TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Labarin su Page 20

 *LABARINSU*

*©SALMA AHMAD ISAH*

*TAURARI WRITERS*

*20*

~~~

*Let your wings be soft enough to carry her, until she remembers how to fly again...*

***

RABI'A POV.

“Rabi!... Rabi!”

Kiran da Anti Saratu ke mata ne ya sa ta tsaya da tafiyar da take a fusace, ta juya tana kallon Anti Saratun, wadda fuskarta ta yi gaje-gaje da hawaye.

“Rabi”

Ta furta a raunane ta na rungume Rabin, tare da fashewa da kuka, har mutanen dake wucewa ta lungun suna kallon su, duk dauriyar Rabin sai da ta zubar da hawaye, Anti Saratu ta saketa ta na dudduba fuskarta ta ɗan hasken dake layin.

“Rabi ina kika shiga haka?... Kusan kullum sai Fu'ad ya je nemanki makarantar da kike aiki, amma haka zai dawo yace min ba a sameki ba, har police station ya kai ƙara, amma babu wani bayani”

Rabi ta ɗan yi murmushi ta na share hawayenta, a ƙalla de tana da wani wanda ya damu da ita a duniya, Allah ya sa har yanzu akwai wani wanda yake santa har zuciyarsa, kuma ta san da ma duk wannan tsawon kwanakin da ta shafe bata gidan babu wanda zai nemeta bayan Saratun.

“Ƙaddara ce ta zaunar da ni a can, ƙaddarar da Allah ya hukunta faruwarta a kaina, irin abun da mahaifinmu yake shi ne aka aikata min, mutum biyar Anti Saratu, su biyar suka haikemin!”

Saratu ta ƙara fashewa da kuka ta na rufe bakinta, tare da girgiza kanta.

“Ki dena kuka Anti Saratu, ya wuce fa, Allah ya hukunta cewar dole sau hakannta faru da ni, kuma ga shi ya farun!”

“Yanzu ina za ki je?”

“Gidan kawu Habu zan tafi”

Ta faɗa don ta san babu inda za ta iya zuwa a yanzu da ya wuce can ɗin. Anti Saratu ta gyaɗa kanta tana saka hannu a aljihun doguwar rigar jikinta, sannan ta zaro kuɗi wurin dubu goma ta kamo hannun Rabin ta danƙa mata.

“Ga shi, ban sani ba ko za su amfane ki”

Rabi ta karɓa, sannan ta gode mata, Saratu na tsaye a ƙofar gidan har Rabin ta fice daga lungun.

Rabi na fita daga lungunsu ta wuce shagon Yaya, don ba za ta iya zuwa ko ina ba tare da ta sanar masa da halin da take ciki ba.

“Ka yi shiru Yaya?”

Rabi ta faɗi cikin hawaye, yayin da take zaune a kan benci tana kallon Yaya, bayan da ta gama tsara masa duk halin da ta shiga, da farko da Yayan ya ganta ya yi farin ciki, amma tun da ta fara bashi labarin abun da ya faru da ita sai ta ga yanayin fuskar Yayan ya sauya.

“Ba komai”

Yayan ya faɗi ya na kawar da kansa, mamaki ya bala'in kama Rabi, yau ita Yaya yakewa magana a haka?, ita ce ta masa magana ya amsa mata ciki-ciki?, me yake faruwa ne?. 

“Yanzu ya kake ganin za ayi”

“Ai yanda za ayi kawai shi ne ki kama gabanki, dan ni babanmu ya min mata, kuma nan da wata ɗaya za ayi auren!”

Da farko sai da Rabi ta ji wani irin duka a ƙirjinta, daga baya kuma sai ta yi murmushi me ciwo, to ita wai yanzu ma miye zai bata tsoro ne?, ai taskun rayuwa ba yau ta fara shigarsa ba, halayen ɗan adam babu kalar wanda bata gani ba, uban da ya haifeta ma ya ƙita, waye wani Yaya?, da dan har ya gujeta za ta ji ciwo?, ai da ma haka rayuwar take, wani zai soka da yini, sai ya ƙika da daddare,wani da ma can ba da zuciya ɗaya yake sanka ba, amma kai da ka so shi da zuciya ɗaya idan ka yi haƙuri Allah zai nuna maka ƙarshensa, ga shi yau ita ma ta ga zahirin Yaya.

Hawayenta ta goge, dan babu amfanin barinsu su zuba, ba za ta ƙara barin hawayenta su zuba a gaban wani ba, ko kukan za ta yi gwara ta ɓoye a wani wurin ta yi, ganin hawayen mutum na ɗaya daga cikin lagonsa,  'A strong woman will always turn pain into power' haka ta faɗawa kanta, dan haka za ta yi iya bakin iyawarta don ta yaƙi abun da zai durƙusar da ita, saboda haka Yaya bai bata mamaki ba.

Miƙewa ta yi tana murmushi ta kalli Yaya a tsakar ido tace.

“To Yaya, Allah ya sanya da alkairi, ka gaida sabuwar amaryar, ni na tafi, sai bayan saduwa kuma!”

Daga haka ta juya ta fice. Yaya ya ja wani dogon tsaki ya na jan wayarsa, shi mahaukacin ina ne zai yarda ya aureta bayan ta faɗa masa cswar maza har biyar sun mata fyaɗe?, ai yanzu a yanda take bata da maraba da karuwa, ko karan hauka ne ya cije shi ai ba ya yi wannan gangancin ba, gwara ta je ta can, ta ƙarata, wata ƙila ta samu wani ɗan tasha kamar babanta, sai ya temaka mata ya aureta, amma shi dai bai ga abun da zai yi da ita ba, da ma ba ita kaɗai ba ce budurwarsa, idan auren yake so ai sai ya zaɓi ɗaya daga cikin 'yan matansa ya ce zai aura, amma ba Rabi ba, dan a yanzu ta riga ta zama tarihi a rayuwarsa, shi da ma can don kyanta yake santa, yanzu kuwa da aka mata bajo a fuska ub*n wa ya aikeshi aurenta.

*

“Haka shi Ɗan Lamin yace”

Cewar kawu Habu, bayan da Rabin ta gama masa bayanin abun da ke faruwa. Dan tana barin shagon Yaya gidansa ta nufa, durƙushe take a gabansa, yayin da shi kuma yake zaune a kan kujera. Rabi ta gyaɗa masa kai, idanunwata a bushe ƙamas, babu wani damshin ƙwalla ko ɗaya a ciki.

Kawu Habu ya ci gaba da kallon Rabi cike da tausayi, ya girgiza kansa sannan yace.

“Babu damuwa, tashi ki shiga ɗakin Laure”

Miƙewa ta yi sannan ta shiga ɗakin matarsa ta biyu, wato Anti Laure, mace me kirki da karamci. Yaranta biyu da Kawu Habun.

Zama ta yi daga bakin gadon Anti Lauren, inda ta sameta tana matsar ƙwalla, kasancewar inda suka yi maganar kusa da windown ɗakinta ne, dan haka Rabi ta fahimci cewar zancen nasu ta ji.

“Sannu kin ji Rabi”

Rabi ta yi murmushi ta na kauda kai.

A hankali Ramatu matar Kawu Habu ta farko ta saki labulen ɗakinta, bayan da ta gama leƙen kawu Habun da Rabi, sannan duk abun da suka tattauna kaf a kunnenta, ita kuma a matsayinta na aminiyar Habiba, ba za ta yi shiri ba tare da ta sanar mata da labarin ba.

Dan haka ta lalubo wayarta ta fesawa Habiba kaf abun da ya faru.

*

Cike da takaici Habiba ta wurga wayarta kan gado, bayan da ta gama sauraron bayanan Ramatun, ita ta ma manta da gidan Habun, ta manta cewar idan aka kori Rabi daga nan can za ta nufa, amma ba komai, wannan ma ba zai gagara ba, ita ta san abun yi.

*No.181,Guzape, Abuja...*

MISHAL POV.

Tana kunna tv a falo aka turo ƙofar falon, hakan ya sa ta juya da sauri ba tare da ta kunna tvn ba, yanayinsa kawai ya bayyanar mata da halin da yake ciki, don ta riga da ta gama gane shi, abu ƙanƙani yake fusata zuciyarsa, kuma kusan kullum haka yake dawowa gidan.

Ba ta ce masa ƙala ba face kallonsa da ta yi har ya wuce ɗakinsa, dan ta riga ta gano cewar idan ya na a fusace baya san a masa magana. Bakinta ta taɓe ta kunna tvn, sannan ta juya ta koma kitchen.

Girkinta ta ƙarasa, sannan ta ɗebe komai ta shirya a kan danning. Ta dawo falo ta zauna tana kallo, ba ta shirya masa magana ba sai bayan shuɗewar muntuna kusan ashirin. Ta miƙe daga kan kijera, sannan ta nufi ɗakinsa.

Bata ƙwanƙwasa ba, dan ta san ko ta ƙwanƙwasa ba lalle ya amsa mata ba, yaya lafiyar kura, balle ta yi zawo, tsaye ta ganshi jikin mirror, ya na taje sumar kansa. Ta ci kin mirror kawai ya kalleta, sanye take da wata farar off shoulder shirt, sai wani baƙin short culottes, wanda bai ƙarasa kan guwarta ba, ya ɗauke kansa ya na ci gaba da taje sumar kansa.

Mishal ba ta damu ba, dan idan da sabo ta saba da wannan abun nasa , babu me iya zama da Kuliya sai me haƙuri, tsayawa ta yi a gefensa tana kallonsa, amma bai ko kalleta ba, sai ta rakaɓa ta gefensa ta shiga gabansa ta tsaya, wata gajeriyar harara ya maka mata, sannan ya kauce ya na ci gaba da tazar, Mishal ta ƙara matsawa ta tsaya a gabansa, sannan ta saka hannayenta ta karɓi matajin hannunsa, ta yi tattage dan ta ƙara tsayi, sannan ta shiga taje masa sumar.

Memakon ya tanka mata, sai ya mata banza ya juya ya barta tsaye da matajin a hannu, Mishal ta girgiza kanta ta na mitar halin wanga bawan Allah, sannan ta aje matajin a kan mirror, ta biyo bayansa.

Zama ya yi a bakin gado ya na kawar da kai. Mishal ta yi murmushi ta na tsayawa a gabansa, hannunta ta sa ta kamo haɓarsa ta juyo da fuskarsa gareta.

“Me nene?”

Fuskarsa ya ƙwace sannan ƙara juyar mata da kai, sunkuyawa ta yi ta kai hannunta kan buttons ɗin gaban rigarsa ta buɗe guda huɗu, duk bai kulata ba, sannan ta hau kan gadon ta zagaya ta bayansa, ta tsaya a kan gwiwoyinta, tare da saka hannayenta a kan kafaɗunsa, ta fara masa tausa.

“Me nene ?”

Muryarta ta tambaya bayan wani lokaci, memakon ya amsa mata, sai ya saka hannunsa na dama ya kamo nata, tare da ƙoƙarin janyota zuwa gabansa, hakan ya sa ta miƙe ta sauƙa daga kan gadon ta tsaya a gaban nasa, sai kuma ya kamo hannunta ya zaunar da ita a kan cinyarsa ta dama.

Ya ɗaga kafaɗarsa ta dama ya na sofara gashin da ya sauƙo mata kan fuskarta a bayan kunnenta, a lokaci guda yana kallon fuskarta. Mishal ta lumshe idonta ta buɗe, sannan a hankali hannayenta suka kewaya bayansa, kafin ta saka kanta a cikin wuyansa.

“Me ya faru ?”

Muryarta ta fito a kan fatar wuyansa, yanayin ya sa Kuliya lumshe idonsa sannan ya buɗe, ya saka hannayensa ya ƙara rungumeta a jikinsa.

“Game da binciken yayarki ne...”

Sai kuma ya yi shiru. Mishal ta sumbaci wuyansa ta na ƙara matse hannunta a bayansa.

“Ummhum?”

Muryar tata ta kuma faɗi a wuyansa.

“Me gadin makarantar ku ne yake san ɓatamin rai, yau da na je, babu yanda ban yi da shi ba kan ya ba ni wasu bayanai, amma yace wai sai na nemo izini daga sama, shi ne na...”

Jin ya yi shiru ya sa Mishal ɗan ɗagowa daga jikinsa ta kalli fuskarsa.

“Ka mare shi, right?”

Sai shi ma ya sunkuyar da kansa ya na kallonta.

“Rai na ne ya ɓaci”

“Na fahimta, amma ba haka ake ba, kamata ya yi ace ka tafi da yaranka, sai ku je a matsayin jami'ai, waɗanda suka je bincike, ko principal ba zai baku matsala ba”

Kuliya ya rage girman idonsa ya na kallonta, me ya sa ahi be yi tunanin hakan ba?, ya sumbaci goshinta ya na ƙara janta jikinsa.

“I love you Teddy Bear...”

Mishal ta yi murmushi.

“I hate you Abu Aswad..... Na gama abinci, mu je ka ci”

Ya gyaɗa mata kai ya na ɗagata daga jikinsa.

RABI'A POV.

Da sanyin safiya ta farka a gidan Kawu Habu, duk da jiya da daddare bata kwanta da wuri ba, kasancewar ramakon sallollinta da ta ci gaba da yi, sai da ta yi ƙoƙarin taya Mama Laure aikin gidan, amma tace ta hutar da ita ta kwanta ta yi ramakon baccinta.

Kuma ba ta musa ba, sai ta kwanta ɗin, don ba ƙaramin bacci take ji ba, wajajen ƙarfe bakwai 'yar Mama Laure ta farko ta tasheta dan ta tashi su ci abinci, abincin suka ci, sannan ta sha magungunanta da ta taho da su. Ba daɗewa kuma ta ƙara komawa baccin.

Sama-sama ta soma jin hayaniya a tsakar gidan, da farko ma kamar a mafarki take jin hayaniyar, jin hayaniyar ta ci gaba ne ya sa ta buɗe idonta. Muryar Abbansu ta ji a tsakar gidan, hakan ya sa ba shiri ta miƙe zaune, mayafinta ta raruma ta yafa a kanta, sannan ta fita tsakar gidan, don ganin meke wakana.

A dai-dai lokacin da ta fita, a Ɗan Lami ya fice daga gidan, Mama Saratu da Mama Ramatu duk sun tsa-tsaya a tsakar gidan, ga kuma Kawu Habu daga gefe. A raunane ya kalleta, sannan yace.

“Rabi sai de ki yi haƙuri, amma ba zan iya haƙura da ɗiban albarkar da Ɗan Lami ya zo ya min ba, dan haka kawai ki zo ki tafi!”

Ta ɗauka cewar ita da tashin hankali sun yi hannun riga, ta ɗauka cewar rayuwarta za ta huta da masifun da suke samunta, ta ɗauka cewar tashin hankalin da ya ɗan yi nisa da rayuwarta ya tafi har abada, ashe yajin aiki ya yi, ashe be je ko ina ba, ashe kawai ya ɗan barta ta huta na kwana ɗaya ne, ina ake so ta sa kanta?, ta fita titi ta yi karuwanci?, a'a, wannan babban kuskure ne, ko kafin Umma ta rasu sai da ta gargaɗeta a kan hakan, to gwara dai ta kashe kanta, hakan zai fi sauƙi!...

Waɗanan su ne ire-iren maganganun da take ta rayawa a ranta yayin da ta fito daga gidan Kawu Habu, babu yanda Mama Laure ba ta yi da ita ba kan kada ta fita, amma tace tun da me gidan ya koreta me za ta zauna ta yi?.

Har ta hau kan titi ba ta cikin hayyacinta, ƙafafunta har harɗewa suke gurin tafiya, ta riga ta saddaƙar da gwara ta mutu, gwara ta bi Baby da Umma ko kowa zai huta, idan ta mutu duniyar za ta fi zama dai-dai, wata ƙila iyaka nan Allah ya hukunta ƙarewar labarinta.

“...Wallahi daga Haɗejia nake!...”

Kalaman suka biyo iska tare da silalowa suka rufta cikin kunnuwanta, nan take ƙwaƙwalwarta ta tuno mata da wani wuri ɗaya da zata iya zuwa dan ta huta, ƙwaƙwalwata ta hasko mata wani wuri ɗaya da ta saba samun farin ciki a duniya, gatanta, tushen mahaifiyarta, Haɗejia!.

*Fall in love when you're ready, not when you're lonely...*

***

*Brickhall School, Kaura District, Abuja*

KULIYA POV.

Ya na tsaye daga bakin gate ɗin fita daga makarantar, kamar yanda Mishal ta bashi shawara kan ya je da yaransa sannan ya je a matsayinsa na ɗan sanda, hakan ya yi, kuma ya yi nasarar samun damar yi wa duka ma'aikatan makarantar tambayoyi.

Da yake lokacin tashi ne, gaba ɗaya ɗalibai sun firfito, 'yan day na ya ƙoƙarin tafiya gida, idan ya ɗan tsaya ya saurari bayanan megadin, sai ya ɗan juya ya ɗan yi kalle-kalle ko zai ganta. Kuma cikin wani ikon Allah a wannan karon sai ya gantan, sannan cikin kyakkyawan gani, dan tana tsaye da wani yaro wanda ke sanye da uniform, yaron na mata wata magana ita kuma ta na dariya.

Nan take Kuliya ya ji wani abu me kama da allura ya caki ƙahon zuciyarsa, ya ji kamar ya ƙarasa inda suke ya kwarfe yaron da mari, hakan ya sa duk sauran bayanan da me gadin ke masa ba ya fahimta.

Idonsa ƙuri a kansu, ya na kallon ikon Allah, juyowar da Mishal za ta yi karaf suka haɗa ido, hakan ya sa ɗan gutin murmushin da take ya ɗauke ɗip, kamar ruwan sama. Ta san yau akwai dabi a gidan nan.

*No.181, Guzape, Abuja...*

*10:30 PM.*

MISHAL POV.

Safa da marwa take a ƙofar ɗakin Kuliya, tun ɗazu ta ya dawo, kuma ta yi maganar duniyar nan amma ya ƙi kulata, ko abincinta ya ƙi ci, ta rasa inda za ta sa kanta, ba ta san ya za ta yi ba, amma dole ta bashi haƙuri a daren nan, dole su sulhunta a daren nan, dan ba za ta iya kwana ita kaɗai ba, ta riga da ta saba da kwana tare shi, bata jin yau za ta iya bacci idan babu shi kusa da ita.

Juyowa ta yi ta kalli ƙofar, sai da ta shaƙi iska, sannan ta furzar, hannunta har karkarwa yake wajen buga ƙofar, amma haka ya mata banza, kuma ya na jinta, dan ya na ganinta ta ƙaramar camerar dake maƙale a ƙofar ɗakin, wadda ido ba ya iya ganinta, kuma ba ma iyaka ƙofar ɗakin nasa kawai ke ɗauke da camerar ba, akwaita a gurare da dama a cikin gidan, kuma ta cikinta ne ya ga abun da ya faru tsakaninta da su Siyama a waccan ranar, a sanda ya ga vedion ba ƙaramin mamaki ya yi ba.

Hannun Mishal ya ƙara buga ƙofar a kusan karo na tara, zuwa lokacin har ta fara hawaye. Kuma ganin ta fara kukan ne ya sa zuciyarsa karyewa, dan haka ya miƙe ya nufi ƙofar, sai da ya yi kicin-kicin da fuskarsa, sannan ya buɗe ƙofar ya na wani cin magani.

“Ya aka yi?”

Ya tambaya ya na kallon fuskarta wadda ta yi ja saboda kuka, kallonsa ta ci gaba da yi tana kuka. Da ta rasa abun yi sai kawai ta faɗa jikinsa, ta saka hannayenta ta kewaye shi ta baya, sannan ta saki kuka me sauti, Kuliya ya ƙi ya riƙeta, duk da zuciyarsa na motsawa da ko wani ɗigon hawaye da take zubarwa. Jin bai riƙeta ba ya sa Mishal ɗagowa daga jikinsa ta na jan zuciya.

“Abu Aswad ka yi haƙuri”

Kansa ya ɗauke ya na wani shan ƙamshi.

“I am sorry”

Ya ƙi ko kallonta.

Haka ta yi ta bashi haƙuri amma ya ƙi ya ko kalleta, da ta gaji da magiyar sai ta juya jiki a sanyaye tana hawaye, taku biyu ta yi ya sa hannunsa ya janyota, bata tashi tsayawa a ko ina ba sai cikin jikinsa, tana jin hannayensa a bayanta kuwa ta sakar masa kuka sosai.

“Ka yi haƙuri please... Note book ɗin chemistry fa kawai ya tambayeni...”

Kuliya ya ƙara matseta a cikin jikinsa.

“Dariya fa na ga kuna yi Teddy Bear, kinsan ai dole na ji ba daɗi”

Ita ma sai ta ƙara riƙe shi ta na faɗin.

“Wallahi ba komai muke ba, ka yarda da ni, ai ni ma na san hakkin aure, ba zan tsaya da wani saurayin ba... Ka yi haƙuri”

Kuliya ya saketa ya na goge mata fuska, ya ɗaga kafaɗarsa ta dama ya na faɗin.

“Is okay, ki dena kukan to”

“Ka yafe min?”

Ya gyaɗa mata kai ya na ɗaga kafaɗa.

“Na yafe miki, amma kada ki ƙara masa magana... Ba ma shi kaɗai ba, ko wani yaro a school ɗinku babu ke babu shi”

Ta gyaɗa masa kai ta na jan hanci, fuskarta ya riƙe ya na kallonta, kafin ya sunkuyo da fuskarsa kan tata, sannan a hankali ya haɗe bakinsa da nata ya na kissing, hakan ya sa ba shiri Mishal ta saka hannayenta ta kewaye wuyansa ta baya tana mayar masa martani.

*Unguwar Jama'are, Haɗejia...*

*08:40 PM.*

Kusan mutum gome ne suka sa salati a tare, bayan da Rabi'a ta kai ƙarshen labarinta, tun bayan barinta gidan shekaru biyar baya har zuwa yau babu abun da ta ɓoye musu.

A ɗazu da yamma ta sauƙa a garin Haɗejia, farkon ganinta sai da 'yan uwan nata suka yi murna, amma kuma ganin yanayinta da kuma damejin dake fuskarta ne ya sace musu gwiwa, haka suka shiga jero mata ruwan tambayoyi, amma bata samu ta amsawa kowa ba.

Har zuwa ƙarfe takwas, kafin kakanta ya aiko kiranta, kuma daga lokacin da ta iso falon kakan nata sai ta tarar da ba shi kaɗai ne a ciki ba, duka kawunnenta da 'yan uwan kakan nata duka suna ɗakin. Sannan ko da suka tambayeta ba ta ɓoye musu komai ba, tun daga wahalar da ta yi ta sha a gidansu, har zuwa aikatau ɗin da take, har kan fyaɗen da aka mata, zuwa korarta da Ɗan Lami ya yi.

Kakanta Alhaji Ali ya ci gaba da kallonta, wani abu na yawo a cikin kansa, ɓaro-ɓaro ya na ganin yanda tarihi ke maimaita kansa, irin abun da ya faru da me sunanta ne ya faru da ita, 'yarsa ta cikinsa da ya kora saboda ta yi cikin da ba na aure ba, wanda ya zo ya yi nadama daga baya, har ya shiga fafutukar nemanta, amma kuma ko da ya samu inda take sai aka sanar da shi ya je a ƙurrarren lokaci, don kuwa ita Rabi'an ta rasu, yaranta 'yan biyu da aka ce ta haifa kuma ba a san duniyar da suka shiga ba. Tsoho Alhaji Ali ya ji ƙwalla ta cika idonsa.

“Irin cin amanar da Ɗan Lami zai mana kenan?, Bayin Allah a nan a gabanku fa nake tura masa kuɗi duk sallah na ce a yi wa Rabu ɗinkin sallah, amma kun ji, rabonta da sabin kaya tun wanɗanda ta bar gidan nan da su”

Cewar kawu Abdullahi, babban ɗa a wurin Alhji Ali, haka kuma babban wa a wurin su Maryam.

“Ni ai ba wannan ne ya bani mamaki ba, kadarorin Maryam ɗin da ya ɗaga ya siyar su ne suka ba ni mamaki”

Cewar Kawu Hassan, ƙani a wurin kawu Abdullahi.

Haka dai suka ci gaba da maida zance, har da masu cewa ƙarar Ɗan Lami ɗin ya kamata a yi, Rabi kuwa jinsu kawai take, dan ita kaf duniya yanzu ba wannan ne a gabanta ba, farin cikinta ɗaya, da danginta suka karɓeta, suka nuna mata ƙauna kamar yanda suka saba. Sai kuma matsalarta; Raja!.

Har yanzu tunaninsa bai bar cikin kanta ba, har yanzu ta na iya hango fuskarsa a cikin kanta, har yanzu ta na iya hango kanta a tsakanin hannayensa, har yanzu akwai sansa a cikin zuciyarta, amma ko ta ƙi ko ta so dole ta cire wannan son, don ba zai amfaneta da komai ba, face ya wagalar da ita, aure tsakaninta da makashi ɗan daba ba abu ne me iyuwa ba, wai ita ya aka yi ma ta yarda da shi har haka?, ina hankalinta ya shiga da har ta bari zuciyarta ta yarda da shi, ta inda har ta kasa tambayarsa wani aiki yake. Me ya sa idonta ya rufe ta kasa ganin gaskiya?. Wani abun farin cikin ma shi ne; da bata faɗa masa cewar shi ɗan uwanta ba ne, wannan shi ne kaɗai arziƙin da aka yi. Ta raya hakan a ranta, don ita ta manta da maganar da ta faɗa masa a sibiti.

Haka suka yi kiɗansu suka yi rawarsu, amma ba ta ƙara cewa kanzil ba, har suka babbata haƙuri, kawu Abdullahi ne yace ta shirya zuwa gobe zai kaita a mata gwaje-gwaje, sai a lokacin ta yi magana, ta sanar masa da cewar duk wasu gwaje-gwaje da suka dace babu wanda ba a mata ba, amma yace shi bai yarda ba, kawai ta shirya zai kaita a sake mata wasu, ba ta ƙara masa musu ba tace to, sannan ta miƙe ta koma cikin gidan.

Kai tsaye ɓaangaren kakarsu ta yi, inda ta san 'yan matan gidan suna tare a can, dan a dai-dai lokaci irin wannan a can suke taruwa. Kuma kamar yanda ta ayyana a ran nata sun taru a can ɗin.

'Yan mata shida ne sa'o'inta a gidan, Momi, Nafisa, Fati, Jidda, Kulsum da Kairiyya, su na ganinta su ka yi shiru, kowa ya zuba mata ido ya na kallo, dan kaf cikinsu babu wanda ya san da zuwanta, a sanda ta shigo garin ma suna islamiyya.

Gaba ki ɗayansu so suke su ganeta, kammaninta na musu kama da na wata da suka sani, kallon ƙurillar da ta ga suna mata ya sa tace.

“Ya da kallo haka 'yanmatan Waliki family?”

Kusan a tare suka fashe da dariya suka iyo kanta. A dai-dai wannan lokacin kakarsu ta fito daga ɗakinta ta na ɗingisa ƙafa, kujera ta samu zauna ta na kallonsu.

“Rabi'a?, wai yaushe ma kika zo garin?”

Cewar Kulsum ta na dariya. Rabi ta zauna a kujera ta na faɗin.

“Ɗazu da yamma, kuna islamiyya lokacin”

“Wayyo Allah, wallahi na ji daɗin zuwanki, kusan shekara biyar fa rabonmu da ke”

Cewar Fati ta na matsawa kusa da ita.

“Ke Allah ya yi da ke kina nan za ayi bikin Nafisa”

Kairiyya ta faɗa, baki buɗe cike da mamaki Rabi ta kalli Nafisan da ta kawar da kanta, saboda Hajiya kakarsu dake wurin.

“Wai dan Allah?”

“Wallahi kuwa, nan da wata ɗaya da sati ɗaya” Jidda ta amsa mata.

“Ke Rabi a ina kika ji wannan raunin na fuskarki?”

Momi ta tambayeta, Rabi ta kai hannu ta shafa gefen fuskarta na hagu, sai da ta haɗiye wani abu sannan tace.

“Haɗari ne... Kai ni yanzu ku ba ni labari, ya ake ciki ?”

Daga haka suka shiga hira a kan batun bikin, suna bawa Rabin labarin yanda suka tsara bikin, da yanda zai kasance, har kusan ƙarfe goma suna can, dan abincin dare ma tare suka ci.

Kasancewar 'yan matan su duka ɗakinsu ɗaya, ya sa ita ma ta kwana a cikinau, dan dana tun can tare auke kwana, gadon Rabin ma na da yana nan, kuma yanzun ma a kansa ta kwana.

*T.O.C Douglas Crescent, Kaura District, Game Village, Abuja.*

RAJA POV.

_🎶It was just two lovers..._

_Sitting in the car, listening to blonde_

_Falling for each other_

_Pink and orange sky_

_Feeling super childish_

_No donald glover🎶..._

Waƙar dake tashi kenan a cikin sifukun gidan, wanda Raja ya ƙure volume.

Tsaye yake daga gaban mirror, ya na taje sumar kansa, sanye yake cikin wata ash shadda, a hankali bakinsa ya ci gaba da biya waƙar Golden hour ɗin dake tashi a falo.

“I was all alone... With the love of my life... She's got glitter for skin... My radiant beam in the night... I don't need no light to see you... Shine... It's your golden hour...”

Sai kuma ya yi shiru ya na kallon kansa a mirror, yayin da ya aje matajin hannunsa, bayan wani lokaci me tsayi yau shi ne sanye da manyan kaya, ya daga kafaɗarsa ya na murmushi, ya gyara wuyan rigar jikinsa, ya ƙara fesa turare a jikinsa, sannan ya finciki hularsa ya fito.

“Huh?! Dude? Yau ina zuwa?”

Cewar Rhoda kenan, yayin da ta fito daga kitchen, hannunta na dama riƙe da plate, Raja ya kama kumatunanta ya na ja.

“Zance zan je”

Rhoda ta shafa kumatunta da ya saki da hannunta na hagu. 

“Guys, ku shigo ku ga ikon God!”

Kiran da ta ƙwalawa su Jagwado ne ya sa suka afko cikin gidan babu shiri. Kallon Rajan su ma suka tsaya suna yi, a karo na farko tun bayan saninsu da Rajan da kuma Rhoda, ba su taɓa ganinsu da mabanbantan kaya ba, a ko da yaushe kaya kala ya suke sawa, sai yau.

“Allah de ya biya oga Raja, ina za ka fasa haka?” Alandi ya tambaya.

“Zance zan je”

“Kutumar dumadu, Kaga Oga Raja namu, Allah ya biya, gayu, oga fa ya rufta ramin ƙauna Allah Wallahi”

Cewar Zuzu ya na wani ɗaɗɗaga hannu. Raja ya yi murmushi ya na girgiza kansa.

“Wai Zuzu ban hanaku magana irin haka ba?”

Zuzu ya shafa kansa ya na kallon ƙasa.

“Sabo ne oga Raja, amma za mu dena da yardar me duka” ya faɗi muryarsa babu wani banbanci da ta ɗazun.

“Ku fa?”

Raja ya tambaya yana kallon sauran.

“Aah, ai muma hakan take oga, ko ya kuka ce gayu?”

Alandi ya faɗi ya na kallon su.

“Haka ne”

Jagwado ya amsa.

“Na zo na raka ka?”

Rhoda ta faɗi ta na aje plate ɗin hannunta, wanda ke ɗuke da alale. Raja ya maka mata harara.

“Wa za ki bi?... Kama hanyar ki can joo!”.

*Unguwar Madallah, Suleja, Niger State.*

Da gudu Fatima ta shigo gidan har tana bangaje Saratu da ta fito daga banɗaki.

“Ke Fatima mi ye hakan?”

Inaa, sam ba ta tsaya ba sai da ta dangana da ɗakin Habiba.

“Ke dallah mi ye hakan za ki faɗo kaina?”

Habiba ta tambaya ta na miƙewa. Fatima ta dafe ƙirji ta na zaro ido, hannunta ta ɗaga tana nunawa Habiban ƙofar ɗakin.

“Wa... Wani na... na ga a waje... Kamarsu ɗaya da... Da Rabi!”

Wani irin juyi kayan cikin Habiba suka yi, don a sanda fatiman ta ambaci kamar mutumin da ta gani da Rabi, ƙwaƙwalwarta ta hasko mata 'yan uwan Maryam na Haɗejia. To ko su ne suka zo kamata ?, wata ƙila Rabi ta sanar musu da duk irin abubuwan da ta mata, shi ne suka zo dan su kamata. Muƙut!, ta haɗiye yawu, tunawa da ta yi da labarin irin kuɗin baban Maryam ɗin da aka bata. Ba shiri gumi ya shiga tsatsafo mata, cikinta har wani ƙugi yake.

Sallamar da Saratu ta ji a waje ya sa ta leƙa, kasancewar akwai hijabi a jikinta. Ita kanta sai da ta firgita, ganin wani mutum sak Rabi, tsaye a soron gidan nasu, amma sai ta ɓoye tsoronta ta amsa sallamar tasa. Ba tare da ta tambayeshi wa yake nema ba, ta masa lamini da ya shigo cikin gidan.

Wata kujerar roba ta bashi, tace ya zauna a kai. Ya na zama a kan kujerar Habiba ta bankaɗo labulai ta fito, Fatima na biye da ita.

Curko-curko suka yi daga bakin ƙofar ɗakin Habiban suna kallon ikon Allah. Saratu ce ta kawo masa ruwa, sannan ta zauna suka gaisa.

“Am... Rabi'a nake nema”

Wani irin ƙara cikin Habiba ya saki, da saida ta saki wata siriyar tusa, shikenan, wata ƙila tata ta ƙare, kenan da Rabin ta bar gidan Abubakar ba can ta yi ba, tun da ga shi su ma nemanta suke, amma garin yaya har aikin nan ya karye?, don kuwa ita ta san ta sa a yiwa 'yan uwan Maryam aikin da duk tsawon shekarun da Rabi za ta yi a gidan ba za su taɓa neman ganinta ba.

“Amma waye kai bawan Allah, ko daga Haɗejia kake ?”

Raja ya sosa kansa ya na faɗin.

“Sunana Zaid, kuma ba daga haɗejia nake ba”

“Laaa!, da ma kai ne Zaid ɗin, ai ko Rabi ta na yawan bani labarinka, sai dai ko da wasa ba ta taɓa faɗa min cewar kuna kama ba”

Raja ya ɗaga kafaɗarsa ya na faɗin.

“Allah sarki”

“To Rabi dai ba ta gidan nan, satin da ya wuce Umma ta koreta, ita kuma sai ta koma gidan kawu Habu, gidan na ɗan gaba da mu”

Da farko har hankalin Habiba ya kwanta, jin shi wannan bawan Allahn ba daga haɗejia yake ba, amma kalaman Saratu su ne suka dawo da tsoron sabo. Kuma cikinta bai ƙara rikicewa ba, sai da Raja ya juya ya kalli side ɗinta. Hatta da idanuwansa irin nata ne, banbancin kawai shi ne na sa a lumshe suke, kuma ƙwayar cikinsu kalar ruwan toka ce.

Raja ya dawo da dubansa kan Saratu.

“Ko za mu je ki raka ni gidan shi kawun?”

Ya faɗi wani abu na masa ɗaci a maƙwagoro, dole ya san yanda zai yi da matar nan, dan ko me ya samu Ammatansa ita ce sila.

“Innallillahi wa inna ilaihi raji'un... Zaid wai sun ce tun washe gari shi Abba ya zo ya yi masifa kan sai Kawu Habu ya koreta, kuma tun a ranar ta bar gidan nan ɗin”

Abun da Saratun ta faɗi kenan, bayan da ta shiga gidan kawu Abubakar ta fito, Raja dake jingine da ƙofar gidan ya gyara tsatuwarsa ya na kallon bakinta, dan so yake ya fahimta shin, da wani yare ma take magana ne?, shi fa bai gane ba, Ammatansa ba ta gidan nan?, to ina ta tafi?.




Post a Comment

0 Comments