TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

RAGON MIJI PAGE 48

 4⃣8⃣





*dedicated to firdausi, F🧕🏼kinsanme? Inasonki sister😍, kina sona kinga ko dole naso ki hausawa na cewa kaso me sonka,shiyasa nakamu over, fans kutayani son firdausi don nima inasonta, tadamu Dani matuka da zanwuce 9am bana online seta kira taji ko lpya nake, I love you F🧕🏼,my masoyiya*





Mommy tarika kallonta hankali tashe takamo fuskarta tace "ban fahimta ba, ki kwantar da hankali sosai kimin bayani"


Tana sheshsheka tace "mommy yaya aure zeyi kuma kawata ce, wlh faseelat ta cuceni ban cancanci haka daga gareta ba"


Momy tafara tafi tana salati tace "nashiga ukku ni faiza, yanzu yazanyi ne? Ke dan ubanki har wata kawa kikasamu wadda bansaniba? "


Ta daga kai tana kuka tana jijjiga mommy tace "dan Allah mommy kice karyayi aurennan wlh zuciyata bugawa zatayi, nide nashiga ukkuna faseelat ta gama da rayuwata "


Mommy tace "keda harkina da guarantee kan kawa? da har zaki saki jiki daita? To yanzu gashinan de kinaso kijamin asara inyi renon banza, nasaki jiki zansamu kudi Amman kinjawomin tsiya, kafin mahaifin fahad ya rasu ya mallaka mishi gidaje da filaye da gonaki da bansan adadinsuba, su ramlat su ukku bazasu samu rabin gadonshi ba shiyasa nasamu nahadaki dashi kinga komi de nawa ne akarshe Amman kinyi sakaci zekawo wata ta ragemin lissafi "



Aisha tace "mommy kihanashi plsss wlh bazan iya sharing dinshi ba da wata "


Mommy tace "aiko sede ki hakuri sanin kanki ne nariga nasaba mishi da goyon bayanshi akan komi, yanzu innace aa to matsala zaasamu saboda yana iya bijiremin gwara na yarda din yafi "


aisha tafasa kuwwa tadora hannu saman kai mommy ta jawota tana rarrashi tace "ki kwantar da hankalinki diyata baabinda ze faru a aurennan kede kirika bin shawarata sannan kirika fadamin duk abinda ake ciki "



Aisha ta cigaba da kuka mommy nata rarrashi tace "dole ki hadiye kishinnan ki nuna mishi kinason abunnan kinga zeji dadi yakara sonki kuma ko tazo ki kauda kai ga alamuransu seki zauna lpya, inkika yi haka se yakara ganin girmanki fiyeda da "



tana kuka tace "mommy wlh bazan iyaba ni ina kishin mijina sosai bazan iya dannewa ba "



Mommy tace "to hauka zaki tayi duk kisure mishi, ?kowane namiji fa inde zaiyi aurennan seyayi doki, kuma yanada damar auren mata hudu in yaso, kita hauka yadena sonki bahaka kikesoba, kinade gani yanda nazauna da babanshi komi atafin hannuna "


Takara volume na kuka "wlh faseelat setayi danasani inta auri mijina "



Mommy tace "aure kam kamar anyi angama ne, kedai kinyi kuskure, yanda mazannan sukai karanci bare naki da kowa zeso kikabari har tasanshi, kiyi hakuri kinji nasan kome zanyi akai "



aisha takara volume itafa inba auren akace anfasa ba bazataji dadi ba,mommy nata bada baki Amman ina, 



Jiki sanyaye fahad yakoma cikin gida yana shiga amira tazo ta rungume tana kuka tana kiran mommy ya dauketa yana rarrashi ya dauko Key yasaka riga suka nufi gidan mommy tunkan hanya amira tai barci, shiko yanata sakesake, 


Yana zuwa yayi parking ya sabi amira awuya suka nufi ciki 


Yana shiga su sadee suka tashi sukai saman bene da gudu don sunajin kukan aisha su azatonsu ko jibgarta yayi ,


Bedamuba ya kwantar da amira kan kujera yana sauraron kukan aisha daga sama, 


Ya kama hanyar benen cikin sanyin jiki, dama yasan bazaa kwashe da kyau ba, 


Mommy nata bata shawarwari koji batayi tanata kuka ya shigo dakin, yana kallon fuskar mommy yaga yanayinta ya zauna gefen gadon yafara magana "dan Allah mommy kiyi hakuri bazan kara aurennan bane don inci mutuncin aisha ba, inason yarinyar ne kawai"


Mommy fuska a sake amma deep down tanajin zafi tace "rabu daita dana ai kai mijin mata hudune, ni nagoyi bayanka kaje kayi aurenka karka biyewa Aisha kishine ya rufe mata ido "


Yayi shiru cikin jin nauyi zaaiwa diyarta kishiya Amman bata damu ba ya kalli aisha ya sadda kai kasa, 


Mommy tace "gobe nidakai na zanje naiwa kawunka magana ayi komi in time akawo maka matarka "


Yayi shiru bece komiba sede yana jinjina irin son da mommy ke mishi, ya matsa ya rungumo aisha jikinshi yana cewa "kiyi hakuri Aisha, zanyi aure ne kawai amma ketadabance kinada special place in my heart, ki kwantar da hankalinki plss honey"


Mommy na zaune na kallo shiyasa aisha bata fizge ba daga rikon da yamata, 


Tana ta kuka taji hannun mommy ta tsunkuleta ta dago ta kalleta mommy tai mata alamun tai shiru da ido, 



Aisha tadan rage kukan, mommy tace "kutashi kutafi Allah yamaku albarka diyana, kiyi hakuri aisha kishi jihadin mata ne se andaure "


Ya mike tana jikinshi yace "seda safe mommy "



Mommy tace "ka kara bata hakuri plsss ka kuma hakuri daita har ta sakko "


Yace "Nagode mommy "yanajin sonta da kaunarta yaja aisha sukafita, 


Ya dauki amira suka tafi gida, 


Aisha naganin amfito takara saka kuka hannuwa biyu saman kai tanayi tana dumumuwa "ni nabani na lalace ni aisha, wayyo Allah na ancuceni an ci amanata "


yana tuki sede yajuya kai ya kalleta yana mamakinta wasu dumuwan dashi takeyi sam bata bashi haushi ba har suka karasa gida, 


Yana parking tabude ta banka cikin gida da gudu, ya girgiza kai ya dauko amira ya medata dakinta ya kulle yafito ya shiga dakin aishar, 


Ya sameta tana ta wurgar da pillows tana hauka, cikin rarrashi ya rikota cikin kwantar da murya yace "Aisha plss stop all this kar kanki yayi ciwo, faseelat ba kowa bace in zan kwatanta ta dake, inasonki sosai Aisha kuma u knew it ki yi hakuri nasan namiki laifi plss pardon me my love "


Yazo ze kaimata kiss ta kwace daga rikonshi tana kuka tace "ni zakuciwa amana? Ni faseelat zataiwa haka after all I did to her? "


Taja tsokii tai wurin mirror tabude Jakarta ta fiddo waya, yana tsaye yana kallonta ta dannawa faseelat kira hannuwa na rawa,


Wajen 1am ne faseelat tayi barci bata kashe wayar ta ba kiran aisha ya shigo, cikin magagin bacci ta lalubo wayar takara akunne, 


ganin andauka aisha tafara balai tace "marar mutunci marar amana faseelat ni zaki ciwa amana? Kirasa wanda zakiso se mijina? Dan kina diyar akuya ko azatona ke diyar arziki ce ashe bansaniba da katuwar karuwa nake tare kinci amanata kuma wlh bazan barki haka ba, kishigo cikin gidan se naci kutumar uwarki jakka yar iska "


Faseelat tuni ta wartsake tafara kuka cikin kukan take cewa"anty dan Allah kitsaya ki saurareni kiji me zance "


Aisha tace "bakida hankali da kike tunanin zan tsaya in saurareki karuwar banza karuwar wofi me bin mazan mutane... "


Kafin taida maganar fahad da kejin kalmar karuwar nan kamar ana zuba mishi wuta ya fige wayar yanajin kamar ya kai mata mari, 


Ta riko hannunshi cikin kwaratsi take cewa "kabani waya ta kabani wayata in kara zagin shegiyar can, yanzu daddyn amira ni zakaiwa kishiya? Nice fa aisharka ur honey "


yazo ze rikota tai kasan bene tana kuka ya zauna dabass kan bed ya dafe kai da hannu biyu saboda tsananin sara mishi da yake, 



Faseelat najin aisha takashe wayar tafashe da kuka me karfi, ummi da jin maganar faseelat tafito tai tsaye jikin window tanajin abinda aishar ke cewa, 


ummi ta tura dakin tashiga tace "ke dama kinsan matarshi ne? "


Faseelat ta daga kai tace "eh inazuwa gidanta "


Ummi tace "amma baki kyauta ba faseelat ai wannan cin amana ne, yakuna tare daita kuma kizo ki auremata miji baki kyautaba gaskiya "


Faseelat cikin jan numfashi tace"ni aganina kowa da yadda Allah yatsara haduwarshi da wani, nita sanadiyarta ne Allah yasa nasanshi be kamata tayimin irin wannan wulakancin ba, saboda banida niyyar cutar daita ko na aure shi, inaganin girmanta bazan manta alherin da tamin ba"



ummi dake tsaye gefen bed tace "to Allah ya kyauta, tundade kinji kingani aishikenan amma kinde fara fahimtar yaki zakijeyi kenan, ita kuma bewar allannan kisamu bayan kwana biyu kikirata kibata hakuri in Allah yasa tayi shikenan, "


faseelat ta daga kai tana kuka, ummi namata kallon tausayi saboda batasan me diyarta zata tarar ba tace "kidena kuka ki kwanta seda safe munyi maganar "


Faseelat ta koma ta kwanta amma takasa bacci tanata tunani ta yanke shawarar gobe taje tabawa aisha hakuri su dedeta, 



Duk yadda fahad yaso ya bawa Aisha hakuri taki hakura a karshe ya barta falon tanata wurge wurge ya shiga dakin amira ya kwanta ya jawota jikinshi, tunani be barshi bacci ba yana ta tunanin ita faseelat ya take ciki yanzu, 



Se asuba bayan yayi salla bacci ya daukeshi itako aisha tana gama salla ta dawo falo ta zauna har tagaji da kukan sede azabar zafin da zuciyarta ke mata ta mikar da kafa tadan kwanta itama bacci ya dauketa amma ba me dadi ba, 



Tun asubar farko faseelat tafito tana aiki ko tarage jin damuwa amma ina hankalinta yaki kwanciya tanata tunanin miake ciki yanzu, 



Ummi na dakin abba dan befita da wuri ba, 


Faseelat tai wanka tasaka doguwar rigarta orange color tasaka farin hijab ta duba wayarta karfe 9 dede ,batare da ta fadawa ummi ba tai wufff tabar gidan tanufi gidan aisha, 


Aisha cikin dan gajeren baccinta taji karar door bell tana yamutsa fuska  taje ta bude ,


Ganin faseelat tsaye tai mutuwar tsaye tanajin kamar ta shakota ta daba mata wuka kotaji daman abinda takeji, 


Ganin tayi tsaye tana kallonta faseelat ta kutsa kai ciki tana tunanin kila su dedeta, ta zukunna gaban aisha kanta Kasa tace "anty nasan ni me laifi ce agunki dan Allah kiyi hakuri bansan taina zan fara fadamiki bane tuntuni cewar muna soyayya da mijinki....."



Bata bari takara saba cikin tsawa tace "keeee dan uwarki harkin isa kifadamin kina soyayya da mijina, karuwar banza kawai wato tunda kikaganshi kika like masa ko? To ki san dasanin nidake har abada wlh nayi danasanin saninki a cikin rayuwata "


Faseelat tafara hawaye tace "anty kitsaya ki saurareni plsss "



Aisha tace "kimaza kibarmin gida wlh kafin inci ubanki "



Faseelat ta dago zatai magana aisha ta rufeta da bugu ta koina, jikake fas! tab!duf!duf ,


Jin Azaba faseelat tafara ihu, cikin barci yaji ihu, ya farka zaune yakasa kunne inyaji da kyau muryar faseelat ce ,yace "oh my God "ya fita dasauri, 


Tunkan bene ya leko yaga yadda aisha tahaye faseelat tana jibga ya kwatsa tsawa "keeeee aisha"


Koji batayi tana ta jibgar faseelat cikin sauri ya sauko daga kan benen ya janye aisha ya dauketa da mari a duka kumatunta, jikake tasss! Tassss, 


Aisha ta dafe duka kumatun da hannu biyu tana kallonshi dan saura kirisss ta kife awurin,


Cikin sauri ya tada faseelat tana ta kuka ya rungumota jikinshi yana......... 




*inajin dadin comments naku jiya anyi ruwan comments godiya lodi lodi, nima inasonku masoyana*💋💋




Post a Comment

0 Comments