TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

ZURI'A DAYA PAGE 19-20

 *PAGE* *19*~*20*










 *Ganin* shi nayi yayi parking cikin wani madaidaicin gida.hankalin shi a tashe yake gaba d'aya. parlour'n gidan ya shiga cikin tashin hankali, wata mata ce zaune a kujera tayi tagumi da hannun ta, Jin an shigo ba tare da sallama ba yasa ta d'ago kai da sauri,


KAMAL ne ya k'arasa gurin ta ya zauna ya dafe kan shi da hannu biyu yayin da yake girgiza kan shi, cikin mamakin abin da ya same shi tace" lafiyan ka kuwa ka shigo ba ko sallama, meke damun ka ne kayi min magana man?"


D'agowa yayi idon shi jajazur yace"Mama ban san me zan ce ba, ban san laifin da na aikata ba aka sallame ni a aiki ba" ya k'are cikin fuskar tausayi.


Ba K'aramin tashin hankali ita ma ta shiga ba Jin abin da d'an ta fad'a tace" innalillahi wa'ina illaihir-raji'un ka dinga mai-maita wannan kalmar zakaji sanyi a ranka Kuma Allah ubanghiji yasa kasa mu aikin da yafi maka alkhairi" 


Yace"Ameen" 


Haka ta dinga mai nasiha da yarda da k'adara Mai kyau da Mara kyau. 


Can yaji wayan shi na ringing d'auka yayi ganin bak'uwar number. 


Yana d'agawa abin da yaji shine" nasan kayi mamakin sallaman ka aiki da akayi to wannan k'adan daga cikin aiki na kenan idan ka shigo gona ta"


Cikin rashin fahimta yace" Kai wane ne menayi maka a rayuwa da zaka sa a sallame ni daga gurin aiki na?"


Dariya yayi can yayi shiru cikin Isa da tak'ama yace"  yaro bai san wuta ba sai ya taka, to nine ABBA kakan NUWAIRA, kazo office na ka same ni yanzu muyi magana ko in tarwatsa rayuwar ka" ya k'ara dariya tare da kashe wayan.


Ba abun mamaki bane dan yasa anyi mai haka yasan zai iya mai fiye da hakan ma, Nan ya shiga mota ya nufi office d'in ABBA.


Yana zaune a kujera sai juyi yakeyi, shiga KAMAL yayi ya zauna kujeren da ke kallon na ABBA, yace"gani nazo nasan maganar ka ba zai wuce kan kud'in Nan ba dai"


Dariya Abba yayi can ya d'aure fuska yace" daga yau ina son ka rabu da NUWAIRA ko kaga tashin hankalin da baka tab'a gani ba a rayuwar ka, zan tarwatsa *ZURI'AR* ka in tozar ta su idan har baka rabu da ita ba Kuma duk inda zaka shiga sai ka shiga ka biya ni kud'in da mahaifin ka ya gudu min da shi kai bari in nuna maka wani abu ma" kunna laptop yayi ya nuna ma KAMAL. wa zai gani k'anin shine cikin uniform an d'aure Mai baki da hannun shi, wani k'aton mutum ya cire mai abin da aka rufe mai baki da sauri yaron ya kalla laptop d'in course suna ganin junan su cikin kuka yaron yace" Yaya Yaya kazo ka tafi da ni zasu kashe ni pl......." maganar ne ta katse lokacin da mutumin Nan ya rufe Mai baki yaron ko sai turjewa yakeyi,


Cikin tashin hankali yace" zan zo  Jamil in tafi da Kai karkayi kuka ba abin da zai same ka" 


Abba ne ya rufe laptop d'in Yana cewa" k'adan daga cikin aiki na kenan, kafin gobe zaka kaga wani abin Kuma idan har baka rabu da NUWAIRA ba"


Kallon Abba yayi idon shi jajazur yace"kar ayi mai komai ku sake shi, ko da NUWAIRA ita ce autar mata to har abada na rabu da ita daga Rana iri na yau" cikin zafi ya k'are maganar.


Dariya Abba yayi yace" hakan kad'ai zai sa ka samu kwanciyar hankali"


Mik'ewa tsaye yayi yace" kasa su sake shi yanzu, ni Kuma na bar NUWAIRA"


Dariyan mugunta yayi ya d'auki waya yasa aka maida Jamil makarantar shi Dan dama daga can akayi kidnapping d'in shi.


Cikin bak'in ciki KAMAL ya bar gurin Yana zuwa makaranta ya d'auki Jamil suka dawo gida. Mama ta shiga tashin hankali lokacin da ta gansu Nan ta fara tambayar Mai ya faru. KAMAL bai b'oye mata komai ba ya fad'a mata. ko k'adan bataji dad'i ba haka dai tayi mai nasiha tace Kuma su barshi da Allah Kuma tace ya fita harkar NUWAIRA tunda zasu iya yin musu komai a kanta, zuciyar shi haka yake mai zafi da rad'ad'i na rashin massoyiyar shi.




**********************






Kafin Daddy ya fad'a ma Mom maganar auren shi da Ummie har Abba ya gaya mata Kuma yace kar ta yarda. aiko ranar ta shiga tashin hankali, lokacin da Daddy ya dawo aiki da massifa ta tare shi, tun Yana bata hak'uri har ranshi ya b'aci sukayi fad'a sosai ya Kuma tabattar mata da cewa sai anyi auren ko ba da yardan ta ba, haka tayi ta kuka tsabar bak'in ciki da kishi.



MEENAL taji dad'in yanda za'ayi auren dan zata cigaba da rayuwa da Ummie'n ta guri d'aya, NUWAIRA ko bata damu ba tunda Babu mai k'aunar ta to ita ma bata k'aunar su Dan damuwar ta ne a gaban ta su k'ara ta can. a cewar ta kenan.




 A yau ne FAWAS ya shirya cikin riga red and black jeans yayi kyau sosai, direct gidan su MEENAL ya nufa. yana zuwa ya Kira ta a waya da k'yar ta d'auka tace mai tana zuwa. dama tana sanye cikin gown d'in material light purple, gyale kawai tasa black ta d'an fesa perform.



Tun daga nesa ta hango shi yayi mata kyau sosai, k'arasawa tayi. murmushi yayi mata mai sanyaya zuciya,



Gaishe shi ta fara yi sannan gurin ya d'auki shiru can yace"MEENAL nazo ne inji amsan ki, ina fatan kinyi tunani?"


Da k'yar ta iya cewa" tohm da farko ina Mai baka hak'uri akan abin da zan fad'a ma, wato a gaskiya bana son in yaudare ka ko in ci amanar ka, FAWAS ina da Wanda nake so, zuciya ta tajima da son shi, ina rok'on kayi hak'uri ka manta dani ka cire soyayyar da kake min Dan Allah"


Wani irin sarawa kan shi yayi ji yayi bazai iya cigaba da tsayuwa ba sai da ya dafe mota wasu irin hawaye ne suka zubo mai masu zafin gaske, MEENAL lokaci d'aya taji wani irin tausayin shi ya kamata ina ma ace ana iya controlling d'in zuciya da tayi controlling d'in zuciyar ta da ta so FAWAS dan dashi ta Dace ba KAMAL ba.


Kneeling yayi a gaban ta ya had'a hannun shi guri d'aya irin mai neman alfarman Nan yace" MEENAL ki taimake ni ki amince da soyayya na gare ki, bazan iya rayuwa Babu ke ba, zuciya na yana min wani irin zafi ki taimake ni kar kice ba Kya so na Dan Allah MEENAL na rok'e ki" ya fashe da kuka, (wallahi Nima sai da nayi hawaye).


Cikin hawaye tace" kayi hak'uri please" da gudu ta bar gurin tana kuka.


FAWAS ya jima a gurin kafin ya iya tashi da k'yar yayi driving zuwa gida, motar ai ko parking da kyau baiyi ba ya shiga parlour,


Mommy na Kitchen taji an shigo, tana fitowa taga FAWAS cikin wani irin yanayi na ban tausayi, da sauri ta k'arasa gurin, d'ago kanshi tayi tana tambayar shi meke damun shi, wani irin kuka ya fashe da shi kamar k'aramin yaro ya rungume ta, da k'yar ya iya yin magana yace" Bata so na, why why Mommy? ina son ta amma bata sona"


Cike da tausayin shi tace" oh my God who is she? wace ce ita FAWAS, shin akwai macen da zata kalle ka tace bata son ka?, tell me wace ce ita ni Kuma nayi *ALK'AWARI* (my novel) sai na San duk yanda zanyi ka aure ta gaya min wace ce?"


Murmushi yayi cikin hawaye yace"no Mommy I want her to love me, ba wai muyi aure tana son wani ba, Mommy zuciya na nayin min zafi" ya d'aura hannun ta a zuciyar shi, bata San lokacin da wasu hawaye suka zubo mata ba cikin tausayin d'an nata Kuma tayi *ALK'AWARI* duk ranar da ta gano wace yake so zata aura mai ko 'yar wace ce kuwa Dan samun farin cikin d'an nata,


Da k'yar ya iya tashi ta rakashi har bedroom d'in shi, sai da taga barci ya d'auke shi sannan ta fita,






MEENAL tana shiga gida ta fad'a kan bed tana wani irin kuka, gaba d'aya duniyar wani iri take Jin ta,






A kwana a tashi ba wuya, Allah ya kawo mu lokacin d'aurin auren su Daddy, 


Ranar asabar da missalin k'arfe 2:00pm mutane suka shaida d'aurin auren *ZAINAB* (Ummie) da *NASIR*(Daddy) akan sadaki mafi daraja, ranar duk kowa na farin ciki, banda su Mom da zuciyarta ta cika da kishi Kuma tayi tanadin zuwan Ummie, yayin da Ummie ke cikin farin ciki at least zata k'ara rayuwa da massoyin ta a karo na biyu, Kuma ta shirya yin hak'uri da duk abinda Mom zatayi mata Dan wata rana sai labari,



An kawo Ummie gidan Daddy, inda taro ya watse,


Bayan sati biyu da yin auren,


Mom batayi komai ba a wannan lokacin Dan ta samu musu ido ne Kuma ta Kuma basu time,


MEENAL na tashin hankali tana tuna Sam abin da tayi ma FAWAS bai Dace ba, haka Kuma tana tunanin KAMAL Wanda bai San ma tana son shi ba,


Yayin da NUWAIRA ke cinyar rashin massoyin ta dan gaba d'aya ta rasa shi, sun daina had'uwa,




FAWAS da KAMAL duk suna fama da rashin masoyiyyar su, 



KAMAL rayuwan shi ya canza suna buk'atar taimako Kuma yak'i nuna ma KAMAL cewa akwai abin da ke damun shi,Dan baya son ya sani,


FAWAS dai yayi k'okarin ganin ya manta da MEENAL sai dai ina kamar k'ara mishi son ta akeyi a zuciyar shi,


Zaune suke suna hira jefi-jefi dan kowa da abin da ke damun shi, FAWAS da KAMAL kenan aminan juna.




Post a Comment

0 Comments