TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Labarin su Page 24

 *LABARINSU*

*©SALMA AHMAD ISAH*

*TAURARI WRITERS*

*24*

~~~

*Handwriting love letters will never go out of style.*

***

*No.86, Garki 2 , Abuja...*

“Adawiyya!”

Raja ya kira sunan yana shiga ɗakinta, saurin juyowa ta yi, yayin da take fitowa daga bayi, kallonsa take kamar yanda shi ma ke kallonta. Sanye take cikin wata green fitted wrap shirt, da wani pink capri pants, gashin kanta nannaɗe a tsakiyar kanta cikin bun.

“Ki shirya za mu fita, ina waje ina jiranki”

Ba tare da ya jira abun da za ta faɗi ba, ya juya ya fita.

“Ina jinki Rhoda”

Muryar Zaid ta faɗi a sanda ya ɗaga kiran Rhoda da ya shigo wayarsa, tsaye yake a compound ɗin gidan, ya jingina da jikin motarsa. Sanye yake cikin wata milk shadda, kansa babu hula, ga wani sunglasses da ya  saka a idonsa, ya kuma sauƙo da shi kan hancinsa.

A hankali yake gyaɗa kansa ya na saurarar bayanin Rhoda, don zuwa yanzu sun kusa kawo ƙarshe  aikin da suke, saboda haka dole su bi a hankali.

Cak, kansa da yake gyaɗawa ya tsaya a iska, sakamakon Rabi'a da ya ga ta fito daga cikin gidan, kasancewar ya na facing kofar entrance ne, sanye take cikin wata atamfa koriya da ratsin milk, ba zai iya faɗar kalar ɗinki da aka mata ba saboda milk ɗin hijabin da ta ɗora a saman kayan, fuskarta babu komai, amma kuma tar yake ganin zanen fuskarta ta cikin hasken ranar da yake haska duniya, kanta a ƙasa take takowa, har ta iso gabansa.

“Ina zuwa Rhoda”

Ba tare da ya jira cewar Rhodan ba ya sauƙe wayar. Hannunsa ya sa yana janyowa Rabi, ta faɗo jikinsa, ba shiri Rabi ta kalli idonsa ta saman glasses ɗin da ya saka, wani kalar kallo yake mata wanda ba za ta iya cewa ga irinsa ba, jikinta ya shiga rawa, a lokaci guda tsigar jikinta ta tashi, ita kam wai yaushe za ta saba?. Da sauri ta juyar da kanta side ɗin me gadi, sai ta ga ba ya ma wurin, su kaɗai ne a tsakar gidan kenan?.

“Irin wannan kyau haka?”

Murmushi ta yi tana sunkuyar da kanta ƙasa.

“You look out of this world 'Yan matana!”

“Na gode... Amma ina za muje?”

Ta tambaya, dan wannan ita ce tambayar da ta yi wa kanta a sanda ya leƙo ya faɗa mata ta shirya.

“Wani wuri... Ko akwai inda kike san zuwa?”

Sai ta gyaɗa kanta.

“Ina san zuwa na ga Anti Saratu, sai kuma Brickhall school, don akwai yarinyar da muke zumunci da ita sosai” 

Zaid ya yi murmushi.

“Ƙanwarki righ?”

Sai ta gyaɗa masa kai ta na mamakin yanda be manta ba.

“Yau de kam ba za mu samu damar zuwa Brickhall ba, sai de Sulejan, amma next fitar da za mu yi sai na kaiki”

Rabi'a ta gyaɗa masa kai. Kuma daga haka suka shiga motar ya tayar suka bar gidan. Jifa-jifa yake mata 'yar hira, amma ita kuma ba ta amsa masa sosai. Don burinta ɗaya, shi ne ta ga inda yace za su je. Kuma sai burin nata ya cika, a sanda ta gansu a Vinca Hospital.

“Ki bita ku je Ammata!”

Umarnin ya biyo baya, lokacin da Zaid ya fito daga office ɗin Huzaifa, bayansa biye da wata nurse, cike da mamaki ta dube shi.

“Ina?”

Ta tambaya, don ita bata gane ba, da shigowarsu asibitin ya zaunar da ita a reception, shi ya sa ba ta san ma me suka tattauna da Dr.n ba,don haka take buƙatar ƙarin bayani.

“Wasu 'yan gwaje-gwaje ne za a miki... Kada ki damu, ki bita kawai!”

Ba dan ta gamsu ba, ta bi bayan nurse ɗin data fara tafiya. 

“Babu wata damuwa... Za ta iya buga ball, amma Zaid wajen mu'amalar aure ka riƙa ɗaga mata ƙafa, dan har yanzu da sauranta, ba ta gama warkewa duka ba, amma nan da wani lokaci za ta dawo normal”

Kalaman Huzaifa kenan gareshi, bayan da aka gama mata gwaje-gwajen da ita har zuwa yanzu ba ta san dalilin yinsu ba, don be ce da ita komai akan hakan ba, duk kuwa da ta tambayeshi. 

Ɗaukin san ganin Anti Saratu ya sa ta ture wata maganar gwaji zuwa bayan ƙwaƙwalwarta, saboda ta ga sanda suka hau titin zuwa Suleja.

*Unguwar Madallah, Suleja, Niger Satate.*

“Zauna”

Cewar Zainab, babbar yayar su Anti Saratu wadda aka mata aure. Mama da ake bawa umarnin ta zauna da ƙyar, don ba ƙaramar azaba take ciki ba. Alhajin da san zuciyarta ya sa ta bi har england shi ne ya haɗata da jafa'ai kala-kala, a da idan zai sadu da ita ta gaba yake saduwa da ita kawai, amma bayan zuwansu england sai ya lakaɗa mata ɗan bazan duka, sannan ya sadu da ita ta baya, a cewarsa wai bokansa ne ya ba shi wannan laƙanin. Haka ya yi ta azabtar da ita na tsawon wannan wattanin da ta yi a wurinsa.

Bayan da ya gama da ita, ya sa aka hankaɗota Nigeria, bayan da ya haɗata da ciki, ga kuma cuta me karya garkuwar jiki da ya bar mata tukuci.

Yanzu haka dawowarsu kenan daga asibiti, sun je an ɗorata akan magunguna, zuwa yanzu ta gane cewa Allah ɗaya ne, kuma hanyar shiriya ɗaya ce, duk wanda ya bi Allah ya dace ya kuma tsira, wanda kuwa yace ba haka ba shi zai jawa kansa asara tun a duniya.

“Sannu Mama”

Cewar Saratu cike da tausayawa, Mama babu bakin magana sai alama ta mata da kai, Anti Zainab ta zauna a gefenta ita ma tana ta jera mata sannun, Habiba na daga kan kujera tana matsar ƙwalla, koma me ya samu Mama ita ce wadda ta jawo mata, ita ta nuna mata hanyar bin maza, har ta kaisu ga wannan hali, kaiconta, kaicon rayuwa irin tata!.

Ɗan Lami ne ya fito daga ɗakinsa yana kallonsu su duka. Kansa ya girgiza cike da nadama, a sanda ya kalli Mama, ya tabbatar da koma miye ya samu 'ya'yansa shi ma akwai nasa sa hannun a ciki, shi ma ya bada gudunmawa ta musamman a lalacewar tarbiyyar yaran gidansa. A matsayinsa na uba, kamata ya yi a ce yana saka ido akan ko wace harka dake kai kawo a cikin gidansa, ya kamata ace shi ne tsaye a kan ko wata harka ta gidan, sannan nauyin ci, sha da suturarsu duka ya rataya a wuyansa ne, amma sai ya yi burus da su, ya kama wata hanya da ba ta haifar masa da ɗa ne ido ba. Zuwa yanzu ya yi nadamar abubuwa da dama da ya aikata a rayuwarsa, kuma hakan ya biyo baya ne, sakamakon nasihar da wannan matashin me kama da matarsa da kuma 'yarsa ya masa. Sosai matashin ya ja hankalinsa kan abubuwan da yake basu da kyau, kamata ya yi ace ya kama sana'a yana kula da gidansa da kansa, ba wai tsinduma cikin harkar caca da bin matan banza ba. Kuma matashin be sallame shi ba sai da ya danƙa masa jari me tsoka, ya shawarce shi da ya kama sana'a, sannan abun da yake ƙoƙarin yi kenan, don hatta da wannan ɗawainiyar asibitin na Mama shi ne a kai. Ya kuma hana habiba saida wannan finiason da take, duka nauyin gidan ya dawo kansa.

“Sannu kin ji Mama!”

Ya faɗi yana jan kujera tare da zama, shi ma kai ta gyaɗa tana kallonsa.

Kamar daga sama suka ji sallamar wata murya me kama da ta Rabi'a. Cikin sauri su duka suka kalli ƙofar soron gidan. Ilai kuwa, Rabin suka gani ta shigo  cikin gidan. Farin cikin ganin Rabi ya sa Saratu miƙewa da gudu ta yi kanta suka rungume juna.

Tun daga Habiba, Mama, Ɗan Lami har da Zainab kallon sabuwar Rabin suke, ba wai ƙiba ta yi ba, don idan aka dangana da jikinta na da sai de ace ta rame, amma ta yi wani irin fari, ta ƙara haske, yanayin fatarta kawai zai sheda maka da irin sauyin rayuwar da ta samu. 

“Ina sirikin nawa?”

Rabi ta yi murmushi tana sunkuyar da kanta.

“Yana waje”

“To shigo mana, bari shi ma na masa iso”

Sai a lokacin idon Rabi ya sauƙa a kansu sauran mutanen dake tsakar gidan, fuskar Ɗan Lami da ta kalla ce ta tuno mata da kashedinsa gareta, na kar ta ƙara dawowa gidansa, hakan ya sa fara'ar fuskarta ta ɗauke ɗip, sannan ta juya da sauri za ta bar gidan.

“Tsaya Rabi'a”

Tsayawar ta yi, saboda jin amon muryar mahaifinta, an ya kiwa yau ba mafarki take ido biyu ba?, to in ba haka ba, ita de tun tasowarta da mahaifinta, ba za ta iya cewa ga rana ɗaya da ta ji ya yi magana cikin nutsuwa kamar haka ba, an ya ma kuwa shi ne?.

A hankali ta juyo ta kallesu, zuwa lokacin su duka sun miƙe tsaye, sai a yanzu ma ta lura da Mama wadda ke zaune a kan tabarma, ita sam ba ya ma ganeta ba, yanzu wannan Mama ce ta zama haka?, oh!, rayuwa kenan. Sai kuma Habiba, wadda ta rame, ga kuma tabbuna a jikinta ta ko ta ina.

“Ki dawo Rabi, nan ɗin gidankimu ne”

Zaune take a gefen Anti Saratu, yayin da Mama da Zainab ke zaune a kan tabarma, Habiba na kan kujera, haka ma Ɗan Lami, daga can gefe kan wata sabuwar sallaya kuma Zaid ne zaune, ya sunkuyar da kansa ƙasa.

Ɗan Lami kallonsa kawai yake yana ƙarawa, ashe de wannan matashin sirikinsa ne?, ashe shi ne yake auren 'yarsa Rabi?!, Ashe e kuma shi ne jinin Rabi 'yar uwar Maryam, me sunan Rabi 'yarsa?. Allah kenan.

Rabi ta share wata ƙwallar da ta silalo daga idonta, wai yau ita ce Abbansu da Habiba suke neman yafiyarta, ita kuwa me za ta iya cewa?. Ba ta da wani abun cewa face ta godewa Allah.

“Na yafe muku Abba, muma Allah ya yafe mana”

Ta furta muryarta a raunane. Habiba ma ta share hawaye tana saka mata albarka, Mama ma kallonta kawai take, tana san tace ita ma Rabin ta yafe mata, amma babu hali.

*06:50 PM.*

Sai a lokacin suka samu damar dawowa gida, Rabi ce a kan gaba, yayin da shi kuma Zaid ke biye da ita, ita ta buɗe ƙofar falon ta shiga, sannan shi ma ya shigo, tsayawa ya yi kukkuna fitilun falon dan babu haske sosai. Kuma fitilun ne suka haska masa ita tar, tsaye a tsakiyar falon tana dubansa, idanuwanta sun cika da ƙwalla. A hankali ya aje jakar kayanta data karɓo a gidansu. Kafin ya ƙara wani yinƙiro, Rabi'a ta tako ta rungime shi tana sakin kuka.

“Na gode Raj, Na gode da duk wani abu da ka san ka taɓa min”

Zaid ya yi murmushi yana shafa kanta.

“Ammatan Raja babu komai fa, babban surprise na tafe nan da next week nan”

Ba komai ta fahimta a kalaman nasa ba, amma ko ba komai sun mata daɗin sauraro, dan haka ta ƙara narkewa a jikinsa tana kukanta.

*No. 213, Naf belly Estate, Asokoro, Abuja.*

MISHAL POV.

Zaune take a falon Annan suna hira. Yau tun safe Kuliya ya kawota, tare da faɗa mata cewar bayan sallahr magrib zai dawo ya ɗauketa. Tana cikin farin ciki yau, dan sai da ya biya da ita gidan yayanta, suka gana da Daala da kuma su Baba Lami, duk da ba su tarar da matar gidan ba, a cewar Baba Lami wai ta fita unguwa ne. 

Da sallama aka turo ƙofar falon, hakan ya sa ita da Anna kallon ƙofar. Siyama ce ta shigo tana ɗan murmushi, sai de kuma cikin sakan ɗaya wannan murmushin ya ɓace daga fuskarta, sakamakon arba da Mishal da ta yi, saboda ba ta manta karonsa ba. 

“Ah-ah, Siyam, ƙaraso mana”

Siyama ta haɗiyi miyau tana ƙarasowa cikin falon, gaba ɗaya yanayinta kaɗai zai fallasa sirrin zuciyarta. A ɗarare ta zauna kusa da Annan tana satar kallon Mishal wadda ke jifanta da murmushin ƙeta.

“A... Anna ina yini”

“Ke! Lafiyarki kuwa?”

Siyama ta yi saurin girgiza kanta, sai kuma ta gyaɗa shi. Har wata zufa take don tashin hankali.

“A'a Siyama, wannan yanayin naki ba lafiya ba, bari na samo miki wani abun sha”

Annan ta faɗi tana miƙewa, tare da nufar hanyar kitchen, da sauri Siyama ta bi bayanta, don zama da Mishal inuwa ɗaya ba nata ba ne, Mishal ta wuce tunaninta, saboda haka gwara ta bar mata falon, kafin ta laƙa mata sharri kan tana shaƙar iskar da ta furzar.

Mishal ta ƙara bajewa a kan kujera tana murmushi, saboda ta tuna abun da ya faru tsakaninta da su last time!.

***

“Me kuke nema?”

Muryar Mishal ta tambaya a waccan ranar, lokacin da Siyama da Karima suka shigo gidanta.

“Rayuwarki muke nema!”

Karima ta amsa mata a hassale tana shigowa cikin falon, duk da Mishal ta tsorota amma ba ta bayyana tsoronta ba, sai ta ɓoye kayanta a cikinta.

“Me ya sa kuke neman rayuwata?”

Ta tambaya tana sakin tsintaiyar hannunta.

“Saboda kin shiga tsakanina da Kuliya, kin raba ni da Kuliya.Ni kuma ina sansa, dan haka ba zan bari ina ji ina gani ki raba ni da shi ba”

Nan take wasu ƙofafi suka buɗe a ƙirjin Mishal, kishi ya soma kamata, wani abu me kama da wuta ya shiga ruruwa a cikin ranta.

“Mijina kike so?”

Ta tambaya ta na nuna kanta. Cike da gadara Siyama tace.

“Ƙwarai kuwa, mijinki nake so, kuma tun kafin ya sanki nake sansa. Dan haka na zo ɗaukar mataki”

Ta ƙarashe tana fitar da wuƙa daga jakarta, Mishal ta zabura ta finciko wayar tvnsu, ta hau dukan Karima da Siyama, abun su kansu ba ƙaramin mamaki ya basu ba, dan ba su taɓa zaton ƙaramar yarinya kamarta za ta iya aikata hakan ba. Dukansu take kamar wadda Allah ya aikota, su kuma banda kururuwa da ihu babu abun da suke.

Jin sautin dirin motar Kuliya ne ya sa Mishal yada wayar, ta leƙa ta wundo ta ga tabbas shi ne, ta dawo da baya, ta buga kanta a jikin bango, tare da fasa ƙara, wanda ta karaɗe gidan baki ɗaya.

*You are not hard to love; You've just run into a few who didn't know how to...*

***

*No.86, Garki 2, Abuja...*

RABI'A POV.

Kwance take cikin style ɗin motsa jiki na plank, tana kan tabarmar motsa jiki ne, a cikin gym ɗin gidan. A rannan da Zaid ya kaiya ganin likita ya shawarceta da yawaita motsa jiki, kuma hakan ne ya sa Zaid ɗin kawo mata mashinan motsa jiki.

Sanye take da wani baƙin leggings, sai wata yar siririyar tanktop da ta saka. Daga gefenta kuma ruwan da ta tanada ne dan sha a sa'ilin da ta gaji. Ba ta yi tsammani ba kawai ta ga ya shigo, hakan ya sa ta kusa tuntsirawa daga yanda take, ba shiri ta tashi daga kwanciyat plank ɗin ta zauna a kan tabarmar tana kallonsa. Sweat pants da wata singlet ne a jikinsa, hannunsa na hagu riƙe da mug.

“Kai kuma me ka shigo yi a nan?”

Kamar wani me neman wanda zai ba shi amsa haka ya juya ya kalli bayansa sannan ya juyo ya kalleta.

“Motsa jiki mana” ya amsa matavikin ɗage gira, na shi bai ga lefin abun da ya yi ba.

“Motsa jiki?”

“Ƙwarai.... Ko da an ƙa'ide cewar maza ba sa yi, mata ne kawai ke yi”

Rabi'a ta girgiza kanta, dan ta ga alamar ba motsa jikin ya zo ba, neman magana ne kawai irin nasa. Dan haka ta juya abunta tana sauya salon motsa jikin nata zuwa cat cow pose. A duk sanda za ta sunkuya cikin motsa jikin sai ta kalli Zaid dake bayanta.

Zaid ya yi murmushi ya na aje mug ɗin hannunsa a kan wata chest drawer, sannan ya tsaya yana kallon kansa ta cikin mirrors ɗin dake zagaye da gym ɗin. Kafaɗarsa ta dama ya ɗaga yana wani jujjuyawa. Kafin ya ɗaga hannayensa ya na auna girman muscle ɗinsa. Duk abun da yake Rabi na leƙensa ta ƙasan ƙafafunta.

Kamar da aka ce ya kalleta ta cikin mirrorn, karaf suka haɗa ido, da sauri Rabi ta waske ta ci gaba da cat cow pose ɗinta. Zaid ya kuma yin wani murmushin yana kama rigarsa ta ƙasa, sannan a hankali ya cireta.

Tsabar gulma Rabi ba ta san sanda ta dungura ta ka ba, saboda wasu tabbubbuna da ta ga a bayansa, ga kuma tsayawar da ya yi babu riga a jikinsa, wani abu da sam bata so, shi kuma ga shi kamar wanda aka yiwa asirin rashin zama da riga, kwata-kwata bay a san zama da riga a jikinsa in dai yana gida.

“Wai dan Allah Raj me ya sa ba ka da kunya ne?”

Rabi ta tambaya tana rufe idonta da hannunta, yayin da ta yi zaman cin tuwo bayan da ta dungura. Zaid ya juyo ya kalleta.

“Me kuma na yi?”

“Dan Allah ka sa rigarka?”

Ta faɗi tana ƙara rufe idon nata. Dariya ya yi mara sauti ya na cillar da rigar gefe, sannan a hankali cikin takun sanɗa ya isa inda take ya zauna a gabanta, har gwiwowunsu na gogar na juna.

“To na meda, buɗe ido naki”

“Ka ta babbatar?”

Yana ƙunshe dariya yace.

“Dubu bisa ɗari”

Kamar me tsoron ganin aljanu haka ta sauƙe hannunta, ai kuwa ta yi kyakkyawan gani, dan shi ɗin ne zaune a gabanta, babu riga a jikinsa, ga wannan chain ɗin sarƙar da ta saba gani a wuyansa ya kwanta a ƙirjinsa, waɗanan tabbubbuna na jikinsa suka mata maraba lale!. Zabura ta yi za ta miƙe, kuma kafin ta miƙe ɗin ya sa hannunsa ya janyota, bata faɗa ko ina ba sai kansa, hannayenta naɗe a ƙirjinsa, yayin da shi kuma ya saka hannunsa ɗaya ta bayansa. 

Ta zazzaro idanunwata tana kallonsa, kamar wadda aka tunawa yadda jikinsa yake a lokacin ta yi saurin kulle idonta.

Zaid ya yi dariya, a wannan karon me sauti ya yi, sannan ya mannata da jikinsa yana rungumewa, har zuwa lokacin idonta a rufe.

“To wai miye na jin kunyar?. Na ga kin...”

Be ƙarashe ba saboda dukan da Rabi ta kaiwa bakinsa, dan ta san me yake shirin faɗa, shi ya sa a ko da yaushe take faɗin ba shi da kunya, bakin nasa ya dafe yana mata dariya.

Da sauri ta miƙe daga kansa ta fita da gudu ta bar masa gym ɗin. Dan da ma kawai ta ɗan shigo dan ta motsa jikin nata ko kaɗan ne, saboda yau za'a ɗaura auren Anti Saratu, kasancewar babu wani shagali ya sa bata shirya da wuri ba, don Abbansu yace daga zarar an ɗaura za a kaita ɗakinta, babu wata bidi'a da za ayi.

Zaid na dariya ya miƙe zai bi bayanta, wayar dake cikin aljihunsa ce ta yi ƙara, hakan ya sa ya fasa binta ya zaro wayar ya ɗaga kira da sauri, ganin lambar abokan aikinsa, kuma wakilan da ya naɗa dan kamo Alhaji Bala da usman, dan tun daren jiya aka basu izinin kamu.

“Sir, mun kamosu, yanzu haka mun wuce headquarter da su!”

Abun da na cikin wayar ya fara faɗi kenan, hakan ya sa Zaid ya ɗaga kansa sama yana lasar lips ɗinsa.

“Na gane, anjima zan samu na leƙo”

“Ok sir”

Daga haka ya sauƙe wayar, shi kenan, duk wannan shekarun da ya kwashe cikin wannan aikin sun zo ƙarshe, assignment ya ƙare, komai ma ya ƙare, yanzu lokaci ne na fara sabuwar rayuwa tare da Adawiyyansa, lokaci ne da Rhoda za ta sake sabuwar rayuwa, lokaci ne da shi kansa zai huta, dan kuwa ba zai karɓi wani sabon aiki kwana kusa ba, zai ɗauki hutu ne dan ya kula da Ammatansa, zai ba ta lokacinsa duka, zai kuma zauna da ita na tsawon lokuta. 

Zuwa yanzu abun da ya rage a aikin nasu kaɗan ne, abun da ya rage bai fi saura ba, dan tun da har an kama Alhaji Bala to an tsallake babban tudun, saura da me kuma?; Alhaji Bala ya amsa lefinsa, sannan ya bayyana sunayen abokan harƙallarsa da kansa, duk kuwa da su ma kansu sun san wasu daga ciki.

Usman da abokansa kuma shi ya san yanda zai yi da su, dan kuwa ɗaya bayan ɗaya ya sa aka kamo su, kuma shi ya san kalar hukuncin da zai musu. Kafin su shiga kotu

“Sai yaushe kuma?”

Cewar Zaid, yayin da motarsa ta yi parking a farkon lungun gidan su Rabi. Rabi da ta haɗe cikin wani kyakkyawan pink lace da bluen hijabinta ta juyo ta kalleshi.

“Sai ka zo ɗauka na mana. za ka je wurin ɗaurin auren ne?”

Ta tambaya tana ƙare masa kallo, dan kuwa yau ya fi mata kyau fiye da ko yaushe, sanye yake cikin wata brown color shadda, ga golden hular dake kansa, ya yi kyau kamar wani ango.

Zaid ya ɗaga kafaɗarsa ta dama ya na gyaɗa mata kai tare da faɗin.

“Insha-Allah. Daga nan ma ai can zan wuce, sai de an jima kawai”

Ta gyaɗa masa kai tana shirin fita daga motar, caraf Zaid ya riƙo hannunta.

“Tafiya za ki yi ba tare da kin min...”

Dukan ta kai masa a baki, ya kaucewa ya na dariya.

“Wai ni ko me zan yi sai an dake ni?”

Rabi ta watsa masa harar wasa.

“Idan baka so ina dukanka ka dena rashin kunya”

Ya buɗe baki yana kama haɓa.

“Ni ne ban da kunyar?”

“To kunyar ce da kai?”

“Allah kuwa Ammata ina da kunya sosai, kowa yana darajanta ni, kowa yana bani kima, ina da kwarjini a idon mutane. Kuma duk da haka sai ke ki ce ba ni da kunya?”

“To idan baka so ina faɗa maka haka ka dena min irin waɗana zantuttukan”

“Wasu zantuttuka ke nan?”

Ya tambaya cikin ɗage gira, har da mata alama da hannu, Rabi ta ja tsaki, dan ta lura da yau 'yan neman tsokanar ne a kusa, gwara ta rabu da shi ta yi tafiyarta.

“Kin ɗau ba shi, idan muka koma gida sai na fanshe da...”

Wani dukan ta ƙara kaiwa bakinsa amma sai ya dafe bakin nasa yana dariya.

“Yi haƙuri damisar Raja, takawarki lafiya uwar gidan Zaid, maman Aliyu da Maryam!”

Baki sake Rabi'a take kallonsa, wato ita nan har an gama zaɓa mata sunan 'ya'yan da zata haifa?. Kuma maganar tasa sai ta tuno mata da shi, Aliyu, mijin Mishal, ɗan uwansa. Ya kamata ace zuwa yanzu ta san meke faruwa a tsakaninsu, amma ba komai za ta tambaya. Motar ta buɗe ta fita, har ta shige lungunsu Zaid na mata dariya, nan duniya babu abun da ke sashi mishaɗi face zolayarta, in dai zai zolayeta sai ta yi fushi, shi kuma fushin nata me ke mugun aika shi duniyar nishaɗi.

Motar tasa ya tayar ya yi gaba, dan masallacin da za'a ɗaura auren a gaba yake. Bayan an ɗaura aure, ya yi wa Abba da Fu'ad barka, ya basu uzurin akwai aikin dake jirans, sannan ya samu ya sulale ya gudu. Gida ya koma ya je ya shirya cikin suit, kai tsaye daga nan ya nufi DSS headquarter.

*DSS Headquarter, Maitama Evenue, Abuja.*

“Sun yi bayani?”

Muryar Zaid ta tambaya, yayin da yake tsaye ya na kallon Usman da abokansu huɗu dake cikin ɗakin horo. Duk sun fita hayyacinsu, dan ba ƙaramin duka suka sha ba. Matemakinsa ya amsa masa da.

“A'a Sir, sun ƙi yin magana”

Ya juyo ya ɗauke idonsa daga kan glashin da yake iya kallon su Usman ta ciki, ya kalli matemakin nasa me suna Marcus. Sannan ya juya ya kalli Rhoda dake tsaye a ɗayan gefen nasa.

“Shi kuma Alhaji Balan fa?”

Rhoda ta amsa masa da.

“Ya magantu, bugu ɗaya ya ji ya saki baki ya shiga koro bayanai”

Kannsa ya gyaɗa yana ci gaba da kallon su Usman, hannayensa rungume a ƙirjinsa.

“Ina Joseph?”

Ya tambaya ba tare da ya kalli ɗaya daga cikinsu ba, Marcus ne ya amsa masa da.

“Sun fita wani aiki...”

Bai jira Marcus ɗin ya gama rufe bakinsa ba, ya fara takawa zuwa ƙofar shiga cikin ɗakin horon. Rhoda ta girgiza kanta, dan ta san ba zai ragawa su Usman ba.

Ilai kuwa, ya na shiga ya bi ɗakin da kallo, zaratan mazan dake tsaye a ɗakin hannayensu riƙe da sandunan duka suka sara masa. Ba tare da ya amsa gaisuwar tasu ba ya kalli sandar dukan hannun guda daga cikinsu.

“Da wannan kuka dake su?”

Ya tambaya yana raba idonsa a kansu. Ɗaya daga ciki ya amsa masa da.

“Yes sir”

Hannun rigarsa ya shiga tattarewa ya na faɗin.

“Ina kwa za su yi magana. Wannan ai ba duka suka sha ba... Marcus!”

Ya ƙarashe yana ƙwalawa Marcus dake tsaye a waje kira. Da hanzari Marcus ya shiga ɗakin yana amsa kiran.

”A kawo min lantarki!”

Cike da iko isa da jzza ya yi maganar, ta yanda babu wanda ya isa ya tanka masa a cikinsu. Marcus ya ammsa yana fita. Shi kuma Zaid ya ja ɗaya daga cikin kujerun ɗakin ya zauna a yana facing su Usman, waɗanda suka jigata sosai, dan ko ɗan yatsa babu wanda ya isa ya ɗaga a cikinsu.

Jim kaɗan Marcus ya dawo da wata na'ura, shi da kansa ya jonata a ɗakin, sannan ya miƙawa Zaid wasu abubuwa guda biyu, masu suffar biro, waɗanda ke jone jikin wannan na'urar da ya jona. Yana kallon Usman ya miƙa hannunsa ya karɓa. Sannan ya karawa Usman  saitin ƙirjinsa, wata zabura da Usman ɗin ya yi ce tasa sauran ma dawowa cikin hayyacinsu, karkarwa yake kamar wani me farfaɗiya, ga bakunansu a kulle, babu damar magana, ihun ma ba sosai ake jiyowa ba, babu ko ɗugon tausayi haka Zaid ya ci gaba da zona masa shocking ɗin nan a jikinsa, dan babu abun da yake hangowa a idonsa face Rabi'a, sanda ya sameta kwance a gadon asibiti, sai kuma hoton result ɗinta da Huzaifa ya danƙa masa.

Kan kace wani wani abu Usman ya suma kusan sau huɗu, sai da ya kusan aika ɗan mutane lahira kafin ya ƙyaleshi, ya dawo kan Jaz, dake kusa da kujerar Usman ɗin, haka ya yi ta gana masa tasa azabar. Sauran tun kafin a zo kansu suka fara shan jinin jikinsu, J boy harda fitsari a wando. Bai ƙyalesu ba saida ya ɗanɗanawa ko wannensu, sannan ya sa aka kawo masa kyakkyawan madoki, ya shiga dukansu yana ƙarawa, saboda gaba ɗaya zuciyarsa ta bushe, ba ya jin ko ɗigon tausayinsu, don suma ba su ji tausayin Adawiyya ba sanda za su haike mata.

Ganin Zaid niyyar kashesu yake ya sa Rhoda saurin shigowa cikin ɗakin tare da faɗin:

“Ya isa haka Zaid...!”

Cak sandar da ha ɗaga dan bugawa Usman a ka ta tsaya a iska, dan niyyarsa ita ce ya masa wani kyakkyawan bugu a tsakiyar kansa, wanda zaisa ya tuno da auren uwarsa. Dan duk cikinsu ya fi jin haushin Usman, saboda shi ya fi kowa irin wannan halin zalincin a cikinsu.

A fusace ya cillar da madokin yana huci, idanuwansa sun firfito waje, ya danne haƙwaransa na ƙasa da na saman, kallonsa kawai idan mutum ya yi sai ya bashi tsoro, dan shi sam bai iya fusta ba.

Kafaɗarsa ya ɗaga yana sharce gumi. Baya ya juya musu baya yana maida numfashi. Ganin kamar Usman na san magana ya sa Rhoda isa gareshi cikin hanzari, tare da buɗe masa bakinsa. Idanuwansa ya lumshe yana buɗewa, dan sam baya cikin hayyacinsa, ya jikkata sosai ba kaɗan ba.

“Wallahi... Mu... Mu ne... Mu... Ne muka... Muka mata f... Fyaɗe!”

Wani irin duka Zaid ya kaiwa katangar dake gabansa kamar zai fasata, a fusace ya juyo zai  kuma dawowa kansu, amma Rhoda ta yi saurin riƙe shi.

“Ya isa haka Zaid.... Ya isa, tun da sun riga da sun amsa lefukansu, ka ƙyalesu kawai!”

Leɓensa na ƙasa ya ciza ya na huci, ji yake kamar wuta ce ke ci a ƙirjinsa, kamar idan be daki bayin Allahn nan ba ba zai huce ba.

KULIYA POV.

“An ce yau Lion ya kawo ziyara fa!”

Da sauri ya ɗauke idonsa daga kan laptop ɗin gabansa ya kalli Symon dake wannan batu. Symon ya gyaɗa masa kai.

“Da gaske nake, haka na ji ɗazu ana ƙus-ƙus ɗin zancen... Amma an ce bai jima ba ya tafi, kuma ma wai na ji ana cewa ya kawo ƙarshen assignment ɗinsa ne”

Ba shiri Kuliya ya saki wani murmushi, dan kuwa burinsa na gab da cika, Chidera ya masa alƙawarin daga zarar Lion ya kammala assignment ɗinsa zai haɗasu. Har ya tashi daga aikin ransa ƙal, haka ya nufi gida cikin farin ciki.

Da sallama a bakinsa ya tura ƙofar falon gidan nasa. Mishal dake zaune a kan kujera tana rubutu ta aje rubutun ta iyo kansa da gudu, shi ma yana dariya ya buɗe mata hannyensa ta shige jikinsa, harda ɗagata sama, dan tsabar farin cikin da yake ciki.

“Wannan farin cikin fa?... Na menene?”

Mishal ta tambaya a sanda ya sauƙeta.

Hancinta ya ɗan ja yana murmushi.

“Kin tuna da labarin wani lion da na baki?”

Ta ɗan yi shiru tana san tunawa, can kuma sai tace.

“Haaaa! Na tuna... Ko ba labarin wannan zakin da yake cinye 'ya'yan wata barewa ba?... Wannan wanda ka karanta min a cikin littafin stories ɗin nan?.”

Kuliya ya dunguri kanta yana faɗin.

“Silly girl, ba shi ba, wannan role model ɗin nawa da na taɓa baki labari, ki tuna”

“Eh yanzu na gano... Kun haɗu ne?”

Kansa ya girgiza yana ɗaga kafaɗarsa.

“A'a, da yarar Allah mun kusa haɗuwa dai”

“To Allah ya yarda... Yanzu ka je ka yi wanka, na tanadar maka abincin da ka fi so”

Peck ya mata a kumatu yana sakinta.

“Ok bari na yi sauri”

Mishal ta bi bayansa da kallo tana murmushi.

*No.86, Garki 2, Abuja...*

*10:30pm*

RABI POV.

Tana daga zaune a falo tana warewa Zaid kayan bikin da Umma ta bata ta kawo masa, dubulan da alkaki ne, cikin wata farar roba guda ta bata tace ta kawowa Zaid.

Ta kasa misalta kalar farin cikin da take ciki a yau, dan sai a yanzu take ganin rayuwarta ta dawo dai-dai, rayuwarta ta hau seti, wani irin setin da a da ma bata dedetu kamar yanzu ba, Allah ya shirya Abbansu, Habiba ta gane kurenta, Mama ta yi nadama, Allah ya bata miji na gari, budu da ƙari yau an ɗaurawa Anti Saratu aure da mijin da take so, kuma a yau ita ma anti Saratun za ta kwanan gidan mijinta, menene ya fi wannan daɗi?.

Jin an banko ƙofa yasa ta miƙe da sauri tana kallon side ɗin ƙofar. Ganin Zaid ya shigo cikin wani irin yanayi ya sa da sauri ta nufe shi tana faɗin.

“Raj!... Me ya sameka?”

Tsayawa ta yi a gabansa tana dubansa, kallonta kawai yake da idanuwansa da suka kusan lumshewa duka. Gaba ɗaya oxford shirt ɗin jikinsa ta jiƙe da gumi, tie ɗin ya warware a wuyansa, ga kuma suit ɗin riƙe a hannunsa. Ba tare da ta ankata ba ta ga ya saki suit ɗin daga hannunsa, sannan ya fincikitota ta faɗo jikinsa, ƙanƙameta ya yi kamar me shirin tsaga ƙasusuwanta.

Wannan sanyi Rabi ta ji ya shiga bin jikinta, ga wata siriryar iska da ta ke bi ta saman kunenta. A hankali ta ɗago da hannunta ɗaya ta ɗora shi a kan bayansa, ɗayan kuma ta ɗora shi a kansa.

“Menene ya faru?”

Ta tambaya da ƙyar. Saboda shirin zamewa ta faɗi ƙasa da take. Zaid ya ƙara matseta a jikinsa ya na faɗin.

“Na je Madallah, sai suka ce min wai kina gida”

Kanta ta gyaɗa tana shafa bayansa.

“Umm... 'Yan kaiwa amarya na bi, kuma da muka gama da gidan amaryar sai kawai na ce su kawoni gida, na san babu abinci a gidan, shi ya sa na dawo na maka girki”

Sai ya saketa yana kallon fuskarta.

“Ammata!”

Rabi ta amsa tana kewaya hannayenta ta bayansa.

“Dan Allah kada ki rabu da ni... Ko me zai faru ki zauna da ni... Dan Allah!”

Rabi ta girgiza masa kai.

“Ban taɓa tunani rabuwa da kai ba Raj... Za ku rayu tare har zuwa lokacin mutuwar ɗayanmu”

Haɓarta ya kama yana matsar da fuskarsa kusa da tata.

“Kin tabbata?”

Ta gyaɗa masa kai, wanda yasa nasa kan ma kotsawa, dan zuwa lokacin ya haɗe goshinsa da nata yana goga mata hancinsa a kan nata. Rabi ta lumshe idonta a hankali, sakamakon ɗumin leɓensa da ya sauƙa kan nata. Zaid ya soma kissing ɗinta kamar yau ya fara. A hankali Rabi ta ture shi tana faɗin.

“Ka je ka yi wanka”

Sai ya girgiza mata kai yana ƙara kamo hannunta.

“No... I just need you”

Ya ƙarashe yana mannata da jikinsa. Rabi ta kuma tureshi.

“Ka fara zuwa ka yi wanka”

Sai ya shinshina jikinsa yana faɗin.

“Wari kika ji ina yi ne?”

Duka ta kai masa a ƙirji tana faɗin.

“Haka na ce?”

Hannunta ya ƙara kamawa ya mayar kan ƙirjin nasa.

“Ba haka kika ce ba...”

“To ka je ka yi wanka”

Kansa ya gyaɗa yana sakin hannunta. Sannan ya kama hanyar stairs.




Post a Comment

0 Comments