TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Babu so page 14

      *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*

                 _(Miya kawo kishi?)_




              *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*





*_14_*



..........Ko parking bai gamayi ba da ƙyau a ƙofar gida ta buɗe motar ta fice. Ya bita da kallo harta shige gida. Ƴar ƙaramar ajiyar zuciya ya saki tare da murmushi. Ikram ta fito tana masa bye-bye. Hanun shima ya ɗaga mata har lokacin da murmushin a fuskarsa. Motarsa ya tada tare dayin reverse yabar anguwar dan baizo da niyyar shiga ko'ina ba tunda ko wanka baiyiba. Ga Fadwa dake buƙatar taimakonsa ya baro tana barcin gajiyar daya tara mata a daren jiya wadda shi kansa barcin bawai ya ishesa bane ba, kawai dai sawun giwa ne ya take na raƙumi.


       Anam batai magana da kowa ba ta haye sama, tasan ɗakinta zai yuwu su Amrah na ciki yanzu, na Mamie ma tana jiyo maganar mutane a ciki. Dan haka tai wucewarta falon Abie. Nan kam kowa bata samuba, hakan ya bata damar kwanciyarta ta saki kuka mara sauti. Kuka tayi sosai bana wasa ba har barci ɓarawo yay awan gaba da ita batare data sani ba. Wajen sha biyu Abie daya shigo ya ganta ya shiga taɓa goshinta da tunanin ko zazzaɓin nata ne ya dawo. Amma sai yaji babu zafi jikinta. Idanu ta buɗe da suka maita nauyi dan kukan data sha. Ta dubi Abie ɗin dake mata murmushi. “Sleeping beauty na ta tashi”. 

      Murmushi tai da tashi zaune. “My Abie good morning”. Ta faɗa a marairaice. “Morning Darling duk gajiyar bikince ta saki zuwa nan ɓuyan barci?”. Fuska ta ɗan ɓata. “Abie su Amrah basa barina nai barci mai ƙyau dan surutunsu. Gashi ƙasa nake kwana dan bana son kwana da kowa ɗakin ma ya mana kaɗan”.

    Murmushi kawai yay da shafa kanta. Sai kuma ya dubi idanunta da suka sake fitowa da ƙyau. “Mamana idanun nan kamar anyi kuka da su?”. Da sauri ta girgiza masa kanta. “Abie rashin barcine fa”. Bai gamsu ba. Sai dai baice komai ba. Itama mikewa tai da faɗin, “Bara naje nayi wanka”. Tai maganar da zuwa ta kama hanunsa ta sumbata. Da kallo kawai ya bita, dan yasan tayi hakane dan karya cigaba da tuhumarta akan kumburin idonta daya tabbatar kukane ya sakasu komawa hakan tunda ba yau ya santa ba.


        Ta fito wanka tana shafa mai Amrah ta shigo ta sanar mata tayi baƙo. Da mamaki take kallonta sai dai batace komai ba. Amrah ma ta juya ta fita abinta. A nutse ta ƙarasa shirinta ranta fal tunanin wanene?. Ba ta da mai bata amsa dan haka ta fesa turare da ɗaukar wayarta ta fito. Tayi ƙyau sosai cikin wando da rigar jikinta, sai siririn mayafi data yana a kanta. A wajenta wannan shigace normal saboda a inda ta tashi, sannan rigar bata kama jikinta ba ta kuma sakko har kan mazaunanta. A falo ta samu su aunty Mimi, har zata zauna Mamie ta harareta. “Bake naji ance anzo nema ba?”. Cikin ɓata fuska tace, “Ni banyi da kowaba fa zai zo Mamie”.

     Aunty Hamida tai dariya. “To ɗiyata kika sani ko a ƴan biki ne wani yay sau da baya?. Tashi kije dan da alama mun kusa dawowa wani shagalin insha ALLAHU”.

       “Hu'um aunty ALLAH ya kiyaye ni karatu ma zan koma”.

    Daƙuwa aunty Hamida tai mata. “Karatun gidan ku, a wannan shekarun naki ai aure ne ya dace ko dan kina ganinki ƴar ficika da ƙaramin jiki? Maza tashi kije ana ɓata masa lokaci”. 

     Badan taso ba ta fito, Mamie na kiranta tazo tasa hijjab bama taji ba dan a fusace take da taikaicin koma wanene.

     

       Dr Jamal dake daƙilar waya ya ɗago fuskarsa ɗauke da murmushi yana kallonta. Itako kallo guda tai masa ta kauda idonta. Kujerar dake gefensa ya gyara mata, ta ƙaraso fuska babu walwala tana masa sallama. Amsawa yay murmushinsa na sake faɗaɗa. “Barka da fitowa gimbiyar mata”.

       “Ina yini”.

Ta faɗa a takaice. 

  “Lafiya lau. Bismillah ki zauna mana”.

          Kamar zatace a'a sai kuma ta zauna. 

    “Kiyi haƙuri nazo babu izini. Sai dai karki manta dama nace zan zo dubiya”. 

     Ɗan murmushin yaƙe tayi, a taƙaice tace, “Babu damuwa”. 

    Idanu ya ɗan kafeta da shi, a ƙasan ransa yana tattaro abinda ya dace ya faɗa. Ɗagowa tai ta dubesa itama fuska a murtike. Ya kauda nasa idon. Cikin zolaya yace, “ALLAH ni sai ma naji ina jin tsoronki kamar”.

      Haka kawai yanda yay maganar ya bata dariya, ta shiga ƙyalƙyalawa shiko ya kafeta da idanu yana murmushi. A dai-dai nan aka buɗe gate ɗin gidan mota ta shigo. Su duka sukabi motar da kallo har lokacin kowanne da dariyar kan fuskarsa. Dr Jamal ya faɗaɗa tasa ganin Shareff, itako haka kawai sai da gabanta ya ɗan faɗi.

      Ya kai kusan mintuna huɗu bai fitoba idonsa kafe a kansu, sai dai shi basa ganinsa kasancewar tinted glass ne da motar. Murfin motar ya buɗe ya fito da nufin shigewarsa ya nuna bai gansu ba kawai. Sai dai Dr Jamal daya taso fuska ɗauke da murmushi ya hana hakan. Fara'ar dole ya ƙaƙaro yana mika masa hannu kamar yanda shima ya miƙamasa. “Ango! Ango!! Ƙyallinka dabanne”.

     “Haka dai kace”.

 Shareff ya bashi amsa hankalinsa nakan Anam data ɗauke kai kamar bata gansa ba.

    “Haka ɗinne ma abokina. Dan ko kamshinka yau ya sake bunƙasa fiye da kullum. Muma dai gamu nan fara kafa foundation mukai matsayin nan naku haka nan”.

         Gabansa ne ya fadi, amma sai ya dake ya saki gajeren murmushi. “ALLAH yasa haka to.”

     “Insha ALLAH wannan karon da gaske nake abokina”.

   Nan ɗin ma murmushin yayi kawai da faɗin, “Bara na shiga na gaida su Mamie”.

       “Okay to a fito lafiya”.

Ido suka haɗa da Anam ya wulla mata wani mugun kallo data jima bata gani daga garesa ba ya wuce. Dr Jamal daba lura yay ba ya dawo ya zauna yana dariya. “Kinga Yayan nan naki da gaske angwancin nan fa ya amshesa. Kwana daya kacal harya canja kamar bashi ba”.

       Ƙin cewa komai tayi, sai dai tayi ƙaramin murmushi. Shima murmushin yayi yanaji kamar ya haɗiyeta. Sallamar Amrah ta katsesa daga kallon da yake mata. Duk suka dubeta. Gaishe da Dr Jamal tai, ya amsa cike da fara'a da tambayarta gajiyar biki. Tace masa Alhmdllhi tana maida kallonta ga Anam. “Anam Yaya Shareff yace yana jiranki zai amshi ajiyar daya baki”.

      Kallon Amrah take cike da mamaki da rashin fahimta, sai dai ta rasa abin cewa. Sai Dr jamal dake kallonsu ne ya katse shirun da faɗin, “Inaga jeki kawai ki basa saƙon sai na jiraki. Dan da muhimmiyar magana nazo”.

          Kamar zatace ita babu wani saƙonsa a wajenta sai tai shiru kawai. Ta mike zuciyarta na mata kaikawo da mamakin Yah Shareff ɗin. Yaushe ma har suka fara shiri dazai bata wani ajiyar abu..? Ita kaɗai ta nufi hanyar falon, dan Amrah fita tai dama cikin gida zata ya bata saƙon. Ta shigo ɗan lungun dazai sadata da ƙofar falonsu ya kuma zama hanyar dake tare data garden taji an fusgota. Ihu tai niyyar yi yay azamar rufe mata baki. Sai da ya maida ƙofar ya rufe sannan ya saki mata baki yana binta da wani shegen kallo data kasa fahimtar na minene.

     Baki ta tura tana gyara mayafinta. Ya sake harararta da binta da kallon sama da ƙasa fuskarsa a tsananin ɗaure. “Daga yau na ƙara ganinki da wannan banzar shigar gaban kowane ɗan iska ki tabbatar saina ɓaɓɓalaki na zubar. Ki kuma koma ciki, kona haɗa k da shi na zafafa. Tashi min anan kona kashe fuskarki da mari stupid”.

      Da gudu tabar wajen hawaye na silalo mata. Yaja tsaki mai kauri yana furzar da zazzafan huci daga bakinsa. Fitowa yay daga garden ɗin ya nufi falon shima dan dama ko shiga baiyi ba. Zama yay suna gaisawa da su aunty Mimi da ƴan uwan Mamie dama Abie ɗin. Kasa haƙuri sukai sai da suka tambayesa ko lafiya? Dan yanayinsa ya nuna ransa a ɓace yake. Ya kaƙaro murmushi yaƙe yana shafa kansa. “Bakomai fa auntys karku damu. Gajiya ce kawai da bata gama sakinmmu ba”.

      Mamie dake fitowa a kitchen tai yar dariya.  “To banda abun babana aida basai mun gankaba yau, sai kai zamanka ka huta sosai a gida ko”. Kansa ya shafa yana ƙara risinarwa. “A'a Mamie gara dai nazo na dubaku kuma hankalina zaifi kwanciya ai”. 

     “To shikenan ALLAH yay maka albarka yaya ɗiyar tawa itama?”.

    “Lafiya lau tana gaisheku da muku bangajiya.”

          “Duk muna amsawa”.

Bai wani jima sosai ba ya fito, a waje ya sake samun Dr Jamal. Ya nufesa fuskarsa kadaran kadahan. Shiko Dr Jamal tasa kawace da murmushi. “A'a ango mijin amarya Fadwa har ka fito kenan?”.

       “Eh, ina so na ɗanje na sake hutawa kasan gajiyar biki. Kaima nayi mamakin ganinka anan kai da ya kamata ace kana can kana kwasar barci”.

       “Tab barci ai sai ku angwaye. Muko kwanciya mutum yayta rungumar fillos ai da gajiya. Gara mu fito farautar namu kayan kamar zaifi”.

            “Hakane, amma sai naga baka tafi farautar ba ai”.

     “Kajimun ɗan iska mi kazo kaga inayi? Inama take? Tunda kai akace kana kiranta”.

              Fuska ya ƙara tsukewa da ƙyau yana kallon Dr Jamal ɗin. “Yaka kafeni da idanu kamar naci bashinka?. Tunda kace babu ruwanka ni nazo da kaina na kafa gwamnatina”. Kansa ya kauda yana jan karamin tsaki. Kafin ya dawo da kallonsa garesa. “Jamal amma kasan bana son jan raini ko? Duk manyan mata dake garin nan da suka amsa sunansu mata karasa wa zaka so sai wannan ƴar abar haihuwar jiya”.

      Dariya sosai Dr Jamal keyi, “Oh badai an haifeta jiyan ba? To ni wlhy ko yanzu aka haifota ina son kayata a haka. Yarinyarnan ta haɗa duk abinda nake so ga matar da nake fata ta zama abokiyar rayuwata. Ni bana ganin waɗancan manyan matan sam a idona. Kai dai tunda ka ɗauka taka barni nima lokacina ne”.

     Tsaki yaja mai karfi da barin wajen. Dr Jamal ya bisa da kallo yana murmushi. “A gaishe da amarya sai munzo cin cin-cin”.

     Bai tanka masa ba, bai kuma juyoba ya shige motarsa ya fice. Agogo shima Dr Jamal ɗin ya kalla. Ganin lokacin da Anam taci babu alamar zata fito yay tunanin bara kawai ya wuce ya dawo anjima da dare. Yaran Aunty Hindu dake can gefe suna wasa ya kira babban. Leda dake dauke da kayan ciye-ciye na kwaɗayi ya bashi yakaima Anam ɗin shi kuma ya nufi motarsa.....


______________________________


            Washe gari monday Anam ta koma aiki, Abie da kansa ya kaita. Hakan ya mata daɗi, ya kuma sakata a farin ciki har fuskarta ta kasa ɓoyewa. Da Yaseer ta fara cin karo, wanda rabonsa da zuwa aiki tun randa ya kaita gida. Kallon kallo suka tsaya yima juna, farin cikin da take ciki ya sata fara sakin murmushi. Cikin harshen turanci da mutsukka idanunta take faɗin, “Ko aljani ne kemin gizo”.

     Duk yanda ya so daurewa sai ya kasa. Ya saki murmushi yana gyara tsaiwarsa. “Ba aljani bane ifiriti ne”. Dariya maganar tasa ta bata. Ta ko ƙyalƙyalawa cike da nutsuwa tana kare bakinta da handkerchief. Jiyay gaba ɗaya ya narke a kallonta, harma zuciyarsa na jin anya kuwa zai iya kiyaye dalilin da ya sashi jin zai nisanceta kuwa?... Matsowarta kusa da shi ta katse masa tunani. Har yanzu fuskarta ɗauke da murmushi mai bayyana haƙwara. “ALLAH da gaske naji kewarka Friend. Wane laifi mukai haka ake fushi damu harda tafiya babu sallama?”.

       Hannayensa ya haɗe alamar ban haƙuri🙏🏻, fuskarsa a marairaice sai dai baice komaiba. Cikin ƴar dariyar data ƙara zuwa mata tace, “Shikenan ya wuce muje ciki”.

       Tare suka shiga, suka cigaba da hidimomin gabansu. Koda aka tashi aiki Maheer ne yazo ɗaukarta. Ta nuna farin ciki anan ma dan tunda yazo hidimar biki ta hana su zauna su gaisa da ƙyau. Maheer baida damuwa, yanada sauƙin kai sosai ga barkwanci, sai dai Shareff ya fisa haƙuri nesa ba kusa ba, kawai dai yafisa sakewa da mutanene shiyyasa ake ganin kirkin Maheer fiye da Shareff ɗin.

       Bai wuce da ita gida kai tsaye ba. Sai da suka biya wani joint sukaci kayan kwaɗayi sukai hira sosai sannan. A hanya yake cemata yaushe zata rakasa gidan amarya yaga gida. Cikin taɓe baki ta bashi amsa da “Yah Maheer kaje abinka kai kaɗai kawai”.

          “Miyasa bazakije ba ke?”.

“Ba komai, kuma ni nama riga naje ai”.

      “Idan kin koma ma ai duk cikin zuminci ne”.

   Maimakon ta amsa masa sai ta canja da wata hirar. Shima sai bai sake maganarba har suka isa gida.


        A kwana a tashi ango da amarya sukaci kwanaki shidda da angwancewa. Soyayya ce ake zubawa tamkar babu gobe. Basu da matsalar abinci, dan kullum sai Mamie ta aika musu na safe na rana harda na dare ma, sai da Yah Shareff ɗin da kansa yace a daina kai na daren sannan Mamie ta hutar da kanta. A komai nane suke da juna tamkar su haɗiye kansu. Basu da wata damuwa sai suci suyi ƴar soyayyarsu. Babu inda yake zuwa dan ya ɗauka hutu na sati biyu dama, duk da sati ɗaya yay niyya Fharhan ya takura masa akan biyu dai sannan gajiyar biki ta sakeshi. Ya dauka sati biyun dai kawai badan yana tunanin zama har su cika baije office ba, dan yasan sunada ayyuka danƙam harma da wasu sabbin projects da yake fatan samu wanda zasu fito ne daga gwamnati.

      Yakan je gidansu a kullum da yamma ya gaida iyayensa, sai dai koya shigo wajen su Mamie basa haɗuwa da Anam. Dan a mafi yawan lokuta yakan zone bata dawo aiki ba. Bakuma dan lokacin dawowar tata baiyiba. Kawai dai yanzu Maheer na matukar ɗauke mata hankaline, yama hana Abie kaita da safe shi ke kaita ya kuma je ya ɗakkota, bakuma su dawowa gida sai sun ɗan zaga gari wani lokacin ma sai bayan magrib. Wannan dalilin yasa duk sanda Yah Shareff yazo baya samunta a gidan. Bai dai taɓa magana ba, hasalima bai nuna ya san da wanzuwarta ko saɓanin haka ba. Itako dama ko'a jikinta harma mantawa take da shi yanzun, dan koba komai ta huta da harara da kallon dake matuƙar ƙona mata rai daga garesa.


      Yau ta kasance juma'a. Da wuri Maheer ya ɗakkota a wajen aiki da jaddada mata ta shirya da wuri zatai masa rakkiya wani waje. Batare data tambayesa ba tace to. Ciki ta shige, bayan ta gaida Mamie da Abie ta wuce ɗakinta. Dan aunty Mimi da yaranta sunje Abuja gidan yayan mijinta, amma yau suke saran dawowarsu. Wanka tai ta shirya tsaf cikin kwalliyar doguwar rigar material dan Yah Maheer yace mata tasa kayan hausawa. A lokacin har tana ɓata fuskar cewar ita suna damunta bata son zafi, lallaɓata yay, dan yafi son ganinta a kayan saboda ƙyawun da suke mata. A bikin nan ba ƙaramin son ganin kwalliyarta ya dingayi ba. Koda Mamie tace ta zauna taci abinci catai a'a zasuci a wajen cin abinci Yah Maheer zata raka wani waje. Mamie ta ɗanyi jimm sai kuma ta sauke numfashi, gargaɗi tamata nata kama kanta tare da jin tsoron ALLAH.

       “Insha ALLAHU Mamie bazaki taɓa yin kaico akaina ba, yanda nake a gaban idonki haka zan cigaba da kasancewa a bayan idonki. Domin UBANGIJIN dake azaba ga wanda ya saɓa masa, yake rahama ga wanda ya bisa yana kallona koda ke baƙya ganina”.

     Murmushi Mamie tayi, cike da jin daɗi da alfaharin tarbiyyar da suka bama gudan jininsu tilo duk da suna rayuwa a inda kowa ke ganin dole ne yaro ya lalace, sai dai ba hakan baneba, kowane tsuntsu kukan gidansu yake yi. “ALLAH yay miki albarka, ya kuma baki ikon tabbatarmin da hakan”.

     “Amin Mamie na uwa ɗaya tilo”.

Ta faɗa tana sumbatar hanun Mamie sannan tai mata sallama ta fice. 


       Tun tafiyar tasu batai nisa ba sosai ta fara fahimtar inda suka dosa. Taso ta share amma saita kasa. ta dubesa a shagwaɓe “Yaya nifa....” Da sauri ya dakatar da ita ta hanyar fadin, “Ban son kice komai. Ai ni zaki raka ko”. Shiru tayi badan taso ba. Dan tana ganin girmansa da kima sosai a zuciya da ayyuka. Hira ya cigaba dayi mata, wani ta amsa wani tai murmushi har suka iso. Har ciki ya shiga da motar, kamar yanda ya saba mata a tsakanin nan shine ya fara fita sannan ya zagaya ya buɗe mata fuskarsa dauke da murmushi kamar yanda tata ma ke ɗauke da murmushin mai bayyana haƙora. Tace, “Kai Yaya Maheer shine har da wani ɗan respect?”.

     Dariya ya sanya, idanunsa akan fuskarta yana ji kamar ya haɗiyeta dan murmushi na mata masifar ƙyau. Ƙara risinawa yay irin na respect ɗin yana nuna mata hanya alamar suje. Dariyar ta sake sanyawa da salute nashi itama....


       A hankali ya lumshe idanunsa da ɗaukesu daga garesu yana sakin siririn tsaki dan komai yana faruwa ne akan idanunsa kasancewar yana daga barandar sashensa tare da Fharhan da Khaleel suna magana akan office. Tsakin nasa yasa Khaleel da Fharhan da suma ke kallon su Anam ɗin maido dubansu garesa. Sai dai kasancewar ya riga ya maida ga lap-top ɗin dake cinyarsa yasa basu fahimci da ainahin wa yake ba. Khaleel ya mike yana miƙama Maheer daya iso wajen hannu yana faɗin, “A'a Brother dama nan kawo ashe?”. 

     “Eh wlhy, ai ban san kaima nan din kayo ba damun haɗa tafiyar ma ai”. 

   “Ai babu damuwa tunda ga ƴar rakiya ka samo”.

   Murmushi kawai Maheer ɗin yayi da maida hankalinsa ga Fharhan suka gaisa cikin mutunci dan duk abokan  Shareff suna ɗaukarsu yayu suma.

        “Babban Yaya barka da yammaci”.

Maheer ya faɗa idonsa akan Shareff. Sai lokacin ya ɗago, ya ɗan dubi Maheer ɗin fuska babu yabo babu fallasa. “Daga ina haka?”.

    “Daga gida muke. Yau dai nace bara nazo na gaida amarya na huta da gorinta”.

         “Hakan nada ƙyau”.

Ya faɗa a taƙaice hankalinsa nakan abinda yakeyi dan dama tuni ya maida kansa ga lap-top ɗin. Shima Maheer maida dubansa yay ga Anam data coge can taki karasowa. “Hajjaju ƙaraso mana ku gaisa da su Yaya”.

     Baki ta tunzura, badan taso hakan ba ta nufesu tana ƙunƙuni. A jimlace ta gaishesu, batare data damu dawa ya amsa ba waye bai amsa mata ba tabar wajen. Shima Maheer bayanta yabi sai dai ganin ta sake cogewa alamar bazata shiga falon ba yaja hanunta. Ƙoƙarin amshewa take amma ya hana hakan sai da suka shige ya saketa. Kowa babu a falon sai uban ƙaurin abinci daya gaurayesa, ga falon a ɗan hargitse alamar dai yau bai samu gyara ba koma ba yau ɗin kawai ba. Anam ta yamutse fuska kamar mai tsantsami tana bi ko'ina da kallo a karo na farko dan waccan ranar batai ba. 

      “Ni kamar ƙaurin abinci nakeji fa?”.

      Ya Maheer ya faɗa yana dubanta. Baki ta taɓe da kauda kanta batare data amsashi ba. Shima sai bai sake magana ba ya shiga ƙwala kiran sunan Fadwa a tunaninsa ko ta shiga wani uzirinne a ciki batasan abincin na ƙunewa ba. Kusan sau uku sannan ta fito daga hanyar bedroom hanunta rike da waya tana murmushi, da alama abu take dubawa da yake sakata nishaɗi...........✍



_😣😣Wayyo Fady baby ya zaki bamu kunya haba selen mu so kike ƴan uba su sami na faɗa yau🤕. Koda yake munada bakin ramawa🚶_




Post a Comment

0 Comments