TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Labarin su Page 14

 RABI'A POV.

Har ta kai gida ba ta cikin hayyacinta, ba ta sani ba ma ko ta haukace ne, haka ta riƙa yin abubuwa sukuku, har Anti Saratu ta lura da ita. Tana zaune a ɗaki ta takure wuri ɗaya, Anti Saratun ta shigo ta zauna kusa da ita ta na taɓata. Yanda ta zabura ya ankarar da Anti Saratun cewa tunani me zurfi ta faɗa.

“Rabi?! Wai me yake damunki?”

Rabi ta sauƙe ajiyar zuciya tana sunkuyar da kanta ƙasa, to wai ita me za ta ce ne?, ta faɗa mata cewar wannan Zaid ɗin da ta take yawa bata labarin suna mutunci ne ya yi faɗa da arniyar budurwarsa  kanta, kuma ya furta cewa ita ce matar da zai aura nan gaba?, yin soyyayar sa da arniya ba laifi ba ne, dom ba haramun ba ne, amma yanda ya mari budurwar tasa, da yanda ya furta 'His wife to be' ɗin nan shi ne abun da ya tsaye mata a rai.

“Ba za ki faɗa min ba ?”

Rabi ta ƙara yin ƙasa da kanta, don ba ta san me za ta faɗa matan ba.

“Rabi! Kin san cewa ba ma ɓoyewa juna komai, duk damuwata ke nake faɗawa, me ya sa ke ba za ki faɗa min taki damuwar ba? Idan har ba zan iya temeka miki ki fita daga cikin dakuwar ba, ni me iya tayaki baƙin ciki ce”

Jin hakan ya sa zuciyarta tsinkewa, ba shiri hawaye ya sauƙo mata, hawayen da ta yi ta riƙe shi tun ɗazu don kar ya zubo, sai kawai ta kwantar da kanta a kafaɗar Anti Saratu.

“Anti Saratu wai ina zan sa kai na ne?.Ya ake so na yi?.Yau Zaid ya yi faɗa da budurwarsa a kaina, kuma ya faɗa mata cewar ni zai aura ba ita ba. Da ma ina da wannan muhummancin?”

Bisa ga mamakinta sai ta ji Anti Saratu na murmushi.

“Kowani ɗan adam ya na da daraja da muhummanci Rabi, kuma kowa ya na da tasa darajar. Ina me miki albirishiri da kasancewarki ɗaya daga cikin masu wanna darajar, saboda kina da daraja fiye da lissafinki Rabi!”

Rabi tasaki kuka me sauti.

“Yanzu ya zan yi da Yaya?, idan na rabu da shi ban masa adalci ba”

Wannan maganar tata ta tabbatarwa da Anti Saratu zarginta a kan Rabin tun lokacin da Zaid ɗin da take ba ta labarinsa ya fara ɗorata a taxi, daga Rabin har shi Zaid ɗin suna san junansu ne ba tare da sun sani ba.

“Rabi ki na son Zaid?!”

Tambayar ta saka Rabi fashewa da matsanancin kuka, ita ba ta san ya za ta yi da rayuwarta ba, ba ta ma san inda za ta sa kanta ba, ina za ta kai kanta da hakkin Yaya?, A gaskiya ta cuci kanta da har ta bari soyyayar Raja ta shiga ranta, haɗuwarta da shi kuskure ce, fara kula shi da ta yi ma kuskure ne, maganar da suka yi kuakure ce, komai ma tsakaninta da shi kuskure ne, a she da da take cewa tana son Yaya faɗi kawai take a baki, yanzu ta fara soyyaya, sai a yanzu ne ta faɗa ramin soyyaya, sai a yanzu ne ta saka ƙafarta a soyyayar, sai a yanzu ne ta fara jin shauƙin soyyaya, amma me ya sa ?, Me ya sa ƙaddarorinta suke zuwa a haka?, Me ya sa duk wani abu me kyau da ta samu sai ya guje mata, don kuwa ba za ta iya auren Raja ba, ko ta na son Yaya ko babta sonsa dole ne ta zauna da shi, don babu yanda za ayi ta kalli tsabar idonsa ta faɗa masa ba ta sonsa.

“Ina sansa Anti Saratu. I LOVE ZAID!, i... i... Love him, i feel like The word 'love' is not enough for me to explain the way i love him!”

Ta fito ta faɗi duk abun da ta san ta na ji a ciki zuciyarta, ba so kawai takewa Raja ba, har da ƙauna ma tana masa, don soyyayar tasu ta jini ce, su jinin mutum ɗaya ne, shi da mijin Mishal 'ya'yan yayar Umma wadda take yawan basu labarinta ne, su ne 'ya'yan me sunanta, su ne 'ya'yan da kakansu ya basu labari kan  an sha nemansu amma ba'a same su ba.

Cike da tausayawa Anti Saratu ta ɗagota daga jikinta.

“Haƙiƙa Rabi kin gamu da jarabawa, amma babu yan da za mu yi, addu'a ita ce mafita, don haka sai ki dage da addu'a!”

*No.189, Radeemer Estate, Lugbe, Abuja*

“To yanzu Anti miye abun yi?”

Cewar Siyama cikin kuka, tun da ta dawo gidan Anti Kariman ma ba ta samu sukuni ba, don ji ta yi hankalinta ma ya fi tashi a nan ɗin. Anti Karima ta kalleta na wasu 'yan sakkani, gaba ɗaya ta sauya, kamar ba Siyamanta ba, ta rame ta ƙara baƙi, kamar kazar mayu.

“Ba de kin ce yarinya ba ce?”

Siyama ta gyaɗamata kai tana share hawaye. Anti Karima ta gyaɗa kai.

“To ai cikin sauƙi za mu yi maganinta, ba tare da kin ɗaga hankalinki ko kin tayar da nawa ba... Zo ki ji”

Siyama ta miƙa mata kunnenta, ido waje take kallon Anti Karima, bayan da ta faɗa mata abinda za su yi.

“Kuka ki na ganin babu matsala?”

Ta faɗa cikin karyewar murya.

“Mtswwww!, Wata matsalar kuma za'a samu, hakan kawai za mu yi”

Siyama ta gyaɗa kanta cike da gamsuwa, duk da ta na jin ɗar-ɗar a cikin ranta, amma sai ta dake ta miƙe ta shige ɗakinta.

Anti Karima ta bi bayanta da kallo cike da tausayawa, idan de har Kuliya ya shigo hannunsa ba za ta masa da sauƙi ba, dan sai ta rama abun da ya yiwa ƙanwarta. Ta yi ƙwafa a bayyane tana jan wani littafi dake aje kan coffee table.

*No.181, Guzape, Abuja...*

MISHAL POV.

Zaune take a falo ta na rubutu a cikin littattafanta,  ta baje takardu da littatafi a ko ina, don wani assignment ɗin math aka basu me wahalar tsiya, duk da ita ba sosai take yin assignment ɗin math ba, wannan ɗin ma don malamin yace shi ne makin C.A ɗinsu. Shi ya sa ta dage take yi.

Ƙofar falon aka turo, Kuliya ya shigo ba tare da ya ko kalleta ba ya kama hanyar corridor, ita ma ba ta takura da sai ta masa magana ba, don ta lura da ba ƙaramin miskili ba ne, ta taɓe baki ta ci gaba da aikinta.

Bayan shuɗewar kusan muntina ashirin sai ga shi ya fito, sanye cikin wata baƙar T-shirt da baƙin sweat trouser. Fuskarsa kawai ta kalla ta ganta a haɗe, babu alamun rahama ko fara'a, da alama dai yau ransa a ɓace yake sosai.

A falon ya zauna ba tare da ya mata magana ba, sai wani cin magani yake, ɗagowa da kanta ta yi ta kalleshi, sannan ta ci gaba da rubutunta tana faɗin.

“Sannu da zuwa”

Ƙin kulata ya yi, don ransa a matuƙar ɓace yake, for the very first time a rayuwarsa ya yi falling assignment, wani abu da kaf tsawon fara aikinsa a wurin bai taɓa faruwa da shi ba, a ko da yauashe shi me nasara ne, kuma ba faɗuwar tasa ce kaɗai ta ɓata masa rai ba, sakin me laifin da aka yi ne ya fi ɓata masa rai. Kuma babban abun haushin shi ne, me laifin fyaɗe ya aikata, duk da tarin hujjojjin da suka gabatar a gaban kotu, haka aka kori ƙarar ba tare da la'akari da rayuwar ƙaramar yarinyar da aka lallata ba.

Mishal ba ta ƙara bi ta kansa ba sai da ta kakare a wani wuri, kuma ba ta da wanda za ta iya tambaya bayan shi, shi ɗin da a yanzu ba ta da kowa kamarsa, shi ɗin da take zaune da shi gida ɗaya a matsayin miji. Hakan yasa ta ɗauki littafin ta matsa kusa da shi tana faɗin.

“Abu Aswad ɗan temaka min...”

Wani kallo ya mata daga ita har littafin nata, kafin ya juyar da kansa gefe, yana ɗaga kafaɗarsa ta dama. Mishal ba ta daddara ba ta ƙara miƙa masa littafin.

“Dan Allah ka ɗan temaka min iyaka nan ne na kasa...”

“Ke wai ba ki da hankali ne?! Ba ki ga a yanayin da na dawo gida ba?!, Ke ba za ki iya yi da kan ki ba?! Dole sai na miki?!”

Cike da hargagi yake mata magannar, yayin da ya miƙe tsaye, har wani ɗaga hannu yake kamar me shirin kai mata duka, cike da dauriya Mishal ta miƙe tsaye, don ba ƙaramin tsorata ta yi ba. Ido cikin ido ta kalleshi, hannunta riƙe da littafin da kuma pen.

“Kai ba ka isa ka ce ba ni da hankali ba, don kawai ina yarinya ba shi zai sa a min kallon mahaukaciya ba, ina da hankali, na kuma san inda ke min ciwo. Don ka dawo gida ranka a ɓace sai ka huce a kaina?, Na ji ina da laifi don na maka magana yayin da kake cikin fishi, amma na roƙeka da kada ka sake min tsawa, saboda ba'a min tsawa!”

Tana kawai nan ta tattara kayanta ta yi ɗakinta cikin ƙunar rai. Kuliya ya dafe kansa ya na rintse ido, me ya shiga kansa haka har ya mata tsawa?, ya rab!, ya kamata a ce ya na iya sarrafa fishinsa.

*

Mishal na zaune a kan wata doguwar kujerar balcony ɗin ɗakinta, littafin math ɗinta ne a je a gefenta, don ta kasa wucewa wurin, ga kuma ranta da ya ɓaci, babban ɗan yatsanta na dama sanye cikin bakinta tana sha, tana kalon hasken farin wata, wai ko zuciyarta za ta washe da wannan baƙin cikin da Abu Aswad ya ɗura mata.

Ƙofar ɗakin ta ji an turo, hakan ya sa ta juya ta kalli cikin ɗakin, Kuliya ta ga ya shigo, ya na wani abu kamar mara gaskiya, hakan ya sa ta yi ƙwafa tana juyawa, ta ci gaba da shan hannunta.

Ƙaraaowa ya yi ya, ya tsaya a bayanta, sannan ya mata gyaran murya, Mishal ta yi kamar ba ta ji shi ba, hakan ya sa ya ƙaraso ya zauna a kusa da ita, littafin math ɗinta dake tsakaninsu ya kalla, sannan ya kalli fuskarta ta cikin hasken farin wata da kuma na wutar nepa.

“Wai har yanzu ba ki dena shan hannu ba?”

Yanzun ma banza ta masa, a karo na farko Kuliya ya ji haushin kansa, ya ji haushin zuciya da ta ingiza shi har ya aikatawa amanarsa haka, a karon farko ya ji cewar ya yi nadama, ya yi nadamar yi wa wani masifa. Hakan yasa ya ɗaga hannayensa, tare da kama kunnensa.

“I am sorry Mishal!”

Wasu kalama da rabonsa da ya furtasu ga kowa tun bayan ranar da ya taso daga asibiti, bayan nan kuma ba zai iya tuna rabonsa da furtasu ba.

Cike da mamaki Mishal ta cire hannunta a baki ta juyo ta kalleshi, ba ta san shi sosai ba, amma tana da tabbacin ba saba faɗar kalaman ya yi ba, yadda suka fito daga kan harshensa ne ya sa ta tabbatar da hakan, sai kuma inkiyarta da ya kira, da idan zai ma ta magana sai dai ya ce Hafsat, amma yau Mishal yace, ga kuma kunnuwansa da ya riƙe. Sai ya zamemata kamar wani maraya

“Raina ne a ɓace, ni kuma ba na san a min magana idan raina ya ɓaci”

Kuliya ya faɗi yana ɗaga ƙafaɗarsa ta dama, Mishal ta juyar da kanta gefe, ta na ci gaba da kallon farin wata, kafin muryarta ta fito.

“Hargagi da ɗaga murya ba ya saka mutum ya huce haushi, sannan ba ya maganin ɓacin rai”

Kuliya ya ci gaba da kallonta ya na mamakin hankalin da ya ga ta yi a yau, kamar ba wannan mashiririciyar ba.

“Me zan yi dan raina ya huce?”

Mishal ta juyo ta kalleshi, jin yanda amon muryarsa ya fito a sanyaye. Ba tare da tace masa komai ba, ta miƙe ta zagaya ta bayansa, shi ya ɗauka ma cikin ɗakin za ta koma, be za ta ba ya ji sauƙar hannayenta a kan kafaɗunsa duka biyu, dai-dai doron wuyansa, hakan ya sa ya lumshe idonsa a hankali, don sauƙar hannun nata a kan jikinsa ya sauƙar masa da wani yanayi mara fasaltuwa.

A hankali Mishal ta shiga matsa gurin tana masa tausa, idonsa a lumshe ya ɗaga kannsa sama, hakan ya sa kansa ya karu da jikinta, ita ma idon nata ta lumshe, dan ta ji sak wannan yanayin da ta taɓa ji a sanda ya rungumeta. Ci gaba ta yi da masa tausar, kafin muryarta ta fito a hankali, kuma har lokacin idonta a lumshe yake, kamar yanda nasa suke a lumshe.

“A duk sanda za ka yi fushi. To wannan kake buƙata!”

Kafaɗar tasa ya motsa, hakan yasa ta buɗe idonta.

“Shin za ki kasance tare da ni a duk sanda zan yi gushi?”

Wani abu me kama da farin ciki ya motsa a ƙirjin Mishal. Hakan ya sa ta kuma lumshe idonta tana danna masa kafaɗar.

“Insha-Allah”

Allah ne kaɗai ya san yanda abun da take masa yake sanyaya zuciyarsa, ya ji duk wata damuwa da ɓacin ransa sun bi iska.

A hankali ya buɗe idonsa, sannan ya janye kansa daga jikinta, hakan yasa ita ma ta buɗe idonta, sai ta ga ya na janyowa littafinta.

A kan idonta ya buɗe littafin, sannan ya tsaya nazartar problem ɗin, kafin ya shiga mata solving. Cikin abun da bai fi minti uku ba, ya gama mata, kuma har lokacin tana masa tausar.

“Nagode”

Ta faɗi a saitin kunnensa, ya ɗaga hannunsa na dama ya ɗora a kan nata dake kan kafaɗarsa. Hakan ya sa Mishal jin wani abu me kama da shock ɗin wutar nepa ya ratsa fatar hannunta.

“You are welcome!”

*T.O.C Douglas Crescent, Kaura District, Game Village, Abuja*

*10:00 PM*

RAJA POV.

“Zaid”

Rhoda ta kira sunansa, hakan ya sa ya ɗaga haɓarsa daga hannunsa da ya yi tagumi, ya juyo ya kalleta, zaune yake a kan kujerar dake ɗakinsa, gaba ɗaya tunani ya hana shi sukuni, ya kasa gane abun da ya kamata ya yi. Kallon Rhodan ya yi na 'yan wasu sakkani, sanye take da pyjamas iri na jikinsa, hannunta a dama riƙe da trayn  abinci. Sai kuma ya juya ya ci gaba da kalon ƙofar bathroom, kamar me jiran fitowar wani daga ciki.

Rhoda ta girgiza kanta ta tako har gabansa, zama ta yi a kusa da shi, sannan ta aje taryn hannunta a kan coffee table, ta dafa kafarsa ta dama tana kallon gefen fuskarsa.

“Me cece damuwar?”

Hannunsa ya sa ya shafa gaba ɗayan fuskarsa, sannan ya sosa kansa.

“Wani tunani kike ga Ammata za ta yi a kaina?”

Rhoda ta yi murmushi.

“Dude! Babu macen da ta isa ta ce bata sanka, baka da wani aibu, look at your self Bro, you are dazzling, smart, athletic, stylish, chaming and elegant!”

“Ummm!, Yaushe ƙanwata ta girma haka?”

Ya tamabaya yana wani murmushi ɗan guntun murmushi, Rhoda ta yi murmushi tana kwantar da kanta a kafaɗarsa. Sun ɗan ɗau lokaci a haka, kafin ta ɗago da kanta ta na ɗaukar trayn dake ɗauke da abinci.

“Yanzu dai ka ci abinci”

Ita da kanta ta shiga bashi a baki yana ci, don zuwan nata ya sauƙa-ƙa masa ruhi, saɓanin da da komai ya jagule masa. Maganarta ta ba shi ƙwarin gwiwa sosai, kuma ya ji cewar tabbas, babu abin da zai hana rabi'a ta so shi.

*Brickhall school, Kaura District, Abuja*

RABI'A POV.

“...Seesee!”

Mishal ta kirata, ganin gaba ɗaya hankalinta ba ya kanta, tun ɗazu take ta famar mata hira, amma ba ta amsa mata, hakan ne ya ankarar da ita cewar Adawiyyan ba ta cikin hayyacinta. Firgi-git Rabi ta kalleta.

“Ummm”

Ta amsa tana kallon Mishal ɗin, Mishal ta kalleta cikin nazari.

“Ba ki da lafiya ne?”

Rabi'a ta girgiza kanta.

“Lafiya ta ƙalau.Tun rannan na ce miki ki riƙa ɗaura ɗankwali ko hula. Me ya sa bakya sakawa?”

Ta faɗi cikin son bagarar da wancan zancen, don Mishal ba za ta iya mata maganin damuwar da take ciki ba, ga shi yau monday, tarradaddinta shi ne yanda za ayi ta haɗu da Raja, ta na son ganinsa, amma kuma wani ɓangare na zuciyarta ba ya maraba da hakan.

Da yake ita ma Mishal ɗin wasu lokutan ba wayo ta ci ka ba, sai ta shafa kanta, ta na sinne kan cikin alamun rashin gaskiya, saboda tun rannan Anti Adawiyyan ta ce mata ta riƙa saka hula ko ɗankwali, don a yanzu ta zama matar aure, kuma sai ba ta yi hakan ba.

“Na zo da hular fa. Ba ri na saka”

Ta faɗi ta na jan jakarta, tare da buɗeta, wata baƙar hular sanyi ta fitar daga cikin jakar, sannan ta saka a kanta.

“Ko ke fa, ai kin fi kyau a haka”

Mishal ta ɗan yi murmushi.

“Kowa a class ɗinmu ya na ta magana a kan ball ɗin da kuka yi rannan, yaushe za ku sake?”

Rabi ta ɗan yi murmushi, don ta ɗan fara samun sauƙi a ranta.

“Duk sanda kuka saka rana, amma ban da yau”

Daga haka suka shiga hirar ball, kafin ɗaya daga cikin masu aikin shara a makarantar ta zo kiran Rabi'a, kan ta zo za ta yi aiki a ɓangaren kwanan ɗalibai.

Wai hausawa suka ce rashin sani ya fi dare duhu, domin da ace ta san abun da zai iya faruwa a wannan tafiyar tata, da ba ta fara ba, domin babbar ƙaddarar rayuwata ta faru ne ta sanadiyyar wannan aikin da aka sakata a wannan lokacin.

Haka suka yi sallama, Rabi ta tafi ɓangaren kwanan ɗaliban ta fara aikin sharar, aikin yau har ya fi na kullum, don ba ita ta gama ba sai wajejen ƙarfe 5, kuma bayan ta gama da can ta dawo ɓangaren ajujuwa, zuwa lokacin an jima da tashi, haka ta bi aji bayan aji ta share ta goge, har lokaci ya ƙure mata, don ba ta gama ba sai 7.

Wani abu sabo da ba ta taɓa yinsa ba, shi ne kaiwa magariba a makarantar, duk da akwai mutane a cikin makarantar, don akwai masu kula da ɗaliban da suke makarantar kwana, ga shi gaba ɗaya ta gaji, haka ta fito a gajiye tiƙis.

Sai da ta ɗan tsaya ta kalli ƙofar estate ɗin su Raja, ta cikin hasken fitilun da aka kunna ta ko ina a layin, sannan ta kama hanyar fita zuwa babban titi.

Yanayin tafiyarta ne kaɗai zai tabbatar maka da gajiyar da ta yi, kamar daga sama ta ji ƙaran harbi a bayanta, hakan ya sa wani abu ya yi ƙulululu!, a cikinta, tsoro mara adadi ya mamayeta, idanuwanta suka zaro waje saboda tsoro, kamar kwaɗon da mota ta take shi a kan titi, haka ta juyo a tsorace ta kalli bayanta.

Wani irin bugu da zuciyarta ta yi ya sa ta dafe ƙirjinta da sauri, don ji ta yi kamar zuciyar tata za ta fashe ne lokaci guda, nan take ta ji kanta ya sara, wani gumi da ba ta san ta inda yake fita ba ya jiƙa jikinta sharkaf, ta cikin waddataccen hasken da ya haske ko ina, ta ga RAJA tsaye a kan wani mutum, hannunsa na dama riƙe da bindiga wadda ya yi pointing ɗinta kan mutumin dake yashe a ƙasa babu rai, alamun dai shi ne ya harbin, wani irin yamutsawa cikin ya yi, hakan ya sa ta rafka wani uban salati.

“Innallillahi wa inna ilaihi raji'un!”

A firgice Raja ya ɗaga kansa ya kalli setin inda ya ji salatin cikin muryar Rabi'a, hasken fitilun wurin ya haske masa fuskarta tar, saboda har ya na iya ganin gumi da hawayen da suka jiƙa fuskarta.

Karo na farko a rayuwarsa ya saki bindiga daga hannunsa, a karo na farko ya yi na damar karɓar wannan assignment ɗin, a karo na farko a rayuwarsa tsoron wanke kansa a gaban wani ya kama shi. A dai-dai lokacin Rhoda, Alandi, Jagwado da Zuzu suka iso wurin cikin gudu, su ma a tsorace suke kallon Rabi'a, wadda ke kuka tana girgiza musu kai, sai kuma ta juya da gudu tana fashewa da kuka.

“Raja ka bita ka mata bayani”

Rhoda ta faɗi hankali a tashe, cikin sanyin jiki Raja ya girgiza mata kai ya na ɗaga kafaɗarsa ta dama. Ko yau ma sai da ya fito ya tsaya a ƙofar estate ɗinsu ko zai ga wucewarta, amma haka ya tsaya a wurin har na tsawon awa biyu, amma babu ita babu dalilinta, hakan ya sa ya ɗauka cewar ba ta zo ba.

Haka ya koma gida cikin rashin jin daɗin zuciya, ba don ransa na so ba, suka shiga dudduba makaman da suka karɓa a wurin wannan mutumin shi da su Rhoda, kuma a lokacin kamar da aka ce ya kalli window ya hango inuwar mutum. Hakan tasa ya tashi ya fita waje don ya duba, kamar yanda ya yi zato, ɗan leƙen asiri ne aka turo musu, daren gudu suka shiga yi a layin shi da mutumin, har zuwa lokacin da Allah ya ba shi iko ya harbi mutumin, ashe rabom Rabi'a za ta gani ne.

“Duk abin da zan faɗa mata yanzu ba za ta fahimta ba. May be next time?”

Ya yi maganar cikin raunin zuciya, kuma ya na gama faɗin hakan ya juya ya fara tafiya.

Abun da be sani ba shi ne, da ace ya bi Rabi'a a wannan lokacin, da wata ƙaddarar ba ta faru ba, wata ƙaddara da za ta tarwatsa komai, ta kuma zama sanadiyyar shiryuwar wasu lamura.

Don a wannan juyawar da ya yi, wata mota ƙirar Lamborghini ta wuce ta gefensa. Har su Rhoda na tare gawar mutumin dake yashe aƙasa, gudun kada me motar ya samu danar ganin gawar.

Sosai Rabi ke kuka, zuwa lokacin ta dena gudun, tafiya kawai take, ba tare da tasan inda take cilla ƙafarta ba. Wai me ya sa ne?, me ya sa ita ba ta da sa'a a rayuwa?, me ya sa komai yake cakuɗe mata?, shin sai yaushe ne za ta saku dawamammen farin ciki?, sai yaushe?, sai yaushe?.

Ta na cikin waɗanan saƙe-saƙen nata, wata mota ta tsaya a bayanta, kuma duk da ta ji kamar tsayuwar mota a bayanta  bai sa ta waiga ba.

USMAN POV.

Shi da abokansa biyar ne ke cikin sabuwar motarsa ƙirar Lamborghini, Bash, J-boy, Jaz, Bareeki sai kuma shi kansa. dawowarsu kenan daga wani club, inda suka je suka yi tatul a can, kuma yawon shaɗancin nasu ne ya biyo da su ta Joy Emodi CI.

“Guys! Kun ga wata can!”

Cewar Bareeki ya na nuna wata yarinya dake tafe a gefen titi, yanayin tafiyar yarinyar kaɗai zai sa ka fahimci cewar ba a hayyacinta take ba, Daga gidan ba ya na motar Usman ya furzar da hayaƙin shishar da ya shaƙa daga bakinsa, sannan ya furta abun da ya zama sanadiyyar faruwar ƙaddarar da Allah ya hukunta faruwarta a cikin wannan daren.

“Sanƙamoma mana ita!”

Su duka suka kwashe da dariya, kafin Bareeki ya yi parking motar ba tare da ya kasheta ba, shi da J-boy suka fita daga motar, suka shiga bin yarinyar a baya suna dudduba layin, ko za su ga wani, sai da suka tabbatar da babu wanda ke ganinsu, kafin suka yi sauri suka suntumi yafinyar, Bareeki ya riƙe ƙafafunta, J-boy kuma ya riƙe kafaɗunta yana rufe mata baki, suka yi maza suka dannata a mota, da mugun gudu suka bar layin. Kai tsaye suka nufi gidan Usman ɗin Kubwa.

MISHAL POV.

Yau a gajiye ta dawo gida, hakan ya sa tana yin wanka ta yi sallah sannan ta kwanta don ta huta, ba tare da ta ankara ba bacci ya kwasheta. Ba ita ta farka ba sai ƙarfe huɗu, haka ta tashi jiki a mace, saboda baccin yamman da ta yi, banɗaki ta shiga ta yi brush, haɗi da alwala, ta futo ta yi sallah.

Saboda yunwar da take ji tana idar da sallahr ta wuce kitchen, ba za ta iya jira sai ta girka wani abu ba, don haka ta ɗauki youghurt da cake, ta zauna ta ci har ta bawa Ayra.

Bayan ta kammala ta tashi ta shiga share gidan, kuma tana cikin sharar falon ne ta ji an turo ƙofar falon, hakan ya sa ta ɗago daga sunkuyen da take, ta kalli ƙofar falon, mata biyu ne suka shigo, ɗayar kawai ta iya ganewa, ita ce wannan wanda Annan ta kira da ƙanwar Kuliya. Amma ba wannan ne abun dubawar ba, kallon da ɗayar ke mata ne abun tuhuma. Saboda wani irin kallo ne da ta saba samun irinsa daga wurin Hajjara, wato kallon tsana.

KULIYA POV.

_“Abu Aswad.Magungunana sun ƙare, please ka siyomin idan ka fita”._

Abun da ta faɗa masa kenan da safe, kuma a lokacin sai ya aje mug ɗin hannunsa wanda yake ɗauke da coffee me zafi, ya kalleta, sannan ya kalli takardar hannunta, hannunsa ya kai ya karɓi takardar, kafin ya karanta, sunayen magunguna ne guda biyu kacal, kansa ya ɗan karkatar gefe yana kallonta. A gefe guda kuma ya na shaƙar ƙamshin ƙwan da ta gama soyawa a kitchen, wanda ta haɗa sandwich da shi, sai da ta masa bismillahr sandwich ɗin, amma ya ƙi ci, don har yanzu miskilancin ba zai bar shi ya ci ba, duk da a kullum idan ta yi girki sai ya burgeshi. 

Ya ɗaga kafaɗarsa ta dama a yayin da yake juya sitiyarin motar zuwa kwanar da za ta kaishi gidansa.

_“Shin ka san wani abu a kan Hysteria?”_

Abun da ya tambayi me pharmacyn da ya siyi maganin a kenan a ɗazu, dom a dazu bayan da ya siyi magungunan ya juya zai tafi, sai kuma ya tsaya ya juyo ya cilla masa wannan tambayar. 

A ɗazun mutumin sai ya ɗan taɓe bakinsa cikin faɗin.

_“Eh to, a gaskiya ba sosai ba. Amma dai na san cewa cutar ta na kama da hauka. Haka dai kamar jinni, mafi akasarin masu ɗauke da cutar mata ne, za ka ga mace ta na gasping kamar me asthma, a wasu lokutan ma harda suma. Abun da kan haddasata kuma shi ne ongoing stress, sannan kuma abun na kama da tsoro, ko tsana. Misali; kai abokina ne, sai muka samu wata matsala a tsakaninmu, sai nake ji a raina ba na san ganinka kwata-kwata, wata ƙila kuma wurin aikin mu ɗaya, wata ƙila kuma ɗakin kwanan mu ne ɗaya, ko kuma dai ya zaman dole da akwai wani aabu da zai haɗamu, to wannan dolen ita take haddasa ciwon, duk abun da kasan ba ka so, kuma ya zama dole ka haɗu da shi, ko ka ji shi, shi ne yake haddasa hysteria, wannan samuwar dolen ita ce sila. Dalilina na cewa abun ya na kama da iska shi ne, yanzu zan ga abun da ba na so, nan take zan shiga gasping, ina breathing kamar me asthma, amma daga zarar wannan abun ya tafi, ko ya bar inda nake, zan dawo normal, kamar komai bai taɓa faruwa ba, kamar ma ba nine na ke gasping ko na suma ba. Sannan akwai hanyoyin magance ta, dole ne a ƙauracewa yin abun da me ɗauke da cutar ba ya so, sannan kuma a duk sanda za ta tashi, a kwantarwa da mutum hankali, a faɗa masa soothing words, a kuma yi gaggawar kawar da abun da ya jawo tashin ciwon. Iyaka abun da na sani kenan!”_

Ɗaya bayan ya ɗauke kalaman mutumin, babu abun da ya bari ƙwaƙwalwasa ta yi missing. A ganin mutumin ba komai ya sani a kan cutar ba, amma  shi a ganinsa wannan abun da ya faɗa masa shi ne komai, don ko da likita zai samu sai de haka.

Fitowa ya yi daga cikin motarsa a sanda ya yi parking a parking lot, da gudu me gadinsa ya taso yana gaisheshi, ciki-ciki ya amsa ya na kama hanyar shiga gidan, amma sai me gadin ya dakatar da shi.

“Ranka ya daɗe kamar akwai matsala a cikin gidan fa...”

Da sauri ya juyo gaba ɗayansa ya kalleshi.

“Me ya faru?!”

“Eh to, ɗazu ina zaune wasu mata  biyu suka zo, suka ce su 'yan uwan hajjiya ne, hakan ya sa na bar su suka shiga, ba jimawa da shigarsu kuma sai na fara jin iface-iface da koke-koke na fitowa daga cikin gidan, ban de yi gangancin shiga ba don ban san me ke aukuwa ba!...”

Be ƙarasa maganar ba saboda wani uban ƙara da suka ji an kwaɗa a cikin gidan, kuma ƙarar ta fito cikin muryar Mishal ne, hakan ya sa Kuliya shiga cikin gidan a ɗari uku da sittin.

Abun da idonsa ya gane masa shi ne, Mishal yashe a ƙasa, kanta ya fashe ya na zubar da jini, sautin kukanta ya cika falon, ga Anti Karima yayar Siyama tsaye a kanta, ga kuma Siyaman tsaye a bayanta, tashin hankali ne ya sa sam bai lura da irin yanayin da su suke ciki ba, ya yi maza ya isa gaban Mishal ya tsugunna ya na tallafo ta jikinsa, hankali tashe yake dudduba jikinta. 

A fusace ya ɗauketa a hannunsa yana miƙewa, sannan ya juya ya kalli Karima da Siyama dake tsaye hankali tashe.

“Ku fice ku bar min gidana!”

Cikin tsawa ya yi maganar, kemar me shirin tsaga gidan, Anti Karima ta fashe da kuka ta na fita daga gidan, Siyama kuwa da ma tuni ta fara hawaye, haka ita ma ta bi bayan yayarta, shi ma kuma sai ya fice daga falon, ya saka Mishal a mota ,  kai tsaye ya wuce asibiti da ita.

*Unguwar Madallah, Suleja, Niger state*

*09:30 PM.*

Anti Saratu ce ke kai kawo a ɗakinsu cikin tashin hankali, tashin hankalin rashin sanin inda Rabi ta shiga, tun ƙarfe biyar na yamma hankalinta ya fara tashi, ganin ta haura lokacin dawowarta, ga shi har 9 ta yi amma babu Rabi bare labarinta, tsoronta ɗaya; shi ne kada Rabin ta je ta iallata kanta, ga shi ta na cikin matsanan ciyar damuwa. Ganin zaman cikin gidan ba zai mata ba ya sa ta figi hijabinta ta fito.

A tsakar gida ta samu Habiba, Mahmud da Fatima suna cin abinci hankalinsu kwance, kamar ba Habiban ba ce ta aika Rabin aikatau, kamar ba ita ce uwar 'yar dake can England ta na aikata saɓon Allah ba, shinkafa da miya har da kaza suke ci, don a cikin kuɗin da Mama ta aiko mata ta ɗauka ta siya musu. Cike da takaici Saratu tace.

“Umma Rabi fa ba ta dawo ba har yanzu”

Habiba ta juyo ta kalleta tana taune ƙashin dake bakinta ta furta.

“To sai me?! Ai da ma ta saba tafiya gantalinta irin wannan, ba wani sabon abu ba ne don ba ta dawo ba!”

Saratu ta girgiza kanta cikin faɗin.

“A'a Umma, Wallahi Rabi ba ta haka, sanin kanki ne a ta makara da yawa ta dawo ƙarfe huɗu ko huɗu da Rabi, amma yau gashi har tara babu alamarta”

“Mtswww! Sai ki yi ai”

Ta ƙarashe tana fusrzar da ƙashin da ta gama taunewa. 

Cikin ƙunar rai Saratu ta kama hanyar fita daga gidan don ta je ta yi magana da Yaya ko za ra iya jin wani abun daga gareshi.

“Gaskiya Anti Saratu ba mu yi wata magana da ita ba. Ba ta faɗa min za ta je ko ina ba!”

Abun da Yayan ya faɗa mata kenan, Saratu ta dafe gashinta ta na karanto 'Innallillah wa inna ilaihi raji'un', kanta ya kulle gaba ɗaya, ta rasa madafa da abun yi, a take a gun kanta ya sara, haka ta bar shagon, duk kuwa da kiranta da yake.

Gida ta koma jiki a saɓule, a ɗakinsu ta zauna, sannan ta lalubo wayarta ta aikawa Fu'ad kira.

“Kin ga Sarah, ki kwantar da hankalinki dan Allah, Insha-Allah zan ga abin da za ayi!”

Kalaman Fu'ad ɗin kenan gareta, bayan da ta gama faɗa masa Abin da ke faruwa, kuma kalaman nasa su ne suka yi nasarar karya mata zuciya, ta fashe da kukan da take riƙe da shi tun ɗazu.

“Fu'ad ban san yanda zan yi ba, Wallahi jikina na bani cewar Rabi ta na cikin matsala, don Allah ka temaka, ka temake ni ka samo min ita. Rabi marainiya ce!”

“Ki kwantar da hankali tukkuna, idan kina kuka irin haka hankalina ba zai yi kwanciyar da zan iya samo miki ita ba, please Habibty, dan Allah!...”

Da ƙyar ta iya shanye kukan nata, saboda lallashin da Fu'ad ɗin ke mata.

“Menene ma kika ce sunan makarantar?”

“Brickhall School, a nan Kaura District take, kusa da game Village”

“Inshaallah zan nemo miki Rabi'a, sai dai idan abun yafi ƙarfina”

Da haka suka yi salama, don yau babu wayar soyyayar da aka saba, saboda yanda take cikin tashin hankali.

Sallamar Babansu ta ji a tsakar gida, hakan ya sa ta fito da sauri, Ɗan Lami ya kalleta a lokacin da yake zama kan tabarmar da su Habiba suke kai, don shi ma ya samu a ɗan lasa masa abun da aka samu.

“Abba sannu da zuwa”

Ta faɗi cikin muryar wanda ya gama kuka. Ɗan Lami ya ɗan kalleta kaɗan, sannan ya kauda kai, don haushinta yake ji, ba ƙaramin ɓaci ransa ya yi ba, a sanda ya ji labarin ta tura manemin aurenta wurin yayansa Habu, a inda ya ji labarin kuɗin yaron ya yi zaton wurinsa za ta turo shi, amma sai ba ta yi hakan ba, kuma haushi bai ƙara kama shi ba, sai da Kawu Habu ya ambata masa yawan kuɗaɗen da shi ma nemin auren nata ya kawo, kuma Kawu Habun ya yi mirƙi si-si ya hana shi ko asi a cikin kuɗin, yace wai da su za'a haɗa a yi wa yarinya kayan ɗaki. Da ace kuɗaɗen hannunsa suka shi, ai da ya morewa rayuwa, don ko karuwarsa Vicky ba ta isa ta ƙara rena masa hankali ba.

“Abba har yanzu Rabi ba ta dawo ba”

Saratun ta kuma faɗi tana durƙusawa a gabansa, sai da ya juyo ta kalli idon Habiba, sannan ya furta.

“Ni na aiketa? Ita wadda ta aiketa ai ita ya kamata ta fita nemanta ba ni ba!”

Habiba ta taɓe baki, a zuciyarta kuwa murmushi take, don bisa ga dukkan alamu aikin wannan malamin ne ya ci, a rannan ta saurari gaba ɗaya zancen da Rabin suka yi iya da Saratu, kuma hakan ya sa ta kira yayarta Hajiya Inno a waya, aka haɗa musu wani laƙani da zai sa duk wani ɗa na mijin da zai kalleta ya yi sha'awarta, kuma a yau ɗin nan aka tura aikin, kuma bisa ga dukkan alamu aikin ya ci, tun da ga shi ba ta dawo ba, kuma shirinta na gaba shi ne; idan Rabin ta dawo, sai ta sa Ɗan Lami ya koreta daga gidan.

Jiki a saɓule Saratu ta miƙe ta koma ɗaki, ta na Allah wadarai da rayuwa irin ta gidansu.




Post a Comment

0 Comments