TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Sanyi da zafi page 8-9

 💫 SANYI DA ZAFI 💫

✍🏻M SHAKUR


EPISODE 8️⃣


BAYAN 1YR!!


Cikeda natsuwa wasu manya manyan fadawa ke bude wani hamshakin kofa da girmanshi zaiyi girman wani karamin gate daidai karfe sha daya na safe, sannan dukansu suka fadi suka zube suna daga hannu irin yanda dai fadawa ke gaisuwa suka fara zuba kirari.

“Lafiya jakadan Baba Ali dan Baba Ali! Lafiya mai kiran gabas da yamma! Lafiya jinjirin wata sha kallo! Lafiya kwankwason jimina mai wuyar shafawa! Lafiya Garkami Wandon Karfe! Lafiya jijigen addini! Lafiya toya matsafa! Lafiya baya goya Marayu! Lafiya toron giwa! Lafiya tufaniyar gabas! Lafiya jinjirin wata shakallo! Taaaakawanka lafiya sarkin mu sarkin Riyad zakaran gwajin dafi mai hasken zuciya da hasken aura!, lafiya dan lellen Mai Babban daki…..”

Tunda suka fara kirarin nan kusan good 10min sai yanzu wani dogon mutum yafito yana sanye da wata milk kokuwar alkyabba dahar walkiya takeyi tsabagen kyanta ga rawani dawani white yadi mai kyau dake walkiya akamai, inda farare tarrr na idanunshi kake iya gani, hannunshi yarike wata sanda mai kyau, rabon da mutanen gari da yan fada suga fuskanshi shekara daya kenan, tun kafin yakaraso inda suke turarenshi yagama gauraye wajen da kamshin dadi dake dauke da yalwataccen ni’ima, ahankali yake tafiya kaman baiso yataka kasa, wani irin kwarjini shiganshi ke dauke dashi da bamaka iya kallonsa, har ya iso inda suke ya tsaya chak na kaman 5secs ya kallesu one by one to check idan kowa is healthy fine and present wanda hakan yana daga cikin abinda yasa jama’a ke sonshi, kaman baiso ya furta magana yace “kun tashi lpy”? Kaman jira suke. “Lapiyanmu kalau Sarkin mu mai adalaci, sannu sannu toron giwa tsintsiya madaurinki daya!” yanda jikinsu har rawa rawa yake sunamai kirari suna yabashi ya kalla sannan kawai yawuce duk suka biyoshi abaya, direct fada suka shige inda mutane suke cike makil wajen zama yayi ya zauna, batare daya hada ido da kowa ba this is mostly method dayayi adopting dayake samai natsuwa cus dazaran ya shigo fada he sees love hatred envy a idanun mutane da dama barinma yayanshi Kabeer, but koda wasa baitaba disrespecting yan uwanshi ba, and so far so good Kabeer din has been supportive bai bashi wani matsala ba haka ma yayyin babbanshi da Waziri ana koyamai komi everything is going smooth Alhamdulillah.


Munir sai kallonshi yake bayan yazauna, yadade baiga sarkin da mabiya keso kaman Riyad ba, anason Baban su but son da akema Riyad daban ne, har lakabi akamai da Sarki me farin jini, dudda akwai yan adawa but wlh ana sonshi barin yan cikin gari, cus kafin ma yazama sarki yana taimako sosai yasaka yara a school da dama, yanzu kawai dan he’s not happy about zama sarkin sai the whole abu yasa he hardly talks, yakara miskilanci da wulakanci fiye da da, he’s so angry sabida he’s feeling kawai responsibility akasamai akai da baya so, responsibility daya tsaya and funny enough he’s doing so good da leadership din saisa har yanzu an kasa fadin wani negative abu akanshi ko kokafadi babu wanda zai yarda ma though yasan alot of people na jiransa to just make a mistake ne and he pray dan uwanshi will not make that mistake dasukeso suke kuma jira yayi.


Almost 2hr yayi afadan sannan aka tashi yakoma side nashi, bayan an bude katon kofan nan kaman gate still akwai tafiya kafin asalin babban gininshi, baya mulki like others, he hardly let anyone a side nashi, daga Muneer sai Mom da Haleema.


Shida Muneer suka jera fadawa na binsu abaya ana kaiwa gate din kowa ya tsaya dan babu bafaden dake shiga ciki ko matarshi bata isa tashigo side dinba without izininshi, sake bude another door sukayi that will lead them to compound din da interlock ya cika ko’ina ga bishiyan mango dake wajen da flowers ko’ina sai wata arniyan jeep bulletproof dake compound din gawani secret gate dayake wajen any private outing tanan yake fita.

Shiga mainflat din sukayi WAN’ı irin crazy sitting room ne dakeda fadi na bala’in yasha funitures that are very beautiful, zama Muneer yayi yadauki laptop dake kan table yace “almost 2yrs bake leka hotel ba Riyad, its only right kaje mana” wucewa sama yayi dan yaje ya cire kayan nan dasuka isheshi.


Binshi da kallo kawai yayi kafin ya shiga replying mails, kai tsaye aka shigo falon dasauri Muneer yadago kanshi dan mamakin waye ya isa yayi hakan ganin Mom tana sanye da wani alkyabba da akayi da crystal yasa yadan taso yace “ina yini Mo….” Baima karasa gaidataba tawuce stairs tai sama fuuu.


Riyad yariga yasaka wandon wani yadi brown da farin singlet ajikinshi yana kokarin saka rigan aka bude kofan bedroom nashi, dago kanshi yayi suka hada ido da Mom data haderai kana ganinta kasan ranta abace, dan lumshe idanu yayi yakarasa saka rigan Mom takaraso ciki har zuwa gabanshi dab dashi ta tsaya cikin tsananin bacinrai tace “yau kwanan ka nawa rabonka da shiga turakan Haleema Riyad”? Hannu yamika ya dauki agogo daga saman bed yana kokarin sawa yace “Mom kinsan I’ve been busy dealing with lot of things, my business, this sarki thing, everything ma” “and so?” Mom tai maganan da fushi tana daga murya tace “sabida business da sauransu bazaka kula matanka ba kusan 1months da 1week baka shiga gidan ta ba, and baka bari ta shigo nan ba, sai gulma ake tell me menene banbancinka da su Muneer da basu da mata”? Dan yatsine fuska yayi still baice komiba yadauki links na hannun riganshi yana kokarin sawa Mom ta fizge links din cikeda masifa tace “Riyad wlh zan mugun sabamaka I hate this new attitude din naka, I’m talking to you baka kulani, ka shiga turakan Haleema koka kirata tazo nan your choice, people are watching and you know that, 1yr kenan kunyi aure ba ciki and it’s all thanks to you, ni bantaba ganin mai gudun mace har mace ba sai kai, badadan na tambaya tacemin kalau kake functioning ba dana fara tunanin kokai mace ce” sauke kanshi yayi kasa yayi shiru why will Mom be asking Haleema irin this kinds of question? Ahankali kanshi na kasa yace “kiyakuri Mom” cikin fushi tace “nayakuri nayakuri me? Get your wife pregnant nagayamaka dagayau nakaraji kun raba kwana” ta ijiye links din akan gado tajuya zata wuce hartakai wajen kofa zata fita ahankali yace “Mom” juyowa tayi tamai wani mugun kallo saikuma ahankali ta tako zuwa gabanshi ta tsaya tana kallon kwayan idanunshi, ahankali takai yatsanta tadaura kan kirjinshi cikin kakkausan murya tace “ni mahaifiyarka na umarceka dakai tarayya da matarka, make her pregnant within period na this sabon month da aka shiga, inba hakaba wlh saika gamu da fushina sosai Riyad” tajuya fuuuu tafice yadade tsaye ahaka idanunshi sunyi jaaa mode nashi ya chanza, he hates yanda Haleema tells Mom literally everything about marriage nasu, koma yace he hates yanda Mom ask everything akan aurensu, he hates both kawai, yana bala’in son sirri, he loves everything about shida matarshi nazama about them, anytime yakalli Haleema he doesn’t even feel like shine mijinta, he feel like Mom ne mijinta, kokarin saita muryanshi yayi yadauki wayanshi dake kan gadon, Munir yakira cikin muryanshi da bata fita sosai tsabagen bacin rai yace “ka aika akiramin Haleema pls” yana maganan ya katse wayan, tashi Munir kawai yayi yafice bayan yabada sakon yashiga mota yabar gidan cus yaji komi da Mom tafadi he just pity his brother, Mom is just over controlling Riyad, she’s in his matter, and baya iya cemata no, itakuma Haleema akanme zata dinga gayama Mamanshi komi gameda aurensu? Sabida taga baya iya tsallake maganan Mom ne, haba it’s annoying mana, Riyad dakeda kunya tagama fallasashi, it doesn’t matter koda Mamanshi ne some private mata barinma harkan auratayyan su baikamata Mom tama sani ba, the girl is sick wlh batasan menene boye sirrin mijinta ba, dashine matarshi tamai haka Allah he will deal with her, yayi tsaki aranshi.

Office yawuce abinshi inyaso yasameshi daga baya.

 💫 SANYI DA ZAFI 💫

✍🏻M SHAKUR


EPISODE 9️⃣


Zaune take a arnen falonta takara kiba yanzu ba kaman da datake so skinny ba, tayi bulbul taciko alamun Riyad ya iya kiwo tasami kwanciyan hankali, wasu bayi ke gyara mata farcen kafa jakadiya ta shigo zubewa tayi tace “Gimbiya Mai Martaba ya aiko akiraki chan bangaren sa” wani irin farin ciki daya lullubeta batasan sanda ta karbe kafanta ba ta mike da sauri tai sama bedroom nata ta shiga tana kiran wayan Mom awayanta kiran iPhone 15, ringing daya Mom ta daga Haleema tai wani ihu tace “Mom I love youuuu, you’re the best Mom, Mom wlh ina sonki sama da tawa Mamar ma, Mom dabanda ke da narasa gata, dana shiga uku, kinga Mom yanzun nan Mai Martaba ya aiko akirani kinmai magana ne?” Dan murmushi Mom tayi mai sauti kanta nawani swelling yanda Riyad baya tsallake dokanta, she just wish kowace uwa zatasami yaro mai taushin zuciya da jin maganan mahaifiyarshi irin Riyad kawai baya jure fushinta ko kadan ne, koyaya tace yayi abu kobayaso sai yayi, shi kawai baison commitment ne da nauyi akansa baison damuwa baison hayaniya but tace yayi kaza saiya yayine, murmushi tasakeyi tana wani ji da kanta tace “Madallah! sai a kimtsa aje, ki farantamai rai” gyadama Mom kai tayi cikin mugun farin cikin dan tana mahaukacin son Riyad tace “Mom banda kamarki me sharemin kukana, Mom thank you for making my husband to call me, bye Mom I love you” katse wayan tayi itakuma Haleeman cikeda jin dadi ta shiga shiryawa, tasha wasu magungunan da Jakadiya ke hada mata ta shiryata tsaf cikin wani hadadden atampa golden, ta daura Al kyabba akai ta feffesa turare sannan sauko kasa, Jakadiya da kuyanginta jaka biye da ita har zuwa side dinshi dayake da dan tazara tsakaninsu, tana zuwa dayake ansan da zuwanta aka barta ta shiga ciki Jakadiya da kuyangin kuma suka tsaya waje, shiga flat nashi tayi ko’ina na falon kamshin shi yake, murmushi tayi ta maida kofa tarufe sannan tacire Al Kyabban ta ijiye kan kujera tawuce sama tsayawa tayi gaban bedroom dinshi tai knocking.



Kusan 2min tayi wanda inda sabo ta saba jira haka duk sanda tai knocking, chan taji muryanshi ciki ciki cikeda isa yace “come…..in” bude kofan tayi gently ta maida kofan tarufe ta shiga dakin dakin tana tafiya ahankali sabida duhu gaske but tana iya ganinshi zaune bakin gado ya tsareta da idanu dake shinning even in the dark saida gabanta yafadi tadai daure ta maida takaraso zuwa gabanshi cikin yar kankanuwan murya dake cikeda yanga da iyayi tace “barka da warhaka Mai Martaba, kayi aike akirani gani” mikewa tsaye yayi yazuba mata ido, chan yace “how many times nagaya miki kidena kaima Mom maganata?” Faduwa gabanta yayi ta daure bata nunaba, cikeda makirci tace “ni kuma?akanme zankai karan mijina?” Wani kallo dayake mata yasa batasan lokaci da lips nata yashiga rawa ba, ganin yariga yagane ita tafadi tace “yes nagayama Mom baka zuwa wajena kuma ko nazo baka bari a barni na shigo? Kayakuri nayi kuskure bazan karaba, wlh bana iya bacci ne, narasa yanda zanyi dakaina” saikuma asanyaye tace “i need youu…”  wani kallo ya mata yace “and sabida hakan saki hadani da Mom”? Ahankali tace “magananta kadai kakeji saisa nagayamata amman kaya kur…” bata karasa maganan ba yawani kalan hankadata kan gado dasauri ta juyo ganin yana bude mazariyan wando wlh har cikin ranta taji kaman tai ihun dadi tadai daure tai shiru tana jiranshi, kafafunta yaja cikin fushi yace “you reported me sabida this I hope nabaki shikenan” ya kwashe skirt nata sama yadage rigan sama addu’a yayi  yashiga ciki, runtse idanu Haleematu tayi tanaji kaman zata shide, wata daya babu abinda ya shiga tsakaninsu sai yau.


Almost 1 good hour yayi cur akanta not because of kanshi but her, ya sauke hakkinta daga kanshi tunda harta fara kai karanshi, saida yaji ta bushe ya tabbatar idan yacigaba zafi kawai zataji sannan ya kyaleta sannan yatashi zaune kafin chan yamike tsaye yawuce bayi ya barta kan gadon wani mugun bacci na daukanta tana numfashi haryau takasa gane kan Riyad, zai iya 2month bai nemeta ba yawanci saitasa Mom a case nasu yake nemanta and he’s so damn good in bed Innalillahi! The way he’s this quiet bazaka taba tunanin zai iyacin mace ba, but en anytime yayi having wani abu da ita jitake kaman she’s the luckiest gurl on earth, Riyad is good on bed, she don’t even know how to explain, yana wasa da jikinta wani kalan dirty play fa, yauma haushin abinda tayine yasa bai tattabata yanda ya sababa, wlh haryau takasa gane yanajin dadin ta ko bayajin dadinta oho ko gurnani bayayi bai tabayiba, he’s just super wired guy data kasa fassara halinshi haryau, and wiredness dinshi ke kara mata sonshi sosai aranta wlh, ahaka tana lumlumshe idanu bacci yayi awon gaba da ita.

**



Around 5 Mama ta tadata daga bacci, da kyar ta tadunma Mama, Mama tace “ke yarinya sai nauyin bacci kaman wani kato, tashi kin manta yau zaku koma makaranta eh? Hope kin dauki permission wajen aiki an baki shift na yamma”? Gyadama Mama kai tayi cikin gajiyan bacci, hannu Mama tasa tadagota ta taro kafadanta hakan yasa Rashida tasauke kanta akan kafadar Mama tana kara lumshe idanu still cikin bacci, dan jijjigata Mama tayi tace “Rashida” ahankali tabude idahunta tass takalli Mama dasu Mama tace “I think drop most of ayyukanki tunda kin koma school kinga yanzu year 5 kike you need to study well, nakosa naga diyata tazama likita, saura 1yr yanzu, Allah ya aramin rai, ranan super wax zan saka amin combination da super lace” dan murmushi kadan Rashida tayi tanason taji Mama na maganganu haka it makes her happy, Mama tace “yanzu dai kinga kina bukatan lokacin hutawa da lokacin karatu bakiga yanda kike gajiya ba da kyar kike tashi, ki saki sauran ayyukan ki rike na hotel din nan kadai tunda anfi biya, su Maman Miwa da sauran wajajen nan ki sakesu” dan murmushi tayi sai kawai tahau yunkurin tashi ahankali dan muryanta baya fita sosai sabida daga bacci ta tashi tace “Mama so kike na bar aiki sabida mudinga karban abincin sadakan da yan anguwan nan suke kawo mana out of pity?” Tadanyi shiru daidai takarasa mikewa tsayen batare data kalli Mama ba tace “this year is clinicals, zamuyi aiki a pediatric da obstetrics&gynecology, I can manage everything Mama trust me, Alhamdulillah kome aka koyamin sau daya ya zauna akaina, sannan daga yanzu koda ranan Sunday ne zan dinga zuwa library duk sati sau daya nayi muraji’an duka abinda aka koya mana na that week, I can study Mama, I can do my duties na kula dake da siyamana kayan abinci da kudin magunguna, I can manage my work also” tana maganan tayaye labule tafita daga dakin tawuce waje saida tafara sa abinci awuta sannan tawuce bayi tayi wanka tafito lokacin har sanwan yayi tazuba taliya sannan takoma daki tashiga saka kaya Mama na zaune kan dadduma tana kallonta, tana kallon yanda taketa ciro kayan ghana masgon dasuke agoge daga gani kasan dan kaya mai kyau take nema na zuwa school abu Mama taji ya tsaya mata a wuya sai kuma ta daure kawai ta dauke kanta daga kallonta.

Wani doguwan rigan atampa maroon ta zaba ta maida gefe, taciro lab coat nata dayake a goge shima ta ijiye gefe sannan ta maida sauran kayan ta shirya tsaf tawuce tafita tasake juya taliyan sannan tadawo tasa hijabi ta kabbatar salla.


Tana idarwa bata tsaya yin azkar ba ta fita ta juyo taliyan a kula tasama Mama ruwan zafi na wanka sannan tadawo tasake zama kan dadduma tafara azkar tana gamawa ta kalli Mama dake kallonta tace “Good Morning Mama na nikadai, Mama naji dadi nikadai kika haifa nake moreki banda kanni dazaki dinga raba attention naki akanmu” most time tana maganan ne idan taga abu na damun Mama dan tasata tai murmushi, ganin Mama batai murmushi ba yasa takama hannunta tarike dasauri ahankali tace “Mamaaaaaaa” tai maganan ashagwabe tana lankwasa kai, ijiyan zuciya Mama ta sauke tace “babban burina arayuwa shine ki zama likita Rashida, banson wani abu dazai hanaki zama, kina bukatan lokacin dazaki karatu, banson ki fadi, banson ki sami carry over, nasan kinada kokari but dudda haka karatu yanada amfani, kina all this ayyuka bazaki sami lokacin yi ba, ki manta da kula dani Allah daya tsaga mana baki bazai hanamu abinda zamusa abakin ba, after this year next year zaki gama, please Rashida kibar ayyukan nan and focus a karatu” tunda Mama ke maganan take kallonta batason sata cikin damuwa hakan yasa tace “to naji Mama amman tunda kinga satın nan muka koma karatu da practicals bazasuyi serious ba kibari nayi aikin zuwa karshen wata abiyani kudina saina dena kinji, zancen night shift ai HOD mu tasan dani bata taba sani a night shift ba sabida ke Mama, so ko yanzu ma bazan bazanyi night shift ba, kinga na karbi albashina saimu ijiye, kuma Mama kidena damuwa yarki ta dauko brain dinki bazan fadiba In sha Allah bayan kinamin addu’a, to yanzu kin hakura na karasa zuwa karshen watan nan duk sai na saki aikin nabar na hotel din?” Shiru Mama tayi tana kallonta Rashida da taurin kai da kafiya hmm, ijiyan zuciya tasauke tace “okay! Yau sha uku ga wata, karshen wata zaki sallame kowa, next month banson ganinki kina zuwa ayyuka nan” gyadama Mama kai tayi tace “naji” tashi Mama tayi tace “ai shikenan” tawuce sip wani akwati zata dauko dasauri Rashida ta tashi tace “Mama stop ki kirani na dauko miki” dasauri tasa hannunta tadauki akwatin tasaukar dashi kasa Mama tazo wajen ta zauna itama Rashida ta zauna gaban box din tana jiran tadauki abinda zata dauka tasake daukan akwatin ta maida sama, wata yar jaka Mama tadauko acıkın box din tamika mata tace “gashi ungo” dasauri Rashida ta kalli jakan data bata tace “na menene Mama”? Tasa hannu tana karba, zage zip din box din Mama tashigayi tace “naki ne kibude” da sauri taciro bakin ledan data gani cikin jakan dayake a kulle tashiga budewa saiga crocs a ledansu pink color mai kyau ba asalin designers one dinba but irin normal wanda ake saidawa a market yan 5k-7k dakuma stethoscope pink shima mai kyau, da mamaki take kallon kayan dakuma murmushi akan fuskanta tama kasa cewa komi Mama ta kalleta tace “bakiso ne oya bani kayana, last month danaje clinic wata Hajiya tarabamana kudi a envelop naduba naga 20k ne shine na shiga kasuwa na siya miki crocs naga shi likitoshi kesawa a clinic dimu duka likitocin wajen shine akafansu shine na shiga kasuwa na sayomiki ashe haka takalmin keda tsada dubu takwas aka saidamin na hada miki da wannan abun gwajin nace nima y’ata tai kaman yan gayun likitocin danake gani a clinic dinmu” hawaye ne yacika idanun Rashida tana kallon Mama na bata labarin Mama takare da “nazo naboyesu nace bazan baki ba sai ranan dazakuyi resuming school” daidai lokacin hawaye ya sauko daga idanunta Mama tace “ke mehaka kuka kikemin”? Kawai rungume Mama tayi da gudu ta kankameta ahankali tace “thank you Mama thank you” shafa bayanta Mama tayi tace “gabaki dayan rayuwanki Rashida nine na cinye miki ita, bakida lokacin kanki, komi kika samu ni, kome kikeyi sabida nine, konace ki sayawa kanki abu bakiyi saisa na saya miki kema ki shiga sahun yan gayu aga y’ata fess fess akara kallonta sabida yanda tai kyau, Allah yakawo miji na gari” cikin shagwaba ta ture Mama tace “ni bazanyi aure ba Mama, bazan taba iya barinki ba” baki Mama ta kama tace “ke kodai zan kaiki gidan zumane amiki rukiya kaman me aljanu bazaki aure ba” gyadama Mama kai tayi tadauki takalminta tana budewa daga leda tace “inhar ban samu mijin dazai yarda na daukeki muje gidanshi tareba ina ganinki ina baki kulawa wlh gara na kare rayuwana ahaka” da sauri Mama tamata dakuwa tace “kinci mai garinku Rashida” dariya Rashida tayi sosai tace “wlh Mama da gaske nake bazan taba rabuwa dake ba Allah Mama” ganin Mama zatai magana yasa ta tashi da sauri tace “bari nasa takalmina” fararen kafanta ta zura cikin crocs din sun mata bala’in kyau Mama tace “Masha Allah Tubarkallah komi kema yarinyana kyau wlh, kinga kafanki aciki kuwa dudda kafan fara ba lalli amman yayi kyau” wani juyi tayi cikin takalmin tace “Mama inason takalmin thank you so much Mamaa, bari na tafi” tawuce tasa doguwan rigan data fito dashi yakamata ya nuna her flat tummy sosai da very full chest nata cus she has boobs kaman Mama, itama Mama harda rama yasa ba’a ganin nata yanzu, dan kwali ta daura tayafa gyalenta tai arranging lab coat nata a bag pack da books da stethoscope da Mama ta siyamata da komi ciki ta goya abaya tasa yar wayanta a aljihun riganta da earpiece tace “natafi Mama” Mama tace “dan Allah kici abinci kinji kada ki manta” dasauri tace “to Mama zanci, bye Mama” Mama tace “ubangiji Allah bada za’a Allah ya taimaka Allah ya tsareki Allah yakuma baki miji nagari”.


Shagon Maman Miwa taje ta gayamata ta koma school da safe zata dinga zuwa aiki, nan da nan tayi wanke wanke ta share ko’ina tai mopping after 8 tagama komi Maman Miwa tabata 2k saikuma ta bata 200 tace “kihau adaidaita kitafi makaranta baki takaba” murmushi kadan tayi tace “nagode Maman Miwa” sannan tawuce tafito MamanMiwa tabita da kallo tace yarinya ga kyau har kyau ba miji.


Adaidaita sahu ta tare ta shiga sai BUK direct department dinsu ta wuce staircase tahau tana tafiya daidai lokacin wani guy da wata young lady kaman mate na Rasheeda suna sanye da kayan gida lab coat a hannunsu na saukowa hada ido Rashida tayi da guy din da sauri ta dauke kai tacigaba da tafiya abinta tana hayowa su suna saukowa hade fuska yarinyar tayi tace “Bilal yaushe zaka fadamin inda kahadamin suprise birthday party”? Gabaki dayan hankalinshi nakan Rashida dake hayowa abinta batare data kara kallon inda suke ba, mintsilin shi yarinyar tayi abaya hakan yasa yakalleta da sauri yace “sorry Layla come again me kikace”? Abu taji ya tsaya mata awuya sai kawai tawuce da sauri tana sauka da sauri yabita da sauri yace “Layla wait common” tuni tafice dan tsayawa yayi daidai Rashida tahau staircase din dayake kai yabita da kallo sabida kyau datamai doguwan atampan riganta yamata kyau over, dudda ko man baki babu a lips nata balle hoda ko kwalli ahankali yace “we’re going to clinic you don’t need to go up kasa zamu” kaman bada ita yake magana ba kala bata cemai ba kawai ta juya tashiga sauka da sauri yabita yace “wai mesa bakimin magana Rashy?” Chak ta tsaya saikuma tajuyo ta kalleshi tace “kada ka sake kuskuren kirana da sunan nan only those that are dear to me ke kirana dashi not you” ta juya, dasauri yabita yace “I don’t understand why exactly you’re angry with me, I told you nace miki ina sonki ne banda knowledge na your mother’s illness, agidanmu baza’a taba barina na auri yar wacce takeda H…….” “Bilal!!!!” Rashida takirashi da karfi ta daga hannu zata kaimai mari ranta abala’in bace tace “the next time bakin nan naka zai ambato mahaifiyata wlh saina zubar da hakoranka! Nataba cemaka wani abu? Nace ka aureni dama? I don’t even know kana existing so go to hell!” Tana maganan tajuya fuuuu yabita da kallo kowa na department nasu yasan Rashida da masifa but shi he just said it badan rashin mutunci ba he was trying to tell her baza’a bari ya aureta agidansu ba knowing Mamanta nada HIV, baza’a taba bari ya auro diyar unholy mace ba, still he was trying to tell her su zama friends dan he was feeling guilty yanda yagama cewa yana sonta last year dan last year yayi joining nasu dan transfer ya karba daga former school dayake medicine a Sudan, sun fara soyayya sosai yan aji sukamai gulma Mamanta nada HiV bai yarda ba dan bata taba fadamai ba saida aka kirashi akace yazo ga Mamanta tazo clinic itama tana wajen Maman shine yaje ko yagani daga ranan yayi ghosting nata yaki kiranta yadaina daukan wayanda kotamai magana a class yayi banza da ita saima yazo yana kula yan matan class nasu sosai danya bakanta mata rai, saikuma during this 2weeks holiday saiyaji wani irin soyayya ta na tasomai yau daya ganta saiyaji tafi ko yaushe kyau sonyayyan yadawomai fresh azuciye kaman yahadiyeta dan wlh duk department nasu baiga me kyanta ba kawai dai no one can approach her ne sabida masifan ta da fitina.



Koda yafito yaga harta shige bus nasu ta zauna taciro yar wayanta ta makala earpiece tasa a kunne sabida yanda zuciya ta ke tafarfasa, ahankali yasauke ijiyan zuciya yawuce wajen motar shi inda Layla take a tsaye tana hararanshi yabude yana mata murmushi yace “wai ke lafiyanki common shiga mota muje” yashiga mota yatada yaja motan Rashida ta kalla sannan tasake sauke ijiyan zuciya taso Bilal last session nasu sabida she thought shine mutum na farko daya sota for who she is dan ta dauka yasan waye ita kowa na department nasu ai yasani so tadauka yasani, tun bata kulashi tafara kulashi sabida yanda yake shige mata, she really liked him suna waya but rana daya kawai yadaina kulata yadaina amsa wayanta yana kula yan matan ajinsu agabanta yana cemusu yana sonsu just to hurt her, abin yamata ciwo sabida tanada kishi but bata taba nunawa ba, bata taba nuna tadamu ba saima daina kallonshi datayi da kallon inda suke cus she’s even blaming herself data budemai zuciyanta bayan tasan duk wanda zatai soyayya dashi baya going anywhere,  idan ba lectures gareta ba earpiece zatasa a kunne tana karatu tanabin everything da aka musu, she’s a fast learner na ban mamaki, takoyama kanta rayuwan she’s enough for herself, she doesn’t need people cus gani take kowa yimata kallon yar mai HIV ake diyar fasuka, babu abinda ba’a kiran Mama dashi har anan ajinsu su ana cewa Mama karuwa ce cus gata kyakkyawa daman, batason wata ko wani yashigo space nata and hurt her saisa she’s always always protecting her space bawai batason tayi kawa bane ko kawance baya burgeta bane, no kawai she don’t wanna get hurt, kawayenta na layinsu duk iyayensu sun raba yaransu da ita saisa ta maida kanta and centered her life to be just she and her mom.


Yan ajin always sees her as mafadaciya ko magana kama Rashida zai iya koma muku fada saisa suna avoiding nata suma but during group work ko wani abu zatai participating that is idan bamata daukin nauyin yin aikin gabaki dayaba dan tanada bala’in kokari haka dai rayuwan ta yake.



Sunkai asibiti dudda sun saba da hospital din still saida akai orientation sannan aka nuna musu roaster gobe zasu fara taduba taba bata night, daga 8 ne shift nata zuwa 1 kullum banda asabar da lahadi all thanks to HOD nata! She’s so happy da roaster sukai few abu by 11 suka tafi direct hotel din ta wuce takai wajajen 1 tawuce wajen changing room nasu tabude locker dinta taciro uniform nata tashiga chanzawa daidai tagama chanza kayan tana kokarin saka karamin farin hijabinta aka turo door aka shigo changing room din wata cleaner na ce Joy tai murmushi tana kallon gashinta dasauri Rashida takarasa saka hijabin Joy tace “Hi kinzo muje Madam zata mana magana kafin mufara aiki a seminar room” maida locker Rashida tayi tarufe tadauki wayanta da earpiece tasaka a aljihun wando tawuce tafito Joy tabiyota abaya  wani babban hall sukaje da kujeru  ke cike su kusan 34 cleaners din na afternoon zama sukayi Madam dinsu dake tsaye gaban hall tace “I called for this meeting sabida na sanar daku Oga na gari he can come anytime, alot of you dakukai joining this hotel like 2yrs ago baku sanshi ba, he can come at any moment or day idan yaga dama, baya tolerating the slitest of dirt dan haka kuyi aiki dakyau, Rashida!” Dago kanta Rashida tayi takalleta Madam tace “since kina afternoon duty yanzu anytime kika shigo before ki goge anywhere ki tabbata kinzo wajena kin amshi key kin goge office din Oga, for afternoon kene mai gyara office din da safe kuma Kola, abubuwan mop na gyaran office dinshi is different dana general gyara after the meeting you will follow me ki karba” Gyadamata kai Rashida tayi tace “Yes Ma” tunda take aiki yau ne rana na farko dataji anyi maganan mai hotel dinma kusan shekara biyu kenan bai taba zuwa ba ko kuma yataba zuwa bata sani bane oho dai, addressing nasu tayi na kusan 20mins sannan tace “dismiss follow me Rashida” binta Rashida tayi abaya suka wuce office nata tamata handing over key card da sabon bucket mop su air freshener da sauransu a cleaning trolly tace “gashi maza maza 5th floor ai kinsan office din” Gyadamata kai Rashida tayi tafice daga office din tawuce elevator ta shiga zuwa 5th floor din, wani special corridor akebi aje office din da shi kadaine a hanyan corridor din, key wanda take kati ta manna a kofan kofan yabudu hakanan kawai gabanta yafadi batasan mesa ba hannunta tasa ta tura kofan ahankali ciki duhu dan an kashe wuta, hannu tasa tafara kunna wutan Babban office ne sosai daya hadu bana wasa ba, akwai dogon sofa banda table da chair ga babban tv ga desktop gawani mini library da akayishi design na tree kowani branch anyi naming nashi countey ga books na garin awajen saikuma wasu kofofi guda biyu daban daban ahankali tasa kafanta ta shiga ciki sannan ta maida kofan tarufe tana kallo dudda bawani datti, sauka idanunta yayı kan zanenta dake bangon office din dayayi wani irin mahaukacin kyau she can’t believe she drew this, daina kallo tayi tashigo ciro brush na cire cobweb.




Post a Comment

0 Comments