TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Nacina ya jawo mini page 53-54

 *Daga alƙalamin* 

🖍️📚*Narrnarhh Bukar* 📚🖍️




*Comments and share 🙏🙏🙏Fisabilillah*.



[5/18, 10:15 PM] Narnarhh Bukar:



 🏵️ *NACINA YA JAWO MIN* 🏵️






*Narrnarhh Bukar* 

( *The Amazing Pen* ✍️)




*TASKIRA WRITER'S FORUM*

*T.W.F*


*BOOK 2*



5⃣3⃣----5⃣4⃣




A cikin labour room ɗin nurses uku ne suke taimaka mata wurin amsar haihuwan wanda Maman Jummalo tasha baƙar wahala kafin ta haihu,nurse ɗin da take a wurin da yaro ya fito hankalinta yayi matuƙar tashi jin *kukan jaki* to a ina haka? Mamaki ne ya cika sosai, to a ina aka samu jaki ne haka,sai kuma wata daga cikin nurses ɗin wacca take kusa da ita  ta ƙwalla abun  ƙara tana nuna wurin da yaro ya faɗo,ai da sauri wacca taji kukan jakin takai dubanta ga wurin,ita ma ƙwalla ƙarar tayi ganin jariri da *kan jaki* amma sassan jikinsa na mutum,ikon Allah haka nurses ɗin suka tsaya suna kallon yadda yake kukan jaki amma an kasa samun wacca zata ɗaukeshi don a goge mishi jiki,ji kake yana


"Hiiiihiiiiih!!! Hiiiiihiiiiih!!! Hiiiihiiiiih!!! "


Ita kuma Maman Jummalo an koma baccin gajiya,a nan wata daga cikin nurses ɗin tayi shahadar ɗaukansa don a goge masa jiki,jikinsa irin na mutane amma kansa exactly na jaki,ga ƙwayar idanunsa idan ya ɗan buɗesu kalar na maguna ne,haka nurses ɗin suna tsoro-tsoro haka suka goge mishi jiki da Olive oil,sannan aka saka mishi kayan da suka amsa wurinsu Umma Kande daman da kayan haihuwa suka zo asibitin,wata a cikin nurses ɗin ta ciro wayarta tare da ɗaukar hotunan jaririn ta ɗora a social media,ai kan kace me hotunan jaririn Maman Jummalo sun karaɗe social media.Bayan an shirya jaririn sai wata nurse ta fito dashi a lokacin yayi bacci tare da miƙa ma Umma Kande kasancewar tafi kusa da ƙofar labour room,da sauri da amsa yaran tana farin cikin amma me tana tozali da kan yaron ƙirjinta ya bada Ras! Cikin rawar murya Umma Kande ta ce


"Innalillahi wa'inna ilaihi Raji'ana!!! Ni Sarere jikar Sarkin ruwa mi zangani haka yaro da kan jaki!!! Kai kuzo su Auta kuga abinda na gani"


Still jikinta na ɗaukar ɗan mazari haka take maganar,su Jummalo da Iklima da sauri suka matso inda take tare da kai dubansu ga yaron,ai kamar haɗin baki haka suka furta


"Inna'illahi Wa'inna Ilaihi Raji'un!!! "


Jummalo ce ta cigaba da magana cike da tashin hankali


"Mun shifa uku mun lalace ɗa mai kan jaki mama ta haifa!!! Ya Salam!!! Tamu ta samemu!!! Wayyo Allah ni Jummalo!!!....."


Kuka take riris tana ƙara duba yaron da kyau kodai idanunta ne basu gani da kyau ba,tabbas mai kan jakin mamanta ta haifa,zuwa wurin boka ya musu riba,kuka take sosai ita kuma Iklima tana lallashinta akan tayi shiru kar mutane su san meke faruwa su taru a wurinsu,ita kuma Umma Kande ƙara kallon yaron take sosai shi kuma bai san ma mai ake ba,baccinsa yake hankali kwance tunda sanda ya fito daga mahaifar uwarsa tare da tsandara kuka irin na jaki bai kuma kuka ba har goge mishi jikin da ake duk yana ta baccinsa.


Nurses ɗin da suka amshi haihuwar ne wata a cikinsu ta cema sauran nurses din da suka tsaya sunyi cirko-cirko suna kallon su Umma Kande da yaron sun ƙi tafiya


"To ya za'ayi da Mom ɗinsa,bacci take kuma ya kamata akaita ɗakin hutu"


"Kuma fa hakane,muje mu kaita ɗakin hutu tunda gadon mai taya ne,abun yazo da sauƙi" cewar wata nurse 


Haka suka koma cikin labour room ɗin tare da turo Maman Jummalo a gado mai taya zuwa ɗakin hutu,still tana nan tana bacci batasan meke going ba.Su Iklima,Jummalo da Umma Kande na biye dasu zuwa ɗakin,ɗakin  mai zaman mutane biyu ne domin akwai empty gado wanda ba mutum akansa,haka suka shimfiɗe Maman Jummalo a gado tare da sake leka yaron sannan suka wuce abinsu.(Oh ni Indo Nurses da shegen gulma,duk hotunan da kuka ɗauka na jaririn bai isheku ba😂😂😂🙃🙃)


Zama su Umma Kande suka yi sannan ta shimfide yaron a bisa gadon jarirai na ɗakin sannan ita ma ta samu wuri kusa dasu Jummalo ta zauna,abin duniya ya addabi zukatan kowannansu,kowa ka gani yayi shiru yana karanta wasiƙar jaki(Au na manta ashe suna da ɗa mai kan jaki😂😂😂)


Maman Jummalo ta kwashe kusan hour biyu cur! Tana bacci sai can yaron ya fara kukan jaki alamun ya farka,itama kukan yaron ya tasheta cikin ɓacin rai irin an hanata bacci Maman Jummalo ta ce


"Wani irin hauka ne haka!!! Wa ya kawo jaki cikin asbiti ne!!! Duk ya ishemu da kuka babu daɗin ji balle sauraro!!!  "


Shiru sukayi dukkaninsu suna kallonta,tausayinta ne ya kama kowannansu musamman ƴarta Jummalo wacca har yanzu sharan hawaye take,shirun nasu ƙara fusata Maman Jummalo yayi saboda kukan jakin a cikin ɗakin take jinsa,cewa tayi


"Wani irin abu ne haka,ina muku magana amma kun tsiramin na mujiya kunki amsani,kukan ma a ɗakin nan nake jinsa"


Umma Kande ce ta da ita


"Ƙawas don Allah ki rage fushin nan haka, duka-duka yaushe kika haihu,ki kwanta ki huta mana"


"Inajin kukan jakin zan kwanta Ƙawas,ce nike kukan ne ya tasar dani daga bacci,wai ma ina ɗana yake"


Kallan-kallo kowa yake acikinsu an rasa mai bata amsa,katse musu tunani tayi da cewa


"Magana nake muku fa"


"To ai yaronki ne ke kukan jakin" cewar Iklima


"Menehhh shike kukan jaki!!!.... "


Tsandara wani sabon kukan jaki jaririn yayi jin anƙi ɗaukarshi tare da katse maganar da Maman Jummalo tayi niyyar faɗa,ji kake


"Hiiiihiiiiih!!! Hiiiihiiiiih!!! Hiiiihiiiiih!!! "


"Innalillahi wa'inna Ilaihi Raji'un ni Hafsy naga ta kaina,ke kawoshi na dubashi nan"


Iklima wacce take kusa da gadon da jaririn yake tayi saurin ɗaukoshi hadi da miƙa matashi still yana tsandara kukan jakin, ana miƙa mata ƙirijinta ya bada wani sautin Ras! Ras! Rarass!!! A lokacin da tayi tozali da kansa irin na jariran jakuna sababbin haihuwa,kuka Maman Jummalo ta fara tare da ƙara duba yaron nata,innalillahi wannan wace sabuwar musiba ce haka yaro da kan jaki,tana kuka shima yaron na kukan jaki, Umma Kande ce ta ce


"Ƙawas nono yaron yake so fa"


"Nono zan ba jaki Umma Kande, tayaya zan shayar da jaki ni Hafsatu wannan wace kalar musiba ce haka,daga wannan bala'in sai wannan duk a sanadiyar zuwa wurin boka,wayyo ni Hafsy,na bani na lalace"


"A'a fa yanzu ba lokacin kuka bane ƙawas ki bashi nono yasha tunda daga cikinki ya fito,albashi idan mun koma gida sai musan abunyi"


Haka da jiro nononta tare da saka mishi a baki,kamar jira yake ai da ya wani zuƙo nonon da sauri Maman Jummalo ta fizge nonon daga bakinsa jin wata azaba ta taso mata tun daga ƙwaƙwalwarta zuwa kan nonanta wanda tunda take bata taba jin irin makamancin azabar ba,ko sanda ta haifi Jummalo bata ji zafi irin haka ba,Umma Kande ta kara cewa


"Haba Ƙawas ki bashi yasha mana kuka fa yake fa,ko so kike ya tara mana jama'a a cikin ɗaki"


"Wai wai waiii ina zan iya Ƙawas wannan azaba haka! Ai don ba nonanki yasha bane shiyasa zaki ce haka"


Ƙara tura mishi nonan tayi a baki,da sauri ya cafke ji kake Zut! Zut! Zut! Yana zuƙar ruwan nonan kasancewar Maman Jummalo akwai ruwan nono, yakai kusan mintuna ashirin yana shan nonan amma baida alamun ƙoshi,ita kuma Maman Jummalo yunwa take ji sosai,tana bukatar tea mai kauri ko hanjin jikinta sa warware,fizge nonan tayi tare da cewa


"Wallahi ko ka ƙoshi ko baka ƙoshi ba ya isa haka, wannan jaraba dame yayi kama haka,ni ku bani abinci yunwa nake ji"


Ɗauko mata shayin da aka siyo mata a waje ne aka bata tare da soyayyan indomie da ƙwai,ci ta fara yi wanda bata daɗe ba saiga likita da nurses ɗin nan da suka amshi haihuwarta,tambayoyi ya mata tare da duba yaron, mamaki da al ajabi ya kama likita ganin yaron da kan jaki sak!,cewa yayi a yau za'a sallamesu tunda uwar da ɗan lafiyarsu lau,fita yayi su Umma Kande sukaje wurin biyan kuɗin sallama,kafin su dawo har su Jummalo sun tattara komai tare da goya yaron,fitowa sukayi zuwa wajen asibitin domin taran keke napep su wuce gida,sunci sa'a ko mintuna biyar basu yi ba saiga empty keke napep sun samu,shiga sukayi sai mai keke napep ya tada suka wuce,a akan hanya yaro da yaji wata sabuwar yunwa kawai ya fara kukan jaki babu ji babu gani,da sauri me keke napep ɗin ya tsayar ta kekensa,Allah ma ya tsaresu da sai sunyi accident saboda firgici hadi da ruɗun da mai keke napep ɗin ya shiga jin kukan jaki a keke napep ɗinsa,bayan yayi parking ya ce


"Malamai lafiya naji kukan jaki a kekena kuma banganku da jaki ba? "


"Kayi haƙuri haka halittar yaron take,kukan jaki yake tunda aka haifesa" cewar Jummalo


Wacca take a gaba tare da mai keke napep ɗin, mamaki ne ya cika shi,girgiza kai yayi tare da tada keken suka cigaba da tafiya har suka isa ƙofar gidansu,sauka sukayi sai Umma Kande ta biya mai keke napep ɗin kuɗinsa sannan suka shiga cikin gidan.


Nusaiba ce da Al Qur'ani izu 10 tana karantawa taji shigowarsu da sallama,amsa musu tayi da fa'arta tana ina yaronsu,su kuma fuskar nan tasu babu yabo babu fallasa,kwance goyan Maman Jummalo tayi lokacin har ya koma baccinsa ta miƙama Nusaiba tare da nufar ɗakinta don ta huta,da sauri Nusaiba ta amsa yaron tana dan murmushin,ai tana buɗe gefen zanin daya rufe fuskar yaron ta tsandara ihu tana cewa


"Na shiga aljanna ban fito ba,yaro da kan jaki!!!"


"Ai saiki faɗa kowa yaji harda maƙwafta!!! " cewar Umma Kande tana amsar yaron zuwa ɗakin Maman Jummalo


Mutuwar tsaye Nusaiba tayi,a zuciyarta tana ƙara tsakake sunan Allah tabbas Allah da girma yake, shike yadda yaso a lokacin da yazo,shike nuna ishara ga bayinsa a sanda yaso kuma a yanayin da yaso,tab! Zuwa wurin boka ko malamin duba baiyi ba,ga ƙarshan zuwa wurin boka an haifo yaro mai kan jaki,Allah ya shiryamu shirin addinin musulunci,haka tayita zancen zuci still tana a tsayan kowa ya shige ɗakin Maman Jummalo anbarta a wajen sai itama da shige ɗakin.


Koda Nusaiba ta shiga ɗakin ta samu Maman Jummalo naba yaron nono,tsira ma yaron ido tayi ganin jariri dashi har ya iya riƙe nono abinsa ikon Allah, ɗakin shiru yayi sai can Umma Kande ta ce


"Ƙawas yanzu ya za'ayi da wannan yaron ne"


"To ya za'ayi dashi tunda Allah ya ƙaddara fitowarsa,ai sai haƙuri zamuyi"


"Nifa wata shawara nazo da ita ko ince dubara"


Taɓe baki Maman Jummalo tayi don tasan maganar *gizo bata wuce da koɗi* ce mata tayi tana saurare,saida Umma Kande ta gyara zama sannan ta ce


"Tunda yaron ya fito duniya,mai zai hana mu sake komawa kun boka Sankeruuu........"


"Dakata Umma Kande!!! Allah ya sittiri- buƙyi ni Hafsy na sake zuwa wurin wani don neman wata biyan buƙatata,da Allah na dora kuma shi zai biyamin bukatuna,wai ke Umma Kande baki ga isharar da take sauka akanmu bane duk saboda zuwa wurin bokan da muke ehhh,ce nike garin yawan zuwa wurin boka na kwaso ciki,sannan yanzu ga wata babbar ishara wacca Allah ya kara nuna mana duk don mu hankalta ,mu gane Allah ne ke biyama mutum bukatunsa ba wani ba,in ba ikon Allah ba tare da nufinsa taya mutum zai haifi yaro mai kan jaki,haba Umma Kande ki tuba mana,ce nike wacca kike zuwa wurin boka don ita tabar miki gidan keda yaranki,amma har yanzu  kin kasa gane Allah ɗaya ne"


Huro guntayan hancinta Umma Kande tayi tare da taɓe baki irin ko ajikinta ɗin nan, magana ta fara cike da ƙasaita


"Ke kikaga wani ishara bani ba,kuma zuwa wurin boka na faɗa na ƙara yanzu na fara zuwa,babu gudu babu ja da baya,domin kuwa naga alfanu da daman a wurin zuwa wurin boka"


"Haba Mama wai yaushe zaki tuba ki gane Allah ɗaya ne,Muhammad (S.A.W) manzonsa ne,kina cewa baki ga wata ishara ba,abubuwan da sukaita samun mu a gidan mazajenmu duk ba isharori bane Mama,yanzu ga yaro an haifa mai kan jaki shima din ba ishara bace a gareku masu zuwa wurin bokaye da malaman zaure,haba don Allah a gaskiya kam ki gyara domin ke kaɗai ce bakiyi nadama ba" cewar Iklima


"Oho dai ni kunga tafiya ta,bara nasa a nemo almajirai su siyomin itace da ɗora ruwan wankanku"


Miƙewa tayi tare da barin ɗakin,su kuma da kallo suka bita tare da yi mata adduar shiriya,haka suka cigaba da jegon wanda kafin ayi suna yaron yace ga garinku nan,daɗi kamar ya kashesu ana damuwa da mutuwa amma su farin ciki suke domin kasancewar yaron a raye ba karamin matsala bane a garesu,saboda gulmursu za'a dinga yi ga ɗan goka an haifa musu.


Haka suka cigaba da rayuwa hankalinsu kwance musamman Maman Jummalo jinta tare sakayau babu abinda ke damunta a yanzu,ibada ta koma yi ka'in da na'in babu wasa,ita ma haka Nusaiba ibadarta take yi ga jin wa'azuzzukan malamai da dama,su Iklima da Jummalo sun cigaba da zuwa Islamiyarsu sannan idan suka dawo sai su koyama Maman Jummalo da Nusaiba ita kuma uwar gayyar saidai ta taɓe baki tare da hura guntayan hancinta sama irin ko ajikinta.Wannan kenan




           @@@@@@@@@@@



A ɓangaren zamantakewar *LOVE BIRDS*  🕊️🕊️wato Sauban da Maryam har yanzu zamansu babu daɗi,kusan ince ita take da matsala bashi ba domin baka taɓajin faɗansu da Khairat saidai ita,kullum da ita suke faɗa suyi su gaji wani lokacin harda doke-doke musamman idan a kamfani an ɓata masa rai akan Maryam yake sauke fushinsa,ita ba hakuri kamar zawo haka take biye mishi shi kuma ya mata dukan tsiya.Har yanzu Maryam batasan me ake kira da aure ba,kuma iyayenta sunƙi ɗorata a turbar gaskiya na bin mijinta da surikarta a kullum cikin zugata suke akan karta yarda a rainata ko  kuma karta sake a wulaƙanta ta,sunƙi koya mata abubuwan da macen kirki ya dace ta sani a gidan auranta irin iya girki,tsafta,sanin darajar miji da hakƙokƙinsa,girmama uwar miji da danginsa,iya lafuzza masu daɗi wurin yima miji magana da dai sauransu.


A zamantakewarta da kishiyarta Khairat babu wani matsala domin Khairat tasan kan zaman duniya sosai,bata biye ma shirman faɗanta,koda Maryam ta takaleta da faɗa bata biye mata saidai ma ta  shige ɗaki abinta.


Har yanzu babu wacca a cikinsu take da ciki ko kuma tayi ɓari,hakan na damun Momin Sauban don ita a tunaninta ada baya kula Maryam shiyasa bata samu ciki ba,to yanzu fa ga Khairat ita shiru babu alamun ko ɓatan wata ta taɓa yi.


A ɓangaren aikin Sauban a kamfani kamar jiya iyau ne domin duk wata hanyar da zasuyi cuta Sadam ya kulleta,komai akan tsari yake, babu muna-muna balle handama da babakere,wani lokacin idan Sauban ya zauna shi kaɗai sai yayita karanta wasikar jaki(bafa ɗan Maman Jummalo nake nufi ba ehehh😂😂😂🙃🙃)


A zuciyarsa yana faɗin 'Anya bada *farar ƙafa* duka matana suka cigo gidana dashi ba,kullum babu cigaba sai baya,duk ƴan uwana sun mallaki gidan kansu amma ni ko fili na gagari siya,Ya Salam a gaskiya akwai inda na samu matsala,gaskiya da sake wallahi,abin haushi saidai kowaccansu tashi tayi kashi amma ko ɓatan wata babu wacca tayi,da alama hauka zanyi musu wallahi dole su haihu don na gaji da ciyar dasu a banza babu haihuwa' haka yayita tunaninsa tare da saƙa-warwarar yadda zai fito musu mutum.Wannan kenan




        @@@@@@@@@@@@




*KEBBI*



Sadam tunda ya isa Kebbi,yake ta tasa Mominsa da shagwaba wai shi aure yake so ayi mishi,dariya maganar Sadam tabama Mom da Daddynsa lokacin dukkaninsu suna falon Dad suna hira,ya samesu da maganar auran Sa'eeda kuma yanaso inda halin nan da ƴan kwanaki haka, Mom ce cikin dariya tace


"Ooohi nii Ruƙayya jikanyar Dikko Auta aure yake so haka da wuri,kaida ada nake binka da zancen aure kana guduna amma yanzu da kanka ba aike ba kake cewa ayi maka aure a nan kusa,O'o'oooo ni jikanyar Dikko,Alhaji kace wani abu"


Dad dake dariyar shirman Sadam ya ce


"A'aaah su Autan Momy aure akeso da wuri haka,a gaskiya ƴata ta ruɗa Autan Mom dayawa"


Dariya suka ƙara tintsirewa dashi ganin yadda yayi tuƙuƙu da fuska kamar mai shirin kuka kamar ba miskilin da kuka sani ba idan yana waje,amma a wurin iyayensa ji yake kamar yaron goye,cikin shagwaɓa Sadam ya ce



"Umm umm Dad dariya kukemin ko,Allah da gaske nake,a ɗaura mana auran ko nan da 2weeks coming ai yayi haka"



"Eh lallai Sadam wato nan da 2weeks kamar an gaji da ita ne aka ce maka,to bari gaji saita kammala school ɗinta complete kafin a ɗaura muku aure tunda semester daya ya rage mata" cewar Mom


Zaro idanu yayi waje jin ance sai ta kammala school ɗinta complete anya zai iya jira har wannan lokacin kuwa,a yadda yake tsananin sonta da ƙaunarta wanda kullum wutar so da kaunarta ƙara ruruwa take a cikin zuciyarsa,tabb da sake wallahi. Tashi yayi tare dayi musu sallama yabar falon zuwa part ɗinsa, yana shiga ya kira wayar Sa'eeda don ya samu haɗin kanta,bugu ɗaya-biyu a na ukun tayi picking tare da sallama cikin sassanyar muryarta mai daɗin sauraro



"Assalamu Alaika Ya Sadam"



"Wa'ailikissalam my darling star"



Rufe fuskarta tayi kamar yana kallonta ita nan taji kunya



"Ya kike,ya kuma school ɗin hope everything is going normal"



"Eh Alhamdulillah Ya Sadam"



"Wai ba nace ki daina kirana da Ya Sadam ba"



"Ka faɗa,to ni bansan wani suna zan dinga kiranka dashi ba"



"Nema yanzun nan ina jinki Sa'eedar Autan Momy"


Ƙara rufe fuskarta tayi,sai kuma tace


"Na kiraka da my Happiness"



"Ummm it sound very usual,nemo wani don wannan mutane sun sanshi,ki tuno Hajiyata" (Jama'ar Annabi Sadam da alama yasan sirrin lobayya😂😂😂)



Ɗan tunani Sa'eeda tayi sai can ta ce 


"In kiraka da My Sadauki"



"Woooow! Excellent! Great! Sunan yamin sosai haba ko kefa amma kullum Ya Sadam Ya Sadam"


Dariya tayi jin yadda yake kwaikwayar maganarta,harda lakwasa murya,katse mata maganar yayi da cewa


"My Darling Star kin mamaye ko'ina a jikina,jijiyoyina da gabɓaina duk kin mamaye,ina matukar so da ƙaunar Sa'eeda"


"My Sadauki duk ni kaɗai haka"


"Eh mana Sa'eeda,saboda kefa na fara jin waƙokin hausa na soyayya musamman waƙoƙin Umar.M.Sharif,kinsan yasan ilimin soyayya"


"Laaaah!!? To rairomin naji My Lifeline"


"Wayyo daɗi wani sabon suna da ɗimi-ɗiminsa *My Lifeline* great my Sa'eedatyyy yanzu saiki shirya jin waƙar"


"Ina saurare"



Saida yayi gyaran murya kafin ya fara rairo waƙar kamar haka


*"Kin sace zuciyata!!! Wayyo kin mallaketa!!! Kinsa inata sonta!!! Dubeni na jigata!!! Zanso kibanita ta!!! Inje in mallaketa!!! Inda za kijji abinda nake ji a cikin zuciya!!! Da ba ko shakka ni nasan da kin tausaya!!! Karda nayo jinya!!! Kibani soyayya!!! Sani akan hanya!!! Kiji daniiii!!! "*


"Wooooow!!! A gaskiya kamafi Umar.M.shariff ɗin iya waƙa"


"Da gaske Sa'eedatyyy"


"Eh wallahi"




"Naji dadi kuwa,yanzu mu buɗe wata chapter my Darling Star"


"To ina sauraranta  my Lifeline"



"A gaskiya bazan ɓoye miki ba Sa'eeda, inason ayi auran mu da wuri,in yaso sai ki kammala school ɗinki a gidana,ko ya kika ce"



Shiru ta ɗanyi kamar baza tayi magana ba,har Sadam ya fara hello! Hello! sai can ta dawo cikin hankalinta tare da cewa


"My Sadauki mai zai hana kabari bayan na kammala school sai a ɗaura mana auran inyaso sai nayi service a ɗakinka,nagana hakan yafi ai"



"Ohhhh kema bakinku ɗaya dasu Mom ko,Sa'eeda na ƙagara naga na aureki,saboda kullum sonki da ƙaunarki ƙara mamaye ko'ina na jikina yake,ni wallahi in don tani ne,a daura mana aure nan da 2weeks coming"



"Ya Sadam in 2weeks coming tabb,to karatun fa"


"Saiki kammala shi a gidana"


"Kai my Lifeline kamar yarda Mom suka ce kabari after my school,i think is more better,kaji nima ai ina kaunarka sosai my Sadauki"



Haka suka cigaba da hirarsu ta soyayya sai wurin 11:12pm suka yanke kira tare da kwanciya.


A bangaren Umman Sa'eeda yanzu hankalinta a kwance yake, bata aikin komai sai kallon television da kwanciya,tayi ɓul-ɓul da ita,haskenta ya kara bayyana,gashi kullum sai sunyi waya da sanyin idaniyarta Sa'eeda,kullum Sa'eeda cikin ce mata take suna yin signout zatazo Kebbi hutu.Haka rayuwar  Umman Sa'eeda a Kebbi ta cigaba da tafiya cikin walwala da nishaɗi,har mantawa take da rayuwar da tayi a baya,kuma koda Uncle Hassan ya tuntuɓi maganar mijinta ya take gani,ce mishi tayi ya kyaleshi sai ya dawo cikin hayyacinshi domin yanzu an riga da an mallakeshi.Wannan Kenan



        @@@@@@@@@@@@@



*ABUJA*




A ɓangaren Haj. Zulfa'u lamari dai ƙara gaba yake domin ko abinci bata ci sai irin na karnuka,duka familin Haj. Zulfa'u suka tattaru a Abujan har dasu Fadila ma tazo Abujan,saboda rashin lafiyar Haj.Zulfa'u,an fito da ita daga wannan dakin zuwa can bedroom ɗinta tare da ɗadɗaureta saboda kaima mutane cizo take tana haushi,sanda Fadila tazo ba karamin kuka tayi ba tare da tsoro saboda halin da ta same lovely grannynta mai sonta.


Family doctor ɗinsu suka kira akan yazo ya dubata amma koda yazo ya dubata sai ya ce lafiyarta lau,shi baiga abinda ke damunta ba,hasalima tama fishi cikakkiyar lafiya inda za'a dubashi,saidai ya basu shawarar a aikata Psychiartry ko matsalar daga ƙwaƙwalwa ne,haka suka bi shawararsa,nan take da nufa da ita wata babbabar asibitin kuɗi na ƙwaƙwalwa,nan ba basu dace ba saboda likitoci kusan uku ne ƙwararru suka duƙufa akanta don ganin meke damunta amma ƙwaƙwalwarta lafiya kalau take babu wata matsala,wani daga cikin likitocin ne ya ce su gwada maganin gargajiya ko zasu dace.haka suka fito daga asibitin da ita akan kujerar guragu wanda jikanta ne yake turata sai faman mutsu-mutsu take tanason ta ƙwace gashi,an rufe bakinta saboda kukan karnukan da take kar ta tara musu jama'ah,suna cikin tafiyar har zun fito daga asibitin zuwa harabar asibitin sai da wani mutum da police dog ɗinsa gabjeje dashi yazo wucewa sai idanun karen dana Haj. Zulfa'u suka sarƙafe dana junansu, ai tuni ta fizge daga daurin da aka mata tana rarrafe tare da haushi,shima karan mutumin fizge kacan da ake rike dashi yayi  tare da gudu zuwa inda Haj. Zulfa'u take yana haushi.................





*Mu haɗu a pages na gaba my Esteem Fans✍️✍️✍️🙃🙃🙃🙃*




*Ali yaga Ali,ga karan asali ga karya Haj. Zulfa'u koya zata ɓarke???*.....




*su Sadam wannan waƙa haka,shin iyayensa zasu yadda ayi auransu kafin Sa'eeda ta kammala makaranta ko kuwa???*......




*Wata Sabuwa inji ƴan caca,Malam Sauban sai yanzu aka tuno da haihuwa,shin wani irin hauka zai ɓallowa matansa???*.....




*Umma Kande har yanzu baki tuba ba,da alama sai ishara ta saula akanki kenan,koya zata kaya a next pages???*....




*Kai! Kai! Kai! Abubuwa da yawa🙃🙃🙃,amsoshinku na nan tafe a pages masu zuwa,kudai  ku cigaba da zubo ruwa comments da reactions🌹🌹💖💖🌼🌼💘💘,ni kuma bazan gaji ba wurin suburbuɗo muku new updates zafafa* 🌹🌹🙃🙃💖💖🌼🌼💘💘😂🔥🔥🔥🔥🔥




*Ina ƙaunarku My Esteem Fans Lodi Lodi* 🌼🌼💖💖🌹🌹🙃🙃💘💘




Post a Comment

0 Comments