TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Labarin su Page 27

 *LABARINSU*

*©SALMA AHMAD ISAH*

*TAURARI WRITERS*

*27*

*END*

~~~

*“How sad to miss someone, who you know doesn't miss you...*

***

*No.86, Garki 2, Abuja...*

RABI POV.

Tun da ta tashi sallahr asuba bata koma bacci ba. Amma da Mishal da ba ta samu bacci jiya da daddrae ba ta koma baccin. Sai Rhoda a bata farka ba. Gyaran gidan ta shiga yi. Bayan ta gama kuma ta ɗora girki, bayan nasu wanda za suci, har da na su Zaid ta girka, ta juye musu nasu a cikin was warmers masu kyau, ta saka a basket ta aje.

Nasu kuna ta kai kan danning ta jera. Ɗakinta ta koma, ta je ta taso Mishal da Rhoda, tace musu su tashi su yi wanka. Ita kuma ta fice ta shiga ɗakin Zaid. A can ta yi wanka, ta ɗauki ɗaya daga cikin kayanta da suke can ta saka, ta fito.

Sanda ta koma ɗakin nata, Mishal ce a banɗakin tana wanka, ita kuma Rhoda ta yi wanka tana shafa mai.

“Rhoda kaya na kuwa zai miki?”

Ta tambaya tana buɗe lokokinta. Rhoda ta juyo ta kalleta.

“Ai ba zai iyu na saka kayanki ba ma, yau za mu shiga kotu, dan haka kayan aiki ya kamata na saka, so ba sai na sauya kaya ba,zan tafi da wannan, daga can kuma sai na wuce Kaura”

Cike da gamsuwa Rabi ta rufe lokarta, bayan da ta ɗaukowa Mishal wata doguwar rigar atamafa da take da tabbacin za ta mata dai-dai, dan kansu ɗaya da wadda ta bata ta saka jiya.

Zama ta yi a bakin gadonta,tana buɗewa wayarta dan kiran Zaid, sai de kuma wayar har ta yi ringing ta katse bai ɗaga ba. Sai kawai ta aje wayar, don ta san da ma balalle ya ɗaga ɗin ba.

A lokacin Mishal ta fito daga banɗakin, jikinta ɗaure da towel. 

“Ga kaya, sai ki sauya”

Rabi'a ta faɗi tana mata nuni da doguwar rigar atamfar dake aje a kan gado, Mishal ta kalli kayan, sannan ta ƙaraso ta ɗauka, ta koma banɗakin dan sakawa.

Cike da jin tausayinta Rabi ta girgiza kai, idanunwata ba ƙaramin kumbura suka yi ba, saboda tsabar kuka.Wayar Rhoda ce ta yi ringing, hakan ya sa ta ɗaga wayar tana fita waje, dan kiran daga headquarter su ne.

Bayan wani lokaci, Mishal ta fito daga banɗakin, jikinta sanye da doguwar rigar. Ba tare da ta saka komai a jikinta ba ta zauna a kusa da Rabi. Fuskar nan cike da damuwa, kana ganinta za ka san cewa tana cikin tashin hankali, idonta ya jeme, fuskar nan ta yi jajir.

“Ga hijabi ki saka”

Kallon hijabin ta yi, kafin ta karɓa tana miƙewa tsaye.

“Mu je mu ci abincin to”

Rabi ta faɗi tana dafata, bayan da ta gama saka hijabin. A falo suka haɗu da Rhoda, wadda ta gama wayar da ta tafi yi, daga nan suka wuce danning suka ci abinci. Kafin suka shirya fita daga gidan.

*Hymill Specialist Hospital, Life camp, Abuja.*

KULIYA POV.

Zaune yake daga bakin gadon marasa lafiyar dake dakin da aka kwantar da shi. Ya zuro ƙafafunsa ƙasan gadon. Jikinsa sanye da kayan marasa kafiya da ake bawa pertinent ɗin asibitin. Hannunsa na dama, sanye cikin arm sling. Daga gefen damansa kuma, Zaid ne zaune yake kallonsa ta gefen ido, dan jinsa yake kamar wani baƙo a gurinsa.

A ɗazu bayan da ya dawo daga masallacin sallahr asuba, ya tarar da Aliyun ya buɗe idonsa, amma kuma yana kwance a kan gadon, hakan ya sa ko ɗakin ma bai ƙarasa shiga ba ya juya da sauri ya tafi kiran nurses. Tare da nurses guda uku suka dawo, su suka dakatar da shi a waje, su kuma suka shiga ɗakin. Jim kaɗan ɗaya daga cikinsu ta fito, bayan ɗan wani lokaci kuma sai gata ta dawo ita da likitan da ya duba Aliyun. Sun jima sosai a ɗakin, dan har sai da ya ƙagu. 

Sai ga su sun fito, da sauri ya shiga tambayar likitan jikin Aliyun. Likitan ya sanar masa da komai lafiya, dan har sun saka masa arm sling, gudun kada ya cika yawan motsa hannun. Amma kuma sun masa wata allura, wadda ta sa ya koma bacci, amma daga lokacin zuwa ƙarfe bakwai na safe zai iya farkawa. Da haka hankalinsa ya kwanta, har ya dawo ɗakin ya zauna ya ci gaba da gadinsa, har zuwa lokacin da ya farka.

“Ya... Ya kake?”

Cewar Kuliya, dan be ma san me ya kamata ya tambayi ɗan uwansa ba, wanda Allah ya haɗasu bayan shuɗewar shekaru masu yawa da rabuwarsu. A ɗazun da ya farka cewa ya yi Zaid ɗin ya ara masa wayarsa, akwai wanda zai kira. Bayan da Zaid din ya ba shi wayar, sai ya kira Anna ya sanar mata halin da yake ciki. Kuma tun bayan wannan maganar, wata magana bata ƙara shiga tsakaninsu ba. 

Zaid ya juyo ya kalleshi, me makon ya amsa tambayar da ya masa, sai ya ja ɗan uwan nasa ya rungumeshi. Duk cikinsu babu wanda be zubar da ƙwalla ba, dan faɗar kalar kewar juna da suka yi ma ɓata baki ne.

“Wannan ne abun da ya kamata ace ka tambayi yayanka bayan kun haɗu?!”

Cewar Zaid yana shafa kansa bayan da suka saki juna. Kuliya ya share hawaye.

“Ban... Ban san me ya kamata na ce ba ne?”

“Dama kai kana rasa abun faɗe ne?”

Sai suka yi dariya.

“Ina Mishal?”

“Wa? Ko matarka ?”

Sai Aliyu ya sunkuyar da kansa yana faɗin.

“Eh ita”

“Suna gidana, ɗazu na ga kiran matata, na san nan da anjima za ka sun iso...”

Daga nan kuma sai aka buɗe babin hira, suka shiga bawa juna labaran abubuwan da suka faru a rayuwarsu bayan rabuwarsu, daga Zaid har Aliyun, Allah ne kaɗai ya san kalar farin cikin da suke ciki, bayan shuɗewar tarin shekaru, yau sai ga su a tare da juna,me ya fi wannan daɗi?. Ba su ɓoye juna komai ba, wani zancen su yi dariya, wani kuma su matse ƙwalla. Kuma cikin hirar tasu ne, Zaid yake sanarwa da Aliyu cewar ya haɗu da dangin Momma, kuma su ne ma suka aura masa matarsa, dan ita ce 'yar anti Maryam da Momma ke basu labarinta. Sosai suka tattauna kan matsalolin da suka faru da su, da kuma nasarorin da ko wannensu ya yi a rayuwa.

“Ni da ma na san baka mutu ba, dan ce mana aka yi ka gudu, ba cewa aka yi ka mutu ba... Kawai de na haƙura na fawallawa Allah ne, fon na san ko ba daɗe, ko ba jima idan har Allah ya hukunta haɗuwar mu da juna za mu haɗu...”

Zaid ya ci gaba da kallon ƙanin nasa cike da alfahari. Ji yake kamar ya buɗe cikinsa ya saka shi ya kulle, gudun kada wani abu ya ƙara zuwa ya shiga tsakaninsu.

Ƙofar ɗakin aka turo, Mishal da Rabi suka bayyana a bayan ƙofar. Daga Zaid ɗin har Aliyu suka juyo suna kallon bakin ƙofar. Mishal na arba da Kuliya, zaune da rai, wata ƙwalla ta silalo daga idonta. Ba ta san ya ka yi ba, amma ita de ta san kowa dake ɗakin ya ɓace a idonta, ba ta ganin kowa sai Aliyuj da ke zaune a bakin gado, sanye cikin wasu bluen riga da wando, hannunsa na dama saƙale cikin arm sling, ya kafeta da idamuwansa ya na kallo. Dan haka ta taka da gudu ta yi kansa, kuma tana zuwa kusa da shi ta faɗa jikinsa ta rungume mijinta.

Kuliya ya ɗan cije lips ɗinsa na ƙasa, saboda zafin famun da Mishal ta masa, amma haka ya ɗago da hannunsa na hagu, ya ɗora avkan gashinta dake cikin hijabi.

“Abu Aswad... Abu Aswad ɗina... Abu Aswad... Da ma na san ba za ka mutu ka barni ba...”

Faɗi take tana ƙara ƙanƙameshi. Hakan ya sa Zaid miƙewa daga bakin gadon ya ja hannun Rabi zuwa waje, tare da rufo musu ƙofar.

Mishal ta ɗago da kanta daga ƙirjin Kuliya, ta shiga dudduba jikinsa, hawaye ya jiƙa mata fuska. Hannunsa ya ɗago ya kama fuskarta.

“Abu Aswad ɗina!”

“My Teddy Bear”

Kuliya ya furta a hankali yana share mata hawayen.

“Da ma ai na faɗa maka cewar ba za ka mutu ka barni ba...”

Fuskarsa ya kara da tata ya na faɗin.

“I love you Mishallyn Aliyu, i love you to the moon and back... I love you my Boo, my last love, my babe, my other half, my treasure, my honey bun...”

Kafin a hankali, ya haɗe bakinsa da nata, suka shiga musayar yawu. Sakinta ya yi yana zaunar da ita a gefensa. Sai kuma ya kalleta sosai. Idonta har wani ƙyallin murna yake na ganin ya samu sauƙi.

”Kin yi kyau, wa ya baki hijabi kika saka?”

Sai ta kalli hijabin jikin nata tana faɗin.

“Anti Adawiyya ce ta bani”

“Ya miki kyau sosai”

Matsawa ta yi kusa da shi, kamar me shirin komawa cikinsa, ta maƙalƙale hannunsa na hagu.

“Abu Aswad! Jiya fa na ɗauka cewar ka mutu. Na yi tunanin ka mutu ka barni.Na ɗauka cewar wani maraicin zan sake shiga”

Kuliya ya yi murmushi ya na sumbatar kanta.

“Insha-Allah zan ci gaba da zama da ke, har zuwa lokacin da zaki kawo mana babynmu!”

Sai ta ɗago da kanta ta kalli fuskarsa.

“Kenan zan samu baby?”

Sai ya yi dariya.

“Haka nake zato, ina da yaƙinin cewa mun kusa samun baby soon”

Sai ita ma ta yi dariya tana kwantar da kanta a kafaɗarsa.

“Ka san suna wa za'a sa masa?”

Dariya shi ma ya yi, har jikinsu na jinjiga a tare.

“Wai an tabbatar ne?”

Ta ɗago tana fadin.

“Me ɗin?”

“Babyn mana. An tabbatar kina ɗauke da shi?”

Nan take ta haɗe rai tana kai masa duka a damtsen hannunsa.

“Auuchhh! Teddy Bear irin wannan duka haka?”

Ta turo baki gaba tana faɗin.

“To ba kai ka ce min na samu baby ba, kuma sai ka dawo kana min wani ƙauli da ba'adi”

Ta faɗi idonta na ciccikowa da ƙwalla, dan ita har ga Allah ta riga da ta yadda da cewar ta kusa samun babyn, ya riga da ya sa mata rai, kuma sai ya zo yace ba haka ba?.

“Wasa fa nake miki, amma idan kina so sai an ƙara!...”

Ta san me yake nufi da sai an ƙara ɗin, dan haka ta ƙara ɗaka masa  wani dukan, wannan karon a cinyarsa, ya dafe wurin yana dariya.

“Ki yi haƙuri, kin ga fa ba ni da lafiya, ya kamata ace an raga min ai”

Mishal ta share ƙwallar da ta silalo mata, dan ita ta mamanta da ba shi da lafiyar.

“To ka yi haƙuri”

“Ke!”

Ta kalleshi.

“Me ya sa kika yi laushi ne?. Abu kaɗan sai ki masa kuka, bayan na san da ba haka kike ba”

Ya tambaya jin a ɗazun da ta yi magana murmuyarta ya fito a raunane.

“To ba girma nake ba!”

“Iyeee, lalle girma, su Mishallyn Aliyu an fara girma”

Sai ta yi dariya tana rufe fuskarta da tafukan hannunta. Shi ma sai ya yi dariyar. A lokacin kuma aka turo ƙofar ɗakin. Anna ta shigo, hakan ya sa su duka suka kalleta.

ZAID POV.

Yana fita da Rabi'a ba su tsaya a ko ina ba sai wani ɗaki dake kusa da wanda aka kwantar da Aliyu, kasancewar ɗakin babu kowa. Suna shiga ɗakin, ya tura ƙofar ɗakin ya rufe, sannan ya jingina bayansa a jikin ƙofar. Yana miƙawa Rabi dake tsaye hannunsa, kamawa ta yi, shi kuma ya jata ta faɗo kan jikinsa, ya saka hanyyensa duka biyu ya rungumeta.

Ita ta ɗago daga jikin nasa tana faɗin.

“Ka ji yanda kayan jikinka suke warin gumi?”

Jikin nasa ya shinshina yana faɗin.

“To ya zan yi da rayuwa, larura ta sa na koma ƙazami, kwana ɗaya ban yi wanka ba fa, ga mu yau a na biyu...”

Ta ɗan yi dariya tana mayar masa da chain ɗin wuyansa ƙasan rigar jikinsa.

“Rhoda tace na faɗa maka, ita ta wuce gida, za ta je ta shirya, wai ku haɗu a kotu”

“Uffff! Kin ga Wallahi shaf na manta!”

Ya faɗi yana dafe kansa.

“Abubuwan nawa ne da yawa, kinga kuma ko su kawu Abdullahi ban kira ba, dan kin san ya kamata na sanar da su halin da ake ciki”

Ta gyaɗa kai.

“Haka ne... Abun da ya fi kawai yanzu ka koma gida ka je ka yi wanka, ka sauya kaya, sai ka wuce kotun... Kuma ga abinci nan ma na kawo maka”

Kansa ya girgiza.

“Ba na jin zan iya tafiya na bar Aliyu shi kaɗai”

“Wa ya faɗa maka cewar Aliyu shi kaɗai ne, akwai ni, ga kuma Mishal”

“Idan kuma wata buƙata ta taso wadda dole sai kun buƙace ni fa?”

“Da yardar Allah har ka dawo babu wata matsala da za ta faru”

“Kin tabbata?”

Ta gyaɗa masa kai. Sai da ya ƙara janta jikinsa ya rungume, sannan suka fita a tare. Ganin wata mata da ban a ɗakin zaune kusa da Aliyu ya basu mamaki.

“Ƙaraso Zaid. Wanan ita ce Anna!”

Cewar Aliyun yana nuna masa matar dake sharar ƙwalla. Anna ta juyo tana kallon me kama da ɗanta.

“Zo nan, ai kai ma ɗana ne”

Anna ta faɗi tana miƙa masa hannu. Zaid ya ƙarasa kusa da ita ya zauna. Suka sakata a tsakiya, idan ta juya ta kalli Zaid, sai ta juya ta kalli Aliyu, kafin idonta ya sauƙa a kan Rabi dake tsaye kusa da Mishal.

“Wannan ita ce matar taka kai ma?”

Zaid ya gyaɗa mata kai. Zaid ya ɗan jima a ɗakin, kafin ya musu sallama, bayan ya faɗa musu uzurin da zai je. Har yabkama hanyar barin ɗakin,maganar Aliyu ta dakatar da shi.

“A dawo lafiya Zaid”

Sai da ya juyo ya kalleshi, kafin ya gyaɗa kansa yana fita. Rabi ta bi bayansa suka fita tare har zuwa jikin motarsa. Shiga ya yi, kana ya buɗe ɗayar ƙofar dake side ɗin da Rabi ke tsaye, ya mata alama da ta shigo, shiga ta yi ta zauna.

“Ban sani ba ko zan jima ban dawo ba, saboda ana gama shari'ar, za mu wuce na kai Rhoda karɓar musulunci”

Sai ta gyaɗa kanta tana ci gaba da kallonsa.

“Me kike so na kawo miki yau?”

“Ba na buƙatar komai, kawai kai nake so?”

Sai ya ɗage mata gira ɗaya yana faɗin.

“Ni da kai na?”

Ta yi dariya tana gyaɗa masa kai.

“In dai ni ne kin samu 'yan matana, and zan kawo miki kifi, ko shi ɗin ma ba kya so?”

Ta girgiza kanta.

“Ina so”

Zaid ya ɗaga kafaɗa cikin faɗin “To sai na dawo?”

“Ummm”

“Kuma tafiya za ki yi ba tare da kin...”

Tureshi ta yi tana dariya. 

“Zaid hoo, baka jin magana Wallahi!”

“To ni ki min”

Juyowa ta yi tana kama fuskarsa, kafin a hankali ta yi kissing ɗinsa.

“Shikenan?”

Ta faɗi tana ja baya. Fita ta yi daga motar, tana rufo masa ƙofar.

“A je a yi wanka, a ƙazan-ƙazan”

Ta faɗi tana leƙo da kanta.

“Lalle kin ci tuwo a kaina Adawiyya, amma zan rama”

Ta bar wurin tana dariya. Ya tayar da motar yana ƙara sinsinar jikinsa.

“Wanka daɗi, wani bai san daɗin wanka ba”

Ya yi waƙar yana juya kan motar.

*Believe in your dreams...*

Anna da Rabi ne suke tafe, bayan da suka dawo daga wani shago da suka je dan siyan ruwa, duk yanda Rabin ta so Anna ta zauna kan ita za ta je, fir Anma ta ƙi yarda, tace sai de su je tare. Dan ita tausayin Rabin take. A kallon farko da ta mata ta gane cewar tana ɗauke da ciki!, shi ya sa take tunanin kamar ba za ta iya ɗaukan ruwan ba. Amma  sai ga shi bayam da suka siyo ruwan ma ba ta bar Annan ta ɗauka ba.

Ba tare da Rabi ta ankara ba,  ta ji juwa ta ɗebeta, ta yi baya luuu za ya faɗi, ledar robobin ruwan dake hannunta ta faɗi ƙasa. Anna ce ta yi saurin kamota.

“Sannu!... Kin ga ko?, shi ya sa na ce ki bari na ɗauka, macen dake cikin hali irin naki ba'a barinta ta ɗauki abu me nauyi!”

Cikin rashin fahimta Rabi'a tace.

“Babu komai fa Anna, wallahi ƙalau nake”

Anna ta ɗauki ledar tana dariya.

“Haba 'yanan, ai mace me ciki ba a rabata da laulayi!...”

Wani shaftareren yanki na zuciyar Rabi'a ne ya yanke ya faɗo ƙasa, wani ɗan ƙwarya-ƙwaryan bomb ya fashe a ƙirjinta, ta sandare a wurin, ta kasa motsa ko da ƙafarta, sai idanuwanta da ta zaro suna duban Anna. Ciki fa?, wai ita ?, ita Rabi'a take da ciki?.

Ganin haka ya sa Anna fahimtar cewa ba ta ma san cewa tana da cikin ba.

”Baki sani ba kenan?”

Kamar wata sokuwa haka ta gyaɗa kanta.

*

Zaune take a kan ɗaya daga cikin kujerun dake wani corridor, har zuwa yanzu ta kasa yarda da abun da ta ji, wai ita ce take da ciki, to garin yaya, daga sau ɗay!...

Kunyar kanta da ta kamata ce ta sa ta kasa ƙarasawa. Ta yi jigum-jigum, tana jiran fitowar result ɗin gwajin da aka mata. Wata nurse ce ta fito daga ɗakin da take fuskanta, ta shiga kiran sunayen mutanen dake zaune a wurin, da haka har aka iso kanta, ta karɓi nata result ɗin tana komawa baya, tare da zama a inda ta tashi.

Hannunta har rawa yake wurin buɗe takardar. Tar manyan rubutun da takardar ke ƙunshe da su ke sanar mata cewar tana ɗauke da ciki na sati huɗu. Kanta ta sunkuyar ƙasa tana shafa cikinta. A lokacin kuma ƙwalla ta zubo mata. Yanzu kenan ciki gareta?, cikin ma kuma ba na kowa ba sai na Zaid!.

ZAID POV.

Bayan hujjojji da aka gabatar a gaban kotu, kotu ta yankewa Alhj Bala hukuncin ɗaurin rai da rai, sauran abokan harƙallarsa kuma, ciki har da Garuje, an yanke musu hukuncin  dai-dai da nasa, Usman da sauran abokansa kuma, an yanke musu shekare ashirin-ashirin a gidan kaso. Kuma da haka shari'ar ta zo ƙarshe. 

Bayan shuɗewar tsawon shekaru, sai a yau ne Rhoda ta samu adalci kan abun da aka aikata mata, ba ma ita kaɗai ba, hatta da Rabi a yau ne aka sama mata 'yanci. Daga kotun kai tsaye Zaid ya wuce da Rhoda masallacin da ya yi magana da limaminsa, dan shi yake so ya bawa Rhoda kalimatu shahadah.

*No.86, Garki 2, Abuja...*

*08:00*

Rabi da Zaid ne zaune a falo suna kallo a tv. Rhoda kuma na ɗakin da Rabi ta ware mata, dan yau a gidan zata kwana.

“Mts! Ammata na manta da kifinki a mota, bari na je na kawo miki”

Cewar Zaid yana miƙewa tare da barin falon. Rabi ta sunkuyar da kanta ta kalli cikinta. Tun bayan dawowarta gidan take ta neman hanyar da za ta faɗawa Zaid wannan kyakkyawan labarin, amma ta rasa ta inda zata fara.

Kallo ta ci gaba da binsa da shi, har ya dawo hannunsa riƙe da leda, ya buɗe ledar, ƙamshin kayan haɗin da aka yi amfani da su wurin haɗa kifin ya bugi hancints, hakan ya sa ta ji amai ya zo mata. Ba shiri ta miƙe da gudu ta nufi ɗakinta.

Baki sake Zaid ya bi bayanta da kallo, kafin shi ma ya miƙe ya nufi ɗakinta da ya ga ta shiga. Ko da ya isa ɗakin sai ya tarar da har ta faɗa bayi, ta kuma kulle kofar bayin. Maganar duniya mata amma ta ƙi amsa shi  hakan ya sa ya juyo, ya na shirin barin ɗakin, idonsa ya sauƙa kan wata takarda aje a kan hijabinta. Don haka sai fasa fitar, ya dawo ya ɗauki takardar ya shiga karantawa.

Sai da Rabi ta gama aman nata, ta wanke bakinta, sannan ta fito. Damm, gabanta ya buga, ganin Zaid tsaye a tsakiyar ɗakin, hannunsa riƙe da takardar da ta manta bata ɓoye ba, kuma ba ma wannan ne ya ɗaga mata hankali ba, wani irin kallo da ta ga yana mata shi ya haɗe kayan cikinta waje guda. Da ƙyar ta haɗiye yawu ta fara takawa tana nufarsa.

“Adawiyya miye wannan?”

Ya tambaya yana nuna mata takardar, sai da cikin Rabi ya yamutsa, jin yanda amon muryarsa ya fito a ƙasashe.

“Ba magana nake miki ba?!”

Ya faɗa cikin tsawa, yana ƙoƙarin saka ƙaton dutse, dan danne ɓacin ran dake taso masa. Abun ya bala'in ɓata masa rai, a matsayinsa na uban ɗan cikinta, kamata ya yi ace ta sanar da shi, amma me ya sa za ta ɓoye masa?.

Sosai Rabi ta tsora, ganin yanda ya buɗe lumsassun idanuwansa a kanta. Hakan wani abu ne da bata taɓa gani ba a tare da shi, nan take ta fara in'ina.

“Ko ba ni ne uban cikin jikinki ba ya kamata ace na sani, ballantana na san da cewa ni ne ubansa, me ya sa za ki ɓoye min?!”

A wannan karon kam ita ma Rabi ranta sai ya fara ɓaci. Dan haka tace.

“Miye laifi na a nan?, ni kai na ban san cewa ina ɗauke da ciki ba, sai bayan da Anna ta ankarar da ni, hakan ya sa na je na yi gwaji a yau ɗin nan, kuma shi ma gwajin ya tabbatar da ina ɗauke da juna biyu. Tun bayan dawowarka nake ta neman hanyar da zan bi na faɗa maka, amma na rasa, shi ne na yi laifi?...”

“A'a kam, ba ki yi laifi ba!. Tun ɗazu na dawo gidan, me yasa da na dawo ba ji faɗa min ba?!”

“Ya isheni haka Zaid!”

Ta faɗi ita ma a tsawace tana kallon cikin idonsa.

“Wai akaina aka fara ciki?. Na ce maka ƙoƙarin gano hanyar da ta dace na faɗa maka nake, amma sai ka hau ni da faɗa?, na ga dai ba wata tara cikin ya yi ba tare da na sanar maka ba!”

“Ya yi kyau Adawiyya, yau kanki tsaye kike kiran sunan, a kan wannan cikin kike gaya mun duk maganar da ta zo bakinki ko?, ki riƙe abunki na bar miki!”

Daga haka ya juya ya fice daga ɗakin ba tare da ya aje mata takardar ba.

Rabi ta zame ƙasa tana fashewa da kuka. Me ya sa ma za ta bari har sheɗan ya shiga tsakaninsu?, kuma ai shi ma ya na da laifi, mi ye na saurin fusatar haka?, tun bayan aurensu ba su taɓa faɗa ba sai yau, hankalinta ba ƙaramin tashi ya yi ba, har ta kwanta bata dena kuka. Bacci ma a ranar sai ya gagareta.  Ta rasa inda za ta sa kanta, musamman idan ta tuna da yanda ta ɗaga masa murya, abun sai ya soketa a zuciya.

Ganin zama cikin kukan ba zai finsheta ba ya sa ta miƙe salin'alin ta nufi ɗakinsa, ƙofar ta tura a hankali tana saka kai ciki. A kunne ta samu wutar ɗakin, shi kuma ya na zaune daga kan gado, ya zuro da ƙafafaunsa ƙasan gadon. Kuma duk da ya bawa ƙofar baya, tana iya ganin yanda ya yi tagumi. Wani kuka me ƙarfi ya ƙwace mata, dan gani take kamar ita ce silar rashin kwanciya baccin nasa. 

Da gudu ta hau kan gadon nasa, ta shiga rarrafe a kan gadon, har ta isa inda yake, tana isa dab da shi, ta zura hannayenta ta bayansa, suka kewayo ta gaba, kanta ta kwantar a bayansa tana fashewa da kuka.

Zaid ya rintse idonsa, zuciyarsa na masa zugi, yanzu haka zaman da ya yi na nadama ne, sai bayan da ya zo  kwanciya ya ga rashin kyautawarsa kan abun da ya mata, be kamata ace ya ɗaga mata murya haka ba, kuma be kanata a ce ya fusata daga ganin takarda ba. Zaman da ya yi anan yana ta tsara yanda za ayi ya bata haƙuri ne gobe da safe, sai ga shi kuma ita ta zo da kanta dan ta ba shi haƙurin.

“Ka yi haƙuri Raj, na tuba!”

Da ƙarfi ya sauƙe ajiyar zuciyar, sannan ya saka hannayensa a kan nata yana rabasu daga ruƙon da ta masa, sannan a hankali ya sauƙo da ido daga kan gadon, ta dawo gabansa ta tsaya. Ya ɗan ɗaga kansa ya kalleta, fuskar nan sharkaf da hawaye. Sai ya raba cinyarsa biyu, ya zaunar da ita akan ta dama. Tana zama a kan cinyar tasa ta ƙara shigewa cikin jikinsa, tana nanata masa kalaman ban haƙuri. Shi ma rungumeta ya yi, ninkun ƙauna da santa na ƙara shiga cikin zuciyarsa.

“Ya isa haka Adawiyya, ko tsakanin harshe da haƙuri ana samun saɓani. Wannan karon sheɗan ya yi nasara a kanmu, dan haka sai mu kiyaye nan gaba”

Kanta ta gyaɗa masa tana shanye kukan nata.

“I'm sorry too, na faɗa miki maganganu masu zafi”

Kanta ta girgiza tana ɗagowa daga jikinsa. Hannunsa ya kai kan  cikinta, yana jin santa da kuma na abun da ke cikinta na ƙara kama shi.

“Ina sonki Ammatana. Wannan babbar kyautar taki ta fi min komai a yanzu”

Ƙara kwanciya ta yi a jikinsa tana lumshe ido.

“Allah alhamdulillah”

Ya faɗi yana ƙara matseta a jikinsa.

“Ina sanki 'yan matan Zaid”

“Ina sanka Kayali! (Arabic:My choice)”

Sai ya ɗan kalleta kaɗan.

“Da ma ke kika zaɓeni?. Ca nake ai ƙaddara ta zaɓa miki ni”

Da sauri ta miƙe daga jikinsa tana shirin saka masa kuka, sai ya yi dariya yana ƙara kwantar da ita.

“Ki yi haƙuri. Gaskiya ni me sa'a ne Ammata, a karon farko?”

Kanta ta ƙara cusawa a ƙirjinsa dan tsabar kunya.

“Diary baka da kunya”

Muryarta ta fito daga ƙasan ƙirjinsa. Ya yi dariya.

“Wallahi ji na nake kamar wani sabon mutum, ji nake kamar yau aka haifo ni, duka burikana ɗaya bayan ɗaya suna cika...”

Ya faɗi a setin kunnenta. Sai ta ƙara narkewa a jikinsa tana lumshe ido. dan wani bacci da take ji na shirin kamata.

KULIYA POV.

Kwance yake a kan gadon marasa lafiya na asibti, yayin da Mishal ke kwance a gefensa, kallon fuskarta kawai yake, yana tuna yadda ta yi mirƙisisi kan ita ba za ta tafi gida ba, don ita tare da shi za ta kwana. Baccinta take hankali kwance, kamar tsimma a cikin randa.

Juyawa ya yi yana kallon window, saboda wata iska me daɗi dake shigowa ta windown. A yanzu komai na rayuwarsa ya hau seti, ba ya jin akwai wani buri nasa da rage bai cika ba, komai ya setu, komai ya hau kan hanya, ya samu dangi, ɗan uwa, uwa, mata ga shi har da suruka, shi ko me zai yi in ba godewa Allahnsa ba.

Da ga nan kuma sai ya shiga tsara abubuwan da zai yi idan ya bar asibtin, dan ba zai yi shiru a kan abun da aka masa ba, kuma ya san ko suwa suka masa hakan, dan case ɗinsu shi ne aiki na ƙarshe da ya yi.

***

Haka Aliyu ya ci gaba da samun kulawar likitoci a asibitin, har zuwa lokacin da ya samu sauƙi, a cikin jinyar da ya yi, 'yan uwansu na haɗejia duka sun zo sun duba shi, ba ƙaramin daɗi suka ji ba a sanda suka ganshi, kuma shi ma ya ji daɗin ganinsu sosai. 

Bayan ya warke ne suka ɗunguma zuwa Hadejia su duka, domin bikin Rhoda, wadda ta zaɓi sunan Rauda a yanzu, dan  bayan ta karɓi musulunci aka tambayeta sunan da take so a sa mata, sai tace Zaid ya zaɓa mata, shi da kansa yace ta karɓi sunan Rauda, dan yana kama da sunanta na da, kuma ma'anar sunan ma me kyau ce.

Haka aka sha bikin amarya Rauda da angonta Zakar. Wanda suka ci gaba da zama a haɗejia, kasancewar shi Zakar ɗin a nan haɗejian yake aiki.

*BAYAN SHEKARU BIYAR...*

*No.275, Asokoro, Abuja...*

Anna ce zaune a kan kujerar daning, su na magana da Aliyu dake zaune a kan kujerar dake facing ɗinta. Mishal ce ta fito daga kitchen, hannunta riƙe da tray, wanda ta ciko shi da wasu warmers, ga tulelen cikinta tana turashi gaba.

“Sannu Hafsat. Kai Aliyu ka tashi ka temaka mata mana” cewar Anna.

Kuliya ya miƙe tsaye yana nufarta, trayn hannun nata ya karɓa, sannan ya ƙaraso ya aje shi a kan danning, ya koma inda Mishal take, ya kamo hannunta, tana takawa a hankali har suka iso danning ɗin, ya zaunar da ita a kusa da Anna ya na jera mata sannu, ita kuma ban da gyaɗa musu kai babu abun da take.

“Sai da na ce miki ki bar girkin nan, amma kika ƙi”

Anna ta faɗi tana dubanta, ita dai ba ta iya cewa komai, don tun bayan samun cikin nata ta koma muiskila, sam ba ta son yawan magana. 

Ƙofar falon aka turo, Zaid da ya je ɗaukan Rabi'a a NFF (Nigerian Football Federation) centre ya shigo, sannan ita ma Rabin ta shigo tana biye da shi, sanye take da wata kimonoh, wadda ta saka jersyn Super Falcons a ƙasanta. Kasancewar yanzu haka suna training a kan gasar WACON (Women's African Cup of Nation) da za'a buga nan da sati me zuwa. Dan zuwa yanzu Rabi ta zama ɗaya daga cikin 'yan ƙwallon da ake ji da su a Nigeria, a taƙaicen-taƙaicewa ma a halun yanzu ita ce kw riƙe da wannan kambun na (Best African Women player). Duk yanda ƙungiyoyi da dama suke son siyanta ta ƙi, don ta ce ba za ta taɓa barin ƙasarta ta koma wata ƙasar ba, saboda mijinta da kuma ɗanta.

“Maman Junior har an dawo?”

Cewar Kuliya dake zubawa Mishal ruwa a cup.

“Wallahi na dawo Papi. Wai Mishal ke kika yi girkin nan?”

Rabin ta ƙarashe tana kallon kayan abincin dake zube a kan danning.

“Sai da na hanata, amma haka ta sulale ta shiga kitchen ɗin ba tare da na sani ba”

Cewar Anna, Mishal ta karɓi ruwan da Kuliya ke miƙa mata ba tare da ta ce musu komai ba.

“Ina Junior?”

Rabi ta tambaya, sakamakon rashin ganinsa a wurin.

“Junior! Junior!...”

Haka ta shuga ƙwala masa kira tana baza idonta, don ganin ta inda zai ɓillo.

Can sai ga wani kyakkyawan yaro dake tsantsar kama da Kuliya ya sauƙo daga kan stairs hannunsa riƙe da Ipad. Rabi ta bishi da kallo tana jinjina kai, wato yana jinta, amsawar ce ba zai iya ba, ita har mamakin lamarin Junior take, ko da ɗiso babu abun da ya baro a hallayar Kuliya.

“Papi na faɗi!”

Cewar Junior ɗin yana miƙawa Kuliya Ipad ɗin hannunsa. Kuliya ya karɓa ya na kallon yaron. Aliyu Zaid Aliyu kenan, a.k.a Junior, a.k.a Kuliya, a.k.a AZA, duka sunansa ne, ɗan auta a wurin kawunsa, kakarsa, mamansa, dadynsa, papinsa da kuma Nininsa. 

Zaid ya ja kujera ya zauna yana faɗin.

“Wata ran  sai na fasa ipad ɗin nan, in yabso na ga ta tsiyar... In ba wulaƙanci irin na Junior ba, ya za ayi mamansa ta dawo daga training, ta kirashi amma ya wuce wurin Aliyu yana faɗin wai ya faɗi a game?”

Kuliya ya kalli Zaid yana zaunar da Junior a kan cinyarsa.

“Ka fasa, ni kuma sai na sai masa sabuwa, ina ruwanka da sha'aninmu?, mu babu ruwanmu da kowa ba ehe”

“Junior Mama fa?”

Rabi ta faɗi tana kallonsa. Juyowa ya yi ya kalleta da gray eyes ɗinsa da shi kaɗai ne abu ɗaya da ya gado a wurin Zaid, amma hatta da buɗar idonsa irin ta Kuliya ce.

Sai kuma ya sauƙo daga kan cinyar Kuliya, ya tako zuwa wurin Rabi, ya ɗan mata wani gutun murmushi yana rungume ƙafafunta.

“Tafi ka bani wuri ba na so”

“Haka fa ni ma suka haɗe mun kai shi da Papi last week, wai dan suna kallon Film ɗin 'Tara Dunken' na zo na sauya, shi kenan suka dena min magan, sai jiya suka kulani”

Cewar Mishal tana aje cup ɗin hannunta.

“Ai ke na sati ɗaya suka miki ma, ni da suka fi sati biyu ba sa kulani fa in ce me?”

Cewar Anna cikin taɓe baki.

“Sorry Mama”

Cewar Junior kamar wanda aka yiwa dole. Rabi ta dunguri kansa tana faɗin.

“Ka dena wannan miskilancin naka, idan ka ce irin halin Papi za ka ɗauko wahala za ka sha, don ma de shi Papi an yi nasarar samun Nini ta seta masa hanya, kai ko sai de ka ci jibga, don dukanka zan fara...”

Shi dai bai ce mata komai ba, sai ƙasan kimonohnta da ya riƙe.

“Nini? Ashe ke kika seta ni?”

Kuliya ya tambaya yana kallon Mishal, ita ko tai masa banza, don ta san idan ta biyashi yanzu sai su zo suna cece ku ce, ita kuwa yanzu a duniyar Allahn nan magana ita ce abun da ke mata wuya, ba ta son yawan magana.

“Sai ku zo mu fara cin abin cin”

Cewar Anna.

“Bari na je na yi wanka tukunna”

Rabi ta faɗi tana ƙwace ƙasan kimonohnta daga hannun Junior. Kafin ta haye sama. Bayan ɗan wani lokaci Zaid ma ya miƙe ya bita. 

Kuliya ya ci gaba da tsokanar Mishal, amma ko ci kanka ba ta ce masa ba, har sai da Anna ta masa magana kafin ya shafa mata lafiya.

“Ammatan Raj”

Zaid ya kira sunanta, yayin da take tsaye a jikin mirror tana shafa mai, juyowa ta yi ta kalleshi, shi ma kuma kallon nata yake, yayin da yake tsaye a bayanta.

“Kai wai baka san ka girma ba ne?”

Ta tambaya tana juyawa.

“Girman me?, ɗa ɗaya ne fa da mu kawai, ki bari sai mun tara kamar yara goma haka, sai ki ce na girma, amma ɗa ɗaya ai ya yi kaɗan ya sa na ga tsufana”

Rabi ta yi murmushi tana shafa mai a wuyanta.

“Saura kwana nawa ku tafi ne?”

Ya tambaya yana zuge mata zip ɗin rigarta da bata zuge ba. Rabi na kallonsa ta cin madubin gabanta ta furta.

“One week”

“Mun gode Allah, dan nan da kwana uku visar mu na iya fitowa”

Sai ta gyaɗa masa kai tana juyowa.

“Mu je ko?”

Ya girgiza mata kai yana kama waist ɗinta. Rabi ta ture shi tana faɗin.

“Su Anna na ƙasa suna jiranmu fa”

Ya ƙara kamota yana faɗin.

”To ina ruwana...”

“Dady! Mama!”

Muryar Junior ta kira daga wajen ɗakin. Rabi ta ƙara tureshi tana nufar ƙofar da sauri, sai ta ga Junior ɗin tsaye a waje yana kallonta.

“Me ya faru?”

“Anna tace wai ku yi sauri”

Rabi ta juyo ta kalli Zaid tana watsa masa hararar wasa, kafin ta juyo ta tsugunna ta ɗauki Junior ta sauƙa ƙasa, Zaid ya bi bayansu da kalli yana murmushi, kafin shi ma ya bi bayan nasu ya sauƙa aka fara cin abincin da shi. Labarin rayuwar sabon gidan da suka gina cike da so ƙaunar juna da farin ciki kenan.

°°°°°°Alhamdullullah°°°°°°

••••••END••••••

-Assalamualaikum-

Barkan mu da wannan lokaci, ina so na yi amfani da wannan damar, wurin nuna muku irin godiyata gareku, kan so da ƙaunar da kuka nuna min, a har kullum ina ganin kamar ‘Na gode' ta yi kaɗan wurin nuna muku jin daɗi na game da yanda kuke support ɗina, my people i can't thank you enough. Allah ya bar zumunci.

Sannan ina so na yi jan hankali gareku, game da darasin dake cikin wannan littafi. Idan kuka tsaya kuka yi nazari, za ku ga cewar wannan littafin na ƙunshe da illollin fyaɗe, da kuma yanda rayuwar 'ya mace kan shiga garari yayin da iyayenta suka koreta daga gida, bacin da ƙaddara fyaɗe ta faɗa kanta.

Kun sani, kuma ni ma na sani, fyaɗe ita ce babbar annobar da ta damu yankin mu na arewa gaba ɗaya, shi ya sa nake so, mu tashe tsaye ni da ku, mu haɗa ƙarfi da ƙarfe, wurin ganin mun kawo ƙarshen wannan annoba, domin fyaɗe masifa ne, kuma bala'ine. Ina kira ga duk wani wanda ya san Allah ya wadata shi da wata baiwa, da ya yi anfani da wannan baiwar tasa wurin ganin mun kawo ƙarshen fyaɗe a arewacin nigeria, idan zai iyu, a gaba ɗayan Nigeria ma.

Ni tawa baiwar ta rubutu ce, shi ya sa na yi amfani da shi, wurin ganin na yaƙi wannan annoba da ta damu sauran 'yan uwana mata. Jama'a mu ƙyamaci fyaɗe.

*Say No to Rape❌*

#Labarinsu

#SalmaAhmadIsah

#TaurariWriters

Best regards

SALMA AHMAD ISAH

2024...




Post a Comment

0 Comments