TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

ZURI'A DAYA PAGE 33-34

*PAGE* *33*~*34*





  *Wannan shafin na sadaukar da shine gare ku massoya na, Haske writer's Asso.fan's, Aysha Ali garkuwa fan's, sangartaciyya fan's and ZURI'A D'AYA fan's, tare da duk sauran groups d'ina, Thanks for your love and care UMMU BASHEER loves you so much*












*Ba K'aramin* tashin hankali Mom ta shiga ba tun bayan barin NUWAIRA gidan ta kasa zama sai zagaye bedroom d'in ta take, yayin da zufa kawai takeyi duk da cewar A.C a kunne yake, can dai ta d'auko wayan ta, tare da call d'in wani number.


 Ana d'auka da sauri tace" ba lafiya nace maka akwai abin da ke faruwa, yanzu kasan halin da nake ciki kuwa? Wait ina son mu had'u first ya za'ayi?"


  Can tace"okay to shikenan make sure kazo da wuri course bana son wasting of times"


 A jiye wayan tayi tare da Zama a gefen bed ta fara tunani, shekaru Ashirin da Biyu da suka wuce.



   Twenty two years ago


     Shekaru ashirin da biyu da suka shud'e


 


Mom tun bayan barin ZAINAB (Ummie) gidan hankalin ta ya kasa kwanciya ji takeyi baza ta iya hak'uri ba dan haka dole taje gidan marayu ta d'auko rainon yaro dan har ga Allah tana k'aunar yara sosai. Ranar tana zaune gurin aiki sai ga Kira ya shigo wayar ta, cikin mamaki ta d'auka ganin bak'uwar number,bayan sun gaisa ne mutumin yace mata shine ALIYU cousin d'in ZAINAB Kuma yasan duk abin da ke faruwa na barin ZAINAB gida, da sauri ta fara tambayar shi ko yasan inda take? Yace shidai gaskiya bai sani ba sai dai yasan da cewar suna tsananin buk'atar haihuwa, dan haka idan har ta amince da shi to zai kawo mata wata jaririya ta raina amma fa da sharad'in zata biya shi kud'i mai tsoka, da sauri tace ta amince domin burin ta taga ta samu abin da zata raina a matsayin abin da ta haifa. Shiyasa lokacin da ya fad'a mata ta amince da sauri, Nan ta fad'a mai su had'u a wani park inda ya same ta sannan ta mik'a mai kud'i mai tsoka ya Kuma bata yarinyan, Nan ta tambaye shi iyayen yarinyan yace ai mahaifiyar ta rasu, tace to kar ya nuna yasan komai akan hakan ita san abin da zata shirya ta fad'a, haka Koh akayi suka rabu inda Mom ta had'a wannan k'aryan cewa ta buge wata  da mota, to tun bayan lokacin basu sake had'uwa ba sai da Ummie ta dawo gidan ko da suka had'u basuyi maganar komai ba amma dai tana da number'n shi. To yanzu da NUWAIRA ta tambaye ta duk ta rikice ta rasa yanda zatayi shine ta fad'a mata sunnan wani k'auyen Dan ta rasa Ina zata ce to shine ta tuna da sunan k'auyen Maman Aliyu, Dan tasan ba yanda zatayi ta gano iyayen ta, 



 Wannan kenan




 Cigaban labari




Lokacin da suka Isa k'auyen sun rasa ta Ina zasu fara, to duk Wanda suka gani sai su dinga tambayar su ko sun San wata da ta bar gida da tsohon ciki shekaru ashirin da biyu da suka shud'e? Kowa sai suce A'a, wasu ma cewa suke amma basu da hankali, abin da ya wuce shekaru ashirin da biyu suke tambaya lalai basu da hankali.



 Ranar duk sun gaji gashi har dare basu samu ansa ba kawai KAMAL suka shiga Kano suka kwana a Hotel, washegari suka koma k'auyen.




Kusan sati d'aya suna zuwa k'auyen nan amma basu samu wani labari ba, Har sun Fara cire rai sun San da k'yar zasu samu wani labari akan iyayen ta.


 NUWAIRA ce zaune kan dakalin wani gida duk ta galabaita rabon ta da abinci tun jiya da daddare shima da k'yar KAMAL yasa ta a gaba taci, mik'o mata swan water yayi tasha, tana gama sha sai wani irin amai ya taho mata, da sauri ta farayi a gefe,



 Wata mata ce ta fito daga gidan, da ta fito taga su NUWAIRA sai taji ta tausaya ma NUWAIRA ganin yanda take amai Nan tace su shiga gidan ta su huta da alama su bak'i ne, 


Bayan sun shiga sun gaisa ne, NUWAIRA ta huta, shine matar ke tambayar su me ya kawo su k'auyen dan taga su bak'i ne,


Nan suka gaya mata abin da ya kawo su, Kuma NUWAIRA ta Bata labarin ta,


Girgiza kai tayi cikin mamakin abin da suka ce, tace"Kai gaskiya da wuya ace matar a k'auyen Nan take, kuyi hak'uri gaskiya Dan abin ya shima"



 Basu ji dad'i ba haka Nan bayan sun huta suka fito Dan tafiya har sun Kai gurin mota matar Nan ta aike wani yaro ya Kira su, da sauri suka dawo Nan take fad'a musu cewa akwai wata kakan ta tsohuwa ce zata iya sanin wani Abu akai Nan suka shiga mota ta Kai su har gidan tsohuwar nan.




 

Suna shiga suka tarar da tsohuwar nan, Nan matar ta gaishe ta, sannan Suma suka gaishe ta, matar ta fad'a ma kakan ta abin da ke tafe da su NUWAIRA, tsohuwar nan ta jinjina musu tace gaskiya ita ba tasan wata da ta bar k'auyen nan da tsohon ciki ba,


NUWAIRA kuka ta fara sosai haka KAMAL yayi ta lalashin ta, har sun fito zasu tafi tsohuwar nan ta Kira su tace musu akwai dai wata mata da tazo k'auyen da tsohon ciki har ta haihu, sai dai wancan matar ta bar gidan auren ta ne tazo Nan k'auyen har ta haihu .



Cikin tunani NUWAIRA tace to matar mai ta haifa? Sai tsohuwar tace ai 'YAN BIYU ta haifa Amma tana da wani cousin shine ya raba 'yan biyun ya tafi da d'aya, dan lokacin da ta haihu bata cikin hayyacin ta, bata san me ta haifa ba ganin hakan ne yasa 'dan uwa'n nata d'aukar guda d'aya, lokacin da nayi mai magana sai yace min zai Kai ma mahaifin yarinyan tunda ita matar 'yan biyu ta haifa, nace to ya bari sai ta farfad'o sai suyi magana idan ta yarda Dan ba dad'i ace mace ta haihu bata sani ba a raba ta da abin da ta haifa, sai yace min to ai baya son ta sani Dan bazata yarda ba, Nima ya rok'e ni kar infad'a mata 'yan biyu ta haifa, duk da banji dad'i ba hakan nan ya tafi da yarinyan, lokacin da matar ta farfad'o na bata yarinyan nace ita ta haifa,



Cikin tsanin mamaki duk suka kalle ta, yayin da KAMAL yace "to ita Mai ya kawo su k'auyen? "


Tsohuwar tace" ai lokacin shi Aliyu ya kawo matar gidan kakan shi ce wato mahaifiyar Maman shi, to kakan shi aminiya ta ce, dalilin da yasa da ta fara nak'uda aka Kira ni Dan a lokacin ni unguwar zoma ce"


Gaba d'aya sunyi mamaki, sai NUWAIRA tace ko zata iya tuna sunan su matar da cousin d'in ta, tace A'a baza ta tuna ba.


NUWAIRA ta d'auko wayan ta tare da shiga gallery ta fito da picture d'in Mom ta nuna ma tsohuwar tace"Iya ko kin san wannan?"


Girgiza kai tayi tace"A'a"


NUWAIRA ta fito da picture d'in Ummie tace"wannan fa ko kin San ta?"


K'ura ma picture d'in ido tayi can ta fara sallati tace"wannan ai ZAINAB CE a Ina Kika san ta?"


Cikin razana da firgici suka kale ta KAMAL yace"iya Ina Kika san wannan waya fad'a Miki sunan ta?"


Tace"ai wannan ita ce matar da nake baku labari yanzu, it's ce ZAINAB wacce ta haifa 'yan biyu, 'dan uwa'n nata ya tafi da d'aya"


Mik'ewa tsaye NUWAIRA tayi lokaci d'aya taji wani irin jiri na d'aukar ta, KAMAL ne ya rik'o ta Yana cewa" iya mene ne sunan 'dan uwa'n matar da Kika ce?"


 Iya tace" ALIYU shine sunan shi"


 Zufa ne ya wanke ma NUWAIRA fuskar ta lokaci d'aya, KAMAL cikin rud'ewa yace"kenan NUWAIRA kece yarinyan da Aliyu ya Kai ma Mom ta Raine ki a matsayin marainiya, Kuma Ummie da Daddy sune iyayen ki sannan MEENAL TWINS SISTER d'in ki ce"


Girgiza kai ta fara tana hawaye tana cewa"A'a ba zai yuwu ba,No that can't be true"


Nan tsohuwar ta tambaye su meke faruwa, suka fad'a mata komai ita ma tace tabbas haka ne Dan haka suje su tambaye Mom da Aliyu sune zasu tabattar musu da ko su waye iyayen NUWAIRA,



Haka ko akayi NUWAIRA da KAMAL suka d'auki hanyar komawa Abuja, 


*Toh fa kenan NUWAIRA da MEENAL TWINS SISTER ne? Ku biyo ni muje dan sanin gaskiyan zancen*

  *Shin idan da gaske ne Kuna ganin NUWAIRA zata so MEENAL?*



  *Idan da gaske ne meyasa ALIYU ya aikata haka?*


  *To ya zata kasance kenan?*


 


Post a Comment

0 Comments