TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

ZURI'A DAYA PAGE 11-12

 *PAGE* *11*~*12*





 *A yau* ne hutun su ya k'are sai shiri MEENAL takeyi,ga wani irin kewa da take ji,haka dai ta cigaba da shiri, Ummie ta had'a mata wasu abubuwan da zata b'ukata har miyan kaji tayi mata dan dai y'ar nata tayi farin ciki,


Bayan ta shirya ne ta zauna tayi tagumi gaba d'aya sai taji bata son rabuwa da Ummie'n ta, Kaka ne ya shigo gidan ganin halin da take ciki sai ya fara mata nasiha, sannan Ummie ta shigo, ita ma wani iri take ji dauriya kawai take yi,


MEENAL na ganin ta, ta rungume ta tare da fashewa da kuka, cikin muryan kuka tace"Ummie na ki gafarce ni idan nayi miki wani abu?"


Mai da hawayen ta tayi tace"Babu abin da kikayi min fatana Allah ya sa ki gama karatun Nan lafiya Allah yayi Miki albarka ya kare min ke a duk inda kike"


Nan tayi mata nasiha sosai har jikinta yayi sanyi, sannan Kawu Aliyu shi ya rakata har tasha inda ta hau motar Abuja,



Bayan ta shigo cikin Abuja ne,tana cikin taxi sai ganin tayi an had'a go slow, fitowa tayi Dan ganin meke faruwa,


Wani almajiri ne gurgu ne ga wasu mutane sun tsatsaya ana ba mai motan hak'uri wanda ko bud'e glass d'in motan baiyi ba sai driver ne ke faman yin massifa,


K'arasawa MEENAL tayi take tambayar mene ne ya faru,Nan wata tshohuwa ke Mata bayani wai yaron ne yana zai tsalake titi shine Mai motan yazo da gudu ya kwashe shi sai da ya buge shi gashi har yaji ciwo amma Mai motan Sam yace ba ruwan shi sai ma yaron ya biya shi Dan ya bugi wata mota ga yaron Kuma na b'ukatar akai shi hospital Dan yaji ciwo, to duk da driver suke magana akan sai ya Kai yaron hospital,shine yak'i,




Cikin mamaki tace"to ina Mai motan?"


Wani mutum yace"ai yana ciki azalumin"


 MEENAL ta nufa motan tare da dukan glass d'in motan da k'arfi tana cewa sai mutumin ya fito,


Cikin jin haushin wace ke buga mai glass ya sauke glass d'in,masu karatu ko kun san wane ne, ABBA ne,


Kallon shi tayi tace"Alhaji Sam wannan abin da kakeyi ba girman ka bane,ya Kamata ka d'auki yaron nan zuwa hospital gudun Kar wani abu ya same shi"


Cikin fushi yace"ke dan uwarki wa kike gaya ma haka ko gidan ku ba manya ne idiot kawai" ya d'aga glass d'in sama,


Taji haushin yanda ya zage ta sai dai tana tausaya ma yaron nan, k'ara dukan glass d'in tayi tace"Alhaji ka fito ka Kai yaron nan hospital,ka had'a go slow"


Cikin fushi ya fito motan yace"ke wace irin mara tarbiyya ce?"


Tace"tarbiyyan da na samu Mai kyau ne yasa har ina iya yin maka magana,ya Kamata kaji tausayin talakawa Dan abin da kakeyi bai dace ba"


Nan dai mutane suka tasa shi a gaba sai da ya Kai yaron hospital, sosai Abba yaji haushin yarinyan Dan yace Bata da tarbiyya, MEENAL Kuma ta shiga taxi aka nufi makaranta da ita,




NUWAIRA ranar da suka fara lecture taga aminiyar ta taji dad'i Nan sukayi ta hiran yaushe gamo,



Haka sukaci gaba da karatu inda duk weekend  MEENAL a gidan su NUWAIRA takeyin shi,Mom najin haushin ta Amma ba yanda zatayi,Dad koh yana Jin k'aunar MEENAL a zuciyar shi kamar ita din,jinin shi ce kamar ita d'in *ZURI'A D'AYA* suke,



Rana d'aya kwatsam mom ta gano cewa NUWAIRA Bata rabu da KAMAL ba ranta ya b'aci sosai haka tayi ta mata fad'a tace Kuma dole ta rabu shi,dan ko mutuwa zatayi baza ta aura KAMAL ba Dan tafi k'arfin shi,


Hankalin MEENAL ba k'aramin tashi yayi ba da taga halin da NUWAIRA take ciki, ji takeyi duk lokacin da NUWAIRA ke cikin bak'in ciki ita ma tana cikin bak'in ciki haka idan farin ciki NUWAIRA ke ciki to ita ma tana ciki,ji takeyi kamar ita d'in jinin tace, haka ta dinga bata hak'uri tana mata nasiha akan tayi ma iyyayen ta biyyaya Kar ta bijire musu,


Mik'ewa tsaye tayi tace"do you know what you're saying,kina nufin in hak'ura da KAMAL never bana Jin zan daina son KAMAL har k'arshen Rayuwa ta"ta fashe da kuka,


Cikin lalashi tace"nasan baza kiji dad'i ba amma Ina son kawai kiyi ma iyyayen ki biyyaya ne"


Cikin fushi tace"to bazanyi musu ba idan har akan KAMAL ne"ta tashi ta bar bedroom d'in,


Washegari da suka shiga makaranta NUWAIRA ta kira KAMAL a waya cewan yazo su had'u a makaranta, ba tare da b'ata lokaci ba yazo, tana ganin shi ta fashe da kuka tana gaya Mai abin da mom tace Kuma ita gaskiya baza ta iya rabuwa da shi ba, hak'uri ya fara Bata yace tunda mom na ganin haka suyi Dan nesa da juna Dan mom taga kamar sun rabu inyaso sai su cigaba da soyyayar su,


Cikin kuka tace dama kawai ba sonta yake ba Dan Mai zai ce haka,barin gurin tayi da kuka, MEENAL dake gefe duk tausayin NUWAIRA ya Kamata,


KAMAL ne ya k'arasa gurin ta Yana cewa"Dan Allah MEENAL ki taimake Ni ki fahimtar da friend d'in ki,ta fahimci Mai nake nufi"


Murmushi tayi Wanda ya k'ara mata kyau tace"karka damu zanyi mata magana Kuma zata fahimci Mai kake nufi,Ni nasan Kuna k'aunar juna baza ku iya rabuwa ba"


Yaji dad'in kalaman ta a gaskiya takan burge shi yace"okay nagode sosai naji dad'in maganar ki"


Murmushi tayi sukayi sallama ta nufa gurin NUWAIRA dake ta faman kuka a cikin hostel, hak'uri ta fara bata sannan tace ta yarda da abin da KAMAL yace tasan KAMAL ba zai yaudare ta ba,


Cikin kuka ta rungume MEENAL tana cewa"MEENAL Ina son KAMAL ki taimake ni Kar in rasa shi"



Zuciyar MEENAL na wani irin suya da d'aci dan tun ranar da ta had'u da KAMAL take jin k'aunar shi,sai dai bata son ta cin amanar NUWAIRA wace take son ta tsakanin ta da Allah Kuma tana son NUWAIRA kamar yar'uwan ta, tabbas taji zafi yanda zuciyar ta ke son KAMAL Kuma zatayi k'okari taga ta cire son shi a ranta,



Post a Comment

0 Comments