TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Babu so page 11

       *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*

                 _(Miya kawo kishi?)_




              *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*





*_11_*



.......Ɗin! Ɗinn!! Horn dake nuna alamar isowar dangin amarya Fadwa ya saka Gwaggo juyowa baki a washe tana faɗin, “A to ga masu ganin gidan nan ma sun iso ai? Kai Alhaji ƙarami muje ka buɗe musu ƙofa ɗin saina tarbesu ai ko”.

      A hankali ya lumshe idanunsa da sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya. Mommy ma bin bayan Gwaggo tayi, suma su Mom sai suka bisu kawai dan abu kaɗan zai iya jawo Gwaggo taita surutu. Har zai bisu ya dawo da baya, zuciyarsace ta bashi shawaran ya sakama ƙofar key, dan haka ya kulle da sauri ya fidda key ɗin ɗakin a cikin keys ya saka aljihu sannan yabi bayansu...

        

       Mota uku ce a jere kai kace jeren kayan sukazo. Motar farko Fadwa ce ta fara fitowa a ciki, sai ƙawayenta uku. Ta biyu kuma ƙannen babanta ne su biyu da cousin ɗinta biyu suma dai duk masu aure ne. Sai aminiyar Gwaggo Haliman. Motar ƙarshe babban yayan Fadwa sauran kuma ƴan kamfanin da zasuyi aikinne dan motarma akwai tambarin kamfanin. Cikin mutunta juna aka gaisa tunda dama akwai alaƙa, kafin su ɗunguma gaba ɗaya zuwa can. Fadwa sai satar kallon Shareff take amma yayi kicin-kicin kamar ma bai ganta ba. Dama tun waccan ranar ko kiransa tai baya ɗagawa, idan tai masa magana koda yana a online kuwa ko buɗewama bayayi. Tabi duk hanyar daya dace su sasanta amma yaƙi kulata dan yayi alwashin koya mata hankali a wannan karon.

     Ko'ina sai da suka shiga kowa na yabawa dan gida kam yayi sai dai maƙiyi. Ma'aikatan kamfanin da zasu saka kayan kuwa nata faman gwaje-gwajensu tunda dama amarya ta gama zaɓar wanda take buƙata tun a gida. Zare jikinsa yay ya koma sashensa batare daya amsa tambaya ko ɗaya ba akan ɗayan sashen dasu Gwaggo sukai magana suma. Shi dariya ma suke bashi da mamaki, ina ruwansu da sashen to tunda basu suka basa kuɗin ginin ba, sashen dama ko ƙarasa masa ayyuka ƙananu ba'aiba ya tsolema kowa ido.

    Baifi mintuna biyar da shigowa ba Fadwa ta biyo bayansa. Bai nuna alamar yasan da shigowar tata ba. Duk da shariyar tasa ta sosa ranta sai ta shanye ta shiga yaba yanda sashen nasa yay matuƙar ƙyau shima. Yanda tsarin ya kasance na black and milk da ratsin ash ya matuƙar ƙayatarwa. 

      “Soulmate!”.

Ta kira sunansa a hankali tana kaiwa zaune kusa da shi. Bai amsa ba, bai kuma ɗago ya dubeta ba yanata aikinsa kamar yanda ta samesa. Murmushin takaici ta ɗanyi tana kallonsa, ta lumshe ido ta buɗe akansa zuciyarta na raya mata abubuwa masu yawa dan ba ƙaramin haɗin kayan mata tasha ba. Sake matsawa tai jikinsa a kasalance ta ɗaura kanta a shoulder ɗinsa ta saki kuka.

      Cak ya tsaya da aikin da yakeyi, yaja numfashi ya fesar yana mai rufe idonsa da buɗewa a lokaci guda.....

          “Dan ALLAH kayi haƙuri ka daina fushi dani haka nan Yaya Al-Mustapha. Karka manta kwanaki takwas kacal ya rage mu zama abu guda, ina buƙatar ganin murmushi a fuskokinmu yayinda jama'a zasu fara taruwa dominmu daga gobe. Naji nayi laifi kuma na amsa na kuma bada haƙuri bazan sake ba mijina”.

      Kalamanta sun ɗan saka masa sassauci, sai dai baida alamar cewa wani abu a zahiri. Kanta ta ɗago daga kafaɗarsa tana kallonsa idanunta na rige-rigen matso hawaye, ta riƙo hanunsa dake dafe da lap-top har yanzu sai dai ba aikin yake ba. “Baka haƙuraba ko My Soulmate? Shike nan na baka damar kaimin kowane irin hukunci amma dan ALLAH banda naƙin kulani na tuba”.

       Karon farko ya ɗago idanu ya dubeta, kafin ya maida ga hanunsu dake cikin na juna. Nasa ya janye tare da ɗan bada tazara daga kusancinsu. “Naji ya wuce, sai dai ki tabbata kika sake hukuncin dazan ɗauka bazakiji da daɗi ba. Ni da ke zamu zauna bada iyayenmu ba, dan haka matsalarmu mune ya kamata mu fuskanceta basai wasu sunyi alƙalanci a ciki ba”.

      “Insha ALLAHU zan kiyaye mijina”. Tai maganar tana faɗawa jikinsa ta rungumesa. Hannu yasa ya janyeta. “Nasha faɗa miki bana son ɗabi'ar nan sam. Domin babu wani hallaci daya halatta hakan garemu”.

           “To kayi haƙuri, amma karka manta kwana takwas ya rage kacal mu zama ma'auratan ai ko, kaga kenan akwai banbanci da da yanzun”.

    “Sai ki bari sai mun zama ɗin, a yanzu dai haramunne”.

     “Hummm” kawai ta faɗa dan bata bukatar su sake wani rikicin kuma saboda kar yay amfani da damar yaƙi halartar duk events da suka shirya gara ta lallaɓasa ayi a tashi lafiya karya kunyatata ga ƙawayenta. “My Soulmate bara na ɗanyi using toilet Please”.

     Ɗagowa yay ya ɗan dubeta dan harya sake maida kansa ga aikin gabansa. “Yanzu a barowanki gida har sai kinzo wani waje kin shiga toilet?”.

           Murmushi tayi daya sake ƙawata ƙyawun fuskarta. “Oh My Soulmate nan ɗin aiba wani waje bane na daban, shine fa gidana nanda kwanaki kaɗan zan dawo rayuwar cikinsa. Bawani abu zanyiba part zan canja dan bana iya wuce awa ɗaya da shi a jikina”.

      Idanunsa ya ɗauke daga kallonta, haka kawai yaji wani iri a ransa ganin babu ko ƴar kunya tattare da ita take faɗin part zata canja. Da hannu ya nuna mata toilet na falon.

           “Ah-ah my Soulmate bara dai na shiga bedroom mana. Nan kuma idan cikin su Mommy wani ya shigo fa”. Komai baice mata ba, harta nufi hanyar bedroom ɗin Anam dake barci a ciki ta faɗo masa. Dakatar da ita yayi. “No ki shiga wannan ɗin can ƙofan nada matsala ne, sai angyarasa a rufe yake”.

    “Okay! To bara naje naga bedroom ɗin namu ko?”. A ɗan kausashe yace, “Shi nake nufi”. Ɗan jimm tai tana kallonsa. Sai kuma tayi murmushi cikin rausaya kai ta nufi na falon kawai. Shima aikinsa ya cigaba dayi, a zuciyarsa yana ALLAH-ALLAH su kammala su tattara subar gidan.

       Addu'arsa kam ta karbu, dan koda ta fito bata zauna ba kasancewar ƙanwar abbanta nata faman kiranta a waya akan ta fito zasu wuce.. Tare da shi suka fita, yaji daɗi sosai da su Mommy sukace suma zasu wuce ne magrib na gabatowa. 


     Bayan duk wucewarsu ya dawo ciki, kai tsaye bedroom ɗinsa ya nufa, key ɗin daya cire yasa ya buɗe babu zato ko tunanin ta tashi a ransa.... Kusan a tare ƙofofin guda biyu suka buɗe. Shi yana shigowa ita tana fitowa daga bathroom. Wata irin ƙara ta fasa da ƙanƙame guntun towel ɗin data ɗauro a jikinta dake ɗigar ruwa tareda faɗawa saman gado ta cukuykuye zanin gado da duvet ɗin gaba ɗaya a jikinta....

        “you are vary stupid!!”.

Ya daka mata tsawa jin tana barazanar fasa masa dodon kunne. 

     “Na shiga uku ni dai ka fita, dan ALLAH ka fita, Yaya wlhy babu ƙyau ganin tsiraicin wani. Wayyo ALLAH Mamie banji maganarkiba nashiga halaka.......

    “Shut up! Stupid!”. 

Ya sake faɗa da matuƙar takaicinta. Bedsheet ɗin ta tusa cikin baki tana gyaɗa masa kai ga hawaye na faman mata gudu a fuska kai kace wani abu yace zai mata. Shiko gaba ɗaya idanunsa sun birkice dan takaici, ya ƙarasa takowa gaban gadon yana watsa mata mugun kallo. “Ubanwa ya saki yin wanka anan ɗin? Ko an faɗa miki nan gidan wanka ne?”. Kanta take girgiza masa tana ƙara maƙurewa waje guda, dan ita a yanzu ba faɗan nasa take tsoro ba a yanda ya ganta da a yanda take. “Dan ALLAH kayi haƙuri Yaya. ALLAH zafine ya dameni kamar fatana zai ɗaye zufa ya jiƙani ina ƙyanƙyami shiyyasa nayi”. Rasama mizai ce mata yay, ga jikinta sai rawa yake matuƙa. Tsaki yaja ya juya ya fita kawai. “Mintuna biyar na baki”. Ya faɗa dai-dai yana jan ƙofar har saida ta zabura saboda bugata da yay.

      Kanta ta cusa tsakanin ƙafafunta ta ta sake sakin wani kukan na baƙin cikin ya ganar mata jiki abinda wani mahaluki bai taɓayiba bayan Aunty Mimi da Mamie. Duk da bawai tsirara ya ganta ba a ganinta ƙanƙantar towel ɗin baida maraba da hakan ita kam. Tuna abinda ya faɗa na karshe da yay yasata zabura. Durowa tai a gadon ta nufi ƙofar ta saka sakata, da sauri ta kwashi kayanta duk da ɗunbin ƙyanƙyamin da take musu ta shiga maidawa a jikinta da sauri-sauri. Bata kammala ɗaure igiyar abayar jikinta ba ta fito. A falo ta samesa tsaye sai faman kai da kawo yake tamkar mai safa da marwa. Tai ƙasa da kai dan a yanzu kam babu abinda take gudu kamar su haɗa ido, wani irin matsanancin kunyarsa takeji har ƙarƙashin zuciyarta. Shima bai dubi inda takenba ya nufi bedroom ɗin nasa, bai koyi mintuna biyu ba ya fito da kayansa da sukazo gidan suna jikinsa. Magungunanta da lap-top ɗinsa ya ɗauka yay waje. Da sauri tabi bayansa dan dama kamar jira take ace ar ta kwasa ana kare.

        A motar ma hankalinta ta maida gaba ɗaya waje badan tana fahimtar abinda take kallo ba, sai dan bata buƙatar koda kallonsa. Shima ɗin dai aikin tuƙinsa yake kawai lokaci-lokaci yakan amsa waya har suka iso gida. Yana gama parking ta fice. “Waye zai biki da wannan?!”. Baya ta dawo kanta a ƙasa ta ɗauka ledar magungunanta daya ɗaura saman mota ta wuce har tana harɗewa saboda yanda take tafiya da sassarfa.

      

     ★★★★


   Shirye-shiryen biki ya ƙara kankama, yayinda Anam ke faman wasan ɓuya da Shareff. Sam ta daina yarda su fita aiki tare, kafin ya fito ta shirya tabi bus ɗin su Fawwaz da ake kaisu school. Data tashi aiki kuma zata saka wani abokan aikinta ya tare mata Napep ta dawo gida. Bata yarda dai ta faɗama kowa abinda ya faru ba, sai dai tun ranar har yanzu bata sake ganin Yaseer ba. Ya daina shigowa aiki ta daina samun number ɗinsa kuma. Ta tambaya iya wanda suke mu'amula a wajen aikin nasu duk sun sanar mata suma basu san miya hanashi zuwa aiki ba. Amma dai ance ya kawo reason nashi wajen oga. Haƙura tai tabar bin kowa, sai ma haushinsa ya kamata. A yanda suke tana ganin ya dace ace ya sanar mata idan zaiyi tafiyane kokuma wani abu ya samesa ai.

        Ranar laraba gidan aka tashi da shirin isowar su Abie. Wannan ne ya ɗauke mata dukkan hankali ta manta da batun Yaseer. Taso ace da ita za'aje tarbo iyayenta airport sai dai batasan waye zaije ɗakkosu ba, dan haka ta haƙura kawai tai zaman jiransu a gida. Aiko ƙarfe huɗu da rabi na yammaci sai ga Shareff da Dr Jamal abokinsa ɗauke dasu a motocinsu ashe sune sukaje tarbosu. Cikin ƙanƙanin lokaci gida ya hautsine da murna dan harda aunty Mimi da yaranta itama. Duk da an share musu nasu gida an gyara komai tsaf anan suka fara sauka. Anam ta rungume iyayenta harda kukan daɗi su Mubarak na mata dariyar ta girma batasan ta girma ba. Duk wannan kaikawo da ihun yara da hayaniya Mommy da Gwaggo ko leƙe basu leƙo ba duk da kuwa sun san su Mamie sunzo ne domin bikin ɗansu. Hasalima duk wani ɗawainiyar biki Abie da Mami suka ɗauka. Acewarsu Shareff ɗansu ne, sune suka cancanci yimasa aure ba kowa ba. Hatta lefe da duk abinda aka kai gidansu Fadwa sai da Abie ya dawowa Daddy da Abba abunsu. Mommy taita masifa amma Daddy ya taka mata burki tun wancan lokacin dan a sanda Abie ya rako Anam ne. Sai da sukaci suka sha sannan suka shiga suka gaida Gwaggo. Mommy kuwa basu nuna sun san da zamanta a gidan ba Gwaggon ma dan uwa ce shiyyasa suka bata girmanta. Ai tuni Anam tabi su Mamie can gidan, dan taci alwashin bazatai zaman gidan nan ba dan bata ra'ayin ayi bikin nan da ita, duk da kuwa katanga ɗayace tasan wasuma zasu shigo gidansu a ƴan bikin, amma dai ko yayane bazai kai nan gidan ba ai. Sai dai kuma batasan tayi gudun gara bane ta faɗa gidan zago😚.


          ★★★


    Acan gidan su amarya Fadwa kam wannan rana itace ranar ƙunshi, suna can ita da taren ƙawayenta wayayyu da gayyar media an ware musu part guda sunata shagalinsu harda su shisha. Ga hotunan amarya sun baje media musamman tiktok da istagram da amaryar ta tara ɗunbin followers da suka sakata yin ƙaurin suna cikin jerin celebrities da akeji dasu. Amarya tasha ƙyau da gyara harta gaji, sai dai ba'ai mata nata ƙunshin bama sai gobe idan ALLAH ya kaimu alhamis.


      ★★★


    Bayan sallar isha'i Mom ta aiko kiran Anam data maƙale taƙi bin su Aysha can gidan yin ƙunshi. Amma hatta da Amrah ɗiyar Aunty Mimi dake kusan sa'anni dasu Anam ɗin tana can itama za'ai mata. Cewa tai bataso itakam, dan ko wankin kai da sukaje yau ita ƙin zuwa tayi. Sai da Mamie tamata jan ido ta biyo ƴar aikin Mom. Amma da ta langaɓe wai kanta ke ciwo. Koda tazo anan ɗin ma faɗa Mom tai mata akan batun ƙunshin. Amma saita hau hawaye wai ita bata da lafiya. Kowa kallonta kawai yake da mamaki a falon, dan kuwa dai ko awanni huɗu bata cikaba da gama murnar isowar su Mamie ai. Ganin yanda take kuka Mom tace mata taje ta kwanta ayi mata gobe idan ALLAH ya kaimu. Ai kafinma ta rufe baki tayo waje. Maimakon taje ta kwanta ɗin can ta samu inda babu wadataccen haske ta zauna taci kukanta da batasan daliliba itama sannan ta koma gidansu tai kwanciyarta.

       Washe gari wajen sha biyu yaran gidan kowa da ƙunshi abin sha'awa amma banda Anam dako wanke kai bataiba balle maganar kitso. Tana gani suka shirya suka fita hausa day itako tace bazataje ba. Sai faman baƙin rai takeyi na babu gaira babu sabar. Mamie dai tunda taimata tambaya ɗaya tace bakomai bata sakebi takanta ba. Sai aunty Mimi ce ke faman lallaɓata da lallashinta. Sai tace kawai ita bata da lafiya ne.

       A wannan lokacin Shareff dake gidan batare da Anam ta sani ba ya shigo. Gabantane yay masifar faɗuwa. Ta miƙe zaram da nufin guduwa aunty Mimi ta dakatar da ita cewar ta kawo masa breakfast ɗinsa dake kitchen wanda Mamie dakanta da girka abinta kuma irin abincin ƙasar Malaysia ne. Jitai kamar ta fashe da kuka dan takaici, koda ta kawo ta ajiye masa ƙoƙarin juya tai zata bar wajen ya watsa mata mugun kallo saboda ido da suka haɗa by mistake. Baki ta murguɗa masa itama ta haura sama da gudu.

      “Kai kaji shasha lafiyarki kuwa Mamana?”. Aunty Mimi da bata lura da abinda ya faru ba ta faɗa da mamaki tana kallon hanyar da Anam ɗin tabi. “Babana wai kaga mi yarinyarnan tayi kuwa? Sai kace mai tsoron wani anan?”. Murmushi kawai yay baice komaiba. Ta hararesa. “Kaifa tsiyarka kenan ai magana ka bama mutum amsa da murmushi”.

     “Oh ALLAH small Mom rigima. Ni yanzu mikike so nace anan kuma? Ina ruwana da shirmenta”.

         Hararsa ta ƙarayi ta ɗauke kai. Yay dariya da shafa kansa yana buɗe kwanikan. Ƙamshin ya sashi lumshe ido murmushinsa na ƙara faɗaɗa. “Lallai na shaida Mamie na kusa dani”. 

     Dariya aunty Mimi ta sanya masa da faɗin, “Makwaɗaicin banza”. Dariyar yayi shima da faɗin “Naji ɗin”. Haka ya fara cin abincin cike da nishaɗi suna hirarsu har Mamie ma ta fito daga sashen Abie ta samesu. Zama tai itama suka ɗora, daka gansu kasan akwai shaƙuwa mai faɗi a tsakaninsa tun ba yanzu ba. Anam na jiyo dariyarsu daga sama taƙi sakkowa har saida ya wuce massalaci sallar azhur. Aunty Mimi kuma ta fita zuwa can cikin gida ita da Mamie.

     Ta idar da salla tana shirin sakkowa ƙasa ta samu abinda zataci suka kusa cin karo da Fawwaz. 

    “A'a autan Mom daga ina haka da gudu?”.

         “Yaya ne yace na kiraki”.

Kafin tace da shi wane yaya ya kwasa da gudu ya fice. Ta girgiza kai tana murmushi. Ɗaki ta koma ta ɗauka abaya kasancewar kayan jikinta wando da rigane marasa nauyi. Duk zatonta Khaleel yake nufi, shiyyasa ta fito hankalinta kwance. Harta nufi gate ɗin shiga cikin gida motar dake fake a tsakanin gidansu da cikin gida tai mata horn. Kamar bazata juyaba sai kuma ta dubi motar ganin an sakeyi alamar da ita ake, tunanin ko Yah Khaleel ɗin ne a ciki ya sata nufar can duk da tasan ba motarsa bace, bama tasan motar ba dan kamar ma sabuwa.

       “Tofa, wai su Yah Khaleel sabuwar mota akayine halan?”. Tai maganar fuskarta ɗauke da murmushi tana shafa motar har side ɗin mazaunin driver. Kanta tsaye ta buɗe murfin. Duk abinda take dama idonsa a kanta, kuma yana jinta dan ya ɗanyi ƙasa da glass kaɗan. Da sauri ta saki murfin tana ambaton ALLAH tamkar wadda taga wani shaiɗan ko aljani. Ɗaga kafa tai da nufin juyawa ya dakatar da ita.

      “Idan kika bar wajen nan sai na mareki”.

   Tsayawar tayi, sai dai taƙi ta juyo. Hasali ma auna yanda zata arta da gudu takeyi.....

            “Zagaya ki shiga”

     Ta tsinkayi muryarsa a dake. Shiɗin ba abun wasanta bane, musamman a yanda yay maganar babu alamar wasa a cikinta. Ta haɗiye ƙwallar da suka taru mata a ido cikin cije lip tabi umarninsa. Sanyin ac da kamshi na musamman suka ratsata a cikin sabuwar motar da ko leda ba'a cirema kujerunta ba. Ɓoyayyar ajiyar zuciya ta sauke da lafewa cikin kujerar ranta fal tunanin ina zai kaita? Bata da mai bata amsa dan haka taja bakinta ta tsuke ta zubama sarautar UBANGIJI idanu..........✍


     

_🤣Tofa, su Shareffudden ango ko'an fara kidnapping ne bamu sani ba😣, to magana ta gaskiya ƴan team ɗinsa ku faɗa mana gaskiya mu fara rigakafin killace kammu kar'a sakamu a ruɗani😂😆?._



_ZAFAFA BIYAR_


*_INAYAH_*

_MamuhGee_


*_GURBIN IDO_*

_Safiya Huguma_


*_SANADIN LABARINA_*

_Hafsat Rano_


*_FARHATAL QALB_*

_(Miss Xoxo)_


*_BABU SO_*

_Billyn Abdul_


_*Littafi daya 300*_

*_Littafi biyu 400_*

*_Littafi uku 500_*

*_Littafi hudu 700_*

*_Littafi biyar 1k_*



YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾


ZENITH BANK

HAFSAT UMAR KABIR

2270637070


SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:

07040727902


IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇

0913484810_ZAFAFA BIYAR_


*_INAYAH_*

_MamuhGee_


*_GURBIN IDO_*

_Safiya Huguma_


*_SANADIN LABARINA_*

_Hafsat Rano_


*_FARHATAL QALB_*

_(Miss Xoxo)_


*_BABU SO_*

_Billyn Abdul_


_*Littafi daya 300*_

*_Littafi biyu 400_*

*_Littafi uku 500_*

*_Littafi hudu 700_*

*_Littafi biyar 1k_*



YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾


ZENITH BANK

HAFSAT UMAR KABIR

2270637070


SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:

07040727902


IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇

09134848107 ko




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*..........A karon farko ta ɗago ta kallesa da mamaki ganin inda yay parking. Magana take so tayi, sai dai ta kasa. Shi kuma yaƙi cemata komai, sai ma wayarsa daya ɗauka yay ƴan danne-danne yakai kunensa. “Fito”. Kawai ya faɗa ya yanke wayar. Ba'a rufe minti uku ba wata budurwa mai tsananin iyayi ta fito daga shagon saloon ɗin tana tafiya kamar tarwaɗa. Haka kawai abin nata ya bama Anam haushi, taja siririn tsaki da taɓe fuska ta janye idonta. Duk da tayine a hankali sai da yaji, sai dai bai nuna yajinba balle ya tanka, sai ma faman daƙilar waya yake, amma ya buɗe murfin kafarsa ɗaya a waje take.

      “Assalamu alaikum Yah Musty barka da zuwa”. Budurwar ta faɗa murya a lanƙwashe lokacin da take isowa wajen. Kansa kawai ya jinjina mata yana janye kunne ɗaya na earpiece dake a kunnensa. Kamarma bata damu da abinda yay matan ba. Murya ta ƙara tausasawa cike da iyayi tace, “To Bismillah muje ko”.

       Nan ɗinma bai tankaba, sai da yaja wasu sakanni ma sannan yay yunƙurin fita a motar.

    Baƙin ciki, haushi da takaicin ballagazanci na wasu mata ya tokare maƙoshin Anam. Lokaci ɗaya taji tama tsani budurwar. 

         “Sai an fito da ke ne?”.

Ya faɗa cike da gatse idonsa akan Anam. Jitai kamar karta fita ɗin, amma sai yaci darajar Yaya da yake gareta tabi umarninsa. Yanda budurwar batai mata magana ba itama bata nuna tama san da zamanta a wajen ba. Gaba sukai tana binsu a baya, budurwar sai ƙoƙarin dai-daita tafiyarta take da shi tamkar dole, ga baki ta saki sai surutu kai kace hanyar kasuwar wanbai aka buɗe da safe. Sosai wajen Saloon ɗin ya haɗu dan yaɗan birge Anam kaɗan, sai dai bata nuna a fuskaba saima kicin-kicin data sakeyi da fuska duk da gaisuwa da ma'aikatan wajen ke musu na girmamawa daya bata mamaki matuƙa. Wajen zama aka basu, harda ajiye musu abinsha kafin budurwar da taji ma'aikatan sun kira da aunty Deena ta dubesa cike da yauƙi da shauƙi.

          “Sir za'a mata kitso ne?”.

    Bai jita ba, saboda earpiece dake manne a kunnensa. Hannu takai ta cire kunne ɗaya, ya ɗago ya dubeta yana sake tsuke fuska. “Am sorry, nayi magana ne bakaji ba, nace za'a mata kitsone?”. Idonsa ya ɗauke daga gareta ya maida ga Anam datai kicin-kicin da fuska fiye da yanda suka shigo dan ta fahimci ita ya kawo kenan. “Komai ma daya dace kumata”. Ya faɗa a taƙaice da maida earpiece ɗinsa.

        “Ni wlhy bance inaso ba. Kuma kaina a wanke yake, hakama......” Hararta yay yana mai zare kunne ɗaya na earpiece ɗin, tai saurin sake haɗiye maganar tana matso hawaye. Ɗauke idonsa yay kamar baima ganta ba. Tanaji tana gani aka kwance mata kalbar kanta aka saka mata relaxer aka wanke fes. Bayan an rage ruwan da towel akai steaming ɗinsa. Wadda take mata gyaran tambayarta tai tana son kitso ne? Amma tai mata banza. Ganin haka ta juya ga Shareff dake zaune komai anayi gaban idonsa.

      “Sir za'a mata kitson ne ko a barta?”.

        “Barta kawai a mata lalli”.

Yay maganar batare da ya kalleta ba yana maida earpiece ɗin kunensa. 

       Ana fara wanke mata ƙafa da gyaran farcen hanunta ya miƙe ya fita, Anam ta bisa da harara ƙasa-ƙasa tana tura baki. Cikin ƙunƙunai tace, “Gwarama da zakai aure mu huta da baƙin halinka”.

    Murmushi mai mata wankin ƙafa tai saboda jin abinda tace. Lokacin da aka fara zana mata lalle harda ɗaukar video, dan tana son lalli sosai kitsone dai kam saida dambe da Mamie tsaye kanta, dan ko Mamie ce tace zata mata ba yarda take ba da arziƙi. Abie kam lallaɓata yake ko yace a barta sai wani lokaci tunda bata so. 

       Sosai ta fito ras tai ƙyau tamkar wata sabuwar amarya. Sai faman kallon kanta take a manyan mirrors na wajen tana murmushi da ɗaukar hoto kamar ba'itace ta gama rikiciba yanzun. Sai da tai mai isarta sannan ta fito waje kamar yanda Deena ta tabbatar mata Yaya Shareff na nan na jiranta a waje. “Okay”. kawai tace mata tai ficewarta. Deena da yaranta suka bita da kallo baki taɓe. Fuska ta haɗe tamau tana cika baki da iska lokacin da take fitowa, ta buɗe motar ta shiga tana wani kauda kai taƙi kallon inda yake.

        A jiyar zuciya ya sauke a hankali yana ɗagowa daga kwanciyar da yay jikin kujerar, murmushin daya tsaya iya laɓɓansa ya ɗan saki ganin yanda taketa faman kauda kai gefe wai ita a dole haushi take da shi. Hanunsa ya kai ya zame veil ɗin, tai saurin riƙewa tana tura baki. Kallon daya wulla mata ya sata sakin masa babu shiri, sai da ya gama ƙarema gashin kallo cikin ɗan lumshe ido da buɗewa ya maida mata ya rufe. Sosai gashin nata yasha gyara sai ƙamshi mai daɗi da ƙyalli yake.


      Koda suka iso a gate yay parking, tana fita yaja motar yay gaba abinsa. Da harara ta raka motar, sai kuma ta kalli hanunta da ƙafa da sukasha lalli tai murmushi. Gidansu tai shigewarta. Dan cikin gida tun daga waje kana iya jiyo hayaniyar daya sake ɗauka alamar baƙi sun ƙaru kenan. Gidan nasu ma cike ta sameshi da baƙin da suka iso bayan fitarta. Sai su Aysha dake shirin komawa gidansu amarya bayan magrib Arabian night. Tambayarta wanda yay mata ƙunshi suka shigayi kowa na yaba ƙyan da yayi. A takaice tace musu Yayane ya kaita wani waje kawai. Koda suka buƙaci jin wane Yaya a ciki bata amsa musu ba tama shige toilet dan son watsa ruwa kasancewar gab ake da kiran sallar magrib saboda sun jima a wajen ƙunshin nan ba laifi, gashi ko sallar la'asar batayi ba.     

      Ana idar da sallar magrib ƴammatan gidan suka sake ficewa wajen event na arabian da aka shirya amma banda Anam yanzu ma. Dan kwanciyarta taima tana kallo a lap-top hankali kwance kamar bata san bikin da akeyi ba. Har magana Amrah tai mata amma tace karta dameta. Yanda tai maganar cikin masifa yasa kowa bai sake magana ba sukai shirinsu suka fice.


          ★★★★★


Washe gari kam gida ya sake cika danƙam da ƴan uwa da abokan arziƙi na nesa dana kusa. Abokan Yah Shareff na Nigeria da wajenta duk wanda ya iso anan ake saukarsa gidansu Anam a sashen Shareff ɗin da tuni Abie ya ware dominsa duk da ba zama yake ba a hanunsu yanzun. Duk hidimar da ake Anam na ɗaki batako fitowa sai yunwa ta isheta. Bamai ganin ko fara'arta. Mamie tayi faɗan harta watsar da lamarinta, hakama Aysha fushi take da ita dan ita bataga mi Anam ɗin kema fushe-fushen ba tunda babu wanda ya mata wani abu ai. Aima gaba ɗaya ta tsame kanta daga shagalin bikin tamkar Shareff ba ɗan uwanta ba. Da yamma kusan rabin jama'ar gidan suka wuce gidansu Fadwa amarya kamu amma nanma Anam bataje ba. Kai barci ma suka wuce suka barta tana sha hankali kwance. Koda suka dawo kuma su Aysha nata labarin yanda kamu ya kasance da ƙayatarwa Anam sai tai tsaki tama fice a ɗakin gaba ɗaya. Da kallon mamaki duk suka bita, sai dai babu wanda ya kawo komai a ransa game da al'amarin nata tunda ansanta da miskilanci da kuma tsanar da sukaima juna ita da ƴan gidan su Fadwa batun yanzu ba.


        *_WASHE GARI* ta kama ranar ɗaurin aure, har sha biyu Anam na ɗakin Abie tana shaƙar barci. Dan tun bayan sallar asuba ta gudo daga ɗakinsu saboda hayaniya tafi ƙarfi acan downstairs. Duk tashin da Mamie ta mata taƙi, sai kawai ta shareta ta cigaba da hidimar baƙinta, dan nan ɗinma dai ya cika taf da dangin Mamie da ƴan uwa da abokan arziƙi kasancewar wannan shine karo na farko da zata fara aurarwa, duk da ba'ita ta haifi Shareff ba an mata karar riƙesa da tai tamkar ɗanta auren ya koma tamkar a hanunsu ne.

      Mutane sai tambayar ina Anam akeyi, sa'ointa ma na family ɗin sunata zuwa nemanta. Bata tashi ba sai kusan ƙarfe ɗaya, batare da tayi ko brush ba ta fito sanye cikin kayan barci fuska a kwaɓe dan yunwa takeji. Fitowar tata yayi dai-dai da shigowar ango da tawagar abokansa, yayi ƙyau har ya gaji cikin ɗanyer shadda fara tas sai baza ƙamshi yake yi. Ga wani kwarjini na musamman da kwalliyar ta basa tabbacin yau ɗin ta daban ce a garesa. Hakama abokansa kowa ya sha ƙyau.

     Anam ta kafesa da manyan idanunta da barci ya sa su yin wani luf-luf da sake girma, shima tunda ya shigo nasa idon a kanta suke, sai dai lokacin ɗaya ɗan murmushi dake a saman fuskarsa ya bace ɓat, ya ɗan harareta ya ɗauke kansa kasantuwar caa da ƴan uwan Mamie sukai masa kowa na faɗin albarkacin bakinsa cikin yabawa.

     Murmushi ya ƙaƙaro yana kaiwa rissine domin gaishe su kamar yanda abokansa sukayi suma, kafin ya miƙe zuwa gaban Mamie da tun shigowarsu idonta ke kansa tana murmushi. Gabanta ya durƙusa ciki sanyin murya mai nuna rauni yace, “Mamie zamu tafi masallaci”.

      Hannu ta ɗora saman hularsa, itama muryarta a raunane da sanyi  tace, “ALLAH yay maka albarka Al-Mustapha. ALLAH yasa a ɗaura a sa'a, kuma yasa abokiyar arziƙinka ce har a aljannah”.

    Gaba ɗaya falon aka amsa da amin. Shareff da kansa ke ƙasa ya kasa ɗagowa, hakan yasa Mamie kamo haɓarsa da yatsunta biyu ta ɗago fuskarsa. A hankali hawayen dake maƙale a idanunsa suka gangaro, murmushi ƙarfin hali tayi da ƙoƙarin son danne nata hawayen dake son zubowa amma hakan ya gagara. Itama sai kawai ta saki kuka mara sauti tana goge masa nasa hawayen da hanunta duka biyu. Sun birge kowa, sun kuma bama kowa tausayi, duk da wasu basu san dalilin kukan nasu ba kai tsaye. 

    Mamie dake murmushi ga hawaye tace, “Tashi kuje karku makara su Abie ɗinku sun wuce tun ɗazun. Kai Shareff ya gyaɗa a hankali, sai kuma ya kai hannu shima ya share mata nata hawayen, ta saki murmushi da shafa kansa. “ALLAH yay maka albarka”.

      Da amin aka sake amsawa. Ya miƙe idonsa na kallon ɗan lungun da zai sadaka da hanyar upstairs inda Anam take. Har yanzu tana gurin, hasalima leƙensu take baki a taɓe dan ita bataga miye na kuka ba inba gulma ba. Harda faɗin, “Su Mamie an iya kalan dangi, Mommyn sa batako kallona da arziki amma ke kinama ɗanta wannan kulan”. Ganin ya miƙene yasata komawa ta maƙale, jin kamar sun nufi hanyar fita ta sake leƙowa. Ido suka haɗa dashi yana tsaye shi da Aunty Mimi suna magana. Fuska ta taɓe da murguɗa baki tabar wajen. Numfashi ya saki a ɗan fisge da lumshe idanunsa ya ɗauke kansa shima. Aunty Mimi da duk taga komai tai murmushi kawai tana kallonsa.

      Fuska ya ɗan kwaɓe. “Miye kuma small Mom?”.

   Dariya tayi da faɗin, “A'a babu komai My son. Kuje karku makara ALLAH yasa a ɗaura a sa'a.” 

     “Humm” 

kawai yace mata yay gaba abinsa. Ta sake ƙyalƙyalewa da dariya. “Ita dai wannan Humm ɗin bata magani Yarona”.

       Murmushi kawai yay batare daya juyo ba ya fice abinsa. Dr Jamal da Fharhan da suka rage na take masa baya.........✍🏻*_Typing📲_*




Post a Comment

0 Comments