TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Zabin mahaifina page 19-21

 🌳🌳UMMU AFFAN🌳🌳


[01/02, 21:02] Halimatu Sadiya Affa Fbk: 🌳🌳🌳🌳🌳

      ZAB'IN MAHAIFINA

        🌳🌳🌳🌳🌳


Written by SADIYA ALHASSAN (Ummu Affan)


    🌐HAJOW 📝🌐


🌐👩‍👧‍👧👩‍👧‍👧👩‍👧‍👧HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS ✍🏾✍🏾✍🏾🌐


Dedicated to PRINCESS ESHAT AYSM

AYSHA BICHIKI


Page 19



Wannan page d'in nakine takwarata Sadiya Abubakar ina yinki irin sosai d'innan ALLAh ya barmu tare k'awata❤💓❣💕💞


Suna isa bakin mota hajiya ta mik'ama salma emvelop d'in da Alh. Abdul-razak ya bata, sannan tace ki dinga yin girkin ki da kanki karki yadda akawo miki wani abu kici,zuwa gobe zan turo miki da yarinya wanda zata rik'a yi miki aiki, Cikin girmamawa salma ta amsa sukayi sallama hajia halimat ta shiga mota driver yaja suka tafi,salma kuma ta juya ta shiga ciki tana shiga ta wuce d'akinta ko kallon A.A dake zaune a falon batayi ba.


                      Ita kuma humaira tana shiga d'akinta ta fashe da kuka tana tsinema hajia halimat.  "Wlh bazai tab'a yuwuwa ba koda zanyi yawo tsirara se yarinyarnan tabar gidannan, wata zuciyar tace kin manta tace idan har ya saketa kema zakibar gidan. tsaki tayi tace aikuwa da alama ajalinta yazo dan kuwa bazan tab'a bari ta zauna min a cikin gidana ba. (kuji fa jama'a kamar ita ta gina gidan da kud'inta😃😃😃)


Waya ta d'auko tayi dialing wani number,  can aka d'auka hellow humy kina lafiya? aka fad'a daga d'aya b'angaren, ina fa lafiya lina wancan shegiyar tsohuwan yanzunnan tabar gidannan, wata tsohuwa? lina ta tambaya.


                   Mahaifiyar Abdul mana, to me tazoyi? lina ta sake tambaya. Waita kawo masa amarya, wani uban ashar lina ta sake sannan tace ki jirani ganinan zuwa wallahi seta raina kanta. To kiyi sauri dan ALLAh humaira tace sannan ta kashe wayarta.


ta nemi bakin gado ta zauna, bata dad'e dazama  ba lina ta shigo cikin d'amammun kaya riga da wando, kanta ba ko d'an kwali se wani siririn gyale data yafa a kafad'a.

      

        tana shiga suka rungume juna, ke ina amaryan take? lina ta tambaya, tana d'akinta, to tashi muje muci uwarta, zatasan ta shigo gidan bala'i. Basu sami A.A a falon ba da alama ya bar gidan.


              ko neman izini basuyi ba suka cusa kai cikin falon salma, salma tana zaune ta sake wanka ta had'e cikin riga da skert na atamfa, d'inkin ya kamata ya fiddo da shape d'inta, kanta ba d'an kwali se gashinta da tayi parking wanda yasha gyara ya sauk'o mata har gadon bayanta.


Plat ne a hannunta tana cin abinci da alama girki tayi. ba humaira ba hatta da lina se da ta raina kwalliyarta dan humaira irin siraran matannan ne wanda basu da k'iba ko kad'an se dai kyau a fuska, dama dama lina tana k'iba se dai bata da shape ko kad'an, sukub take kamar namiji. 


            kallo d'aya tayi musu ta d'auke kanta kamar bata san da mutane a wajenba. Kallon juna su humaira sukayi da alama wannan ba kamar wanda aka saba kawo musu bane.


Lina ce tayi k'arfin halin zuwa ta tsaya akan salma tace ke inason yanzu-yanzu ki tattara kayanki kibar gidannan, in har kina son tsira da ranki da kuma lafiyar ki.


                    Kallonta salma tayi up and dawn  sannan tace a matsayinki nawa kike bani umurni? mijina ko iyayena ne kad'ai suke da ikon bani umurni nabi amma ba ke ba. 


              ke barima kiji ko megidannan duk da zaman shi nakeyi to shima be isa yace nabar gidannan ba.


shi me gidan be fad'a miki cewa nice nake da iko da gidan da abinda yake cikinta ba? ko shi a k'ark'ashin ikona yake kinga kuwa se yanda nayi dashi, humaira ta fad'a tana k'arasowa cikin falon.


Murmushi salma tayi tace idan su kina iko dasu to nikam baki isa kiyi iko dani ba wallahi dan nafi k'arfinki.


           Nunata humaira tayi da yatsa tace wallahi ke baki isa kizo har gidana kice zaki yimin rashin kunya ba, kodan kinga tun farko na k'yaleki banyi maganin ki ba, to ki kiyaye harshen ki tun kafin ki had'u da mummunan sakamako.   


Mik'ewa salma tayi tace don't point your pinger at me or else... "me zaki iyayi? humaira ta katseta tana huci"


             Duk randa kika sake nuna min yatsa wallahi sena karyashi, kuma da kike cewa ina miki rashin kunya ai kece baki rik'e girman ki ba. kuma baki isa kiyimin komaiba se abinda ALLAh ya k'addaro min. sannan ta nuna musu kofa, ku fice min daga falo yanzu ko kuma na nuna miki abinda zan'iyayi yanzu.


           Tsaki humaira tayi tace wallahi salma se naga bayanki ki rubuta ki ajiye dan ni kad'ai akayi Abdul kuma dani kad'ai zeyi tarayya babu wata 'ya macen da ta isa ta zauna a matsayin matar sa bayan ni, sannan ta ruk'o hannun lina wanda ta kasa magana  suka bar falon dan taga alamar salma bata da mutunci.


            suna fita salma taje tasama kofarta key ta dawo ta zauna taci gaba dacin abincinta,tana mamakin kanta yanda ta iya sa'insa da humaira ba tare da taji tsoronta ba abinda bata tab'ayi ba. lallai idan kaga mutum baya magana to ba'a tab'o shi bane ta fad'a a fili.


Daki suka koma lina ta kalli humaira tace lallai humy wallahi sekin tashi tsaye,dan naga yarinyar nan ba kamar wad'ancan bane dan bata da tsoro da alama ta taki wani abu.


               Ajiyar zuciya humaira tayi, tace lina banci ta zama ba, yanzu zamu tafi wajen boka me gani har hanji, idan nayi sake yarinyar nan zata rusamin budget, kin dai san dalilin da yasa na auri Abdul bawai dan tsananin k'aunar sa bane kawai dan dukiyar sa ce.Wannan ne dalilin da yasa nake zubar da ciki idan na samu, k'arshe zuwa nayi aka fitar da mahaifar saboda bana buk'atar haihuwa balle idan ya mutu d'an ya gajeshi.


shiyasa nake son nasashi ya rubuta sunana a dukkan kadarorinsa kafin na aikashi zuwa lahira.


                ihu lina tasa irin nasu na 'yan bariki tace shiyasa kike burgeni k'awata, dan bakya wasa da hanyar samun kud'i. yanzu ki tashi mu tafi wajen bokannan dan kinsan masu iya magana sunce da zafl-zafi akan bugi k'arfe,kuma ba'a bori da sanyin jiki. 


tashi humaira tayi ta d'auko gyalenta ta yafa ba wanda zai ganta yayi zaton matan aure ce. Wata benz arsh colour naga sun shiga, da k'arfi ta danna horn cikin hanzari me gadi yazo ya bud'e mata get da mugun gudu ta fita dan kad'an ya rage ta take masa k'afa, girgiza kai yayi yana yi masu fatan shiriya.


Jin fitan motane yasa salma ta fito ta kawowa me gadi sauran abincin data dafa, har k'asa mallam musa ya durk'usa yana yi mata godiya, dan tunda ya fara aiki a gidan ba'a tab'a bashi abinci ba se dai a kawo masa daga gida.







readers ina son na dena posting har sena gama typing nayi muku gaba d'aya amma menene ra'ayin ku???? ina jiran amsoshin ku.



🌳🌳UMMU AFFAN🌳🌳

[01/02, 21:03] Halimatu Sadiya Affa Fbk: 🌳🌳🌳🌳🌳

      ZAB'IN MAHAIFINA

        🌳🌳🌳🌳🌳


Written by SADIYA ALHASSAN (Ummu Affan)


    🌐HAJOW 📝🌐


🌐👩‍👧‍👧👩‍👧‍👧👩‍👧‍👧HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS ✍🏾✍🏾✍🏾🌐


Dedicated to PRINCESS ESHAT AYSM

AYSHA BICHIKI


Page 20


Wannan page d'in nakine ne my daughter(hapsert bnt hassan Ameen) kinfi kowa son novel d'innan😃😃😃 ina yinki irin sosai d'innan❤



Wani k'ungurmin jeji naga humaira sun shiga, ba gida ko daya a wajen, tun a bakin jejin suka ajiye motarsu, da k'afa suke takawa ga uban nisa.  A can na hango wani bukka  wanda shi kad'aine a wajen, suna k'arasawa sukaji an daka musu tsawa, saida suka firgita, karku yadda ku k'araso ku tsaya daga wajen da kuke, saboda sarkin aljanu da mutanensa suna zaune a wajen, meke tafe daku???


                   Cikin rawan murya humaira ta fara magana, dama akan maganar kishiyar da aka min ne. Me kike so ayi mata?? bokan ya tambayeta wanda basa ganin shi sai dai suji muryar sa.  Ina so a bani maganin da zai zamo ajalinta. Bushewa yayi da dariya wanda saida jejin ya amsa, yace ke humaira lallai yanzu na tabbatar baki da iyami, tabbas irinku muke buk'ata. Amma zan fad'a miki gaskiya wannan yarinyar idan bakiyi da gaske ba ita ce silar tonuwar asirinki.


               Aljanun mu baza su iya zuwa kusa da ita ba, saboda jikinta akwai tsari, kuma tana yawan addu'a bata zama babu alwala, aikinki akwai tsada.


Cikin sauri tace boka kasan kud'i ba matsalata ba ce,ko nawa ne zan biya. Zaki bada dubu d'ari biyar,aciki za'a siyama sarkin aljanu bak'ar saniya da bak'ar tinkiya, da bakin bunsuru da bakin zakara, za'a yanka mishi saboda jinin yake buk'ata.


               Da hanzari humaira ta ciro kud'in ta ajiye a wajen. tana ajiyewa aka wurgo musu k'ullin magani. Ki d'auki wannan maganin kisa mata a abinci, ki tabbatar  taci, dan iya abinda zamu iya yi miki kenan, danko kusa da ita bazamu iya zuwa ba,  wannan ne temakon da zamu iya baki.


sunkuyawa humaira tayi ta d'auka, sannan suka fara tafiya da baya da baya, har saida suka dena hango bukkar tukunna suka juya, dan haka dokar bokan take.


K'arasawa sukayi wajen motar su suka shiga suka tafi. A hanya humaira ta kalli lina tace, nifa bansan ta yaya zan saka mata maganin nan a cikin abinci ba, dan nasan ko na bata abu baci zatayi ba.


Amma humy har yanzu kwakwalwar ki bata ja wallahi. ina ce mijin a hannun ki yake? kuma kinsan se abinda kika tsara masa yake yi, gyad'a kai humaira tayi.


to yanzuma haka zakiyi, kawo kunnen ki kiji,gani nayi lina ta fad'a mata wani magana sukayi dariya suka tafa, ko me tace mata oho.


                Bayan sun koma gida suka shige bedroom suka rufo k'ofar, direct kan bed suka nufa tun kafin su k'arasa naga sun fara shafa junansu.


                A'UZUBILLAHI. Abinda na furta kenan, dama su 'yan lesbian ne? A guje na juya na bar musu d'akin ina nema musu shiriya,


Bayan sun gama watsewar su, lina ta fito ta tafi tana jaddadawa humaira akan tasan yanda zatayi ta bata maganin taci


MENENE DANGANTAKAR LINA DA HUMAIRA??? 



Humaira sun had'u da lina ne a wajen party, asalin lina bayarbiya ce amma ba musulma ba ce.


tun tashin lina yarinya ce hatsabibiya tun wana k'aramar ta take bin maza, data girma ta zama budurwa ne idanunta suka dad'a bud'ewa, daga k'arshe tattarawa tayi tabar garinsu OYO  ta biyo saurayinta suka zo BAUCHI.


Tunda tazo ta bud'e bariki kala-kala ba iya bin maza ta tsaya ba, hatta hajiyoyi d'aukanta sukeyi


sun had'u da humaira ne a wajen birthday partyn da saurayinta ya had'a mata, tun daga lokacin suka k'ulla k'awance, ita ta koyama humaira lesbian da bin bokaye,(ALLAh ka had'amu da k'awaye nagari AMEEN🙏🙏)


Da daddare bayan A.A ya dawo yana zaune a falo, humaira ta fito cikin shigar riga da skert english wears, sun kamata se dai ko kadan basuyi mata kyauba, kasancewarta siririyar mace da bata da shape ko kad'an, se tayi kamar an d'aura wa muciya zani.😜😜


                      Kusa dashi tazo ta zauna tana mishi barka da dawowa kamar ba abinda ya faru(duk plan d'in lina ne). Ya amsa mata cikin jin dad'i, saboda shima fargaba ce ta hana shi dawowa gidan tun da ya fita da safe.


tace mishi su tashi suje suci abinci, wanda me aikinta blessing ta girka ta jera akan dining table. mik'ewa yayi suka nufi kan dining d'in, bayan sun kammala cin abincin suka dawo falon suka ci gaba da hiransu suna kallo kamar yanda suka saba.



Humaira ne ta dubi A.A tace babyna daman akwai maganar da nake son muyi dakai, ina jinki ya amsa mata ba tare daya kalle ta ba.('yan mulkin sun juyo kanta kenan).


                Naga har yanzu baka kirata ka fada mata yanda tsarin gidan nan yake ba. Kallonta yayi sannan yace wani tsari kenan??? had'e rai tayi tace ina so ne ka fad'a mata duk wacce take da girki ta fito a dinga cin abinci tare da ita, ban yarda kowa ta dinga yin nata ba.


kauda kanshi yayi cikin jinkai yace kije ki kirata, tashi humaira tayi ta nufi part d'in salma.


k'wank'wasa k'ofar tayi, salma dake zaune tana kallon tashar Arewa 24 ta taso ta bud'e k'ofar, tana ganin humaira ta b'ata fuska tace lafiya?



murmushin mugunta humaira tayi, tace "kizo mijina yana kiranki" ta juya tayi tafiyarta. d'an tsaki salma taja tace da wayace ba mijinki bane? (ina fatan salma ba haushi kikaji ba😃😃) juyawa tayi ta Koma cikin daki ta dad'a gyara fuskarta ta fesa turare me dad'in k'amshi, ko hijab bata d'auka ba ta nufi falon da suke.


                   Tunda ta doso wajen yake binta da kallo, kasancewar kayan baccine a jikinta riga da wando cotton, sun kamata tsam rigan me hannun shimi ne, wandon a iya guiwa ya tsaya mata, ta saka hulan turban kalan kayan pink.


tana zuwa ta nemi waje ta zauna ba tare data ce musu komai ba, humaira da tun fitowar salma tayi dana sanin kiranta da tace ayi ganin irin kallon da A.A yake mata. Gashi ba daman tayi magana kar plan d'inta yargaje🤣🤣🤣🤣



Ta wurga ma salma harara sannan ta juya ta kalli A.A daya maida hankalinsa ga kallon t.v ta daure tace "babyna gatanan ta fito ka fad'a mata" beko kalle ta ba yace ki fad'a mata mana tunda tsarinki ne hakan.


Da sauri ta dube shi jin tana mishi magana yana bata amsa wani iri. wai meke faruwa ne kodai asirin da namishi ya fara warwarewa ne? daga zuwan ta komai ya fara warware wa, aikuwa zanyi saurin aikata lahira tun kafin komai ya kmab'e min, tayi maganar cikin zuciyarta.


duban salma tayi dakanta yake kallon wani gefe na falon tace "to amarya dama maganar girki ne, kinsan hajiya tace yayi miki kwana 7 d'inki kafin araba kwana bibbiyu. saboda haka yanzu duk wacce take da girki zata fito a had'u a dinga cin abinci tare. Akwai wacce take yi mana girki, ina fatan ba matsala?" ta k'arasa tana murmushin yak'e



mamaki ne ya kama salma,tabbas akwai abinda take shiryawa dan tasan ruma baya tsami banza, ita zata nuna ma kirsa? wato dan tana gaban mijinta shine zata nuna ita na ALLAh ne, aikuma zata nuna mata itama macece tana da irin nata salon.


               Murmushi salma tayi tace "haba Aunty ai duk abinda kika yanke dai-dai ne, amma ni inso samune nafison na dinga yima mijina abinci, dan banason masu aiki su dinga yima mijina hidima.....


Tun kan salma ta k'arasa humaira tayi saurin katseta, ganin tana neman wargaza mata plan. tace"haba k'anwata kamar ke kina auren Alh. A.A me dala ace kina girki da kanki. ai wannan abin kunya ne a gare mu.


girgiza kai salma tayi tace ba abin kunya bane Aunty tunda aikin ladane kuma wa mijina zan yima, ni inaga ai ba lefi aciki.


A.A da yake kallon news a t.v amma hankalinsa yana wajensu,yana jin maganganun da sukeyi, ya juyo ya kalli humaira yace "tunda tace zata iya ki rabu da ita mana, kun cika min kunne da surutunku, kun hana na fahimci abinda ake fad'a a news d'in. Yana maganar yana satan kallon salma da take jifansa da murmushi duk dan ta k'ular da humaira.



humaira da ranta ya gama b'aci ta kalle shi ta fara magana ta ma manta da batun wani plan tace "wallahi duk abinda na tsara shi za'abi, koka manta haka akeyi aduk lokacin da kayi aure? kaine ka bani damar tsara duk yanda nake so dan haka yanzuma haka nake buk'atar ayi.



kallonta salma tayi tana murmushi tace "Aunty menene abin d'aga hankali anan? kawai dan zan dinga yima mijina hidima ai ba wani abu bane.... 



Keee!... Badake nake yiba da wanda ya ajiyeki nake magana. humaira ta fad'a tana huci kamar kububuwa


Look humaira kinsan fa ban cika son hayaniya ba, please kowa ta tafi d'akinta banson tashin hankali.



Mik'ewa salma tayi fuskarta cike da murmushi ta wuce d'akinta. itama humaira tashi tayi ta dube shi tace, "Abdul nika wulak'anta a gaban wancan banzan ko? to wallahi se nayi maganinku daga kai har ita. ta wuce shi ta shige d'aki" 


Tsaki yaja ya kashe kallon ya nufi d'akin salma, hakanan yake jin ya rage tsoron humaira yana ganin yanzu bazai d'auki rashin mutuncin ta ba.    


kuyi hakuri da wannan wallahi har nayi ya goge.


Readers naji k'orafin ku zan dingayi kullum insha ALLAhu, wanda ba'abi ra'ayin ku ba ina me baku hak'uri.



🌳🌳UMMU AFFAN🌳🌳

[01/02, 21:03] Halimatu Sadiya Affa Fbk: 🌳🌳🌳🌳🌳

      ZAB'IN MAHAIFINA

        🌳🌳🌳🌳🌳


Written by SADIYA ALHASSAN (Ummu Affan)


    🌐HAJOW 📝🌐


🌐👩‍👧‍👧👩‍👧‍👧👩‍👧‍👧HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS ✍🏾✍🏾✍🏾🌐


Dedicated to PRINCESS ESHAT AYSM

AYSHA BICHIKI


Page 21


Sistr eyshert Aysm ina miki murna da fara sabon novel d'inki (WAZAN SO) ALLAh ya k'ara d'aukaka,yanda kika fara lafiya ALLAh yasa ki gama lafiya. Inayin ki sistr irin sosai d'innan.😘



Akashe ya samu wutan falon amma yana iya hango d'an haske ta cikin bedroom d'in. Sallama yayi sannan ya shiga d'akin a kwance ya sameta ta bama k'ofar baya, tayi nisa a tunani da alama batasan mutum ya shigo d'akin ba.


Gefenta yaje ya kwanta ya juya mata baya,sannan yaja bargo ya lullube jikinsa. ya kashe bedsite lamp dake gefenshi, se a lokacin salma tasan ya shigo d'akin. Cikin sauri ta mik'e zaune ta ce mallam lafiya zaka shigo min d'aki ba ko sallama,


                   Ko juyowa beyiba bare ya nuna yasan tana magana. duk da haka batayi shiru ba, gaskiya ka tashi ka koma d'ayan d'akin dan ni bansa ba kwana da wani namiji a cikin d'aki d'aya ba.



Batare daya juyo ba ya fara magana "Nan gidana ne ina da ikon shiga duk inda naso a kowani lokaci, kuma ya kamata kisan banbancin dake tsakanin da da kuma yanzu, ki iya bakinki saboda yanzu a k'ark'ashin iko na kike, ba k'ark'ashin ikon iyayenki ba. Agidana kike ba gidanku naje ba.



Shiru salma tayi batare da ta sake cewa komai ba ta mik'e domin ta koma d'ayan d'akin. Muryar shi taji yana bata umurni koma ki kwanta, dan ni bana raba makwanci da matata ki kiyaye ko saboda gaba, komawa salma tayi ta kwanta amma ta gagara runtsawa saboda fargaba da rashin sabo, ga sanyi da takeji.


Shima ba baccin yakeyi ba, tunani ne ya cika kwakwalwar sa, ya rasa me yake damunsa ga wani feeling dayake ji wanda be tab'a jin irinsa akan wata 'ya mace ba.


Sauk'ar numfashinta yaji abayansa alamar bacci ya d'auketa, juyowa yayi yana kallonta tana baccinta cikin kwanciyar hankali, ta dunk'ule jikinta waje d'aya. Tsintar kansa yayi da rungumota zuwa jikin sa, a tare suka sauk'e ajiyar zuciya, itakam cikin bacci ne ba tare datasani ba, yayin dashi kuma najin dad'in jinta dayayi ajikinsa ne.


                     Kallonta yakeyi be tab'a sanin tana da kyau sosai haka ba, tayi mishi kyau datake bacci, sleeping beauty ya furta a hankali.



Jawo bargon yayi ya lullub'a musu gaba d'aya, yayi addua ya shafa musu. abinda ya juma beyi ba wato addu'an kwanciya.


Cikin dare salma ta farka tajita a jikin mutum, hannu takai ta kunna lamp d'in dake gepenta, zuba mishi ido tayi tana kallon fuskarshi ga kwantaccen sajen shi wanda ya kwanta a fuskar shi, ya k'arama fuskar shi kyau da kamala gaskiya ta yarda Abdul me kyau ne.


Hannun shi ta kalla wanda ya zagayeta dashi tunani takeyi ta yanda zata cire hannun batare data tashe shi, gashi so take yi ta tashi ta d'auro alwala tayi sallan nafila.



A hankali ta zare jikinta a cikin nashi ta nufi toilet domin ta d'auro alwala, k'aran bud'e kofar toilet d'inne ya tashe shi. Yana kallonta ta cikin hasken dayake d'akin, ta fito ta d'auki hijab d'inta ta tada kabbara.



Raka'a hud'u tayi tadad'e a sujjadarta ta k'arshe tana kaima ALLAh kukanta kafin ta d'ago ta sallame. 


bayan tayi zikiri tayima annabi salati,ta d'auko alqur'ani ta fara karatu cikin sanyin muryanta. Duk abinda takeyi A.A yana kallonta nan take farin ciki ya rufeshi, Salma itace irin matar dayake burin ya aura tun farko. Haka kawai shima yaji yana sha'awar yin nafilan koda raka'a 2 ne, idan be manta ba rabonshi da ya tashi sallah da daddare tun kafin yayi aure. mik'ewa yayi ya shiga toilet d'in ya d'aura alwala,ya fito ya shimfid'a sallaya ya tada kabbara.


Bayan ya idar yayi addu'o'inshi, sannan shima ya d'auko alqur'ani daya gani a gefe ya fara karantawa. Salma tabar karatun da takeyi ta juyo tana kallon shi jin yanda yake k'ira'ar sa kamar sudes, A.A daya kammala karatun shi ya juyo ya kalleta jin dayayi tayi shiru da barin karatun. 


Gani yayi ta zuba mishi ido da alama hankainta baya wajen. hure mata ido yayi, yace "yadai 'yan mata kallon fa?" cikin sauri ta kauda kanta cike dajin kunyar kamata da yayi tana kallon shi.



Rufe qur'anin tayi ta mik'e ta cire hijabin ta ninke ta adana shi, sannan taje ta kwanta, Shima tashi yayi yaje ya kwanta ya jawota  jikinsa, ya lullub'a musu bargo suka koma bacci.



               ASUBA TA GARI SAL-AZEEZ.



Humaira kuwa tana shiga d'akinta ta d'auki waya ta kira lina ta fad'a mata duk abinda ya faru, masifa lina tahauta dashi,tace bakiji abinda boka ya fad'a bane? yace fa idan kikayi wasa ita ce silar tonuwar asirinki. gashi kin jawo har yana miki musu a gabanta. humaira tace "wallahi lina rainane ya b'aci shiyasa" humy sefa kinyi hakuri kin daure zuciyar ki kafin komai ya tafi yanda muke so. dad'a bata shawari lina tayi sannan sukayi sallama


Shiru-shiru humaira bataga A.A ya biyo bayanta ba kamar yanda ya saba, tashi tayi ta leka falon gani tayi bakowa da alama d'akin salma ya tafi. dawowa tayi d'aki ta kasa zama duk tunanin kar wani abu ya shiga tsakanin su, gashi ba daman taje d'akin Saboda kar plan d'insu ya wargaje. A tak'aice ranar haka humaira takwana tsabar kishi kamar zatayi hauka.


                   Da asuba ya riga salma tashi, saida yayi alwala sannan yazo ya tasheta ya shimfida sallaya yayi raka'atainil fajri.


Bayan salma ta d'auro alwala yaja su sallar asuba, bayan sun idar sukaci gaba da karatun alqur'ani har gari ya k'arasa wayewa.



Salma ce ta gaishe shi ya amsa fuskar shi d'auke da murmushi, dan jinshi yake cikin farin ciki. 


Mik'ewa tayi tashiga toilet ta had'a mishi ruwan wanka ta fito ta fad'a masa, binta yayi da kallon mamaki da tunda suke da humaira bata tab'a  had'a masa ruwan wanka ba dan komai da kansa yake yi.


thanks yace sannan ya tashi ya nufi toilet d'in ita kuma ta nufi kitchen  dan ta d'aura musu breakfast



                  dankali ta soya musu da kwai, tayi musu farfesun kayan ciki, se ruwan lipton dayaji kayan k'amshi. bayan ta kammala ta debi kayan breakfast d'in takai babban falo dan tana da tabbacin humaira bata tashiba a lokacin.



d'ayan bedroom d'in ta shiga do tayi wanka. A.A ya fito daga wanka daga shi se towel a daure a k'ugunsa, se k'arami a hannunsa yana goge sumar kanshi. gaban mirror yaje yana k'arewa mayukanta dake kan mirron kallo.  hannu yasa ya d'auko wani lotion me k'amshi ya shafa.


Fitowa yayi yanufi d'ayan d'akin dan ya shirya, saboda akwai sauran kayanshi daya manta be kwashe ba a d'akin.


shigarsa tayi dai-dai da fitowar salma daga wanka, tana d'aure da towel wanda ko cinyoyinta be gama rufewa ba. Daskarewa yayi a wajen, ganinta d'aure da towel ya d'aga masa hankali, takowa ya farayi zuwa inda take tsaye, salma data kasa yin gaba bare baya tsabar kunya daya rufeta kamar k'asa ta tsage ta shiga haka takeji.


Ganin yana nufota ne yasa ta juya a guje ta koma toilet d'in ta rufo kofa. murmushi kawai yayi ya girgiza kai.


kan mirron d'akin ya nufa ya shafa ma sumar sa mayuka ya fesa hairsprayer. sannan ya nufi wall drop ya ciro kayan da zai saka. Black jeans ya ciro da farar t-shirt me guntun hannu, a gaban rigan an rubuta HANDSOME da bak'ak'en harufa. Ya saka farin takalmi cover shoe se bak'in  jacket daya d'aura akan kayan kasancewa lokacin hunturu ne. turaruka ya d'auka ya fesa san ya bar d'akin ya nufi part d'in humaira




Salma saida taji fitar shi ta fito ta koma d'ayan bedroom d'in ta shirya cikin doguwar rigar material fitted gawn bata d'aura d'ankwali ba se tayi rolling da siririn mayafi kalan kayan, ta fesa turarukanta ta fito ta nufi falo.


Bata tarar da kowa ba, zama tayi akan kujeran dining d'in ta fara had'a tea dan baza ta iya zaman jiran su ba.


bata dad'e da zama ba A.A ya fito da alama har yanzu humaira bata tashi ba, hanyar fita taga ya nufa ta d'an d'aga murya tace "ga breakfast d'inka fa"


Juyowa yayi yana kallon ta shi abin natama ya dena bashi mamaki se burgeshi da takeyi. Yaushe rabon da yayi breakfast a gidansa ai harya manta, se dai kullum idan yaje office ya aika a siyo mishi a restaurant, indai kaga ya karya a gidansa to ranar weekend ne shima se 11:00am. shi harya ma saba, duk lokacin da zai tafi office harya shirya humaira bata farka daga bacci ba bare ta bama mai aiki umurnin abinda za'a girka(mata dan ALLAh mu gyara)


K'arasowa yayi ya zauna, cup ta d'auka ta had'a mishi tea ta d'auki plate ta zuba mishi dankalin da farfesun. be wani ci da yawa ba ya tashi duk da abincin yayi masa dad'i. briefcase d'insa ya d'auka ya nufi hanyar fita daga falon,


               "A dawo lafiya ALLAh ya tsare ya bada sa'a" salma ta fada tana bin bayansa da kallo. Juyo wa yayi, yayi mata k'ayataccen murmushi dan har a ransa yaji dadin adduar datayi masa, sannan ya juya ya fita,


muje zuwa




Post a Comment

0 Comments