TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Nacina ya jawo mini page 55-56

 *Daga alƙalamin* 

🖍️📚 *Narrnarhh Bukar*  📚🖍️



*Comments and share 🙏🙏🙏Fisabilillah*.


[5/21, 8:09 PM] Narnarhh Bukar: 


🏵️ *NACINA YA JAWO MIN* 🏵️






*Narrnarhh Bukar* 

( *The Amazing Pen* ✍️)




*TASKIRA WRITER'S FORUM*

*T.W.F*


*BOOK 2*




5⃣5⃣----5⃣6⃣




An rufe bakinta saboda kukan karnukan da take kar ta tara musu jama'ah,suna cikin tafiyar har zun fito daga asibitin zuwa harabar asibitin sai da wani mutum da police dog ɗinsa gabjeje dashi yazo wucewa sai idanun karen dana Haj. Zulfa'u suka sarƙafe dana juna, ai tuni ta fizge daga daurin da aka mata tana rarrafe tare da haushi,shima karan mutumin fizge kacan da ake riƙe dashi yayi  tare da gudu zuwa inda Haj. Zulfa'u take yana haushi,habawa da karen mutumin ya iso inda Haj. Zulfa'u take cak! Ya tsaya yana wani gurnani,itama gurnanin take kan kace me tuni suka ɓarke da faɗa,karan mutumin sai cizon Haj. Zulfa'u yake a ko'ina  s jikinta gashi jini sai zuba yake,ita kuma sai faman haushi take,mai karan da ahalin Haj. Zulfa'u kafin suzo wurin ya mata jina-jina,da sauri jikanta ya ɗau wani ƙaton dutse ya bugama wannan karan,a nan take karan ya baje,da sauri suka cicciɓi Haj. Zulfa'u ranga-ranga zuwa cikin asibitin,Allah yasa ba asibitin nada ɓangarori da dama bayan ɓangaren gwajin ƙwalƙwalwa,da sauri nurses suka amsheta zuwa emergency room domin bata taimakon gaggawa saboda taji ciwuka sosai,likitoci har uku suka duƙufa akanta don ganin jinin dake zuba a jikinta ya tsaya,haka likitocin sukaita faman kaikawo a emergency room ɗin,saida jikanta ya bada jininsa don a ƙara mata,duk da Haj. Zulfa'u tana a wannan yanayi hakan bai hanata haushin kare ba,amma ba'a cikin kuzari take haushin ba saboda cizon da tasha wurin karan mutumin nan,wani daga cikin likitocin ne yazo wurin ahalinta don sanar musu akan su shiga ciki su gana saboda su sunyi iya yinsu amma jikin nata gashi nan dai,cike da tashin hankali ahalinta suka dugunzuma zuwa cikin emergency room ɗin,koda suka iso cikin emergency room ɗin still tana nan tana haushi amma ba'a jinta sosai saboda galabaitar da tayi,lokaci guda ta fara jijjiga harta gadon nata jijjiga yake,da sauri su Haj. Amina suka nufo inda take suna matsar ƙwalla,miƙa musu hannu take tana haushi,ga idanunta duk sun kakkafe tana wani girgiza kai haɗi da cije lips ɗina kamar zata ciresu,takai kusan mintuna goma tana a wannan yanayi sai can sukaji tayi slowwww  haɗe da haushi daga nan sai komai na jikinta ya tsaya cak! Alamun rai yayi halinsa,ɓarkewa ahalinta suka yi da matsanancin kuka mai tsuma ran duk mai sauraro,Haj. Amina sai ƙara tattaɓa Hajiyarta take tana kuka,Uwa-Uwa ce ba kowa ke amsa sunan ba,koda Uwarta ta kasance muguwa hakan bazaisa ta kasa jin zafi da raɗaɗin mutuwarta ba domin ta musu gata a rayuwarsu,ta inganta musu rayuwa,ta sadaukar da farin cikinta akansu,hasalima saboda su ne ta kasance azzaluma,haka sukaita kuka,sai can aka dauketa zuwa gida,tare da ɗaukar wata malama domin suturceta dayi mata wanka saboda akaita zuwa makwancinta a kan kari.



Haka su Haj. Amina da sauran ahalinta sukaita kiran ƴan uwa da abokan arziƙi don sanar ta mutuwar Haj. Zulfa'u,hardasu Uncle Hassan da Umman Sa'eeda aka sanar musu da mutuwar Haj. Zulfa'u, sunyi mata addu'a tare da cewa zasu zo Abujan ta'aziyya.A ranar adduar uku Uncle Hassan,Umman Sa'eeda,Momin Sadam da Mai Babban Gida suka zo ta'azaiyya wanda a ranar suka koma saboda masu uzurirrika a cikinsu.Su Fadila da mijinta da danginsa duk sun zo wanda a lokacin tana da ciki amma baiyi ƙwari ba wanda sai bayan addu'ar bakwai ƴan uwanta na can Niger da wa'inda suke nesa suka koma garurrukansu,ƴaƴanta  ne kawai suke gidan basu koma ba amma su Fadila da jikanta namiji da kuma yaran Haj. Amina duk sun wuce gidajansu,anyi sadaka sosai a lokacin addu'ar uku da bakwai,har da masallatai da makarantun islamiyoyi aka bi da sadaka saboda ladar takai gareta.Haka yaran nata suka cigaba da zaman makoki har akayi addu'ar arba'in wanda a nan ne kowa ya koma gidansa,kasancewar har gidan da Haj. Zulfa'u take ciki an raba gado dashi wanda ita Haj. Zulfa'u taci gidan a matsayin gadonta,a yanzu saida aka  sake raba sabon gado wanda siyar da gidan yarannata suka yi  sai aka sake raba musu.Wannan kenan



*TUNATARWA*




*Duniya! Duniya!! Duniya!!! Ba matabbata bace,duk wanda yayi ɗamarar zama a cikinta ya taimaka ya kwance domin kuwa bata da tabbas,duniya ta kasance kamar bishiya ce🌴🌴🌴 wacca muka zo domin shan isa a ƙarƙashinta,kuma kowanne a cikinmu idan ya gama shan isa tashi zaiyi  yabarta ko yana so ko baya so,muyi nazari tare da tunani akan abinda ya kawomu duniya dominsa, kamar yadda a cikin Al Qur'ani mai girma Allah (S.W.T) yake faɗa:"BAN HALICCI MUTUM KO ALJAN BA FACE DON SU BAUTAMIN" ita duniyar nan mun shigota ne domin bautama Ubangijinmu,amma wasunmu ba hakan yake acikin zukatansu ba saidai son abin duniya tare da ƙyaleƙyalanta,a kullum mutane suna faɗi tashi akan duniya wanda nace bishiya ce kuma kowa a cikin mu wataran zai barta*.


*Ƴan Uwana mata harda maza ma yau na haɗa daku,ina zamu kai son abin duniya da dogon buri,shin bakwa ganin yadda ƙarshan Haj. Zulfa'u ya kasance? Mata da kuma maza nawa ne masu irin halinta wa'inda akwaisu da dama a cikin duniyar nan,kamar yadda son abin duniya da dogon buri yakaita ga halata haka wasu mutanan a cikinmu suke da hali irin nata,in fact akwai wa'inda suka takata haɗi da murjeta wurin son abin duniya da dogon buri.ƴan uwana mu koma ga Allah musani idan mutuwa tana tsallakeka ta ɗau waninka to ka tabbata wataran tsallake wani zatayi ta daukeka,Allah ka tsaremu daga yin mugun ƙarshe,kasa mucika da kyau da Imani,ka kuma tsakake zukatanmu,ka hanamu aikata haram duk ƙanƙantarta ka kuma bamu idan aikata halas a duk inda muke,ka albarkacemu da ahalinmu baki ɗaya*.



           @@@@@@@@@@@@@




*KADUNA*



A ɓangaren karatun Sa'eeda a final semseter ɗinta,komai yana tafiya a yadda ya kamata,yanzu haka baifi saura ƴan kwanaki ya rage musu su fara final exams ɗinsu,babu laifi ta jajir ce sosai tana karatu babu ji babu gani,ko wayan da suke yawan yi da Sadam yanzu sun rage,shi yace mata ya kamata su rage wayan ta bari idan sun kammala exams ɗinsu sai su cigaba da gashi(Ni kuma nace tuya sai ranar Sallah😂😂😂🙃🙃🙃),dadi taji sosai saboda daman kunyar fada masa take akan ya kamata ya rage kiranta,ashe shima haka yakeso yayi,kasancewar Dr. Nabila ce project supervisor dinta,sai komai ya ƙara tafiyar ma Sa'eeda normal.Sa'eeda a school ita da aminiyarta Iman zaka samu a kullum suna tare ko suna library karatu.


Rahma tunda tayi tozali da Sadam ta kasa komai kullum cikin tunani take tare da neman yadda zata kwace Sadam daga hannun Sa'eeda, abin kullum cin zuciyarta yake wanda a karshe ta nemi shawarar Maryam akan wannan al'amari,daman itama Maryam tun sanda taga Sadam sabon bakin ciki da hassada suka kara mamaye zuciyarta tare da neman yadda Sadam zai bar Sa'eeda don da alamu yafi mijinta kuɗi, sai kuma yanzu faɗuwa tazo daidai da zama,seat din baya Rahma da Maryam suka zauna suna tattaunawa,can Rahma tace


"Besty mai zai hana mu tambayi Emmanuella ta amsa wayar Sa'eeda tunda suna shiri,kinga sai mu nemi numban Sadam,hakan zaizo mana da sauƙi"


Ɗan nazari Maryam tayi tana kallon ceilling,sai can ta ce


"Kuma fa hakane,tunda nasan ba bamu wayar zatayi ba yadda naga yanzu sai wani faman jijji da kai take tana ƙwanbo ita ga masu kuɗi"


"Mtws!!! Na banza wallahi,domin kuwa mun rigata jin daɗin kuɗi ita yanzu ta fara ,kinga gama Emmanuella can bari nayi mata magana yanzu nan"


"Ok,ina jiranki"


Tsamm! Rahma ta mike zuwa wurin Emmanuella,zama tayi a seat ɗinta sannan ta ce


"Emmanuella please can you help us lend Sa'eeda's phone"


"What did you want to do with her phone"


Ɗan tabe baki Rahma tayi sannan ta ce


"We just want to check something please Emma,if we ask her she will not give us,please, please"


Shiru Emmanuella tayi tana kallonta,sai can ta ce


"Ok"


Godiya Rahma tayi mata sannan ta koma bayan wurin Maryam, miƙewa Emmanuella tayi zuwa wurinsu Sa'eeda,Allah yasa yanzu Sa'eedar ta shigo cikin ajin,zama tayi tare dasu Sannan ta ce


"Sa'eeda please lend me your phone I want to make call,mine is switched off"


Babu musu ta miƙa ma Emmanuella wayar,sannan ta cigaba da abinda take ko a jikinta.Ita kuma Emmanuella wurinsu Maryam ta nufa tare da miƙa musu wayar,sosai suka shiga godema Emmanuella, ita kuma ta wuce wani seat kusa dasu duk don kar Sa'eeda ta gane tare da lallatsa waya.Kasancewar wayar Sa'eeda a buɗe take babu key yasa sukayi saurin shiga contact ɗinta da murmushi a fuskokinsu,scrollimg suke yi a hankali suna duba sunayan numbobinta,Rahma ce ke riƙe da wayan ita kuma Maryam ta riƙe biro da jotter,Rahma na cikin scrolling taji an fizge wayan,da sauri suka ɗago kansu,Ras! Ƙirjinsu ya bada ganin Sa'eeda,Iman da Emmanuella a gabansu,gashi ƴan aji kowa ya dawo ciki kasancewar yawancinsu Sallah da cin abinci ne ya fitar dasu,Iman ce ta fara magana


"Mai hali dai baya fasa halinsa,a'ahhh hhhaaa! Su Rahma anyi ilimin snatching ɗin saurayi,ke duniya ina zaki damu"


Taɓe baki Sa'eeda tayi still idanunta akansu,Iman ta cigaba da cewa


"Saboda rashin ta ido shi ne zaku cema Emmanuella ta amso wayan Sa'eeda ku ɗauki numban saurayinta ko"


Emmanuella ce tayi magana da turanci kasancewar bata iya hausa sosai ba


"You guys are too envy of Saheeda,before Meryam you snatch her boyfriend she leaves you and now you  Rahama want to snatch her boyfriend again,are not ashame of yourselves"


Tsuru-tsuru suka yi,ƴan aji sai kallansu suke,ga wata iriyar zufa da ta mamaye goshinsu,hausawa daman sunce *mara gaskiya ko a ruwa gumi yake* Sa'eeda ce ta fara magana cike da izza haɗi da gargadi


"Ada da yanzu ba ɗaya bane,idan ada kunyi yadda kukaso a kaina ban kula ku bato yanzu kusani ba Sa'eedar da kuka sani a baya bace,yanzu da wata Sa'eeda ta daban kuke tare,bani da mutunci kuma bana daukar raini wallahi,hmmmm wato ku ga ƙungiyar snatchers ko,kunyi snatching saurayi a baya kunji daɗi shiyasa kuka yi tunanin ƙara snatching ɗin wannan ko,to kusani mijina yafi ƙarfinku(O'ooh ni Indo babu kunya wai miji,to su miji anji jiki😂🙃),ba irin mazan da kuka sani bane,sannan koda kun bincike wayata tsaf! Bazaku taɓa samun wani information dangane dashi ba domin I always  used my *Mendulla Oblangata* a duk lamurrana,sannan tattaunawar da kuka yi ɗazu,komai ya shiga cikin kunnena"



*Waiwaye*


Abin su Maryam da Rahma basu sani ba shi ne,a lokacin da suka zauna a seat ɗin baya tare da ƙulla-ƙullar yadda zasu yi snatching ɗin Sadam daga wurin Sa'eeda, ita kuma lokacin mararta na  mata ciwo ta fito waje tare da zama wurin windon baya don tasha iska,kasancewar kusa da windon take duk da yana a can sama amma kana jin abinda ake a cikin ajin,to a nan ne tajiyo muryar Maryam da Rahma suna zancen yadda zasuyi snatching ɗin Sadam daga wurinta,murmushi tayi sannan ta ciro wayarta tare da ɓoye duk wani informations na Sadam,contact dinsa ne,pictures ɗinsa ne, da dai sauransu kasancewar taji sunce zasu aiki Emmanuella ta karɓo musu wayar su duba.


Kuma koda Emmanuella ta karɓa,itama ta ma Iman text a wayarta akan su Maryam da Rahma na investigating wayar Sa'eeda,a sanda Iman taga text ɗin already Sa'eeda ta sanar mata abinda taji suke faɗa,a sannan ne Iman tayi ma Emmanuella reply akan da taga sun miƙe zuwa wurinsu itama ta biyosu,haka kuwa akayi,a tare suka isa wurinsu Maryam,sai Sa'eeda ta fizge wayan su kuma da basu san da wannan plan ɗin ba hadi ta tsayiwarsu Sa'eeda akansu,shiya assasa firgici haɗi da tsoro a lokaci guda.


*Cikin labari*


Cigaba da magana Sa'eeda tayi da cewa


"Wallahi! Wallahi!! Wallahi!!! Nawa na rantse!!! "


Da sauri suka amsa da 


"Uuku!"


"Idan na kuskura na ƙara ganin kun shiga harkata wani duk abinda nayi muku to ku kuka da  kanku,Sannan ke kuma Maryam har yanzu ina nan akan bakana,Wallahi duk ran daɗewa sai kinzo keda wannan yalolon mijin naki a inda nake kun nemi yafiyata,ku rubuta ku ajiye don ban yafe yaudara hadi da cin amanar da kukamin ba,sai Allah ya sakamin tata-izan da gaggawa,ke kuma Rahma annamimiya"


Nuna Rahma tayi da hannu sannan ta cigaba da cewa 


"Sadam yafi ƙarfinki,ke dashi sai hangen nesa,domin kuwa Sadam nawa ne ni kaɗai,banza,akuya,jaka,ke a tunaninki idan kika dauki contact ɗinsa sai ki kirashi,lallai ma kuwa a gaskiya sai yau na tabbatar da karyace ke ta bugawa a jarida,baki da aji ko kadan wallahi,don haka ni naimi wani bashi saboda ko drivansa yafi ƙarfinki balle shi,Mtws! Garori kawai,Iman zo mu wuce banda lokacin shirmansu"


Jan hannun Iman tayi tare da barin wajen fuuuuu!,ƴan aji  kuwa sai binsu da kallo suke,kowa na mamakin canjawar Sa'eeda, yarinyar da ko hannu kasa a bakinta bazata ciza ba amma yau ita take faffaɗama ƴan gayun aji maganganu son ranta,Allah kenan mai canja abinda yazo a lokacin da yaso,ada ita take tsoransu Maryam amma kuma yanzu su suke tsoranta.


Tun daga ranan su Rahma basu kara shiga sabgar Sa'eeda ba,sannan Rahma ta cire Sadam a ranta ganin Sa'eedar yanzu ba kanwar lasa bace,dole da haƙura da mutuwar son da take mishi.


Bai wuce kwana uku su Sa'eeda su fara final exams ɗinsu ba,a lokacin suna falo harda Uncle Hassan da Dr. Nabila suna hira,can Uncle Hassan ya dubi Sa'eeda tare da cewa


"Ansa ranar auranki da Autan Momy nan da wata shida masu zuwa"


Dammm! Daram! Dam! Dadammm!!! Haka ƙirjin Sa'eeda ya bata jin wannan maganar a bazata,waro idanunta tayi waje tana kallonsa,taɓe baki yayi sannan ya ce


"Kin wani zubamin manyan idanunki salan na kasa bacci saboda firgici,ce nike harda ke a wurin assasa maganar auran,kin wani ruɗa yaran mutane shi kuma yazo ya hauka ce mana,akan shifa a ɗaura muku aure"


Me Dr. Nabila zatayi inba dariya ba,sosai take tintsirar dariyarta son ranta,ita kuma Sa'eeda babu abinda ƙirjinta yake inba Ras! Ras! Rarass! Ras! Ras!  A zuciyarta tana cews 'Amma Sadam ka kasheni wallahi, wannan wani irin jaraba ne haka,ba nace ka bari bayan school ɗina sai a saka rana bikin ba amma yanzu duk plans ɗina sun ruguje,Shit men! ' can Dr Nabila ta ce


"A gaskiya ƴarka ta haɗu da ɗan anaci Auntan Mom,haka halinsa yake tun yana ƙarami,idan yana son abu hmmm ya dinga zumuɗi akan abun haka kuma idan ya tsani abu,Wa'iyazubillah! "


"Ai gashi nan kuwa,yanata zumuɗi, todafa aka saka ranar nan da shekara ɗaya kuka ya fashe dashi sanda aka sanar masa wai shi gaskiya a dawo da auran nan da wata ɗaya kenan immediately after exams ɗinsu Sa'eeda, lallashi da ban baki aka shiga basa akan yayi haƙuri zuwa nan da one year amma ina,haka Mai ran ƙarfe yace to yayi haƙuri nan da wata shida sai ayi bikin,kinsan duk da haka saida ya koka,nifa abin nasa har dariya yake bani,irin wannan so haka,anya Sa'eeda bake kike zugashi ba kuwa" cewa Uncle Hassan


"Wallahi tallahi Uncle ba ruwana,babu abinda nace masa,shi da kansa yayi kiɗinsa kuma yayi rawarsa,Allah ka yarda dani Uncle"


Idanunta har sun ciko da ƙwalla,mai zasuyi inba dariya ba,ita Dr. Nabila harda riƙe ciki,sai can  Dr Nabila bayan ta tsagaita dariyar tace


"Is quiet ok my beloved daughter kinji,kaunarki ce tasa yake wannan zumuɗin kuma naji daɗin haka,domin alamu sun nuna zai kula mana dake sosai,karki damu kinji,sannan kuma karki nuna fushinki a garesa saboda wannan magana don nasan zaki aikata haka irin ɗaure fuskar nan da kike"


"To Aunty bazan masa maganar ba"


"Yawwa yanzu tashi kije ki cigaba da karatunki,Allah ya bada sa'a"


Tsam! Ta miƙe tare da barin wajan zuwa sama,kamar jira yake ta shiga ɗaki saiga kiransa,picking tayi tare da sallama,kasancewar yasan exams ɗinsu a nan kusa ne yasa kawai yace mata an saka ranar auransu amma bayan exams zasuyi maganar,sai sukayi sallama,haka Sa'eeda ta cigaba da karatunta na exams har Allah yasa suka fara final exams ɗinsu.Wannan kenan



             @@@@@@@@@@@



A ɓangaren *LOVE BIRDS* 🕊️🕊️ wato Sauban da Maryam kai harda Khairat abubuwa ƙara ta'azzara suke domin tun sanda Sauban ya fara zancen rashin haihuwarsu ya fara samun matsala daga kowannansu,kowacce sauke mishi kwandon rashin mutunci tayi harda Khairat wanda a dalilin haka saida mahaifiyarsa tazo part ɗinsu,a main falon part ɗinsa kowa ya samu wuri ya zauna sannan Momin Sauban ta ce


"Meke faruwa"


Sauban cikin ɓacin rai ya fara magana bayan ya cillawa kowaccansu harara,Khairat tabe baki tayi,ita kuma Hajjaju Maryamu murguɗa masa baki tayi


"Mom a gaskiya na gaji da zaman ciyarsu a gidan nan,saboda bazaiyu ina wahalar nemo abinci ba,su kuma suna zaune gida sa faman ɗirka ƙiba suke amma  kowaccansu bata da alamar ciki balle haihuwa,dole ayita ta ƙare yau ɗin nan,don na gaji da ciyar dasu,kawai saidai suci suyi kashi,haba!"



Shiru Mominsa tayi tana kallansa,ada taga canji sosai bayan auransa da Khairat amma yanzu fa,komai ya sake taɓarɓarewa,ƙara duhu yayi da ƴar rama,can bayan ta sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya sannan ta fara magana



"Duk wannan faɗan da kake ba shi ne ya dace kayi ba Sauban,kaga da,aure,haihuwa,mutuwa duk suna da lokaci,idan lokacinsu yayi ko kaso ko baka so ba sai ya faru,da wannan ɓaɓatun da kake da matanka babu gaira babu dalili,mai zai hana ka ɗaukesu zuwa asibiti a gwada a ga ina ne matsalar take sannan wa yake da matsala a cikinku"



Tab! Ai shi sai yanzu tunanin asibiti ya hau kansa,yooo da tuntuni ya tuna da maganar zuwa asibiti ai da sunje,cikin girmamawa Sauban ya amsa ma Mominsa da cewa



"Wallahi sai yanzu na tuna da asibiti,in shaa Allahu zuwa gobe zamuje mu duka don a gwada waye keda matsalar a cikinmu"


"Yawwa hakan yafi ai,kudai cigaba da hakuri domin shi aure daman akwai ƙalubale a cikinsa,sannan mafi rinjayan maganinsa shi ne *Haƙuri* sannan kai kuma Sauban ka rage wannan faɗace-faɗacan da kake da matanka,baka ganin sauran yayyinka yadda suke zaman lafiya da matansu amma kai kullum da akwai wata ɓaraka a gidanka,haba don Allah ka dinga haƙuri dasu domin kuwa kowani namiji haƙuri yake da matarsa saboda baka taɓa samunsu daidai yadda kake so dole ta wani fannin su gaza"



Haka ta cigaba dayi musu nasiha mai ratsa zuciya,kuma dukkaninsu harda Maryam saida jikinsu yayi sanyi,bata banbantasu ba,kamar yadda take ma Khairat faɗa haka ita ma Maryam ɗin take ma faɗa,ta daɗe tana yi musu faɗa sai can tabar part ɗinsu. Haka kowa ya kwasa jikinsa zuwa ɗakinsa,shi kuma Sauban ya fita.


Washe gari da safe suka shirya zuwa asibiti, Maryam a gaba tare da Sauban sai Khairat a baya,daman ita  Khairat bamai son hayaniya bace,koda Maryam ta nufi front seat ko a jikinta ta wuce baya ta zauna,tada motar yayi sannan suka nufi asibitin, a lokacin da suka isa asibiti sun tarar da layi sai suka bi layin wanda mintuna basu kai ashirin ba layi yazo kansu sai suka shiga ciki su duka.Bayani Sauban yama likitan dan gane da abinda ya kawosu,kasancewar likitan abinda ya karanta kenan shiyasa ya ce babu matsala,bara ya gwada kowannansu a gano inda matsalar take,tests akama kowannansu sannan ya ce nan da awa huɗu su dawo domin amsar results,babu musu suka fita daga office ɗin,gida ya komar dasu sai can bayan awa huɗu ta cika da kusan ƴan mintuna ya sake ɗaukarsu zuwa asibitin, nan da nan layi ya sake zuwa kansu suka shiga office ɗin a tare,bayan sun zauna likitan ya dubi kowanne daga cikinsu tare da yin nazari,su kuma dana mujiya suke binsa dashi ƙirjin kowa yana bada Fat! Fat! Fat! Kowa na addu'ar Allah yasa baida wata matsala,gyaran muryar yayi wanda ya jayo hankalin kowannansu sannan ya fara magana



"To Alhamdulillah bayan dogon bincike da mukayi mun gano matanka basu da wata matsala ata kowani fanni....."




"To waya keda matsalar" cewar Sauban wanda ƙirjinsa yake dukan uku-uku



"Calm down Alhaji,kwantar da hankalinka mana ,miye na gaggawa wanda bayani ne gashi a rubutu ce zan sanar mu"



"Ok toh muna sauraranka" cewar Sauban



"Yawwa kamar yadda na sanar maka matanka basu da matsala ata kowani fanni,kaine dai keda matsala amma bana rashin haihuwa ba, saidai sperm ɗinka is very weak to the extent baizai iya ƙyanƙyasa ƙwayayan  matanka ba"



Dammmm! Damm! Dadammm! Haka ƙirjin Sauban ya bada,zuciyarsa kamar zatayi zullo ta fito waje saboda tsabar ruɗun daya shigesa lokaci guda *Sperm ɗinsa is very weak bazai iya ƙyankyasa ƙwayayansu ba* ,tab!! Katse tunanin Sauban likitan yayi da cewa



"Kwantar da hankalinka Alhaji domin akwai mafita kuma nasan za'a dace da yaddar Allah (S.W.T),zamu ɗoraka akan magunguna wa'inda idan kayi amfani dasu a yadda ya dace in shaa Allah komai zai daidaita"



Wata nauyayan ajiyar zuciya ya sauke wanda har saida matansa suka ji,likitan ɗauko wata paper yayi tare da rubuta masa sunayan magungunan da zaisha sannan ya miƙasa paper da cewa



"Gashi kaje pharmacy ka siya,duk yadda zaka sha maganin za'a rubuta maka a can Allah yasa a dace"



"Ameen na gode sosai"


Miƙewa suka yi tare da barin office ɗin,su Maryam da Khairat mota suka nufa shi kuma ya wuce pharmacy don siyan magungunan,bayan ya siya sai suka ɗunguma zuwa gida,kowaccansu tana farin cikin bata da matsala shi kuma,yana baƙin ciki tare da shiga damuwa akan shi keda matsala basu ba.



Tun daga wannan ranar ya daina faɗan rashin haihuwarsu,sannan ya dage da shan magani babu kama hannun yaro saboda a gaskiya yana son haihuwa, Mominsa ma bata ji daɗin cewa ɗanta keda matsala ba,ƙara jadda mishi tayi akan ya maida hankalinsa ga shan magunguna kar yasa wasa,har misali take mishi akan duk taga yaran yayyinsa da ƙanansa sauran sa kaɗai ne bataga yaransa ba,da wannan magana Sauban kamar ta ƙara mara gwarin gwiwar shan maganin ne. Wannan kenan




           @@@@@@@@@@@@@



A ɓangarensu Umma Kande da Maman Jummalo komai nasu na tafiya daidai babu wata matsala sai matsalar siyan pampers ɗin Nusaiba,wanda a wata suke siyan jakar pampers ɗin amma da ƙyar pampers ɗin yake kaiwa har ƙarshan wata,kullum sau biyu ko sau uku take canja pampers idan kuma tace manage zata yi to ranar gidan nasu ɗumewa da wari zaiyi haɗi da ƙudaje,Allah yasa ma suna ɗan samun kuɗin hayan shagunan da mariganyi Musa ya barmu da ba haka ba,sai dai ta koma amfani da ƙunzugu saboda na abinci kaɗai Abban Sa'eeda yake da halin badawa.Kamar baki har yanzu babu mai saurayi ko ɗaya a cikinsu ba'a ma maganar Nusaiba wacca ta riga da ta tashi aiki domim babu namijin da zai kwasar ma kansa wahalar siyan pampers.(My Esteem fans a taimaka a samoma Nusaiba mai pampers miji,ita ma auran take so😂😂😂🙃🙃🙃)



Yau Jumma'ah,tun safe su Umma Kande suka bar gidan saboda bikin yarinyar wata ƙawarsu a bayan layi,suna mutunci da ita sosai kuma lokacin bikinsu Iklima da sassafe tazo akayi aikin biki da ita tare da kawo musu gudunmuwar kuɗi masu yawa,wannan shi ne dalilin dayasa suma suna son nuna tasu bajintar tare da shiga ayi aikin biki dasu.



Su Nusaiba da Jummalo suna a two seater,Jummalo na koyama Nusaiba *Khamsuna Hadith* ita kuma Iklima tana faman rubutu,Jummalo na cikin koyama Nusaiba karatu sai da wani ƙaton kyankyaso ya hau saman hadisin,ai da sauri Jummalo ta kakkaɓe liffatin haɗi da mikewa tsaye ita da Nusaiba,Iklima ce ta ce



"Lafiya kuka miƙe lokaci guda"


"Ƴan iskan kyakyasan nan ne,shegu mara jin magani" cewar Nusaiba


"Ai nace ma Mama *kwalema* kadai ne zaiyi maganinsu amma ta ce ita bataso,sai dai a siya magani a saka musu,ai gashi nan suna dumunmu,harta baccin kirki gagarar mutum yake da daddare"



"Gaskiya kwalema ɗakinku yake buƙata,yaushe rabon da ayi kwalema a gidan nan" cewar Jummalo



"Ai kuwa an daɗe,ke! Bara kiga duk faɗan da mama zatayi wallahi sai munyi kwalemar ɗakin nan a yau,koma ji daɗin bacci da daddare" cewar Iklima tana miƙewa da kayan rubutunta



Haka suka fara kwalema babu ji babu gani,da falo suka fara,sannan sai bedroom wanda a nan ne dandalin kyankyasan harda ƴan matan Kaduna da kuɗin cizo suke,suna kwalema suna saka magani, Nusaiba da Jummalo ne suka ɗaga katifar  tare da ajiyeta gefe,sai suka cire flow bed din gadon,ita kuma Iklima ta fara ɗadɗauke abubuwan da suke a ƙarƙashin gadon,can tana cikin ɗaukewa sai tayi tozali da wani akwati mai kyau dashi,har ta  dauke akwati ta ajiye zuwa wani gefe sai can zuciyarta ta kwaɗaitu da ganin maike a cikin akwatin,tana a duƙen ta buɗe akwatin turus! Tayi ganin ashe duk kyawun akwatin wata ƴar ɓaƙar kwalba ce kawai a ciki miƙewa tayi tare da kwalbar tana ƙara dubawa,tana a haka sai wani kyankyaso yayi fiffike zuwa wuyanta wanda nan take ta daka tsalle tare da *sakin kwalbar a ƙasa*  ji kake tTusssss!!! Kwalbar ta bada a ƙasa(ta fashe) wanda ko second biyar da fashewar kwalbar ba'ayi ba saiga su Umma Kande da Maman Jummalo sun shigo cikin bedroom ɗin da saurinsu saboda a tun shigowarsu gidan suka ga Nusaiba da Jummalo na faman rarrafke kaya,ai tuni hankalinsu ya tashi musamman Umma Kande da sauri suka nufi bedrrom suna shiga ciki Turus! sukayi gani Iklima ga kumar kwalbar a ƙasa  ta fashe ai kan kace me Umma Kande ta........





*Mu haɗu a pages na gaba,hmmmm next pages akwai ƙura 🔥🔥🔥😂😂😂😂*




*Bara nayi waƙar yara suna cewa KWALBA TA FASHE A GABAN ƊAN KOLI TANGARARARASSS!!! To fa yau dai ga kwalbar boka Sankeru a tarwatse a ƙasa,ya makomar Umma Kande dashi kansa boka Sankeru???*....





*Shin Abban Sa'eeda zai dawo ciki hayyacinsa kuwa???*.....




*Shin Maganin da Sauban ya amsa a asibiti zai mishi aiki kuwa???*......


*gashi an saka ranar Sadam da Sa'eeda,anya kuna ganin Sadam zai yarda har zuwa wata shida kuwa???*....


*wai ina Gwaggo Ladi da Baba ƴan ƙauyan Damari nd,shin su Umman Sa'eeda zasu sake komawa garin ko kuwa???*......


*Kai! Kai! Kai! Abubuwa da yawa🙃🙃🙃,amsoshinku na nan tafe a pages masu zuwa,kudai  ku cigaba da zubo ruwa comments da reactions🌹🌹💖💖🌼🌼💘💘,ni kuma bazan gaji ba wurin suburbuɗo muku new updates zafafa* 🌹🌹🙃🙃💖💖🌼🌼💘💘😂🔥🔥🔥🔥🔥

*Ina ƙaunarku My Esteem Fans Lodi Lodi* 🌼🌼💖💖🌹🌹🙃🙃💘💘




Post a Comment

0 Comments