TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

RAGON MIJI PAGE 50

 5⃣0⃣





*🎶🎶ashe haka soyake shiga zuciya yake,yasamu wurin fake cireshi wuya yake 🎻🎻🎸araina kena rike ,kimance komi kirike, koina kin mallake, nakine amshi kirike🎼this page is for you lady my habibaty Nagode da alherin da kikamin Allah yakara budi, thanks once again lady*




*Dedicated to lady*😘😘





Ummi nagama gasa mata taja tsoki tace "shasha kawai seki tashi ki wankan abinda kukai kizo ki amshi magani "


Tafita tabar mata toilet din, faseelat ta rufe ido da hannu daya tana kuka, ranta na mugun baci idan ummi taimata mummunan zato ,bare na yau da har abba seda yaji, ta share hawayenta tafito tai wanka saboda ruwan da ummi tai mata gashi sunyi duhu dan haka tasaka soso da sabulu ta wanke jikinta ta fito ta koma daki tasamu tasaka vest ta koma ta kwanta, 


Wajen 2:00 ummi ta dawo da abinci da paracetamol and ibuprofen tana kallon ta tace "kitashi kisha magani seki koma ki kwantan"


Faseelat ta tashi zaune tana yamutsa fuska tai spoons biyu na jelop din pasta din ta dauki maganin tasha, duk ummi na tsaye na kallonta ta koma ta kwanta, 


Ummi tadade tsaye tana kallonta sannan ta dauki plate din tafita, 


Karfe 3:00 abba ya dawo, bayan ummi takawomishi abinci yaci yake bata labarin yadda sukayi da baba babba, 


Ummi tace "ai gwara dakamishi maganar dan faseelat tayi nisa inajin yadda takeson yaran nan koni bataso haka "


Ana haka akaiwa abba sallama ya tashi ya fita, ganin sabuwar fuska dabe taba ganiba sukai musabaha da alhaji rabiu, 


Sannan alhaji rabiu yace "nasan baka sanniba nine kanin mahaifin fahad yaron dake neman yar wajenka, nazo ne neman izini muzo neman aurenta "


abba yace"to alhamdulillah sede banine madaurin aurenta ba, don haka zan baka number din yayana shi medaura mata auren se kuyi magana dashi"


Alhaji rabiu yace "to masha Allahu badamuwa "


abba yabashi number din baba babba tareda yimishi kwatancen gidanshi, 


Alhaji rabiu gidan baba babba yawuce sukai kicibus kofar gida dede shi kuma ze fita, bayan Sun gaisa yafadi abinda yakawoshi, baba babba yace "bamatsala zakuiya turowa amma zuwa gobe don zan danyi tafiya zuwa niger,"


Alhaji rabiu yace "alhamdulillah haka ma yayi insha Allah munanan zuwa goben"


Baba babba yace,"Allah yakaimu lpya "


Alhaji rabiu yace "da karfe nawa zamuzo?"


baba babba yace "zuwa de 10 to above"


Alhaji rabiu yayi godiya ya tafi, 


Fahad bayan ya bar wurin alhaji yawuce gida ya kimtsa yafita aiki, zuwa 3 ya dawo tunda ya shigo gidan yaji gidan ba dadi, yanata kallon falon da yanzu amira nanan na wasa, tunanin Aisha yafado mai da yanzu tazo ta tarbeshi ,ya samu kujera ya zauna ya fiddo waya ya kira Aisha tana ta ringing taki dagawa, har ta tsinke ya ja tsoki besan haka aisharshi take ba sedaga jiya zuwa yau, 


Ya tashi ya haye sama ya watsa ruwa yayi sallah, ya shiga kitchen ya hada ruwan tea ya dawo dashi ahannu da snack ya zauna yana ci yana latsa waya ya shiga gallery ya latso pics din faseelat yana binsu one by one yana kallo besan meyasa ba ko kallon pic dinta kadai yayi seyaji yana samun natsuwa sosai, 


Aje tea din yayi dukda bawani abu yaci ba rabonshi ma da abinci tunjiya amma yakasa shan tea din saboda rashin kwanciyar hankali, 

Yayi dialing number faseelat yanabin screen din da kallo yaji tana kashe abun yabashi mamaki jin wayarta kashe ya tashi yakoma bedroom yana aiki da system dinshi yaji yanajin bacci ya kwanta ,yana baccinshi har 4:30 sannan yatashi yana duba agogo yayi sauri ya tashi ya shiga shaf shaf yayo alwala ya dawo ya kabbara salla ,



 aisha ko tasha kuka har tagaji, mommy de batako leko taba tunda batajin magana ta shareta,


ramlat tashigo dakin tazauna gefen Aisha tace "anty maganar da mommy ke fadamiki fa gaskiya ne, yanzu an waye kishi da kissa ake baa fitowa aita haukannan nide kinmun dede da kika jibgi shegiya Amman tunda kin rage zafi seki hakura kinga har mommy tayi fushi tafita har karki ,kiyi yadda tace kurum tun kafin asamu matsala dan kinga fayanzu har marinki yayi akanta nangaba Allah abinda yafi mari ze miki, kirika daurewa de hakanan"



Aisha tana kallonta tace "yanzunnan yaya har seya iya kwana da wata baniba ?"


Ramlat tace "namiji nefa, cabb bare yaya da dama can beda wata kunya sosai, kinagani agabanmu se ya rungumoki ko yamiki kiss fa ,aikede ai shaani kawai "


Ramlat tacigaba da dorawa Aisha darasi, tana budurwa amma ba makircin da bata iyaba don tafi aisha wayau, 




Har marece fahad nata trying number faseelat amma bata shiga duk se hankalinshi ya tashi ya rasa me zeyi, 


Itakuma faseelat jikinta ne yayi tsanani dan amai tarika yi ma daga baya, ummi duk ta rude ta dawo jinyarta, 


Da daddare fahad yaje gidan alhaji suka zauna alhaji yafada mishi yadda sukayi yace "yanzu de in Allah yakaimu gobe zamuje nida su alhaji yunus "


Fahad yace "Nagode daddy ga kudin nama cirosu daga banki one million kudin neman auren se 200,0000 taka "


Alhaji yace "to godiya nake insha Allah goben zan nemeka idan mundawo "



fahad yatashi yafita cikin farin ciki, koda yakoma gida yata kiran faseelat amma akashe itako wayar har ta mutu saboda rashin caji da bata saka ba,, ya hakura ya dena kiran yanajin ba dadi dan yariga ya saba da jin muryarta, ya danyi aiki a computer shi ya kwanta da niyyar gobe zeje gidansu faseelat tunda wuri ko hankalinshi ya kwanta, yadade da kwanciya amma yakasa barci, gabadaya desire ta hanashi baccin he's missing Aisha yanata juye juye har kusan 2 nadare yatashi ya jawo laptop dinshi ya cigaba da aiki saboda ta dauke mai hankali, 



Wan safe da karfe 10:30 su alhaji rabiu su ukku sukaje nemawa fahad auren faseelat, baba babba ya karramasu sosai sannan suka mika mishi kudin a leda 1 million cifff, batare da alhaji yasan adadin kudinba yace "faseelat deba budurwa bace don haka base kunkara ba kanku wahala ba munbashi ita idan kun shirya nan da 1 month ma seayi biki "


Alhaji rabiu fuska a sake yace "shi yaron yace bayason amata komi zeyi duk wata hidima, inde babu damuwa alhaji munason a ragoshi ya koma 3wks "



Alhaji babba yace "ba matsala mu ashirye muke Allah yakaimu nanda 3wks din Amman muma iyaye zamuyi mata abunda yakamata ace munyi"


Su alhaji sukayi godiya aka rufe taro da addua aka tashi bayan ansaka rana nanda 3 wks,



fahad ko se 10 yatashi ya kimtsa cikin sauri ya kama hanyar gidansu faseelat yana kan hanya ne alhaji rabiu ya kirashi danhaka ya juyar da motar zuwa gidan kawunnashi, 


Yana zuwa yakirashi alhajin ya fito a harabar gidanshi, suna kan resting chair alhaji yace "to alhsmdulillah yanzu de faseelat ta zama taka, munje munyi magana da iyayenta sunbaka ita kuma sunsaka ranar aurenku nanda 3wks"


Fahad ya rumtse ido yanajin mugun dadi na ratsa dukkan gabar jikinshi, ya bude ido ya Saki kayataccen murmushinda besan yayi ba ya kamo hannun alhaji yace "Nagode daddy I'm very proud of you ,naji dadin wannan labari sosai da sosai "


Ya saki hannunshi ya fara shafar sumar kanshi da ya saba, 


alhaji yace "badamuwa danbaba, yanzu seku fara shiryeshirye kafin lokacin "


fahad yayi zumbur ya tashi tsaye yanzu ba abunda yake son gani sama da faseelat yafada mata wannan gud news din, ya kalli alhaji yace "daddy zantafi semunyi waya thanks you so much"


alhaji yayi murmushi ganin irin farin cikin da fahad ke ciki yace "welcome son "


fahad ya juya ya fita daga gidan ya shiga mota ya kama hanyar zuwa gidansu faseelat cikin farin ciki. 



Yana zuwa ya bude mota ya fito don samun yaronda ze tura yakira mishi ita don haryau wayarta kashe take, 


Sega Mubarak yafito daga gidan fahad yayi sauri ya rufe motar ya karasa kofar gidan yacewa Mubarak yakira masa faseelat, 


Mubarak yace "yaya batajin dadi tunjiya bata lpy "


Fahad ya zaro ido ya dafe kai yasan bakomi yaja ba se dukan da Aisha ta mata, ya dafa Mubarak yace "tana gidan ne? "


Mubarak yace "eh dazun suka dawo daga asibity "



Fahad yace "to kashiga kacewa ummi fahad zeshigo gaidata kaji? "


Mubarak ya gyada kai ya juya cikin gidan, fahad ya fitarda iska daga baki ya cusa hannaye cikin aljihun wandon, 


Mubarak yashiga ummi na cikn aikinta na yau da kullum Mubarak yafada mata abinda fahad yace ,ummi tace "to jira karka fita bari na saka hijab na kimtsa waccan tukunna, aibawani gaidani dayazoyi faseelat de yazo gani yazo duba barnar da yayi "


Ta juya ta shiga daki ta sako hijab dinta ta shiga dakin faseelat tana barci ko hijab da suka dawo daga hospital bata cireba ta kwanta, 


ummi tafita tacewa Mubarak "jekace ya shigo "


Mubarak yafita har lokacin fahad na tsaye yace mishi ya shigo, fahad ya taka zuwa cikin gidan ,


Da sallama ya shiga ummi tafito ta amsa ta masa iso zuwa dakinta, tana kara kallon kyawunshi ya shiga ya zauna akasa ya tankwashe kafa daya dayar kuma ya tsaidata cikin sanyin murya yace "ina wuni"tareda sunkuyar da kai, 


Ummi tace"lpya lau ya iyali? "


Yace "alhamdulilah ya me jiki? "


ummi tace "dasauki "


Yace "Allah yakara sawwakewa, ayi hakuri ummi haukansu ne na mata bana kusa lokacin da abun yafaru "


Ummi na kallon hannunshi dake nannade da bandage tace "ai bakomi Allah ya kyauta gaba "


Cikin jin nauyi yace "zaniya ganin faseelat din? "


Ummi tace "eh bismillah "tatashi ta fita, 

ya tashi yabi bayanta, 


Ummi ta shiga dakin faseelat ta dan bubbuga gefen gadon faseelat ta bude idanunta da sukai ja ta kalli ummi, ummi tace "ga fahad nan ze shigo ku gaisa "


Ummi na rufe baki fahad ya shigo dakin faseelat tafara kallonshi daga Kasa zuwa sama tana akwancen yana sanye da white shirt da golden trouser, 


shima kallonta yake tunda ya shigo room din fuskarta kadai yake iya kallo duk tayi ja saboda kuka da yar ramar datayi daga jiya zuwa yau, 


Ummi na gefe, fahad ya tsaya daga nesa yana kallon faseelat baruwanshi da ummi da takafa ta tsare yace "cutie ya jiki? "


Tadan Saki murmushi kawai yace "I'm sorry "


ta lumshe ido tabude alamun OK, 


ganin ga ummi tsaye yace "ina wayarki I have call you several times "


murya dishe tace "banida chargy "


yace "alright Allah yabaki lpya "


 yacewa ummi "Allah yabata lpy "



Ummi tace "amin "



Ya juya yafita,yana fita ummi tace "Ashe de faseelat bakida hankali wani lokaci idan kikai abu se inga kamar kece yar farin, inba rashin wayau ba ki kwasa ki tafi gidan ta dankina sakarai? To Allah yatemakeki dan wlh inda nice ko fuskarki bazata ganu ba "


Faseelat lumshe ido kawai tayi, kashi biyar na ciwonta ya tafi taga habibinta da kuma gaskiyar da ummi ta gano, 



fahad nashiga mota ya dauko power ban ya ba Mubarak yakaiwa faseelat tareda bashi 2000, Mubarak ya amsa ya shiga cikin gidan, 


Yashiga dakin faseelat ummi nata surutu ya mikawa faseelat power ban din, Ta mike zaune dasauri kamar ba Marar lpy ba ta dauko wayarta ta jona chargy, ummi tace "hmmmm Allah ya kyauta "tatashi tabar dakin saboda takaici, 


Faseelat takoma ta kwanta bayan ta saka chargyn danba warkewa simul tayi ba, 


Fahad bebar kofar gidanba ya dauki wayarshi yakira daya daga cikin yaran dake aiki a plaza dinshi yace mishi yana bukatar engine good quality kuma ai masa full tank, da 2 cartoons of peak milk ,2 cartoons of maltina kwalin holandia ya fadawa yaron address din gidnsu faseelat,




 sannan ya tada mota yana tuki Ahankali yana ta tunanin faseelat ya kama hanyar gidan mommy.



Post a Comment

0 Comments