TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Nacina ya jawo mini page 57-58

 *Daga alƙalamin* 

🖍️📚 *Narrnarhh Bukar*  📚🖍️



*Comments and share 🙏🙏🙏Fisabilillah*.



[5/22, 10:17 PM] Narnarhh Bukar: 


🏵️ *NACINA YA JAWO MIN* 🏵️





*Narrnarhh Bukar* 

( *The Amazing Pen* ✍️)



*TASKIRA WRITER'S FORUM*

*T.W.F*


*BOOK 2*




5⃣7⃣----5⃣8⃣





har ta  dauke akwatin ta ajiye zuwa wani gefen sai can zuciyarta ta kwaɗaitu da ganin maike a cikin akwatin,tana a duƙen ta buɗe akwatin turus! Tayi ganin ashe duk kyawun akwatin wata ƴar ɓaƙar kwalba ce kawai a ciki miƙewa tayi tare da kwalbar tana ƙara dubawa,tana a haka sai wani kyankyaso yayi fiffike zuwa wuyanta wanda nan take ta daka tsalle tare da *sakin kwalbar a ƙasa*  ji kake Tusssss!!! Kwalbar ta bada a ƙasa(ta fashe) wanda ko second biyar da fashewar kwalbar ba'ayi ba saiga su Umma Kande da Maman Jummalo sun shigo cikin bedroom ɗin da saurinsu saboda  tun shigowarsu gidan suka ga Nusaiba da Jummalo na faman rarrafke kaya,ai tuni hankalinsu ya tashi musamman Umma Kande da sauri suka nufi bedroom suna shiga ciki Turus! sukayi ganin Iklima ga kuma kwalbar a ƙasa  ta fashe ai kan kace me Umma Kande ta zaro idanu waje tana Kallon kwalbar, lokaci guda ta tuno da kashedin da boka Sankeru ya mata akan kwalbar kamar ana tariyo mata maganar



*"Akwai sharaɗi mai girma Umma Kande!!! Sharaɗi babba Umma Kande!!! Sharaɗin shi ne,zamu baki kwalba wanda ruhinsa ke aciki,sannan karki sake!!! Karki kibari!!! Karki yarda !!! A hir ɗinki !!! Kibari kwalbar nan ta fashe!!! Idan kuma ba haka ba asirin zai karye kuma zaki kuka da kanki Umma Kande!!! Tabbas zaki kuka da kanki!!! Sannan muma zai shafe mu, don haka dole ki kula !!! Dole ne ki kula !!! Ki kula da kwalbar kamar ruhinki Umma Kande!!! Idan ba haka ba komai naki zai rushe!!! Komai zai taɓarɓare miki Umma Kande!!! "*



Hannu biyu ta ɗora a kai tare da tsandara wani mahaukacin ihu tana cewa



" Na shiga uku ni Sarere jikar Sarkin ruwa,kwalbar ta fashe,tayi warwas a ƙasa......."


Kan ta ƙarasa maganar taga wani baƙin hayaƙi a dunƙule ya fito daga fashasshiyar kwalbar ya ɓace ɓat! Lokaci guda kuma wata guguwa mai ƙarfi ta taso  cikin gidan nasu,sai ɗibar kaya take tana tafiya dasu kasancewar har waje su Jummalo suka fito da kaya suna gogewa,Nusaiba da Jummalo da gudu suka shige ɗaki,kowa a cikinsu tsoro ya kamashi musamman Umma Kande,kusan mintuna ashirin guguwar nan nata ɗibe-ɗibe sai can ta tsaya kamar ba'a taɓa guguwar ba,guguwar na tsayawa Umma Kande ta fara kallon ƴan ɗakin😳,idan ta kalli Iklima saita tintsire da dariya,can kuma sai ta koma kallon Maman Jummalo nan ma tintsirewa da dariya tayi,haka ta koma kallon Nusaiba da Jummalo,can ta tintsire da dariya,idanu kawai suka tsura mata suna ganin ikon Allah,ana haka sai kuma ta cire gyalen da ɗankwalin nata duk a lokaci guda tana busar dariya hakan nan babu gaira dalili,falon ta fito suma suka biyota falon,sai faman dube-dube take kamar ta ajiye wani abu,can sai ta fara susar gabanta tana dariya,Iklima kasa haƙuri tayi tare da tambayi mamanta da cewa


"Mama lafiya kike dariya ke kaɗai,yanzu kuma kin fara susar gabanki kina dariya"


Mai Umma Kande zata sake yi inba dariya ba still hannunta a gabanta tana susa,saida tayi dariya ma'isarta sannan tace


"Ahhayeeeehhhh Nanayeeeee!!! lafiya! Lafiya! Lafiya! ai tana wurin Sakeruna,Sankeru nawa a'ahhh! Sankeru namu a'ahhhhh! Kai! kai! kakai! Ni Sarere ta Sankeruuuuu!!!"


Wani uban daka tsalle tayi haɗi da kama ƙugunta tana wata irin girgiza,can idanunta suka hango gwagwanin madara babba,ai da sauri ta ɗauko sai ta fara dube-dube a ɗakin su Maman Jummalo suna nan a tsayan suna ganin ikon Allah,cokali ta samu tana wata girgiza tare da cewa


"Yeeeeeh!!! Na gani! Honi! Honi! Honi! ta Sankeru"


Kiɗi ta fara tana taka rawa,can kuma da ajiye gwangwanin sai ta ɗau cokalin tana susar gabanta dashi tana dariya, sai kuma kamar an tsikareta saita ɗauki gwangwanin ta fara kiɗi tana cewa


"Ni ce Sareree!!! Gan!!! Gan!!! Ta boka Sankeru Gan!!! Gan!!! Ni ce Sarere Gan!!! Gan!!! Ta boka Sankeru Gan!!! Gan!!!"


Tana cikin kiɗin haɗi da waka saiga Abban Sa'eeda ya faɗo gidan kamar an koroshi,duk jikinshi yayi biji-biji da ƙasa




*Waiwaye*


A lokacin da wannan kwalbar ta fashe,Abban Sa'eeda na zaune a shagonsa kasancewar yanzu hatsi ya koma saidawa,suna hira da maƙocinshi tare da wani abokinshi sai kawai suka ga ya faɗi ƙasa yata murgine-murgine ga wani baƙin hayaƙi na fita daga ido,hanci,kunne da bakinsa sannan baƙin hayaƙin ya dunƙule wuri ɗaya tare da ɓatacewa ɓat! Da sauri sukayo kansu suna faɗin


"Sule lafiya! Meya sameka! Innalillahi mu kaishi asibiti"


Ya daina murgine-murginan ga miyau sai dalala yake a bakinsa yayi lamo,duk jikinshi ya sake,suna kici-kicin ɗaukarsa sai can suka ji yana magana a hankali wanda ba'a jin me yake cewa,maƙocinshi ne yakai kunnansa kusa da saitin bakinsa sannan yaji me yake cewa


"Hussainata,ƴata Sa'eeda,Hussainata,ƴata Sa'eeda"


Maimaita sunayan yakeyi babu full stop,fasa kaishi asibitin sukayi tare da taimaka mishi  ya zauna a saman bencinsa,sai faman sauke ajiyar zuciya yake akai-akai,yi yake kamar yanzu ya fara rayuwa,ada ba mutum bane sai yanzu,sachet water mai sanyi maƙocinshi ya taimaka mishi dashi,amsa yayi tare da huje ledar ya kafa a bakinsa,ji kake Ƙwal! Ƙwal! Ƙwal! Har ya shanye ruwa,wurgar da ledan yayi tare da miƙewa,maƙocinsa ya tambayi


"Sule ina zaka baka da lafiya"


"Gida zani wurin Hussainata da ƴata Sa'eeda yanzu"


"To kabari ka ƙara natsuwa mana,kaga yadda jikinka ya koma kuwa"


"Na gani,a haka zani gida wurin Hussainata da ƴata Sa'eeda"


Bai jira me makocin nasa zai faɗa ba,ya ƙara gaba da sauri har ya iso gida.



*Cikin Labari*


Yana shigowa gidan direct ya nufa ƙofarsu Umman Sa'eeda amma yajita a rufe,sai kawai ya wuce ɗakin Umma Kande,kallon Umma Kande yayi  a lokacin da ya shigo ɗakin tare da cewa 


"Ina Hussainata da ƴata Sa'eeda suka je"


Cak! Ta tsaya da kiɗin da take tare da kallonsa,cikin zaƙuwa ya sake tambayarta


"Ina Hussainata da ƴata Sa'eeda suka je"


Tintsirewa da wata mahukaciyar dariya tayi tare da cigaba da susar gabanta tana cewa


"Kwalbar ruhinka ta fashe!!! Eh-eh eh-eh eh-eh-eh!!! Kwalbar ruhinka ta fashe!!! Lala lala laa lalala!!! Kwalbar ruhinka ta fashe!!! Um-um  um-um um um-um-um!!! "


"Miye haka Saratu kina hauka ne,ina tambayarki kinamin waƙa,nace ina Hussainata da ƴata Sa'eeda"


"Suna wurin Sankerunaa!!! Nima zan je wurin Sankerunaaaa!!! Sankeru nawa kai kai!!! Sankeru namu ku-ku!!! Sankeru nasu susu!!!....."


"Haba Ƙawas ki daina wa'innan abubuwan mana sai kace wata motsattsa,tambayarki yake amma kina masa waƙa,haba don Allah ki dawo hankalinki mana"cewar Maman Jummalo


"Hankali!!! Hankali!!! Hankali!!! Ai sai wurin Sankeru!!! "


Kuka yaran suka fara ganin tabbass! mamansu hauka take ,gashi idan ta kalli wannan saita tintsire da dariya tare da susar gabanta.Abban Sa'eeda ne ya tambayi Maman Jummalo ganin ita wannan yanzu babu *Man kai* inasu Hussainata, ce masa tayi


"A gaskiya anyi watanni rabonmu dasu Umman Sa'eeda da Sa'eeda, tun ranar da Sa'eeda da wani mai kama da Ummanta Sak! suka zo a wata babbar mota,ɗaukar wani ɗan karamin akwati tayi tare dayi mana sallama nida Umma Kande akan sun bar gidan nan kenan har abada,har da ce mana a yayyafe su sun wuce"


"Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un! Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un!! Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un!!! Kuma bata sanar miki ina suka koma ba"


"Wallahi bata sanar mana ba"


"Ta sanarmin!!! Ta sanarmin!!! Lala la lalala!!! " cewar Umma Kande tana rawa


Can kuma ta wani daka tsalle haɗi da zaman ƴan bori a ƙasa ta kururuwa tana cewa


"Yiiii!!! Huhuuu!!! Ni Sarere jikar sarkin ruwa ta Sankeru, ni nama Hussaina asiriii! Na rabata na Sulaimannu!!! Na saka ruhinsa a kwalba!!! Kuma kwalbar ta fashe a gaban ɗan koli tangararasss!!! Hhhhhh!!!! Hohohohooo!!! Yihihihiii!!!"


Sai kuma ta tintsire da dariya tare da susar gabanta, can kuma ta ce


"Yaakuu Bil Adamomiiii!!! Ni ce Sarere ta Sankeruuuuu!!! Ni ce ta Sankeruuuuu !!! Ni na saka ruhin Sulaiman a kwalbaaaa! Kuma ta fashe kai kai kakai!!!! Ta fashe la la lalaa!!!"


Salati Abban Sa'eeda ya fara,cikin mamaki yake kallon Umma Kande wacca duk ta rikice lokaci guda,kasa magana ma yayi a zuciyarsa yana cewa 'Asiri Asiri Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un' can kuma ya fara magana cike da takaici


"Amma kinyi babbar asara Saratu,asiri kikamin saboda kar na kula Hussaina da ƴata Sa'eeda, Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un yanzu miye ribarki,wace riba kika samu na yin haka,gashi yanzu alhakinmu yasa kin koma mahaukaciya tuburan,Ya Salam! kuma daga yau na sakeki saki uku!!!,sai dai ki zauna don ƴaƴanki,muguwa!!! Sai Allah ya saka mana"


Fuuuuu! Ya wuce waje,yama rasa meke mai daɗi,shi babban tashin hankalinshi a yanzu baisan ina zai fara neman matarsa ba,wa zai tambaya ya Rahman! hawaye ne masu ɗumi suka kwararo a bisa kuncinsa ba tare da ya gogesu ba,zama bai ganshi ba dole ya nemi inda sahibarsa take ko'ina ne a cikin fadin duniyar nan,miƙewa yayi tare da barin unguwar ma baki ɗaya.


A cikin gida kuwa rirriƙe Umma Kande sukayi saboda sanda Abban Sa'eeda yabar ɗakin ita ma tashi tayi zata bishi,dole aka rirriƙeta saboda ba'a san ina zata tafi ba tunda yanzu ba cikin hankalinta take ba.Su Iklima suna rirriƙe da ita sai kuka suke sosai.


*Bari Mu leƙa Dajin Boka Sankeru*


A can dajin da boka Sankeru yake, mata ne suke layi a wurin Bukkarsa,wata Hajiya ce ta shiga bayan layi yazo kanta,kamar yadda idan aka shiga ciki ake masa kirari kafin ya bayyana haka itama tayi,bata karasa kirarin ba sai gashi ya bayyana kamar walƙiya,bayyana masa abinda ya kawota tayi sannan suka lula masha'arsu,suna a wannan yanayi sai kuma yayi daidai da fashewar wannan kwalbar,lokaci guda jikin boka Sankeru ya faraci da wuta tare da ita wannan Hajiyar still suna a wannan yanayin,ga wata guguwa da ta taso gadan-gadan ta turnuƙe ilahirin wurin da ƙura,bishiyoyin wurin nan take suka faraci da wuta,lokaci guda sai kuma guguwar ta tsaya Cak! Bukkar kanta ta kama da wuta,matan da suke wurin kowacce *susar gabanta ta fara* tana faɗin


"Wayyo ƙyaiƙayi!!! Wayyo ƙyaiƙayi!!! Wayyo!!! Wayyo!!! Daɗiiii!!! Ƙyaiƙayi da daɗi!!! "


Haka kowacce ta samu wuri da fara susar gabanta babu ji babu gani,ga bukkar ta ƙone ƙurmus!!! Tare da boka Sankeru da wannan Hajiyar a ciki,su kuma matan suna ta faman susar gabansu suna surutai.



*Ƙarin bayani*


Ashe duk macen da boka Sankeru ya sadu da ita ko'ina take a faɗin duniyar nan sai tayi susan gabanta saboda wasu ƙwayoyi ne yake zuba musu a lokacin da suke saduwa,kuma ƙwayoyin cuta ne,wanda a ƙarshe zasu haɗu da cutar *Cancer* a ta gabansu,domin boka Sankeru ƙazami ne,yana ɗauke da najasa iri-iri gashi kuma yana saduwa dasu.Yanzu Haka duk macen da boka Sankeru ya taɓa saduwa da ita tana nan tana susar gabanta a ko'ina take a faɗin duniyar nan.


Allah ne ya taimaki Maman Jummalo,domin ta tsarkake zuciyarta sannan ta koma ibada babu ji babu gani tare da neman gafarar Ubangijinta akan laifuffunkan da ta aikita na fili dana ɓoye,da badan wannan tuban da tayi ba da tuni tana nan tana susar gabanta haɗi da sambatu iri-iri kamar yadda matanta boka Sankeru ya sadu dasu sukeyi.Itama kanta Umma Kande susar gabanta take yi tare da hauka wanda daman hakan zata faru idan wannan kwalbar ta fashe.


*Mu dawo Gidansu Sarere ta Sankeru😂😂😂🙃🙃🙃*


Umma Kande dai hauka tuburan take,a duk minti ɗaya kamar ƙara mata ƙarfin haukan ake don yanzu yage kayan jikinta tayi tana dariya haɗi da surutai iri-iri,sai rirriƙeta ake saboda fita daga gidan take so tayi,da ƙyar suka kaita wani ɗaki wanda a lokacin bikinsu Iklima aka ginashi saboda baƙi,su duka suka rirriƙeta zuwa ɗakin saboda ciccijewan da take tare da kururuwa tana iface-iface har maƙota suna ji,kulle ɗakin sukayi da key saboda karka fito,a cikin ɗakin kuwa sai faman dukan ƙofar take tana cewa


"Kubarni naje naga Sankeruna! Kubar ni nace muku!!! Yeeeeeh!!! Ni ce Sarere ta Sankeruuuuu!!! Nice ta Sankeru!!!"


Sosai take bubbuga ƙofar tanaso a buɗe mata amma sunƙi,saima zama da kowannansu yayi,wasu suna kuka wasu tunani jimami,ko girkin dare basu ɗaura ba saboda tashin hankali gashi taƙi yin shiru.


A ɓangaren Abban Sa'eeda tunda yabar layin ya fara gararamba a garin,yanabi lungu-lungu layi-layi yana neman inda suka koma,harda Islamiyarsu Sa'eeda saida yaje ko akwai wanda yasan idan suka koma,amma kamar haɗin baki duk inda yaje sai suce basun inda suka koma ba.Haka ya gaji ya dawo gidam,ko takan ƴan gidan baibi ba ya wuce turakarsa,daman ya siyo tsiransa da maltinarsa da gora,tas! Ya cin namansa tare da kora maltinarsa mai sanyi ya kwanta,tsaƙa da warwara ya fara gami da tunanin ina zai fara neman Sahibarshi da ƴarshi wacca tafi soyuwa a garesa a duk yaransa,haka ya cigaba da tunani har ɓarawo bacci ya sureshi ba tare da ya sani ba.


Tun daga ranar Umma Kande ta koma zama cikin wannan ɗakin ba tare da an ɓudeta ba,abinci ma ta dubara ake bata saboda karka fito,a ciki take kashi take fitsari,sai idan anyi kwana biyu suke taron dangi, wasu su riketa wasu kuma su wanke ɗakin,shi kuma Abban Sa'eeda yana nan ya nemansu Umman Sa'eeda ko Allah zaisa ya gansu.Wannan kenan


*TUNATARWA*



*Ƙarshan tika-tiki-tik!!! Daman hausawa  sunce idan zaka gina ramin mugunta,to ka ginashi ƙadan saboda wataran kai zata faɗa. Yau dai ga Umma Kande ta faɗa ramin da ta gina,ba tare da ta ankara ba,haka kuma hausawa suna cewa Shi sharri ɗan aike ne,duk inda yaje wata rana sai ya dawowa mai shi,yau ga sharrin da Umma Kande ta aika ya dawo mata ba tare da tasan da dawowarsa ba.Ƴan Uwana mata gadai misali nan agareku akan Umma Kande mai zuwa wurin boka,kunga irin nata ƙarshan,kai bama ita ba har da wa'inda suke zuwa wurin boka Sankeru nasu ƙarshan yazo domin kuwa kowaccansu sai ciwon daji ya sameta saboda saduwar da boka Sankeru yakeyi dasu.Shin bakwa tunanin akwai ire-iren mata masu hali irin na Umma Kande, sannan kuma suna zuwa wurin bokaye da malam tsubbu suna saduwa dasu duk don buƙatarsu ta biya* ( *Wa'iyazubillah😞😞😞* )*


*Allah ka tsaremu daga hali irin nasu Umma Kande, kasa mufi ƙarfin zuciyoyinmu,ka tsare mana imaninmu,kasa muyi kyakkyawan ƙarshe*



        @@@@@@@@@@@@



*KEBBI*


A ɓangaren Umman Sa'eeda kuwa rayuwa tana tafiyar mata cikin kwanciyar hankali da annashuwa,babu hayaniya balle haya-gaga,saidai ta ci,ta sha,tayi kallo ko kuma suyi hira da Momin Sadam kasancewar taƙi barinta ta koma family house,sannan gidan da Uncle Hassan ya siyan mata shima ta hanata komawa wai sai bayan bikimsu Sadam,dukiyar da ta samu na gadon mahaifinta tuni Uncle Hassan ya amsa tare da cigaba tafiyar mata da dukiyar ta hanyar kasuwanci dasu wanda ribar direct take shigo mata cikin account ɗinta.


Bayan Sa'eeda ta kammala final exams dinta tare da celebration sannan sukayi project defence sai ta tattaro ƴan komatsanta zuwa Kebbi wurin Ummanta.Zuwanta Kebbi da kwana biyu Sadam ya dawo daga tafiyar da yayi zuwa Ghana shida Mukhtar P.A ɗinsa don harkar wani kasuwanci da suka fara a can.


Farkon zuwan Sa'eeda gidan,kunyar Momin Sadam ta fara sai Momin Sadam ta ce mata ta daina wannan kunyar domin ita a matsayin ƴarta ta ɗauke ba wai suruka ba,sai a sannan ne ta rage kunyarta,shi kuma Sadam babu ruwanshi,ko'ina  nuna soyayyar Sa'eeda yake koda suna gaban iyayen ma,saidai ita taji kunya amma shi ko a kwalar rigansa.


Umman Sa'eeda da Sa'eeda suna ɗakinsu wanda aka ba Umman Sa'eeda ta zauna suna hira sai can Sa'eeda ta ce


"Ummina Baba da Gwaggo Ladi ta ƙauyan Damari suna nan har yanzu kuwa"


"Ƴar albarkha abinda ke raina kenan wallahi,inaso nayi ma Kawunki maganar ya kamata muje ƙauyan Damari har dashi yaga wa'inda suka taimake mu"


"Hakane Ummina,a gaskiya ya kamata,har dani za'ayi tafiyar domin na kashe ma idanuna ƙwarƙwata"


"Ki kashema idanunki ƙwarƙwata kuma,nami kenan" cewar Umman Sa'eeda


"Na yadda zaku kaya da Gwaggo Ladi,ba ta ce baki da asali ba,har tana cewa  tsintsacciyar mage  bata taɓa zamowa mage,to yanzu kuma fa ai nasan sai baƙin ciki ya kusa kaita barzagu"


"Ooohni Hussaina yaushe Sa'eeda kika koma haka,a ina kika koya surutu ne haka kamar zuban ruwan fanfo,Uwar tawa kike cema ta kusa tafiya barzagu"


"Allah ya tsareki da zamowa ɗiyarta,nifa tunda na shiga gidan haka nan naji tsohuwar batamin ba,ashe batason Ummina ne shiyasa zuciyata bata sonta"


"Sa'eeda! Sa'eeda! Sa'eeda! "


"Na'aam my Everlasting mom"


"Allah ya shiryeki da surutai"


"Ameeen Ummina ta kainaa"


"Yawwa na tuna,kafin bikinku zamuje Hajji nida ke da Aunty Ruƙayya in shaa Allah"


"Alhamdulillahi! kai! kai! kai! maa shaa Allah! Wa yaga Sa'eedar Ummi a ɗakin Allah, wayyo daɗi! Allah ya kaimu rai da lafiya"


"Ameen ya Rahman"


Shiru ɗakin yayi sai can Sa'eeda ta ce


"Ummina kina jin ɗuriyar Abbana kuwa"


Ras! Ƙirjin Umman Sa'eeda ya bada saboda tuno mata da mijinta wanda har yanzu bata manta dashi ba a cikin zuciyarta kusan kullum zai tayi tunaninsa,batasan wani hali yake ciki ba duk da tasan an riga da an mallake zuciyarsa amma har yanzu bata cire rai  da dawowar hankalinsa garesu ba,ƙarin daɗi bayan Sauke faralinsu harda adduar Allah ya maido da hankalinsa garesu zatayi don har yanzu tana son mijinta,katse mata tunani Sa'eeda tayi da cewa


"I'm sorry Ummina tunda bakya so bazan sake ba"


Ashe hawaye ne suka gangaro bisa kuncin Umman Sa'eeda ba tare da ita kanta Umman Sa'eedar ta sani ba,girgiza mata kai tayi da cewa


"A'ahhh Sanyin idaniyata kawai ina tunanin halin da Abbanki yake ciki ne duk da nasan hankalinsa ba'a jikinsa yake ba har yanzu"


"Kenan ba Abbana yayi jagoran aurena ba"


"Eh Sa'eeda, kawunki ya sanarmin da cin kashin da yayi muku a bainar jama'a,shiyasa kawai yace shi zaiyi walicci tunda koda anje wurinsa maganar auranki ba kulasu zaiyi ba,shiyasa basu je wurinsa ba"


"Hmmmm a gaskiya Abba yana cikin matsala,tausayinsa nake saboda ba laifinsa bane,laifin wa'innan shayɗanun ne"


"A'a Sa'eeda daina kiransu da shayɗanu,kiyi musu fatan shiriya,domin shi suke buƙata a yanzu"


"Allah ya shiryesu yasa su dawo kan hanyar Allah da manzonsa"


"Ameen ya Rahman"


Haka suka cigaba da hirar cikin farin ciki da annashuwa,babu wata matsala a tattare dasu.


Washe gari da safe bayan kowa ya gama break fast har da Sadam,suna zaune a main falo harda Daddyn Sadam suna hira,Sa'eeda kuma tana kusa da Momin Sadam, sai Sadam ya  yazo kusa da Mom ya cewa cikin shagwaɓa


"A gaskiya Mom kin daina sona"


"Ni!!! Na isa na daina son Autana"


Ƙara kumbure fuska yayi tare da

cewa


"Ba gashi ba,tunda Sa'eeda tazo gidan nan kika daina sona "


Ba Momin Sadam kaɗai ba harta da sauran ƴan ɗakin dariya suka tintsire dashi,oganiyya Sa'eeda har da ita a masu yi mishi dariya har da gwalo tayi masa,shi kuma ƙara ɗaure fuska yayi yana cilla mata harara irin zamu haɗu ɗin nan,saida sukayi dariya son ransu,sannan Umman Sa'eeda ta ce


"Barta kawai Sadam ɗina,dawo wurina,nima na yaye Sa'eedar suje can su ƙarata,zon nan ɗana na kaina"


Murmushi yayi tare dayi ma Sa'eeda gwalo irin yadda tayi masa sannan ya koma wurin da Umman Sa'eeda take,Dad ne yace


"Auta da kishi,yanzu miye a ciki don daughter da gajema mazauninka wurin Mominka,Allah ya kyauta"


"Barshi kawai,naji daɗin wannan musayar da akayi,ni daman can manage nike dashi,tunda yanzu na samu ƴar maceta kyakkyawa,kuje ku ƙarata"


"Mom!!! Daman managi kike dani,wayyo ni Sadam autan Aunty Hussaina"


Wata sabuwar dariya a kwalinta suka buɗe,ji kake  Ƙya! Ƙya! Ƙya! Babu ji babu gani,Sadam da shirme wani lokacin,idan kuma a waje ne ya Rahman! zaka sameshi very serious and quiet.


Haka su Sa'eeda da Sadam suka cigaba da gudanar da soyayyarsu mai tsafta,idan Sadam yana gidan baya cin abinci kowa sai wanda Sa'eeda ta girka da hannunta ko abinci Mom ya daɗe da Sallama dashi.(Oh ni Indo,tun kan ayi auran har ka fara kwasa romon girkin Sa'eeda, kai mai yawo koh,to mun ganoka wallah😂😂😂🙃🙃🙃) 



Umman Sa'eeda tayi ma Uncle Hassan maganar zuwansu ƙauyan Damari kuma ya amince tare dashi za'a je domin mika godiya ga wannan ahalin da suka taimake Mamansa da ƴar uwarsa.Fixing ranar zuwa ƙauyan sukayi harda Momin Sadam a tawagar ƴan tafiya.(Baba kaɗai za'a yima godiya banda su O'ooo wato Gwaggo Ladi😏😏😏)



Mota uku suka yi tafiyar dasu ,su Momin Sadam sunzo da biyu daga Kebbi wanda ɗaya suna ciki ɗayan motan bodyguards ɗin sune ciki,direct gidan Uncle Hassan suka yada zango,sai washe garin ranar suka kama hanyar zuwa *ƙauyan Damari*  Wannan kenan




             @@@@@@@@@@@



*ƘAUYAN DAMARI*



Kasancewar da sassafe suka doshi ƙauyan,da wuri suka isa garin,direct motocin suka nufi unguwansu Baba,gidan har yanzu yana nan a yadda yake kamar shekarun baya,fitowa sukayi dukkaninsu daga motar,Sa'eeda sai kalle-kalle take tana ƙara duba unguwar da kyau ganin babu wani canji,suna a tsaye ne saiga wani tsoho yana tafiya da sanda zai shiga gidan ba tare daya lura dasu ba Umman Sa'eeda tayi saurin cewa



"Baba"


Da sauri ya juyo jin muryar da baiza taɓa mantawa da ita ba,muryar wacca yake tunaninta kusan kullum,kasancewar yasan da wuya ta dawo garin saboda matarsa,cikin muryar tsufa ya fara magana



"Hussainata ashe zaki zo gareni,ashe zaki dawo gareni"


Kowa a wurin saida yaji tausayin Baba,gashi ya tsufa amma har yanzu yana fita,Umman Sa'eeda ta ce



"Eh Baba na dawo gareka tare da ahalina"



"Da gaske Hussaina, kin sadu da ahalinki,da gaske Hussaina"



"Eh Baba"



"Ku shigo ciki,bara na aika a kira Mairo yanzu nan"



Haka su Umman Sa'eeda, Momin Sadam da Sa'eeda suka shiga ciki,sai Uncle Hassan ya jira,idan an mishi iso sai ya shiga ciki.Da Sallama suka shiga cikin gidan bayan Baba shima yayi tashi sallamar,wata tsohuwa ce tana zaune a bisa tabarmarta,radio na kusa da ita tana jin kanun labarai taji Sallama har sau biyu,dana mijinta da kuma muryoyin wasu,to suwaye haka da yawa gashi bata san wa'innan muryoyin ba,tana cikin wannan tunani wata Sallamar ta sake shiga cikin dodon kunnanta,da sauri ta ce cikin muryar tsufa



"Umm umm Wa'alaikumussalamu,sannunku da zuwa"


Miƙewa tayi tare dayi musu sannu da zuwa,ai karab! Gwaggo Ladi tayi ido biyu da Umman Sa'eeda tuni annurin fuskarta da ɗauke,cikin masifa Gwaggo Ladi ta ce



"Meya kawoki gidan nan tsintacciyar mage,marar asali,ƴar kwararo,mai kalan dangi........"



Bata ƙasara maganar da tayi niyya ba Baba ya daka mata wata uwar tsawa wanda har jikinsa saida ya girgiza saboda tsufan da yayi,cike da ɓacin rai ya fara magana



"Wai ke yaushe zakiyi hankali da tunani ne,mutane ko zama basuyi ba,kin fara zazzaga musu masifarki haba don Allah,to buɗe kunnuwanki dakyau ciki,Hussaina Allah ya haɗata da asalinta,tare dasu take,gorin rashin asalin da kike yi mata sai ki jiƙa ki sha"


Dammm!!! Darammmm!!! Dadammmm!!! Haka ƙirjin Gwaggo Ladi ya bada,lokaci guda ta dafe ƙirjinta tare da waro ƙananun idanunta waje tana cewa...............





*Mu haɗu a pages na gaba domin cigaba da jin wannan chakwakiyar🙃🙃🙃✍️✍️✍️💘💘💘💘🌼🌼🌼*





*A'ahhh Gwaggo Ladi yada dafe ƙirji😏,ko mai za'a ce???*....



*Su Umma Kande an fara girbar abinda aka shuka,ko zata cigaba da kasancewa a haukan???*....


*Wayyo Abban Sa'eeda kana shan wuya,shin kuna tunanin zaiga su Umman Sa'eeda nan kusa ko kuwa???*........


*Kai! Kai! Kai! Abubuwa da yawa🙃🙃🙃,amsoshinku na nan tafe a pages masu zuwa,kudai  ku cigaba da zubo ruwa comments da reactions🌹🌹💖💖🌼🌼💘💘,ni kuma bazan gaji ba wurin suburbuɗo muku new updates zafafa* 🌹🌹🙃🙃💖💖🌼🌼💘💘😂🔥🔥🔥🔥🔥


*Ina ƙaunarku My Esteem Fans Lodi Lodi* 🌼🌼💖💖🌹🌹🙃🙃💘💘




Post a Comment

0 Comments