TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Zabin mahaifina page 30

๐ŸŒณ๐ŸŒณ๐ŸŒณ๐ŸŒณ๐ŸŒณ

      ZAB'IN MAHAIFINA

        ๐ŸŒณ๐ŸŒณ๐ŸŒณ๐ŸŒณ๐ŸŒณ


Written by SADIYA ALHASSAN (Ummu Affan)


    ๐ŸŒHAJOW ๐Ÿ“๐ŸŒ


๐ŸŒ๐Ÿ‘ฉ‍๐Ÿ‘ง‍๐Ÿ‘ง๐Ÿ‘ฉ‍๐Ÿ‘ง‍๐Ÿ‘ง๐Ÿ‘ฉ‍๐Ÿ‘ง‍๐Ÿ‘งHAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS ✍๐Ÿพ✍๐Ÿพ✍๐Ÿพ๐ŸŒ


Dedicated to PRINCESS ESHAT AYSM

AYSHA BICHIKI


Page 30



Washe gari yace ta shirya suje ya gaishe da iyayanta, murna salma ta dingayi yau zataje taga innarta.



A kofar gidan ya tsaya ta shiga tayi mishi iso sannan ya shiga.


cikin mutunci da girmamawa suka gaisa inna, tayi mishi godiyar dawainiyar da yake musu. basu samu mallam Amadi ba dan lokacin yana kasuwa. barinta yayi a gidan yace se dare ze dawo ya dauke ta.


hira suka shigayi cikin farin ciki, se a lokacin salma tasan da maganar kayan abinci daya kawo musu .


cike da mamaki salma tace "ai kuwa inna ko fada min beyi ba"


murmushi inna tayi irin nasu na manya tace 


"ai haka ake son mutum,idan yayi abin alkhairi ya boye, kar hannun damansa  yasan abinda hagunsa yake ciki"


sannan ki sake yi masa godia, nasiha inna ta sake yi mata akan zama da miji.


kayan da salma tazo masu dashi ta ciro ta bata.


turamen atamfa guda 3,se yadin shadda 3 da turaruka. sosai inna tayi farin ciki, albarka tayita sa mata('yan uwana mata da maza, ya kamata komai kankantar kyauta mu dinga kaima iyayen mu saboda kyautatawa da kuma neman albarka, Allah yasa mu dace amin)


salma ce tayi musu abincin rana dana dare. da yamma mallam amadi ya dawo, murna ya dinga yi daya ga salma.


sosai salma taga canji a wajen mahaifinta kuma hakan yayi mata dadi ba kadan ba.


da dare Abdul yazo daukan salma, ya tarar da malam Amadi, suka gaisa yake musu albishir da insha Allahu hajjin bana dasu za'ayi harda Aunty hadiza.


sannan su hada kayansu zuwa jibi zasu koma sabon gida. tsabar farin ciki malam Amadi kuka ya fashe dashi, godia suka dinga yi mishi har saida yaji kunya.


Amota salma take dada yi masa godian abinda yake yima iyayenta, shafo gefen fuskarta yayi da yadayan hannun shi yace


"kidena yimin godia princess nima iyaye nane"


           。。。。。


soyayya suka suke zubawa bawani zancen kunyar juna, amarcin su suke ci A.A irin mazannan ne mabukata, haka salma take jure duk wani bukatar sa ko kadan bata nuna gajiyawarta.


                 A yaune jirginsu ya daga zuwa england bayan sunyi sallama da 'yan uwa.


daganan kuma suje india, america, saudi arabia.


sunyi honey moon dinsu cikin farin ciki, sun zaga gidajen shakatawa dana tarihi.



sun fahinci junan su,ta yanda ko kadan basayin abinda zai bata ran junansu, kowa yasan abinda kowa yake so da abinda baya so, koda daya yayi lefi ma dayan cikin rashin sani nantake ze neman afuwan dayan, wanda akayima lefi kuma ya hakura ba tare dajan rai ba.


 salma ta danyi kiba tayi kyau fatarta tayi fresh.


zuwansu saudia salma ta fara rashin lapia, bayan sunje asibiti gwajin farko likita ya tabbatar musu da tana dauke da ciki na tswon sati takwas.



murna da farin ciki a wajen A.A abin har baya faduwa, kyauta me tsoka ya bama likitan kafin subartasibitin.


wani sabon kulawa yake bata baya barinta tayi komai dan karta wahala, se da cikin yakai wata 7 kafin sukayi haramar dawowa NIGERIA.


sunyo tsaraba sosai ga kayan jarirai da A.A ya jibgo kamar za'a bude shago.


da saukar su a jirgi driver yazo ya dauke su, hajia halimat ta aiko musu da abinci.


washe gari sukaje gaisheta tare da kai mata tsarabar ta, alokacin da taga salma da ciki murnar da tayi ma bata bakine.


 daganan suka wuce gidansu salma, maganin zak'i inna ta hada mata taje ta dinga sha, da zasu dawo ta taho da jamila me aikinta,


dayake da zasuyi tafiya can takaita, blessing kuma ta sallameta tare dayi mata kyauta me tsoka.



cikinta yana wata tara ta haifo yaranta tagwaye dukka maza, aka saka musu Abdul-razak da Ahmad. 


Ana kiransu taufeeq da rafeeq, fadan irin shagalin da akayima bata bakine,Sedai fatan Allah ya raya.


          。。。。。


ya labarin humaira?


humaira duniya sabuma data koma gida taci gaba da yawota ba abinda ta fasa,


wata rana cikin dare suna bacci gobara ta kama gidansu, ba abinda aka cire a gidan iyayenta duk sun kone, itama ta kone fuskarta duk tayi dameji ba'a iya gane kamanninta,


ta dade a asibiti tana jinya kafin a sallameta, abokan shashancinta irin su lina duk sun gujeta, 'yan uwanta kuwa dama ba zumunci take dasu ba, rabonta da zuwa garin tun tana karama. gashi ko taje baza ta iya gane gidan ba.


ba yanda ta iya haka ta dawo yin bara a titi.


salma da A.A  suna cikin mota da yaran su 'yan shekara 2, sunyi wayo idan kagansu zaka zata sunyi shekara 3 saboda girman su.


dai-dai traffic wata mata tazo tana bara, Abdul ne ya mika mata sadaka, suna hada ido ta zabura taja da baya ta fashe da kuka,kallonta yayi yace


"malama lafiya?"


cikin kuka tace


"dan Allah Abdul ka yafemin abinda nayi maka,nasan na cutar dakai na zalunce ka, kaga yanda rayuwa ta dawo dani, tun a gidan duniya Allah ya fara saka maka, iyayena sun mutu sanadin gobara, gashi yanzu banda kowa banda komai, dan Allah ka yafemin ko zan samu sassauci a wajen ubangiji๐Ÿ™๐Ÿ™"



shiru yayi be ce mata komai ba se da salma tasa baki kafin yace ya yafe mata.


salma ce ta mika mata damin kudi ta ce tanemi gida ta zauna ta kuma kama sana'a wanda zata rike kanta dashi.


godia humaira ta dingi yimata, suka ja motar su suka wuce bayan da traffic ya basu hannu.


Anan na kawo karshen littafina me suna ZAB'IN MAHAIFINA, kuyi hakuri naso  naso littafin yafin yafi haka tsayi amma hakan be samu ba, dalilin akwai abubuwa da yawa a gabana, duk kuskuren danayi Allah ya yafemin, wannan labarin k'irkirarrene, kuma ina rokon ku idan kunga kuskure acikin littafin kumin uzuri dan shine littafina na farko. Masoyana ina godia a gareku da irin karfin guiwa da kuke bani, a karshe ina yi muku fatan alkhairi tare da addu'an Allah ya kare mu gaba daya, se mun sake haduma a sabon littafina nan bada dadewa ba.






๐ŸŒณ๐ŸŒณUMMU AFFAN๐ŸŒณ๐ŸŒณ



 

Post a Comment

0 Comments