TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

ZURI'A DAYA PAGE 9-10

 *PAGE* *9*~*10**


 *Sun* shak'u da juna NUWAIRA da MEENAL duk inda zasu cikin makarantar suna tare, haka kuma su KAMAL suna zuwa makarantar, tsakanin MEENAL da FAWAS sai harara dan ko kad'an basa shiri, KAMAL yana yawan yin ma MEENAL harka sun Saba da juna,


A yau ne sukayi dasu NUWAIRA cewan zasu zo su kaisu shopping,haka ko akayi sun had'u a cikin makaranta,


NUWAIRA ce sanye cikin matsatsun riga da wando sai gyale da ta rufe rabin gashin ta ga Sunglass da tasa, yayin da MEENAL ke sanye cikin riga da skirt na wani material sai dai tasa hijab iya gwiwa,


Gaisawa sukayi sannan suka shiga mota,suka nufa SAHAD STORE, duk abin da suke so suke zab'a ita dai MEENAL tafi d'aukan abubuwan ciye-ciye, sai NUWAIRA ke bata wasu abubuwan, bayan sun gama ne,suka biya Restaurant suka d'an yi lunch dayake rana tayi,


Ko da suka dawo makaranta har hostel NUWAIRA ta raka MEENAL, sannan suka wuce,




Bayan wani lokaci



Suna ta Shiri zasu fara exams, ga NUWAIRA ba wani Mai da hankali take a karatu ba,Nan ta rok'i alfarman MEENAL da ta dinga kwana a gidansu tana koya mata karatu, nan ta amince,ta shirya suka nufa gidansu NUWAIRA,



Gida ne babba Mai shegen kyau, ga wasu flowers da suka k'awata cikin gidan,a parking lot driver yayi parking inda su MEENAL suka fito, cikin farin ciki taja hannun MEENAL tace" you're highly welcome to our house"


Murmushi tayi kawai tana mamakin kyawun gidan tun bata shiga ba, straight parlour'n gidan suka shiga,


Mom na zaune tana ta faman aiki a laptop, Jin wata murya da ba zata tab'a mancewa bane yasa ta mik'e tsaye ba shiri, wata kyakyawar budurwa ta gani tare da NUWAIRA, 


K'arasawa ciki sukayi yayin da NUWAIRA ke cewa"mom ga friend d'ina"


MEENAL ta gaishe ta cikin sanyin muryan ta,ba k'aramin rikicewa mom tayi ba dan maganar su iri d'aya da ZAINAB, da k'yar ta dai-dai ta kanta ta amsa cikin k'arfin hali,


Zama sukayi yayin da Mai aiki ta kawo musu drinks, da k'yar mom tace" ke y'ar nan garin ce?"


Da sauri NUWAIRA tace"No mom a wani k'auye take karatu ne ya kawo ta nan"


Ba haka mom taso ba gaba d'aya bata son y'ar ta na hurd'a da talakawa, sai dai ba yanda zatayi tunda karatu zata dinga koya mata zuwa su fara exams,


NUWAIRA ce tace su nufi bedroom dan su huta, nan suka shiga bedroom,Masha Allah shine abin da MEENAL tace a ranta,dan kamar Kuna k'asar waje ne tsabar had'uwan bedroom d'in,babba ne sosai, akwai wani corridor ta ciki akwai wani toilet da wani bedroom Kuma Wanda Kaya ne dasu takalma da handbags ne, Kai gaskiya an kashe ma bedroom d'in NUWAIRA dukiya, 


Wanka tayi sannan tace ita ma taje tayi, ai da ta ga toilet d'in ba k'aramin kyau yayi mata ba gashi komai orange and white colour ne, haka tayi wanka ta fito, can hannun ta NUWAIRA tayi ta shigar da ita d'akin kayan nan tace ta zab'a duk abin da take so ta d'auka tayi amfani da shi,


Da k'yar ta d'auka wasu dogayen riguna na English wears tare da veils d'in su, 


Da missalin k'arfe 8:00pm


Duk sun halara a dinning table don yin dinner, sai dai Babu MEENAL dan cikin ta na ciwo shine aka Kai mata nata bedroom,


Da sauri NUWAIRA ta nufa upstairs dan bata son barin MEENAL ita kad'ai tunda ba ta jin dad'i, cikin mamaki Daddy yake tambayar mom ko lafiya NUWAIRA ke sauri haka, Nan ta fad'a Mai komai, yaji dad'in yanda yanzu NUWAIRA ta maida hankali tana son karatu, 




Two days later


 

Sosai takejin dad'in yanda MEENAL ke koya mata karatu gashi tana ganewa, sannan tana jin dad'in zama da MEENAL ita ma haka take jin dad'in zama da NUWAIRA, Kuma har yanzu basu had'u da Daddy ba,



Ranar suna zaune a parlour sai ga Daddy ya dawo, kallon MEENAL yayi nan take yaji k'aunar yarinyan bai san meyasa ba, cike da ladabi da biyyaya ta gaishe shi,ya amsa cikin farin ciki, gaskiya zai so NUWAIRA tayi k'awance da wannan yarinyan mai ladabi Dan iyyayen ta da gani sun bata tarbiyya nagari, wucewa yayi yana murmushi,




Sun fara Exams, sun dage sosai ba wasa sun maida hankali, har suka gama lafiya sai jiran results, MEENAL ta shirya kayanta dan tafiya k'auye, NUWAIRA Kuma tace sai ta Kai ta har gida duk da Mom ta hana ta amma tak'i,





K'arfe 2:00pm suka Isa k'auyen, a k'ofar wani gidan k'asa driver yayi parking, NUWAIRA tayi mamaki sosai dama nan friend d'in ta ke Rayuwa wannan ai ko gidan Mai aikin su sai yafi wannan,haka ta suka shiga daga ciki,


Ummie na zaune a tsakar gida tana tankad'en garin tuwo, sai ganin y'ar ta tayi MEENAL, cikin farin ciki ta k'arasa tace"Ummie na I really miss you" cike da k'aunar y'ar ta take mata barka da dawowa,


D'aga kan da zatayi sai taga wata kyakyawar budurwa lokaci d'aya taji k'aunar ta Nan tace"Bissmillah shigo" ta mik'e tare da gyara tabarma, zama NUWAIRA tayi ta gaishe ta cikin farin ciki ta amsa nan tace" ke haka akeyi MEENAL sai ki shigo ki bar ta?"


Cikin dariya tace" No ba haka bane Ummie na farin cikin ganin ki ne, sorry NUWAIRA"


Murmushi kawai tayi, Nan MEENAL ta kawo ma NUWAIRA ruwa duk da tasan da wuya tasha tunda bottle water taga take Sha, ga mamakin ta sai taga ta sha, 


Bayan sallar la'asar ne, NUWAIRA tayi musu sallama zata tafi, cike da kulawa Ummie tace"tafiyan dare zakuyi gashi yamma yayi da kin hak'ura kin kwana zuwa gobe Kar kuyi dare"


Murmushi tayi tace"ba komai,"


Haka sukayi sallama NUWAIRA ta shiga mota suka d'auki hanya,yayin da take jin k'aunar mahaifiyar MEENAL a ranta bata san meyasa ba,ko don ta nuna kulawar ta gare ta ne, 




Sai bayan isha'i ne Kaka ya shigo gidan, ganin MEENAL ta dawo yayi farin ciki sosai, can sai ga Aliyu da yake gidansu na kusa da nasu MEENAL ne, cikin farin ciki suka gaisa Nan akayi ta hira cikin nishad'i,



******************




 Kwance yake kan bed,yayi zurfi cikin tunani a gaskiya yayi missing d'in ta ko dan fad'an da sukeyi, gashi sai yanzu ya gano cewa yana k'aunar ta, Dan ko rufe ido yayi sai ya ganta, d'aukan wayan shi yayi da sauri ya kira NUWAIRA yace please ta bashi address d'in inda MEENAL take, tayi mamaki amma sai ta share nan ta fad'a Mai sunan k'auyen da gidan su, godiya yayi mata ya kashe wayar,


Shiryawa yayi cikin riga navy blue da black jeans,wow looking handsome, fitowa yayi, Nan ya tarar da Mommy'n shi a parlour sai faman aiki take a system,


Tana ganin shi tace"FAWAS sai Ina haka naga kamar you're in hurry?"


B'ata fuska yayi yace" Mommy zanje wani guri ne"


Mik'ewa tayi tace" What how many times have I told you not to call me Mommy, meyasa kake son tsufar da nine haka da wuri?"


Rik'e Kan shi yayi dan ya Saba da halin Mommy'n nashi, Dad d'in shine ya shigo yana dariya yace" my son meyasa kake tsufar min da mata ne wai?"


Murmushi yayi yace"Dad she's already old"


D'auko pillow tayi ta jefa mai, tunda ya fad'i abin da ta tsana, Dad ne yayi saurin tarewa yace FAWAS ya tafi abin shi, fita yayi ya shiga mota yana ma Mommy'n shi dariya,



Cikin lalashi Dad yace" ai Mata ta bata tsufa, ko ya Kika ce my one"


Hararan shi tayi da wasa tace"bayan sai da ka gama goyon bayan shi"


Da sauri ya k'arasa yana lalashin ta,







Lokacin da ya Isa k'auyen bai wani Sha wahala ba ya gane gidan, parking yayi ya fito, wani yaro ya samu ya aika ciki ya kira MEENAL,




Ummie ce zaune a tsakar gida, yaron ya fad'in aiken da akayi mai, tambayar shi tayi ko wane ne Nan yace ai wani Mai mota ne Mai kyau,Jin haka sai Ummie taji tsoro Kar dai yarinyan Nan ta fara soyyaya da maza ne, d'aukan hijab tayi ta fita Dan ta ci mai mutunci,



Yana zaune kan mota sai ga Ummie ta fito, kallon shi tayi tace"Kai lafiya dai,meye ne kake neman MEENAL?"


Saukowa yayi ya gaishe ta cikin ladabi, amma ya rasa wani amsa zai bata,


Ummie tace"to Bari in gaya maka, ni y'a ta ba irin marasa kamun Kai bane,tukuna ma wai tsaya, mai kazo yi a k'auyen nan?"


MEENAL ce ta dawo daga aiken da akayi mata,da mamaki ta k'arasa gurin ganin FAWAS, Ummie na ganin MEENAL tace"wuce kema ki shiga ciki gani nan zuwa kanki"


Cikin rashin fahimta tace"meya faru ne Ummie na?"


Tace"rufe min baki a Ina Kika san wannan da yake neman ki?"


Dariya tayi tace"oh ai d'an'uwan NUWAIRA ne shi"


Jikin Ummie ne yayi sanyi tace"shine bakayi min bayani ba ka barni Ina ta massifa, to ai sai ki wuce ki kawo tabarma da ruwa"


Shigewa ciki tayi yayin da Ummie tace"kayi hak'uri kaji rashin sani ne,ai NUWAIRA yarinyan kirki ce"


Murmushi yayi yace ba komai, ta yaba da halin shi a lokacin Nan take tambayar shi ko Yana zuwa makarantar su MEENAL ne dan tasan idan MEENAL bata yin samari ko k'awayen banza, shine yace Yana zuwa ba sosai ba Kuma MEENAL bata da k'awaye bare samari, ta yarda da shi Nan ta bashi amanar MEENAL ta Kuma rok'e shi da ya dinga kula da ita, ya Kuma amince,



Shiga ciki Ummie tayi ya rage daga ita sai shi, 


Tace"Ya akayi kasan gidan mu ne?"


Kawar da Kai yayi yace"ban sani ba"


Tab'e baki tayi tace"to ai ya rage naka,yanzu dai yasu KAMAL dafatan suna lafiya?"


Yace"lafiya suke"


An d'auki 15minute bai k'ara magana ba can ya mik'e tsaye yayi mata sallama, godiya tayi Mai na ziyaran da ya kawo mata, Nan ta shiga gida yayin da shi ya d'auki hanyar cikin Abuja,









Da daddare suna zaune ana Hira ana cin tuwo miyar kuka da yaji dadawa, Ummie ce ta fad'a ma Kaka Wanda yazo,inda yace"to ke in Banda abin ki ai ya Kamata ki bar yarinyan Nan ta tsayar da mijin aure amma inkin Hana ta soyyaya kenan baza tayi aure ba ko sai karatu?"


Tace"ba haka nake nufi ba,Ina son dai ta natsu ne guri d'aya Kar ta had'a soyyaya da karatu"


Yace"Eh na fahimce ki,in ma ta tsufa a gida ai sai muyi auren mu ko Mata ta?"ya k'are da dariyan Wasa,





Turo Baki tayi tace"Allah ya kyauta, gara ka samu wata tshohuwa dai-dai da kai,ka aura,tunda kak'i aure"ta wanke hannun ta ta shiga d'aki, dariya yayi yace ai gara ta dage ko ya bada ta sadaka tunda tace ya ttsuf


*Nima nace da gaskiyar ka Kaka*😂


Post a Comment

0 Comments