TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Zabin mahaifina page 22-25

 πŸŒ³πŸŒ³UMMU AFFAN🌳🌳


      ZAB'IN MAHAIFINA

        🌳🌳🌳🌳🌳


Written by SADIYA ALHASSAN (Ummu Affan)


    🌐HAJOW πŸ“πŸŒ


πŸŒπŸ‘©‍πŸ‘§‍πŸ‘§πŸ‘©‍πŸ‘§‍πŸ‘§πŸ‘©‍πŸ‘§‍πŸ‘§HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS ✍🏾✍🏾✍🏾🌐


Dedicated to PRINCESS ESHAT AYSM

AYSHA BICHIKI


Page 22











Tattara wajen salma tayi, sannan ta dauki plate ta d'ebama me gadi ta hada masa tea ta fita domin takai masa.


A zaune ta tarar dashi yanajin radio, bayan sun gaisa ta mik'amishi, karb'a yayi yanata zuba mata godiya. Salma ta kalle shi tace "Baba dan ALLAh  za'a samu ganyen magarya anan kusa?"  eh baza a rasa ba, akwai anan baya bari naje natsunko miki. Godiya salma tayi masa sannan ta koma ciki.


Tana zaune a falo taji ana sallama tashi tayi ta lek'a, taga me gadin ne ya dawo hannunsa d'auke da bak'in leda, mik'amata ledan yayi "hajiya gashi ansamu amma d'anye ne" karb'a tayi tana murmushi bakomai baba daman nafi buk'atar d'anyen, godiya ta sake mishi.


part d'inta ta koma ta tsinki ganyen magaryan guda 7 ta zuba a wani roba ta jik'a da ruwa, ta tofa ayoyin shifa aciki da wasu adduo'i ta barshi ya jik'a. Zob'onta ta hada me dadin gaske,da ruwan addu'an ta saka a fridge.


Falon ta koma ta tattara kayan da sukayi breakfast wanda suka bata, ta wanke ta maida komai yanda yake. Ta gyara part d'inta ta fesa room fresh, ta kunna turaren wuta a burner, ko ina ya dau kamshi.



Humaira ta fito tayi wankan ta tayi kyau ba lefi se dai idanunta sun kumbura da alama taci kuka ta k'oshi. dining taje tayi breakfast sannan takoma kan kujeran falon ta zauna.


k'arfe 11:00 salma ta d'aura abincin rana, shinkafa da miya tayi wanda yaji naman kaza, tayi had'in coslow. ta zuba shinkafar a cooler, coslow d'in ta zuba awani d'an tangaran ta rufe da farin leda ta saka a fridge




Tunanin wanda zata samu yakaima A.A office takeyi, knocking taji anayi mata, zuwa tayi ta bud'e humaira tagani a tsaye " malama kizo kinyi bak'i, ta juya abinta fitowa salma tayi tabi bayanta. Ita dai bataga kowa a falon ba,  waje ta lek'a ta tarar da drivern gidansu A.A tare da wata yarinya wanda baza tafi 14years ba. Bayan sun gaisa yake fad'a mata hajiya ne ta aiko shi ya kawo mata 'YAR AIKIN. Ya mik'o mata wani leda yace "ga wannan tace zakiga bayanin komai a ciki. karb'a tayi tace yace ta gode, harya juya zai tafi ta tsayar dashi "dan Allah ko kasan wajen aikin Alh. Abdul?"Alh. gidan nan? ya tambaye ta  "eh shi nake nufi" salma ta bashi amsa. 


                   Nasani ranki ya dad'e, dan Allah aika zan baka ka kai mishi idan bazan takura ka ba.salma ta fad'a, A'a hajiya bakomai ki kawo sena kai mishi. 


Hannun yarinyar salma ta kama suka shiga ciki bata tarar da humaira a falonta ba, Abincin ta had'a acikin basket ta d'auko had'in zob'onta wanda yayi sanyi ta zuba a jug, ta d'eba ma yarinyar abinci a plate ta bata sannan ja d'auki basket d'in takaima drivern.






Manage with this






🌳🌳UMMU AFFAN🌳🌳

[01/02, 03:32] Halimatu Sadiya Affa Fbk: 🌳🌳🌳🌳🌳

      ZAB'IN MAHAIFINA

        🌳🌳🌳🌳🌳


Written by SADIYA ALHASSAN (Ummu Affan)


    🌐HAJOW πŸ“πŸŒ


πŸŒπŸ‘©‍πŸ‘§‍πŸ‘§πŸ‘©‍πŸ‘§‍πŸ‘§πŸ‘©‍πŸ‘§‍πŸ‘§HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS ✍🏾✍🏾✍🏾🌐


Dedicated to PRINCESS ESHAT AYSM

AYSHA BICHIKI


Page 23


Ledan da aka kawo mata tadauko ta bude,turaruka ne masu kamshi na jiki, se hadin zuma ,dabino da ridi, se mad'i da sauran kayan mata masu inganci. Kowanne an rubuta yanda zatayi amfani dashi ajikin takarda.



Mayarwa tayi cikin ledar aranta tana raya mezatayi dashi, ita tagaji dashan irin wadannan abubuwae, dan tun tana gida Aunty hadiza take d'ura mata su. gwanda ma turaren xata iya amfani dasu.


dauka tayi takai cikin dakinta, ta bude wall drop dinta tasa a ciki ta rufe. ta dawo falon ta tarar da yarinyar ta gama cin abinci. zama tayi akan kujera ta kalli yarinyar tace "menene sunanki?" sunana jamila, yarinyar ta amsa mata. To jamila zaki dinga yimin wanke-wanke da shara se mopping, iya kacin ki falo da kitchen banda cikin d'aki wannan zan gyara da kaina. ina fatan zakiyi aikin ki ba tare dakin bani matsala ba?


Insha Allahu aunty zan kiyaye, zaki sameni mebin umurninki. to shykenan yanzu kije kitchen akwai wanke-wanke se kiyi, amsawa tayi sannan ta mike ta shiga kitchen din domin ta aiwatar da aikin da aka sata.


tananan zaune har yarinyar tagama ta fito, mik'ewa tayi tace"dauko kayanki muje na nuna miki yanda zaki zauna.


           B.Q takaita dakunane guda 2 kowanne da toilet a ciki se falo a tsakiya, se k'aton kitchen a gefe da alama shine manda ake girki a ciki. daki daya blessing ne a ciki, d'ayan d'akin wanda ba kowa salma tace ta shiga, ta juya ta koma part d'inta. 


Toilet ta shiga ta d'auro alwala tayi sallar azahar. ta dawo falo ta zauna ta kunna tashar arewa24, ta samu suna hasko film din dawo-dawo.



Tana zaune taji an turo k'ofarta an shigo ba neman izini, d'aga kai tayi dan taga waye me k'arfin halin shigo mata d'aki haka.


Blessing ta gani 'yar aikin humaira, cikin b'acin rai salma ta daka mata tsawa "Ke!.. baki da hankali ne? da zaki shigo min d'aki ba neman izini, haka aka koya miki a gidanku?" Jikinta yana b'ari ta durk'usa tana bawa salma hakuri.


Fuska ba fara'a salma tace "me kikazo yimin a d'aki?" cikin girmamawa ta amsa hajia babba ce ta aiko ni nazo na karb'a mata abinci a wajenki. 


shek'ek'e salma take kallonta tace kije kice mata ban girka da ita ba. cikin sauri ta mik'e ta fita


Bugo kofar akayi aka shigo, humaira ce cikin masifa ta fara magana " ke salma ina abincina?" ban girka dake ba salma ta fad'a. kutman uba..πŸ™Š ina cikin gidannan kiyi abinci kice baki girka dani ba? to wallahi baki isa ba, da wani tsugudidin ne yasa  kikace zaki dingayi da kanki?


                 kallonta salma tayi tace "ai da nace zan dingayi da kaina bance hardake zan dinga girkawa ba, wa mijina nace zan girka. Alfarma d'aya zan iya miki, shine zan dinga yi dake safe da dare, da rana kuma seki nemi abinda zakici. Hakan ma albarkacin mijina kikaci, dan haka karki  sake zuwa kice na baki abinci danni ba 'yar aikinki bane.


Dubanta humaira takeyi cike da mamakinta,yarinya k'arama ta tsaya tana fad'a mata magana , wanda inda tana da k'anne tayi k'anwa ta 2 da ita, lalle ta samu waje da yawa tace " wallahi salma ina tausaya miki, ni humaira nayi alk'awarin sena LALATA (littafin sad-naf) miki rayuwa, se kinyi nadamar shiga gonata da kikayi.



Tab'e baki salma tayi tace " ni nafi k'arfinki wallahi, idan kina takama dabin malamai ne to ni kuma na rike addu'aπŸ™πŸ™ kuma da yardan Allah ba abinda kika isa kiyi min.


Mu zuba ni dake aga wanda zeyi nasara,humaira ta fad'a kafin ta juya ta fita daga falon. tsaki salma tayi, taci gaba da kallonta.


Driver  ya kai abinci office d'in A.A  masinja yayi masa izinin shiga bayan yaje ya fad'a masa yayi bak'o, tura k'ofar yayi ya shiga da sallama.


Duban shi A.A yakeyi cikin mamakin ganinshi, yace lafiya kuwa mallam haladu?  lapia lau Alh. k'arami(dayake haka suke fad'a masa) gaishe shi yayi kafin yace "daman hajiya karama ce tace na kawo maka wannanπŸ‘‰ . duban basket din  A.A yayi yana yamutsa fuska kafin yace wacece kuma hajia karama? 


Amaryanka nake nufi ranka ya dad'e. kallon basket d'in ya sakeyi cikin mamaki yace "gidan kaje"? eh ranka ya dad'e hajia ce ta aikeni nakai mata 'YAR AIKI. Gyada kai yayi ya nuna masa kan centre table yace ya ajiye a wajen. 


5000k ya mik'a masa, karb'a drivern yayi yana zuba godiya kafin ya fece daga office d'in. basket d'in ya d'auko ya ciro cooler da jug d'in. Ya bud'e ya zuba abincin tare da had'in coslow, sannan ya fara ci.



yana ci yana lumshe ido rabon daya ci abinci me dadin wannan harya manta, ko abincin restaurant dayake aikawa asiyo masa ba yanda ya iya ne kawai, gidan hajiyar sa ne idan yaje yake cin abinci kamar wannan. to shikuma yanzu ba zuwa yakeyi sosai ba. dan ko yaje baya dad'ewa bare har yaci girkinta me dad'i. 


sosai yaci abincin yasha zob'on, a ransa yana jinjina ma yarinyar dan komai nata dabanne, gaskiya yanzu yana farin ciki da ZAB'IN MAHAIFINSA. kiran masinja yayi ya bashi saurae abincin, zob'on kuma ya saka a fridge, zuwa anjuma zai sha dan yayi masa dad'i sosai.





🌳🌳UMMU AFFAN🌳🌳

[01/02, 15:22] Halimatu Sadiya Affa Fbk: 🌳🌳🌳🌳🌳

      ZAB'IN MAHAIFINA

        🌳🌳🌳🌳🌳


Written by SADIYA ALHASSAN (Ummu Affan)


    🌐HAJOW πŸ“πŸŒ


πŸŒπŸ‘©‍πŸ‘§‍πŸ‘§πŸ‘©‍πŸ‘§‍πŸ‘§πŸ‘©‍πŸ‘§‍πŸ‘§HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS ✍🏾✍🏾✍🏾🌐


Dedicated to PRINCESS ESHAT AYSM

AYSHA BICHIKI


Page 24


Da daddare salma ta tuka tuwon  shinkafa miyar egusi wanda yaji ganda, da jallop din taliya da kifi, ta hada da sauran zob'onta na cikin fridge. bata kai abincin dining ba saboda bata yarda da humaira ba.  Me aikinta ta kira ta bata abincin su dana megadi.



Kwalliyarta tayi cikin riga da skert na jan leshi, babban falon taje ta zauna tana jiran dawowar A.A. tana zaune humaira ta fito waje ta nema ta zauna se zabga ma salma harara takeyi.



Da sallam ya shigo falon cikin husky voice d'insa, mik'ewa salma tayi tana amsa sallamar, k'arasawa tayi ta karbi briefcase d'in hannunshi, cikin yanga tayi mishi barka da  dawowa.



d'akinta ta wuce taje ta ajiye briefcase d'in, ta hada masa ruwan wanka, ta d'auko masa jallabiyya da gajeren wando ta ajiye masa akan gado ta fito daga dakin.


                    A kusa da humaira ta same shi kome suke tattaunawa oho musu da alama dai rarrashinta yakeyi. Aranta tace kudai kuka sani jarababbu kawai🀣🀣🀣🀣, kuma insha Allahu duk sihirin da tayi maka seya karye in dai kana shan zob'on nan.



Cikin murmushi ta kalle shi tace na hada maka ruman manka.  dubanta yayi shima murmushin dauke akan fuskar sa ya amsa mata, sannan ya tashi ya shiga d'akin. Mugun kallo humaira ta jefa mata tace "tsabar iya karuwanci ne harda had'a masa wani ruwan wanka?"  murmushi salma tayi tace aiba lefi bane tunda wa mijina nayi, kuma kowa yasan ban taba yawan bin maza ba, bare a kirani da sunan karuwa tayi wucewarta d'aki. bin bayanta da kallo humaira tayi dan tasan magana ta fada mata, wato ita ce tayi yawan karuwancin lalle wannan shine in kasan nafad'a bakasan na mayarwa ba.


Atare suka fito yayi wankan shi se kamshi yake zubawa, ita kuma tana dauke da abinci akan tray, se da ta bari sun k'araso cikin falon sannan ta kalleshi tace " Akan dining zaka ci ko na ajiye akan carpet?


A k'ule humaira ta ce kin taba ganin munci abinci akan carpet?? murmushi salma tayi kafin tace aunty wai ai naga ya dawo daga aikine ya gaji bansani ba ko zai iya hawa kan dining d'in.


ki ajiye akan carpet d'in, inaga zaifi. ya fada yana zama akan kujera, ajiyewa salma tayi sannan ta zuba musu. Abincin suke ci ba wanda yake magana a cikin su, sosai yaci abincin dan ya manta rabon dayaci tuwo, dan shine best food d'insa amma humaira bata taba sawa anyi masa ba. Humaira ma taci taliyar sosai amma bata sha zob'on ba, exotic ta dauko a cikin fridge din falon.


Bayan sun gama salma ta tattara kayan takai kitchen, ta sake wanka tasa kayan bacci tayi kwanciyarta.  Ganin salma bata dawo bane yasa A.A yima humaira se da safe, ya ce mata bacci yakeji dan ya gaji da yawa, be jira jin abinda zata ce ba yayi shigewar sa part din salma, ya barta a zaune ta rasa ma abinda ya dace tayi.πŸ™‰


Yana shiga dakin ya cire jallabiyar ya saka kayan bacci, kwanciya yayi ya jawota jikinsa yayi musu addu'a.


yauma haka suka tashi cikin dare sukayi sallah,da karatun alqurani. da asuba bayan sunyi sallah, ganin da salma tayi fuskar sa a sake yasa ta dauko hisnul muslim ta mik'a masa tace ya karanta azkar d'in. beyi musu ba ya karb'a ya fara karantawa.


bayan ya gama ya dubeta yace " please idan akwai saura tuwon nan kiyi min dumamensa" Amsawa tayi sannan ta gaishe shi, ta tashi ta had'a masa ruwan wanka.



A gurguje ta hada breakfast tayi wanka ta shirya. Bayan da suka gama karyawa  ta d'auki briefcase d'in, har bakin mota ta raka shi. Basket d'in jiya ya ciro mata, tayi masa fatan alkhairi, har ya tayar da motan ya lek'o yace "kina da waya kuwa?" Kallon shi takeyi cike da mamakin canjawar shi. kafin ta girgiza kai, bece komai ba yaja motar sa ya fita bayan me gadi ya bud'e masa get.



Da rana tayi jallop din cous-cous wanda yasha kayan lambu da hanta, tayi had'in coslow, ta had'a zob'onta kamar yanda tayi jiya, tunani takeyi yau wazata samu yakai masa? sega jamila me aikinta ta shigo "aunty ga drivern gidan hajia yazo" 



fitowa tayi bayan sun gaisa yake ce mata " hajia ce ta aikoni akan zan dinga zuwa ina kaiwa Alh. karami abinci, saboda jiya dana koma take tambayata ya akayi na dad'e shine nayi mata bayani"


Godiya salma tayi ta d'auko abincin ta kawo masa,ta mika masa bak'in leda wanda ta saka turmin atamfa da shadda se turaruka masu tsada, tace ya kaima hajia.  Duk da tasan suna da kudin da zasu siya wanda yafi wannan amma ihsani yana da dad'i.



Aikuma hajia halimat taji dadin kyautar dan har Abdul takira take fad'a masa, sosai yayi farin ciki k'imarta ya sake daduwa a idanunsa (mata mu kula yin kyauta ma 'yan uwan miji yana dada miki kima a idanun mijinki, koda su d'in basa kaunar ki to karki ce baza kiyi musu komai ba kiyi musu gwargwadon iyawan ki ALLAh yasa mu dace)


 Da daddare da A.A zai dawo ya siyo ma salma waya ki'ran iphone 7. sosai salma tayi farin ciki,tayi masa godia sannan tace ya bata numbern hajia tana son zasu dinga gaisawa, yaji dad'i kuwa ganin yanda take nuna tana son iyayen sa.


Atak'aice haka suka cinye kwana 7 ba abinda ya tab'a shiga tsakanin su na auratayya, sannan kullum se sun tashi cikin dare sunyi nafila da karatun alqur'ani da safe ta bashi littafi yayi azkar ga kuma zob'o da take hada masa da ganyen magarya da ayoyin shifa dan karya sihiri.



Acikin kwana 7 dinnan kusan duk wani sihiri dake jikinsa ya karye, har tunani yakeyi ta yanda ya auri humaira.


Yanzu kullum seyaje ya gaishe da iyayensa ga wata irin shak'uwa da ta shiga tsakanin su, sosai yake jinta aransa. Iyayensa sunyi farin cikin ganin yaron su ya dawo gare su lallai sun yarda salma ALKHAIRI ce a gare su.



🌳🌳UMMU AFFAN🌳🌳

[02/02, 15:38] Halimatu Sadiya Affa Fbk: 🌳🌳🌳🌳🌳

      ZAB'IN MAHAIFINA

        🌳🌳🌳🌳🌳


Written by SADIYA ALHASSAN (Ummu Affan)


    🌐HAJOW πŸ“πŸŒ


πŸŒπŸ‘©‍πŸ‘§‍πŸ‘§πŸ‘©‍πŸ‘§‍πŸ‘§πŸ‘©‍πŸ‘§‍πŸ‘§HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS ✍🏾✍🏾✍🏾🌐


Dedicated to PRINCESS ESHAT AYSM

AYSHA BICHIKI


Page 25


A gidan su salma washegarin da akayi yini 'yan uwa suka shirya domin suje ganin dakin amarya saboda aranar kowa zai watse.  Har zasu tafi mallam amadi ya shigo yake tambayar su ina zasu je? suka fada masa, masifa yahau yi yace ba wacce zataje kalan suje su bata musu gida, haka kowa ya tattara ya kama gabansd.



Wata rana suna zaune a majalisan su na dattawa, wani daga cikinsu yake bada labari "wato wani mutumi ne ya aurawa 'yarsa wani mekudi, wai shi a zaton sa idan 'yar ta auri Alhajin shima za'a bashi dukiya ne, ashe be sani ba Alhajin d'an yankan kai ne, tunda ya auri yarinyar aka kaita gidansa har yau har gobe ba'a sake ganin suba" ansha zuwa gidan da aka kai yarinyar se a tarar da bakowa agidan.


kuma daman beyi bincike ba ya aura mata mutumin, besan kowa yana shi ba, kudi kawai ya zuba mishi.  Tunda mallam Amadi yaji wannan labarin hankalinsa ya tashi, ya shiga damuwa sosai, fatansa kawai Allah yasa kar wani abu ya samu salma, duk da yasan mijinta baida wani mugun hali amma yasan kishiyarta muguwar mace ce.



Da sallama ya shigo gidan inna saude tana zaune akan taburma tana ninke kayanta data wanke,ta amsa masa sallamar tare dayi masa sannu da dawowa.


                  A kusa da ita ya zauna ya kalleta yace nikam saude kinajin labarin halin da salma take ciki kuma? kallon shi inna saude tayi cikin jin haushin tambayar tace " mallam ai kai zan tambaya, tunda 'yarka ce, kuma kaika aurar da ita, nida ko gidanta bansani ba zaka zo kana tambaya na?


shiru yayi cikin nadamar abinda ya aikata, kasa daurewa yayi ya jefo mata wata tambayar "ina ce su hadiza sunje sunga gidan? me zasuje suyi mallam? ko ka manta bakayi mata komai bane? duk da yaron yace baya bukatar akaita da komai amma ai ya kamata ko gara kayi mata. data maka magana kace ko cokali baza ka saya ba. inda kasaya ne to da wanda suka kai se susan gidan.


kuma ai kasan ba gidanta aka fara kaita ba gidansu mijin aka kaita  se washegari ta wuce gidanta.kuma a washegarin 'yan uwa aka shirya za'aje kace baza'aje ba ko ka manta? 


dan haka nina riga na fidda tunanin salma a raina tunda ta riga ta shiga wannan gidan. 


tana gama magana ta tattara kayanta ta shige d'aki ta barshi a wajen cikin tsananin mamaki, dan be tab'a tunanin zata iya kallon idon shi ta fad'a masa wad'annan maganganun ba, lallai me hakuri be iya fushi.


tashi yayi ya bita cikin dakin ya nemi waje ya zauna sannan ya fara magana "saude kiyi hakuri nasan ban kyauta muku ba, amma ki dubi girman Allah ki fada min halin da salma take ciki"


hawayen da take b'oyewa ne suka zubo ta kalleshi tace "mallam kenan se yanzu ne ka damu da halin da salma take ciki? tunda salma ta girma ta mallaki hankalin kanta kake tsangwanar ta, duk da ita kadai muka haifa hakan besa ka kyautata mata ba a matsayinka na mahaifinta, duk da haka bata fasa yi maka biyayya ba.



A karshe ka aura mata mijin da matar sa tafi k'arfinsa duk dan saboda abin duniya. se yanzu da lokaci ya kure zaka zo kace a fada maka halin da take ciki to nima bansan halin datake ba, se kaje ka samu uban mijin ka tambaye shi.


Girgiza kai yayi yace tabbas nasan ni me lefine amma wallahi saude ki yarda nayi nadama dan Allah ki yafe min insha Allahu zan canja daga yanda kika sanni.


Mallam ni ai baki min komai ba saboda haka kama dena neman yafiyata, ta fad'a tana barin d'akin, dan idan taci gaba da zama tana iya yi mishi abinda bai tab'a zato ba.


         。。。。。


Humaira tana zaune ta zuba tagumi ta rasa abinda yake yi mata dadi, tanaji tana gani komai ya kwab'e mata, gashi lina cta gari tayi tafiya bare susan yanda zasu b'ullowa al'amarin.



Amma tunda gobe zata karbi girki zatasan yanda zatayi ta zubama yarinyar nan maganin taci ta mutu kowa ma ya huta.


Washe gari da safe bayan sunyi wanka sun shirya A.A yace yau baza'a bani breakfast bane?  kayi hakuri yau ba girki na bane aunty humaira ce zatayi maka breakfast.


b'ata fuska yayi yace ashe yau kina son natafi office da yunwa kenan?? ita da take bacci  yaushe lokacin tashinta yayi bare har ta bani breakfast? ki tashi kawai ki nema min abinda zanci dan lokaci na k'urema ya fada yana kallon agogon dake daure a hannun shi.  


mik'ewa tayi ta shiga kitchen ta hada mishi tea ta soya mishi kwai ta dauro akan taray. akan centre table d'in dake tsakiyar falonta ta daura mishi. Bayan ya kammala ta raka shi zuwa bakin k'ofar falon ta mik'a mishi briefcase din, kallonta yayi yace yau kuma anan zaki barni?


yaufa ba girki na bane, dukda bata tashi ba amma ya kamata na kiyaye wani abin saboda gudun shiga hak'k'i dan ko mani akayima haka bazanji dad'i ba. sannan ya ba lallai ne akawo maka abinci ba saboda bani ce da girki ba.



karb'an briefcase d'in kawai yayi ya juya ya tafi, tana mishi a dawo lapia beko kulata ba.




Post a Comment

0 Comments