TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Kaddara ceh page 3

 *ƘADDARA CE!*



      *©SALMA AHMAD ISAH.*

            *CANDY🦋*


_ArewaBooks @SalmaAhmad_

_Wattpad @Salma_Ahmad_Isah_



*04*



*Unguwar Fantai, Haɗejia local government, Jigawa state.*


MAIMUNA POV.


Su uku ne jere a bakin titi. Kuma ko wacce a cikinsu kayan siyarwarta ne a gabanta. Ɗaya tana suyar awara, ɗaya tana soya wainar fulawa, sai kuma ita da bokitin kununta ke aje a gabanta.


Tun daga nesa ta hangi kawunta, ƙanin mahaifinta wato Kawu Barau. Duk da duhun magariba da ya fara sauƙa bai sa ta kasa gane shi ba. Baki ta washe ta miƙe tsaye tun kafin ya iso inda suke. Kuma shi ma har ya iso inda suke murmushi yake.


“Kawu ina wuni!”


“Lafiya ƙalau me sunan Hajja”


Kawu Barau ya amsa yana kallon tilon 'yar ɗan uwansa. A lokacin ya lura da hannunta na dama dake ɗauke da tabon ƙuna. Lokaci guda fara'ar kan fuskarsa ta yi balaguro. 


“Me sunan Hajja ya aka yi kika ƙone?”


Maimuna ta kalli hannunta, sannan ta kalli kawu tana faɗin.


“Auwwa ce ta ƙonani rannan. Amma ai ya fara warkewa, saboda Mummynsu Maryam ta kaini asibiti, kuma har magunguna ta sai min”


Cike da tausayawa Kawu ya girgiza kansa yana faɗin.


“Wa cece kuma Mummyn su Maryam?”


“Wannan ƙawar tawa, jikar tsohon Kaigama”


“To to. Na gane, 'yar gidan Bara'atu ko?. 'Yar Alhaji Haruna Kaigama me rasuwa, ƙanwar Alhaji Bello Kaigama na yanzu!”


Maimuna ta gyaɗa masa kai.


“Amma ko ta kyauta. Allah ya biyata da gidan aljanna... Amma baki faɗawa Hajja ba?”


Ta yi saurin gyaɗa masa kai. Dan bata faɗawa kakar tata ba. Saboda a tsakanin kwanakin ba ta je gidanta ba. Kuma ko ta je ma ballale ta faɗa ba idan har ba tambaya Hajjan ta yi ba.


“To Allah ya kyauta. Ya saka miki da abin da Auwwa take miki. Ki ci gaba da haƙuri kin ji ko me sunan Hajja?. Allah na sane da ke, kuma zai kawo miki ƙarshen wannan wahalar taki. Ki ci gaba da addu'a. Kan Allah ya baki ikon cinye wannan jarabawar da yake miki”


Faɗin Kawu Barau yana lissafo 'yan kuɗaɗen da suka sa aljihunsa yin nauyi a safiyar yau. Cike da damuwa Maimuna ta gyaɗa masa kai.


“To Kawu. Inshallah zan yi”


“Karɓi wannan ba yawa. Na san magungunanki sun ƙare, dan wallahi suna raina, shi ya sa na kasa sukuni har sai da na samo kuɗin siyansu, dan na san a yanzu lokacin sanyi kin fi buƙatarsu”


Maimuna ta yi murmushi tana girgiza masa kai.


“Ai duka Mummy ta siya min har da folic acid da palludrine”


Cike da mamaki Kawu ya kalli kuɗin hannunsa, sannan ya ƙara miƙa mata.


“Duk da haka dai ki karɓa, ba zaki rasa amfanin da za su miki ba. Ko sabulu kika siya kika wanke kayanki ai kin rage”


Maimuna ta karɓi kuɗin hanu biyu, tana kallon kawunta da yalayen idanuwanta.


“Na gode Kawu. Allah ya ƙara buɗi”


Kawu ya yi murmushi. Sannan ya mata sallama ya ɗale kekensa ya nufi gida. Kasancewar tun bayan rasuwar matarsa bai sake yin wani auren ba ya sa yake zaune tare da mahaifiyarsu. A soro ya jingine kekensa, sannan ya yi sallama ya shigo cikin gidan. Inda ya iske mahaifiyarsu Hajja, zaune a tsakar gida, da alamun alwala ta yi, dan ga buta nan aje a gabanta.


“Barau an dawo?”


“Eh Hajja. Na dawo”


Hajja ta miƙe tana faɗin.


“To sannu da hanya”


“Yauwwa Hajja”


Daga haka ta shiga rumfar dake gidan, ta ɗauki hijabinta dake aje a kan sallaya. Ta saka ta tayar da sallah. Yayin da Kawu ya kama ruwa, sannan ya yi alwala ya fita masallaci.


Sanda ya dawo Hajja na zaune a nan rumfar tsakar gidan tana jan carbi. Zama ya yi a kan kujera 'yar tsugguno yana jiran ta kammala. Kuma sai da ta kammala ɗin ya faɗi abin da ke bakinsa.


“Hajja magana nake so mu yi a kan Me sunanki!”


Hajja ta aje carbin hannunta tana tattara hankalinta gare shi, jin batun magana a kan tilon jikarta.


“Me ya samu Maimunatun?”


Cikin damuwa Kawu ya tsara mata abin da Auwwa ta yi wa Maimuna, sannan ya ƙara da.


“... Ni Wallahi dan de kin ƙi ta tawa ne, tun yarinyar nan tana ƙarama na so ta dawo wurinki da zama, amma kika ce can shi ne dolenta, dan haka ba za ta dawo nan ta zauna ba, yanzu bayan talla da Auwwa ke ɗora mata har da su hukunci da wuta take mata, ya kamata mu yi wani abin a kan lamarin me sunanki Hajja. Ko da wannan cutar dake damunta aka barta ya isheta ƙaddara, ballantana a ƙara mata da izayar matar uba!”


Hajja ta ci gaba da kallonsa har ya kai aya, sannan tace.


“Barau! Ba wai na ƙi amincewa da shawararka ba ne. A'a, ni akwai abin da nake hangowa. Yanda Auwwa take da masifar son abin duniya za ta iya cinyewa wannan gidan. Bayan kuma shi ne kaɗai gadon da mahaifinsu ya bar musu ita da Gambo. Ina da tabbacin idan har Maimuna ta bar gidan nan Auwwa da ɗanta za su iya mallake mata gado. Kuma ko ba komai ɗa a gidan ubansa ya fi daraja, idan tana can ɗin ita kanta sai ta fi jin cewa a gidan ubanta take!”


Kawu ya yi shiru. Can kuma yace.


“A gaskiya Hajja ni na fara tunanin yi mata aure. Dan na lura da auren shi kaɗai ne zai kuɓutar da ita daga wanna baƙar azabar da take sha!”


Hajja ta girgiza kanta.


“Barau kenan! A auren yanzu masu lafiya ma ba auruwa suke da daɗin rai ba. Ballantana ita da take da jinya. Jinyar da iyaye ma kan guji 'ya'yansu idan suna ɗauke da ita, saboda gudun wahala, ballantana kuma miji. Kuma a irin auren yanzu ba na jin akwai wanda zai iya kula da Maimuna. Ka sani ba sai na nanata maka ba cewar cutar da Maimuna ke da ita na matuƙar bukatar kulawa. Kuma fa ni tun da nake da ita ban taɓa ji tace yau ga wani saurayi yace yana sonta ba, saboda kawai tana da sickler!”


Hajja ta ƙarasa maganarta a raunane. Saboda tausayin jikarta dake ƙara kamata. Shi dai Kawu shiru ya yi kawai, dan a zahirin gaskiya ya fara gajiya da abubuwan da Auwwa takewa 'yar ɗan uwansa. Kuma yana ganin kamar lokacin da zai ɗauki mataki ya yi.




MARIYA POV.


Zaune take a kan kujerar falo. Ta saka Hilal dake wasa a cikin car toy ɗinsa a gaba tana kallo. Kamar ta samu tv, a hankali ta ciro yatsun hannunta biyu da ta cusa a cikin gashin kanta. 


Sannan ta gyara zamanta tana kallon yaron, sai kuma ta kai hannunta saitin da motar wasan nasa take. Sannan ta motsa hanun nata. Na take motar ta iyo gabanta kamar yanda ta motsa hanun nata.


Kallon yaron ta ci gaba da yi, kamar yanda shi ma yake kallonta. Sannan a hankali ta ɗaga hannunta na dama, ta saka a cikin sumar kansa me laushi, sannan ta ciro gashin kansa da mugun ƙarfi. Amma kuma ko gezau yaron bai yi ba.


Ya yi shiru kawai yana kallonta, hannunsa riƙe da rattle yana karkaɗawa. Gashin ta ɗaga tana kallo. A take ƙwayar idonta ta sauya kala zuwa ja. Sannan ta kalli Hilal, ta buɗe baki da shirin yin magana, fiƙoƙin haƙwaranta na sama suka ɗan ƙara tsayi kaɗan.


“Na gode Hilal. Saboda da ban haifeka ba da ba zan zama ta hannun daman shugaban bayin shaiɗan ba. Ina sonka!”


Ta ƙarashe tana shafa gefen fuskarsa. Shi dai kallonta yake kawai, kamar me fahimtar abin da take faɗi. Mariya ta janye hannunta daga kansa, sannan ta yi amfani da ƙarfin tsafinta ta tura car toy ɗin nasa inda take da.


Ta miƙe ta fita daga falo, ta zagaya bayan gidan, sai ta tsaya ta waiga hagu da dama, sanna ta rufe idonta, ta ɗora hannunta a bayan wuyanta, inda tambarin ƙungiyarsu ta bayin shaiɗan ke zane a wurin. Sannan ta furta.


“Mishk baksh hushk!”


Bata kai ga rufe bakinta ba wani farin matashi ya bayyana a gabanta, sanye da jajayen kaya. Idonta ta buɗe ta kalle shi, sannan ta miƙa masa gashin Hilal.


“Saƙo ne zuwa wurin Wahash!”


Matashin ya karɓi silin gashin guda ɗaya. Sannan ya kalleta.


“Saƙo zai isa ga shugaban bayin shaɗan!”


Yana gama faɗin hakan ya ɓace ɓat kamar almara. Tunawa da cewar yanzu haka ta kusa zama ta hannun daman Wahash ya sa ta yi murmushi. Sannan ta saka yatsun hannunta biyu cikin bakinta, ta fito da reza sabuwa daga ƙasan harshenta. Cike da nishaɗi ta shiga juya rezar tana murmushi.


Har ta koma falon ta zauna. Bata daɗe da zama ba wayarta ta shiga ringing, ganin Daddy ne me kiran ya sa ta ɗaga tana saita nustuwarta.


“Barka da safiya Daddy. Ina kwana!”


Ta gaida shi cikin sanyinta. Kuma cikin kamalarta dake burge kowa da ita. Daga ɗayan bangaren Daddy ya amsa sallamar, sannan ya faɗi abin da ya sa ya kirata.


“Yau da daddare ina son ganinku ke da mijinki!”


Ta tatare girarta wuri guda. Zuciyarta na raya mata ko dai Faruk ne ya je ya kai ƙararta?. Sanin zurfin ciki irin nasa ya sa ta kore wanna zargin, dan tana da yaƙinin cewa ba lalle ace ko Hajiyarsa ta sani ba ballantana Mu'az ya sani, har a je ga kan Daddy.


“To Daddy, bari na sanar da shi”


“A'a, ba sai kin yi hakan ba. Dan na faɗawa Mu'az ya sanar masa”


Ta gyaɗa kanta. Daga haka suka yi salama. Tunani barkatai a ranta. Dan ta kasa hasaso dalilin da ya sa Daddy ke son ganinta ita da Faruk.


*FCID (Force Criminal Investigation Department), Moshood Abiola Road, Garki, Abuja.*


MUKTAR POV.


“Wallahil azim da gaske nake muku yallaɓai!. Wallahi ba ni na kashe Munira ba!”


Faɗin Mubarak saurayin Munira. Yayin da yake zaune a cikin ɗakin tuhuma na headquartern. Muktar da ya sa shi a gaba da tambayoyi, ya harɗe hannayensa a ƙirji, yana daga tsaye a kan Mubarak ɗin da tsoro ya sauyawa kamanni.


“Ni ma ban ce ka kasheta ba. Amma me ya kaika hotel ɗin a waccan ranar, da har ka tura mata saƙo ta wata lambar da ba taka ba?”


Mubarak ya haɗiye miyau. Sanna yace.


“Eh, na... Na tura mata da saƙo ne saboda ina so mu tattauna wata magana ni da ita!”


“Amma me ya sa ka tura nata saƙo da baƙuwar lamba, saɓanin wadda ka saba amfani da ita!”


A tsorace yace.


“Sati biyu kafin lokacin aka sace min wayata a Almart farm. Kasancewar ba ni ne wanda ya yi rigistern waccan layin nawa ba ya sa na jinkirta yin welcome back. A maimakon na zauna haka sai na siyi wani sabo na fara amfani da shi!”


“Me ya sa ka zaɓi haɗuwa da ita a hotel. Saɓanin gidansu ko wani wurin da ban”


“Da... Dama... Da dama!”


Suna haɗa ido da Muktar ya ji cikinsa ya saki ƙarar tsoro. Ganin yana kame-kame ya sa Muktar ya saki hannayensa. Sannan ya ɗora su a kan table ɗin dake wurin.


“Zai fi maka kyau ka sanar da ni komai. Tun kafin nasa a kaika ɗakin horo. Dan wallahi ka ji na rantse idan ka je can ba za ka fito da kammaninka na asali ba!”


A take Mubarak ya soma hawaye, ya haɗiye miyau ya fi sau ƙirgen yatsunsa. Ganin babu sarki sai Allah ya sa ya buɗe baki ya faɗi gaskiya.


“Ƙwarai. Na kirata hotel ne saboda ina so mu sasanta wata matsala da ta shiga tsakanina da ita. Bayan ta zo sai na nemi da ta bani kanta. Hakan ya sa muka yi wani sabon faɗan da ita. Har ta bar hotel ɗin ranta a ɓace yake. Amma daga wannan ban san komai ba yallaɓai...”


Ya kai ƙarshe yana fashewa da kuka me sauti.


*


“Duk abubuwan da ya faɗa gaskiya ne. Saboda na sa an yi bincike a Almart farm, inda yace an sace masa wayar, kuma masu gadin wurin sun tabbatar da hakan. Dan sun ce a lokacin da aka rasa wayar su ya fara sanarwa... Shi ya sa tun farko ni ban yi zarginsa da kashe Munira ba. Tun bayan sanda muka gano cewa shi ne wanda ya aiko mata da saƙo kan ta zo ta same shi a hotel ɗin!”


Muktar ya korowa Faruk dake jiransa a office tun ɗazu bayanin, bayan da ya baro ɗakin tuhuma. Faruk ya sauƙe numfashi. Yana jin ko ina na duniyarsa na ƙara cika da hargitsi. A gida Mariya da matsalolinta, a waje kuma damuwar mutuwar Munira.


“So yanzu me nene mataki na gaba?”


Muktar ya sauƙe numfashi, sannan ya ɗora hannayensa a kan table ɗin da ya raba tsakiyarsu da Faruk ɗin.


“Duk wani CCTV camera footage na hotel ɗin an goge shi. Hakan ke nuna cewa wanda ya aikata kisan ya iya takunsa. Amma kuma duk da haka ya tafka wani kuskure da zai iya sawa mu kama shi cikin sauƙi!”


Cike da zaƙuwa Faruk yace.


“Wani kuskure ya aikata?”


“Duk yanda mai laifi zai yi wurin binne laifinsa a ƙarƙarshin ƙasa yana kuskurewa ta wata hanyar. To haka shi ma wannan ya kuskure. Domin akwai ɗaya daga cikin masu aiki a hotel ɗin da muka tambaya, ta sanar mana da cewa ta ga sanda Munira ta fito daga ɗakin da Mubarak ya kama. Amma kuma kafin ta kai ga sauƙa ƙasa ta tsaya a ƙofar ɗaki me lamba 24. Sannan ita matar tana zargin cewa akwai abin da Munira ta ga a ɗaki me lamba 24, wanda zai iya zama sanadiyyar mutuwarta!”


Girar Faruk na tattarewa wuri guda ya furta.


“Ban gane ba Muktar!”


Muktar ya jinjina kansa.


“A ranar da Munira suka haɗu da Mubarak aka kashe wani ba'indiye a cikin hotel ɗin, me sunan Danesh Kumar. Danesh Kumar shi ne mutumin da ya kama ɗaki me lamba 24. Idan har za ka iya zurfafa tunaninka. Za ka iya gane alaƙar zance na da kuma mutuwar Danesh!”


Faruk ya yi shiru. Can kuma yace.


“Idan na fahimta dai-dai, wata ƙila a sanda Munira ta baro ɗakin da Mubarak ya kama ta ga sanda aka kashe Danesh, ko kuma ta ga masu kisan, ko kuma ta ma san wanda ya yi kisan, shi ya sa ita ma aka bita aka kasheta!”


“Wanna shi ne abin da bake so ka gane”


“Amma abin tambayar a nan shi ne. Me ya sa makashin ko makasan ba su kasheta a nan cikin hotel ɗin ba, sai da suka bari ta fita, sannan kuma suka bita suka saceta. Sai kuma kirana da ta yi a waccan ranar, kafin su saceta!”


“Idan za ka iya tunawa tun farko na sanar maka da cewa masu gadin hotel ɗin sun sanar mana da cewa Munira ta bar hotel ɗin. Kuma a ƙafa, saɓanin sanda ta shigo wurin da mota, ka ga wannan ma zai ƙara tabbatar mana da cewa lallai akwai abin da ta gani. Shi ya sa ta ruɗe har ta manta da motarta da ta je wurin da ita. Kuma wata ƙila makashin yana ganin idan har ya kasheta a hotel ɗin asirinsa zai iya tonuwa. Shi ya sa ya zaɓi ya barta ta fita daga hotel ɗin, domin ya kauda tunanin jami'an tsaro kan alaƙar kisan Danesh da na Munira. Kuma ya zaɓi sace ma duk akan wannan dalilin. Batun kiranka kuma zai iya kasancewa ta gane makashin na bibiyarta, shi ya sa ta kiraka dan neman taimako!... Amma duk da haka akwai lauje cikin naɗi! Sai dai na maka alƙawarin gano shi nan ba da jimawa ba abokina!”


Faruk ya sa hannayensa duk biyu ya shafa fuskarsa zuwa ƙeyarsa. Ya furzar da iska yana jin kansa na ƙara dulmiyewa cikin kogin matsaloli.


“Yanzu abin da za mu yi nagaba shi ne gano ainahin inda aka saceta. Kuma za mu iya gane hakan ta hanyar wayarta. Dan a lokacin da ta kiraka aka saceta!”


Faruk ya gyaɗa kansa. Kafin ya miƙe ya bawa Muktar hannu suka gaisa, haka ya bar headquartern da nauyin zuciya, ya nufi barrack.


MU'AZ POV.


“Shigo!”


Ya bada umarnin bayan da aka ƙwanƙwasa ƙofar office ɗinsa. Kansa ya ɗaga ya kalli me shigowar. 


“Sir!”


Sojan da ya shigo ya faɗi yana sara masa da hannunsa na hagu. Mu'az ya aje pen ɗin dake riƙe a hannunsa yana kallonsa.


“Dismiss!”


Sojan ya sauƙe hannunsa.


“Barka da safiya sir”


“Barka. Eze me ya sa jiya baka je duty ba?”


Ya tambaya yana shafa fatar bakinsa. Sargent Chiku Eze ya washe baki, sannan ya yi taku biyu zuwa jikin table ɗin Mu'az, ya aje masa containerr da ya shigo da ita. Mu'az ya kalli containerr, sannan ya kalli Eze. Da ido ya masa alama da wannan fa?. Eze ya sosa ƙeya yana faɗin.


“Eh Sir. Grilled fish and potato ne matana ya girka maka!”


Mu'az ya yi murmushi. Wai shi za'a bawa cin hanci da abinci. Sai ya sauƙe hannunsa a kan bakinsa, sannan ya kai hannu ya buɗe containern. Ba tare da tunanin komai ba ya fara cin abincin. Yau abinci ne fa, ai ba yaƙi ci ba. 


“Oh lord of mercy! Matarka ta iya girki Eze!”


Ya faɗi yana kai loma. Eze ya yi 'yar dariya, ganin dabarar kawowa oga cin hancin abinci ta yi aiki. Dan shi kam baka isa ka siye shi da kuɗi ba. Ko da ace shi ba shi da kuɗi kowa ya san irin arziƙin mahaifinsa. Kasancewar ɗan kasuwa ne, kuma tsohon ministern kuɗi a Nigeria.


Sai da Mu'az ya kusa cinyewa, sannan ya miƙe tsaye, hannunsa riƙe da containerr. Ya nufi Eze dake tsaye har zuwa lokacin. Sai ya dafa kafaɗarsa suka fita zuwa wajen office ɗin. Kuma har zuwa lokacin yana cin abincin.


“Eze me ya sa jiya baka zo aiki ba?”


Ya kuma dawo masa da tambayar ɗazu. Lokaci guda yanayin fuskar Eze ya sauya daga fara'a zuwa mamaki da tsoro.


“Sir... Sir da ma. Matana ne ba shi da lafiya”


Mu'az ya kai loma yana gyaɗa kai.


“Na fahimta. Amma kuma ya aka yi matarka ta yi girki yau. Ita da bata da lafiya. Ko dan manta da wanan batun, ai lafiya ta Allah ce, haka ma jinya, zai iya ɗorawa kowa ya kuma sauƙe masa s sanda ya so, haka ne ba?”


Ya tambaya yana ɗage masa gira. A tsorace Eze ya gyaɗa kansa.


“Eh haka ne. To amma me ya sa baka sanar ba. Ai ya kamata ace ka sanar da mu. Yanda matarka ta iya girki irin wannan ai ya  kamata ace na je na dubata!”


Eze ya kuma haɗiye miyau. Sannan yace.


“Sir! Sir”


“Ya isa. Na san haka kawai ka ƙi zuwa duty. Kuma wannan abincin bai isa ya hanani sakawa a maka hukunci ba. Dan haka ka je wurin lieutenant Bala, ka ce na ce a maka bulala hamsin!”


A take Eze ya fara rawar tsoro, hawaye suka zibo masa.


“Sir dan Allah ka yi haƙuri. Na tuba Sir, ba zan sake ba!”


“Hamsin ta yi yawa. Tun da ka haɗani da Allah ka je a maka talatin. Idan ka kuskura ka sake magana kuma zan sa a ninka maka ita, daga talatin zuwa wasu masu kamarta sau uku. Na san ka iya lissafi!”


Eze ya ja bakinsa ya yi shiru. Ya sara masa a tsorace, sannan ya juya ya fita daga sashen office ɗin nasa. Mu'az na tsaye a ƙofar office ɗinsa yana cin abinci Faruk ya shigo.


“Yanzu ba za ka iya haƙuri ka ci a zaune ba MJ?”


Mu'az ya kalle shi yana cusa loma a bakinsa. Kafin ya miƙa masa containern.


“Za ka ci ne?. Amma fa kayan haram ne, cin hancinsa aka kawo min!”


Faruk ya yi murmushi yana girgiza kai.


“A ci daɗi lafiya. Ni ba na ci”


Ya faɗi yana shirin wucewa, amma sai Mu'az ya dakatar da shi.


“Daddy yace yau yana son ganinku a gida kai da Mariya!”


Cak Faruk ya tsaya. Sannan ya juyo ya kalle shi.


“Fatan dai ba wani abin ne ya faru ba?”


Mu'az ya girgiza kansa alamun bai sani ba. 


“To Allah ya kaimu an jima ɗin. Zamu zo”


“Sai kun zo”


Mu'az ya faɗi yana shiga office ɗinsa. A kan table ya aje containern da ya cinye abin ciki tas. Sannan ya shiga banɗaki ya wanke hannunsa da bakinsa. A sanda ya dawo cikin office ɗin ya ja ya tsaya yana kallon Yasmin da bai ji shigowarta ba. Yasmin na ganinsa ta miƙe tsaye.


“We need to talk MJ!”


“Bani da wannan lokacin Yamin. Na sha faɗa miki cewar kada ki sake zuwa office ɗina. Bana tattauna abubuwan da suka shafi rayuwata a office, ki bari idan na koma gida sai ki zo mu yi magana!”


Ya kai ƙarshe yana zaunawa a kan kujera. Takaici ya sa Yasmin cewa.


“A nan nake so mu yi maganar, saboda bana jin za mu sake haɗuwa bayan yau!”


“Mutuwa za ki yi ke nan?. Yasmin bai kamata ki kashe kanki a kan wanda bai damu da ke ba!”


Yasmin ta kai hannu ta goge ƙwallar da ta zubo mata.


“Ko kaɗan ban taɓa tunanin kashe kaina ba, domin kuwa da ace zan yi hakan da na yi tuntuni. Nan da next week zan tafi Cairo, zan je na ƙarasa makarantar da soyyayarka ta hanani ƙarasaww!”


Mu'az ya yi dariya.


“Da kuwa kin taimaki kanki”


Yasmin ta kuma goge ƙwalla.


“Mu'az ya kamata ka ji tsoron Allah. Ko da kaɗan ne ya kamata ka nuna kulawa ga wanda yake sonka...”


Ya nuna kansa yana faɗin.


“Ni? Ni kuma me na yi bawan Allah?”


“A'a, ba ka yi komai ba, ni ce wadda ta yi kuskuren fara sonka, har ina zaton cewa wata rana kai ma za ka fara sona. Ashe na aikata babban kuskure. Mu'az ina maka addu'ar Allah ya ɗora maka son da zai wahalar da kai. Allah ya sakawa zuciyarka son da zai sa ka yi ƙoƙarin kashe kanka. Allah ya sa maka son wadda za ta hana rayuwarka sukuni, Allah ya saka maka son da zai gana maka kwatankwacin azabar da ka bani. Allah ya ɗora maka son da zai sa ka ga fari ka ce baƙi ne. Wata ƙila a lokacin za ka fahimci irin abin da nake ji. Bana maka addu'ar fara son wadda ba ta sonka, dan nasan yanda raɗaɗin son ma so wani yake. Na barka lafiya!”


Ta ƙarashe tana ɗaukan jakarta da ta aje a kan table sanda ta shigo office ɗin. Kuma har ta fice Mu'az bai ce mata ƙala ba.  Dan shi yana farin cikin ficewa daga rayuwarsa da za ta yi. Kuma ko kaɗan bai sa a ransa cewa addu'o'inta za su bishi ba. Tun da ya san shi bai zalunceta ba.


_Share fi sabillilah❤️_


*Daga alƙalamin Salma Ahmad Isah✍️.*

 *CANDY CE🦋.*




Post a Comment

0 Comments