da zasuyi da AIRAS company,


Aisha ko kwantawa tayi don huce gajiya, 


Bayan 2 days aka kawo lefen da yayi wasu Aisha iri daya Kowace 3 set that make 12, set daya me 6 se 2 set nada 3,3 color dinsu purple da pink da brown, ya kashi kudi sosai he spend more than 10 millions akan lefen ba kaya masu arha ne acikin akwatunan ba, 


Lokacin da Aisha taga lefen she's not happy at all sede tayi pretending tana murna tai hugging dinshi tana godiya, 


yayi murmushi yace "don't take them as kayan fadar kishiya, nayi miki sune kawai kyautar ki na nan se munkoma gida, saboda naji dadi ganin kin kwantar da hankalinki "


Aisha tai murmushi given him kiss tace "thank you "



bayan yafita tana kuka ta kira mommy suna vedio call Aisha cikin tashin hankali ta nuna mata lefen, 


Mommy ta tabe baki tace "lalle fahad kudi sunmishi yawa ke kuma me kike wa kuka tunda gashi kema ya miki naki "



Aisha na kuka tace "mommy nide nagaji wlh kullum innaduba wayar yaya bakomai ciki se pictures din faseelat ba iyaka da messages nata birjik, mommy badanni ba fa yayi wadannan kayan saboda ita ne, bakiga ba yanata doki invitations ma anan aka buga yanata rabawa bussines friends nashi "



mommy taja tsoki "waya aike ki duba mishi waya ai bin diddikin ki yaja miki gobe ma seki kara dubawa, kina jina ki cigaba da daurewa kinji diyata na lokaci ne ki dena damun kanki kibari ta shigo gidan mugani yadda zaman nasu yake "



Aisha tace" to mommy "


mommy ta cigaba da kwantar mata da hankali suna gama waya ta tashi tsaye tafara zagayar daki ,abin ya daga mata hankali, 


Bayan kwana 4 a Nigeria, inkaga faseelat bazaka iya ganeta ba takara kyawu se kyalli take itakanta intana kallon kanta a madubi batason daukewa ga wani daddadan kamshi da ya kama jikinta batun HQ kam baa magana dan a matse take akagare,niima available ajikinta, 


Fahad sukayi magana da faseelat sabeer da wasu friends nashi biyu zasu hadu da kawayenta suyi maganar yadda event ze kasance, 


Faseelat tace "ai munyi magana da su dinner kadai zamuyi se setting da zamuyi agida ni banason events dinnan suyi yawa "


Fahad yace "yeah cutie shiyasa kike burgeni yadda kikace haka zaai "


faseelat tace "ama fasa dinner din ma "


Yace "noo akwai friends nawa dazasu zo from different countries zanso suyi attending koda event daya ne "


Faseelat tace "okay Allah ya kaimu I'm very eager "ta rufe fuska tana dariya, 


yasaki beautiful smile yace "ai dagawa zaayi se nanda 2 more month"


Ba kunya tace "da nashiga uku "


ya kyalkyale da dariya hardasu tafi seda ya tsagaita yace "inasonki cutie the way da kike dokin kasancewa dani yana kara ruramin wutar sonki, kinsanme nafiki kaguwa don yadda kikara kyawunnan make me go crazy "


faseelat ta rufe fuska tana dan budewa tana kallonshi, 


Yace "but plss karki fita in wancan mayen zezo su hadu da yanmata kurum ke ki boye min kanki "


Tai dariya "abokin kan? "


Yace "noo ni ban yadda da kowa akanki ba "


Faseelat ta jinjina kai tuno marin da tasha, 


Sukai sallama wansafe su zainab da wsu friends nata suka hadu da friends nashi, kudin setting kawai 200,000 suka amsa saboda angwayen suka dauki nauyin komai na dinner din, 


Washegari su fahad suka sauka Nigeria kusan 5pm, lokacin kuma saura kwana ukku aure saboda jumaa zaayi shi, 


In a hasty yayi wanka ya saka kaya ze tafi air port su dauki kaya akai gidan mommy daganan yawuce wurin gimbiyarshi, zuwa gobe da safe zaakai su gidan baba babba saukinma akwai dinkakku irinsu Sari da gownt da zata saka da wasu materials da laces, 


Aisha tana falo zaune taga yafito yana taka step dasauri, 


ta tashi tsaye tana jin kishi tai murmushi tace "harka fito nima zanje gidan mommy yanzuu ko muje kaaje ni"


Ya Kalli agogon hannunshi yace "I'm sorry sauri nake yi ki hau motarki kitafi nima airport zanje daga can zanwuce gidan, "ya zaro cek daga aljihunshi na 15 million yace" gashi ki Yi shirye shiryenki "


Ta amsa tana dan murna ganin 15 million tace "thank you dear "

Tai masa kiss awuya yace "I love you "kawai ya fita dasauri ta bishi da kallon takaici tunda suka dawo taga gidan yakoma sabo ta shiga dakinta taga bakomai nata he then take her 2 his room yace daga yanzu shine nata, abun haushin komi iri daya, tunda tafito ta dawo falo ta kime jiki ba kwari, 


Cikin dakiya tanajin kamar ta sawa gidan wuta ta hau step dasauri going to take her motor key ta bar gidan zuwa gidan mommy.




Post a Comment

0 Comments