TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

RAGON MIJI PAGE 43

 4⃣3⃣




*Dedicated to husnah ta riri yar fullo,inasonki sister kamar yadda kike sona Allah yakara mana son juna yabarmu tare har karshen numfashi luv u dear, ga good addua ta agareki , Allah ya kara maki dadin.....😂🤭 kita  zama tauraruwa awurin oga*




*FANS I'm sorry wani dan bayani da nayi abaya cewar faseelat tana da gadon khalil I'm sorry namanta romance ba sex bane 😂 tunda be taba kusantar ta ba ko idda ma batada ita, inafatan kungane, sannan masu cewa haramunne fahad ya aureta to gaskiya  ba haramun bane Sabida shi besan tana da aure ba kuma Allah baya kama bawa da lefin da besaniba kuma koda yasani aure be haramta tsakaninsu ba, sannan akwai masu cewa halak ne namiji yakarewa macen da yakeso kallo eh hakane amma seta suturce jikinta, mazhabobi da dama sunyi magana akan haka wasu suna ganin zata iya bayyana ado gareshi toni gaskiya nafi ganewa wadanda sukace bazata bayyana ado gareshi ba, sena fuska da tafukan hannaye da kafa,, kuma yawancin malamai suntafi akan haka, ga misali namiji yazo yana sonki se yazam yasan komi na jikinki to in yazo yafasa fa? Shikenan ya kalli banza? 😂 kuma hakan mabudin aikata zina ne, to nide shawara ta yanmata ko gobe ne aurenki da namiji ki kame kamkam ta hanyar zumbula katuwar hijabinki komi kenan in an daura yagani, amma ki tabbatar bawani aibu kike boyewa ba wannan kam kin yi yaudara da zalunci , kuma inyagani komi na iya faruwa, Allah yasa mudace.*



*koda yaushe in anga kuskure amin magana plsss zan kasance me daukar gyara, haka ma kuna iya bani shawara, Nagode da irin kaunar da kukewa buk dinnan.*




Yana tuki yanajan tsoki, yarasa ina hankalinsa ya tafi harya kai hannu jikinta, ta madubi ya kalli siyayyar da yamata da suke aje a back seat yakara jan tsoki, ya fiddo waya yayi dialing number dinta tana ta ringing bata dauka ba cikin takaici yace "pick my call mana I want to apologize for my mistake"yakara dialing number din, 


Faseelat nashiga gida ta fada kan bed tana kuka,cikin kuka take cewa "ya daukeni yariska ne kome? Daze tabani kamar wata matarshi, saboda inasonshi doesn't mean zan bari ya rika tabamin jikina "


Tana kukan tace "duk laifina ne da nake sonka sosai tunda kasan haka ai zakamin komi kaga dama don kasan bazan iya rabuwa da kai ba "


Tanaji wayarta na ringing bata dauka ba se kuka kawai take aganinta bama sonta yakeba jikinta kawai yakeso, 


Ganin ya mata 3 missed calls bata dauka ba yasa ya aje wayar, direct kofar gidan sabeer yawuce ya mishi waya ya fito, 


Yana shiga motar fahad ya dago da kanshi daga jikin sitiyarin motar yana kallon sabeer, 


sabeer yace "mutumina lpya de? "


Fahad yaja tsoki mtswwww yana shafar sumanshi da hannu daya yace "ansamu matsala wlh"


sabeer yace "wace kalar matsala kuma?"


Fahad yace "daga gun faseelat nake, cikin kuskure muna fira na taba breast dinta, shine fa tai fushi tafita tana kuka nakirata fiye da 2 taki dagawa "


Sabeer ya fashe da dariya yace "kai meyasa kai haka ko Kasa aisha ce? "


Fahad ya daga mai hannu yace "please stop joking take it seriously "


Sabeer yace "gaskiya u have made a very big mistake, kaga yanzu setayi tunanin ko ba aurenta kakeson yi ba, wai kana aikinmi ma kayi haka? "


Ya hura iskar baki yace "bana cikin hayyaci na ne, ni tunda na shaki kamshin perfume dinta ma naji ni somehow gashi taci gayu, Allah nema ya takaita don jinayi kamar nai hugging dinta "


Sabeer ya fashe da dariya yace "plsss katafi dani wataran nima in shako irin perfume dinnan inji me kaji "


Fahad ya harareshi yace "bazako kataba jinshi ba, nide kawai kabani shawara "


Sabeer yace "yanzu ka tura mata text kabata hakuri kafada mata u didn't do that intentionally "


Fahad yace "bana tunanin zata hakura na lura taurin kai ne daita amma bari natura mata "


Sabeer yace "zata hakura mana tunda tana sonka kai de ka kula kar hakan ta sake faruwa "


Yace "OK I will try "


Sabeer yace "bari na shiga ciki se munhadu anjima "


Fahad yace "OK thanks "


Sabeer ya bude mota yafita, 


Fahad ya turawa faseelat message, 


Tana ta ajiyar heart ta bude message din "cutie I'm very sorry karki daukeni da wata manufa I don't did it intentionally, I just lost control ,kiyi hakuri ki dauki wayata, ina tsananin sonki cutie I'm ready to marry you ko da gobe ne, kimin hakuri I apologize for my misbehaving amma kisani ke kika rudar dani har nayi haka ,kuma I'm regretting forgive me please "


Tana karantawa setaji dan sauki aranta unlike b4 da takejin kamar zuciyarta naci da wuta, 


Tanata bin message din ya kira ta vedio call ta dauka tana kwance, 


Yana kallon fuskarta duk hawaye yayi fuskar tausayi yace "cutie I'm sorry kidena kuka "


Tai shiru kawai tana kallonshi yace "kinmin hakurin? "


Seda akadau minutes ta jijjiga kai alamun eh, 


Ya lumshe ido ya bude yana sauke ajiyar heart yace "thank you very much "


Ta daga kai yace "talk to me mana "


Tai shiru yace "kince kin hakura kimin magana "


Tana turo baki tace "nayi hakurin shikenan"


Yace "I'm happy, wai dama cutie dina ustaziya ce bansaniba, ai da I'm about to hug you and give you a good kiss"


Tai dariya tace "just try it u will see "


Yayi dariya yace "I'm just joking, nayi miki shopping baki bari kin amsa ba, zandawo nakawo miki "


Tace "noo Nagode banaso kabarsu "


Yace "plsss mana bangaji da ganinki ba"


Tace "aa karka dawo"


Yace "to I will tomorrow "


Tace "aa bazan fito ba "


Ranshi ya baci yace "for god sake ya kkso nayi ne? Tunda nabaki hakuri ai komi yawuce kuma bawani abu zanmiki ba wani abu kawai zanbaki"


Cikin bacin rai tana ganin yama rainata tace "nace bazan fito ba ko dole ne? E ye "


Rai bace yace "saboda kawai na tabaki kike wannan abun amma ahaka kikaje kina bari wani ya kwana samanki, bakiji komi ba sedan tabawar da namiki itace tashin hankali "


ta kure shi da ido tana mamaki kuka ne yazo mata tace "kome zaka fada kafada amma bazan fito ba, ka daukeni yar iska ne? Da kake kiran dan tabawa?kuma naje nabari wani ya kwanta akaina din bama kwanciya yayi ba cinye ni yayi "


Idanun fahad sukai jawur yace "dan kinga ana sonki kike gayawa mutane magana bayan cutata da kikayi?kada kifito din nima bana bukatar ganinki useless girl "


Diff yakashe wayar ta kara rushewa da kuka saboda kalamanshi Sun mata zafi, tai ta kuka har tagaji kanta na ciwo barci ya dauketa. 


fahad huci kawai yake fiddawa yana tada mota yakecewa "what she take her self?  da zata rika medomin magana ni tsaranta ne? "


Yana tuki da hannu daya dayan kan bakinshi yana tunani yace "bazata fito ba,nitake fadawa haka it's okay duk ni najawo danake sonki sosai harma nadamu da son ganinki, yanata surutu har ya shiga gida aisha na ganin yanayinshi taja baya fuuuu ya haye Sama ya shige dakinshi ya kulle,aisha bata bishi ba don karta kai kanta karamin aikinshi ne ya wanka mata mari inta tsaya tambayarshi meke faruwa, 



Faseelat taita barci har 2 dawowar Mubarak ne ya tadata yana tambayar "yaya ina abinci na? "


Idanu kumbure tace "banyi ba ban lpya kaina ke ciwo ka bari ishak ya dawo ya dafa maku ko taliya ce "


Cikin jin tausayi yace "sannu yaya amma ni yunwa nakeji "


Tace "jeka kitchen kaduba akwai sauran tuwo se kaci"


Ya juya yafita ta tashi tayo alwala ta kabbara salla cikin salla tana kuka take rokon Allah zabi in fahad ba alheri bane agunta Allah ya cire mata sonshi,


Har dare be kira ba itama bata kirashi ba cikin dare batai barci ba kwana tai salla da addua, shima fahad sama sama yayi barci tunanin faseelat ya hanashi barcin, seda ga baya ne yake ji be kyauta ba, 



Da safe yayi ta kiranta taki dagawa yaja tsoki ya aje wayar, 


Har akai kwana ukku bata daukar kiranshi har ummi ta dawo, 


Gabadaya fahad so yake yaji muryarta saboda tafiya zeyi yanaso ya fadamata amma taki dauka wanda seda ta nuna jarumta sosai sannan take hakan don ji take kamar ta dauka inyakira amma take sharewa dan yagane itace yayiwa laifi, 


ummi taga sauyawar walwalar faseelat ta Kasa hakuri yau da safe take tambayarta "mike damunki faseelat? Naganki sukuku tunda nadawo "


Faseelat ta kakaro murmushi tace "bakomi ummi "


Ummi tace "hmmmm"ta kyaleta Amman tasan da wani abu kam, 



Karfe biyu na rana jirgin su fahad ze tashi karfe 1 saura ya tura mata message "cutie I'm sorry for everything that happened, nata kiranki Amman u ignored my calls, zan tafi Italy I will  spend only 10 days there need ur prayer and remember that I love you ,take care of yourself bye "


Tana karantawa tafara hawaye tana jiran yakirata ta dauka itama she's suffering ,amma shiru be kira ba setayi niyyar kira zuciyarta seta bata shawara karta kira tajirashi ina har 2 be kira ba koda ta yakice shawarar zuciyarta ta kirashi har Sun daga, ta aje wayar tasa kuka don takaicin wahalar da kanta da takeyi gashi har ya tafi, 


Shima yana cikin jirgi yana tunaninta, saboda he's wondering rashin kiranshi da tayi bayan karanta text nashi, 


Faseelat na kwance tana duba pictures nashi da yanzu dasu take fira ummi tashigo, tana kallonta tace "ke tashi ubanwa ye akaganku dashi shekaran jiya?"


Faseelat tai wuf ta mike tana sadda kai tana mamakin yaakai ummi tasani bayan ranar ma bakowa unguwar tasu "


Ummi tace "dake nake magana "


Faseelat na inda inda tace "saurayi nane "


Ummi ta watsa mata harara tace "saboda bakida gaskiya seda nayi tafiya sannan kika gayyaceshi gidannan ko? Wato ni bama haushin fitar nakeji ba haushina mutane zasuyita ganin baki gama idda ba kike fita gun wasu tunda ba kowa yasan abinda ke faruwa ba yanzunnan daga fitata can gidan safiya take cewa wai ranar nan ta leko ta ganki zaki shiga mota, ina amfanin haka faseelat? Shi din waye shi saurayin naki? "


Tace "sunanshi fahad ga pic dinshi nan "

Ta nunawa ummi, 


ummi ta amsa tagani tace "immm shi kinasonshi kenan? "


Faseelat ta daga kai ummi tace "Allah yasa alheri anshi nan"


tamika wa faseelat wayarta tafita, 


Bayan su fahad Sun isa Italy be kira faseelat ba itakuma ko takira bata samu, faseelat takara shiga tashin hankali kar ya shareta don istiharar da takeyi setaji tana kara sonshima fiyeda da, 


Shi ko fahad kyaleta yayi yabata lokaci amma da niyyar ranar da ya dawo zeje gidansu. 



************************


Bangaren khalil lpya lau suke zaune da jamila har yasata islamiya tana zuwa kullum, yana iya kokarinshi wurin kyautata mata itama haka kuma yana hakuri da yarintar ta, maganar harka kau yanzu Sun zama yan hannu itama har magani yake siyomata yabata tasha suji dadinsu, 

Kullum inbe shiga da leda ba inyadawo daga shago jamila zatai ta kumburi wani lokaci taita jaje har se yafita ya siyo mata wani abu, hjya ko tananan tana fama da haushi don duk jumaa se yakai jamila gidan, bayan antaso masallaci ya dawo su zauna su baje hira suna dariya, jamila ba ruwanta da wani taya hjya aiki intaga tanayi shi kuma be taba mata maganar ba, 




Yau jamila tun tsakar dare take sheka amai gabadaya ta jigata, khalil na gefe yanata mata sannu yana zubda hawaye, saboda tausayi cikin kuka jamila tace "yaya ka temakamin cikina zafi "


Yace "kiyi hakuri kinji kibari 4 dede zamu tafi asibity kita innalillahi zaki warke"



tun karfe ukku da rabi ya mike ya daura mata zani don zindir tayi daurin zanen daban ita daban yasa mata hijab suka tafi asibity da temakon makwabciyar jamilan, 


suna zuwa aka bata gado ana dubata dan tayi yaushi sosai, sukai mata tests, 


Bayan tests din sunfito likita yakira khalil office yabashi albishir matar shi na dauke da ciki wata daya, 


Khalil ya daga hannu sama cikin tsananin farin ciki yake fadin "alhamdulillah, alhamdulillah Nagode likita "


Likita yayi murmushi yace "Amma tana bukatar kulawa sosai saboda ta wahala yanzu zaku cigaba da zama anan hospital har taji sauki dan gudun matsala "


khalil yace "to mungode doctor Allah yasaka "


Ya tashi ya fita yana murna lokacin anata kiraye kirayen salla cikin zumudi yakira hjya, ganin kiranshi hjya dake zaune tana tasbihi ta dauka cikn faduwar gaba tace "lpya de khalil? "


Yana murna yace "ai ai muna asibity jamila ce ba lpya likita yace she's 1 month pregnant "



to bari muga ya hjya zataji, 

      Amma a next page 🤣




Post a Comment

0 Comments