TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

RAGON MIJI PAGE 54

 5⃣4⃣






*dedicated to lady*😘😘😘





Cikin over speed take tuki tanayi tana share hawaye ,gabadaya gani takeyi faseelat tafi ta awurin fahad yadda taga yana dokin bikinta beyi a nasuba ,har taisa gidansu tana ta goge hawaye da hannunta, tana shiga cikin harabar gidan ta bude mota tafita dasauri, tana shiga amira ta taso da gudu tai hugging dinta, tana fadin "oyoyo mommy I missed you "Aisha bata amira take ba ta janyeta ta haye step da gudu, 


Ta bude dakin mommy tashiga, tasamu sunbaje ankon su suna dubawa, tana shiga tafada kan mommy saying "mommy zuciya ta zata buga mommy "


Mommy ta rungumeta tace "zuciyarki bazata buga ba, waini Aisha se yaushe zaki fahimceni ne? "


Ta daga kai ta kalli su ramlat duk Sun zubamusu ido tace "kubamu wuri kuntasamu gaba kamar TV da Allah kufita "


Su sadiya suka kwashi kayan su suka fita ramlat nata zumbura baki gaba 


Mommy ta dawo da kallonta gun Aisha tace "se yaushe zaki gane manufata duk fa tashin hankalinki baze hana aurennan ba gwara ki nutsu ki kwantar da hankalinki yafi miki ki tsira da girmanki ,kinata wani hauka su kulsum shiri suke sosai har ta samar miki wadda zata gyaraki kafin ya dawo gunki, ga anko ta muku har da na nadiya, matar da zata miki gyaran tace kwararra ce, cewa ma tai in yadawo wurinki zeji kinfi amaryar ma, amma in kin kwantar da hankalinki kenan"



Aisha tace "mommy ya zanyi ne inata trying amma gajiya nake "


Mommy tace "seki ta hauka to shikuma ya cigaba da jibgarki a banza "


Mommy tabata rai dan har tagaji da kwatantawa Aisha, 


Aisha ta fiddo check din da yabata ta mikawa mommy, ta juya tana kallon gown gown dake zube kan cushion, 


mommy ta duba tana jindadi tace "kingani ko? Fahad na sonki sosai 15 million fa yabaki ni dake uwarshi biyar ma yabani, yanzu da kinata tashin hankali da me ze baki inba duka ba? Ki kara kwantar da hankali kici arziki yarinya "


aisha ta bata fuska tace "ni mijina nakeso ba kudi ba "


Mommy tace "sekiyi ai ana gwada miki hanya kina kaucewa, yanzu 1 million kawai zan baki Sun isheki abinda zakiyi sauran zan saving nasu a account "



Fahad yayi sallama while drivernshi na shigowa da akwatina, 


Amira taje wurin shi tana goge hawaye ya yi sama daita ya janye hannunta yace "waya taba minke? Baki murna da zuwan daddy ba ? "


Tana kara murza ido tace "mommy is crying "


ya fiddo ido waje yace "tana ina? "


ta nuna mishi sama, ya ajiye amira ya haura saman, 


Da sallama ya tura kofar, memakon ya samu tana kuka se yasameta tsaye tana gwada gown dinta, 


Ya shiga ya zauna cikin ladabi ya gaida mommy ,ta amsa fuska asake ,


Yana kallon Aisha yace "mommy lefene nakawo ki gani kisamana albarka "


Aisha ta daga ido tana kallonshi ,


mommy tace "to Allah yasa alheri bari muje mugani kusanma anyi late din kaishi "15 million whipped all her sadness 


Yace "eh gobe su alhaji zasu kaishi dayake de akwai dinkakku sosai "


Tace "Allah ya kaimu mu je muga ni "ta tashi tafita ya Kalli Aisha ya sakarmata murmushi ta meda mishi yabar dakin, 


Ya samesu a falon itada su ramlat sunata dubawa suna ta fadin "wow wow! "da alamu kayan Sun masu kyau sosai, 


Wayarshi tai ring yana dubawa yaga cutie dasauri ya fita yana daukar wayar, 


Faseelat tace "my handsome se yaushe zakazo ne?Allah zanfara kuka " cikin shagwaba, 


ya bude murfin mota ya shiga ciki sannan yace "I'm on my way to you "


tace "okay se kaxo "

Takashe kiran, 


Cikin minti da bewuce 15 ba yaisa gidansu, 


Yana kira bata tsaya dauka ba ta ja hijab ta saka tafita dasauri, 


tun acikin glass yake kallonta, se yaga kamar an sauya mai ita wannan faseelat din da yake gani tafi ta da haduwa da kome, 


Be dawo tunaninshi ba ta bude mota ta shiga ta juya tana kallonshi, 


 kamshi me dadi tuni ya cika motar, ya rumtse ido ya bude yana kara bude hanci don kamshin ya mishi dadi over, 


Sunata kallon juna yaja dogon numfashi ya sauke yace "cutie wannan kamshin fa daga ina "

Tai murmushi "daga gareka mana "


ya duko ze kai hanci kan hijab dinta ta matsa tana karewa da hannu tana dariya tace "a, aa plsss bayanzuba, kabari nan da 3 days har abinda yafi shakar kamshi duk sekayi "


ya tsaya ya fasa kai hancin yace "kuma fa hakane, kin rudani ne, kamar ba keba kinkara kyau da, da da "


Tai dariya "dame da kafada mana "


Yayi dariya yace "kema kinsansu kar nafada nayi lefi "


Tace "hmmm ,nayi missing naka sosai kamar kayi shekara nakeji "


Yace "sorry amarya, ya shirye shirye? "


Taja numfashi tace "anatayi gobe bazaka samu gani naba saboda I'm busy jibi ma I will be very busy gaskiya inaga daga yau se kuma in an kai maka ni "ta rufe fuska da tafin hannaye, 


Ya tsura mata idanu yana kallonta yace "amma wasa kike ko? Don bazan iya ba ina gari ace nayi 2 day's bansaki aido ba it will be difficult "


Ta sauke hannu tace "I'm serious gobe zanje saloon da henna nida friends dina nasan very late zan dawo, jibi muna event jumaa kuma kaima ai u r busy too"


Ya sauke numfashi yace "bazan iya bafa yadda kikayi kyau banajin ko 1day zan iya tsallakewa batare da naganki ba, batare da na ji kamshinki ba"


Tace "ya zamuyi nima dole ne tasaka, ina anty da amira? "


Yace "duk Sun kagara ayi bikinnan "


tai dariya tace "lalala,lah amira de ke son haka anty ko ai bataki afasa ba "


Ya girgizakai yace "Aisha ta sauya sosai trust me yanzu tanason aurennan "


Faseelat tace "Allah yasa "


Yace "amin yakamata na tafi Maghreb tayi se goben kenan "


Ya mika mata 200k yace "manage it"


Ta amsa tace "thank you lovely "


Ta bude motar tafita yabita da kallo kafin ta rufe ta leka tana murmushi tace "se munhadu a dinner "

Ta juya tashige gida, 


Yabita da kallo kugunta ma yakara girma maybe shima gyaran yasha lol


Yayi murmushi ya juya yabar unguwar gidan alhaji yaje sukai magana yakira alhaji babba yafada mishi zasu kawo lefe gobe, shi kuma alhajin ya fada mishi zaazo yiwa faseelat jere goben 


bayan sun gama wayan alhaji yafadawa fahad yadda sukayi da alhaji kan jere, yace badamuwa tunda akwai space se su kara mata kayan, 


Da safe aka kai lefe mutane sukafara tururuwar zuwa ganinshi, 


Yan jere kau basuma samu Aisha ba don tatafi wurin wadda zata gyarata tun safe,

Sun sha kauyanci sosai agidan set din kujerunta suka samata a dayan bedroom nata da beda su, suka sa mata katuwar plasma dinta, gadonta ko bawuri sede suka koma dashi ganin na fahad yafi kyau, 



Shima fahad is busy sunata shirye shiryen yadda dinner zata kasance da daurin aure, don manyan mutane zasu halarta ,



faseelat amarya tun 10 sukafita itada friends dinta, 50k tabiya me mata saloon, akai mata da kunshi se 3 akagama sannan akafara yiwa friends nasu,


dukda he's busy so biyu yana kiranta yana fadin ayi me kyau, 



Se after Maghreb suka dawo ta gaji sosai kanta ma Ke ciwo saboda zama da hayaniya, 


Fahad ya kirata tana lumshe ido ta dauka kanta a bude yana bin gashin kanta da kallo yace "cutie ya gajiya, naga kingaji kuma ni gani nan zuwa naga kunshin da saloon din in ga ko yayi kyau "



Ta lumshe ido tace "kayi hakuri kaina ke ciwo bazan iya fitowa ba inajin kamar ze rabe biyu ko bude ido banasonyi "


yace "sorry "cikinn nuna tausayi yace "ki daure kiyi salla kisha magani ki kwanta "


Tace "nasha magani ai "


Yace "sallar fa? "


Tana ya mutsa fuska tace "I'm off "


Gabanshi ya bada dummm ya dafe heart yace "Dan Allah kice wasa kike "


ta kalleshi tace "dagaske nake "


Yace "oh my God please help me out" 


tai dariya ganin dagaske ya rikice gashi tana son yabarta ta kalleshi tace "gobe ne fa zan gama miye na damuwa "


Ya sauke ajiyar heart kusan so biyu yace "har nadawo dede ai akwai matsala cutie idan kika shigo haka, bari na barki ki kwanta ki huta se gobe Allah yabaki lpy"


tace "amin thank you for your love "


takashe kiran ta lumshe ido sede bacci sam yaki zuwar mata yau a Karon farko tafara tunanin ya zataji idan suna sex, mutane na cewa na farko da zafi itade gani takeyi labari ne yadda takejinta haka gani takeyi dadi kawai zataji, Da wannan tunanin bacci ya dauketa, 


Washe gari tun 9 sukabar gida suka tafi gidan wata sistern abbansu can zasuyi setting aka kira masu decorating suka fara gyara wurin, 


10 baki sukafara cika gida na nesa dana kusa yan Niger karfe 2:30 suka iso, 



yan matan suka nufi gidan setting din lokacin an gama decorating wurin anata shigowa da kayan ciye ciye, se kaikawo akeyi agidan,suka ci abinci sukafara shiri, 


Seda akai laasar bayan faseelat ta yi salla ifti ta zauna ta tsara mata kwalliya takoma kamar aljana saboda kyau, ta saka purple da milk lace riga da sket, har mamaki tayi yadda fahad yasan size din ta har dana shouse da brezia, head dinta milk ta yafa dankwalin kayan 

ta saka shoes dinta milk me makeup din tace "wow amarya kinfito bari na daukeki pics "


Faseelat ta gyara tanayin different styles with smile on her face, nan fa suka fara daukar ta pics, suna kuma yi tare, 



Nan da nan gida ya cika faseelat faraa taki barin fuskarta duk inda ta gifta sekaga kyallin hakoran, 


Zuwa biyar bayan yan ciye ciye DJ yadora wuta, 


Faseelat cire mayafin tayi ta dage rawa bakin rai, friends nata da yanuwa suma sunata takawa, 



Suko su mommy suna can suma suna nasu shirin Aisha ma cikin 2days din nan takara yin fresh saboda gyara, 


Fahad da friends nashi suka kama hotel guda duk bakin da sukayi daga abroad anan suka saukesu kuma anan cikin hole din hotel din zaai dinner. 



Se 6:40 taro ya tashi saboda sallar Maghreb, se lokacin faseelat ta Tuna da wayarta, ta dauko milk pose dinta ta fiddo wayar wajen kira biyar na fahad, 


Hannu na rawa tai calling back yana dauka Kafin yace wani abu tace "kayi hakuri my handsome ina cikin taro banji ringing wayar ba ma se yanzu na Daukota"


yace "OK kina ina zanzo naganki, bazan iya hakura har gobe ba "


Tai shiru seda ta nemo abun fada tace "kayi hakuri plss har goben yanzunnan zaafara waazi kuma se 10 zaa gama "


Cikin takaici yace "yanzu shikenan bazan gankiba? "


Tace "kayi hakuri gobe fa warhaka nazama taka, ta harabada miye na damuwa da yau kadai ?"


Fahad yaja numfashi yace "Amman kisani a takure nake wlh "


Tace "kadaure plss yau kadai de "


Yace "naji shikenan se anjima ko? "


Tace "noo se gobe de don baki bazasu bari nai waya ba "


Yace "to yayi "ya kashe kiran ,bataji dadi ba amma ba yadda zatai ta koma cikin dangi aka cigaba da hidima, 


se 1:00am su faseelat suka kwanta don hira kawai suke anayi ana shewa, 


Da safe ranar daurin aure tun asuba su faseelat suka tashi, gabadaya tunda tatashi seta rikajin kamar ansaka mata kankara a heart dinta saboda dadin da takeji cikin kwanciyar hankali suke ta hidimarsu, 


Aisha ko jiya batai bacci ba da tunani ta kwana cewa gobe iwar haka fahad na tare da wata baita ba ko barawon bacci be dauketa ba da safe dangin ta suka cika gidan su nadiya yan abuja su anty kulsum yan balai su ramlat su mommy hanan sister din mommy da yayan yayarsu mommy wajen su 5 sunata hidima itako tayi sukuku ba damar tai kuka su taso mata suce batai gadonsu ba, tana kuka akan kishiya, don haka tai gum, 




karfe 1:30 faseelat tai wanka tana ta faraa, baaba ta shigo dakin taga sunata shiri ta kalli rahma tana dariya tace "rahma wannan karon banji kina batun sandar famfo ba "


Rahma ta kalli faseelat tace "baaba ainaga tazama yar hannu nagama akagare take kamar ta kai kanta can "yan dakin suka kwashe da dariya, 


Rahma tace "to wannan karon shawara zan baki, kinaji ki dage kirika wage kafa sosai ba wata kunya kuma kina gyara can din don kifi tunkiyarki armashi "suka sa dariya faseelat ta harareta tana ganin rashin kunyarta, 


Se biyu me mata makeup tazo tayi salla akaimata kwalliyar tasaka wani tsadadden Sari red color, 


Tana jujjuyawa tace "seni matar fahad "


sukayo mata ca wai ta cika zumudi tun baa daura ba, 



ango fahad yasha white shadda taji aiki yanata jindadi suka nufi masallacin da zaa daura auren, 


After salla karfe 2:40 aka daura auren fahad dawood da faseelat maaruf akan sadaki dubu 100, tunda fahad yaji andaura yakara fadada fararshi mutane sukafara bashi hannu suna mishi Allah yasa alheri, shiko tunaninshi duk ya koma kan faseelat soyake yakirata duk yau basu gaisa ba, bayan an daura akafara reception, 


Samarin gidan ne sukafara shigowa wannan ya tabbatarwa da faseelat andora, 


da gudu tana murna tayakice mayafin sarin tai hanyar toilet, 


Zainab tace "Dan Allah amarya kibi sannu karki bata makeup din kinsan yanzu zamu tafi wurin waazi "


Faseelat ta juya ta kalleta tace "ke alwala zanyi ma bakidaya se asauya wata "


Zainab ta bude baki zatai magana faseelat ta shige toilet tayo alwala tazo ta kabbara salla tana godiya ga Allah da ya nuna mata wannan rana, 



Bayan tagama aka zauna sauya mata makeup ana cikin mata makeup din fahad ya kira jin ringing din jiki na bari tace "anty fadila mikomin waya ta dasauri "


Fadila ta mika mata tana sauri ta dauka takara a kunne tanajin sanyi nabin gabban jikinta, 




Post a Comment

0 Comments