TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Zabin mahaifina page 11-15

 🌳🌳UMMU AFFAN🌳🌳

[29/12/2017, 16:39] Halimatu Sadiya Affa Fbk: 🌳🌳🌳🌳🌳

      *ZAB'IN MAHAIFINA*

        🌳🌳🌳🌳🌳



Writen by *SADIYA ALHASSAN(ummu Affan)*



Dedicated to *PRINCESS ESHAT AYSM*

_AYSHA BICHIKI_





Page 11


A tsakar gida ta samu mahaifinta yana jiran dawowarta. Sannu baba ta fada tana kokarin wuce shi ta shige daki.


ke zonan ya kirata dawowa tayi ta tsuguna a gefensa. Ya kukayi dashi?? ina fatan baki masa rashin kunya ba?


Sunkuyar da kanta tayi cikin sanyin murya tayi mishi bayanin yanda sukayi,sannan ta daura da cewa baba ni inaga be kamata ace an kaini gidansa ba komaiba dan zai iya zamamin abin gori watarana.


Kinci kaniyar ki wani irin gori? to bari kiji koda ma beyi wannan maganar ba ni bani da kudin da zan saya miki kayan daki. dan haka ko cokali bazan saya va, kuma wallahi daga yau na sake jin kin fada masa maganar data bata masa rai zaki gamu dani kinji na gaya miki.

Tashi ki ban waje ya daka mata tsawa shashan yarinya mutum yana nema mana sauki  kina son ki mana bakin ciki.


Cike da sanyin jiki salma ta tashi ta shige daki. inna ta gani zaune akan sallaya ta idar da sallan isha'i da alama ta gama jin maganganun da sukayi da mahaifinta.


sallaya ta shimfida itama tayi sallah  bayan ta idar ne take sake yima inna bayanin yanda sukayi da A.A


inna tace salma kiyi hakuri tunda yace baya bukatar a kaiki da komai to kibar maganar a haka tunda kinsan mahaifinki bazai saya ba.


Akwai kudin da nake tarawa saboda zuwan irin wannan ranar ko vaxa a miki komaiba zan hada kudin ko kayan kitchen a saya miki da gara komai kankantar sa saboda gudun gorin kishiya.

Rungumeta salma tayi cike da jin dadi nagode inna ALLAh ya bar min ke.🙏🙏🙏. ai duk avinda nayi miki nayima kainane salma tunda ke kadai  ALLAh ya bani.


yanzu ki tashi kije ki kwanta, saketa tayi taje ta kwanta  inna se da safe, to salma kiyi addu'a kafin ki kwanta. to inna ta amsa sannan tayi addu'a ta shafa ta gyara kwanciyarta.

ASUBA TA GARI



🌳🌳UMMU AFFAN🌳🌳

[06/01, 14:59] Halimatu Sadiya Affa Fbk: 🌳🌳🌳🌳🌳

      *ZAB'IN MAHAIFINA*

        🌳🌳🌳🌳🌳



Writen by *SADIYA ALHASSAN(ummu Affan)*



Dedicated to *PRINCESS ESHAT AYSM*

_AYSHA BICHIKI_





Page 12


Kuyi hakuri na jina shiru da kukayi kwana 2 hakan ta farune dalilin abubuwa da suka yimin yawa amma insha ALLAhu zaku dinga jina yanzu akan lokaci.


masoya littafin ZABIN MAHAIFINA nagode a bisa kaunar da kuke nuna ma litta fina. masu min magana ta whatsapp,facebook, da masu kiran waya kai harma da wanda basu samu damar min magana va duk ina godiya a gareku.



Washe gari da safe bayan sun gama karin kumallo. Mallam Amadi ya wuce kasuwa, salma ta tattara kwanuka ta fara wanke-wanke, sallama akayi aka shigo, wata matace  wanda daka ganta kasan kanwar mallam Amadi ce saboda kamar da sukeyi.


Da hanzari salma ta mike, sannu da zuwa aunty hadiza ta fada fuskarta dauke da murmushi. Cikin fara'a matar ta amsa mata, yawwa sannu salma aiki akeyi ne? eh aunty. Ina innar taki? tana cikin daki salma ta amsa mata.


Sallama aunty hadiza tayi inna ta amsa mata, sannan ta shiga dakin, A'a hadiza ne yau a gidan namu? wallahi ni ce yaya, da yake haka take kiranta dashi kasancewarta matar yayanta.


ta nemi waje ta zauna, gaisawa sukayi, sannan inna tace hadiza kwana 2 shiru kamar bakyanan. wallahi yaya inanan  kawai fitanne se a hankali kafita kabar yara su kadai suyita maka barna. Yanzu ma yaya Ahmad ne  ya aika nazo. Ina fatan dai lafiya?


Hmm inna tayi ajiyar zuciya,sannan tace Hadiza ina fa lafiya, mallam ya dage wai aure zaima salma,harma ya za6a mata miji.


Wani irin aure kuma yaya? nawa salma take da za'a dage se an mata aure? yanzu pa zamani ya canja, yarinya se takai 25years  to above  ba'ayi mata aure ba.


Gaskiya yaya Ahmad be kyauta ba. Bari ya dawo ni zanyi masa magana, A'a hadiza ki rufa min asiri karkiyi wa mallam maganar nan dan cewa zeyi nakai karar sa wajenki.


Kin dai san halinsa. to shikenan bazan yi masa maganar ba ALLAh yasa hakan shine alkhairi Amin inna ta amsa mata. sannan suka ci gaba da tattaunawa game da yanda bikin zai kasance.


Salma ce ta shigo ta gaishe da AUNTY hadiza. Amsawa tayi tace salma kiyi hakuri komai na rayuwa mukaddari ne, haka taki jarabawan take badon ALLAh baya sonki bane yasa yayi miki haka A'a yayi ne domin ya gwada imanin ki. kiyi kokari ki cinye jarabawan ki kinji 'yata?


Gyada kai kawai salma tayi dan idan tace zatayi  magana zata iya fashewa da kuka. tashi kije aunty hadiza tace mata, mikewa tayi ta fita,ta fara shirye-shiryen daura abincin rana.


🌳🌳UMMU AFFAN🌳🌳

[07/01, 17:53] Halimatu Sadiya Affa Fbk: 🌳🌳🌳🌳🌳

      *ZAB'IN MAHAIFINA*

        🌳🌳🌳🌳🌳



Writen by *SADIYA ALHASSAN(ummu Affan)*



Dedicated to *PRINCESS ESHAT AYSM*

_AYSHA BICHIKI_





Page 13


Da yamma bayan mallam Amadi ya dawo daga kasuwa, inna ta kawo masa abincinsa yaci sannan ta kira masa Aunty hadiza. gaisawa sukayi suka dan taba hiransu xa 'yan uwan taka.


Mallam Amadine ya fara mata bayani akan auren salma,bata ce komai ba se sanya alkhairi da tayima auren. yaji dadi sosai da yaga bata daga hankalinta ba.


kamar yanda inna tayi,hakanne yasa ya daura da cewa dazu ALH. Abdul-Razak yazo kasuwa ya same ni, akan suna so a sa musu auren da wuri, dan haka na yanke musu nan da wata 1. se ku fara shirye-shirye.


Ita dai Aunty hadiza bata ce komai ba tunda inna ta hanata magana amma abin ya bata mamaki ace aure wata daya, seka ce ana neman kai da yarinya koda yake aure lokacine idan lokacin yazo dole se anyi shi.


Tashi tayi tayi musu sallama akan zata dawo washe gari su tsara yanda bikin zai kasance.


          。  。 。 。



Lokaci yanata karatowa biki ya rage saura , salma tana shan gyara a wajen Aunty hadiza. Magunguna masu amfani take bata ba wanda zai mata illa a jiki ba.


Gyara kam salma tasha shi, dan ita kanta tana jin canji ajikinta sosai. Dilka da halawa kullum se anzo anyi mata shi, bata fita ko ina, makarantar hadda ma ta dena zuwa.


Tayi kyau tayi jajir abinka da farar mace duk inda tayi kamshine yake tashi, indai ta zauna a waje kamshinta yana dadewa kafin yabar wajen.


Tun ranar da Abdul yazo be sake zuwa ba, har yau daya rage saura 2weeks biki. An kawo lefe na gani a fada. Akwati 12. kayan cikima kawai abin kallo ne. kai komai hassadan mutum idan yaga wannan lefen dole da rude.


Aunty hadiza ne ta zaba mata wanda zatayi fitar biki dashi aka kai dinki.


inna ta fidda kudin da take tarawa saboda auren salma. an siyo mata kayan kitchen da gara. anyi cincin din biki da dubulan,tawaita,alkaki,tsatstsafa,nakiya. An siya mata duk avinda akasan zata bukata.komai dai sunyi dai-dai karfinsu.



🌳🌳UMMU AFFAN🌳🌳

[11/01, 02:42] Halimatu Sadiya Affa Fbk: 🌳🌳🌳🌳🌳

      *ZAB'IN MAHAIFINA*

        🌳🌳🌳🌳🌳



Writen by *SADIYA ALHASSAN(ummu Affan)*



Dedicated to *PRINCESS ESHAT AYSM*

_AYSHA BICHIKI_





Page 14


Yau ya rage saura  sati 1  biki gida ya fara cika da 'yan uwa na kusa da na nesa.


sallama akayi aka ce wai ana sallama da salma. Aunty hadiza ce ta cema yaron kace tana zuwa, da yake yanzu kusan kullum se tazo saboda hidiman biki.


salma kije ana sallama dake a waje aunty hadiza tace, tashi salma tayi ta dauki hijabinta tayi hanyar waje,kiranta aunty hadiza tayi, kina nufin haka zaki fita wai? ko kwalliya bakiyi ba bare ki fesa turare? maza jeki  shafa ko hoda ce ki goga jan baki ki fesa turare.


tura baki salma tayi sannan ta koma daki ta danyi make up  ta fesa turare ta fito. Har lokacin aunty hadiza tana tsaye a wajen data barta, to ko kefa ta fada tana murmushi da zaki fita kamar ba amarya ba,zakije wajen miji fuska farau-farau ba kwalliya.


ko kulata salma batayi ba ta fita ta barta tana ci gaba da maganar ta.


A jingine a jikin mota ta hango su, wannan karon su 2 suka zo, shida wani saurayi kamar shi black beauty dagani zeyi saukin kai dan fuskar shi cike take da murmushi. ba kamar A A ba daya hada rai kamar an aiko masa da sakon mutuwa.


Tun da ta fito yake kallonta yana kare mata kallo, ba lefi tayi mishi kyau se dai fa shi kowacce mace bata burge shi inba matarsa humaira ba.



Sallamarta ne ya dawo dashi daga tunanin daya fada. kauda kai yayi se abokin sane ya amsa sallamar. Gaisawa sukayi sannan yace hajiya salma nasan baki sanni ba, sunana SALEEM nine babban abokin Abdul.


Munzo ne domin muji irin shirye-shiryen da kuke yi. seki fada mana event nawa zakiyi da yawan kudin dazai isheki se mu baki.  cikin sanyin muryanta ta ce ba abinda zanyi kuma bana bukatar komai.tokai kaji abokina, ta yaya za'ace amarya bata bukatar komai? ai bazai yuwuba.


ko kallon shi A A beyi ba balle ya nuna yaji abinda yake fada. dan tsaki saleem yaja sannan ya maida kallon shi gun salma yace to mu ta bangaren mu akwai dinner da muka shirya bayan ankai amarya  karfe 8:30pm. Ina fatan ba matsala?


Gyada mishi kai kawai tayi duk da a ranta bata so hakan ba, bude mota saleem yayi ya fito da wani leda tare da emvelop ga wannan kayan shi  zaki sa a wajen dinner. wannan kuma ki rike a wajenki saboda hidiman biki duk da kince bazakiyi komai ba 500k ne ba yawa.


dan rusunawa salma tayi ta karba sannan tayi masa godiya. Murmushi  saleem yayi mata dan ba karamin burgeshi tayi ba, bakomai amaryar mu ya fada sannan ya dubi A A ko akwai wani abin da ban fada ba? kauda kansa yayi cike da jinkai yace idan ka gama surutun zamu iya tafiya. ya fada tare da shigewa mota


Murmushi saleem yayi danshi ya saba da halin Abdul,mutum ne wanda baya son hayaniya se kayi magana goma be amsa maka daya ba.  shiyasa baya damuwa da duk abinda zeyi masa saboda yasan halinsa in and out. Tun suna yara suke tare kasan cewar iyayen su aminan juna ne. ko sunyi fada a lokacin suke shiryawa


To amaryar mu, mu zamu tafi se munzo daukan ki nan da sati. godiya salma tayi masa tare da juyawa ta shiga gida suma sukaja motar su suka tafi.


salma tana shiga ta mikawa aunty hadiza ledan da kuma emvelop din, bude ledan tayi taga kayane a ciki. wani hadadden material ne purple colour da ratsin fari anyi masa dinkin doguwar riga. se farin takalmi hill da farin poss, se head purple da kuma sarka da dan kunne fashion purple da fari. 


wannan kayan fa? aunty hadiza ta tambaya, bayani salma tayi mata.  aikuwa kudinnan se dai a bude miki account a saka miki. bari na kaima innarki ta ajiye zuwa a gama biki se akai banki.


   WAI WAYE  A A ne??? 

ku biyo ni a next page domin muji cikekken tarihin A A me dala



🌳🌳UMMU AFFAN🌳🌳

[14/01, 11:33] Halimatu Sadiya Affa Fbk: 🌳🌳🌳🌳🌳

      *ZAB'IN MAHAIFINA*

        🌳🌳🌳🌳🌳



Writen by *SADIYA ALHASSAN(ummu Affan)*



Dedicated to *PRINCESS ESHAT AYSM*

_AYSHA BICHIKI_





Page 15


Ina jin dadin yawan comment dinku da nake gani, nagode sosai ALLah ya bar kauna.


WANENE AA ME DALA??


ABDUL-AZEEZ ABDUL-RAZAK ME DALA shine cikekken sunanshi, mahaifinsa Alh. Abdul-razak me kudine na gaske yana da kamfanin saida motoci har guda uku bayan haka kuma dan kasuwa ne sosai. Abdul saurayine meji da kansa ga kyau ga nera uwa uba ilimin boko da arabic.


yayi karatunsa har zuwa matakin masters akan business. Abdul mutum ne miskilin gaske, danshi mutum ne da baya son hayaniya. Idan kaga yanda mata suke binshi abin zai baka mamaki,amma ko kallo basu isheshi ba.


Shikadai ne da namiji agun iyayensa,shine first born sai kannen shi mata guda uku Hafsat,Amina da ummul khairi. Sun samu tarbiyya a gurin iyayen su, kasancewar su masu arziki hakan besa sun sangarta su ba.


Abdul sun hadu da matar sa humaira ne a wani super market,sunje shopping shida abokinsa Saleem. tunda ta ganshi ta rikice akansa amma shi ko kallo bata ishe shi ba. hakanne yasa tabi duk hanyar da tasan zata jawo hankalin shi gareta kasan cewarta mace me budadden ido  dan gidansu 'yan boko ne ita kadaice 'ya awajen iyayenta. ko kadan iyayenta ba ruwansu da irin rayuwar da take yi dan ko zata kwana a wajene ba wanda zai tambayeta dalili. wannan ne ya bata damar sheke ayanta yanda take so. dan gidan malamai ba wanda bata sani ba, idan dai taga kayi mata yanzu zata kai sunanka gun malaminta a mallake mata zuciyar ka. Hakanne ta kasance lokacin da taga A A.


tunda taga alamun dan jin kaine taje ta sanar da malaminta akayi mata aiki a kansa. Aikuwa aiki yayi kyau dan a hakane ta samu har ta aure shi. iyayensa basuso auren ba kasancewar ta me karancin tarbiyya, amma ba yanda suka iya tunda ya dage akan yana sonta a haka, se dai kawai suka ci gaba dayi masa addu'a.


Bayan anyi auren ne ta fara fiddo da asalin halayyarta, ko sau 1 bata taba daga waya ta kira iyayen mijinta ba domin ta gaishe su,ballantana ta taka da kafarta taje har gida.


koda kannensa sunzo bata bari su ganshi,se dai tace musu bayanan. daga karshe ma zuwa tayi ta samu me gadi akan ko sunzo kar ya yadda ya barsu su shigo gidan, duk randa ya barsu to abakin aikinsa.


Abdul mutum ne me son iyayensa da 'yan uwansa, hakan ne tasa suka fara samun sabani da ita. Wata rana da yayi mata maganar ta shirya suje su gaida iyayensa aikuwa ta rufe ido tace ba inda zataje. ranar taga bacin ran da bata taba gani tare da shi ba dan ce mata yayi indai bata je ba to saidai ta tafi gidansu. Badan ranta yaso ba ta bishi suka tafi.


Ganin hakan da yayi mata yasa ta koma gun malaminta aka hana shi zuwa wajen iyayen shi, a cewarta tunda akansu ne yace taje gidansu to suma seta rabashi da su. Indai kaga yaje wajen su to se dai ya saci hanya ba tare da tasani ba


Wani zuwa da yayi ne mahaifiyar sa take yi masa maganar karin aure,tunda shekaransu 5 da matar sa amma bata taba koda batan wata ba. ce mata yayi baida matar da zai aura se dai su zaba mishi kasan cewar sa mutum ne me biyayya, abinda basu sani ba humaira bawai haihuwa ne batayi ba, ta samu ciki har sau 2 tana zubarwa dan tace bata shirya haihuwa yanzu ba.


Aikuwa yasha albarka a wajen iyayensa. hakanne yasa suka aura masa 'yar kanwar Alh. Abdul-razak. kwata-kwata auren be wuce 2 month ba ya rabu da ita.


Bayan ita seda suka aura masa mata har guda 3,duk yana rabuwa da su. ta karshen kamma da hauka tabar gidan. saboda taso ta basu wahala kasancewarta ma'abociyar karatun al-qur'ani me girma. hakanne yasa tace kawai a haukatar da ita bokan yace gaskiya shi bazai iya ba, se dai a bari lokacin da bata da tsarki, Wannan ne dalilin dayasa ta samu galaba akanta. Tun daga lokacin basu sake aura masa wata ba dan ko sunje ba'a basu.


To a wannan karonne aka dace da mahaifinsa yazo wajen mallam Amadi nema masa auren salma,shikuma ya amince, saboda son abin duniya yajefa rayuwar 'yarsa a halaka.


yanzu labarin zai fara kudai ku biyo ni domin jin abinda zai faru nan gaba




Post a Comment

0 Comments