TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Zabin mahaifina page 26-28

 🌳🌳UMMU AFFAN🌳🌳

[04/02, 03:06] Halimatu Sadiya Affa Fbk: 🌳🌳🌳🌳🌳

      ZAB'IN MAHAIFINA

        🌳🌳🌳🌳🌳


Written by SADIYA ALHASSAN (Ummu Affan)


    🌐HAJOW 📝🌐


🌐👩‍👧‍👧👩‍👧‍👧👩‍👧‍👧HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS ✍🏾✍🏾✍🏾🌐


Dedicated to PRINCESS ESHAT AYSM

AYSHA BICHIKI


Page 26


Yana zuwa office ya kira mahaifiyar sa akan ta aiko masa da abinci da rana,


" ina matan naka suke da zan aiko maka abinci daga nan?" ta tambaya


"Momy yau fa girkin humaira ne"



"Ita 'yar mulkin naka bazata iya aikowa da abincin ba kenan ko?"



to momy yaushe ta tashi ma bare tayi wani girki ita da take tashi 11:00am   ko breakfast batayi ba alokacin bare ayi maganan na rana. 


"Allah ya kyauta"


 tace sannan ta kashe wayarta.


karfe d'aya ta aiko driver ya kawo masa abincin.



Da rana humaira tasa blessing tayi jallop din shinka fa da wake da nama, ta aikawa salma dashi.



Zuciya d'aya salma ta karb'a, har zata faraci sega me aikinta ta shigo.


Tsugunawa tayi a gnfenta tace 


"sannu aunty"



Kallonta salma tayi ta amsa, sannan tace lapia dai jamila??ko kina bukatar wani abu ne?



sunkuyar dakai jamila tayi kafin tace "aunty daman akwai maganar da nake son zan fada miki amma dan Allah kar kice a bakina kikaji🙏🙏"



"Ina sauraronki" salma ta fad'a.


dan Allah Aunty kar kici abincin nan, yanzu blessing take fada min wai tazo shiga falon taga hajia tana zuba wani abu a cikin abincin.


kuma tace ta tabajintana waya akan zata zuba miki magani abinci kici ki mutu.


"Nagode!jamila" amma dan ALLAh banason naji maganar nan a bakin kowa."


"to aunty" jamila ta amsa


tashi salma tayi ta dauko bakin leda ta juye abincin aciki ta mika mata 


"gashi kije ki saka a cikin shara amma ki boye kar wani ya gani"


karba jamila tayi ta saka a cikin hijabinta ta fita.


Ajiyar zuciya salma ta sauke, tanayi ma Allah godia daya kubutar da ita daga fadawa kaidin humaira.


karfe 8:00pm abdul ya shigo gidan, be tarar dasu a falon ba kamar yanda suka saba zama.


part din salma ya fara shiga, a kwance ya sameta tana chatting, tun randa ya bata wayar tayi dawlooding whatsapp da facebook.


ba wasu mutane bane a contact dinta daga numbern surukanta sena kannen shi sannan nashi.


wani group ta shiga a whatsap .


"UMMU AFFAN NOVELS"


wanda hafsat kanwar shi tayi adding dinta a ciki.


gaskiya ana turo  littafai masu dadi da ma'ana.


yanzu ma wani littafi take karanta KAINUWA (dashen Allah) na ayusha littafin yayi mata dadi sosai.


sallama yayi ya shigo falon, ajiye wayar tayi ta mike ka karbi jakar hannu shi, tana mishi barka da dawowa.


waje ya nema ya zauna,yana cewa


"wash!gaskia na gaji da yawa, hada min ruwan wanka nayi, Ko gajiyan zai ragu.


kusa dashi ta zauna kamar zata shige jikinsa tace "wannan ai aikin aunty humaira ne yau"


jawota yayi jikinsa yana shakar daddad'an kamshinta, se da ya gaji dan kansa sannan ya saketa ya dauki briefcase dinsa ya fita ya nufi part din humaira.


kuyi hakuri da wannan wallahi se da nayi ya goge. 



🌳🌳UMMU AFFAN🌳🌳

[05/02, 02:33] Halimatu Sadiya Affa Fbk: 🌳🌳🌳🌳🌳

      ZAB'IN MAHAIFINA

        🌳🌳🌳🌳🌳


Written by SADIYA ALHASSAN (Ummu Affan)


    🌐HAJOW 📝🌐


🌐👩‍👧‍👧👩‍👧‍👧👩‍👧‍👧HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS ✍🏾✍🏾✍🏾🌐


Dedicated to PRINCESS ESHAT AYSM

AYSHA BICHIKI


Page 27


Masu cewa a kara yawae post ku kara hakuri na kusa gama littafin ma gaba daya insha Allahu.



Se da yayi wanka kafin ya fito domintcin abinci, tare suka fito da humaira. yace taje ta kira salma suci abinci..


dukkan su suna zaune akan dining, kowa ya zuba abinda yake so ya faraci amma banda salma.


dubanta yayi yace, yaya bakya cin abincin?


cikin shagwaba tace


"cikina ne yake ciwo"


A rude yace amma kinsha magani?


gyada mishi kai tayi kafin ta mike tana cewa "bari naje na kwanta seda safenku"


cikin farin ciki humaira ta amsa, dan a tunaninta maganin ne ya fara aiki.


ita kuma salma ta fadi hakanne saboda bata son taci abincin,dan bata san me aka sake sawa a ciki ba.


cikin dare abdul ya kasa bacci se juyi yakeyi, salma kawai yake son gani a lokacin.


kallon yakai kan humaira datake kwance tana baccinta harda minshari.


A hankali ya mike ya fita daga dakin ya nufi part din salma.


yaci sa'a kuma kofar a bude take,ta manta bata rufe ba.


A zaune ya sameta akan sallaya tana karatun al-qurani. kusa da ita yaje ya zauna se da takai aya kafin ta dakata.


"ya jikin naki?"


ya fada fuskar sa dauke da damuwa.


murmushi tayi masa tace "jiki yayi sauki Alhmdlillh"


"kin tabbata?" ya tambaya


gyada kanta tayi


"to shikenan daman zuwa nayi na duba jikin naki"


to nagode! ta fada sannan tace "ina fatan kayi nafilfilinka?"



dan murmusawa yayi yace "yanzu dai zanyi idan nakoma daki"


mikewa yayi, kissing dinta yayi a goshi kafin yabar dakin.


binshi tayi da kallo tana me jin dadi aranta, na irin kulawar dayake mata.


Da safe bayan yayi wanka ya shirya wajen salma yazo ya karya, kafin ya wuce office.



karfe goma lina ta shigo gidan, salma ta gani zaune a falon tana kallo.


ko kallonta batayi ba ta nufi part din humaira. 


tab'e baki salma tayi tace "arniyan banza kawai, in banda kafirci tayaya mutum zai shigowa mutane gida ba sallama? kamar wani gidan ubansa"


juyowa lina tayi ta kalli salma kamar zatayi magana sekuma ta fasa ta shige ciki.


tsaki salma taja tace dakinyi magana ai wallahi da bakinki yayi jini. nace lallai salma da karfin hali kike.



 tana shiga ta samu humaira kwance tana bacci da alama ko sallar asuba batayi ba.


kan gadon tahau ta fara shafata kamar ta samu mage,


cikin bacci humaira taji mutum a jikinta, bude idonta tayi ta sauke su akan lina.


ihu ta saka ta rungumeta cike da farin cikin ganinta.


"shegia yaushe a gari?" 


cigaba da shafata lina tayi tana lumshe ido kafin tace


"jiya cikin dare muka shigo, nayi kewarki ne shiyasa kika ganni yanzu"


biye mata humaira tayi suka fada shashancin su (Allah ya dada karemu ga fadawa halaka ameen)


A dai-dai lokacin kuma A.A ya shigo gidan, bakowa a falon salma ta shiga dauko wayarta.


ya dawo daukar wasu takardu daya manta su a dakin humaira, direct bedroom dinta ya wuce.


Abinda yaganine yayi mugun daga masa hankali, wanda yasa ganinsa ya dauke na d'an lokaci.


"innalillahi wa'inna ilaihiraji'un kawai  yake maimaitawa"


sukam basusan  da zaman mutum a wajen ba,bidirin su kawai sukeyi dan su riga da sunyi nisa.


juyawa yayi, ya pitadaga dakin ya koma falo ya zauna, yana me dafe kansa da yake sara masa kamar ze rabe gida 2.


salma da tafito daga dakinta se ganin mutum tayi a zaune.


Mamaki ne ya kamata ganin be dade da fita ba, to me ya dawo dashi?


Zama tayi kusa dashi ta dafa kafadarsa


"Abdul lapia kuwa naga ka dawo yanzu?"


dago da idon shi yayi wanda suka canja kala ya kalleta.


cikin firgici ta janye hannunta, ganin hawaye nabin kumatun sa.


A rude tashiga share masa hawayen tana tambayan abinda yake damunsa.


kasa yi mata magana yayi se kawai ya mike ya nufi dakinta, tashi tayi tabi bayanshi.


Akwance a kwance ta same shi akan kujera, zama tayi ta dauki kanshi ta daura akan cinyarta ta fara bashi baki.


"kayi hakuri komai yayi zafi maganin shi Allah, koda wanine ya bata maka rai  dont get angry please calm dawn"


"how can i come dawn?"


kinsan abinda nagani kuma? kinsan girman zunubin da nagani ana aikatawa a cikin gidana?


cikin rashin fahimta salma ta ce


"bangane me kake nufi ba"


tashi yayi yace "ki jirani ina zuwa yanzu"


Fita yayi ya nufi part din humaira, tun kafin ya shiga yaji suna wasu maganganun daya saka shi tsayawa.


"Amma humy kin tabbatar kin zuba mata maganin nan a cikin abinci?"


tabbas na saka mata kuma nasan zata ci, dan jiya da daddare tace cikinta yana mata ciwo.


"to nidai humy yarinyar nan garau naganta dazu da zan shigo, ba wani alamar rashin lafia a tare da ita, dan har magana taso ta fada min ban kulata ba."


shiru humaira tayi tana nazari, can ta tabe baki tace 


" koda bata ci ba to yau zan zuba musu a cikin abinci suci su mutu tare"


 dan shima nagaji da zama dashi, gwanda ya mutu naci dukiyar,tuna yanzu naga duk asirin da nayi masa ya karye.


kullum se yaje ya gaida iyayensa, kuma be damu dani ba kwata-kwata,


yanzu kamar ma ya tsane ni a dole yake zaune dani.


bugo kofar da akayi ne yasata tsaida maganarta


kallon su yakeyi cikin tsana da kuma kyama yace


"tabbas humaira bakiyi k'arya ba natsane ki, tsanar da ban taba yima wani mutum ba a duniya,


kin cutar dani humaira, ashe daman 'yan uwanki mata kike bi shiyasa bakya bani hakkina?


Ashe abinda kikeyi kenan? wannan be isheki ba seda kika rabani da iyayena, daga karshe kuma kizo kina neman rayuwata?


Nagode ma Allah dayasa yau naji👂🏻kuma nagani da idanuna👀


saboda haka ina son ki tattara duk wani kayan da kika san nakine kibar min gidana


"na sakeki saki 2"


kuma insha Allahu se kinga karshen ki.


ya juya ya fita ya barsu a wajen cikin tashin hankali.




🌳🌳UMMU AFFAN🌳🌳


🌳🌳🌳🌳🌳

      ZAB'IN MAHAIFINA

        🌳🌳🌳🌳🌳


Written by SADIYA ALHASSAN (Ummu Affan)


    🌐HAJOW 📝🌐


🌐👩‍👧‍👧👩‍👧‍👧👩‍👧‍👧HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS ✍🏾✍🏾✍🏾🌐


Dedicated to PRINCESS ESHAT AYSM

AYSHA BICHIKI


Page 28



Yana fita motar shi ya shiga ya bar gidan,ya nufi gidan iyayenshi.  A zaune a falo ya tarar da mahaifiyar sa, zuwa yayi ya zauna a kasa, kusa da kafafunta ya daura kanshi a jikinta ya fashe da kuka.


Cikin hanzari ta dago kanshi tana tambayar shi, abinda yake faruwa. dan tasan duk abinda zaisa Abdul ya zubda hawaye ba k'arami bane.


dago kanshi yaye ya share hawayen shi kafin ya zayyane mata duk abinda ya faru.


tausayin ya bata ganin yanda yake kuka har fuskar shi tayi ja abinka da farin mutud.


Rarra shinsa ta shiga yi, tana nuna masa godia ya kamata yayi wa ubangiji daya nuna masa komai a zahiri.


A gidan ya zauna har dare seda yayi sallar isha'i kafin ya nufo gidan sa.


A can kuma salma hankalinta ya kasa kwanciya, ta kira numbers dinshi  yafi a kirga amma ana cemata wayar akashe take.


main falo ta fito ta zauna ta buga tagumi, tana nan a zaune taga ana fito da kayayyakin humaira, bata kawo komai a ranta ba dan ita a zatonta koya canja mata gidane (ada kenan)


Humaira ce da lina suka fito, suka zo suka tsaya a gabanta. humaira ta kalli salma tace


"kar kiga kinyi nasaran rabani da Abdul ki dauka na barki kenan, kisani koda ban dawo gidannan ba to wallahi kema baki isa ki zauna a cikinsa ba"


"bake kadai ba, duk wata 'ya mace🙎🏻 Abdul be isa ya kwanta da ita ba"



se alokacin salma ta gane abinda ke tafiya 


kallon humaira tayi sama da kasa  tace


"kina nufin abinda ya gagare ki yi kina cikin gidan🏡  shine kike zaton zaki iya idan kin fita?"


to muzuba, kije shedan ya baki sa'a dama ke danginsa ce (shedan din😳)


jan hannun humaira lina tayi suka fita,dan a yanzu ba lokacin cacar baki bane,kar me gidan ya dawo ya tarar dasu a cikin gidan, basusan me zai musu ba kuma.



karfe 8:30pm  ya shigo gidan a falonta wna tarar da ita, tana ganin shi ta mike da sauri taje ta rungume shi.


tana kukan shagwaba, ruko ta yayi suka zauna a kan kujera, yace 


"meya faru?"


kwanciya tayi ajikin sa cikin shagwaba


"bakai bane ka kashe wayarka nayita kiranka yak'i tafiya, kasa hankalina ya tashi na zata wani abune ya faru"


I am sorry kinji? wayar ne na barta a cikin mota, inaga kuma ba caji ne shiyasa yaki shiga"


"to muje kaci abinci, nasan kunajin yunwa"


girgiza kai yayi yace,naci abinci a gidan hajiya se dai wanka.


mikewa tayi taje ta hada masa ruwan wankan ya shiga yaje yayi.


bayan sun gama duk abinda zasu yi,


suna kwance, kanta yana bisa kirjin sa ta fara magana


"dan Allah meya faru dakai dazu?"


 kuma sannan naga aunty humaira tana kwashe kaya dazu,harta fada min wasu maganganu wanda ban gane me take nufi ba.


"me tace miki?"


ya tambaya, fada masa tayi, sannan ta bashi labarin maganin data sa mata a cikin abinci. tace 


"ni fa ina jin tsoron kar taje tayi mana wani abun"


shiru yayi nadan wani lokaci kafin yace "karki damu, gobe da safe idan Allah ya kaimu zansa ayi saukar Qur'ani, ba abinda zata iya mana da yardan ubangiji"


ba kadan ba salma ta firgita da abinda akace humaira tayi, duk da tasan zata iya aikata makaman cinsa, amma bata zata zaikai haka ba.


                      Haka ta daure taci gaba da kwantar masa da hankali har bacci ya dauke su.


            。。。。。


Inna saude tana zaune a tsakar gida tana tankaden garin da zatayi tuwo dashi.


sallama taji anayi a kofar gida, maya finta ta dauko ta nufi kofar gidan dan ganin meyin sallaman.


wani mutum ta gani, bayan sun gaisa yake fada mata aiko shi akayi ya kawo kaya, yanzu za'a shigo dashi.


komawa inna tayi cikin gidan tana tunanin wani irin kaya ne haka?


gani tayi ana shigotda buhunhunan shinkafa,wake,doya,dankali,semo, kwalin taliya,indomie,cous-cous, jarkan mangyada,manja da duk wani nau'i na abinci harda su kwandon kayan miya.


karasawa tayi kusa da mutumin bakinta yana rawa tace


"anya malam bakuyi batan kai ba kuma?"


 A Gaskiya mama bamuyi batan kai ba,nan gidan yayi mana kwatance.


"ko ba nan bane gidan su salma?"


"ba shakka nan ne gidan su salma"


to waye ya aiko ku?


Alh. A.A me dala


"shi Abdul dinne ya aiko ku?" inna ta tambaya


eh shine ya turo mu mu kawo.


to bari na kawo muku tukuici. inna tace tana shirin shiga daki.


dakatar da ita yayi

"A'a kibar shi, danya riga da ya sallame mu, kuma yace kar mu karbi komai a wajen ku"


godia sosai inna tayi musu,tace shima suyi masa godia.


komawa tayi ta zauna tana bin kayan da suka mamaye tsakar gidan da kallo, dan bata san ina zata ajiye su ba.


tana zaune mallam Amadi ya shigo, shima kayan yabi da kallo kafin ya maida kallon sa inna saude yace


"saude wannan kayanfa?"


fuska ba yabo ba fallasa tace "surukin kane ya kawo maka"


kallonta kawai yakeyi ya rasa me zece yana tsoron ya furta wani magana tashi tayi zafi.


zama yayi a kusa da ita yaci gaba da bata hakuri kamar yanda ya saba.


"mallam nifa komai ya wuce a wajena, fatana kamai Allah ya zaunar da salma a gidanta lafia"


murmushi yayi, ya bata labarin abinda ya faru a gidan salma yace " dazu ina kasuwa mahaifinsa yazo yana fada min, yayi godia sosai yace salma alkhairi ce a gare su, dan a sanadinta komai ya dai-daita.



Farin cikine ya bayyana akan fuskar inna saude,


"Alhmamdulillahi" kawai take ta maimaitawa.


kallon ta malam amadi yayi cikin tsokana yace "yanzu se a dena fushi dani  tunda komai ya wuce"



tashi tayi ta nufi kitchen cike da jin kunyar abinda ta dinga yi mishi.


           。。。。。



Shakuwa ce sosai ta shiga tsakanin salma da Abdul, kulawa suke bawa junan su fiye da zaton mutum.


 burin kowannen su shine ya farantawa dan uwan sa rai, ko kadan basa son yin nesa da juna.


A yanzu A.A baya kaiwa dare a office karfe 4:00pm yake dawowa gida.


ya saka anayi musu saukar Qur'ani a masallatai da niyyar Allah ya kare su daga sharrin me sharri.


                    yau ne salma ta shirya domin zuwa gaishe da surukanta, peppe chicken tayi da cake and dunnut domin takai musu.


A cikin mota yake tsokanar ta wai bata bashi nashi ba, bata ko kulashi ba har suka karasa gidan.


cikin farin ciki hajia halimat ta tarbesu, se nan-nan takeyi da ita ta rasa inda zata saka ta.


haka aka cika mata gabanta da kayan ciye-ciye, kayan da suka zo dashi ya dauko, cikin jin dadin kyautar hajia halimat ta karba tana sa mata albarka.


hanun sa yakai dan ya bude food flask din, bige hannun sa tayi tace 


"karka yadda ka dauka min ai bama kai aka kawo ba"


cikin shagwaba kamar wani karamin yaro yace momy to ni bazan ci ba kenan?


"eh baza kaci ba wannan nawa ne, idan kana son ci ne se ka tashi kaje kasa masu aiki suyi maka"


Murmushi salma takeyi dan ba kadan ba suke burgeta, yanda taga suna wasa darlya a tsanin su.


ta kudurta a ranta idan har ta haifi 'ya'yanta  zata janyo su a jiki ta yanda zasu dinga fada mata matsalolin su.


yini sukayi musu da zasu tafi kayan kwalliya hajia halimat ta hada mata,mahaifin sa kuma ya bata kyautar kudi.


A kan hanya A.A ya tsaya ya saya musu gasheshshiyar kaza a bauchi club, dan yau ya shirya angwancewa🙈


kuyi hakuri da rashin ganin posting dina jiya wayata ba cajine.




Post a Comment

0 Comments