TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Yadda Kaddara taso page 34

 *BABI NA TALATIN DA HUƊU (34)*


*West Pavilion, Tafawa balewa square TBS complex, Victoria Island, Lagos...*

Heleen ce zaune a kan ɗaya daga cikin kujerun dake falon gidan, codeine take shaƙa, dan kanta ya ɗau zafi, bata ganewa komai, babu abinda yake ƙona mata rai irin yanda taga matar Tafida, Tafida ?, ta yi imani cewa san Tafida shine ajalinta.

Ta ɗaga kanta sama bayan ta shaƙo hodar ibilis ɗin, a hankali kuma ta sauƙe kan nata, ta dishi-dishin da take gani taga siffar Tafida tsaye a bakin ƙofar falon, tunaninta shaye-shayen da ta yi yau ne yasa har take ganin siffar Tafidan, dan haka ta jingin da jikin kujerar, hawaye na sauƙo mata a ido, kalabar kanta ta sauƙo mata kan fuska.

Idonta ta rintse ko wannan siffar ta gabanta zata b'ace, amma sai taga tana nan bata b'ace ba, hakan yasa ta tabuɗe idonta da kyau, ta yanda zata samu tagan shi da kyau, wata iriyar wutar bala'i da masifa ta gani a idonsa, duk da a bige take ta ga yanda yake mata wani irin kallo, babu abinda ya ƙara kaɗa hanjin cikinta irin yanda kalar idonsa ta rikiɗe mata zuwa ja. Ta kafeshi da ido har ya ƙaraso gabanta.

A yau Tafida ya yi wa kansa alƙawarin kawo ƙarshen iskanci Heleen, he will make sure that he crash her fucking life.

Babban kuskuren da ta tafka shi ne tab'a masa Maryam da ta yi, ya tabbatar da wannan shi ne babban kuskuren da ta tab'a tafka irinsa a gaba ɗayan rayuwarta.

 Yana ƙarasa inda take be yi wata-wata ba, ya damƙi wuyanta ya ɗagata sama, ya shiga naushin fuskarta da ɗayan hannun nasa.

 Heleen ta shiga bubbuge hannunsa cikin neman ɗauki, kafin da ƙyar ta samo miryarta ta ƙwalawa yaranta kira a wahalce.

Babu b'ata lokaci suka fito daga ɗakunansu, kuma suna ganin yanda aka shaƙe ogar tasu sai suka yi kan Tafida, suka shiga dukansa amma ko gezau be yi ba, ji ya yi suna takura masa dan haka ya saketa ya komo kansu, ya shiga dukansu kamar da aka aiko shi, bai barsu ba saida ya kai kowannen su masa.

Sannan ya dawo kan bakar she**yar dake yashe a ƙasa, da ƙyar ta samu ta iya miƙewa a kan ƙafafunta, ganin kamar idan ta ƙyale Tafida kushewa zai kaita yasa ta kai masa naushi, kasan cewar a bige take, babu wani kuzari a jikinta, gashi kuma shi na miji ne, marfin ba ɗaya ba, kuma ga ba shi kaɗai ba ne, akwai baƙin ruhinsa tare da shi.

Hannun nata ya murɗe, jI kake ƙass!,ƙass!, ƙashin hannun na karyewa, ƙarar karyewar ƙashin ta fito tare da ƙarar Heleen ɗin, ta kai ɗayan hannun nata ta dafe wurin tsabar azaba, duk wahalar da ta sha a rayuwa bata tab'a shan makamanciyar wannan ba, bata tab'a sanin cewa haka Tafida yake ba sai yau.

Ɗayan hannun nata ya kama shima ya karya, yanzu kam saida ta cika gidan da ihu, be ƙyaleta haka na seda ya mata kara uku.

Kafin ya saketa ta faɗi ƙasa, sai kukan azaba take, a hankali ta dube shi, taga kalar ƙwayar idonsa, ga fiƙar da ke bakinsa data sauƙo, nan take wani tsoro ya ƙara mamayeta, rabonta da ta ji tsoro a rayuwarta tun sanda ta shiga kungiyar su, amma yau gata tana jin tsoron wani abun da ta so a baya.

“Idan kika ƙara kusantar koda inuwar matata ne, da ranki zan rabaki, fatan kin gane ?”

Kuma bai jira cewarta ba ya miƙe ya fita, Heleen ta ƙarawa kukanta volume, bata tab'a sanin cewa aljani take so ba sai yau, ashe dama Tafida aljanine ?, to me yasa ita bata tab'a ganin hakan ba ?, kawai kyansa ne ya ruɗeta yasa ta fara sansa, yanzu azabar da ƙasusuwan jikinta ke mata itace ta dameta, ko sanda aka harbeta bata ji azaba irin wannan ba.

Da ƙyar muryarta ke fita wajen kiran sunan ɗaya daga cikin yaranta, shima da ƙyar ya miƙe kan ƙafafunsa, ya dafe ƙafarsa dake masa zugin azaba.

“Ka kira min doctor”

“A'a oga, asibiti ya kamata ace an kaiki”

“Ka kiramin likita nace, bana buƙatar ƙara zuwa asibit, ka kiramin wani likitan!!”

Ba zata ƙara wannan gangancin ba, dole ne ta kaucewa hanyar da zata ƙara haɗata da wannan aljanin, ba zata ƙara zuwa asibiti bama, balle taje ta ga wani aljanin shi ma ta fara sansa. Ita da Tafida kuma wata ƙila se a wata rayuwar, babu ita babu shi, ba zata ƙara bin hanyarsa ba ma.

***

“Ka shiga ta farfaɗo”

Cewar Dr. Ola yana kallon Tafida, wanda bayan ya bar gidan Heleen gidansa ya koma, ya yi wanka sannan ya sauya kaya, ya ɗebarwa Maryam wasu kayan da zata saka gobe idan zasu dawo gida, dan ya riga ya yanke cewar daga yau bazata ƙara kwanan asibiti ba. Bayan ya fito shi ne ya shiga gidansu Ilham, ya faɗawa babanta sannan ya dawo asibitin. 

Ya ɗago da idanuwansa da suka koma blue bayan ya sauƙe fishinsa ya kalli Dr. Ola.

“Me ya sameta ?”

Dr. Ola ya ɗan tab'e baki cikin faɗin.

“Kada ka damu fa, she is alright, babu wata damuwa yanz.....”

“Me ya....sameta ?”

Ya maimaita tambayar cikin wata murya da shi kansa zai iya cewa ba tasa bace. Dr. Ola ya haɗiye wani abu sannan yace.

“Akwai rauni a gefen fuskarta, da alama dukan wurin a kayi, sannan an buga mata kai da bango, sai kuma wunyanta da aka saka ƙafa a ka taka, shi ne kawai”

Tafida ya ɗaga kansa sama yana hasaso yanda abun ya kasance, ina!, gaskiya hukuncin da ya yiwa Heleen ya yi kaɗan, bai kamata ace ya barta haka ba, tana buƙatar ƙari, saide kuma lokaci ya ƙure, dan zuwa yanzu yasan wata ƙila tana asibiti, domin karaya uku ya mata a kowani hannu, ga kuma yanda ya daki gefen fuskarta.

Kansa ya sauƙe yana karb'ar file ɗin Maryam daga hannun Dr. Ola, sannan cikin dakiya yace.

“Ka bamu takardar sallama zuwa gobe, dan bazata ƙara kwana a nan ba”

Da mamaki Dr. Ola yake kallonsa, can kuma sai ya tab'e baki, tunawa da ya yi ashe shima likita ne. Sai kawai ya gyaɗa masa kai.Daga haka ya yi gaba ya bar ƙofar ɗakin.

Saida Tafida ya haɗiye wata busasshiyar iska a maƙogwaron sa, sannan ya murɗa handle ɗin ƙofar ɗakin, tun daga inda yake ya fara jiyo sahibin nasa, wato bugun zuciyarta, saide ba a tsorace yake bugawa ba, ba kuma cikin nishaɗi ba, ba cikin farin ciki ba, haka kuma ba cikin ƙunci ko damuwa ba, yana bugawa ne cikin rauni da gazawa.

Saida ya ɗanyi jimm, yana kallonta a kan gadon, kafin ya iya daurewa kansa ya ƙarasa jikin gadon, a lokacin da itama ta kai dubanta kansa, wuyanta naɗe da bandage ga iskar oxygen da aka saka mata, dan bata iya jan numfashi me kyau, sai kanta da aka naɗe da bandage.

Tana ganinsa ƙwalla ta taru a idonta, kuma a hankali ta silalo, sai yanzu ta shiga tuna yanda ta ji raɗaɗi da azaba bayan matar nan ta take mata wuya da ƙafarta, cike da rashin imani take mitsika mata wuyan nata, kuma har yanzu ji take kamar ma ta karya mata ƙashin wuyan ne.

Tafida na ganin ta fara hawaye, ya yi saurin ake jakar dake hannunsa sannan ya danna wani switch a jiki gadon, gadon ya ɗan ɗago sama daga wurin kanta, ya zama kamar a zaune take, zama ya yi a gefen gadon, yana dubanta cike da tausayawa.

So take ta yi kuka me sauti, amma ta rasa sautin nata, ko yawu bata jin zata iya haɗiyewa, Ita da Allah ne kaɗai suka san yanda take ji, hatta da numfashin ta da ƙyar take iya kamoshi.

Tafida ya riƙo hannayenta ya kai setin bakinsa ya sumbata, bisa ga mamakin Maryam sai ta ga yana hawaye, ta ji zuciyarta ta karye, ashe har akwai abinda zai saka Tafida kuka ?, bata tab'a ɗaukarsa a irin wannan mutanen ba, hawaye yake sosai kuma yana kallonta, itama nata hawayen suka ƙara gudu tana ci gaba da kallonsa, yayin da take jan iska da ƙyar.

“I am so sorry, Miriam, duk abinda ya sameki nine sila, ni naja miki Maryam, kullum bani da addu'a da ta wuce kada Allah yasa na zama sanadiyyar cutuwarki Miriam, amma na makara, ki yafeni Miriam, ki yafeni”

Muryartasa har wani rawa take sbd hawayen da yake, wani abu da ba sabonsa ba, bai cika yin kuka ba koda lokacin da yake tasowa, kome za'a masa zai jure, amma yau akan Miriam ɗinsa ya koma me rauni, ya ji bazai iya jurewa ba, dole ne ya zubar da hawaye, wata ƙila ta ji tausayinsa ta yafe masa.

Duk da Maryam na cikin halin raɗaɗin azaba saida ta ɗago da hannunta ta kai kan fuskarsa tana share masa hawaye da ƙyar, ya kama hannun nata yana sumbata, sannan yace.

“Kinajin zafi ko ?”

Bazata iya gyaɗa masa kai ba, bare ta bashi amsa, kuma shima yasan amsar tata, dan haka ya saki hannyenta, ya kai nasa hannyen duka biyu setin wuyanta, sannan ya lumshe idonsa.

Maryam tana ganin yanda tafukan hannunsa ke zama jajawur, kamar garwashi, kuma tana ganin yanda yake ciccije baki, kamar yana zuƙe ciwon jikin nata zuwa nasa jikin.

Kuma a hankali, a hankali raɗaɗin yake raguwa daga wuyanta, taji kamar ana zare mata ciwon.


*Washe gari...*

*Da misalin 04:00am*

“Miriam!”

Kamar a mafarki ta ji ana kiranta, sunan da aka ƙara kira yasa ta buɗe idonta a cikin hasken ɗakin, har yanzu suna asibitin nan, idonta yaci gaba da yawatawa a cikin ɗakin, kafin suka sauƙa akan Tafida dake riƙe da hannunta, ɗayan hannun nasa kuma yana shafa sumarta data baje akan pillown da take kwance.

Duk abinda ya faru jiya ya dawo mata sabo, ta tuna yanda bayan ya mata wannan abun ta nemi ciwon ta rasa, bayan nan kuma ya samu waje ya zauna a ɗakin yana gadinta.

Amma kuma ba'a ɗakin ya kwana ba, dan ta farka cikin dare taga baya ɗakin.

Kuma sau biyu tana farkawa bayan nan, duka bata ganinsa a ɗakin, sai yaunzu da yake tashinta. Ƙwayar idonsa taga ta sauya zuwa ja, hakan yasa ta kauda nata idon daga cikin nasa.

“Ki tashi ki yi sallah...”

Kanta kawai ta gyaɗa masa, tana jira taga ya fita daga ɗakin ta koma baccinta, dan fashin sallah take, amma sai taga ya samu kujerar dake ɗakin ya zauna yana kallonta.

Maryam ta kasa ko motsi, duk da ciwon da take jinsa babu, saide wuyanta dake mata ciwon shima kaɗan.

Tafida yaci gaba da kallonta da shanyayyun idanuwansu, dan bacci yake ji sosai, jiya bayan ya tabbatar da ta yi bacci ya gyara mata kwanciya haɗi da mata kiss a goshi, sannan ya fice, ya tafi can saman rufin asibitin ya yi jinyar kansa, dan duka ciwon jikinta baƙin ruhin nan ya shanye, sannan kuma yake sakar masa a nasa jikinsa.

Be damuba, inde har Miriam ɗinsa zata samu sauƙi, burinsa shine samun sauƙinta, ko da kuwa shi zai cutu, ganin an shafe kusan minti goma sha ba tare da ta tashi ba yasa ya gyara zamansa da kyau yana kallonta.

“Ko ba zaki iya tashi ba ?”

Maryam ta girgiza masa kai

“Zan iya mana...”

Tun jiya sai yanzu muryarta ta fito, kwata-kwata ta rasa magana jiya sbd azaba, dan ji take kamar idan ta yi maganar wani ƙashi zai karye a wuyanta.

“To ki tashi mana“

“Umhm, zan tashi ai“

Sai kuma ya koma ya jingina da jikin kujerar yana ci gaba da kallonta,wani tunani ya haska a cikin kansa, dan haka kawai sai ya yi shiru, ya lumshe idonsa dan yana buƙatar komawa bacci.

Maryam ta ɗan juyo ta kalleshi jin ya yi shiru, sai ta ga kamar bacci ma yake, idanunsa a rufe, ga yanda numfashinsa ke fita a hankali.

Sai ta samu kanta da kasa dena kallonsa, ya ƙara ƙiba a kan yanda ta san shi da, dan yanzu har ɗan wani kumatu ta ga ya yi, kamar yanda ta saba ganinsa, yauma sanye yake cikin ƙananun kaya, wani plane brown yadi ne a jikin nasa, kansa babu hula, dan yanzu ta lura da baya saka hula sosai, wata ƙila sbd gashin da ya tara ne, dan yanzu ma gashin ya sauƙo masa, daga gaba a kan goshinsa, daga gefe a kan kunnuwansa, daga baya kuma a kan wuyansa.

Hannunsa na dama ɗore a kan cikinsa, wannan stamped bracelet ɗin ɗaure a hannunsa kamar kullum, rubutun dake jiki an rubuta shi da manyan baƙi 'TAFEEDAH', shine abinda aka rubuta ɗin, idonta ya kai kan ƙafarsa, wannan baƙin zaren da ta lura baya rabo da shi ɗaure a ƙafarsa ta dama.

Sai kuma idanuwanta suka yi sama zuwa kan fuskarsa, taci gaba da kallon yanda fuskar tasa ta yi yayin da yake baccin, kamar wani baby me jan kumatu haka ya koma.

Sai taji inama su dawwama a haka, yana baccinsa yayin da ita take kallonsa.


HARIS POV.

“Iza ana bi kun zaujek, la takriji min hun!”

(inde har nine mijnki, kada ki fita daga nan!)

Haris ke maganar cikin wani iko, yana kallon Hanam, wadda ta juya zata fita daga falon Abba.

Hanam ta rintse idonta, tare da juyowa, Yau ake kwana bakwai da rasuwar Abba, kuma tana zaune a ɗakinta na gidansu ita da su Falaƙ, wayar Haris ɗin ta sameta, yace tazo falon Abba yana san ganinta, shine ta sa'ba hijabinta ta nufi falon, tana shiga falon idonta ya sauƙa a kan mutanen dake falon, gaba ɗaya 'yan uwanta wanda suke uba ɗaya ne, matan babanta guda biyu, Baba kakansu da kuma ƙannen Abba, a takaice de duka 'yan uwanta akwaisu a falon, saide ba wannan bane abinda yasa ta yi yunƙurin fita ba, Massarat da ta gani ita da yaranta uku ne yasa ta juya.

Ta zuba idonta a kan Haris wanda ya haɗe girar sama da ta kasa.

“Ki dawo ki zauna”

Yanda yake mata maganar cikin iko yasa ta haɗiye wani abu, bazata iya masa musu ba, dan haka ta dawo a hankali ta zauna a kusa da shi, domin shi a ƙasa kan carpet yake zaune.

Babane ya soma magana, ya yi musu nasiha da kuma ta'aziyya, kafin ya kawo musu maganar yanda gidan zaici gaba da tafiya bayan rasuwar Abba, sun yanke cewa Kamal ne zai ci gaba da kula da Hakuɗau group of industries, tunda shine babba, kuma Baba ya umarce shi da ya yi aure.

Daga nan ya shiga ƙoƙarin sallamar su, amma sai Haris yace aa kowa ya zauna, suka zauna ɗin suna binsa da kallo dan jin abinda zai faɗi, Hanam ya kalla sannan ya kalli Masarrat.

“Hanam, atazri min immik, Ki nemi yafiyar mahaifiyar ki”

Ya faɗi cikin harshe biyu, Hanam ta kalleshi sannan ta kalli Masarrat ɗin, wadda a cikin kwanaki ukun ta rame, sai ido ga fuskarta jawur da ita, Haris ya bawa kowa mamaki, musamman ma Baba, dan wannan shine abinda ya kamata ace ya yi tun farko.

“Ba kiji bane, nace ki nemi yafiyarta!”

Bata ce komai ba, sai kallonsa da take, bisa ga dukkan alamu baisan abinda matar nan ta mata bane, amma babu komai zata zauna ta bashi labari dalla-dalla, kuma tana da tabbacin zai goyi bayanta idan har ya ji abinda Masarrat ɗin ta mata.

“Masima'ati ? (Bakiji bane ?), Kome zata miki tana nan a mahaifiyar ki, koda zata ɗauko wuƙa tana yankar naman jikinki, bazata tab'a canjawa daga wannan matsayin ba, kisani idan fa har tana fishi da ke to Allah ma fishi yake da ke, kuma duk abinda zata miki ke baki isa kin yi fishi da ita ba, sai de ma ke ki bata haƙuri, ba dan ni ba, ba dan na isa ba, ki bata haƙuri”

Maganar ta doketa, bama ita kaɗai ba, harma da kowa dake wurin, nan take ta fara hawaye, babu abinda ya faɗa wanda yake ba dai-dai ba, dan haka ta ɗago da kanta tana sharar hawaye, ta kalli Masarrat wadda take a tsallakenta, sannan tace.

“Ana asfe immi, bitmanna inik tisamihini”

(ina me baki hakuri Mamana, kuma ina fatan zaki yafemin).

Masarrat ta fashe da kuka ta miƙe tsaye ta ƙaraso kusa da 'yarta ta rungumeta, Hanam ta saki wani kuka a lokacin da tajita a jikin mahaifiyar ta, haƙiƙa ɗumin uwa da ban yake, ashe haka Arya yake ji a duk sanda yake hannunta ?, da ace tana samun irin wannan ɗumin to da duk wata damuwa ta duniya bazata dameta ba, me yasa Masarrat ta rabata da wannan ɗumin ?, me yasa ta nisance ta ?.

“Ana yalli rah uɗulubu samah minnik ya binti, anal galɗane”

(nice zan nemi yafiyarki 'yata, nice me laifi)

Ta faɗi a lokacin da ta saketa, Hanam ta girgiza mata kai.

“A'a immi, baki da lefi, Allah ya yafe mana”

Kowa saida ya share ƙwalla, dan tsabar tausayi, Masarrat tabi kishiyoyinta ɗaya bayan ɗaya tana neman yafiyarsu, haka ma Baba, kuma duka sun yafe mata, su Mero ma sun nemi yafiyar Hanam, itama kuma tace ta yafe musu.

“Ya walad ta'al ila hina”

(kai yaro, zo nan)

Hanam ta faɗi tana kallon ƙanenenta, gaba ɗayan su suka taso zuwa wajenta, ta rungumesu tana kuka kafin ta sake su tana kallon su.

“Shu ismiki inti ?”

(menene sunan ki?)

Macen me tsananin kamarta ta tambaya, yarinyar na kallonta tace.

“Salwa”

“Wa inti ? (kai kuma fa?)”

Ta tambayi babban.

“Ana Al'amin”

“Wa ana Khalil”

Ƙaramin ya amsa mata tun kafin ta tambaya.

“Wa ana bi kun...”

(ni kuma suna....)

“....Hanam”

yaran suka katseta a tare, ta yi dariya cikin kuka tana shafa kansu, ɗaya bayan ɗaya tabi ta sumbaci kawunansu.

“Ammi ƙalat na inik uktina”

(Ammi ta fada mana ke yayarmu ce)

Macen me zaƙin murya ta faɗi, Haman ta gyaɗa musu kai.

“Ana ukutukuml kabira”

(Ni yayar ku ce)

“Haz bi kun ibnik ?”

(Wannan ɗan ki ne?)

Al'amin ya tambaya yana nuna mata Arya dake hannun Rafi'a, Hanam ta kalli wurin da yake nunawa, Arya sai sabgar gabansa yake, tunda Abba ya rasu bata ƙara ɗaukarsa ba, jiya ba ma ta ganshi ba kwata-kwata, sai yau ta ganshi a wurin maman Uchenna da ta zo ta mata ta'aziyya, kuma Uchennan ya faɗa mata cewar Arya ɗin yana wurin maman tasa ne, sai ta juyo ta kallesu tare da gyaɗa musu kai.

“Bishbahani mu ?”

(Yana kama da ni ko?)

Khalil ya dungurewa Salwa kai.

“La, huwa bishbahani ili”

(a'a dani yake kama)

“Ya kazzab kras wulaik, huwa ibni wa bishbahani ili mu intim”

(kai taron makaryata kumana shiru, wannan fa ɗana ne, dani yake kama ba ku ba).

Cewar Al'amin, Hanam ta yi dariya, dan musun nasu ya bata dariya, irin wannan farin cikin take buƙata, ta daɗe tana nemansa kuma bata samu ba sai bayan rasuwar Abba, inama a ce yana raye, ya ganta cikin yan uwanta, tana dariya da raha, sai kuma ƙunci ya mamaye fuskarta, a cikin zuciyata ta ƙara nemawa Abba rahamar Allah.

Ɗaya bayan ɗaya aka shiga watsewa daga falon, bayan da su Al'amin suka gama musun su akan da wa Arya yake kama a cikin su, Kuma har suka fice musun bai ƙare ba, dan Arya ɗinma a hannun Salwa yake.

Ya rage daga Haris sai ita sai Baba, Baba ya shigayiwa Haris godiya akan yanda ya haɗa kan iyalin ɗan nasa, kafin shima ya tashi ya fice.

Hanam taci gaba da kallon Haris, wani abu na yawatawa a kanta, wai me Abba yace mata ne ?, cewa ya yi bai tab'a zab'a mata abunda yake mara kyau a gareta ba, yanzu gashi tana gani.

 Wannan ɗin da Abba ya aura mata shine ya zama silar shiryawarta da mahaifiyar ta, da 'yan uwanta ma baki ɗaya. Shima ɗin juyowa ya yi ya kalleta, Hanam ta saka hannunta na dama a cikin nasa.

“Nagode Harees, Allah ya biyaka abinda ka min”

Kansa ya girgiza mata sannan yace.

“Duk abinda zan yiwa Abba ban faɗi ba Bannute (baby girl), Abba ya yi min komai, ya zamemin uba a sanda nawa ya ƙini, burinsa shine yaga kan iyalansa a haɗe, kuma shine abinda yake ta ƙoƙarin yi a sanda yake da rai, amma haƙarsa bata cimma ruwa ba, ni kuma na cika masa hakan, wata ƙila ruhinsa zai samu salama”

Hanam ta kwantar da kanta a kafaɗarsa.

“Kasan me yasa muka b'ata da immi ?”

Tana jin sanda ya girgiza mata kansa dake kan nata, sai taci gaba.

“Ok zan baka labarin......”




Post a Comment

0 Comments