TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

RAGON MIJI PAGE 67

6⃣7⃣





*Banga dalilin da zesa mutum ya rika karanta abunda yasan baya koyarda komi se iskanci ba , idan har ragon miji iskanci yake  koyarda ke kidena karantawa ko dole ne se kin karanta,tunda akwai iskanci aciki Adena bi plss ,bazan fasa rubuta fahad ya tsotsi faseelat ba ahakan naga damar rubuta kayana,kuma inke baki fahimtar komi wasu na fahimta kuma kar adena zagi na acigaba baya karamin komi se lpy*💁🏼




Ya saki ajiyar zuciya yanajin natsuwarshi ta dawo jikinshi na dan lokaci tana jikinshi tace "I miss you badly Hero "


Yawa hair dinta kisss yace "me too honey "


Yayi breaking hug din ya sungumeta zuwa sama tai kwance akan jikinshi, 



Mansura tabisu da kallo takoma ta zauna tace "muma de Allah ya gwadamana namu ahaka 🤣"


Asaman bed ya shimfidar da ita ya kwanta gefenta fuskokin su suna kallon  juna sunata sakin murmushi fahad ya dora hannu saman hancinta da yakara fitowa saboda rama yace "yace u have change "


Ta lumshe ido ta fadada murmushinta tace "like you duk ka rame why? "


Yayi murmushi yace"ya kk tunanin zan samu kwanciyar hankali bana tare dake, dakyar nake bacci saboda tunanin ki "


Tai murmushi ya tashi zaune ya jawota jikinshi ya zura hannu a rigarta ya rika shafa mararta to above yana lumshe ido yace "thanks u I'm very happy da cikinnan plss kihaifamin cuties twins masu kamarki "


Tai dariya tace "noo zande haifama baby boy kasamu friend"


Yayi dariya" but kinsan de kinmana alkawari zaki haifamana triplet nida princess seki haifo mana 2 girls one boy "


Tace "ni banyi alkawari ba"


Yarika mata wani kallo 

Ta zare hannnunshi tafara kokarin cire masa riga tanacewa "nasan kagaji sosai muje nama wanka kaci abinci kayi salla ka kwanta kahuta "



Ya harareta "ni nacemiki nagaji? To nivbawata gajiya jikina"


Harta ida cire masa rigar ya jawota jikinshi yana shakar kamshin jikinta yace "bari nafara gaisawa da baby na sannan muji dadin wankan"


Seda gabanta yafadi tai yake tace "ban lpya wlh dauriya kawai nake "



Yana dariya yace "toki kara daurewa dan a matse nake "ya kamo face dinta ze cafke mata baki, 


Tana zare ido tai sauri tace "Dan Allah kamin a sannu ba sosai ba ni I'm scared "


Ya saki fuskar ta yana kallonta da mamaki yace "kinajin tsoro nane is this your first night? kibarni in samu natsuwa plssss I miss your sweet HQ"


Ta hadiye miyau me daci ta daga mai kai ya kara rike fuskarta yace "don't be scared I will do it gently u just cooperate"

Yakai baki kannata ya fara kissing dinta passionately, itama she miss him so much takama mai, 


Yana cikin sucking din HQ dinta ta fara zuciyarta ta rika tashi tafara kakarin amai ta toshe bakinta da hannu, 


Gabadaya ya rikice idanunshi Sun kankance saboda bukata ya dago yana kallonta taja gefe ta ruga toilet ta fara kwara amai ,


Yaja tsoki ya kwanta agadon yabi toilet din da harara,yanajin haushi kamar me, 


Har ta gama aman tafito dafe da cikinta ta kwanta kanshi tana lumshe ido tana meda numfashi , 



shida ze mata sannu se yafara fada "waike wace irin yar kauye ce daga yin aure ko wata baaiba zaki samu ciki ,sekace wadda bata waye ba kinzo kin fara amaye amayan banza da wofi duka yaushe akai auren one month amma wai kinada ciki one month don kawai ki takura ni ina laifin kibari senan da 2 month amma yanzu duka duka me na kwasa "



Ta sauka akanshi cikin kasalalliyar murya tace "hero cikin naka dana dauka shine kauyanci? kaida zakaiwa Allah godiya, nikam ina cikin farin ciki marar misaltuwa da wannan kyautar da Allah yamin kuma bandamu da wuyar da nake ciki ba koda zan mutu ne inde zan haihu to nagode ma Allah "



Yaja tsoki "u r not serious ne da kike fadin mutuwa saboda ciki ,kuma kigama amaye amayen ki kizo kibani hakkina "


Tai dariyar karfin hali ta matsa can gefe ta kwanta ta juya mai baya tace "sede kai hakuri bazan iya ba Allah nagani kuma baze kama ni da laifi ba, nasan kaima kanason cikinnan amma kake batarai saboda yau kadai ai ba  haka zaaita tafiya kullum ba, da ka sameni a kwance mana mana fa ahakan zakayi? "


cikeda takaici yaga samu yaga rashi yace "is better na sameki a kwance seda kika gama rikitani sannan zaki fara kakarin banza, thank God ba ke kadai na mallaka ba I have my Aisha zata kashemin kishirwata"


Ya tashi yana niyyar sauka ta riko shi se hawaye sharr tace "haba hero yanzu seka tafi kabarni bayan kasan nadade ban saka a ido ba ita kuwa kullum kuna tare, wlh dan bani lpy ne nace maka haka amma kasan kullum cikin shiri nake"


Zuciyarshi tai sanyi ya koma ya zauna duk abinnan dukansu they are naked ta jawo hannunshi ta dora saman boob's dinta tace "kazo kayi duk yadda kakeso amma kasani cikina shine buri na a yanzu shi nake fatan gani a rayuwa ta plss karka bari yasamu matsala "


Tabashi tausayi ya zare hannunshi yace "I will not going to harm my baby na hakura le me go and take my birth "


Ta girgizakai tace "kazo kayi kawai nasan ba iya hakura zakaiba kuma ni ban yarda kaje wurin anty ba "


Yace "nace na hakura kuma ni bazanje wurinta ba shikenan? "


Ta kura mai ido ta riga tasan shi sosai Tai dariya tace "Allah? Ko se dare yayi kadan zagaya can "ta kashemai ido daya, 


Ya kyalkyace da dariya yajawota jikinshi yace "ashe kinsani"ya dora baki kan breast dinta yana tsotsa with fashion, 



Se kusan karfe 4 saura suka kwanta, ana kiran sallar farko ya tashi yayo brush da alwala yayi rakaatul fajr ya tafi masjid tana kwance idonta biyu sede kallonshi da take tayi tanajin sonshi nata circulating a jininta tunda ta fada mishi falalar zuwa masallaci be sake salla gida ba, 


Aman da ya taho mata ne yasa ta tashi ba shiri ta nufi toilet bakomai ma cikinta se ruwa ta samu tai wanka tafito ta zauna yin salla azaune don juwa take gani, 


Bayan tagama ta kwanta kan daddumar ta kudundune tanajin sanyi, 


Da yadawo daga masjid dakin Aisha yafara shiga tagama salla idanunta jawur ta dago ta kalleshi, 


Ya jawota jikinshi yana tambayarta "Aisha lpy kike? "


Tace "lpy lau inaga idanuwa nane zasuyi ciwo tun jiya dana kwanta suke kaikayi"



yazuba mata ido ta sadda kai kasa yace "da kinyi karya nake ganewa saboda baki sabayi ba haba Aisha se yaushe zaki sawa zuciyarki hakuri? "


Tace "but kafin muzo nace kadena mata komai agabana nima haka kadena min "


Ya rumtse ido ya bude yace "kiyi hakuri mantawa nai amma nadena "


"plss kidena damuwa kar ciwon zuciya ya kamaki "


Ta daga mishi kai ya mata kisss a forehead ya tashi ya fita, 


Dakin amira yawuce ya sameta ita da Mansura suna karatu dan harsun saba, 


Yarika jifan Mansura da wani kaskantaccen kallo ta sadda kai kasa gabanta na faduwa, 


Bece mata komi ba amira taje ta rungumeshi tana fadin "oyoyo daddyna "


ya daga ta sama zuwa cikinshi yana kallon fuskarta yace "how are you doing? "


tace "great "


Yace "okay nayo miki tsaraba after breakfast zan baki "


Amira tace "kayowa triplet suma? "


Yayi dariya yace "tasu ta musamman ce nariga nabawa antinsu"


Ta mai kisss tace "I love you daddy "ya sauketa kasa ya kalli Mansura yace "oya get her ready to school"


Ya juya ya fita ya shiga dakin shi ya dauko laptop dinshi ya nufi dakin faseelat, 


A kwance ya sameta ta dukunkune yaje ya zukunna gabanta ya kai hannu ya taba goshinta yaji zafi, ya rumtse ido yanajin badadi ya dauketa ya meda kan bed ya rufa mata blanket ya fita ba jimawa ya dawo da tea a hannu ya hau gadon ya jingina ta jikinshi yakanga mata cup din abaki, 


Idanunuta nata lumlumshewa ta bude baki tadansha ko rabi batai ba ta daga hannu dakyar ta matsar da cup din tanajin tashin zuciya, ya kuma medawa a bakinta yace "kidan kara sha nabaki drugs dinki kokin samu dan sauk......"


Bema ida maganar ba se amai duk tabata jikinta da nashi har tea din ya kare taita yunkuri sannan ta tsaya, takoma takwanta jikinshi 


Shi ko duk tausayin ta ya cika shi yace "sannu faseelat "



tai shiru ya dora hannu kan cikinta yace "baby dan Allah adan raga mana hakanan mommy nashan wuya kuma katakura daddy"


Ta danyi murmushi ya sauke ta ya zare rigar jikinshi ya dauketa ya kaita toilet sukai wanka tare ya dawo ya janye bed shit din ya sauya wani ya daukota yazo ya kwantar daita, 


Ya dauko shirt da single sket ya samata ya bata drugs tasha tana kwance a kan cinyarshi shi kuma yana aiki a system dandanan ya mata sannu, 


Basu sani ba lokaci yaja sosai, 


Da Aisha dasu amira sukai breakfast Mansura ta kaita school daga can tawuce gida, 


Aisha ta koma daki batada mafita dole se tafadawa mommy komai tai wanka ta kimtsa wajen 9:30 tafito takira wayar fahad don tafada mishi amma be dauka ba saboda wayar na vibrate, hakan yasa ta nufi dakin faseelat tafara knocking, 


Fahad yabata izini ta shiga kallo daya taiwa kan bed din ta dauke ido  faseelat a cinyarshi ya rungumeta se faman shafa gashin kanta yake, 


Bakinta na kyarma tace "ya me jiki? dama gidan mommy zanje to nakira ka baka dauka ba "


Yace "alright Allah yakiyaye inanan shigowa anjima"


Ta juya dasauri tafita yabi bayanta da kallo se yanzu ya lura da muguwar ramar da tayi, ya girgiza kai, 



Aisha na driving tana goge hawaye har ta isa gida duk sister's nata na school mommy na zaune tana kallon wani series film game of love Aisha ta shigo, 


Mommy tajuya ta bude baki tana kallonta har tazo ta zauna kusa da mommy ,


Mommy ta jawota tana kara duba jikinta tace "Aisha rashin lpy kikayi?duk kika bi kika koma kashi "


Ta girgiza kai mommy tace "to meyafaru keda kuka bar kasa keda miji ai kamata yayi ki dawo bulbul dake "


Aisha ta share hawaye kanta kasa tace "mommy wai faseelat ciki ne daita "



Gaban mommy ya fadi tace "ciki a yanzu? "


Aisha ta daga kai tace "tunda mukaje kullum suna like awaya inbe kira ba ita take kira jiya bata lpy akace tana da ciki shine ya kwasomu muka dawo, mommy dan Allah nima so nake nasamu ciki kwanan nan "


mommy tai shiru ranta ya mugun baci tace "ai zezo ya sameni wannan karan kam bazanyi shiru ba, kuma ke da kike maganar ciki kikasan ko ma kinadashi kema dan wannan ramar tayi yawa "



Aisha ta girgiza kai tana kuka tace "babu mommy dama zuwa nai akasamin implant ta 5years amma naje anciremin inajin tsoro kar naki haihuwa nankusa"



mommy taja dogon tsoki tanajin kamar ta daketa tace "amma de Aisha anyi shasha wato duk abinnan planing kike wawa kawai Wadda batasan ciwan kanta ba ai haihuwa abarso ce keda ba rarratsa kike ba bakomi ba to yanzu de gashinan zaa nuna maki yadda ake haihuwa seki hankali inkinso marar hankali ki tashi kibarmin gida kafin ranki ya baci "taida maganar a tsawace, 


Aisha na kuka ta tashi  tsaye da nufin tafiya tai baya luuuu zata fadi mommy ta tarota tana innalillahi, 


hannun Aisha dafe da zuciyarta tace "mommy kibani ruwan sanyi zuciya ta zata fashe "



Mommy ta kwantar daita duwawu na rawa dasauri ta dauko ruwa tazo tafara bawa Aisha hankalinta tashe,sede aishar takasa shan ruwan duk sanyinsu sunki wucewa a zuciyar, 


Mommy ta janye ruwan jikinta na rawa tace "Aisha kice har hawan jini da ciwon zuciya yagama kamaki, wai Aisha so hauka ne? "


Aisha nata kuka tace "inasonshi mommy shine rayuwa ta "


Tafara tari mommy ta tashi ta dauko gyale ta tallabo Aisha suka shiga mota suka nufi hospital, acikin mota tace "bazan kira shegiyar faith dinnan ba ta kwashe komi tafadawa fahad gwara na kaiki different wuri"


Abakin wata private hospital suka tsaya suka shiga bayn Sun samu ganin likita sukamai bayani ya aunata bp dinta ya hau sosai ga ciwon zuciyarta da take bugawa da karfi ya rubuta musu drugs ya zauna yanabawa mommy advice akan adena bata mata rai akiyaye duk abinda ze bata mata rai sannan ta kula da drugs dinta kuma she's normal kodawane lokaci tana iya daukar ciki,  sannan suka fita bayan aishar tasha wasu drugs din, 



Daga asibitin gidan anty salma suka wuce suka shiga me aikin salma tahau bene tafada mata ta sauko tana faraa tace "I'm very surprise yaushe rabonki da nan anty"


Ganin fuskokinsu duk a dakune yasa tabata fuska itama taje takamo hannun Aisha dake kwance ta jinjina ta Kalli mommy tace "anty mi kefaruwa haka? "



Mommy taja tsoki ta kwashe komi tafada mata a karshe tace "kawota nai kibata shawara tunda ni batajin tawa ta watsar da wata soyayya da kishin banza ta zauna lpy, tade riga taiwa kanta tsiya seta jira ganin ikon Allah "


Anty salma tace "yo anty haka zaku zuba ido tazo tafara haihuwa agidan ai dole a dauki mataki wurin boka kawai zamu a zubar da cikin araba su "



mommy tace "a, a salma ni ban taba zuwa wurin boka ba bakuma zanfara ba ban kuma yadda taje ba kide bata shawara kawai "



salma tace "toni iyakar shawarar da zanbada kenan daganan kuma sede nabata hakuri kawai "



Mommy tace "Allah yasa taji tashi mutafi ai duk ke kikaja"


Salma tayo masu rakiya suka tafi takoma tana fada "wai anty bazataje wurin boka ba tasan kishiyar tata ko dacan ta dogara saboda abun yayi yawa ai munanan de watarana kundawo hanya "



Su mommy gida suka wuce tanata rarrashin Aisha abinci ma abaki tabata tana ta kwantar mata da hankali, 




Se 1 dawani abu faseelat taji sauki sukayo wanka suka fito tana kokarin shiga kitchen ya hanata yayi waya aka kawomasu abinci daga motel suka zauna sukai feeding juna tana gama cin abincin tasaka cingum baki, 



Daga masallaci ya wuce gidan umma yayi saa har daddynsu nanan bayan sun gaisa  umma ta tambayeshi jikin faseelat yafada mata dasauki kanshi kasa yace "daddy dama akwai wata magana da nakeso muyi "


Daddy Yace "go ahead,"


Fahad yace "akan Mansura da safiyya ne, dan Allah daddy ayi hakuri da school dinsu amusu aure Sun ida karatun agidan aurensu,"


Daddy yace "lpy kake maganar aure kosu suka fada ne naga de yaranan ko fira basayi"


Yace "daddy Mansura aure takeso kuma wani friend dina ya nunamin yanasonta kuma I know him sosai idan Sun dedeta se akara bincike akai "


Umma tace "wlh batun yanzu na fahimci tanason aure ba nadeyi shiru ne Allah yasa bawani abu tayi ba? "



Fahad yace "batai komi ba umma "



Daddy yace "dukda a tsarina ba wacce zanwa aure seta gama school amma saboda kayi magana zan amince da auren sede duk wadanda zasu aura se Sun amince zasu barsu su wuce school "


Fahad yace "nagode daddy insha Allah ba matsala "


Sannan ya masu sallama ya fita yana niyyar fita Lady ta shigo ta dukar dakai ganin yanata mata banzan kallo, 


Ya dauke ido yace "kowane lokaci zakiga kira da bakuwar number bata kasar nan ba ki mutunta shi ki soshi he's my friend"


Mansura ta daga kai tawuce dasauri fahad yaja tsoki yace "nonsense"


Akan hanya ya kira Hussein yafada mashi yayi ta murna yana fadin "alhamdulillah"


fahad ya tura mishi number lady, 



gidan mommy ya wuce da tsarabarta dana sisters  yana shiga yasamesu zaune a kasan carpet kan Aisha kan kafafun mommy sisters nashi zaune akujeru sadiya na shan yoghurt while ramlat na chart ga drugs nan gefen mommy, 


Jikinshi sanyaye yaje ya zauna ganin banzan kallon da mommy ke masa da be saba gani ba 


Yace "Mommy ina wuni "


Mommy tadaga mai hannu tace "karka wani gaidani marar mutunci ,saboda kayi aure shikenan seka nemi kashemin diya a

da tarin kayan takaicinka, ka dauketa kuntafi uwa duniya amma seda ciwon zuciya da hawan jini zata dawo? To kayi dede ka rubuta mata takardarta ka saketa ta huta "


Fahad ya zaro ido ya shido kasa, 


Aisha tai wuff zata tashi jin mommy tace Saki mommy ta danne ta, tai shiru zuciyarta takara gudu,


Fahad ya sadda kai ya rasa me zece mommy takalli ramlat tace "ke tashi kije ki daukomin tests da akamata suna jakana "



Ramlat ta dauko ta dawo tabawa mommy, mommy tawtsa su jikinshi tace "read them kakuma saketa ai inason diyata bawai banasonta bane na dauka nabata a tunanina kowani kaga zesata awani hali bazaka bari ba se gashi kaine ka  jefata ciki "


Fahad ya dauki papers din ya karanta ya kalli aisha ya lumshe ido yabude, shide ganin kokarin kanshi yake he's trying his best, 


Da ladabi yace "mommy Dan Allah kiyi hakuri wlh ina kaucewa bacin ran Aisha saboda inasonta sosai kishi ne ke damunta bansan bata lpy ba dani ne zan kula daita "


Mommy tace "ba abinda na tambayeka kenan ba ban bukatar bada hakurin ka just divorced her "


Fahad ya dafe goshi zuciyar shi na zafi yace "mommy Dan Allah kimin hakuri zan gyara zankara bata kulawa fiyeda da wlh bazan iya rabuwa daita ba inasonta sosai kuma itama tana sona "


Su ramlat se tunzurar baki sukeyi sunajin takaicn shi ze halaka masu yaruwa, 



Mommy tace "ko kanason ta seka saketa ita kuma ta mutu da sonka dan kagane tana sonka shiyasa kake kuntata mata "


Yace "wlh aa mommy kiyi hakuri plsss "


Taja tsoki" ka saketa yanzunnan nace "


Ya dago kai arazane idanunshi Sun cika da hawaye yace "I can't bazan iya ba wlh I love my wife "


Ya matsa kusa daita yana hawaye " dan Allah mommy kibarmu tare we love each other bazan kara sakaci ba "


Cikin zuciyar mommy tace yayi dede ,


ta kalleshi tace "this is the last time da zanga Aisha awannan halin na barmaka ita, ka kiyaye inason kayata amma kullum ina bayanka yanzu bazan bari bakin ciki ya kashe ta ba kanajina ai"


Yadaga kai yace "thank you mommy "


Se yanzu Aisha taji dede batasan lokacin da taja doguwar ajiyar zuciya ba, 


Mommy ta ajiye ta ta tashi ta haye sama yawatsa wa su ramlat harara duk suka mike sukai sama ya meda kan Aisha kanshi duk busassun hawaye a fuskarta ya mata kisss yace "sorry Aisha ki kara hakuri dani I will change kinji? "

Ta daga mai kai ta lumshe ido, 


Ya dade nan sannan ya tafi office, 



Da dare suna wurin dinner faseelat takasa cin abinci yana dan kaucewa be tabata ba yace mata me takeso tace quaker oats ya tashi yaje ya hadomata ya bata ahannu yakoma ya zauna, har suka gama kasancewar Aisha ce kedashi yaje yawa faseelat seda safe ya fito yanata  jin kamar ya kwana acan. 




Yanzu cikin jamila yakai 7month da weeks cikin yayi narkeke kamar zata haihu yan biyu haryanzu dabiar hajya nanan ta rike khalil se 11ko 11 saura jamila har hakurinta ya kare tayi mai magana so baadadi sede yabata hakuri kawai yace watarana se labari, 


Yau har 11:15 tsit ba khalil ba alamunshi ta fito tsakar gida tanata sintiri, 


Tana ta surutu kunsan masu tsohon ciki dasaurin hawa dama,


takasa hakuri bako tsoro ta fito daga gidan ko tsayawa kullewa batai ba tai hanyar titi, 


tana cikin tafiya tasamu mashin tahaye tafada mai unguwar, 



Khalil da hjya yau fira tayi dadi dukda de rabin hankinshi nagun jamila, matsakaicin bowl ne a saman shi yana cin dambun kaza sunata labari da angama wannan se ajawo wannan, 


Kamar daga sama sede suka ga jamila cikin dakin fuskar nan ta kumbura tai jawur saboda bacin rai hannunta kan kugu, 


Khalil yafara slowing da cin naman yakura mata ido hjy ma kallon ikon Allah take duk sunkasa magana, 


Rai bace jamila tace "hjya yau shine na karshe da zaki rikemin miji har wannan lokacin, haba kamar baki da imani kinsan inada tsohon ciki ki rikeshi har tsakar dare, koke kika haifeshi ainima inada hakki akanshi "



hjy is very shocked abunda bata tabajin ko labari ba shine yake faruwa kanta ni kaina nakasa gane wane yanayi take ciki, 



khalil ko kallon jamila kawai yake yadena taunar naman, ya dade yana tunanin kamar jamila kanta da motsi se yau ya tabbatar, 


Jamila tana jijjige jijjige tacigaba da cewa "wlh in kika kara gigin rikemin miji se ranki yayi mummunan baci zan baki mamaki dan zan..... "


Khalil ya furzar da naman bakinshi yana zare mata ido ya kaseta da tsawa" ke!!! bamusan hauka anan "



Jamila tadan tsorata tai shiru yace "bacewa mutane dagani mahaukaciya "


Tafashe da kuka ta juya tafita tana kukan, 


khalil ya dafe goshi 


Tsittttt dakin yayi har lokacin kofa kawai hjya ke kallo bazaka gane ya take cikiba, 


Khalil ya saci kallonta yayi shiru zuciyarshi na zafi he know her bazata bar abunnan haka ba, 


Kusan minti biyar sannan murya asanyaye batare da yakalli hjya ba yace "hjya kiyi hakuri dan Allah tanada iskokai I'm sure ba ita bace ba"



Hjya takasa ko motsi, se lokacin ya duba wayarshi 12:00am shaf besan lokaci yaja haka ba ,


Tunawa yayi da jamila kar haukannata ya tillata wani wuri ya ajiye bowl din hannunshi yace wa hjya "seda safe "ya juya yafita dasauri, 


Hjya de na zaune kamar gunki , shi ko da yafita ba jamila ba labarinta hankali tashe ya tada mashin yakama hanyar gida.



 

Post a Comment

0 Comments