TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Babu so page 17

 


      *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*

                 _(Miya kawo kishi?)_




              *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*



*_BABU SO.. 👉🏻AREWABOOKS🫶🏻_*



https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718



*_17_*



........Kasancewar Abie a wajen ya sashi ƙin cewa komai ya ɗauketa gaba ɗayanta ya haura sama aunty Mimi biye da shi. Ɗakin Mamie suka nufa kamar yanda Aunty mimi tace.

     Wata wawuyar ajiyar zuciya ta saki mai ƙarfin gaske lokacin da yake ajiyeta akan gado, dan tunda ya ɗakkota ta ɗauke numfashinta da rumtse idanu zuciyarta na bugawa da sauri-sauri. Shi ɗimma dake ƙoƙarin dannewar tashi zuciyar bugu take da gudu a ƙirjinsa har numfashinsa na seizing. Ajiyar zuciyar ya sauke tamkar ita, sai dai tasa ta fitane a ɓoye. Sallamar Mamie ta sashi haɗiye abinda ke masa kaikawo, tray ɗin hanunta ya amsa yana ɗan murmushi da faɗin, “Mamie da kanki”.

      Murmushin itama tayi batare da tace komai ba, ta harari Anam dake kwance lamo tana sauke ajiyar zuciya. “Mai rakin tsiya yanzu waye yaji daɗin? Nikam zanga yanda zaki ƙare lokacin rainon ciki balle ranar haihuwa, mijinki dai yaga takansa ai”.

     Dariya aunty Mimi ta sanya, yayinda Anam ke tura baki gaba, taɗan saci kallon Shareff sai ko idonta cikin nashi. Sosai ya sarƙeta da su, sai da ƙyar ta samu damar fisgewa tari mai alamar sarƙewar yawu na kufce mata. Wani irin yanayi data kasa bama fassara ta karanto a cikin ƙwayoyin idanunsa, hatta da tsigar jikinta yamutsawa ta shigayi, ga tarin yaƙi tsayawa har sai da Aunty Mimi ta tadata zaune tana bubbuga bayanta. Kamar ba shine sanadin komaiba cike da basarwa ya miƙama Aunty Mimi ruwan, a baki ta saka mata, sai da tasha sosai kafin tarin ya lafa idanunta har sunyi jajir. Sannu Mamie tai mata tana ƙoƙarin ficewa domin nuna kara garesu tunda dai duk suna ƙoƙarin nuna kulawa gareta bai kamata ita saita tsaya ba. 

     Yana daga tsaye har Aunty Mimi ta bata umarnin fara cin abinci bayan ta ɗaura mata tray ɗin akan cinyarta. A hankali ta fara cin abinci, sai ƙunƙuni take a zuciyarta na zamansa ɗakin. Oho bai san tanayi ba, dan babu alamar zai fita ɗin. Aunty Mimi ta miƙe ta fita saboda kiran mijinta daya shigo mata a waya. 

       Shiru ɗakin bakajin motsin komai sai na ƙarar spoon da take juyawa a plate, dan gaba ɗaya tama kasa cin abincin yanda ya kamata, tarasa mike damunta, kunyarsa ko haushinsa, dan abinda ya faru a gidanta ɗazun ya gagara barin zuciyarta. Jin shiru kamar baya ɗakin ya sata ɗan ɗagowa da nufin satar kallonsa sai suka sake haɗa ido. Kanta ta maida ga abincinta tana sake tsuke fuska.

     (Sai kallon tsiya) ta faɗa a ranta. Kamar yaji mitake faɗa ya zura wayarsa a aljihu yana ɗan jan siririn tsaki. “Baki iya komai ba sai kallon mutane laziness”. 

     Kasa daurewa tai sai da ta ɗago ta kallesa idanunta cike da tsiwa. “Toni da baka kalleniba zaka san ina kallonka ne.....”

       “What!”.

  Ya faɗa cikin ɗan kausasa murya da waro idanunsa kanta sosai. “K! Wai yaushe na zama abokin wasanki ne a gidan nan?”.

       Ƙin cewa komai tai, sai dai bakinta a sama kamar zai taɓo silin. A ranta ko addu'a take aunty Mimi ta dawo kafin ya fara zazzabga mata maruka. Ganin yana matsota tai saurin faɗin, “Amma matarka ɗazun datai iskanci agaban mutane baka hukuntata ba sai ni, kuma jinina da aka zubar sai na rama”. Ta ƙare maganar wasu zafafan hawaye dake nuna tabbacin abun na ranta kamar zanen dutse har yanzu suka shiga rige-rigen sakkowa. Cak ya tsaya yana kallonta, kuka take sosai kamar wadda aka doka, kusan tsahon minti guda da wasu sakanni ta gagara tsaidasu. A hankali ya rumtse idanunsa, tare da furzar da ƙaramin huci daga bakinsa. Shiru bashi da alamar cewa komai balle lallashinta, itako sai ƙara matso hawayen take wani baƙin ciki da takaicinsa na sake hasalata, tabbas da ace lafiyar ƙafarta ƙalau ɗakin zata bar masa....

       “K sau nawa ina hanaki tarayya da wannan yaron amma kika maidani sauna? Bayan shi ba muharraminki ba itako *Matata ce!*”.

     Karan farko da tunda ta fara kukan ta ɗago jajayen idanunta tana kallonsa cikin tsakkiyar ido. Shima kallon nata yake a tsakkiyar idon......

       Ita ta fara janyewa cikin ƙunƙuni tana faɗin, “Ni dai baza'a rabani da masoyina ba”.

     Sosai kalaman nata suka daki ƙirjinsa. Sai dai kafin yay wani yunƙuri aka dakatar da shi.

    “Mike faruwa anan?”.

   Aunty Mimi dake shigowa ta faɗa cikin dariya. Ita ta fara janye nata idanun, batare da tace komai ba ta zame ta kwanta. Shima numfashi ya ɗan fisga, cikin yanayi kamar mai borin kunya ya ɗaga kafaɗarsa. “Nothing Aunty. Zan wuce gidane goodnight”. Kafin ta samu damar cewa wani abu yayi ficewarsa. Da kallo ta bisa har ya fice, kafin ta juyo ga Anam dake faman sauke ajiyar zuciya.

     Komai batace mataba, sai da ta tadata zaune ta bata abincin da kanta tare da magungunanta sannan ta fiskanceta da ƙyau. Kai tsaye tace, “Mamana kina son Shareff ko??!...”

        “God for bid Ummie”. 

  Ta faɗa cikin tarar numfashin Aunty Mimi da saurai.

    “Sure?”.

“Yes Ummie”.

Yanda ta bada amsar da ƙwarin gwiwa yasa Aunty Mimin haɗe fuska tana mata kallon sama da ƙasa. Cikin rashin wasa tace, “To *_BABU SO MIYA KAWO KISHI?!”*.

        “Kishi kuma Aunty? A dalilin mi zanyi kishinsa?”.

     Ko amsa ɗaya Aunty mimi bata amsa mata ba, sai dai ta kafeta da ido ganin hawaye na ciko mata ido. cikin ɗan ɗage kafaɗa tace, “Okay fine kwanta kiyi barci”.

    Kwanciyar tayi, tana ta faman ALLAH ya kiyaye ta so wannan mutumin a zuciyarta, a fili dai bakinne kawai ke motsawa babu sautin fitar magana......


    ★★


   A hankali yake driving ɗin tamkar baya so ko kuma shi kaɗaine a titin, motoci da yawa sai sun masa horn yake ɗan kaucewa ya basu hanya su wuce, ga kiran Fadwa dake faman shigo masa waya babu ƙaƙƙautawa. Sai da tai wajen bakwai baida alamar ɗauka, ana takwas ɗinne ya fisgi wayar a fusace daga change daya sata yakai kunne. Sai dai baiyi magana ba dan inhar ransa ya ɓaci baya son ya ringa cewa komai....

      “My son!”.

Muryar aunty Mimi tazo masa a bazata. Da sauri ya cire wayar a kunensa ya kalla. Tabbas Aunty Mimi ɗince ba Fadwa ba. Yawu ya haɗiye da ƙoƙarin saisaita kansa. “Yes small Mom ko nayi mantuwa ne?”.

      “Da alama tunda ka tambaya ƙila kayo ɗin”. 

  Ƴar dariya yayi yana shafa kansa da lanƙwasa kan motar ya shiga layin gidansa. “Aunty kenan, da alama magana kike nema dai kawai”.

         “Kusan hakan, sai dai kai tsaye zan yita, kamar yanda nayi a ɗayan ɓangaren”.

      A hankali ya tsaida motar a ƙofar gate, sai dai baiyi horn ba. “To ina saurarenki mamana!”.

        “Babana kana son Anam ko?!”.

    Da ace ruwa yake sha ko cin abinci babu shakka sai ya ƙware dan abinda Small mom ɗin nasa ta faɗa yazo masa a baza. Ya haɗiyi yawu da sauri jin maƙoshinsa na ƙafewar danshi. Yay ƙoƙarin saisaita kansa kai tsaye yace ni da nai aure sati guda kuma”.

     “Ba labarin aurenka nake tambaya ba, dan nima ban manta lissafin ba. Ka bani amsata kawai”.

          Steering ya ɗan daka yana cije lips, cikin son kauda mata dukkan wani tunani babu ko gargadar murya ya bata amsa.

     “Aunty ni matata kawai nake so, bayan ita babu wata a raina”.

        Shiru Aunty Mimi tai, sai kuma ta saki murmushi mai sautin da har yaji, cikin dakewa tace “Sure?”.

     “Babu kokwanto a maganata Mom”.

“Okay fine. To amma *_BABU SO MIYA KAWO KISHI?!*”.

        “Kishi kuma?! Sai dai na zuminci”.

     Ƴar dariya aunty Mimi tai da faɗin, “Lallai kam”. Tana yanke wayar.

      Tamkar wanda aka zarema lakar jiki haka yay baya luuu jikin sit ya kwanta, idanunsa da suka canja launi ya lumshe, tsahon mintuna ya kasa horn balle yunƙurin shiga gidan. Ga kiran dake shigo masa waya da baya raba ɗayan biyu Fadwa ce amma ya kasa yin komai. Sai da ya sake shafe kusan mintuna goma sha biyu har mai gadi ya gaji da leƙowa ransa fal mamakin lafiya sannan yay masa horn.

       Da ɗan gudunta ta fito, duk da ranta a ɓace yake saboda kiran da take jera masa yaƙi dagawa sai ta danne saboda shawarar su Sima da take hange mafita a gareta basai ta cigaba da tada jijiyar wuya a wajensa ba. Ta ɗanesa tare da maƙalƙalesa, ko kulada yanayinsa batai ba ta haɗe bakinsu. Ƙoƙarin janyeta yay yana kauda kansa kodan maigadi da yake da tabbacin zai iya hangosu amma ta hanashi damar hakan. Dole yay ta maza ya tura murfin motar da kafarsa ya ɗauketa gaba ɗayanta yay sasheta bayan ya raba bakinsu da ƙyar. A kujera ya zube da ita jikinsa, babu wani ɗaga kafa ta sake maida bakinta kan nasa. Baya buƙatar komai a halin yanzun, sai dai bazai iya ƙin bata hakkintaba koda ace faɗan doke-doke sukai indai ta nema zai biya mata, balle ma baya buƙatar haɗa wata matsala tasa ta waje da cisgunawa iyalinsa  wannan alƙawarine ya daukama kansa insha ALLAH, laifinta kuma zai mata hukunci a lokacin daya shirya. Duk da babu wani karsashi tare da shi ita ke kiɗanta tana rawarta bata damuba, sai da ta tabbatar ta isar da saƙon da take bukata sannan ta barsa tana mai kallonsa cikin ido cike da so da kaunarsa.

    “I love you my Soulmate”.

Idanunsa ya ɗan lumshe ya buɗe akanta. Batare da yace komai ba ya lakaci hancinta da yatsansa. Sai kuma ya ɗanbi falon da kallo. Ganin komai tsaf yaji haushinta ya ragu a ransa. Ya ɗan rungumota jikinsa da sumbatar hancinta. “Haka nake so na dinga ganinki k da gidan nan a koda yaushe”.

     Kai ta jinjina masa tana murmushi da faɗin, “Zaka sameni mai aikatawa”.

         “ALLAH yay miki albarka bari naje na ɗan watsa ruwa”.

     “Kodai ka fara cin abinci”.

Ɗan kallonta yayi na wasu ƴan mintuna, “Sure baiyi ƙauri ba na yau?”.

         “ALLAH bai yiba”.

   “Okay muje”.

Duk da ba son cin abinci yake ba haka ya dinga turawa, dan babu makusa a girkin sai abinda ba'a rasa ba. Dan kawai ya bata ƙwarin gwiwar cigaba dayi kamar hakan ya yaba tare da saka mata albarka..


       ★★★★★


   Kwanaki sun cigaba da shurawa Anam na samun lafiyar ƙafarta. Tun daga ranar dai bata sake ganin Shareff a ƴan dubiya ba. Sai dai takanji maganarsa yazo gidan ko su Amrah suce mata yazo. Dan kamar da gayya sai ya daidaici lokacin da bata falon yake zuwa. Bata damu ba, dan a wannan gaɓar bama ta buƙatar ganin nasa sam. Tana son ƙara zama nesa da shi dan tunanin da aunty Mimi keyi a kanta ya gushe har abada. Kwanakinta biyar ta take ƙafarta sarai ta koma zuwa aiki. Kullum takan shiga gaida matan gidan cikin gida kamar yanda Mamie ke jaddada mata. Sai dai kuma iyakar Mom da Aunty Amarya kawai take zuwa ta gaida bata shiga sashen Mommy dana Gwaggo. Wajen aiki kam tare suke fita da Khaleel, wataran ya dawo da ita wataran Yaseer ya maidota dan yanzu ta ɗan fara sakin jiki da shi ganin bai nuna mata wata alama data danganci soyayya sai abota kawai. Muzzaffar ma yasha gwada zuwa ɗaukarta a office ɗin amma taƙi bashi fuska sam, hakan yasa ya fara zuwa gida kai tsaye dan shikam dai yaga matar aure. Tun tana noƙewa harta ɗan fara sakewa saboda huɗubar Aysha. Sai dai duk da hakan taƙi yarda ta amsa tayin son sa. Tana dai saurarensa darajar Abbansa abokin Abie ne kuma abota mai ƙarfi tun ƙuruciya dan tare sukai secondary school, a yanzu haka kuma suna ɗan huɗɗar kasuwanci tare. 

       A haka kwanakin hutun Shareff suka cika, Maheer ma ya koma katsina wajen nasa aikin tun satin daya shige. Da farko Shareff baya zuwa gidan da safe sai ya taso aiki yake shigowa ya gaidasu. Sai randa yazo sallama da su aunty Mimi da zasu koma Malaysia saboda yara makaranta ya samu Yaseer ya kawo Anam gida. Kuma har cikin gida Yaseer ɗin ya shigo gaishe da su Mamie, a yanda suka amshesa da alama ba wannan ne ma farko ba kamarma ya zama ɗan gida. Komai baice ba, sai dai koda Yaseer ya gaida shi hannu kawai ya ɗaga masa, daga karshe ma ya miƙe ya fice batare da an kammala sallamar ba. Da kallo kawai aunty Mimi ta bisa tana ƴar dariya, Anam kam ta taɓe baki da sake maida hankalinta ga Yaseer tana dariyar maganar Amrah kamar ma bata san da Shareff ɗin ba. Dan koda ta shigo ta gansa a taƙaice tace “Yaya good evening” tai wucewarta. Shi kuma bai amsa mata ba sai hararar da yabi ƙafafunta da su dan kansa a duƙe yake yana daƙilar waya.

        Washe gari da shi akaima su aunty Mimi rakkiya airport, daga can kuma yay wucewarsa office. Anam kuma suka wuce tare da Khaleel daya buga mata warning ɗin kar ta sake tabi wata mota zai zo ya maidata gida da kansa koda bai tashi aiki ba. Badai tace masa komai ba, amma ta bisa da kallon mamaki. Hakan kuwa akai, tun kan ma a tashi aiki yazo yana zaman jiranta, washe gari ma haka sukai haka har kusan sati biyu da su Mamie suka fara shirin komawa suma. Nan fa hankalin Anam ya tashi, ta dinga kuka da magiyar zata bisu Mamie tace bata isa ba. Daga ƙarshe tai mata kaca-kaca sannan ta dawo lallashi da nasiha. Haka tanaji tana gani suka tafi suka sake barinta a Nigeria ita kaɗai. Cikin gida ta sake komawar dai sashen Mom dan nasu gidan an rufe kuma, ranar haka ta yini sukuku kamar mara lafiya, da ga ƙarshe ma har zazzaɓin sai da tayi. Sai da Khaleel ya samo mata magani.

    Su Mamie juma'a suka wuce, dan haka bata fita ko'ina ba sai monday tai shirin zuwa wajen aiki. A cikin ɗaya a dogayen abaya da Mamie tazo mata da su tai shirin, bayan ta saka kayan hidimar ƙasa a ciki dan sanyi takeji yau. A hankali ƙamshinta ke fita, ga black skin nata na shining exactly cikakkiyar ƴar Africa. Bisa matsawar Mom ta zaman yin breakfast da abinda take iya ci da Mom ta jura girka mata batare da gajiyawa ba. Kaɗan ma taci ta miƙe tana faɗin, “Alhmdllhi”.

        “Badai ƙoshi ba?”.

  Mom ta faɗa tana kallonta. Murmushi tayi mai sanyi tana jinjina kanta, dan gaba ɗaya ta zama wata sukuku. “ALLAH Mom na ƙoshi, yau kwata-kwata banajin cin komai ne”.

     “Anjima fa zaki iya jin yunwa”.

“To Mom bara naje da shi office ɗin”.

Babu musu Mom ta juye mata a kula mai ƙyau. Sai da ta jira  Khaleel yasha shayi shima sannan, fita yay akan ta samesa waje zai shiga ya gaida jama'ar gidan. Saboda kar yasata binsa zuwa gaida su Mommy da tun kan su Mamie su wuce bata zuwa gaida su, shiyyasa ta noke akan zata samesa a mota. Sai da ya fita da kusan mintuna huɗu sannan ta fito. Waige-waige ta shigayi a harabar gidan babu alamar motarsa, tasan yakan kaita waje wani lokacin, dan haka ta nufi gate idan ya fito kawai sai su wuce.

      A wajen gate ɗin kuwa ta samu motar Khaleel tare da makanike, ta ɗanyi tsai tana kallon motar da tai fakin a kusa da motar Khaleel ɗin. Kamar tasan motar, sai dai ta manta mai ita dama yaushe ta taɓa ganinta.... Horn ɗin da akai ya sata haɗiye sauran tunaninta. Makaniken dake duba motar Khaleel ya ɗago yana kallonta “Hajiya kamar dake ake fa”.

    Ba laifi yanzu kanta ya ƙara buɗewa da jin hausa fiye da yanda tazo, ta jinjina masa kanta kawai batare da tace komai ba. Da farko bataji zataje ba, sai kuma ta canja shawara da tunanin ko Yaseer ne ya ɓadda kama. Murmushi ta saki akan wannan tunanin tana nufar motar. 

     Yanayin sanyinta a tafiyar ya sashi kafeta da ido cike da nazari, gashi bayan murmushin dake fuskarta babu wani alamun nishaɗi ko farin ciki a tattare da ita. 

    Zuciyarta ta gama yanke mata shawarar Yaseer ne, hakan yasata nufar ɗayan gefen batare da neman sanin waye ba ta buɗe ta shiga cikin ƴar dariya tana faɗin “Lallai ma Yaseer, kana tunanin ɓadda kama zata sa na gaza gane k.....” Sauran kalmomin suka kasa ƙarasa fita a bakinta saboda ƙamshin turaren da sai a yanzu ta samu nutsuwar banbancewa. Da sauri ta juyo batare data ƙarasa rufe motar datai yunƙurin yi ba. Har cikin rai ta tsorata da katoɓararta, amma sai ta dake cikin son kame kanta tace, “Oh Yaya yi haƙuri, ALLAH nama zata Yaseer ne ina kwana!”.

        Shiru kamar bazai amsaba, dan tunda ta shigo bai kalleta ba ko sau ɗaya. Idanunsa da suka surku da ɗan ja ya ɗago ya zuba mata. Ƙoƙarin dannewa da ɓoye tsoranta take a fili, ta kai hannu kan ƙofar da nufin buɗewa ta fice ko zata samu damar shaƙar iska yasa lock.

    (Ya ALLAH, wannan mutumin zai iya cinyeni fa a motar nan wlhy gara na lallaɓa) ta ayyana a zuciyarta. Idanu ta marairaice kamar gaske ta ɗago tana kallonsa, “Yaya kayi haƙuri ALLAH ban san kai bane”. Motar yayma key batare da yace mata komai ba ya fisgeta har yana bulama bakaniken dake duba motar Khaleel ƙasa.

     Sunayen ALLAH kawai take ambata a ranta dan tasan itakan yau sai romanta za'a samu a hanun mugun nan......

     “Mina faɗa miki akan yaron nan kwanaki?!”. Ya faɗa a kausashe dai-dai yana hawa kan babban titi. Kallonsa tai fuska a dake, ta kuma ɗauke da sauri saboda tasa fuskar ma tafi tata dakewar. Cikin ɓata fuska da tura baki tace, “Toni Yaya bamfa san wa kake nufi ba ai”.

     Komai baice mata ba, ya cigaba da driving nasa, sai da suka iso dai-dai wajen nata aikin yay fakin daga ɗan nesa. Da mamaki ta kallesa, “Yaya yanaga ka tsaya na.....?”

        Rinannun idanunsa daya dasa a kanta ya sata haɗiye sauran maganar muƙut, tai ƙoƙarin ɗauke idonta ya hana hakan cikin tsareta da nasa da duk suka firgitata. “Ni kike faɗama bakisan wa nake magana akai ba.”

      Da ƙyar ta fisgi idanunta tai ƙasa da su zuciyarta na bugawa da sauri saboda yanayinsa ya masifar tsoratata. Da sauri ta rumtse idanunta saboda jin yatsun hanunsa a kan haɓarta, ya ɗago fuskarta sosai tare da matsota garesa har suna iya shaƙar numfashin juna. “Buɗesu kona mareki!!”.

      Buɗewar tai da sauri saboda kusancinsu ba ƙaramar rikitata yay ba, hatta shi kansa yana iya jin sautin bugun zuciyarta ta hanyar ɗagawa da ƙirjinta ke ɗanyi da sauri-sauri..........✍  




Post a Comment

0 Comments