TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Sanyi da zafi page 10-11

 💫 SANYI DA ZAFI 💫

✍🏻M SHAKUR


EPISODE 🔟

Cobweb tafara ciccirewa kafin tafara shara da vacum cleaner sannan tafara goge goge tundaga kan su desktop din, frames na bango,  admiring design da komi na office din kowaye maishi really shows love nashi ma simplicity and art, gyara ko’ina tayi har labule saida tai dusting sannan tabude first kofan data gani ga mamakinta saitaga bedroom ne ga lafiyayyen gado awajen ga closet gyara komi tayi sharp sharp tai moping har bayin dake dakin sannan tafito tabude dayan kofan taga nan ma bayi ne ta gyara kusan 1hr tabata sannan tagama komi tafito takoma station nasu, kafin akira waya anason tazo room 456 ta gyara ta wuce taje ta gyara haka dai tai aiki had 5 sannan ta tashi.


Changing room takoma ta chanza kayan aikinta ta maida atampanta na safe tasaka pink crocs dinta na safe tana murmushin tuna Mama data siyamata sanan ta goya jakan nata tafito tana tafiya ahankali receptionist dinsu dake wajen tana ganinta cikeda fara’a tamata waving hannu tace “bye beautiful Rashy” dan kallonta Rashida tayi hatta daga hannu zata mata waving itama saikuma tasauke hannun like a weirdo, tadan kyafta ido sau biyu kafin tace “thanks” tawuce da sauri tafita dayan receptionist din tace “when will you stop throwing kanki on Rashida? Ko Madam dinmu tasan yarinyar is a weirdo” dan murmushi tayi tace “is because she’s like that nake sonta, I don’t want normal people irinmu as friends inason irinsu Rashida as friends, the girl is lovely” tabe baki dayan tayi tace “nidai nawuce asha night duty lafiya see you in the morning”.



Tana fitowa waje ta tsaya saikuma ta juyo jakanta da sauri zuwa baya tana kallon jakanta taja zip tashiga budewa tana kokarin ciro wayanta….


Ahankali yasauko da kafanshi dake sanye dawani Bottega veneta coffee color takalmi mai tsinannen kyau daga cikin motan, kumbunan shi farare kal kal agyare kaman an musu fenti tsabagen sheki dasuke, kafin gentle yakarasa saukowa yafito daga motan, dogone sosai yana sanye dawani coffee color soft yard na yan Malaysia mai bala’in taushi anmai simple aiki a wuyan, idanunshi sanye da bakin glasses na Cartier, glasses din yasa baka ganin idanunshi sai pink lips nashi dayayi so pinkish gawani irin lafiyayen bakin saje dayabi fuskanshi zuwa gemunshi da gashin baki daya karama fuskan shi kyau sosai da kwarjini da haiba kaman wani balarabe, hannunshi na daure da agogon Cartier shima latest collection dinsu, his entire body speaks luxury, he looks squeaky clean kaman ka lashesa,

daidai taciro wayan tana kokarin manna earpiece a kunnenta dan Mama takeso takira kawai taji sahun gudu gudu sauri sauri dasauri tajuyo dan taga meke faruwa, daidai lokacin itama Mirabel data fito daga cikin hotel din tazaro ido tace “Oga yazo OMG” tai parking space dagudu itama same with sauran ma’aikatan dake waje, kallon inda sukayi Rashida tayi har tana dage but still bama ta iya hango wanda ake kira da Oga sabida yanda ma’aikatan suka zagayeshi cikeda farinciki sunamai sannu da zuwa, dauke kanta kawai tayi takarasa makala earpiece din tafara tafiya abinta tana dialing number Mama….


Shifa he hates too much attention, the way suka zagayeshi ana gaidashi kaman wani celebrity yazo sai abin yakara batamai rai dan har yanzu abinda Mom tamai da Haleema na batamai rai, the way suka wani fito suna gaidashi abin kular dashi ma yayi wucewa kawai yayi batare daya kula ko mutum daya cikinsu ba yana tafiya a kasaitacce Munir shine ya tsaya amsasu daidai takai gate zata fita taji wani iska ya kadata kamshi mai dadi gaske wanda bata taba jin irin shi aduniya ba yadaki hancinta da saida ta lumshe idanu sabida dadin kamshin daidai an budemai kofa shima ya tsaya sabida sanyin dayaji yakai 10secs ahaka kafin yadaga kafa yashiga cikin lobby su dan security sun budemai glass door din, ya shiga ciki yana bin ko’ina da kallo sai kawai yawuce wajen elevator manager tafito dasaurin ta daga office dinta tana murmushi tace “welcome Sir” Gyadamata kai yayi yadauke kai yadaga hannunshi yana kallon agogon hannunshi daidai kofan na rufewa 5th floor yawuce direct office nashi yaje hannu yasa a aljihunshi yaciro wayanshi kawai ya manna a kofan kofan yabude yashiga ciki an kunna AC wajen sanyi, tsayawa yayi chak yana kallon frame na artwork dake bango dudda manager ta turama Munir hotunansu ta email shikuma ya nunamai but yanzu daya gansu in reality sai sukamai mugun kyau. Daga kafanshi yayi yataka zuwa wajen yasa hannunshi yasauko dashi yana kallo sai kawai yayi murmushi for the first time today yaji abu yasashi farin ciki. Zama yayi akan kujera tareda lumshe idanu yadaura hannunshi aka yayi shiruu he don’t like the way Mom kesashi yin abubuwan dabayaso yayi, she made him king dudda bayaso, she made him marry dudda bayaso, yanzu kuma she’s telling him how to handle family shi, bude kofan office din akayi aka shigo hakan yasa yabude ido kadan Munir ne yamaida kofan yarufe yashigo yaja kujera ya zauna kai tsaye tace “waikai meke damunka eh”? Kallonshi Riyad yayi saikuma yayi shiru tareda fuzar da iska, tashi Munir yayi yasan bazai gayamai ba yawuce wajen kofan bathroom haryasa hannu a kofan yajuyo yakalleshi yace “Riyad I hate seeing the slightest damuwa akan fuskan ka, banda you’re my brother, you are  also my best friend, kowani yanayi kake ciki affects me, life can be colorful idan you let it be that to you, be the Man of your life karka bari kowa yagaya maka ga yanda zakayi, you are loved, jama’a harda wayanda basu sanka ba na yabonka, kana adalci asarautan dakake yi kadena bari anything na damunka kaji”? Dan kallonshi Riyad yayi for the second time yayi murmushi yace “okay” bude kofan bathroom din Munir yayi harzai shiga ahankali Riyad yace “thanks” kallonshi Munir yayi sai kawai yayi murmushi yawuce yashiga bayin maganan Munir yasa yaji sanyi aranshi he will take things easy on kanshi and everyday he will try and do wat makes him happy he will live his life, daga yanzu kullum saiya fita zai chanza schedule nashi daga 4:00 har dare ya warema kanshi da  safiya kuma fada, he will leave 2 separate life dinshi privately and peacefully, tashi yayi ahankali shima yawuto yabude kofan dakin yashiga bathroom yawuce direct yadauro alwala yafito abu yataka dayaji ya chaki kafanshi dasauri ya tsaya yadaga kafar ya kalli kasan carpet din yaga karamin dankunne ne baki ya shiga kafanshi dudda bai shiga sosai ba, ahankali yakai hannunshi yacire daga kafanshi yakalli earring din murya chan kasa yace “who dropped this here?” Yayi shiru yanabin dan kunnen da kallo daidai Munir yace “kana alwala ne koka fito? Muje mosque” dasauri ya zura dan kunnen a aljihunshi absentmindedly gudun kar wani yataka, yataho yabude kofan yadauki glasses nashi da waya Munir yace “ba nan kasa zamuje salla mudawo muyi aikin ba” wucewa yayi yace “I thought kaikace i should always be happy, zanje na buga golf yau, tunda Mom tasamin aikin sarki ban buga golf ba” murmushi Munir yayi sai kawai yabiyoshi suka wuce suka fita.

 💫 SANYI DA ZAFI 💫

  ✍🏻M SHAKUR


EPISODE 1️⃣1️⃣

 


Salla sukayi a mosque nan ma anata gaidashi still few ya amsa dazasu wuce yasa Munir ya basu bandir na kudi dake pocket nashi, sannan yawuce mota ya shiga mazaunin direba Munir yana zuwa yazaro ido yace “mehaka rabon dakai driving da kanka about 1year kai tunda kazama sarki” murmushi yayi yamikamai hannu ya karbi key baice komi ba yatada mota suka wuce wani private waje dayake buga golf chanza kaya sukayi ga ma’aikatan shi yafara buga golf din yanayi yana murmushi, sosai Munir yaji dadi ganin he’s very happy today kullum ganinshi zakayi so moody. Anan sukai Isha’i sai wajajen 11 na dare sannan yagama yatafi office nashi na wajen yayi wanka ya maida kayanshi yana kallon yanda wayanshi ke ringing yakalli screen yaga Haleema a rubuce kaman bazai dauki wayan ba saikuma ya dauka yakai kunnenshi yayi shiru daga ta dayan bangaren tace “ina kajene yau Mai Martaba? 11 nadare yanzu fa” lumshe idanu kadan yayi bayabo ba fallasa yace “yanzu zan fara dawowa, make tea for me before i come” yana maganan yacire wayan daga kunnenshi ya katse ya ijiye ya karasa saka boturan riganshi shima Munir yashigo yace “mutafi” wucewa sukayi wannan karan Munir yayi tukin har gida, ta private gate dinshi as usual suka shigo parking sukayi yafito yana tafiya a natse har flat nashi, he’s very hungry but tea yakeso dan is late, waya yadaga yayi dailing number Haleema tana dagawa kafin tai magana yace “ina tea”? Dasauri tace “bari natashi na daura tunda kadawo” jiyayi ranshi yabaci but baiso ranshi yayta baci sabida ita hakan yasa yace “kibarshi banso” ya katse wayan yajuya yafito daga flat nashi, shi kawai bai iyajin yunwa ba ne, wajen kofan dazai sadashi da cikin gida yayi yabude fadawa na ganinshi suka zube zasu faramai kirarin rai abace yace “kuje kuyi bacci na sallameku” sauke kansu duka sukayi kasa yawuce fuuu direct flat din Ammi yawuce yana addu’a Allah sa Munir daya shiga bai rufe kofa ba kai tsaye yabude kofan, babu kowa a falo sai TV dake aiki tashar CNN, dinning ya kalla ganin kuloli akai ga flask na shayi yasa yawuce wajen sadaf sadaf kaman barawo yashiga bude warmers din sinasir yagani dake tururi kaman yanzu akayi abunka da kula mai kyau da miyan taushe dayasha cow tail dudda ba abinci yaso yaci ba dan dare yayi sosai saiyaji abun yabiyamai rai zama yayi ahankali yadauki plate ya ijiye yasa sinasir guda 3 da Miya yasa nama dayawa yadauki spoon yafara ci ahankali he loves abincin Ammi har ranshi, tafiya yaji a stairs hakan yasa yadago kanshi dasauri ganin Ammi tana sanye da lullubi ga carbi a hannunta yasa yasauke kanshi kasa da sauri murya chan kasa yace “ina yini Ammi” batace kala ba cigaba da saukowa tayi daga stairs din shikuma yakasa ci gaba da cin abinci sai ahankali ya yunkura zai tashi strictly tace “ina zaka?” Kanshi akasa still yace “uhmm dama nagama ci zan tafi ne” “sit down” tafadi babu wasa a muryanta, baiyi musu ba zama yakoma yayi har dinning din tazo tsayuwa tayi kusada shi rabon dayaji Ammi tsaye kusadashi haka harya manta he can’t even remember when, hannu tasa ahankali tadauki flask da cup mai kyau ta tsiyayamai ruwan shayi tadauki spoon da bottle na honey ta digamai aciki ta tura agabanshi kafin ahankali tace “idan kanaso katafi finish abincin daka faraci, nobody waste abincina in this house” kanshi na kasa har lokacin yakasa dago kanshi ya kalleta, juyawa tayi tawuce takoma falo tazauna tadauki remote ta chanza channel din zuwa Aljazeera ta maida idanunta wajen, adan hankali ya wiago ya kalleta sannan yajuyo da kanshi yacigaba da cin abincin kadan kadan tass ya cinye ya kora da ruwan shayin saiyaji hankalinshi ya kwanta, yanada cin abinci shi but only yasamu abinda yakeso, tashi yayi ahankali yajuyo yadan kalleta hada ido sukayi da sauri ya sauke kanshi kasa cikeda ladabi yace “good night Ammi” “Allah tashemu lafiya Riyad” tana maganan yawuce da sauri yabude kofa yafice tareda maido kofan yarufe ahankali karyayi kara, ahankali ta sauke ijiyan zuciya sannan ta lumshe ido kaman irin she’s hurt ko akwai wani abu azuciyanta, kafin ta tashi tawuce inda yatashi zama tayi wajen ta dauki cup din dayasha tea ta kalla tai shiru kaman wacce ke tunanin wani abu sai chan tadaga flask din ta tsiyaya tea dazun nan ta dafa shayin tawuce taje tai wankan dare, itama bata iya bacci idan batasha shayi da daddare ba, daukan cup din tayi takai bakinta ta kurba sannan ta taso tadawo falo ta zauna tana shan shayin.






Yana shiga side nashi yaga Haleema azaune ga tray shayin tasa wasu arnayen kayan bacci da sauri ta taso tace “ina kaje nakawo maka shayin baka nan babu masu gadinka ka koresu ne”? Rigan jikinshi yahau cirewa yace “yes, kidau shayin kitafi dashi I don’t want” Shiru tayi tana kallonshi tana bin jikinshi da kallo wucewa bayi kawai yayi bayan ya rataye rigan a hanger dake dakin mai kyau ijiyan zuciya tasauke tace “wash Allah na mutum kaman shi yayi kanshi” wucewa tayi ta dauke tray takai falo ta ijiye sannan tadawo dakin tai kwanciyarta akan gadonshi tana jiranshi yafito, yadan jima a bathroom din sannan yafito daure da towel a waist daya a hannunshi yana tsane kai, kallo daya yamata yadauke kai yashiga shafe shafenshi yana fesa turare kafin yawuce walk in closet room nashi yasaka wani dark blue pajamas sannan yafito ko kallon inda take baiyiba iPad nashi yadauka yawuce ya zauna kan sofa ya makala EarPod yayi playing video ranan da akaso kasheshi wanda yarinyar nan ta ceceshi ke ciki, ya kalli video nan yafi sau dubu he is just looking for the girl number datasa a file nata baya shiga, yatura anje address datasa a file nata ba’a ganta ba, yaje da kanshi shima bai ganta ba ance babu wata kamanta ma a layin he’s just greatful yarinyar saved his life, video always give him peace he don’t even know why he don’t care ko sata take koma wacece ita he just wants to reward her yabata better job for saving his life, and huge money to startup business or anything datakeso, gama kallon yayi sai ya zare EarPod din ya rufe iPad din ya ijiye yadan kalli gadon hada ido yayi da Haleema ba yabo ba fallasa yace “wat”? Dan murmushi tayi tace “let’s try having Baby, nakosa naga ina dauke da cikinka na haifo maka magaji” dan yatsine fuska yayi da ita da Mom baisan mesa duk suka damu da cikiba kaman auren yayi 10yrs this is just a year, Allah ke bada haihuwa not him, kaman bazai tashiba saikuma yatashi ya kashe wuta yawuce yahau gadon ya kwanta tareda juya mata baya da sauri ta mirgino ta kankameshi ta baya kaman zata fashe da kuka tace “let’s make Baby kaji My love” shiru yayi shi baisan kodan baida feelings for her kawai an auramai itane koko shine baida lafiyane amman kwata kwata bayajin sha’awan Haleematu ko zata tsaya gabanshi tsirara, everything he’s doing yanayi ne sabida matarshi ce dole ya kyautata mata yakuma sauke hakkin ta daga kanshi, before ya ankara hawa jikinshi tayi tana kokarin mai kiss yadauke kanshi haryau bai taba hada bakinshi da nata ba, jefar da ita gefenshi, hannunshi yakai yaja wandon pajamas dinshi kasa dasauri tashiga daga riganta sama itama, ahankali yakai hannunshi kan boobs nata ya shiga squeezing nasu sannan yayi addu’a yayi sliding in, nishinta ke tashi kawai daga dakin kaman zata shide, dakin yayi tsit, if there’s one thing she kind of understood about him yanada son wasa da boobs, anytime zaiyi abu da ita sunashan squeezing a hannunshi saisa bayan aurensu boobs nata suka kara girma sosai dudda baya sha but ya iya wasu dasu abin namata mugun dadi almost hour and half yayi duk tagama ficewa hayyacinta sannan ya rirriketa tasan he’s cumming cus that’s only time din dayake rirriketa and just be in her body itakuma she uses that opportunity to cuddle him, alokacin zai fara nishi da karfi kaman zai fashe mata da kuka like a baby, kankameta yayi sosai kanshi nakan kirjinta yafara nishi da karfi he just wants to cum yahuta baida kawowa dawuri, idan yakawo once idan he’s going for 2nd round zai iyakai 4hrs bai kawowa, rirrikeshi Haleema tayi tana shafamai kai kalan nishin dayake mata a kunne da fuska na kara tafiya da imaninta yana hitting wajen da kyau chan yayi karaaaa mai sauti wanda haka yake yajuye mata komi ciki, yakai almost 2min ahaka baitashiba yagama tsiyayewa ciki kotayi cikin shima yahuta da jaraban Mom sannan yasauka daga jikinta tareda maida wandonshi yajuya mata baya yana sauke ijiyan zuciya, dasauri tabiyoshi ta hugging nashi ta side, ko 1min baiyi da gamawa ba sai bacci jikinta yamata dadi, yakai kusan 1hr a kwance sannan yajanye jikinshi yatashi yawuce bayi yasake wanka ya chanza kaya yafito sai kawai yawuce dayan sakin yaje ya kwanta awajen.


***

Wuraren 6 takai gida da kafa takoma tana shiga taga Mama tareda Uwargida Baba Liman, Baba Liman shi kadai ke mutunci dasu a unguwan, yana tursasa matanshi suzo su duba Mama once in a while hakkin makotaka, anytime yayi noma ko wasu yan kudade suka shigomai he always send something to Mama dudda Rashida bataso dan shima bukatan taimakon yake, but tana girmamashi kodan mutunci da suke da Mama da yanda Mama ta daukeshi itama. Uwargidan tana shigowa once in a while tazo gaida Mama dudda ko ruwa batasha aka bata kujera ma saita share da dankwalinta take zama akai kaman irin idan ta zauna ko ta taba wani abu nasu zata kamu da HIV itama, Rashida bata sonta sabida Mama ne ma take gaidata dan da wannan zuwa tana kyama tana kaffa kaffa gwara tayi zamanta agidansu ai babu wanda yace dole saitazo, tana ganinta ta kirne rai ganin ta shimfida dan kwalinta saman kan tabarman da aka bata a tsakar gida ta zauna kai tsaye bayan tai sallama ta wuce wajen Mama dake zaune kan dakalin bakin kofansu ta rungumeta tace “Mama nadawo” murmushi Mama tayi tace “sannu da zuwa ga Indo baki gaidataba” kallon Matan tayi dake kallonta tana washe baki, mugun kallon da Rashida tama matan yasa da sauri Indo tamike tsaye tana dauke dankwalinta tace “bari naje Maryam Allah Kara sauki” Mama tace “nagode Indo saida safe a gaida yara” takalli Rashida tace “waike mesa fitinanniya ce”? Tashi tayi tace “Mama tunda ba dole akamata tadinga zuwa gidanmu ba ai sai tadena wannan kyama kyaman bazan dauka ba” shiru Mama tayi ta buga tagumi tana kallonta hakanma saiyasa tayi dariya tace “Mama mehaka kikai tagumi kina kallona kaman kinga hoto”? Cikeda damuwa Mama tace “tunani nake wakika biyo da temper nan naki Rashida? Kap dangina babu mai fada masifa, fushi, taurin kai da kafiya irin naki, to maybe sai dangin mahaifinki dan bangama saninasu ba abinki da yan Sarauta sunada yawa” tamau Rashida ta daure fuska sai kawai ta tashi tace “Mama inaga harda kallan son da mutumin nan yaga kinmai saisa ya wulakantaki, baki magana baki kawoshi ba after how many years Mama you still remember mutanen da mutumin that hurt and destroyed life dinki” kallonta Mama tayi tace “babanki yamin kirki abaya dudda ya wulakantanin amman hakan bazaisa na manta kirkinshi ba” ayanda fuskan Rashida yayi da ace zata iya dukan Mama datayi akufule tace “Allah karya dauramin son wani haka Mama cus inaaa! Mama you have no idea yanda na tsani mutumin nan and duk randa na sami opportunity wlh I will hurt him sama da yanda yayi hurting naki, bari nagama makaranta nazama wani abu saizan ya wulakantamini uwa!” Mama zata kara magana Rashida ta tashi da sauri kawai tashige ciki Mama tai murmushi kawai tareda sauke ijiyan zuciya.

***




Around 7 na safe yadawo daga masallaci wanda haka yakeyi daman before yayi bacci yatashi 10 ya shirya yaje fada by 11. Bacci yakoma adakin daya kwana ya kwanta, harya fara bacci yaji hayaniya sama sama da alamun kuka, dan bude idanunshi kadan yayi trying yaji da gaske anan side yaji kuka, knocking kofar dakin dayake ciki akayi saikuma yaji muryan Mom afadace tace “open this door Riyad nasan kana jina” tashi yayi ahankali ya kunna wutan dakin yana mamakin meya faru, yadauki jallabiya ya zura dan dagashi sai short yayi wajen kofan ahankali yabude kofan Mami yagani ranta abace saikuma ya hango Haleema duke tsakiyan corridor tana kuka sosai kaman an mata mutu har yanzu rigan baccin jiya ne ajikinta, yadai daure yace “good morning Mom…” hannu Mom tadagamai ranta amasifan bace tace “hold greeting naka I don’t want it Riyad” confusingly yake kallon Mom saikuma yakalli Haleema dake kuka sosai trying to ask meya sameta kawai yaga Mom ta mikamai hannunta da karamin dankunne ke kai tace “a ina kasamo wannan Riyad”? Kallon dan kunnen yayi harga Allah baigane dan kunnen bama hakan yasa yace “Mom wat is this”? Cikin fushi sosai Mom tarufeshi da fada tace “nikake tambaya wat is this? Matanka ta tsinci dan kunnen mace a aljihun rigan kayan dakasa jiya kadawo very late kusan to 12 nadare” sai alokacin yama gane dan kunnen nan dayatake ne akasa a office nashi dasauri yawani ma Haleema dake kuka kallo kai tsaye yace “kayana kika duba kika bincika is that abinda kikeyi anytime kikazo this side?”  Mami tace “look at me here nine nazo nike magana dakai not Haleema” authoritatively tace “tell me, me dan kunnen mata keyi a aljihun ka wanda bana matarka ba, mata kake bi yanzu Riyad? Me ka nema wajen Haleematu karasa? Dan kunnen waye tell me now”? Tunda yake baitaba jin Mom ta batamai rai irin na yau ba kanshi ya nuna yanama Mom wani irin kallo yace “Mom I’m your Son, kin sanni sama da kowa a duniyan nan, Mom yanzu akazo aka cemiki ina neman mata bazaki iya shedana ba? Do I look like ina neman Mata? Ni?” Harga Allah tun Riyad na yaro bai taso dason Mata ba, ko kallonsu bayayi hasalima kunya suke bashi amman dai cikeda kafiya dason nunama Haleema she own her Son tace “how do you want me to trust me bayan matarka taga dan kunne akayan dakasa jiya and kadawo very late eh? Look at the way the poor thing is crying” tanuna Haleematu dake wani irin mummunan kuka tace “ko kadan banso kayi hurting yarinyar nan cus she’s a good gurl, tadaukeni mahaifiyarta, Babanta yataka rawan gani sosai wajen zamanka sarki, he’s the one blocking all kulle kulle da akeyi yanzu daka zama sarki” “did I ask him to do anything for me?” Riyad yayi maganan da karfi da saida Mom tabude idanunta cikeda mamaki ta kalleshi, yau Riyad ya daga mata murya haka? Agaban matarshi, cikeda mamaki tace “Nikake dayama Murya Riyad?” Cikin fushi sosai yace “Mom abinda kikemin is totally wrong, sabida Haleema tace inabin mata saikizo ki yarda da maganan ta kinamin fada agabanta baki san danki ba? You’re not allowing me to be the man in my marriage, nagaji I can’t continue with this marriage because of Babanta kikasa ya nemamin sarki dagayau…….” da sauri Haleematu ta taso tana kuka sosai afirgice kawai ta zube agabanshi tarike kafanshi tace “dan Allah kayakuri wlh nasan bakabin mata bansan menakeyi ba danaga dan kunnen saisa nakira Mom” fizge kafanshi yayi yakalli Mom yace “dagayau tell her bata babu this side I forbid her from coming to my side, duk sanda nake bukatanta zan nemeta!” Rushewa da kuka sosai Haleematou tayi takama kafan Mom tace “Mom do something, dan Allah kimai magana ya yakuri, bazan karaba”

Yakalli yanda Haleema ke rokon Mom ya cije baki ya kalli Mom din dake kallonshi mamaki yagama kasheta yace “and for your question Mom” sai kawai yadaga mata kafanshi yanuna mata tafin kafan inda dan kunnen ya shiga yace “nataka dan kunnen nan akasa ya shigan min kafa, na cire zan yarda ganin ina cikin premises kar wani yaje yataka yasa nasa a pocket with the hope nafito i will trash it but I forgot” ya maida kafanshi ya ijiye yace “I don’t want the sarauta ki nemo wani kibashi, I need a break” yana maganan yabi ta gefensu yawuce dagashi sai jallabiyan jikinshi yanda ranshi yabaci ko waya bai daukaba Mom tajuya tabiyoshi dasauri ganin ahaka zai fita tace “Riyad, Riyad” hannu yasa yabude kofa azuciye yafito key motar compound nashi na wajen Munir hakan yasa yayi gate yafice fadawa zasumai kirari ya buga musu tsawa “leave me alone!” Kawai yawuce fuuuuuuuu shi kadai yana tafiya a bala’in zuciye kawai yawuce side din su Munir bude kofa yayi azuciye key daya hango akan table yawuce kaman zaki yadauka daidai Ammi na lekowa daga kitchen ganin shi yadau key dinta ranshi abace yasa tai shiru daidai yabude kofa yafice parking space nasu yaje yana danna key wani jeep yayi kara motar Ammi ce direct yawuce yabude ya shiga yanda ya danna horn zakasan ba lafiya aka budemai key yawuce yafita.


Kusan yaune rana na farko da Mom take ganin serious fushin Riyad haka, and for him to provoke like this that means abinda yafadi gaskiya ne babu matan dayake nema, hankalinta yatashi sosai, wayanta dake hannunta ta daga zata kirashi saitaga wayanshi akan gado kawai cike da takaici takalli Haleema dake kuka tace “you are not sure of something akan wani dalili da rashin hankali zaki tafka shirmen nan eh Halimatu? Jibi abinda kika jawo yanzu? Bakisan idan mai hakuri yayi fushi yafi zama worst ba? Jibi yanda yafita ko wanka baiyiba bai dauki wayanshi ba tsabagen bacinrai, sabida kinga dan kunne in this pocket mesa zaki assuming mata yakebi”? Cikin kuka Halimatu tace “Mami kishi ne yarufeni I can’t share mijina with anybody wlh, kiyakuri Mom kiyafemin dan Allah” dan tsukin takaici Mom tayi tace “naji is not your fault nima daban biyemiki ba nasan waye Riyad, yana tashen samartaka ma beyi neman mata ba sai yanzu, tashi kitafi side naki zansa azo agyara dakinshi lemme handle the situation” Kama hannun Mom Haleema tayi tace “Mom kinsan baya tsallake maganan ki, please kice yayi hakuri karyayi fushi dani koya chanzamin fuska” “naji tafi” Alkyabban tadauko tasaka tawuce tafita daga side din, Mom itama tafito ta tafi sauro da idanu takira babban bafaden gate din yataho da sauri ya zube yace “an gaida Mai Babban daki matan da darajanta yakai…..” Mom bata bari ya karasa maganan ba cikin whispering yace “inada aiki for you Sarki baida lafiya bazai iya fitowa ba shine abinda zaka sanar kaida yaranka bansan kowa yasan Sarki bayanan, zakaga babban sakon tukuici kai haka” Gyadamata Kai yayi yace “angama me Babban daki” juyawa Mom tayi takoma ciki takira Dr su kaman da gaske, kazo gida by 10 duba Riyad”.

**


1 dot tagama da hospital wanda a outpatient department group nasu yake tareda wani consultant na pediatrics, she’s happy sosai yanda itada Bilal da crew dinsa na yanmata basa group daya, salla tawuce tafarayi a masallaci sannan ta linke lab coat nata tasa a bagpack tawuce tafito daga mosque din tagoya jakan abaya tasa takalmi tafito Keke napep ta tare zuwa hotel, sauka tayi tabiyashi ta shiga ciki ko kallon receptionist wajen batayiba as usual changing room tawuce tashiga cire kayan jikinta tayi ta saka dark blue dogon wandon da light blue shirt mai botur tundaga kasan rigan har sama wajajen wuya, farin fatan jikinta ya haska kayan sosai kaman dan ita akai uniform din, clean baby hijab nata farı ta dauka ta saka wanda yarufe mata kirji sannan tasa takalminta, fitowa tayi  zuwa office din Madam tai knocking akace mata ta shigo, shiga tayi tace “good afternoon” “Afternoon Rashida oya ga card din jeki goge office din maza maza, ki dauko kayan gyaran office din a store” karban katin tayi tace “okay” fitowa tayi tawuce store tahada duka abubuwan dazatai amfani dashi sannan tawuce elevator zuwa 5th floor tayi corridor office din, manna katin tayi kofan yayi kara sannan ta tura kofan ahankali hakanan kawai taji gabanta yafadi ga office din yayi mahaukacin sanyi kaman kankara AC a kunne, ahankali ta shiga tareda maida kofan tarufe cikin yar muryanta tace “wayyoo sanyi” dasauri tawuce wajen kashe AC ta kashe tanabin office din da kallo alamun an shigo dama jiya ance Oga yazo lokacin da zata tafi saisa ya shigo office dinshi kenan, a aljihunta tasa hannu ta zaro yar wayanta ta makala earpiece din a kunnenta ta danna wakan Araina Grande mai suna Into You, sannan takoma wajen kofa tadauko kayan ayyukanta tawuce bayi ta tara ruwa tafara bin wakan tafito tadauki handglove black na aiki tazura a hannu tadauki brush din share kura tafara aikinta tana waka……


Ko manager shi batasan yana nan ba babu wanda yasani sabida yanda yazo da jallabiya he looks like normal guest yawuce direct elevator, tunda yazo yake kwance dazun nan ne ma ya iya tashi yayi zuhur yakoma ya kwanta though ba bacci yakeba but ya lumshe idanu kawai having moment of peace, tunda aka bude kofan office din aka shigo yaji, sai chan kuma yaji murya mai bala’in zaki tace wayyoo sanyi, saikuma ga same muryan tafara waka tana aikace aikace dake making sound, shi kadai yace “is she some sort of DJ ko wata Artist?” Cus muryanta dadi bata missing ko harafi daya, kaman tana performing a stage, chan kuma kawai saiya tashi zaune sabida ta kunna vacuum cleaner bayajin muryan nata da kyau kaman da, karan vacuum cleaner yafi muryanta kara, ahankali yataso yataka zuwa wajen kofan hannunshi yakai ahankali zai kama handle na kofan yabude kofan sai kawai yaji yafasa cus baimason aganshi amman kuma saiya tsaya chak awajen yanajin the way she’s singing din cus takashe machine din yanzu tana bin wakan Into your arms na Witty Lowry, God! Her voice is captivating kawai yaji yakasa matsawa.


Daukan bucket na mop din tayi a hannu tarike vacuum cleaner shima a dayan hannun ta tako zuwa gaban dakin sabida tagama da office sai uwardakan before wanke bayuka, juyar da fusknata tayi tana ijiye vacuum cleaner akasa still holding on to the bucket na mop takai free hand din tabude kofan ahankali fuskanta na kallon side din tana rera waka tadawo da hannun tana kokarin daukan vacuum cleaner back danta shigo tunda tabude kofan…

Tunda tabude kofan yayi setting eyes nashi chak akanta yana kallonta tundaga kan pink crocs din dake kafanta dayay finding nasu so funny, dogon dark blue wandonta dabai kamata ba at all kusan ma yaso yamata yawa ya kalla, zuwa navy blue rigan dashi ma bai kamata ba zuwa farin hijab din jikinta that looks extremely neat da side na face nata da he could see sajenta da dan gashinta baki sidik daya leko, daidai tadaga vacuum cleaner ta juyo da kanta kawai taga dogon farin mutum da farin jallabiya ajikinshi ya tsaya chak kaman gunki yazuba hannu a aljihun jallabiyan yana kallonta batada tsoro but saida ta tsorata tayi baya da sauri ganin namiji hakan yasa cord (wayan) vacuum cleaner ya kwasheta jikake timmm tafadi akasa ruwa mopping din hannunta ya kware mata daga ciki zuwa wando, zaro ido tayi atsorace tace “wayyoo Allah na” tai maza maza ta tashi tama rasa mezatayi arude tace “I am sorry” ganin kaman ba ghost bane maybe shine me hotel din takai hannu tana kakkabe jikinta da cinyanta da sauri chan ta lura da aljihuta ajike dasauri tace “Innalillahi wayana” hannu tasa a aljihun taciro wayanta ta cisge earpiece din tashiga tattaba wayan baya haske tace “innalillahi Innalillahi” bude wayan tayi da sauri taciro battery ta huhure wayan sannan tawuce table dagudu ta ijiye wayan awajen danya bushe sannan tajuyo tama kasa kallonshi taduka tana daukan mop tace “sorry i will clean everything yanzu” chak yake kallonta dan yana ganin full fuskanta ya ganeta the girl from the airport! The feisty gurl! Yarinyar daya dade yana nema to reward her for saving his life….



Post a Comment

0 Comments