TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Zabin mahaifina page 5-10

       *ZAB'IN MAHAIFINA*

        🌳🌳🌳🌳🌳



Writen by *SADIYA ALHASSAN(ummu Affan)*



Dedicated to *PRINCESS ESHAT AYSM*

_AYSHA BICHIKI_





Page 5


Bayan mallam Amadi ya dawo daga sallah, ya nemi waje ya zauna inna saude ta kawo masa abincin shi. Bayan ya gama cine ya dubeta  yace ina fatan kin fadama salma sakon da na baki???

inna tace ban fada mata ba mallam, amma yanzu zan fada mata insha ALLAhu


Da harara ya bita dashi,sannan yace kira min ita nina fada mata tunda ke baza ki iya ba.kayi hakuri mallam yanzu zan fada mata.


Tsawa ya daka mata yana cewa ki kiramin ita nace, da hanzari inna ta tashi ta shige daki tana me kwalama salma kira.


Amsawa salma tayi sannan tace inna wani abu xan yi miki? girgiza kai tayi tace mahaifinki ne yake kiranki.


Gaban salma ne ya fadi ta shiga maimaita INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIRAJI,UN!a cikin zuciyarta dan tasan idan taji kira daga wajen mahaifinta, tofa ranar da bakin ciki zata kwana


Inna ta juya ta fice daga dakin tana cewa ki fito yanxu karki bata lokaci. Da hanzari ta biyo bayan mahaifiyar nata,can gepe ta tsuguna cikin girmamawj tace baba gani.Ya dubeta yace dama ba wani magana bane maganar auren kine nagajr da ganinki a haka ba miji,saboda haka na zaba miki miji kuma anjumj zezo saura naji kin masa wani abu. Wallahi jikinki zai gaya miki, yanzu ki tashi kije ki shirya kafin yazo.



a hankali salma ta mike tana hada hanya  ta nufi daki,jin irin hukuncin da mahaifinta ya yanke ba tare daya tuntubeta yaji ra'ayinta kona mahaifiyarta ba. tana shiga daki ta fashe da kuka 😭

tana me cewa ya ALLAh ina rokonka kasa hakan ya zamomin alkhairi a rayuwata🙏🙏🙏


kuyi hakuri da wannan.

[22/12/2017, 18:33] Halimatu Sadiya Affa Fbk: 🌳🌳🌳🌳🌳

      *ZAB'IN MAHAIFINA*

        🌳🌳🌳🌳🌳



Writen by *SADIYA ALHASSAN(ummu Affan)*



Dedicated to *PRINCESS ESHAT AYSM*

_AYSHA BICHIKI_




Masoya makaranta novel dina ina jin dadin yanda kuke nuna kaunar littafina. Nagode sosai ALLAh ya bar kauna.


Page 6


WANENE MALLAM AMADI???


Mallam Amadi dan asalin garin Bauchi ne, a karamar hukumar Ningi. kasuwanci ne ya kawo mahaifinsa cikin garin bauchi


Mahaifinsa yana da rufin asiri daidai gwargwado, su 2 ne a wajen iyanyen su. shi da kanwar sa hadiza wanda take aure a cikia anguwar nassarawa jahun.


Bayan rasuwar iyayen su shiyaci gaba da kula da kasuwancin da mahaifin su yakeyi, yana sayar da kayan yara a kasuwan central.


Mallam Amadi mutum ne me son abin duniya, ko kadan baida godiyan ALLAh.

Matarsa daya inna saude tun auren saurayi da budurwa be sake wani auren ba. macece me kawaici  da hakuri.


ko kadan bata da tashin hankali shiyasa suke zaune lafiya da mallam Amadi dan bata ketare umurnin sa.suna zaune ne a unguwar liman.'yarsu daya ce ummu salmawanda baza ta wuce 18years ba. yarinya ce me hankali dan duk halin inna saude ba abinda ta bari. Tayi karatunta har zuwa matakin secondary, taso taci gaba amma mallam Amadi yace ba'a gidansa ba se dai ta fitar da mijin aure.


Hakane ma yasa ta shiga makarantar hadda dake kan tudu. salma yarinya ce me farin jini kowa sonta yakeyi se dai ita ko kadan bata kula su. Gashi duk wanda zezo wajenta zaka samu me kudine.Hakane yasa mallam Amadi yake jin haushinta, acewar sa tana masa bakin ciki ne.


A hakane watarana ta dawo daga makarantar hadda Alh.Abdul-Razak me dala ya ganta. Tunda ya ganta yaji ta kwanta masa arai, hakane yasa yayi bincike akanta kuma ya yaba da tarbiyanta. Wannan ne dalilin dayasa yazo wajen Mallam Amadi domin ya nemawa tilon dansa namiji aurenta.


Daman me neman kukane aka jefe shi da kashin awaki,nan take mallam Amadi ya amince ba tare daya tuntubi salma da mahaifiyar ta ba. Acewar sa koda tana da wanda take so to se dai yayi hakuri.

[23/12/2017, 12:02] Halimatu Sadiya Affa Fbk: 🌳🌳🌳🌳🌳

      *ZAB'IN MAHAIFINA*

        🌳🌳🌳🌳🌳



Writen by *SADIYA ALHASSAN(ummu Affan)*



Dedicated to *PRINCESS ESHAT AYSM*

_AYSHA BICHIKI_





Page 7 and 8


Readers naji korafin ku akan a kara yawan page kuyi hakuri yaronah ne baida lafiya,amma insha ALLAhu idan ya samu sauki za'a kara yawan pages din. ina godiya a bisa comment din da kuke yi ALLAh yabar kauna.


BACK TO STORY


Salma tana cikin kukanne inna ta shigo ta same ta, samun waje tayi ta zauna sa'annan ta dubeta tace salma kiyi hakuri ki dena kukan haka dan ba'abin da kukan ze miki se dai ya jawo miki wani ciwon.


Nasan ki yarinya ce me biyayya, a wannan karon ma ina son kibi umurnin mahaifin ki. Insha Allah zai zamo alkhairi a gareki.


cikin sheshshekar kuka salma tace inna ni damuwata bansan wanda za'a aura min ba, bansan halinshi ba, kuma ma inna nawa nake da za'ace angaji da ganina ba miji?


Dan murmushi inna tayi wanda daga gani bai kai ciki ba,iya fatan bakin ta ya tsaya. Salma addu'a zakici gaba dayi,dan kinsan halin mahaifin ki indai ya fadi magana tofa ba wanda ya isa yasa shi canjawa. to inna wa za'a aura min? salma ta tambaya tana me share hawayen ta.


ALH. ABDUL-AZEEZ ME DALA. Cikin mamaki salma take kallon inna, wai inna kina nufin A-Azeez me dala da nasani?


shidin dai nake nupi inna ta tabbatar mata. cikin gigicewa salma ta fashe da kuka tace inna yanzu a rasa wanda za'a aura min se A.A? Mutumin da kowa yasan halin matarsa,ko iyayen shi fa bata bari yaje wajen su balle 'yan uwansa.


Duk wacce ya aura fa seta raba su ko kuma ta haukatar da ita. gaskiya inna nikam bazan iya auran A.A ba.


se kije ki fada ma mahaifin naki cewa kefa baza ki iya auran wanda ya za6a miki ba.

Kafin salma tace wani abu suka jiyo muryan yaro a tsakar gida yana sallama,inna ce ta amsa. Yaron yace wai ana sallama da salma,kace tana zuwa.


Inna ta dubi salma tace ki tashi ki fita tun kafin mahaifin ki  ya fito yazo ya same ki.


Cikin sanyin jiki salma ta tashi ta dauki jibin ta ta fita.



🌳🌳UMMU AFFAN🌳🌳

[24/12/2017, 16:55] Halimatu Sadiya Affa Fbk: 🌳🌳🌳🌳🌳

      *ZAB'IN MAHAIFINA*

        🌳🌳🌳🌳🌳



Writen by *SADIYA ALHASSAN(ummu Affan)*



Dedicated to *PRINCESS ESHAT AYSM*

_AYSHA BICHIKI_





Page 9 and 10


Readers nagode da addu'o'in da kuke min ALLAh ya saka da alkhairi. AMEEN


A jingine yake a jikin wata mota ruwan toka kirar marcedez benz c-class 2018.


Matashin saurayine wanda bazai wuce 35yrs ba, fari dogo kyakykyawa ne ajin farko daka kalle shi zakaga yana maka yanayi da jarumin film dinnan na indi'a wato sharukh-khan.


yana da faffadan fuska da kwantaccen saje, idanuwansa madaidaita ne, yana da dogon hanci da madaidaicin baki wanda ke zagaye da siririn gashin baki, wanda ya dada kawata fuskar shi.


yana da faffadan  kirji wanda yake cike da gashi, baida kiba sosai. Mekaratu zanso ka ganshi gayen ya hadu iyakan haduwa ko a kasar india iyakaci😜😜😜


yana sanye da shadda skye blue be saka hula ba, se kwantaccen gashin kansa dayasha gyara atakaice duk yanda ake neman hadadden saurayi to ABDUL-AZEEZ Yakai.


Ba wanda zai ganshi yayi zaton yanada aure. Sallama tayi cikin zazzakar muryarta ASSALAMU ALAIKUM. cike da kasaita da jin kai ya amsa mata, ina wuni? ta fada kanta yana kallon kasa. saida yaja aji dan har tayi tunanin bazai amsa ba sannan yace lafiya.


kamar wanda akayi masa dole,shiru ne yadan ratsa wajen kowa da abinda yake sakawa a cikin ransa. ita tana tunanin wani irin zama zasuyi da shi, yayin dashi kuma yake tunanin an takura masa da akasa yazo wajenta. A ganinsa tayi masa karama, sunkai wajen 15mnt ba tare da dayansu yace uffan ba.


Cikin izza ya fara magana, ina fatan anyi miki bayanin zuwana? be jira abinda zata ce ba yaci gaba.


inason ki sani a tsarina bani da niyan auren mace fiye da guda daya matata kadai ta isheni rayuwa ban damu da tana haihuwa ko batayi ba, dan ita haihuwa nufin ALLAh ce duk lokacin daya so zai bamu


kisani takura min akayi akan sena aure ki, i love my wife, i dont think zan iya hada sonta da wata 'ya mace a duniya bayan mahaifiya ta. Mahaifina shi ya zaba min ke, saboda haka ke ZABIN MAHAIFINA ce.


ina fatan kin fahimta?  shiru tayi masa batace komaiba. tabe baki yayi sannan yaci gaba nazo nan ne saboda umurnin mahaifina, yace na sanar daku baya son aja dogon lokaci. Zaizo ya samu mahaifinki zasuyi magana, kuma bana bukatar a cika min gida da tarkace dan haka ba se an kawo ki da komai ba hope u understand???


Cikin jin haushi salma ta dago tana binshi da wani mugun kallo, cikin kumar rai ta fara magana.


Nima ai kai ba zabina bane kai ZABIN MAHAIFINA ne. kuma da kake cewa kar a cika maka gida da tarkace ai dai kasan komai talaucin mu dole za'a kaini da abinda ALLAh ya hore mana, dan haka maganar kar a cika maka gida da tarkace ma bai tasa ba, we do what ever we want.


iyaka bacin rai Abdul yakai 😡😡😡😡😡shi mutum ne wanda baya son raini. tunda yake a rayuwar sa ba macen data taba fada masa magana makamanciyar wacce salma ta fada masa. wacece ita? da zata ce shiba zabinta bane. har akwai macen da zata kalle shi ta nuna masa bata kaunar sa??


ke wacece dazan fadi magana kice baza kibiba??? TO wallahi bari kiji kar wanda yazo min da tarkace gidana  this is an order. ya karashe maganar yana huci. kuma kisan irin maganar da zaki dinga fada min idan kuma ba haka ba wallahi saina  koya miki hankali.


yana gama magana ya shige motar sa yabar wajen. kada kai salma tayi itama ta shige gida tana jinjina rashin mutunci irin na A.A.



Post a Comment

0 Comments