TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Labarin su Page 22

 *LABARINSU*

*©SALMA AHMAD ISAH*

*TAURARI WRITERS*

*22*

~~~

*Keep on letting your love shine...*

***

RAJA POV.

Zaune yake a falon kakansu wanda mutanen gidan ke kiransa da Baba, Baba Munzali da kuma Kawu Abdullahi ne tare da Baban. Kawu Abdullahi ne ya masa tambayoyi kan yanayin yanda rayuwarsa take a can garin Abuja da ya faɗa musu ya na da zama, sun masa tambayoyi sosai, kafin suka tambayeshi alaƙarsu da Rabi'a.

“Na gamu da ita ne a hanyar makarantar da take zuwa aikatau, kuma daga haka ne muka soma soyyaya, har muka fahimci juna, giftawar wannan iftila'in ne ya kawo mana tsaiku”

Kawu Abdullahi ya gyaɗa kansa a sanda Zaid ɗin ya kai ƙarshe a maganganunsa.

“Ke nan ka san abun da ya faru da ita?”

Kansa a ƙasa ya gyaɗa shi.

“Na sani Kawu, dan ni ne ma da kaina na yi jinyarta a asibitin da aka kwanatar da ita”

Baba Munzali ne yace.

“Kuma kai yanzu kana santa a hakan?”

“Sosai ma kuwa Baba, ina san aurenta a yanda take, abun da ya faru da ita ƙaddara ce,wadda ta wuce fata, kuma san aurenta da nake ne ya sa na biyota har nan...”

Ko kafin wani a cikinsu ya sake cewa komai, wayar Zaid ɗin ta yi ringing alamun shigowar kira.

“A min afuwa...”

“Ba damuwa za ka iya ɗaga kiranka”

Kawu Abdullahi ya amsa masa. Kansa ya gyaɗa ya  na ɗaga kiran.

“Ok”

Kawai yace sannan ya katse kiran, cikin WhatsApp ya shiga, ya buɗe chat ɗin wani contact, a inda aka turo masa wani vedio, buɗe vedion ya yi, kafin a hankali ya matsa ya miƙawa Kawu Abdullahi wayar.

“Ka duba ka ga”

Kawu Abdullahi ya karɓa cike da mamaki, kafin ya danna play, vedion ya buɗe, sannan hoton Habiba dake garƙame a cell ɗin 'yan sanda ya bayyana, fuskarta ta ji duka ba na wasa ba, muryarta ce ta shiga fitowa raɗau daga cikin wayar.

Hakan ya sa Kawu ya karkata fuskar waya zuwa ga su Baba dan su ma su gani.

“...Ni ce na yi wa Maryam asirin da ya sa Ɗan Lami ya saketa, kuma ni ce na yi mata asirin da ya sakata jinya, har ta kai ga mutuwa, har ila yau ni na saka Ɗan Lami ya karɓo min Rabi daga wajen 'yan uwan Maryam. Har ta dawowa wuri na da zama, kuma... Kuma ni ce na yi wa Rabin asirin da zai sa idolan wani namiji ya kalleta zai ji sha'awarta, har aka samu wasu suka mata fyaɗe!...”

Daga haka vedion ya tsaya cak, alamun dai ya ƙare ne. Cike da mamaki ko wannensu ya kalli Zaid ɗin dake durƙushe gabansu.

“Kun gane ta?”

Ya tambaya ya na kallonsu, don ya ga kamar ba su fahimci zancen da ake ba. Baki buɗe Kawu Abdullahi yace.

“Na ganeta. Habiba ce... Abokiyar zaman Maryam”

Zaid ya gyaɗa kansa.

“Ƙwarai ita ce... A lokacin da na rasa Rabi'a, na sa aka kamata, don ta mana bayanin inda take, a memakon mu samo bayani kan inda Rabi'a take, sai muka samu wannan bayanin”

Baba ya share ƙwalla ya na kallon jikansa, jini ba ƙarya ba, hatta da yanayin maganarsa irin na mahaifiyarsa ne, shi yanzu ba shi da wani fata godewa Allah, da kuma neman yafiyar Allah, kan zunubansa na baya.

“Matso nan jikana”

Zaid ya ɗaga kafaɗarsa ta dama ya na matsawa kusa da Baban da ya kira shi, kansa ya shafa ya na faɗin.

“Allah ya mamka albarka, Allah ya ji ƙan mahaifiyarku.... Kuma ni da kaina na baka auren Rabi'a, ba za'a ɗau wani dogon lokaci ba, akwai bikin ɗaya daga cikin ƙannen naka da za ayi nan da sati huɗu, dan haka in Allah ya yarje mana tare za ayi da naku!”

Wani abu ne ya shiga ratsawa tun daga kan Zaid har zuwa ƙafafunsa, farin ciki ya buɗe ƙofar zuciyarsa ya rufta, ƙaunar 'yan uwansa ta ƙara kama shi, a hankali ya kwanta a jikin kakansa ya na nemawa Momma da Aliyu rahamar Allah.

*

“Bros”

Cewar Zakar ya na duban Zaid, wanda ke cire takalman kafarsa bayan da ya dawo daga wurin su Baba. Zaid ya amsa ya na cire takalman ƙafarsa. Tare da shigowa ɗan madai-dai cin falon samarin, ya zauna a kan kujera yana dubansu.

“Ya ake ciki ne?”

Sani ya tambaya. Zaid ya yi murmushi.

“Baba ne ya bani aure...”

Zakar ya aje mug ɗin hannunsa ya na zaro ido.

“Ikon Allah... Wai da gaske?”

Zaid ya yi murmushi ya na shafa kansa.

“Da gaske ne mana, kuma kun san wani abun farin cikin ma?, tare da na ɗayar ƙanwar tawa za ayi!”

“Wai auren Nafisa?” 

Auwal ya tambaya ya na zaro ido.

“Ban san sunanta ba. Kawai de yace auren nan da wata ɗaya ne”

“Gaskiya muna taya ka murna, amma ai kana nan har zuwa lokacin bikin?”

Cewar Yunus. Zaid ya girgiza kansa.

“Akwai wani aikin da ban ƙarasa ba a Abuja. So dole zan koma, amma biki saura sati biyu zan dawo”

“Ni fa ɗan uwa, ina san wannan ƙanwar taka da kuka zo tare!”

Zaid ya yi shiru ya na kallon Zakar dake wannan batu.

“Rhoda?”

Ya tambaya dan tabbatarwa. Zakar ya gyaɗa kai.

“Of course ita, ina santa, and i mean it”

“She is not musulim, ka bari ta musulunta tukunna”

“Wai har sai ka jira?. To tun da me ya sa bata musulunta ba ?”

Auwal ya ta baya ya na gyara zama.

“Akwai abun da muke jira kafin faruwar hakan, amma ina da tabbacin lokacin shigarta musulunci ya kusa”

“To Allah ya tabbatar, amma dan Allah kar ka bari a yanka ni, dan Wallahi ina santa”

Zaid ya yi dariya ya na ɗaga kafaɗarsa ta dama.

“Idan an yi auren Abuja za ka bita?”

“Abuja kuma?”

Zakar ya tanbaya ya na kallonsa. Zaid ya gyaɗa kansa.

“Ƙwarai Abuja, ma aikaciyar DSS ce”

“Jar uba! Kace ƙanwar taka me zafi ce”

Zaid ya ɓata fuska, ya na kallon Yunus.

“Ban san irin wannan abun Yunus”

“Allah baka haƙuri, wasa ne”

“Rabu da shi sirikina, zan maka maganinsa”

Zakar ya faɗi yana hararar Yunus.

“Har mun zama surukai kenan?”

Zaid ya tambaya.

“Eh mana, na ga dai kai ma ƙanwarmu zaka aura, ni ma kuma ka ga zaka bani ƙanwarka, mun zama surukai”

Gaba ɗayansu suka sa dariya.

RABI'A POV.

“Kin yi shiru?”

Cewar Baba ya na kallonta, ɗagowa ta yi yo da kanta ta kalleshi, yayin da take zaune a ƙasa daga gefensa. Allah ya sani tun bayan zuwan Zaid gidan nan hankalinta ba a kwance yake ba, hatta da baccin dare ba ta samu ta yi, ko na rana ma a firgice take yinsa, duk da ba wai haɗuwa suka yi ba, dan tun bayan zuwansa ba su haɗu ba, kawai de ta na jin tsoron abun da zai je ya zo. Ilai kuwa, yau suna zaune sai ga kiran Baban ya risketa, kan ta zo ya na san ganinta, kuma ta na zuwa suka tarbeta da maganar auren Zaid, shi ne ta musu shiru ta kasa cewa komai, to me za ta ce wai?, tace musu shi ɗin da suka ƙwallafa rai a kai ba mutumin kirki ba ne?, ko ta yi wa kanta ƙarya tace bata san aurensa?.

Haƙiƙa ta ga farin ciki a idon kakansu, ta ga farin ciki a idon Hajiya, kuma ta ga farin ciki a idon kowa na gidan, don kwana uku kenan da zuwan Zaid ɗin, amma kamar yau ya zo, sai nan-nan suke da shi. Ta tabbatar da idan har ta nuna ƙin amincewarta da auren nan, babu wanda zai ƙara kulata, babu wanda ma zai ƙara yin alfahari da ita a gidan. Kuma ita kanta ta san cewa tan na son Zaid, amma halinsa ne kwata-kwata ba ta so, mutum fa?! Mutum ta ga ya kashe a gabanta, ran mutum ta ga ya ɗauka kamar wani kiyashi. Sai de kuma duk da haka babu komai, za ta jure komai a kan ahalalinta, wata ƙila ita ƙaddararta ce ta zo a haka, Allah ya riga ya tsara cewar har ta koma gareshi ba za ta taɓa jin daɗin rayuwa ba, ko wani jin daɗinta na duniya ƙayadajje ne.

Kanta ta ƙara sun kuyarwa kamar ɗazu, ta kasa furta komai, hakan ya sa Baba fahimtar inda ta dosa, tana san auren, amma wata ƙila kunya ce ta hanata furta hakan.

“Na gane.... Ki je ki fara shirye-shirye, dan nan da sati huɗu kema za'a ɗaura aurenki tare da na 'yar uwarki Nafisa!”

*Bayan sati huɗu...*

*Wakili Family House, Unguwar Jama'are, Haɗejia*

Ta ko wani ɓangare na gidan a cike yake maƙil da jama'a, ko ina ka kalla jama'a ne fal, kowa  sai kai kawo yake ana ta hidimar biki, domin kuwa yanzu-yanzu aka dawo daga ɗaurin auren jikoki uku na gidan, hakan ya sa gidan ya cika fal da jama'a. Saboda wannan aure gidan har sabon fenti aka sake masa, babba da yaro na wannan ahali na cikin farin ciki.

Daga can ɓangaren samarin gidan kuwa, Zaid ne tare da samarin gidan, jiko da 'ya'ya, wasu ma bai sansu ba a cikin wata ɗayan, sai yau yake ganawa da su, kuma a yau din ne yake ƙara tabbatar da girma da kuma yawa irin na ahalin nasu.

Daga can gefen kuwa Jagwado, Alandi da Zuzu ne sanye cikin manyan kaya, kai ka rantse da Allah na gari ne, yanda suka haɗe cikin manyan kaya sai zare idanu suke, kowa ya zo sai ya tambaya su waye su? Zaid ne yake amsawa da abokansa ne.

Allah ya sani, ba ƙaramin farin ciki yake ciki ba yau, a yau din nan ya mallaki Ammata a matsayin matarsa, a yau ɗin nan ya zama cikakken mutum, shi kansa ya kasa yarda, wai shi da ya saba rayuwa shi kaɗai, shi ne yau ya wayi gari ya ganshi kewaye da tarin ahali masu matuƙar ƙaunarsa, banda matar da suka ɗauka suka ba shi, har auren gata suka masa, dan kuwa babu wata wahala da aka barshi ya yi a auren, Baba da su Kawu Abdullahi su ne suka ɗauke masa komai.

Lokacin da ya koma Abuja ya siyi wani kyakkyawan madai-daicin gida, wanda yake da niyyar aje Rabi'a a ciki, ya na shirin siyan kayan furnitures Kawu Abdullah ya dakatar da shi da faɗin su ne za su yiwa 'yarsu kayan ɗaki, kuma hakan aka yi, don a jiya aka cika gidan da kayan furnitures da kuma na kitchen, da ma duk wani abu na buƙatar gida.

Kuma hatta da sadaki Baba ne ya biya masa, shi kansa ba zai iya misalta kalar farin cikin da yake ciki ba, babu abun da zai ce sai godewa Allah, domin kuwa ita ma Rhoda ya na gab da aurar da ita, saboda sun riga da sun ɗinke da Zakar, hujjojjin dake hannunsa kawai ya rage ya miƙa, da zarar ya miƙa su za'a kama Alhaji Bala, kuma kamar yanda suka yi da Rhoda daga zarar an kama Alhaji Bala za ta musulunta.

Sannan sun yi magana da Kawu Abdullah kan daga zarar Rhoda ta musulunta za ayi aurensu da Zakar ɗin. Don haka farin cikin da yake ciki ba me misaltuwa ba ne, baki ya yi kaɗan ya faɗeshi, sai dai kawai ya ci gaba da godewa Allah.

RABI'A POV.

Daga ɓangaren Ammatan Raja kuwa, duma suna can nasu ɗakin ana wa amaren kwalliya, cikin wata ɗayan ba ƙaramar rama ta yi ba, don har mutanen gidan sun fara zargin ko auren ne ba ta so, amma ta nuna musu ba haka ba ne. A can ƙarƙashin zuciyarta kuwa tunanninnika ne birgit ta ko ina, ita kanta a yanzu ba za ta iya cewa ga takamemen abun da yake damunta ba, amma ta san cewa ba ta jin daɗi, duniyar ba ta mata daɗi sam.

Don har zargin wannan auren take, tun bayan rabuwarta da Zaid a Abuja ba su ƙara magana ba, hasali ma rabonta da shi tun ranan da za su islamiyya ta hangeshi shi da su Yunus suna hira, bayan nan ba ta ƙara saka shi a idonta ba, idan za ta ce ga abun da ya ramar da ita to har da kewarsa ma za ta iya shigowa ciki, ta na son ganinsa, ko da faɗa ne ma su ɗan yi, amma wannan zaman nesan ba ya mata daɗi.

“Kai! Amma fa kin yi kyau Rabi'a”

Cewar Rhoda, a sanda aka gama ɗaura mata ɗankwalin farin leshin da suka yi ankonsa ita da Nafisa, kanta ta kalla a mudubi. Tabbas ta yi kyau, dan hatta da wannan tabon yankan na gefe fuskarta an ɓoye shi da hoda, kwalliyar ta bal'in hawa fuskarta. Hannunta ta kai kan ƙashin wuyan da ta yi a kwanankin, ta ɗan ja guntin tsaki ta na jan wayarta.

“Kai ku yi sauri ku fito ga masu ɗaukar hoto nan sun zo”

Cewar Jidda, a yayin da take shigowa ɗakin da gudunta, ta ci uwar kwalliya kai kace ita ma amaryar ce.

“Dan Allah Ummi ki yi sauri ki gama min”

Momi ta faɗa a sigar magiya, ta na kallon me kwalliyar.

“To”

Me kwalliya ta amsa, a gefe guda kuma Rhoda da Rabi ne suke ɗaukar hoto a waya, daga can kuma Kairiyya ce takewa Nafisa da Kulsum hoto a waya.

Haka suka gama shiriritarsu kafin suka fita. Dangi da jama'ar da aka gayyata haka suka riƙa zuba musu ruwan hotuna ana ta Allah sanya da alkairi.

Da yamma kuwa walima aka haɗa musu, amma ba su yi dinner ba, dan Baba yace ba za'a yi ba, duk da suna son yi haka suka haƙura saboda babu yanda za su yi.

*10:30 PM.*

“Ke wai ina za ki kai ni ne?”

Rabi ta tambaya tana kallon Jidda dake ta janta tun ɗazu, tafe suke a harabar gidan, har ta fara bacci saboda gajiyar da ta yi Jiddan ta taso ta tace mata wai ta zo ta rakata, maganar duniya ta yi amma Jiddan ta ƙi ta amsata. Har ta gaji ta rabu da Jiddan.

Mamaki ne ya kamata a sanda ta ga sun nufi ɓangaren samarin gidan, kuma kafin ta gano abun da ke shirin faruwa, har Jiddan ta buɗe ƙofar wani ɗaki, ta turata ciki, sannan ta ja yo ƙofar ta kulle. Ba tare da ta iya tsayawa ta ga abun da ke cikin ɗakin ba, ta yi saurin juyawa tana bubbuga ƙofar, tare da faɗin.

“Jidda!, ke Jidda! Wai miye ne hakan?”

Daga waje ta ji muryar Jidda na faɗin.

“Tsakar dare mijinki ya kira ni yace ya na san ganinki, shi ya sa na kawo masa ke!”

Dammm!, gabanta ya buga, hakan ya sa ta juya da sauri, ta shiga ƙarewa ɗakin kallo, kuma idonta bai tashi sauƙa a ko ina ba sai a kan Raja dake zaune daga can gefen gadon ɗakin, waya riƙe a hannunsa, ya kafeta da shanyayyun idanuwansa. Da ƙyar ta iya haɗiyewa wani yawu me ɗaci. A sanda ta ga Zaid ɗin ya miƙe ya na nufota.

Kanta ta kawar gefe tana ƙara matse jikinta a jikin ƙofar, banda lugudan bugu babu abun da zuciyarta ke yi, ƙamshin turarensa da ya cika hancinta ya sanar mata da isowarsa gabanta.

Zaid ya saki wani murmushi ya na ɗaga hannunsa tare da dafa shi jikin ƙofar, ya mata rumfa a tsakiyarsa. Rabi ta ji kamar numfashinta ba ya fita da kyau, kamar ma ba ta shaƙar isaka ne. Kuma hakan be isa ba sai da Zaid ya kai hannunsa ya kamo fuskarta, hakan ya sa ta lumshe idonta ta kuma buɗewa, saboda ji ta yi kamar ya ɗora mata ƙanƙare a kan fuskarta, sakamakon sanyin da ta ke ji na rata jijiyon jikinta, ba shiri ta rintse idanuwanta gam-gam.

“Ammatan Raja!”

Amon muryarsa da kuma sunan suka sa ta ware idanunwata tar, ya ilahi!, ashe haka ta yi kewar jin sunan nata daga bakinsa?, ashe ta yi kewar wannan muryar tasa?, ashe shi kansa ta yi kewar ganinsa?, duk ba ta fahimci hakan ba sai yau, sai yau da take tsaye gabansa, a tsakiyar hannayensa.

“Ba ki yi kewata ba?”

Zaid ya tambaya ya na motsa hannunsa a gefe  fuskarta, Rabi ta lumshe idonta sannan ta buɗe, a hankali ta juyo da kanta ta kalli fuskarsa wadda ta kusa haɗewa da tata, hatta da ɗumin numfashinsa ta na jin sauƙarsa a kan fuskarta, tazarar tsakanin hancinta da nasa bata da wani yawa, hatta da jikunansu sun kusa haɗewa. Ba ta san me ya sa ba, amma ta ga yanda idanuwansa suka ƙara lumshewa fiye da yadda ta sansu a da. Sai de ba za ta bari abun da take ji ya rinjayi kanta ba, ba za ta bari wannan salihar fuskar tasa ta rinjayi tunaninta ba, ita ta san waye shi, ta san ainahin gaskiyarsa. Don haka ta sa hannayenta biyu, ta ture shi zuwa baya.

Sannan ta juya ta shiga fafutukar buɗe ƙofar. Zaid ya tsaya a bayanta kawai ya na kallonta. Babu yanda Rabi ba ta yi ba kan ƙofar ta buɗe ama ta ƙi buɗuwa, hakan ya sa ta juyo ta kalli Zaid dake tsaye a bayanta ya na mata murmushi.

“Ka buɗe min ƙofa,ina san na fita”

Kafaɗunsa duka ya ɗaga mata alamun shi fa babu ruwansa.

“Magana kawai nake so mu yi, da zarar mun gama, zan barki ki koma”

Muryarsa ta faɗa bayan wani lokaci, Rabi da ta ci gaba da kokawar buɗe ƙofar ta juyo ta kalleshi.

“Me kake buƙata?”

Ta tambaya idonta cikin nasa, Raja ya kuma yin murmushi ya na isowa gareta, hannunta na dama ya kama ya shiga janta, duk yadda ta kai da tirjewa sai da ya sadata da bakin gadon ɗakin. Ya zauna a bakin gadon, sannan ta ƙarfi ya zaunar da ita a kan cinyarsa. Rabi'a ta shiga mutsu-mutsun ƙwacewa, amma fur Raja ya hanata.

“Idan har ba ki tsaya mun yi magana ba, ba zan barki ki fita ba, sai de ki kwana a nan”

Jin maganar tasa ya sa ta tsaya da abun da take, Zaid ya saka hannunsa ɗaya ya kama ƙugunta baya, jin hakan ya sa Rabi jan wata iska, idanuwansa ta ci gaba da kalla, kammar tana shirin gano abun da yake shirin furtawa a cikinsu. Mustu-mutsun ta ci gaba da yi hakan yasa yace.

“Sshhhhh!, ki dena”

Muryarsa ta fito a hankanli cikin duhun daren, kuma amon muryar tasa ne ya haddasarwa Rabi jin kasala, ba ta san lokacin da ta saka hannayenta ta ƙanƙame gaban rigarsa ba.

“Good girl”

Ya faɗi a setin kunnenta, jikin Rabi ya shiga rawa, wani abu ya shiga bi ta kan zuciyarta tun daga samanta har zuwa ƙasa.

“Wani abu nake san nuna miki”

Jin hakan ya sa ta yi saurin kallon fuskarsa. Wayarsa ta ga ya kunna, don haka ta kalli fuskar wayar, tar take iya ganin fuskar Habiba cikin wayar, sannan kuma kar sautin muryar Habiban yake shiga cikin kunnuwanta.

“Ke ce wadda aka cutar, dan haka dole sai da izininki maganar za ta iya zuwa gaba, shi ya sa na buƙaci da na nuna miki. Shin kina san ki shigar da ƙara a kanta?”

Muryarsa ta faɗa bayan da vedion ya kai ƙarshe, Rabi da idanuwanta suke a ƙafe ta kalli fuskarsa, abun da Habiban ta faɗi sam bai ba ta mamaki ba, tun ba yau ba ta san cewa Habiba ce a bayan ko wani abu dake faruwa da su, amma abun da ya ba ta mamakin shi ne, yanda Habiban tace ita silar yi mata fyaɗe, ko da yake ai abun ba na mamaki ba ne, tun da har Yaya ya ƙita ita kuwa me zai ba ta mamaki a duniyar nan.

Jin ta yi shiru ya sa Zaid ya matse hannunsa dake kan ƙugunta ta baya, Rabi'a ta zabura tana ƙara iyowa cikin jikinsa sosai.

“Kin yi shiru?”

“Ba na buƙatar shigar da wani ƙara! A saketa kawai, ta ci darajar Anti Saratu, be side ai ba ma ita ya kamata a kama ba, ga babban me laifi a nan!”

Zaid ya yi murmushi, duk kuwa da ya san cewa hakan za ta iya faruwa. Ita har wa yau a wurinta shi me laifi ne.

“Kar ki damu, za su kama ni ai, dubuna ce ba ta cika ba. Kuma ko sun zo kama ni zan ce su bari sai na yi ajiya tukkuna, sai su kama ni”

Girar Rabi ta haɗe cike da mamaki.

“Ajiya? A ina?”

Hannunsa ya ɗaga zai taɓa fuskarta, amma sai ta janye fuskar tata, sai ya yi murmushi.

“Well! Yanzu ba za ki gane karatun ba, sai nan da wani lokacin... Kuma miye na kawar da fuskar? A zaune kike a cinyata fa!...”

Tunowa da hakan ya sa ta zabura za ta miƙe, amma sai Zaid ya sa duka ƙarfinsa ya dawo da ita, ita kuma sai ta tura shi, kasancewar ya na riƙe da ita sai ya yi baya tare a ita, bayansa ya faɗa kan gadon, yayin da ita kuma take kwance a ƙirjinsa. Fuskarta yake kallo a hankali, yayin da ita ma take kallon tasa fuskar. Hannunsa na dama ya ɗago ya na kama fuskarta, kafin a hankali ya matso da fuskarsa, ya karkatar da ita gefe kaɗan, leɓɓansa masu ɗumi suka sauƙa a kan nata, ba shiri Rabi ta zaro idanuwanta waje gaba ɗaya, ta saka hannunta ta cukukuye gaban rigarsa, ta ƙanƙame yatsun ƙafarta da suka ɗaga sama saboda kwanciyar da suka yi, ta buɗe bakinta ta na shirin yin magana Zaid ya saka harshensa a cikin bakinta, shi kenan kuma!. Ɗan ragowar hankalin nata da ya rage Raja ya ɓarar mata da shi, ya ɗauketa daga wannan duniyar da muke ciki ya kaita wata can da nisa. Ba ta gane komai, ba kuma ta jin komai sai fitar nunmfashinsa a kan fuskarta, babu abun da take gani sai idanuwansa kusa sosai da nata. Kanta ya cilla zuwa wata nahiyar, ba ta fahimtar komai sai Raja da abin da yake mata a yanzu.

“Rabi'a!”

Jidda ta kuma kiranta a karo na barkatai, bayan da suka baro wurin Zaid, amma Rabi fur taƙi amsa mata, don haushinta take ji, duk abun da ya sameta a yanzu ita ta jawo mata, ita ta kawota wurin har Zaid ya yi amfani da damar hakan ya sumbaceta cikin wannan daren. Ƙwafa ta yi a ranta tana goge bakinta da hannunta, ita ji take ma kamar har yanzu leɓen nasa na kan nata ne, ji take kamar har yanzu harshensa na cikin bakinta, sarƙafe da nata harshen, shi take kamar har yanzu hannunsa na kan ƙugunta ne, ji take kamar har yanzu tana kwance a kan jikinsa ne. Ƙafa ta sa ta yi fatali da wannan tunanin da ya addabeta, a sanda suka iso ɗakinsu. Bargo ta ɗaga sannan ta kwanta kusa da Rhoda wadda ke kwance a kan gadonta ta na sharɓar bacci.

A kai a kai take jan tsaki har da ƙwafa, Jidda na jinta amma ta yi luƙus tana mata dariyar mugunta.




Post a Comment

0 Comments