TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Zabin mahaifina page 16-18

 🌳🌳UMMU AFFAN🌳🌳

[16/01, 03:45] Halimatu Sadiya Affa Fbk: 🌳🌳🌳🌳🌳

      *ZAB'IN MAHAIFINA*

        🌳🌳🌳🌳🌳



Writen by *SADIYA ALHASSAN(ummu Affan)*


Yau dai nayi k'ok'ari nad'anyi muku da dan yawa kuyi hakuri da wannan. Nagode da addu'o'in ku gareni.


Dedicated to *PRINCESS ESHAT AYSM*

_AYSHA BICHIKI_





Page 16


Yau asabar 11/12/2017 aka daura auren UMMU SALMA AHMAD DA ABDUL-AZEEZ ME DALA. Akan sadaki 100k.Daurin auren daya tara dubban mutane da manyan masu kudi da mukamai na NIGERIA.  ba abinda kakeji se busan algaita da karan ganguna ana

 yima ango kirari.


Ango kam yayi kyau ya hade cikin wani yadi milk kyau me tsadar gaske,fuskar sa sai fidda annuri take yi baza ka fahimci halin da yake ciki ba dan fuskar sa ba yabo ba fallasa. A can na hango HASSAN ATK yana gaisawa da ango yasha babban riga da 'yar ciki kai kace shine ma angon😁😁😁


Acikin gida kuwa ana daurawa anty hadiza ta sake guda, salma tana zaune a bakin gado tayi tagumi,tayi kwalliyarta cikin swiss lace red colour da ratsin blue and white.tasha sarkan gold da awarwaro ba karya tayi kyau sosai. Abokan wasanta sa'anninta suna gefe se tsokanarta sukeyi, da yake salma ita ba ma'abociyar kawaye bane indai ka ganta da kawa to 'yar uwanta ne. Yanzu ma su suka zame mata  kawaye kowa a cikin su tasha ado se zuba kamshi suke yi.


Aunty hadiza ne ta shigo tana fada musu akan sunce yanzu zasu zo su dauki amaryan su, saboda mahaifiyar A.A ta hada walima a gidanta.

salma tana jin haka ta fashe da kuka.


Rarrashinta aunty hadiza ta shigayi, inna ce ta shigo dakin ta zauna a gefen salma ta ruk'o hannunta ta fara mata nasiha.


Salma nasan ke yarinya ce me biyayya da hakuri "ina so ki rik'e wannan a zaman auren ki" ki kasance me tsabta da rik'o da addini karki yadda mijinki ya shinshino wari a jikinki, ki kasance kullum cikin k'amshi. karki zamo me sa'insa da miji karki raina abokiyar zamanki ki bata girmanta a matsayinta na wanda ta girme ki, karki shiga harkan ta koda ta nemiki da fada.


tsakaninki da kowa girmamawa, ki kasance me hak'uri a gidan mijinki, kiji kik'i ji, ki gani kik'i gani wannan ne zesa ki zauna lafiya a gidanki. ki zama me girmama 'yan uwan mijinki, karki yarda mijinki ya fahimci bakya son 'yan uwansa. ki kasance me gyara SHIMFIDAR MIJINKI (princess eyshat Aysm)



A karshe ina miki nasiha da ki zama mace me yima mijinta Addu'a da rike sirrin mijinta, ki yawaita addu'a da kaima ALLAh kukanki, ki rik'e azkar safe da yamma insha ALLAhu zai zamo kariya a gareki.


ALLAh yayi miki albarka, ALLAh yasa gidan zamanki ne 🙏🙏🙏🙏 AMEEN aunty hadiza ta amsa.Inna tadan goge kwallan daya taru mata, tace hadiza rakata wajen malam kafin su k'araso. Aunty hadiza ta ruko hannun salma da tunda aka fara mata nasiha take kuka harda sheshsheka suka fita. Kofar dakin mallam Amadi sukaje sukayi sallama ya amsa musu ya basu umurnin su shiga.


Suka shiga suka nemi waje suka zauna. "Aunty hadiza tace yaya ga salma nan kayi mata nasiha sunce yanzu zasuzo daukan amaryan"Duban salma yayi wacce take kuka k'asa-k'asa yace "to salma menene abin kukan? keda za'a kaiki gidan da zaki huta" ba ruwanki da aikin wahala, to nidai abinda zance miki kawai shine kiyima mijinki biyayya, duk abinda yace miki karki yadda kiyi masa gardama. Karki sake ya kawo min k'aranki. in kuma kika bari ya kawo min k'aranki to wallahi ba abinda zai hana naje har gidan nayi miki shegen duka. Dan baza kiyi min bak'in cikin zuwa hajji wannan shekaran ba.



Kallonsa kawai Aunty hadiza ta tsaya yi, tana jinjina son money irin na yayanta. an daura auren ma be dena  abinda yakeyi ba maimakon yayi mata nasiha irin wanda iyaye suke yima 'ya'yansu amma ya tsaya yin maganar CIKAR BURIN SA (littafina na gaba insha Allahu)Kallonsa kawai Aunty hadiza ta tsaya yi, tana jinjina son money irin na yayanta. an daura auren ma be dena  abinda yakeyi ba maimakon yayi mata nasiha irin wanda iyaye suke yima 'ya'yansu amma ya tsaya yin maganar CIKAR BURIN SA (littafina na gaba insha Allahu)


Hadiza kamata kuje gashican naji ana neman amarya may be masu daukanta ne sukazo kar suyita jira. Maganar shice ta dawo da ita daga duniyar thinking data fada, kama salma salma tayi suka fice daga dakin ba tare da tace masa wani abu ba.



Dakin inna saude ta maida ita,ta dauko mata make-up kit tace ta sake gyara fuskarta. Bayan tadan gyara, Aunty hadiza tadan yi mata nata nasihan sannan tace karki yadda ki zama bora a gidan mijinki, kuma karki sake kishiya ta raina ki duk yanda za'ayi kiyi domin juyo da hankalin mijinki gareki kuma ki dage da addu'a. insha ALLAhu se kinfi k'arfinta. ba abinda ta isa tayi miki. kuma................ bata kai ga fadan abinda take soba sukaji sallamar masu daukan amaryan har sun k'araso.



Bayan sun shigo an gaggaisa Aunty hadiza ta rik'e hannun salma ta kaita wajen innarta sukayi sallama, sannan suka fito suka shishshiga motoci. salma se aikin kuka takeyi😭😭😭😭 tana bak'in cikin rabuwa da innarta😡😡😡.


Gidan su A.A dake unguwar tambari estate suka nufa. Babban Gidane ya hadu iya haduwa tun daga get zakasan nera tayi kuka. dan ko a layin yafi ko wani gida kyau da tsaruwa. A haraban gidan motocin sukayi parking, fito da salma akayi wanda kanta yake lullube cikin mayafi aka nufi cikin gidan da ita.



Wani hadadden falo naga an shiga wanda ban taba ganin irinsa a k'asar mu ta NIGERIA ba. se dai kasashen turawa. falo ne dayaji kujeru ash da baki ga chanise carpet da labulaye duk arsh da baki. ga k'atuwar plasma da home tiatre se aiki sukeyi kai gaskiya falon ya hudu.



Daga kan da zanyi na hango wata hamshak'iyar mata daga ganinta jin dad'i da hutu sun samu zama a jikinta. Kyakykawa ce doguwa fara tana da d'an k'iba amma ba sosaiba. baza ta wuce 55years ba amma idan ka ganta zakayi zaton batafi 45years ba saboda yanayin hutu da take ciki. Hajiya Halimat me dala kenan uwargida a wajen Alh. Abdul razak me dala kuma mahaifiya Awajen A.A.



Tana zaune tare da k'awayenta se murmushi take zubawa. Tasowa tayi cikin takunta na manyan mata ta k'araso ta rungume salma daka kalleta zakasan tana cikin farin ciki."well come to our family my daughter" ta fada tana murmushi, sannan ta jata suka zauna akan daya daga cikin kujerun da suke falon. Duk mutanen wajen ba wanda bata burgesu ba. wanda suka santa kam basuyi mamaki ba dan sun santa macece me son mutane bata da girman kai ko kadan.



Su aunty hadiza  waje suka nema suma suka zauna, bayan 'yan gaishe-gaishe suka damk'a musu amanar salma, suka ce sun kar6a da fatan Allah ya tayasu ruk'o. 


Agurguje

Salma na hango an fito da ita daga wani daki tasha lufaya milk colour fuskarta tasha make-up, tayi kyau sosai.  Haraban gidan suka nupa wanda aka k'awata su da kujeru saboda gudanar da walimah. Batare da bata lokaci ba malama juwairiyya ta fara gudanar da lecture bayan ta bude taro da addu'a. Tayi bayani akan hakkokin miji akan matar sa da kuma yanda mace zata tafiyar da rayuwar aurenta da dai sauran su.


Bayan ta kammala ne aka rarraba bags wanda suke dauke da hoton ango da amarya a ciki akwai hankacif,memo,key holder,calender da juice kala-kala wanda suma suna dauke ne da pics din ango da amarya. se take away wanda akasa rabin kaza,donnut da meat pie. Ba'a tashi daga waliman ba se 5:00pm.


Wani daki na musamman aka kai salma,wata budurwa naga ta shigo dakin wanda batafi 21years ba,kyakykyawa doguwa bata da jiki sosai black beauty sadiya Abubakar kenan (my namecy😜) wanda aka daukota tun daga sokoto domin tazo ta shirya salma zuwa wajen dinner.



Toilet ta shiga ta hada ruwan wanka wanda yasha turaruka masu kamshi,ta fito ta umurci salma da ta shiga tayi wanka ta dauro alwala saboda lokacin sallar magriba ta k'arato.Bayan salma ta fito ta shafa mai  se sady ta dauko make-up kit dinta ta fara tsantsara ma salma kwalliya. Wanda ya dauke su tsawan awa daya da rabi. 


MASHA ALLAH abinda ya fito daga bakina kenan lokacin danayi arba da fuskar salma.


A gaskiya me karatu zanso kaga salma a lokacin.Indai ba farin sani kayi mata ba zeyi wuya ka shedata. nima dan na lab'e a lungun gado ne shiyasa har na ganeta.😜 Azuciyata kuwa nace anya A.A zai gane salma kuwa shida ko gama saninta ma beyi ba. 



muje zuwa 



🌳🌳UMMU AFFAN🌳🌳

[17/01, 10:45] Halimatu Sadiya Affa Fbk: 🌳🌳🌳🌳🌳

      ZAB'IN MAHAIFINA

        🌳🌳🌳🌳🌳


Written by SADIYA ALHASSAN (Ummu Affan)


    🌐HAJOW 📝🌐


🌐👩‍👧‍👧👩‍👧‍👧👩‍👧‍👧HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS ✍🏾✍🏾✍🏾🌐


Dedicated to PRINCESS ESHAT AYSM

AYSHA BICHIKI


page 17


Bayan sady ta gama mata make-up din salma ta saka hijab d'inta tayi sallar magriba dan lokacinsa harya kusa fita, tana idarwa aka kira isha'i. Tashi tayi ta yi sallar isha'i. Bayan ta idar tayi addu'o'inta aka shiryata cikin doguwar rigan material fitted gawn, wanda A.A suka kawo mata akan tasa ranar dinner. tasaka mahadin kayan ta fesa turare. Gaskiya salma tayi kyau dan kuwa my namecy taci kudinta, inso samune ayi mata k'ari😜.dan ta'iya shirya amare.


Hajiya halimat ce tayi sallama ta shigo dakin. waw! my daughter kinyi kyau sosai,ta kai dubanta ga sady tace gaskiya takwara kin iya tsara kwalliya,ai wannan indai baka santa ba baza ka iya ganeta bama. Lallai kina da kyauta me tsoka tunda kika sa daughter tayi kyau haka.


Ita kuma sady jin an yabeta ne yasa ta fara magana cike da iyayi,ai hajiya inayi fiye da hakama. murmushi Hajiya halimat tayi ta kama hannun salma suka nufi falo. Kawayen amarya na zaune sunyi kwalliyar su cikin lace orange  da touch din blue a jiki, se suka saka head blue suma sunyi kyau ba lefi.


Har bakin mota hajiya halimat takai salma, wata had'ad'd'iyar mota naga ta bud'e ta saka salma a ciki, galases din motar tint ne baka iya hango wanda yake ciki.


ta dubi saleem  dake zaune a gaban motar  tace ga amanar 'yata,kar ku bari wani abu ya tab'a min ita dan kunsan bazan bari ba. Sake juyowa tayi ta kalli A.A wanda ke zaune a bayan motar. yana sanye da shadda purple colour anyi design fari a gaban rigan, ya saka farin hula da farin takalmi se agogo silver colour. Shima yayi kyau sosai a takaice dai sunyi anko ne da salma. Ya hade fuskarnan  kanshi yana kasa yana daddana waya be ko nuna alamun yasan da zaman mutane a wajen ba.


Girgiza kai kawai tayi ta rufe motar ta juya ta koma cikin gida. Bayan k'awaye da sauran mutane sun shishshiga mota ne, motoci suka fara tafiya suka nufi hanyar da zata kaisu "ME SANDA GREEN GARDEN" sbd acan zasu gudanar da dinner. Tafiya akeyi amma ba wanda yayima dan uwansa magana. Salma kanta yana k'asa tana wasa da zoben azurfan dake hannunta shikuma ya maida hankali wajen danna waya ko me yake dannawa oho.


Da saleem yaji shirun yayi yawa ne yayi magana"amaryan mu yau ba gaisuwa ne?" murmushi salma tayi ta dago kanta ta kalle shi ta cikin mirro tace ina wuni yaya saleem. Lafiya lau ya amsa mata cike da jindadin girmama shi da tayi. Ya hidiman biki? Alhmdlh! ta amsa. Duk abinda sukeyi A.A be ko d'ago kanshi ba balle ya tanka musu. Ba wanda ya sake magana har aka k'arasa wajen. Bayan motocin sun gama parking mutane suka fiffito  suka nufi cikin hall din.


Juyowa salim yayi ya kalli A.A yace Friend dan ALLAh karka fita ku d'an jira ayi arranging din k'awayen,🙏🙏🙏 be d'ago ba balle ya amsa masa. Bayan fitan saleem ne ya d'an juyo da kansa ya kalli salma da kanta yake k'asa, zuba mata ido yayi gabansa yana faduwa ya rasa dalilin dayasa idan ya kalli yarinyar se yaji faduwan gaba.


A gaskiya tayi mishi kyau sosai, daman haka take da kyau? duk da mata basa gabansa amma ya tabbatar wa kansa wannan ta dabance. dan tana da wani sirrin kyau wanda mutum bazai saniba d idan yana tare da ita ga wani kwarjini da tayi masa. Besan lokacin daya saki murmushi ba, adai-dai lokacinne salma ta d'ago da kanta dan taji a jikinta kamar ana kallonta. Suna had'a ido ya d'auke kansa ya murtuk'e fuska kamar be tab'a dariya ba.


Kallonsa kawai salma takeyi tana mamakin halinsa mutum se miskilancin tsiya, gashi dai ta kama shi yana kallonta amma ya kauda kai kamar bashi ba. Dani kake zance zakama dawo kan hanya indai nice  ta fad'a a zuciyar ta.


muje zuwa



🌳🌳UMMU AFFAN🌳🌳

[20/01, 01:40] Halimatu Sadiya Affa Fbk: 🌳🌳🌳🌳🌳

      ZAB'IN MAHAIFINA

        🌳🌳🌳🌳🌳


Written by SADIYA ALHASSAN (Ummu Affan)


    🌐HAJOW 📝🌐


🌐👩‍👧‍👧👩‍👧‍👧👩‍👧‍👧HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS ✍🏾✍🏾✍🏾🌐


Dedicated to PRINCESS ESHAT AYSM

AYSHA BICHIKI


Page 18


Wannan shafin nakine ke kadai UMMU LAILA. kiyi yanda kike so dashi, Nagode da k'aunar ki gareni ALLAh ya bar Zumunci🤝





Bude murfin motan akayi ta gefen salma,aunty hadiza ce ta fito da ita. Shima A.A ya bud'e ya fito


K'awayen amarya ne da abokanan ango suna tsatstsaye. Salma da A.A suka shiga tsakiya aka nufi cikin hall din abokai da k'awaye suna watsa musu flower. Tun daga wajen hall din kake jin kid'a yana tashi. D.J ya bada sanarwan shigowan ango da amarya, duk wanda suke cikin hall din suka mimmik'e. Saida sukaje suka zauna sannan mutanen suka zazzauna.


Bayannan D.J ya tashi yayima ango da amarya barka da zuwa. Aka nemi abokin ango da k'awar amarya suzo su bada tarihin ango dana amarya. Saleem ne ya tashi ya bada na ango, wata 'yar uwar salma tazo itama ta bayar. Bayan sun koma sun zauna aka umurci ango yazo ya yanka cake shida amaryar sa.


Ruk'o hannun salma A.A yayi,da sauri ta dube shi ko kallonta beyi ba ya mik'e tsaye,dole tasa itama ta tashi suka je wajen da zasu yanka cake din. kid'a  aka sake  cikin wak'ar nura m inuwa wanda yayi musu na bikin. Cake d'in me hawa uku ne, an rubuta sunayesu a jiki.  hannunta da nashi suka had'a suka yanka, nan hall d'in yad'au tafi. ya d'auka yasa mata a baki cikin jin kunya ta karb'a itama ta yanka ta bashi.



Bawanda zai gansu yayi zaton ba masoya bane se dai idan ka sani, juyawa sukayi suka koma wajen zansu. Nan akaci gaba da gudanar da taron yanda ya kamata, anci ansha an goge wuya. Wajen diban abinci ne na hango 'yan group d'in just hausa novels da 'yan group din princess eyshat Aysm da 'yan group d'in ummun sadiq novels se ture-ture sukeyi kowa yana son ya cika timbinsa.😃😃😃😃😃


Bayan an tashi daga taron aka maida salma gidansu A.A ita da k'awayenta dan acan zata zauna har agama bikin. Washe gari ya kama yini tun safe sady tasa salma tayi wanka dan tanason tayi mata kwalliyar datafi ta jiya. Aikuwa ta tsara mata dan har taso tafi jiya kyau, tayi shigar jan atamfar sufer wax da ratsin green a jiki. ta saka sark'an diamond da abin hannunsa. Anyi wunin biki lafiya sunyi hotuna se fatan ALLAh ya bada zaman lafiya. Da daddare bayan mutane sun watse angwaye sun sallami k'awaye kowa ta tafi.


Salma tana zaune a kan kujera a dakin hajiya halimat, Aunty hadiza ta shigo ta sameta, to salma nizan tafi tunda ance ba yau za'a kaiki ba,in yaso gobe zan dawo ina fatan babu matsala??? girgiza kai salma tayi idonta ya cuko da hawaye tace bakomai aunty ki gaida min da  innata. murmushi Aunty hadiza kawai tayi  sannan tayi mata sallama ta tafi.


A gurguje



mahaifiyar A.A ce ta shigo ta sami salma a zaune tayi tagumi. zama tayi kusa da ita ta janye hannun tace, ki dena damuwa daughter  ki daukeni kamar mahaifiyar ki, duk abinda yake damunki ki sanar dani karkiji kunyata kinji? gyada mata kai salma tayi, yanzu ki tashi kije ki kwanta kinga dare yayi. Ta ruk'o hannun salma ta kaita bakin gado tace ta kwanta, ta lullub'a mata bargo kasancewar lokacin sanyi ne, ta kashe mata wuta ta fita ta nufi d'akin me gidanta.

            ASUBA TA GARI SAL-AZEEZ.


Washe gari bayan sunyi breakfast, salma tayi wanka sady tayi mata make-up kasancewar itama a ranar zata koma garinsu sokoto dan aikinta ya k'are. Salma ta shirya cikin shadda light brown d'inkin doguwar riga yasha aiki, ta yapa gyale dark brown tasa takalminta flat shima dark brown.

                k'arfe 11:00am Aunty hadiza ta iso ita da wata k'anwar inna saude Aunty Asma'u. Bayan an gaggaisa hajiya halimat takai salma falon Alh. Abdul-razak me dala domin su gaisa dan tunda tazo basu had'u ba saboda sha'anin biki. Kanta a k'asa ta durk'usa a gefe cikin jin kunya  ta gaida shi, fuskar sa d'auke da murmushi ya amsa mata, sannan ya d'anyi mata nasiha. Ya mik'a ma hajiya halimata emvelop  ki bata wannan ATM ne dana bud'e mata account saboda idan tana buk'atar kud'i ba saita tambaya ba, yanzu haka akwai kudin dana zuba a ciki 1million naira, zan dunga tura mata 500k duk wata insha ALLAhu. Godiya sosai salma tayi mishi tana jinjina karamci irin nasu.


Hajia halimat ta ruk'o hannun salma suka fito daga falon, suka iske su Aunty hadiza suna jiransu, gyalenta ta d'auko dan tace harda ita za'a raka salma gidanta 'ya'yanta mata se tsokananta sukeyi, kowacce tana rataye da jakanta kowa zata koma gidan mijinta tunda an gama bikin.  Motoci suka shishshiga Aunty hadiza da Aunty asma'u suna cikin mota d'aya,  se hajiya halimat da salma suma suna 1 dukkansu driver ne yake jansu.


Wanr had'ad'd'en gida naga  sun nufa dake cikin  G.R.A(sir kashim)  bud'e musu get me gadi yayi saboda besan amarya bane, dan tun jiya matar gidan tayi masa warning  akan karya yadda ya barsu su shiga.

                  Bayan motocin sunyi parking a haraban gidan, suka fiffito salma bakinta d'auke da addu'an neman tsari ta fito da k'afar dama, gabanta se  calugude yakeyi. da gudu me gadi ya k'araso daya fahimci su wanene su.

              dan Allah hajia kuyi hakuri wallahi tace min karna barku ku shigo,in kuma na barku to a bakin aikina ya fad'a yana durk'usawa.



                 kallonsa hajia halimat tayi tace ka kwantar da hankalinka mallam musa ba wanda ya isa ya rabaka da aikinka, Nan take ya fara murmushi dan yaga kamanninta da me gidan ya tabbatar mahaifiyasa ce, godiya yayi mata sannan ya koma bakin aikinsa.


Ita kuwa hajiya halimat dama dalilin zuwanta gidan kenan, dan ta tabbatar za'ayi hakan.


Cikin gidan suka shiga, gidan flat ne baida girma sosai  amma ya tsaru. idan ka shiga zaka tarar da babban falo wanda yasha had'ad'd'un kujeru seti 2, brown da milk, se labulaye da chanise carpe da t.v plasma babba. a can gefe kuma dining room ne an k'awata shi da dining table da kujeru.

    

              Akwai k'ofofi guda 2 a cikin falon  left and right. kowani kofa yana d'auke falo madaidaici da 2 bedroom da toilet, se kuma kitchen wanda yake d'auke da store aciki.  Akwai  babban kitchen ta baya wanda yake kusa da BQ da alama a ciki masu aiki suke girki.



             D'aki 1 na uwargida humaira ce, d'ayan kuma na A.A ne wanda yanzu ya barma salma shikuma ya koma d'akin gimbiya humaira.                Gidan dai-dai zaman mata d'ayane ita da mijinta, dan basu dad'e da komawa gidan  ba. Basu samu kowa a falon ba da alama masu gidan har lokacin basu tashi ba.


Aunty hadiza ce ta ska key ta bud'e dakin dake mazaunin na salma suka shiga. Gaskiya d'akin ya tsaru readers na barku ku wassafo yanda d'akin yake basai nayi muku bayani ba.



                    Dad'a gyara ko ina sukayi sannan Aunty hadiza taja hannun salma d'aki suka d'anyi maganganunsu ta bata shawaran yanda zata zauna da kishiyarta, karta yarda taji tsoronta, ta fiddo da hisnul muslim a jakarta ta bata, tace ta dage da addu'a. ta kuma yi k'ok'arin juyo da hankalin mijinta gareta.


                     suka fito sukayi musu sallama dan ita hajia halimat tace ba yanzu zata tafiba se tayima matarsa warning akan salma.


        to kunji pa readers koya zata kasance ko biyo ni.


Bayan su Aunty hadiza sun tafine suma suka fito babban falo suka zaunag


                 Hajiya ta dubi salma tace daughter ki dage da addu'a pa da kuma azumin litinin da alhamis, kin riga kinsan komai ba sena fad'a miki ba.


                 K'arar bud'e k'ofa sukaji  A.A ne ya fara fitowa bayansa humaira ce tasha riga da skirt na lace golden sun matseta kanta ba d'ankwali se kitson attach da ya zubo mata har baya, ba lefi tana da kyau amma bata kama k'afar salma ba.


             Ido hud'u sukayi da mahaifiyar sa da sauri ya k'araso cikin falon yana murmushi. Zama yayi akan kujera sannan yace "Gud morning cwt Mom ai bansan kinzo ba" itama murmushin tayi dan taji dad'in ganin d'an nata dan rabonta dashi tun ranar dinner.


Gud mornin son da fatan na same ku lafiya?? ko kad'an bata nuna masa b'acin ranta ba dan tasan bayin kansa bane. lafiya lau ya amsa mata.


               Se alokacin humaira ta k'arasa shigowa falon  dan mutuwar tsaye tayi da ta gansu, batayi tsammanin ganin hajiyar ba saboda bata tab'a zuwa gidan su ba, bayan hakama ai tayi wa get man warning,wato bejiba seda ya bud'e musu aikuwa yayima aikinsa. ta fad'a a cikin zuciyarta.


Akan kujera ta zauna 1 seater ta gaida hajiyar ta amsa mata ba yabo ba fallasa.


                      idonta ta kai kan salma wanda ko kallo basu isheta ba balle ta gaishe su.

                           Gabantane yayi mugun fad'uwa ganin tsantsar kyau irin na salma tunda ake mata kishiya ba'a tab'a mata me kyau da kwarjini kamar salma ba.





                  Hajia halimat tayi musu nasiha sannan tace "Abdul ga salma nida kaina na kawo maka ita inaso kayi adalci ban yarda ko bayan raina ka rabu da ita ba, kasani duk randa kasake ta to wallahi seka saki wannan matar taka" kuma ina so yanzu ka raba musu kwana. idan ka gama 7days dinka a dakin salma se su fara raba kwanakin. 




                    Ba tare daya kalli humaira ba yace ya raba kwana bibbiyu. Iyakan b'acin rai humaira takai, lallai wannan matar wato tanan ta b'ullo ai kuwa intasan wata batasan wata ba. Matsalan da take samu 1 ne duk yanda takai ga son ta raba Abdul da iyayensa ta kasa. danta kasa cire masa sonsu a zuciyar sa, ta waje d'aya ta samu nasara data hanashi zuwa gidan se dai yaje a b'oye ba tare data sani ba.


Kuma indai zasu bashi umurni to seya aikata ko ita bata isa hanashi yi ba.


                  Amma ta mallake shi yanda take so, duk abinda taga dama shi za'ayi.




                 mik'ewa hajia tayi ta ruk'o hannun salma tace toni zan tafi. Mik'ewa A.A yayi dan ya rakata amma ta dakatar dashi,kayi zamanka nagode. Jiki a sanyaye ya koma ya zauna ALLAh yasa badai fushi Momynsa tayi dashi ba. 


                 Har takai bakin k'ofa zata fita ta juyo tace maganar malam musa me gadi ban yarda a canja shi ba. Da hanzari ya amsa mata, duk miskilancin A.A baya yima iyayenshi saboda baya k'aunar b'acin ransu. Aikuwa nan humaira ta dad'a cika dan tasan bata isa tayi masa komai ba tunda wannan tsohuwar ta hana.


             Fuuuu... ta mik'e ta shige daki cikin tsanin b'acin rai. da kallo kawai ya bita ba tare da yace mata komai ba.


Kai aradu nagaji wanga typing ya ban wuya, har ya cinye min chaji kowa wamin karo-karo.




Post a Comment

0 Comments