TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Nacina ya jawo mini page 59-60

 *Daga alƙalamin* 

🖍️📚 *Narrnarhh Bukar*  📚🖍️


*Comments and share 🙏🙏🙏Fisabilillah*.



[5/26, 9:20 PM] Narnarhh Bukar:


 🏵️ *NACINA YA JAWO MIN* 🏵️






*Narrnarhh Bukar* 

( *The Amazing Pen* ✍️)





*TASKIRA WRITER'S FORUM*

*T.W.F*



*BOOK 2*




5⃣9⃣----6⃣0⃣




Bata ƙasara maganar da tayi niyya ba Baba ya daka mata wata uwar tsawa wanda har jikinsa saida ya girgiza saboda tsufan da yayi,cike da ɓacin rai ya fara magana



"Wai ke yaushe zakiyi hankali da tunani ne,mutane ko zama basuyi ba, amma kin fara zazzaga musu masifarki haba don Allah,to buɗe kunnuwanki dakyau kiji,Hussaina Allah ya haɗata da ahalinta,tare dasu take,gorin rashin asalin da kike  mata sai ki jiƙa ki sha"



Dammm!!! Darammmm!!! Dadammmm!!! Haka ƙirjin Gwaggo Ladi ya bada,lokaci guda ta dafe ƙirjinta tare da waro ƙananun idanunta waje tana cewa



"Ta haɗu da ahalintaaa!!! Da gaske ne? "



"Eh Gwaggo,Allah ya haɗani da ahalina yanzu ma haka abokin haihuwata Hassan yana waje......"




Bata ƙara maganar ba Babs ya katseta da cewa



"Me kike jira Hussaina,shigo dashi mana,ai na zaci tare kuka shigo" cewar Baba



Komawa Sa'eeda tayi tare da kiran Uncle Hassan tana ce masa ance ya shigo ciki,babu musu ya biyota,a lokacin su Umman Sa'eeda da Momin Sadam suna zaune a saman tabarma suna ƙara gaisawa da Baba,ita kuma Gwaggo Ladi abin duniya ya isheta,'wai yau wacca take ma hassada da baƙin ciki gashi sai ƙara ɗaukaka take,jiba sitirun da suka saka shima abin kallo ne,gata tayi ƙiba da haske ba kamar da ba,da alama tana cikin kwanciyar hankali,a gaskiya hassada batayi ba,gashi yanzu hassadan dana mata ya zamo mata taki,sai ƙara yabanya kawai take,ohnii! Ladi yanzu ne ya dace na sauke makaman yaƙina akan Hussaina saboda wahalar banza nake kawai....'  Bata ƙarasa tunanin da take ba,Baba ya katse mata da cewa



"Ladi ga abokin haihuwar Hussaina yazo,kinga suna kama Sak! Allah sarki Maimuna,Allah ya cigaba da haskaka miki ƙabarinki"



"Ameen ya Hayyu ya Qayyum"



Tare suka haɗa baki,Gwaggo Ladi cikin sanyin murya haɗi da nadama ta ce



"Hussaina ki yafe kusakuran da nayi miki a baya,sharrin shaiɗan ne,yau na tabbatar da hassada*Taki ce ga wanda kake ma hassadar* a duk sanda kayi ma wani hassada da baƙin ciki to kamar ka ƙara masa taki kake a gonarsa,shi yana ƙara ɗaukaka kai kuma kana durƙushe hasken tauraronka,don Allah ki yafe neee.."



Kuka sosai Gwaggo Ladi take tuno da abubuwan da tama Umman Sa'eeda barasa daɗi,tunda Umman Sa'eeda take bata taɓa samun wani farin ciki ko sakin fuska a wurinta ba,saidai kyara,tsangwana,cin mutunci,wahalarwa,mugunta da dai sauransu,gashi yanzu ya zamowa  Umman Sa'eeda labari.Da sauri Umman Sa'eeda ta ce



"A'a Gwaggo bar kukan,na yafe miki,ni dama can ban riƙeki ba,saboda ɗan Adam ajizi ne,wataran yakanyi kuskure,nima ban wuce yin kuskure irin naki ba,na yafe miki duniya da lahira,Allah ya yafe mana baki ɗaya"



"Ameen Ameen Hussaina a gaskiya kin cika ƴar halak mai maida sharri zuwa ga alkhairi, Allah yayi miki albarkha da ƴarki" cewar Baba



Ita kuma Gwaggo har yanzu matsar ƙwalla take,saboda bata taɓa tunanin Umman Sa'eeda zata yafe mata a nan kusa ba.Hira suka ɓarke dashi,har da Gwaggo Ladi don har ta saki ranta tare da aikan yaran maƙotansu su kira duka yaranta su gaisa(Hmmm su Gwaggo Ladi kodai kodai don Hajiya Naira ne ake wannan ladabin ɗan tsakon,kawai daga ce miki ta haɗu da ahalinta shikenan kin ajiye makaman yaƙinki,O'o'oooo🤔🤔🤔😂😂😂)



Ruwan randa mai sanyi Gwaggo Ladi ta ɗebo musu a kwanon sha mai kyau dashi,daman tun a da can Gwaggo Ladi gwanar tsafta ce,baka taɓa samunta da datti a gidanta,kuma koda ta tsufa jikokinta suna gyara mata gidan duk da  suna cin faɗa akan basu iya gyaran gida ba,amma haka suke gyarawa babu yadda suka iya.Suna cikin wannan hirar saiga Mairo ta shigo gidan da sallamarta,kana ganin fuskarta kasan tana cikin ɗumbin farin ciki,amsa mata sukayi,da sauri Umman Sa'eeda ta miƙe tare da rungume ƴar uwarta wacca take jinta aranta,cikin farin ciki mara misaltuwa Umman Sa'eeda tace



"Ƴar uwa rabin jiki,nayi kewarki sosai wallahi"



"Allah sarki ƴar uwa,ai fushi nake dake yanzu" cewar Mairo tana juya fuskarta gefe



"Ayi min afuwa,wani laifi na aikata in bada haƙuri yanzu-yanzun nan"



"Daɗina dake akwaiki da saurin yafiya"



"Naji nidai yanzu sanar min da laifina,ko hankalina ya kwanta"



Dariya Mairo tayi sannan ta ce lokaci guda tana zama a bisa tabarma



"Ummm bisimillahi Allah,ai kya bari na huta tukunna ko,Hajiyar zumuɗi"



Dariya kowa yayi a wurin harda Gwaggo Ladi, bata daɗe da zama ba saiga sauran yaran Gwaggo Ladi su biyu sun shigo gidan da sallama,amsa musu su Umman Sa'eeda sukayi sannan suka samu wuri suka zauna sai faman wani cije-cijewa suke(Ai da kuma kun ajiye makaman yaƙinku tun wuri kafin dare yayi muku domin ita uwar gayyar taku ta ajiye nata makaman to me kuke jira ƙananun ƙwari😂😂😂)



Ganin yadda yaran nata suke faman shan ƙamshi,dole Gwaggo Ladi tayi musu magana da cewa



"Kunga duk wani cije-cije da ɗaure fuska ku ajiyeshi gefe domin babu ribar da zaku samu,nima nayi hakan a baya amma banga ribar dana samu ba hasalima hasken taurarona nayita durƙushewa ba tare da nasani ba,daman saboda dani kuke yi,to na janye makaman yaƙina,kuma ku janye naku"



Shiru yaran sukayi suna jinta,ta biyun jikinta yayi sanyi sosai amma babbar sai faman huro hancinta take, tana ɓata fuska, ita daman ko ba don mamanta ba,tun fil-azal ba ƙaunar Umman Sa'eeda take ba saboda duk tafi su komai,ga shegen kyau da farin jini uwa-uba samari masu kuɗi,to taya zata ƙaunaceta,tabb ai yanzu ta fara tata hassadar,babu gudu babu ja da baya,ƴar Gwaggo Ladi ta biyu ce wato Na'ima ta fara magana cikin sanyin murya mai nuni da nadama



"Hussaina ki yafe mana laifukan da muka miki a baya,ni da ƴar uwata...."



"Ke kaɗai banda ni wallahi,Allah ya tsareni da neman yafiya gun wannan marar asalin" cewar babbar ɗiyar Gwaggo Ladi wato ƴar yaya



Kowa a wurin mamaki ne ya cikasu,musamman Gwaggo Ladi wacca tayi mutuwar zaune jin babbar ɗiyar ta da irin wannan magana,koda yake daman tun suna ƙananu ba ƙaunar Hussaina take ba,wani lokacin ma ita take ƙara zuga Gwaggo Ladi, to amma yanzu fa tunds ba  wani riba suke samu ba,cikin ɓacin rai Gwaggo Ladi ta ce



"Yanzu ke ƴar yaya bazaki hankalta ba,ƴar uwarki tayi nadama amma banda ke,yanzu wani riba kika samu ne,amma kije kiyi mudai mun tsame hannayanmu daman Mairo tun fil-azal tana ƙaunar Hussaina, ita bana shakku akanta,amma ke ɗin nan"



Nuna ƴarta tayi sannan ta cigaba da cewa



"Kije ya rage naki"



"Ƙyale wawuya wacca batasan meke mata ciwo a kwanyar kanta ba,kowa ya ajiye makaman yaƙinsa banda ke, kije da halinki"

Cewar Baba ransa a ɓace



Tsam! Ta miƙe ba tare da ta kalli kowa ba ta fita abinta,kowa da ido ya bita dashi,tare da adduar Allah ya dawo da ita hanyar gaskiya. Gyaran murya Uncle Hassan yayi,daman tunda ake hirar bai ce *Ta tafasa balle sauke ba* Sai yanzu yakeson yayi bayanin maƙasudin abinda ya kawosu garin,magana ya fara



"To Alhamdulillah ala kulli halin,sannan muna godiya a gareka da taimakon mahaifiyarmu tare da ƴar uwata da kayi,bansan da wasu lafuzza zanyi amfani dasu  wurin maka godiya akan taimakon da kayi mana wanda da badan Allah ya ƙaddaro ka taimakesu ba da bamusan wani hali zasu shiga ba,muna jinjina a gareka,sannan magana ta biyu shi ne sakanya Alkhairi da alkhairi zamuyi iya ƙoƙarinmu  akan sakanya maka da taimakon da ka mana,duk da nasan bazamu taɓa iya saka mata da alkhairin da kayi mana ba,mun yanke shawarar kaika aikin hajji na wannan shekarar sannan zamu siyan maka gida a birni bayan haka za'a siya maka shaguna wa'inda zaka dinga samun kuɗin shigowa duk da zamu dinga turo maka da kuɗi duk wata na siyan kayan abinci,bancin haka idan ka yarda yayan mahaifiyata ya ce inda hali yanaso kazo kaida ahalinka ku ɗanyi kwanaki acan saboda za'a tara ƴan uwa domin suyi maka godiya akan taimakon da kayi mana"



"Allahu Akbar,Tsarki ya tabbata ga Ubangijin Talikai,domin nufinsa ne ba namu ba,wa'innan abubuwan alkhairai haka duk saboda taimakon da nayi muku na cancanci dumbin alkhairai haka,na rasa wasu kalamai zanyi amfani dasu wurin gode maka...."



"A'a Baba muke da godiya domin kafi haka,mu mukafi cancanta mu gode maka har ƙarshan rayuwarmu domin samun mutum irinka a wannan duniya akwai wahala,babu abinda zamu ce maka sai godiya"



"A'a ɗana kyaututtukan nan sunyi yawa,kabar maganar siyan gida a birni,wannan da muke ciki ya ishemu,kwata-kwata rayuwar kwana nawa ne zakaji ance mun tafi"



"A'a Malam ya yaro yayi niyyar siyan mana gida a birni zakace a'a,haba ai wannan *Buƙulu ne* wallahi ,Allah yace mu huta kaiku kana a'a Tab!" cewar Gwaggo Ladi tana gyara zamanta.



"Yanzu Ladi a wannan shekarun naki kike magana hutu,keda kike fuskantar ƙabari amma kina maganar zuwa birni"




"A'a Malam bana fuskantar ƙabari,mutuwa ba yanzu ba da yardar Allah kuwa"



Dariya maganar Gwaggo Ladi tabama kowa,wato tsoran mutuwa take haka,shima kansa Baba saida ya dara irin wannan tsoro haka,ita kuwa sai faman ƙanƙance idanunta take tana ɓata fuska irin an ɓata mata rai,a cikin zuciyarta tana cewa 'Al Qur'an sai munje birni ko kaƙi ko kaso,kawai muga samu muga rashi,idan kai kaƙi zuwa toni tafiyata zanyi wallah,muje can muyi *Ƙara'i* kuwa.Umman Sa'eeda ne ta ce




"Wata shawarar ta faɗomin,tunda Baba zaije Hajji kaga saisu tafi tare da Gwaggo Ladi, hakan zaifi dacewa"



"Ɗiyar nan da gaske wayyo daɗi,ashe zanga ɗakin Allah da dabinon annabi harda zam-zam da safa da marwa,wayyo daɗi,ke ƴar nan Allah yayi miki albarkha da ahalinki,ya jiƙan Maimunatu  mutuniyar kirki,ayyyiririiiiiiiii!!! "



Guɗa Gwaggo Ladi ta cillara wanda ya karaɗe gidan baki ɗaya kasan mutan da an iya guɗa,tare da miƙe tana juya tana cewa



"Ɗiyar albarkha Hussainatu!!! Ɗiyar alkhairi Hussainatu!!! Mai imani sai Hussainatu!!! Um-um-um-um um-um-um!!! Mace mai kyauta sai Hussainatu!!! Kai aaaayyyyiiiririiiiiiiii Hussainata!!! "



Babu wanda bai dara ba musamman Sa'eeda cikinta kamar zaiyi ciwo saboda dariya koni mai ɗauko muku rahoton saida na dara domin yadda take tiƙar rawa babu ji babu gani dole kayi dariya,harta Uncle Hassan ya dara tare da mamakin wannan tsohuwar da alama tayi rawar kai a sanda take yarinya.Baba tsoho ne ta katse musu dariya da cewa



"Haba Ladi wannan ba girmanki bane rawa,kin tsufa amma bakisan kin tsufa ba,haba don Allah,kinga amfani taimako a rayuwa ko Ladi,kinga a sanadin taimako Allah ya nufemu da tafiya aikin hajji a wannan shekarar,shiyasa nake ce miki a kullum ka taimaki wanda yake buƙatar taimako domin bakasan wataran ya rayuwa zata kasance ba,ban taɓa kawowa zanje aikin hajji a rayuwata ba,amma a *sanadin taimako* Allah ya nufeni da ziyartar ɗakin Allah"



"Hakane malam sai yanzu na tabbatar alkhairi danƙone,sannan hassada ciwo ce babba maganinta sai Lillahi,gashi wacca nake ganin ba kowa bace ta biyamin aikin hajji,Allah kenan don Allah Hussaina ki ƙara yafemun"



"Haba Gwaggo ai na daɗe da yafe miki,Allah ya yafe mana baki ɗaya"



Ameen kowa ya furta a bisa labɓansu,sai wurin yayi shiru kamar mutuwa ta gitta,sai can Baba yace a ɗaura ma baƙi abinci,Uncle Hassan ne yace yazo musu da kayan abinci a booth bara a kwaso cikin gidan,fita yayi sannan yasa bodyguards kwaso kayan abinci zuwa cikin gidan kama daga buhun shinkafa ƴar gwamnati,katon ɗin taliya,maccaroni,kwalin indomie,galoon ɗin mangyaɗa,manja,krate-krate din kwai,madara da dai sauransu,haka akayita shigo dasu ciki gidan,mai Gwaggo Ladi zatayi inba callara uban guɗa ba tana rawa harda juyi tana cewa



"Alkhairi ya samesu!!! Alkhairi ya samesu!!! Yiririii nanaye!!! Yiriri nanaye!!! Zamuci daɗi kai kai!!! Zami ci daɗi kai kai!!! Casssss!!!! "



A nan ba su Sa'eeda saida suka dara sosai,ashe haka wannan tsohuwar take da darun tsiya,saima taje birni a gaskiya akwai cin dariya wallah,cewar Sa'eeda a cikin ranta tana dariya. Haka aka gama shigo da kayan sannan Uncle Hassan da Baba suka tafi masallaci tare da wasu bodyguards,a gida kuma Mairo da yayarta Na suka ɗora sanwar rana saboda baƙi,bayan Mairo tasa an yanka zabbi har biyar daga gidan saboda baƙin,su Umman Sa'eeda da Momin Sadam da Sa'eeda wani babban ɗaki aka ware musu ba kamar ɗakin da aka bama su Umman Sa'eeda a shekarun baya da sukazo ba,wannan ɗakin babba ne ga kuma babbar kafita da wata ƙarama,ciki suka shiga tare da ɗaukar butoci domin alwala tare da sallah.su Mairo da yayarta sai gyaran kaji suke harda Gwaggo Ladi uwar daru,babbar yayarta tasu wacca Gwaggo Ladi take kiranta da ƴar yaya har yanzu bata dawo ba,tana can baƙin ciki ya ƙara lulluɓe zuciyarta ganin Umman Sa'eeda cikin kwanciyar hankali da wadata ba kamar a da ba duk da ada ɗin ma tafisu.A can gidan ƴar yaya sai kai da kawo take tana neman yadda zata illata rayuwar  Umman Sa'eeda ,sai can tayi wani munafikin murmushi,tare da fita daga gidanta.



Gidansu Gwaggo Ladi ƴar yaya ta koma tare da ƴarta lokacin har sun kammala cin abinci suna hira,Uncle Hassan da Baba suna zaure suna hira abinsu,su kuma bodyguards da drivers an kai musu nasu abincin kasancewar sai gobe zasu koma Kaduna.Da sallama ƴar yaya ta shiga gidan,amsa mata sukayi sai tazo wurin Umman Sa'eeda tare da durƙusawa tana neman yafiyarta akan laifukan da ta aikata mata,da murmushi a fuskar Umman Sa'eeda tace ta yafe mata,zama ƴar yaya ta samu tayi tare da shiga hirar anayi da ita,Gwaggo Ladi sai kallon ƴar yaya take saboda tasan halinta akwai manufa a wannan neman yafiyarta ta,tasanta tun tana yarinya bata bada haƙuri balle neman yafiya,uwa-uba harda durƙusawa,lallai akwai *Lauje cikin naɗi*  tana da manufa kenan,sannan bazata taɓa bari ta cutar da Umman Sa'eeda ba saboda itama tayi taga babu riba balle ita,dole ta saka ido a duk motsinta, cewar Gwaggo Ladi wacca ta lula cikin kogon tunaninta akan babbar ƴarta ƴar yaya.



Haka suka cigaba da hirarsu wanda sallah ce ke tasar dasu,su Mairo da Naima sai wurin ƙarfe 8:45pm na dare suka tafi gidan,ita ƴar yaya bata wani daɗe ba tace zata wuce gida sai  gobe zata dawo, da Allah ya kiyaye hanyar gida suka bita dashi sannan suka cigaba da hirarsu.




Washe gari  bayan kowa ya karya kasancewar da sassafe mairo ta kawo musu da abin karyawa,koda ƴar yaya tazo da nata abin karin ta samu har sun shirya harda su Baba da Gwaggo Ladi za'ayi tafiyan domin har kebbi State zasu bayan sunje anyi musu passport tare da visar tafiya ƙasa mai tsarki,ciza yatsa ƴar yaya tayi saboda *plan A* ɗinta ya rushe,saura *plan B* wanda shi ne ƙarshe,suna shirin tafiya sai ƴar yaya ta dubi Umman Sa'eeda tare da cewa 




"Hussaina ni bana manta ba,ƴata ta tafi miki  da gyalenki gidana ba,yoo ni ina na sani ashe gyalen yana a hannunta,saida muka isa gida sannan na lura"



Lokaci guda take maganar tare da ciro gyalen,murmushi Umman Sa'eeda tayi tare da cewa



"Karki damu ƴar yaya ɗauka kawai nabar miki,kinga ga wasu kayan ma ki haɗa dasu na baki kyauta"



Rasss!!! Rass!!! Rarasss!!! Rass!!! Rass!!! Haka ƙirjin ƴar yaya ya daba domin idan Umman Sa'eeda bata yafa gyalen ba babbar matsala ce ba ƙarama ba,saboda abinda tayi ma Umman Sa'eeda kanta zai koma idan Umman Sa'eeda bata amsa ba.




*Waiwaye*




A lokacin da ƴar yaya tabar gidan zuwa gidanta,tafiya take amma zuciyarta na *saƙa da warwara* akan yadda zataga ƙarshan Umman Sa'eeda, daman ita tun tali-tali ba ƙaunarta take ba,koda ta shiga ɗakinta wanda ciki ɗaya kuma ƙarami ga uban tarkace kala-kala saboda ƙazama ce sosai ,ƴar yaya batayo gadon tsafta wurin Gwaggo Ladi ba,Mairo da ƴar uwarta sunfita tsafta da ɗaki mai kyau,su uku ne a wajen mijinsu kuma kowacce ita take cida kanta da ƴaranta saboda mijin bai ciyar dasu gashi lusari ne na ƙarshe,saidai idan ma sunyi su ɗan sammishi yaci,malalaci ne na ajin ƙarshe.



Kasa zama ƴar yaya tayi tana tufka da warwarar yadda zata ɓullowa Umman Sa'eeda da sauri kafin su koma birni don ta lashi takobin kodai ta halaka Umman Sa'eeda ko kuma ta illata rayuwarta ta har abada,tafiya take a ɗakin idan takai *Gauro sai takai mari* can ta saki wani munafikin murmushi tuno da malam Tanko Kwandi,babban malamin zaure ne a garin nasu,kuma malamin duba,yanada almajirai sosai a gidan nasa,nan da nan tafita daga gidan zuwa gidansu Gwaggo Ladi domin ɗaukar wani kaya na Umman Sa'eeda saboda shi malam Tanko Kwandi da kaya mutum yake amfani wurin yin sihirinsa,tare da wata ƴarta taje gidan,daman tun a hanya ta tsara yadda zata nemi yafiyar Umman Sa'eeda tare da durƙusa mata wurin neman yafiya domin *Durƙusama wada ba gajiyawa bane* sannan dole ta koyi *ladabin kunama* ta yadda haƙarta zatafi saurin cimma ruwa,haka kuwa akayi domin duk plans ɗinta sun tafi a daidai har tayi sa'ar ɗaukar gyalen Umman Sa'eeda tare da ma ƴarta lokacin hankalin kowa baya wurin,yarinyar ce ta fara fita sannan sai ƴar yaya daman tun a hanya ta sanar ma ƴarta yadda zasuyi aikin,itama ra fita.(Ya Rahman tun yarinya na ƙarama har ankoya mata makirci🤔🤔🤔)



Komawa gida tayi tare da siyar da wtea tunkiyarta ga maƙociyarsu sannan ta nufa gidan Malam Tanko Kwandi,tana isa babu ɓata lokaci ta sanar masa abinda ke tafe da ita,bayan ta kammala bayananta ya fara zane-zane a ƙasar dake gabansa,can ya ɗago ya dubeta bayan ya kammala, saida ya fara sauke wata nauyayyar ajiyar zuciya kafin ya fara magana



"A gaskiya bazamu iya kasheta ba,saidai mu illata ta idan kinaso,saboda ruhinta mai ƙarfi ne bata wasa da addu'ah"



Shiru ƴar yaya tayi tana kallonsa,can ta ce



"Tunda shegiyar tanada ruhi mai ƙarfi,jefa mata susar jiki,kaga shikenan kullum batada sukuni saina susar jiki"



Dariya sosai Malam Tanko Kwandi yayi can ya ce



"A gaskiya kinsan kan mugunta wallahi, zamuyi yadda kikashe amma fa akwai sharaɗi mai girma atattare da wannan sihirin"



"Faɗamin ko mene ne,zan cikashi indai har waccan shegiyar zatayi susar jiki a shirye nake"



Gyaran murya Malam Tanko Kwandi yayi kafin ya fara da cewa



"Sharaɗin shi ne,yanzu zanyi aiki akan abinda kika kawo sannan dole ki bata kayan tayi amfani dasu,idan kuma taƙi amsar kayan to kisani susar jikin kanki zata dawo sannan naki sai yafi nata sau miliyan"



Shiru ƴar yaya tayi tana nazari,ta yarda ko kuwa,wata zuciyar tana cemata *a'a* karta yarda wata zuciya tana cemata *Eh* ta yarda tunda tasan yadda zatayi ta amsa gyalen, gyaɗa mishi kai tayi tare da cewa



"Na yarda"



"To shikenan idan aka samu matsala ba daga ni bane,ki kuka da kanki"



Ɗaukar gyalen yayi tare da yin wasu *Surkullensa* sannan ya yamutsa gyalen tare da tottofe gyalen da wasu surutai wanda ni kaina gwanar ɗauko muku rahoto na kasan ganewa,yakai kusan mintuna sha-biyar yana wannan surutan sannan ya miƙata,tare da cewa



"Ki tabbatar da kin miƙa mata hannu da hannu kuma ta yafa sannan "



Tsayawa yayi da maganar tare da ɗauko wani ƙullin magani a wata ƴar jakar fata irin na wanzamai haɗi da miƙa mata,sai ya cigaba da cewa



"Ga wannan ki saka a cikin abincinta,ki tabbatar da taci abincin sannan ki miƙa mata gyalen,idan ta amsa ta yafa a jikinta,hmmmm lokaci guda zata fara susar jiki tare da iface-iface,sannan duk maganin duniyar da za'ayi mata bazata taɓa warkewa ba,don haka ina miki kashedi akan ki kula!!! Ki kula sosai!!! Ki tabbatar da taci abincin sannan ta yafa gyalen!!! "



Amsar gyalen tayi jiki na rawa tana ce masa zata kula sosai,kuɗin aikin ya umurta ta bashi babu musu ta ƙirgo kuɗin ta miƙa masa har da ɗori a sama wai ya ƙara(Ƴar yaya hmmmmm muje zuwa,My Esteem fans ince wani ko kuma inyi😷😷😷 )



Haka ta nufo gidanta cike da murnar nasara,shirye-shiryen karin kumallon da zata girka musu ta fara yi tun cikin daren,wanda da safen da ya dace taje da wuri sai akayi rashin sa'a iccan da aka siyo mata duk jiƙakƙu ne ba masu ci bane,sai wurin 9:21am na safe takai girkin kuma koda takai su har sun karya suna ma shirin tafiya harda su Baba da Gwaggo Ladi.




*Cikin Labari*




Ƴar yaya da taga alamun idan tayi wasa Umman Sa'eeda taƙi yafa gyalen to faɗin hausawa da suke cewa *Ƙaiƙayi koma kan masheƙiya* to lallai zai tabbata akanta,nan takai ta fara roƙonta Allah da annabi ta amsa gyalen ta ita bataso ta yafe tana cewa



"Don Allah kibar kyautan nan wallahi,amshi kayanki ina ni ina saka gyale mai tsada haka"



"A'a wallahi na baki duniya da lahira, ɗauka ai kinfi ƙarfin gyale a wurina ƴar yaya"cewar Umman Sa'eeda



"Na  roƙeki da Sarkin Sammai da Ƙassai ki amshi gyalen nan,wallahi ban iya yafashi don yafi ƙarfina" cewar ƴar yaya har idanunta sun ciko da ƙwalla



Sheƙeƙe kowa a wurin ya bita da kallo har Gwaggo Ladi wacca tasha sabbin kayanta,Gwaggo Ladi ce lamarin ƴar yaya ya fara bata haushi saboda ta ƙosa su hau mota mai A.C suje birni tana magana cike da ɓacin rai tana cewa



"Wai dole ne sai ta saka gyalen ƴar yaya,ce  nike ta ce kiɗau gyalen tare da sauran kayan nata kyauta,amma kina maida mana agogon hunnu baya,da yanzu har mun isa birni "



Cikin murya mai cike da damuwa haɗi da tashin hankali ta ce



"Nawa ne da zan saka gyalen, ai ba nawa bane,ta amshi gyalenta banaso wallahi"



"To bazata yafa gyalen ba idan ma wani ƙulla-ƙulla kikayi a cikin gyalen saidai ki saka,mara imani" cewar Momin Sadam wacca tun jiya take ankare da duk motsin ƴar yaya ita haka nan taji bata kwanta mata a rai ba kamar sauran.



Ce musu akayi su ake jira nan da nan suka miƙe,zumbur ƴar yaya ta miƙe tana cewa



"Wallahi baki isa ba!!! Sai kin yafa gyalen nan!!! Dole ne ki yafa gyalen!!!"



Da sauri tayo kan Umman Sa'eeda da gyalen, kafin da iso wurinta Sa'eeda ta saka mata ƙafa nan take ƴar yaya ta faɗi ƙasa ji kake timmmm!!! Lokaci guda ta fara susar jiki tana ihu,ai cak!!! Su Umman Sa'eeda suka tsaya hadi da juyowa saboda ihun da sukaji,ihu take sosai tana susar jiki tana cewa



"Wayyo!!! Wayyo!!! Wayyo!!! Ku sosamin jikina!!! Ku kawomin wuƙa ko laujeeee !!! Kai kai kai a sosamin!!! Kai kai kai a sosamin!!! Nace ku sosamin"



Kallonta kowa yake yana mamaki,wasu harda dariya musamman Sa'eeda saboda yadda take susar jikin nata sai kace motsattsa,can kuma ta miƙe tare da bin bangon ɗakin gidan tana susar jikinta kasancewar gidan babu flastan bango,sai faman goga bayanta take a bangon gidan ta ihu haɗi da cewa



"A sosamin!!! Ayimin susar jiki!!! Wayyo ƙyaiƙyayi!!! Na cuci kaina na biyewa ruɗin zuciyataaa,akaini gun Malam Tanko Kwandi!!! Kwandiiiii!!!!"



Ai wani irin daka tsalle tayi tana cire rigar jikinta saiga nonuwanta masu kama da slippers sun bayyana suna rangaji,susar jikinta tare babu ki babu gani,su kuma sun kasa cemata komai ko kuma kawo mata ɗauki domin yawancinsu mutuwar tsaye sukayi suna kallonta musamman Umman Sa'eeda wacca ta lula kogon tunani a zuciyarta tana cewa 'Lallai Allah da girma yake,kenan cutar susar jiki ƴar yaya taso sakamin,wato shiyasa ta dage saina yafa gyalen, ɗan Adam hmmm Allah kasa mufi ƙarfin zucoyoyinmu' haka tayita zancen zuci,suna a haka suka ji sallamar Baba da Uncle Hassan  kasancewar Sa'eeda ta ruga waje ta sanar musu  abinda ke faruwa,ai da sauri suka iso gidan,Cak! Uncle Hassan da Baba sukayi ganin ikon Allah,ƴar yaya susar jikinta take haiƙan babu ji babu gani tana ihu tana kiran sunan Malam Tanko Kwandi yazo ya taimaketa,shiru kowa yayi yana kallon ikon Allah musamman Gwaggo Ladi tana kallon yadda babbar ɗiyarta ta koma saboda mugun nufi lallai hassada batayi ba,suna a haka sai can Uncle Hassan ya ce



"Waye Malam Tanko Kwandi din da take cewa a kaita wurinshi" 

 


Baba ne ya ce



"Wani Hatsabibin malamin duba ne a wannan garin,wurinshi taje ƙila,wai meye ya faru ne kunƙi mana bayani"



Sa'eeda ce ta fara koro musu bayani tiryan-tiryan harda dramar da akayi akayi akan gyalen sannan ta taɗiyetan da tayi saboda nufo Ummanta da tayi da gyalen da susar jikinta da tayi duk babu abinda ta tsame komai ta sanar musu, shiru su Uncle Hassan da Baba sukayi suna kallon ƴar yaya wacca ta fita daga hayyacinta tana faman susar jiki tana iface-iface tare da kiran Malam Tanko Kwandi ya kawo mata agaji.Duk da muguntar da taso yima ƴar uwarsa amma haka yace su shigo da ita mota akaita wurin malamin da take faman kira,ai nan Baba yace babu inda zasuje,ita da taso illata Hussaina shi ne zai kaita,murmushi Uncle Hassan sannan ya ce



"Baba komai ahalinka zasu mana bazan damu ba saboda a baya ka taimake mu,sannan ita wacca tayi muguntar ai gashi ya faɗa kanta,shi daman sharri ɗan aike ne yanzu ba gashi ya dawo mata ba,ta gina ramin mugunta babba  gashi yanzu ta fada cikinsa,kawai yanzu mukaita wurin malamin, tafiyar mu sai mubari gobe in shaa Allah"



"Tabbas ka cika ɗan halak kaida ƴar uwarka da Mahaifiyarka,shikenan tunda kace haka a kaita ɗin,ashe daman ladabin kunama tayi jiya tanada munafa a cikin ranta"



"Ni daman tun tuni ban yarda da ƴar yaya ba,saboda tun tasowarta bata bada hakuri balle neman yafiya koda ta laifi tayi,nima nayi kokwanto a jiyan wallah ashe tanada manufa ai gashi nan abinda nake miki tsoro gashi ya sameki saboda hassada,nace miki nima nayi babu riba balle ke" cewar Gwaggo Ladi wacca sai yanzu ta tsoma baki a tattaunawar da ake.



Haka su Mairo da yayarta mai suna Na'ima suka taimaka ta shiga motar,su Umman Sa'eeda, Momin Sadam,Sa'eeda tare da Gwaggo Ladi suka shiga mota ta biyu,lokacin shiga motar saida akayi daru da Gwaggo Ladi,su Mairo aka bari gida.kasancewar Baba yasan gidan Malam shi ne a gaba da Uncle Hassan yana mishi kwatance ,a bayan mota ƴar yaya cw ra bodyguards har biyu,a haka har suka iso gidan Malam Tanko Kwandi,gida ne babban mai kyau saboda Malam Tanko Kwandi shahararran Malamin duba ne,wanda har ƴan siyasa ne,ƴan kasuwa ne,manyan mata ne karuwai ne da dai sauransu suna zuwa wurinsa saboda aikinsa yanayi sosai.



Suna isa lokacin yana zaune tare da manyan almajiransa,sai bodyguards dinsu Momin Sadam suka fito da ƴar yayaya tanata faman ihu da susar jiki,Malam Tanko Kwandi yana ganinta ya tintsire da wata muguwar dariya harda bubbuga ƙafa,miƙewa yayi tare da ce masu Uncle Hassan da sauran mutanan bisimillah,su shigo ciki da ita,babu musu kowa ya shigo cikin ɗakin da yake duban nasa a ciki,dayake ɗakin babba ne shiyasa ya ɗaukesu baki ɗaya,bayan kowa ya samu wuri ya zauna tare dayin shiru saidai ihun ƴar yaya da susar jikin da take yi babu ji babu gani, gyaran murya Malam Tanko Kwandi yayi sannan ya fara magana



"Sannunku da zuwa baƙina,meke tafe daku"



"Magani mukazo ka mata" cewar Uncle Hassan yana cilla masa harara



Dariya ya tintsire dashi ji kake Kya! Kya! Kya! Babu ƙakƙautawa,saida yayi dariya ma'isarsa sannan ya ce



"Magani! Magani! Hmmmm! Da alama bata sanar muku da sharadin dana gindaya mata ba"



"Wani sharaɗi kenan,sannan ko zaka iya sanar mana abubuwan da ta ce maka"cewar Baba



" Eh zan iya sanarmu sosai ma kuwa, farko da tazo ta sanar min tanaso a kashe wata mata mai suna Hussaina wacca tazo gidan iyayanta"



Dummmmmmmmmm!!!!!!!!!!!!! Haka ƙirjin Umman Sa'eeda ya bada kamar bomb ya tashi a ƙahon zuciyarta haka taji,lokaci guda ta dafe ƙirji tare da waro manya-manyan idanunta waje tana cewa



"Kasheni!!! Ƴar yaya kikeso ayi,Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un,yanzu har ƙiyayyar da kikemin takai ki bada kuɗi ayi min asirin mutuwa, ya Rahman"



Kuka Umman Sa'eeda ta fashe dashi mai ratsa zuciyar duk mai sauraronta,kowa a ɗakin mamaki da al'ajab ta cikasu,harda Baba da Gwaggo Ladi suma maganar da rikita musu ƙwaƙwalwa,Malam Tanko Kwandi baibi takan kukan Umman Sa'eeda ya cigaba da cewa



"Bayan ta sanarmin ta ƙudurinta akan ita Hussainar, sai na duba mata,faɗa mata nayi sihiri bazai taɓa iya kasheta ba saboda addu'o'in da take a kullum saidai ta faɗi wani abun da take so ayi mata,sanarmin tayi tana so a saka mata susar jiki har ƙashan rayuwarta,ni kuma nace mata akwai sharaɗi akan idan ita Hussainar taƙi yafa gyalen to ta tabbas susar jikin sai koma mata sannan nata zaifi na wacca takeso a saka mata yawa,kuma na ce mata babu maganin susar jiki a duk inda za'a je,koni kaina banda maganinta balle makarinta"



Shiru ɗakin yayi kowa yana nata karanta wasiƙar jaki,sai can Baba yace



"A dauketa mu tafi,daman *duk wanda ya ɗibo da zafi ya kai bakinsa* shi daman sharri ɗan aiki ne duk idan yaje sai ya dawowa mai shi,gashi nan ya koma miki,wallahi *Albasa batayo halin ruwa ba* idan kuwa da tayi da baki aikata abinda zaije ya dawo miki ba"



Miƙewa yayi,suma sauran suka miƙe,Gwaggo Ladi ta ce



"Na nutsar dake akan illar Hassada da baƙin ciki amma kinƙi ji,nidai babu ruwana kuma gobe-goben nan zamu tafi birni musha A.C ,ke kika jiyowa kanki"



Wucewa tayi abinta zuwa mota,har a lokacin Umman Sa'eeda na kuka jin wannan mugunta haka,amma Alhamdulillah tunda Allah ya tsareta daga sharrinta,ita kuwa ƴar yaya haka aka ɗauketa tana susar jiki haɗi da iface-iface tana kiran Malam Tanko Kwandi ya kawo mata agaji, shi kuws babu abinda yake inba dariya ba,suma almajiran nasa sai dariya suke mata suna nunata,ko nima na ɗan dara saboda yadda take susar jikin nata dole ka ɗan dara😂.



Haka bodyguards suka shiga da ita cikin motar,da farko gidan mijinta Baba ya ce akaita sai mijim yace inaa ba'a gidansa ba taje can ya saketa saki ɗaya daman  ya taɓa sakinta saki biyu a baya shikenan ta cike uku reras! Haka suka dawo da ita gidan,gashi su Baba da Gwaggo Ladi sunce tafiya birni babi fashi tunda ita ta siyowa kanta da kanta,yarinyar wacca bata wuce shekara 14 yanzu zata dinga zama da ita kafin su Baba su dawo garin domin yarinyar bazats iya kula da ita ba.




Washe gari da wuri suka karya kumallonsu tare da shirin cikin sauri saboda Uncle Hassan yanada ayyuka a gabansa,haka sukayi ma su Mairo da Na'ima sallama sannan suka fito wanda lokacin ƙarfe 9:12am na safe,suna cikin niyyar shiga mota saiga wani mai machine da mutum a bayansa ya faka a wurin motocin nasu,sauka yayi tare da biyan mai machine kuɗinsa,juyawan da zaiyi Karaf! idanunsa ya sarƙafe dana Umman Sa'eeda,nan take zuciyoyinsu suka bada Daramm!!! Damm!!! Dadammm!!! Lokaci guda Umman Sa'eeda ta rikice tare da nuna wannan mutumin,muryarta na rawa tana cewa..............................






*Mu haɗu a pages na gaba don cigaba da karanta wannan littafi mai cike da chakwakiya iri-iri haɗi da darussa da dama✍️🙃🙃🙃🔥🔥🔥🔥🔥🌼🌼🌼🌼🌼*





*Hmmmmm waye wannan mutumin daya rikita Umman Sa'eeda lokaci guda???*...........







*Wai Ina Love birds  ne 🕊️🕊️ da amarya khairat,wace chakwakiyar suke ciki,ko kuma komai ya daidai a wurinsu???*.........



*Wai Ina Sarere ta Sankeru,tare da su Nusaiba masu pampers???*.............



*Kai! Kai! Kai! Abubuwa da yawa🙃🙃🙃,amsoshinku na nan tafe a pages masu zuwa,kudai  ku cigaba da zubo ruwa comments da reactions🌹🌹💖💖🌼🌼💘💘,ni kuma bazan gaji ba wurin suburbuɗo muku new updates zafafa* 🌹🌹🙃🙃💖💖🌼🌼💘💘😂🔥🔥🔥🔥🔥



*Ina ƙaunarku My Esteem Fans Lodi Lodi* 🌼🌼💖💖🌹🌹🙃🙃💘💘




Post a Comment

0 Comments